Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bansan mizance mashi ba.
Kuka ne yaci karfina har ina hade numfashi raina ba dadi komai ya gama dagule mani narasa amsar da zan bashi.

U re very stupid ina tambayar ki waye shi kina mani kuka,are u in ur sense.?"

Zuciya ta tagama tsinke mani tsoro ya gama kamani nace.
"Bansan shiba.?"
"Miya hada wayar ki dashi.?"
"Na yarda wayar ne,i don't know anything about him."

"Look Minal idan kika bari na gano truth din maganar nan,wlh saina baki mamaki,kin amince.?"
Eh na amince."
Nafada will full confidence duk da nasan karya nike,amman narasa dalilin dayasa nakasa fadar gaskia akan abinda ke faruwa nida JJ miyasa zan yaudari kaina bayan nasamu wanda zai kawo mani dauki why zan hidden ma Ya Taufiq wannan issue din bayan yai trusting dina mi wannan case din zai janyo mani a wajen mutanen da suka yarda dani?.
Kuka na saki Fatash ke bani baki duk ta shiga damuwa.


"Ki daina kuka insha Allah Ya Taufiq zai dauki mataki akan wannan mutumin nasan zaisa agano mashi shi,wannan ai rubbish ne akan mi zai tsinci wayar ki kuma yana cewa wai mijinki ne,amman wanda naganki dashi a resturant waye shi.?"

"Yayan Maryam wai sona yake shine na bashi hakuri dan Allah kibar wannan zancen Fatash."
Okay shikenan."
Da haka tabar zancen saidai zuciya ta, ta tsinke bansan wane kalar bincike Ya Taufiq zaiba.


Bayan kwana biyu naje Class kana ganina kasan ina cikin mawuyacin hali banda kallan tara saura kwata ba abinda su Maryam ke jifana dashi tinda suka ganni nida JJ sai nafara samun sauyi ga Course Mate dina a sirace nike domin kuwa nasan banda gaskia,a wannan karan ko magana na gazayi.

Sanda goma zatayi Dr JJ ya shigo mana ba wani Lecture yai ba kawai Revision yai mana,ya fita wani kallo yai mani yana daga wayata a hannun shi.

"Nasan manufar shi,ana tashi nasa Humaira tarakani office din shi,da sallama abakina muka shiga, da kallo ya rakamu shiru nayi shima baice komai ba.
Kiran Humaira akai waya hakan yasa ta fita kamar jira ya maida kallon shi kaina yace.

"Wayarki,da kika bari shine na kawo maki,amman ba zan bakiba wani Yayan ki yace yau zaizo karba,da kanshi waye shidin.?"
Gabana ya fadi nace.
"Wana ne,mikace mashi.?"
"Matata mana mi zance mashi da yawuce wannan.
Gabana na duka da sauri da sauri nace in yazo mi zakace mashi.?"

Tunda yayan kine zance tsintar wayar nayi,in fact kawai dai ni nasan mizance mashi ki kwantar da hankalin ki."

Uhummm kawai nace.

Albishirin ki."
Wani bakin cikine ya tokareni wai albishiri na,inama inada hali dana kashe JJ na tsane shi har cikin zuciya ta.
"Beauty albishirin ki.?"
Goro fari ko ja.?"
Fari."nace raina dagule.

Naje Caranci munyi magana da Baba kuma yace intura iyayena ayi maganar aurenmu re you happy.?"

Zaro idanuna nayi zuciya ta na bugawa da sauri da sauri girgiza kai na iya dan bansan mi zance ba.
Shima basarwa yayi yace.
"Nasan idan yayanki ya kawo maki wayarki zakuyi magana da Baba,u can go."

Raina yagama baci rai bace nahau masifa nace.
Haba JJ miyasa zakaimin haka ai saika gaya mani zakaje wajen Baba bawai inji har kaje ba minene haka.?"

Soyayyarki ce ke dawainiya dani wai mi kike nufi?bake kika bani dama ba so kike ki maidani na goye komi kike nufi.?"
Okay shikenan naji sai anjima."

Ina zuwa daidai kofa na kama handle zan bude naji yace.
"Love u my wife my happiness."
Fita nayi ina bugo kofar ga mamakina kusan yan Course Mate dinmu a bakin office din Dr Salim zasuyi submitting Assignment nima,zuwa nayi a cikin su na tsaya a darare kamar mujiya cikin tsuntsaye,suma kallona sukeyi nan na iske Humaira itama zatayi submitting miko mai nawa tayi.

Harkin fito.?"
Gyada mata kaina kawai na iya,duk idanu sunman yawa ga kwalla nasan zubo mani amman na dake,har na shiga kai Assignment wani kallo yake yimani nima kallan tsana nike jifar shi dashi,da ace JJ ya cimman burin shi akaina Dr Salim ne silar komai shiyasa nakara tsanar shi.
Mrs JJ how re you.?"
Kallan up and down nai mashi,amsa yayi yana murmushi yace.

"Karki damu koda baki kawo ba Automatically Kinada A a Course dina,ai kin canci abaki marks."
Juyawa nayi bance dashi komai ba domin innace zan maida mashi martani tabbas zan iya fashewa da kuka,ina fitowa Maryam na shiga nida Humaira mukatafi hall zamuyi Lecture din Dr Fatima.


"Humaira zanje daki ban lafiya."
Ayyah kawata idan mun tashi da wuri zan biyo."
Okay nagode.
Da haka na wuce daki kwantawa kawai nayi Fatash na dawowa tace.
"Minal Baba yaita kirana in baki waya nace muna Lecture bari in kira shi."

A kidime na zauna jinake kamar raina zai bar gangar jikina ko magana bata bari nayi ba ta kara mani wayar a kunne bayan tace mashi gani.


"Waye Junaid,kika turoshi neman izinin auren ki.?"
Shiru nayi ina zare idanuna atunani wasa yake mani baije ba.

Tattaro jarumtata nayi nace.
"Baba ba haka nace mashi ba,nace dai karatu zanyi kuma banda iko dakaina,shine yazo nan ban saniba."

Mamana yaushe kika fara yimani karya?"
Samun kaina nayi dajin kunyar mahaifina nasan na lalata komai da ban fadi matsalata ba nabarma raina ga abinda zurfin ciki yajawo mani.
"Aaa Baba gaskia ta kenan wlh bansan yazo ba."

Miyasa zaki fara soyayya ni mahaifin ki baki gaya mani ba?miyasa kike neman fara munafunci?ina tarbiyar da nai maki?duk ina kika barota?"

Baba kayi Hakuri.?"
Shut up Aminatu, indai aure kikeso zan maki shi wlh zan bicika wanene Junaid zan baki shi,na gamsu da maganar shi ke kikace yazo dayake kin rainani kece zakiba saurayi damar zuwa wajena kai tsaye harma yafara mani maganar aure ba neman izinin fara magana dake ba kin kyauta."
Zuciyata ba duka da sauri da sauri nafara ba Baba hakuri.
"Baba kayi hakuri dan Allah banda wani zabi shiyasa kayafe mani."


"Ni bazan fushi dake ba amman kisani ba fashi tunda nikike cema baki da zabi ashe soyayyar da kike mashi harta sakaki wannan hali da kyau."
"Baba dan Allah ba haka. nike nufi......Ɗit ya kashe wayar shi gunjin kuka na saki kamar raina zaibar gangar jikina.

Fatash batai yunkurin tambayata dalilin kuka naba,dan yanda taga nakara rikicewa da nai waya da Baba tasan ba lafiya komawa tayi ta zauna tarasa abinyi nima kukan naitayi saida akayi sallar la'asar na mike nayi wanka nai sallah Addu'a nafara ta neman mafita saida ance anbaro bida baya nacuci kaina da kaina!.



Minal Ya Taufiq yana waje yace muje."
Mikewa nayi da hijab din jikina kawai nafita tabiyo bayana har muka isa cikin mota muka shiga,kallona yai ya maida kanshi kasa yana latsa waya sai kuma yace.
"Ga wayar ki."
Amsa nayi nace nagode.
Baki da lafiya ne.?"
Ya jefo mani tambayar yana kallan mirrow alamun yana kallan Fatash.

Lafiya na lau."
Okay.
Yaka mata ace kina kula da abubuwan ki,wannan mutumin naso in kamashi but yace yai hakan ne dan ya razanaki wannan kuma ba hujja bane,kuma yabada hakuri sosai shiyasa na kyale shi wlh dasai nayi maganin shi dayayi danasin daukar maki waya!
inasan ki kula sannan ki kara maida hankali akan karatunki."
Insha Allah zan kiyaye."


"Good girl.
"Fatima Mukhtar mike damun kawarki ban yarda da itaba mi take hidden.?"
Numfashi Fatash tayi tace.
"Wlh Yaya bansa niba bata da aiki sai kuka musamman yau datayi waya da Baba i don't know mike faruwa."

"Amina Yusuf Caranci,mike damunki pls tell me.?"
Yai maganar raunane wani irin tausayin shi naji a raina,yanata bani kulawa ya maida damuwata tashi ya bata lokuta akaina ya zabeni a matsayin wadda yakeson ya aure,baitaba yimani zancen banza ba bare yai yunkurin tabani,kullin baida buri daya wuce yaga ina neman ilimi,ya maida farin cikina nashi bai boye mani komai narayuwar shi,mi yasa zan zama mai boye mashi nawa sirrin bayan nasan zai taimakeni wane sakarci nikeyi har haka miya rike mani bakina nashiga ukku ni Aminatu!.

Tunda yai mani wannan tambayar nakasa daina kallan shi,shima ni yake kallo ga tsantsar sona da tausayina a cikin kwayar idon shi,dauke kanshi yayi akaina yace.

"Baki daukeni yanda na daukeki ba ko Minal? Baki maidani dan uwanki ba,masoyin ki,abokin ki,aminin ki kamar yanda ni Hussein Mukhtar na daukeki ba,kin kyauta zaku iya tafiya.!"

Ya ida maganar yana ma matar shi key.
"Ya Taufiq kayi hakuri wlh kaine farin cikina duk wani hope dina kaine karka ce haka, dagske nike bakomai Baba ne yaimani fada na yarda waya har wani nacewa wai shi mijina ne,kaji dalilin kukana."


Jinjina kai yai yace.
Alright ni kaina naso nai maganin shi dan dai ya razana kuma yace baiso hakan ta kasance ba,shiyasa nai mashi uzuri dan Allah kidaina kuka kinji.?"
"Toh Yayana na daina."


Goge kwallan idanuna nayi, sallama yai mana muka koma hostel na bude wayata saiga text messages harda Ahmad,wai waye ya daukar mani waya yana cewa mijinane mike faruwa.
Damuwa iya damuwa yayi,text iri iri duk yai mani su.
Aje wayar nayi har Asma'u taiman text din amman ban replay ba.


Haka rayuwa ta kasance kullin kiran Baba nike ina neman afuwar shi ina kuka ko Allah zaisa ya sauko.

Mahaifina mutun ne mai saurin fushi amman yanada zuciya mai sauki saidai idan kai breaking trust din da yake maka bai kara yarda dakai komai zakayi Allah yasa masallaci kake kwana dan imani,shiyasa idan ya yarda da mutun baisan ya kamaka da rashin gaskia,nasan shiyasa yaki kulani.


Saidai inkira Mama,itake bani hakuri,nakai sati ina begging Baba da kyal ya hakura yace tunda bansan Junaid din bazai mani auren dole ba amman indai kula samari da karatu yasanni inda ina year 4 a halin yanzun.


Nida Ya Taufiq kullin son juna muke har abin yafara bani tsoro,yanda muka shaku lamarin sai addu'a gashi kowa na shakkun yanda iyayen mu zasu kara ansar maganar mu a karo na biyu.
Yau yakama Friday Fatima ce ta shirya zataje week end gida,tace inzo muje nace bazan jeba hatta Ya Tariq yaso inbita naki yarda dole suka kyaleni,Usama yazo daukar ta dakaina na rakata tafi gida ni kuma nadawo hostel ina karatu,ba laifi nasamu nutsuwa zuwa yanzun.

Ahmad ma,yakara sabawa dani nima ina bashi attention aganina da kyal idan Qaddara zata bari in auri masoyina Ya Taufiq wannan dalilin yasa nikeba Ahmad Lokacina.

A Kaduna kuwa abubuwa marassa dadi sun faru zuwan Fatash gida ta iske lamura sun cabe a gidan su musamman wajen Ya Taufiq da Abba ashe yafini shiga damuwa shidai jarumta yafini,Abban su ya nace saiya auri abokiyar aikin shi,shikuwa yaki amincewa kullin takon saka suke shida mahaifin shi akan maganar yaki amincewa lamarin yai kamari har ya yanke shawarar sama Ya Taufiq rana da yarinyar wanda iyayen ta suka nace,dayake Baban ta abokin mahaifin shine.
Mami kuwa itace uwar yan ziga tayi ruwa tayi tsaki a cikin lamarin amman duk abin nan Mum batace komai ba,hakan yasa Fatash da ya Taufiq sukaje gidan kakansu sukai karar Abba akan case din.

Alhaji Munzali dattijone mai dattako da sanin yaka mata kuma duk abinda suka tattauna akai ya fahimce su kuma yace zaima tufkar hanci da haka suka koma gida washe gari haka Fatima ta dawo makaranta batasan yanda lamarin zai kasance ba,saidai Ya Taufiq bai taba fada mani gudun kada intada hankalina shiyasa ya boye mani,koda take bani labarin hankalina ya tashi,ba abinda na iya cema ta,sai Allah ya kyauta yakawo sasanci tsakanin Ya Taufiq da Abba kuma ya tabbatar mana da alkhairi da ameen ta amsa haka muka cigaba da karatun mu,wannan kenan.


*Gaisuwar agareku masoyana ina alfahari daku akoda yaushe.*


Fatima Idris
Maman Intisar
Bontol
Maman Dr
Mufeedah
Cwt mom
Maman ihsan
Nafeesa S Ado
Maryam Usaman
Nusaiba S Muhammad
Ummu Madina
Mom Sultan
Mama n Abdullahi
Zainab BBK
Hafsat kn
Amina Abk
Amatu baiwar Allah
Sa'ada
Meenarht
Asmy
_Allah yabar so da kauna Yar Mutan Kankia na maku so dan lilllahi💕_


*Note:- masoyana ina kaunar ku, dan Allah kuyi mani uzuri duk wadda tai mani DM taga Jameey batai mata replay dan Allah tayimin afuwa ina busy dayawa shiyasa,kuma indai naga text dinki insha Allah zanyi replay,kunsan abubuwan da yawa,nagode much kauna🤍*




_Yar Mutan Kankia ce❣️_




Share
Pls
❣️



*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E37&38



Sosai nakara nisanta kaina da lamarin JJ ko tutorial daina zuwa nayi domin kananun maganganu ko zargi da Course Mate dina sukeyi mani,wannan dalilin yasa saidai inyi karatuna ni kadai indai ba mutun yazo da kanshi ba wajena ban koyama kowa karatu saboda duk sun hade mani kai.

Gobe zamu zana Jarabawar Dr JJ ina daki sai karatu nike nida Fatima mukajiyo hayaniya kamar ana dambe zance ko kuma rayoit.

"Wai mike faruwa hostel din nan ake wannan hayaniyar wlh mutane basu kyautawa kansu,ana karatun Exam suna disturbing din mutane,dan kawai ance Jami'a bashi ke nuna kai duk abinda kaga dama ba.!"

Cewar Fatash daketa faman sababi ga Course din da zatayi gobe yana wuta da yawa shiyasa ko motsi mai karfi bata son anayi.

Uhmm kawai nace, nima inaji da nawa karatun.
Ban kado dakin mu akayi,hakan yasa muka maida attention dinmu a kofar,su Maryam ne da sauran Course Mate dinmu mata sunfi su goma suka shigo kai tsaye kaina sukayo suka cakumoni suka fara dukana,bansan hawa ba bansan sauka ba.

A firgice na mike ina kare fuskata nace.
"Lafiya zaku hauni da duka mi nai maku har tsanar taku takai nan.!"

"Wato dan kin raina mana hankali bakimasan abinda kikai mana ba ko?ubanwa yace ki sabe kije wajen JJ yabaki Exam questions din da zamuyi gobe?wato muda shan karatu kedacin bulus,to yau din nan sai mun fiddaki waje munci ubanki dan bazamu lamun taba."

Kukan kura Fatash tayi ta fisgini hannun su wanda har sunfara dungurina wasu nakai mani duka.
Niko harna fara kwalla saboda bakin cikin daya tokare ni,inaji ina gani ammani kage,sharri duk lokaci daya.


"Haba bayin Allah akanmi zakuzo kuna zargin ta,kun shaida yabata Exam Question miye hadin ta dashi dahar zai bata satar amsa.?"
Ta ida maganar a fusace.

"Ke dakata mana malama kama kanki,ita tasan komai saurayin ta,koma muce kwartan tane,kuma dole......

tas tas Fatash ta wanke Maryam da mari aiko suka rufeta da duka.
kwalla ihu nayi,dandanan neighbours dinmu da yan kallo suka shigo da kyal aka kwace Fatash a hannun su,domin ta gama fusata itama dukan take kaimasu ranta a bace.

Dan uwarki yar uwata kike cema tanada kwarto wlh saina karyaki,yar iska.!"
Waje akai da Fatash sai kuka take ranta gama hassala.

Jacking din sukayi dole sai sunkaini waje gun Course Mate dinmu maza an mani duka,tunda har JJ yabani amsar Jarabawa wai su da karatu nida kwashe amsa.
Tirjewa nayi suna dukana wani in rama wani kuma insa ido,nagama yarda koma minene ni na jawa kaina danaki faɗama kowa halin da nike ciki tsakanina da Dr JJ gashi har wannan sharrin ya bullo kuma banda wata mafita.

Dakyal aka kwaceni wajen su musamman Maryam dakeji kamar ta halakani daman compatition take dani ta tsani nafita maki daidai da kwayar zarra a rayuwar ta.

Ku kyalemu mu karyata mu za'a ha'inta taje tana soyayya da malami yana bata amsa mu kuwa muna fama da karatu wlh bata sabuwa bindinga aruwa.!"

Wasu sun goyi bayan su,suna cewa munafuka bayin Allah na karatu ke kina iskanci dan kici Exam Allah ya toni asirin ki,wasu nacewa aiban taba aikata zargin da ake mani kowa yasan ina karatu musamman mazauna hostel,ranar dai naga tashin hankali tun karfe ɗaya ake bala'i har la'asar.

Tunda aka fidda Fatash ban kuma ganin taba,saidai wasu neighbours dinmu suka rakoni sai kuka nike kamar raina zai fita,suka maidani daki suna bani hakuri sai lokacin Fatash ta shigo itama tasha kukan harta gode Allah,hijab ta zira muryar ta na rabewa tace.

Kije Ya Taufiq na kiranki yana bakin gate,tashi muje.!"

Wani kululu cikina ya ansa da kara tsabar tsoro,fargaba duk suka rufeni ina tambayar kaina mi zance mashi,kuma ya zanyi da Mate dina dake dakona a waje anya zan iya fita.

Wayata tahau ruri,dagawa nayi muryata asanyaye nayi sallama,ina waje kufito yanzun nan.!"

Mikewa nayi na yafa gyalen doguwar rigata muka fita aiko kamar jira su Yunus sukayo kaina suna kiran.
"Sai kin fiddo Questions din daya baki fasika wlh bamu yarda dole sai kinyi bayani.!"


Ganin maza sunyo kaina hakan yasa Ya Taufiq fitowa a motar da sauri nima da gudu na koma bayan shi,sai bala'i sukeyi.

Suna zuwa wajen shi suka tsaya sukace.
"Kaine yayan ta wlh bazamu yardaba kanwarka tana isakancin ta,da malami yabata amsar jarabawa dan haka bamu yarda muda shan karatu ita da satar amsa dole ta fiddota ko mu nakasata fasika.!"
Cewar Yunus sai cika yake yana batsewa.


Wanke shi da kyakkyawan mari Ya Taufiq yayi har saida ya wuntsile kasa ya fadi.
Ranshi Ya Taufiq kuwa duk ya baci.
Sukayo kanshi wani fitinan nan kallo daya aika masu dole sukasha jinin jikin su.

Da kausassar muryar shi yace.

Kunada hankali zaku jefeta da wannan mummunar kalmar kuma wayace maku yabata amsar jarawa kuma wanene malamin.?"

Dr JJ ne kuma munga sample ne da mukaje tutorial a Lecture room dazun gashi nan harda sunan ta da short note ta fiddo mana original din.!"


Ansa Ya Taufiq yayi yaga gashi nan sunana da question amman ba dukaba daga kasa ansa masoyiyata ina sonki Dr JJ.

Mika masu yayi saiya kwantar da muryar shi ƙasa yace.

"Kuyi hakuri ni kaina bazan bar case din nan ba wlh sai inda karfina yakare saina gano mike faruwa kuma kubarni da ita zanji komai,kunsan definately dole tinda wannan issue din ya fita za'ayi cancel exam din sai ansake sabon Questions dan Allah ina baku hakuri amman kusani Amina ba jakka bace tanada kokarin ta."

Eh munsani Oga amman ai duk kokarinta baza muji dadiba idan muka kama tana ha'intar mu.

"Hakane kuyi hakuri kuje komai kenan nasan zakuga saka mako,da taimakon Securities suka tafi nikan nasha kukana nagode Allah."

Kallan daya kara jifana dashi yasani sauke kaina kasa shigewa yayi mota hakan yasa muma muka shiga,tadawa yayi mukabar makarantar munyi nisa kamar zamu dauki hanyar Kaduna sai kuma ya tsaya idanun shi jajir yace.

"Waye JJ.?"
Kukane ya kufce mani muryata na rabewa nace.
"Lecturer din mune.!"

A fusace yace.
"U are very stupid ba wannan na tambayeki ba,miye hadin ki dashi?"
Shiru nayi bude motar yayi ya fita yace.
All of you come out.!"
Fitowa mukayi jikina sai rawa yake.

Tell me waye JJ!?"
Ya sake yi mani tambayar ba alamun wasa a fuskar shi.
"Saurayina ne."
Nasamu kaina da furtawa.


Wani irin kallan shock suke aika mani banda kuka ba abinda nikeyi.
Saurayi! Ya maimata a bakin shi.
"Zargin da ake maki gaskia ne kenan.?"
Aaa wlh ba gaskia bane Ya Taufiq kafahimce ni....


Wani kyakkyawan mari ya aiko mani duk ya gama ƙulewa dani saidai bansan na duke ƙasa ba,hucin shi naji amman saida ya tabani ji nayi kamar in fitsari dan tsoro daya dirar mani,dan danan mode din Ya Taufiq yagama canzawa.


"Saurayi daman soyayya kikeyi a Makarantar amman kinci amanar iyayenki,da kanki yanzun wannan tabon da akai maki ina zaki kai shi?"

"Ya wlh kaji abinda ke tsakanina da JJ nan nagaya mashi komai da barazanar da yai mani zai kasheni da iyayena,dason lalatani dayaita yunkurin yi,har gida danace yaje dan in kubucema tarkon shi,da wayata daya rike duk na gaya mashi.''


Wani irin duka Ya Taufiq yakaima motar shi da karfi yana fidda huci mai zafi banda Fatash dake kukan jin labarina.

A fusace yayo kaina,duk nagama tsorata na daukama saiya dakeni sai kuma yace.
"Kinada hankali kuwa da ace ya lalata kifa ya zakiyi da rayuwar ki Amina,ashe bakida hankali baki da tunani,anya kinsan ciwon kanki,kika boye wannan big case din daman kin iya munafuncin irin wannan daman bansani ba.?"

Ganin yanda ya fusata idanun shi kamar rushi,saina kara tsorata da lamarin Ya Taufiq
Bansan na dukaba nace.

"Dan Allah karufa mani asiri kada Baba yaji zancen nan wlh karshen karatuna yazo.!
Ya Taufiq nayi hakan ne dan gudun kada ya kashe mani iyaye tinda yasan gidan mu,shiyasa wlh blh bantaba son shiba forcing dina yake."


"Yiman shiru wlh zan zaneki wajen nan Amina,ni zakima munafunci,kinsan irin sonki da nike maki da kaunarki amman na daurewa soyayyar ki dan kawai kisamu cikakken ilimi,naki kowa nace ke nike so,na tsaya jiranki duk yanda shekaruna sukaja amman naki aure duk ke nikejira duk da nasan kilan gaibu nike jira ba lallai insameki ba,amman ban karaya ba,saike zakiyi soyayya da wani banza haryake ikirarin lalataki,Amina kin yaudareni kin cuci mahaifin ki da duk wani makusancin ki.!"

Bansan na riko hannun shiba ina kuka nahau bashi hakuri.
"Wlh Ya Taufiq ban maka hidden komai wannan shine gaskiar abinda ya faru kayarda dani pls."

Fisge hannun shi yayi rai bace yace.

"Karya kike tunda har kikai mani karya,nan ya dinga cewa mijinki ne a cikin waya amman dayake kin kware da munafunci cewa kikayi yarda wayar kikai,kigaya mani taya akai ya samu wayarki.?"

Yai tambayar a kufule.
Kuka nafara banda zabi haka nagaya mashi komai nasan duk kimata da zube idanun Ya Taufiq a halin yanzun."

Kin kyauta kuma kin bani mamaki.
Juyaman baya yayi idanun sun kada kamar rushi yace.
"Bansan ki breaking trust dina akanki Amina amman sai gashi kin bani mamaki nayarda dake nagaya maki sirrikana ban boye maki komai na maidaki kawata,kanwata,aminiya ta,kuma jigona wadda nike fatan inyi rayuwar aure da ita ashe ke ba haka kika daukeni ba.!"

Banda kuka ba abinda nike sai begging dinshi nikeyi,mota ya koma ya tada jiki mace nashiga hakama Fatash data kasa furta uffan banda aikin kuka a takeyi makaranta nayi naganin yakara fusata nufa,waya ya dauka ya kira wata number a handfree yasa ana dagawa daga can akace.

"Yes sir."
Zan turomaka details din wani within 2hrs agano mani komai nashi yanzun nan."
Angama ranka shidade."
Muna shigowa school ya saukemu ya juya da motar shi,haka na koma daki da kyal nai sallah naci kukana na gode Allah,dagani har Fatash ba wanda yaima kowa magana.

Washe gari muka shirya kowa ya tafi exam,niko kamar mujiya a cikin tsuntsaye haka na koma cikin Course Mate dinmu ako akace anyi cancel din Course din JJ akai shifting dinshi shine last exam dinmu,sai lokacin suka samu sukuni aransu.

Dan a duniya ba abinda kema students ƙuna irin yayi karatu ace anba wani satar exam,kwara ayi cancel a canza Question yafi masu alkhairi da dai ace anrubuta jarabawar duk da ba dadi kowa yasha karatu a soke.

Nan ma saida nasha bala'i da tsina wajen su,haka kowa yatafi daman ranar ita kadai zamuyi.

Kirana Dr Fatima tayi ina zuwa office dinta na isake Ya Taufiq da wasu malamai sai JJ kana ganin shi kasan yana cikin tashin hankali,dan idanun shi kadai zaka kalla kagane hakan.

Tambayoyi akai mani na fadi abin da nasani nan aka sallameni banda kallan tsana ba abinda yake jifata dashi.

Bayan kwana biyu ba laifi case din ya lafa nafara sakewa cikin Mate da sukaji sharri ne bai bani satar amsa ba yayi hakan ne dan akoreni a school tunda naki karbar soyayyar shi,nanfa wasu suka fara zuwa bani hakuri suna cewa,ai sunsan yana sona kuma su takardar da suka gani ce yasa su kara xargina dan Allah inyafe masu,nidai nayafe ma kowa domin nasan koma minene nice silar komai da naki fadar matsalata zurfin ciki yajaza mani hakan.


Shiko Ya Taufiq duk wata hanya da zaibi yabi daga sama zuwa kasa saida aka tabbatar da case din akan Dr JJ na yunkuri lalata da daliba,yanzun hukunci ake jira ayanke akan case din.


Washe gari ina zaune a daki wayana ya hau kara saidai bakuwar number ce ina dagawa naji muryar JJ gabana ya fadi.


Ke nizaki cima mutuncin ki wulakantani a idon duniya wlh blh sai nasa kinyi nadama ke mai ɗan uwa harda mani cinne ko?saina hanaki kwanciyar hankali da JJ kike magana.!"
Ɗit ya kashe kiran kallan juna muke nida Fatash dayake handfree nasata dan tajima kunnen ta.

Waya nike da Husna saboda yau take final exam dinta sai wishing muke mata nida Fatash zata kammakala BSC Bio Chemistry sosai nai mata murna.

Bayan kwana biyu mukayi last Exam dinmu Course din Dr JJ muka zana duk da Exam din tai zafi amman kuma kowa ya amsa sosai da haka muka koma gida.

Haka rayuwa ta kasance gwanin dadi Baba bai taba jin labarin case dina da JJ ba saidai tsakanina da Ya Taufiq ya sakani a kwadon shara bai min murmushi bare dariya ya koma ainahin Major Taufiq dinshi dole nakama kaina gashi kullin ruruwar son shi nakara tasiri a zuciya ta,ko kiran shi nayi yana dagawa zaice
Lfy."
Dolena a darare zan gaida shi,atakaice yake amsa mani inaji ina gani nafara jin tsoron shi akan dole mukabar waya.
tsorona daya kadama ya daina sona gashi nayi nisa a son shi.

Hutu yaja sosai har muna shirin komawa Year 5 ana saura sati mukoma aka samana result abin mamaki nafaɗi Course din Dr JJ gashi 3 credit unit ne,nasha kuka the first time dana taba C.O a Jami'a koda nakira Ya Taufiq nagaya mashi cewa yayi.......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️



*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E39&40



"So what i dont have any bussiness in ur issue Minal,dan haka karki kuma gaya mani matsalar ki.!"

Kashe wayar yayi,saida naji buguwar zuciyata,kallan da Mama

Please Login or Register in order to submit comment