Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
yayi ya tadda Mami da Abban shi suna breakfast , shima zama yayi yace."Good morning my parent." "Good morning too, how are you."!? "Am fine Abba, Abba imiss you tooo." Murmushi Alhaji Mubarak yayi sannan yace."miss you tooo Son, but fatan lafiya naga kwana biyu bamu haduwa sosai."!? Murmushi yayi yace...."Lafiya lau Alhmdulh Abba, wallahi aiki ne yayi man yawa shiyasa bamu cika haduwa ba, yanzun ma sauri nike bansan nayi late." "Ok Allah ya bada sa'a." "Amin ya Allah Abba." Nan suka zauna suka cigaba da yin breakfast, bayan sun gama ci ya tashi, ya tafi wajen aiki, tunda ya tafi wajen aiki, kasa yin aikin yayi so yake ya koma ya ida jin labarin rayuwar Salma, dan ya matsu yaji karshen labarin nata, dan ya lura *Labarina Salma akwai rikitarwa* dan tunda ta fara bashi labarin ya kasa samun idan labarin ya kunsa, amman ai ance waka a bakin mai ita yafi dadi. Haka ya kama tunanin yana aiki, bayan ya gama cika file, ya gama rubutun shi sannan ya tashi ya tafi gidan Salma. Parking yayi a parking space din gidan sannan ya gaisa da masu gadi. Sannan ya shiga cikin gida, wajen Momy ya fara zuwa, kwance take kamar kullun ba uhmm, ba uhm uhmm, kallonta yake ji yayi hawaye nabin kuncin shi, sa hannu yayi ya share, dan sosai take bashi tausayi, ita dai ba mai rai ba kuma ba marar rai ba, kuma kullun idan Doctor yazo cewa yake yi jiki yana samun sauki, shi dai dan karka yayi sabo da yace bai ga wani sauki a jikin Momy ba, yana tsigune gabanta yaji takun takalmin Salma, kallonta yake har ta iso kusa dashi, zaunawa tayi bisa kujera sannan tace."Barrister Sannu da zuwa, ina wuni."!? Kallonta yayi sosai, dan tayi mashi kyau yau sosai, duk da ba wata kwaliya tayi ba, amman kayan jikinta sun anshe ta sosai, murmushi yayi yace."lafiya lau Salma, ya jikin Momy."!? Numfasawa tayi gami ga maida kallonta wajen Momy a sanyaye tace."To jiki Alhmdulh, ga shi nan dai." "Masha Allah,Allah ya karo sauki, Doctor yazo kenan."!? "Eh yazo dazun, ya yi mata allurai, sannan kuma ya sake duba ta, ya kuma ce man jiki ana samun cigaba." Shiru yayi na wani dan lokaci, sannan yace."niko ta fara yin wani moving ne."!? Cikin da kiya dan bata son tana yawan kuka gabanshi, cewa tayi...... "Nidai ban gani ba, dan har yanzun bata bude ido ba, balle ta daga hannu, yanda ka ganta haka, haka take, ni abun har tsoro ma yake bani Barrister."tashi yayi yana kama hannunta yana murzawa a natse yake mata maganar yanda hankalinta zai kwanta yace...."Karki damu, kedai ki cigaba da yi mata addu'a, insha Allah zata samu sauki, karki manta ko wace cuta da maganinta, insha Allah sai Momy ta samu lafiya." "Allah Amin, bari na kawo maka abincinka, yanzun na sauke shi daman." "Ok, amman kin san dai ba da yawa zanci ba dai ko."!? "Yes of course, let me go.".... "Uhmmm." Bayan ta kawo mashi abinci, itama ta samu black tea ta tasha, tashi tayi ta kama Momy taje tayi mata wanka ta shirya ta, tayi mata komai ba, sannan ta kwantar da ita, kiss tayi mata a goshi sannan tace."Allah ya baki lafiya Momy,Allah kuma ya baiya na mana Basma da Baffah."hawaye ne ta goge, duk abunda take yana tsaye yana kallonta, sai ji tayi yace."Amin ya Allah." Waigowa tayi tayi mashi smile sannan ta tashi tace "mu koma parlour ko."!? "Ok." Tunda suka zauna ta tashi ta kunna masu kallo, Tauraruwa tv ta kunna masu, sannan tace."har ka gama cin abincin."!? Daga mata kafaWa yayi, gami da gira daya, girgiza kai tayi, tana mamaki hali irin na Barrister Salim, yanzun ya bude baki ya bata ansa shine ya gagara sai dai yayi mata singing da kai gami da gira, watarana takan zauna tayi mamakin halin shi, dan yana iya zuwa wuni zungur basu yi magana ba, da ya gama tambayar ta jikin Momy shikenan, sai dai ya kama danna waya yana murmushi ka rasa mai yake yi da waya, tana cikin tunanin taji anyi mata waving da hannunshi sai yace."tunanin mai kike har haka."!? Cute baby smile tayi sannan tace."bakomai, kawai dai ina tunanin rayuwa ne, ina tsoron randa zaka ce mu tafi mu barmaka gida, bansan inda zani ba, asalima ban taba fita dai dai da kofar gate din gidan nan ba, balle nasan ya garin yobe yake, ta sanadiyarka nazo yobe,amman ai da nisa sosai tsakanin Katsina da yobe." Murtukewa yayi, sannan yace."daga yau karki kuma yi man irin wannan nonsense maganar understand."!? "Yes."tace jiki a sanyaye dan ga alamu nan sun nuna yaji haushin maganar da tayi mashi, tashi tayi taje kitchen ta dauko masu ruwa mai sanyi gami da juices din da ta hada mai, yarda cake da dononut duk ta dauko ta zauna kusa dashi, ta marairaice fuska gami da karkatar da kai gefe, tace. "Barrister am so sorry, ba zan sake ba, ga wannan kasha please sai na cigaba da baka labarin nawa." Yanda ta fara maganar da kuma gamata, sai ya nemi fushin nashi ya rasa, dan tayi mashi kyau sosai, cewa yayi."OK be careful karki kuma." Hada hannunta tayi waje daya sannan tace."insha Allah."mike mashi juices din tayi itama ta zuba, shi dai ba wani sha yake ba, dan ya kosa ta cigaba da bashi labarin, fahimta da tayi da hakan ajiye cup din hannunta tayi bisa center table din dake gabansu sannan ta cigaba da cewa...... ?%??%??%??%??%??%??%??%??%? "Bayan mun dawo da sati d'aya zaune muke a corner nida Basma, shiru mukayi mu duka biyun ba abunda muke tunani sai Momy, dan munsan mun baro ta cikin wani yanayi, matar Baba Mala da shi kanshi Baba Mala din ba dadin zaman muke yi dasu ba, dan tun muna yara muka lura ba san Momy suke ba, balle yanzun da hankali ya fara zama jikinmu, kallon Basma nayi sannan nace."nifa Basma har yanzun hankali ya kasa kwanciya, ina ta tunanin halin da nabar Momy fa." Kallona tayi sannan tace."wallahi Salma ji nike kamar nayi siliking naje gida naga halin da take ciki, tunda naga Baffah ba yarda yake da abunda muke gaya mashi ba akansu, dan ni gani nike yafi sonsu akan mu, kiji fa abunda yayi maki randa kukayi fada da Dahira, kuma kece keda gaskiya amman Baffah ya rufe ido yana ta yi mana fada at the end har bugunki yayi fa Salma." Shiru nayi ina tunanin maganar Basma, kallonta nayi nace."Aa Basma kibar yin maganar zakiyi siliking, kinga za'a bada shadows sai ayi tunanin tsoro ne ya saki kikayi siliking, nidai abunda naga yafi shine gobe muje wajen Malam Aliyu mai kudi ya kira mana Momy muji lafiyarta, amman ya kika gani."!? "Hakan ma yayi, dan ni ban taSa dawowa dai dai sai nayi waya da Momy naji lafiyarta." Washe gari bayan munje class, anayin breakfast muka wuce wajen Malan Aliyu, muka taibaye shi waya aiko munci sa'a ko gardama bai yi mana ba, ya bamu, number din Momy mukasa, s mukayi darling tana dauka muka ce ta kira mune, bayan ta kira mukayi waya da ita, bayan mun gama gaisawa muka tambaye lafiya, ce mana tayi lafiya lau, komai na tafiya dai dai, ashe boye mana tayi dan kawai ta kwantar mana da hankali muyi karatu, amman ko babu dadi zaman da su Baba Mala, munji dadi da tace tana lafiya haka mukayi sallama da ita muka koma class cikin farinciki,bayan an gama yin lesson muka koma hostel, da yake gobe ake bada shadows ko wace yarinya a G.G. Sandamu jininta ya dawo bisa hakaifa, wanda bata da roba da kofi taje ta saya, idan kasan baka da abunda kasan za'a taSa lafiyar jikinka kaje ka sawo, muda bamu da yaya bamu san ya zamuyi ba, wajen zuwa Wabo ruwa da yi ma kanmu wanki, haka muka shiga cikin damuwa sosai, dan ranar Basma wuni tayi kuka, nice mai bata hakuri, da dare yayi mukaje mono muka ciko da botikanmu dukansu harda su jarkar oki mu sandamu muna cema mata oki, wasu makarantun kuma suna ce nata tasko da 25, har da bokitin fanti babba muke dashi guda uku, muna kiranshi da diram haka muka ciko su muka boye, mukayi hadi da komai abunda mukasan ya dace. Washe gari munaka tashi da shirin cin ubanmu dan yau ake bada shadows...... *Muje zuw.....=ؤ?* *Yar'mutan kankia ce c'?* Share pls=?O? *BANSAN INDA SUKE BA* _A HALIN YANZUN_ *NA* *Jameelah Jameey* *Yar'mutan kankia cec'?* *MANAZARTA* *WRITERS ASSOC* *BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM* *SURPRISE PAGE, dan naji dadin comment dinku yasa na baku two page yau=??d'?* *Chapter ten and elevent?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n daya na dare sannan muka gama karatun qur'ani mai girma mukayi sannan muka tashi muka kwanta lokacin biyu tayi ,sannan muka rintsa. Kwantawa mukayi ,Amman ni maganar gaskiya bacci ya kaurace ma idona,dan dana kulle ido ba abunda nike hango wa sai Baba Mala da yake ce mana sai yayi maganinmu daga mu har iyayanmu,tuna sanda suka dawo gidan mu nike yanda Momy tace mana shima Baffahnmu ne Kamar yanda Baffah Hussaini yake Baffahnmu shima Baba Mala Baffahnmu ne,Amman gashi da bakinshi yana cemana sai ya ga bayanmu harda ma Baffahn namu ina cikin tunani na ina juyi na naga Basma ta tashi ta shiga toilet ta fito,kallo na tayi sannan ta kwanta ,haka mukai ta juye juye daga ni har ita har aka kira sallahr asuba,lokaci daya muka tashi a tare kallonta nayi gami da yi mata murmushi,itama murmurshin tayi man,dan Musan ba Wanda yayi bacci kenan cikin mu ,tunda muka tashi sallah ba tare da Momy tazo ta tadamu ba. Nashiga toilet dan yin alwallah Momy ta shigo kallon Basma tayi kawai ta juya dan tasan itama ba muyi bacci ba kenan,dan da munyi bacci sai tasha fama sosai wajen tadamu yin sallah. Koda na fito sallah na tada na cigaba da yi,itama Basma tana fitowa ta cigaba da yin sallah muna gama mukayi azkar sannan muka yi wanka muka shiga kitchen dan samun abunda zamu garki a gidan. Tunda muka shigo kitchen Momy take mana wani kallo nice nayi karfin halin cewa."Momy ina Kwana."!?....ko kallona batayi ba balle na samu arziki ansawa cigaba da yin aikin gabanta tayi, bayan ba haka mukeyi ba idan muka dawo hutu to bata sake yin aikin komai mu zamuyi,Amman yau tun kafin mu shigo Momy har ta kusa gama hada breakfast ,Basma ma cewa tayi."Momynmu ina Kwana"!?....tsaki kawai Momy tayi ta barmana kitchen din ta ficewarta,kallona Basma tayi tace."Salma kinga fa?wata Sabuwa kenan yau Momy bata ansa gaisuwarmu.".ta ida maganar cikin damuwa tsantsa a fuskantar,nima kallonta nayi cikin damuwa nace."Basma banga laifin Momy ba dan bata ansa gaisuwarmu ba,ko kin manta abunda Baffah yace mana jiya?duk da Momy bata parlour nasan taji mu,Kuma Nasan kafin su kwanta jiya sai yayi mata fada sosai,ke Basma ba zan mace fada ba warning kawai zance yayi mata, dan muma ba warning din yayi mana ba kan Mala ba,wanda basu hada komai da Mala ba sai zaman unguwa."!? "Eh hakane Salma jiya Baffah warning yayi mana,Amman Baffah ya bani mamaki Salma kyau ace yayi bincike kafin ya yanke hukunci Allah sarki Momy,mun ja mata." Ta ida maganar tana hawaye, dan Basma kuka bai yi mata wahala, hawayen nike goge mata ina cewa....."To ya zamuyi Basma kawai idan mun gama aiki mu ba Momy hakuri kuma karmu sake gaya ma Baffah duk abunda ake mana a gidan nan." "Hakane ko Salma kin kawo shawara mai kyau." Haka muka kama yin aiki jiki duk a sanyaye,dan da na tuna yanda Momy tayi mana a kitchen sai naji duk banda lafiya dan bani san abunda zai bata rain Momy,bayan mun gama mopping da komai muka sake yin wanka sannan muka fito yin breakfast,haka kowa yayi breakfast fuska a jagule dan koda muka gaida Baffah a daure ya ansa shi ma fushin yake damu ,bayan mun gama breakfast kafin ya tafi muka bashi hakuri,da yake Baffah yana sonmu sosai bai iya fushi damu mai tsawo ,shiyasa ya fe mana sannan yayi mana tsakani da Mala yace karmu sake shiga harkarshi inba haka ba si yasan abunda zaiyi mana,koda zai fita ko kallon inda Momy take baiyi ba ,balle yace mata sai ya dawo har tayi mashi rakiya Kamar yanda muka taso mukaga suna yi,sai mu muka yi mashi rakiya a ranar ,nan muka hadu da Mala a compound yana motsa jiki,daman shi Mala bai zuwa ko ina tun daga cin shi da sha harda sutura ma Baffah yake yi mai,har makka sai da Baffah yakai Mala,sannan ya siya mashi mota,gaidashi mukayi abun mamaki ya ansa sosai harda tsokanarmu a gaban Baffah,shi kuma Baffah dadi yake

Chapter 3 of 5