Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yai mani."
Dukar dakaina nayi jin abinda Anty Aisha ke cewa sai kunya ta kamani."

Kinji Mrs Taufiq kin gama komai amman kin manta da jigon kema Fatash kin manta."

Baki dayanmu mukace minene.?"
Wani irin kallo Ya Taufiq ya jefomani wanda bansan ya zansa shiba har saida na maida idona kasa yace.
"Ba wanda yai maganar Chicken and Beefs."
Gaskia kam Hussein kowa ya manta sai abada aikin komai zuwa gobe."

Eh komai zansa akawo insha Alalh."
Allah yasa Hussein."
Waya ya ciro ya kirawo Usama yace.
"Kasa a shigo da kayan nan ciki."
Kashe wayar yayi yace.
"Miko mani Amna."
Yai maganar yana kallona.
Ansarta nayi na mika mashi na amshi Major sunkuyowar dani a hankali yace mani.

"Kinyi kyau Minal u re so beautiful."
Samun kaina nayi da murmusawa,har saida hakorana suka bayyana."
Like U yayana.

Wai mi kuke cewa ne Hussein?"
Ya Tariq ya jefo mana tambayar komawa nayi na zauna ina Murmushi.

"All ur eyes on me ko Hassan,I love u nace mata."
Dariya sukayi nikam nasha mur abuna haka akaita fira kowa yana fadin albarkacin bakin shi.

Sallamar Usama mukaji shida wasu masu aiki dauke da trolys har guda biyu ba abinda ke cikin shi sai kayan jarirai dana Anty Aisha kala biyar ya sakomata sai fashion sarka daya siyo mata,saijin dadi takeyi,godiya tayi mashi,hakama Ya Tariq nan mai aikinta takai mata su dakinta nan mukaci gaba da firar mu cikin aminci

Ya Taufiq baibar gidan ba sai karfe tare na dare sannan ya tafi yace gobe kafin muje school zamuje kai deposit na aikin suna da za'ayi.



"""""Washe gari da misalin karfe goma su Anty Wasila da Mami sai Samira matar ya Samir sukazo ganin babies kowa da kaya niki niki ankawoma Babies,a bedroom dinta suka shiga kanwar Maman ta,ta mika masu Major suka gani,Anty Wasila ke tambayar ina gudar ance twins ne,kirana Anty tayi awaya lokacin tana wajen mu ana gamam shiryata na dauketa nakaita wajen mu,shigowa nayi bakina dauke da salama,wani irin kallan tsana Mami kejifana dashi hakama Anty Wasila,sainaji wani irin jiki sage nakaraso ciki na basu Amna.

Amsa Mami tayi tace.
"Su kuda wajen kwadayi akan mutu Allah yarabamu da kwakwa,ke kishiyata barka da zuwa Allah yaraya yabaki lafiyar shayarwa Aishatu."
Ameen sukace.
Niko juyawa nayi duk ba dadi haka nakoma daki sainaji harna kagara inkoma makaranta ganin su Mami dan nasan tana iyacin zarafina tunda ta tsaneni.

Ina komawa bada jimawa Ya Taufiq yace yana waje mufito muyake jira.
Kamar jira nike na ziri gyale muka fita,ai kamar an banko su Mami suka fito suma zasu tafi gida.

Daidai na bude kofar motar zan shiga naji Mami nacewa.
"Mi idanuna zasu ganemi Hussein har yanzun kana tareda mayyar yarinyar nan,uban naka ya rabaka da ita shine zaka nace anya kana neman albarka.?"

Barka da fitowa Mami."
Ba gaisuwa na tambayeka ba,amsa zaka bani."

"Mami karfa ki manta kanwata ce taya zan kita.?"
Yiman shiru kamar kayi gaban mahaifin kane tunsa baka da kishin zuci,muje Wasila."
Haka suka shiga mota driver dinta ya tafi dasu.

Jikina ya mutu likis ganin haka Ya Taufiq yace.
Ku shiga muje mudawo,Minal kikai tsaye miye abin damuwa."
Shiga nayi nidai bance komai ba har muka isa.

List na abinci aka kawo duk muka zaba,Ya Taufiq yabiya kudi,mukace zuwa karfe shabiyu za'akawo su,nan muka bada address bamujima ba muka dawo gidan.

Nan muka fara shirin komawa school,Anty tace sai munyi lunch baki dayan muka zauna bisa katan capet din falon Ya Tariq kowa ya zuba abinda yakeso,haka mukaci saidai bansaki ciki naci ba ga maganar Mami ba dawo mani,wani gefen kuma idanun Ya Taufiq sun dameni hardai nace na koshi."
Itama.Fatash tashi tayi nan mukayi sallama da Anty Aisha mukatafi Ya Taufiq yasa Usama ya maidamu makaranta,har mukabar compound din gidan yana waving dinmu,har school ya maidamu wannan kenan.



********Caranci


Sosaima Mama da Anty Mubara suke shirin bikin Umaima ko lokacin kanta bata dashi sosai kaikace itace mai aurarwar domin kusan kullin tana gidan Anty ko kuma ita tana gidan mu.

Yauma tunda safe ta tada Mama tatafi kano hadowa Umaima kayan kitchen saina kore wanda Anty bata ida siyaba,haka Mama taita bilayi bata wannan kasuwa bata waccan har saida tagama komai sannan ta taho gida ba ita tadawo gidaba sai gab da isha'i kuma gidan su Umaima ta sauka nanfa sukaita murna suna shima Mama albarka kaya sunyi kyau komai ya tsaru iya tsaruwa ba ita ta dawo gidaba sai karfe tara na dare,amman Baba bai mata korafi ba acewar ranar bikin dole sai dole shiyasa bai hanata wannan zaryar ba.


Nikam a wajena washe gari da karfe biyu nikeda Class haka natafi duk da Lecture idan ta ranace bata da dadi sam saidai hakuri amman naje wani abun ingane wani kuma ban ganewa har na taso 4pm.

Inadawowa Complex da madara kawai nasha,na duba gass dinmu ya kare ga kalanzir dinmu babu,kuma nasan Fatash tana dawowa da yunwa zata shigo ba dadi tana kokarin yi mana abinci ni ace banyi sosai,dakin su wata Luba naje na aro Electric Gas dinta nadafa mana Cus-Cus da Vegetable Sos kowa yasa Zaria akwai kayan Vegetables shiyasa muke yawan anfani da kayan lambu a cikin abinci saidai muce alhmmdullh.

Ina gamawa a kula na juye mana,na kimtsa dakin sannan na saka Gas dinmu a wata bag da jarkar kalanzir dinmu na saka goguwar hijab na saka handbag dina,na maidama Luba Electric dinta na rufe daki natafi gari Repling Gas.

Commercial Motor nahau na tafi,hankalina kwance ha wata kasuwa da ake kira gada Kwangila akwai wani mai zuba gas kuma a nisa gaba kadan akwai mai saida kalanzir nan na siya harda kayan miya da Cabages su Carrot Cocumber da sauran kayan lambu na sai mana, sai mango da lemu,haka nagama aka saman aleda.

Gefe nakoma ina jiran abin hawa naso samun taxi saidai babu hakan yasa nahau dan acaba nace yakaini Samaru.

Tafiya muka fara a hankali sai naga yabi ta wani hanya nace malan taya zakabi dani da wannan hanyar.?"

Aaa Hajia kedai ba Samaru zakiba kibari zan kaiki shot court ne daga nan har Main Hostel dinku zamu isa.

Raina nidai bai kwanta ba,sai naga kamar dai zamubar gari dan dole nafara kaima mai acabar nan duka a baya amman ko gezau.

Ihu nafara kwalawa inacewa Kutai makeni zai saceni dan Allah."
Amman abanza domin munbar gari fintin kau,wata motace naga ta tunkaro mu saina fara murna ina dukan shi harya aje mashin din mun hau kokowa inasan kwacewa in gudu ya rike hannuna tamau bai rama dukan danai mashi ba.

Motar na tsayawa ganin wanda yafito saida yasa cikina katsawa dan azaba.
Da karfi aka kawoni gaban shi yace inshiga mota naki jikina na rawa idona sun saiya kala.

Fiddo wuka yayi sai kyalli take dal da ita yace,zaki shiga ko saina kasheki.
Jiki na bari na shiga gidan gaba ina kwalla.

Kai samata kayanta a boot mikoman wayar ta da jikkar ta
Sawa yayi ya miko mashi wayar ta da jikkar tawa nidai na tsure dan bala'i.
Shiga yayi ya figi motar da karfi yai cikin daji dani kuka nike ina bashin hakuri,wani wawan kallo ya dalla mani dole nai shiru ajemani wayata da jikkata yayi bisa cinyata saida yai nisa dani cikin dajin Allah ya waigo ya kalleni fuskar shi ba alamun imani a cikin ta yace.......



_Yar Mutan Kankia ce❣️_





Share
Pls
❣️


*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E23&24


"Bakin ce baki sona ba?harkike mani wata yar karamar bazaranar ki!to yau sainayi caka caka dake zaki gane ruwa ba sa'an kwando bane.!"

Hade hannayena nayi ina hawaye kamar famfo nace.
"Dan girman Allah karufa mani asiri Dr JJ kada ka wulakanta ni na tuba.!"
"Karya kike Caranci kin tabka babban kuskuren kin bin umurnina ni bazan tafka asaraba saina biya bukatata akanki koda zaki mutu."

Kara matsoni yai ya rike mani hijab da karfi na fisge ina kokarin bude marfin motar saidai a garkame take da Lock dan dole na kwala uban ihu ina,inalillahi wa'inna ilahirraji'un nashiga ukkuna ni Amina Allah ka kawo mani dauki zai cutar dani.!"
Shut up zan kasheki kin dauka duk wani motsin da zakiyi ban sane dake baki dayan ki a tafin hannuna kike ni ba sakarai bane kamar ke,har kin isa ingama fallasamaki sirrina kiki yarda wlh baki hauhu ba."

Rufe idanuna nayi gam ganin yana kusanto da fuskar shi gab da tawa addu'a nike harda ban daki dai inajin na karanta sai kuma naji ya tsaya cak ya dauke hannun shi gefen fuskata daya aza yace.

"Open ur eyes."
Da sauri ba bude su na,aza saman tashi fuskar dake murtuke idanun shi kamar rushi jijiyoyin fuskar kanshi sunyi raɗo raɗo dan bacin rai,wanda bi nakasa gane wai sona yake ko dai ƙina yakeyi dan ni banga alamun soba atakaice dai nasan shi a shi'awata yakeyi shine kwance a fuskar shi ba sona ba.

Munkai minti ɗaya muna kallan juna ni natsare shi da firgitattun idanuna watakila yaji shakkata ko in mashi kwarjini yafasa abinda yake ranshi,shi kuma ya rufeni da kallo dan na tsorata incika mashi burin shi,wanda bi agareni ba haka yake ba.

"Kina son in kyaleki.?"

Eh wlh inaso ka rufamani asiri."
Wata uwar dariya ya kece dashi take yasha mur yace.
"Zaki amince da bukata ta inkaiki waje mafi daraja da tsada kuma in baki makudan kudade ko kuwa bazaki amince in wulakantaki in barki wanda ba kowa zai iya kawo maki dauki ba.!?"

"Aaa dan Allah kada ka wulakanta naji zan amince amman da sharadina da zan fada maka."

Hahahaha Caranci ke har wani sharadine dake,lokacin da nike begging naki kin saurareni ne?dan haka nima banda lokacin ki.!"

Bansan sadda na rike hannun shiba.
Dan Allah kataimaka mani kaji minene uzurina.!"
"Okay inajinki."

"Dan Allah naji abinda kace JJ inasan kasoni dan Allah ina nufin kayi soyayya dani karka tabani domin insan dadin so,inaga tahakan zaka cika burin ka,akaina cikin jin dadi da sakewa amman kada kai forcing dina (rape)sai nike ganin girman ka bazai bari kaci zarafina ba har haka.!"

Zuciya ta keda bugawa da sauri kamar zai fado kasa.
"Wayau zaki mani kenan.?"
Wlh ba wayau bane Allah."
Zaki iya soyayya dani bare harki iya aurena.?"
Kwarai kuwa zan iya soyayya dakai JJ kuma in muka fahimci junan mu wlh zan iya auren ka,nidai kada ka wulakantani na rokeka."

"Alqawali ni kadai zaki kula a matsayin mosiyinki sannan bazan tabaki ba koda hannun ki kin amince.?"

"Eh na amince,amman zaka boye soyyarka agareni a idon mutane ko.?"

Kwarai kuwa ba matsala na yarda da duk wani sharudan ki."
Amma inada sharadina na karshe a gareki."
Inajinka."

"Idan na kuskura nagane kina mani wasa da hankali ba gaske kike ba wlh saina caka caka dake kinajina kuma dagske nike ba wasa."
"Naji na amince da duk sharadin ka."
Yayi Beauty ki kwantar da hankalinki baki ba fargaba indai kina tare dani."

Toh nagode."
Hawaye na sauka a idanuna kaina na mani ciwo a hankali na kwantar da kaina bisa kujera nakara jinjina bayana.
Anshi sakala ma hannun kin wannan zoben alqawali."

Nakaraga mubar wajen ganin 5:30 tayi ban musaba na ansa na saka a yatsani ina kiran sunan Allah,handkichief ya miko mani na share hawayen idanuna nagode nace.

Tada motar yayi,muka tafi sai labari yake mani daga Eh sai Um um nike cewa har muka iso daidai gate daga nesa ya tsaya yace.
"Ki ida cikin School ya ajaza mani 10k a jikina nidai banki amsaba a jika na sakasu raina ba dadi daga nesa ya tsaya yana hangena,da haka nasamu mai shiga dani cikin Makaranta raina ba dadi,hawa nakira Fatash wanda na iske miscall dinta ba adadi da sauri ta daga muryar ta ba breaking nace tazo ta kwasar mana kaya,keda karama na iya dauka ina isa dakin ta fito daukar kayan aje ledar kawai nayi ko hijab din ban iya cirewa ba na kwanta kwalla masu dumi nabin fillon dana aza kaina haka nai shiru kamar mai bacci,amman tunanin duniya da zullumi ya hanani sukuni dan tsoro.

Haka Fatash ta shigo da kaya tambayar duniyar nan taimani naki bata amsa hardai tasami ido ni kaina inajin tausan Fatash domin ina daga nata hankali tsorona ma Kada in dauki hakkin ta dan banji zan iya gaya mata Abinda ke faruwa dani gudun kada tajuye dani in rasa karatuna matukar Baba zaiji.


*******Bayan kwana biyu naje Class still as usual da safe duk Monday JJ ne koda nashiga na dan makara amman ba sosai ba,ina isowa Maryam ta matsa mani na zauna,dago kaina nayi na maida ga Lecture din da akayi idanun mu suka hadu dana JJ,murmushi yakasar mani a sirince nikam dai yake nayi saidai still gunmu yake kallan kallo,maida kaina nayi kasa danji nike wlh inda za'a bani wuka zan iya kashe shi.

"Stand up."
Kowa kanshi yake kallo kowa ya gama tsarguwa nikam ko ajiki ganin mun sasanta dashi ba lallai yaci gaba da takura mani ba.
"I say stand up.!"
Still kaina akasa danna fara nisa a tunani.

"Marafa yimata magana."
taboni tayi kallan ta nayi nace lafiya."
Nuna mani step takeyi ni kuma bansan hada ido dashi sake maida idona kasa nayi.
"Ke Amina dake yake fa."
Da sauri na mike tsaye na maida kallona kanshi.

Jinjina kai yayi yana mani wani kallo yace.
"Kin makara ina maki magana kin shareni i think kin rainani get out of my Class.!"
Sorry Sir."
Nace fuskata ba alamun annuri
I Said Get out."
Sorry sir!"
Cewar Yunusa.

Baki ɗaya yan Course mate dinmu sukafara sorry sir dan dole yace.
"This is last warning sit down."
Thank u sir.
Zama nayi inajin yana Lecture yafara tambayoyi Maryam na bashi amsa nidai bance komai ba har ya gama ya fita.

After 30mint Dr Zainab ta shigo mana tafara mana Lecture,shigowar text naji budewa nayi ina karantawa."

_My beautiful ya kikaga wannan game din yai maki dadi ko? Don't worry duk cikin so ne masoyiyata,I love u._

Shiru nayi bance komai saidai Uhmmm dana furta bayan nagama karanta text din dan bansan mi zan maida mashi ba.
Aje wayar nayi nacigaba da sauraran Dr Zainab bamu muka gama Lecture dinba sai 4pm daki na wuce a gajiye nike jikana.


******Akwai wata rana ina zaune a hostel kiran Ahmad ya shigo cikin phone dina murmushi nayi dan naji dadin kiran shi,zan iya cemaku kaf cikin masoyana daga Ya Taufiq sai Ahmad nikejin dadin kiran su,domin basu gaya mani abubuwa marassa dadi sukan gaya mani abinda zai sanyayya mani rai musamman Ya Taufiq dana gama yarda cewa indai yawan tunawa da mutun shike nuna kana son shi tabbas na kamu da son Ya Taufiq araina wanda ban tunanin so ne na yan uwanta saidai so nakasan cewa abokin rayuwata na har abada,tsundumar danayi a tunani yasa kiran ya tsinke saida ya kuma dankaro mani wani sannan na daga,da sallama abakina.

"Wa'alaikissalam gimbiya ta,aminci Allah yatabbata agareki farinciki na."

Ya tabbata agremu baki daya dafatan kana lfy.?"
Da sauki ba lafiya."
Cike da kulawa nace.
"mike damunka.?"
"Soyayyar ki ke wahalar da Mina kimani izini inzo inganki yanzun nan."

Dariya nayi saina nemi damuwata narasa nace.
"How bayan kana Katsina ni kuma nina Zaria."
Wlh ko yanzun kikace inzo ko minti ukku ba'ayi zanzo."
A dan tsoro ce nai mashi gatse nace ingani a kasa sai kazo."
Okay shikenan,give me some minutes."
Okay."


Kashe wayar yayi nikam dariya nayi ina cewa Fatash wai kinji Ahmad dinnan wai yanzun zaizo tayama hakan zai faru bayan yana Katsina."

Ke ni kada kidameni da wani Ahmad din banza kinki Ɗan uwana jinina kina mani zance wani sakarai can yasani."

Haba Fatash taya zanki Ya Taufiq naga shima wannan har yanzun ban furta kalmar so agreshi ba,kuma so kike in wulakanta shine.?"
Mtsw can ta matse maki,yan yan waike Ahmad,Aaa Amadu zaki wani dameni aikin banza."
"Allah yabaki hakuri Fatima."
Ameen."


Miscall din danagani dankare yasani zaro ido kadan JJ ne ya kirani kuma da alama tun ina waya da Ahmad ya kirani
rasa mi zanyi nayi kiranshi ko in share shi.
Sake kirana yayi na daga zanyi sallama yace.
"Hi Beauty dawa kike waya tun dazun har haka.?"
"Babana."
Nasamu kaina da bashi amsa.
Fine kigaida mani dashi kice ɗan shi nagaida shi kafin inje in gaidashi dakaina."
Okay zaiji."
Anjima zan baki labarin soyayya kinji Beauty."
Okay Allah yakaimu lafiya."
Nace raina na kuna domin JJ ya takura mani
I love u with all my heart."
Thank u sir."

No beauty call me JJ idan ina tare dake a waje, Class kuma kikirani da Sir,kinajina.?"
"Eh naji."
"Okay love u my love."


Dit na kashe wayar dan duk duniya na tsani ya furta kalmar so agareni tafi komai muni a kunnuwa na,tashi nayi zan dauki ruwa insha kiran Ahmad yakara shigowa.
Kallan screen din Fatash tayi ta saki uban tsaki taci gaba da jorting dinta.
Dauka nayi naji yace.
"Ina wajen hostel dinku gimbiya ta."
Me kace serious.?"

Nayi mashi tambayar with shock a fuskata.
"Wlh dagaske,ke kadai nike jira tun dazun nakira ki kina waiting nasan waya kikeyi."

Ajiyar zuciya na sauke nace..
"Sorry Ahmad bazan ganka ba,saboda nifa wasa nai maka ba dagske nike ba."


Ni kuma da gaske nike gimbiyata, takanas takano nazo ganin ki daga Katsina Amina,nasan zakiki amincewa shiyasa ban sanar makiba saida na iso Zaria ki taimaka mani inzo inganki dan Allah."

OMG na furta abayya ne.
Pls am beg of u."
yace cikeda da rauni a muryar shi.
samun kaina nayi dajin tausayin shi nace.
Ka amince 15mint zan baka."
"Yes ina amince aikin bani da yawama."
Ina zuwa."
Okay cikin blue black din Corolla zaki ganni."
Okay."
Kina nufin fita zakiyi ganin shi."
Ya zanyi Fatash yazo sai in wulakanta shi,muje ki rakani."
Banzuwa saikin dawo."
Duk yanda naso taki rakani.

Harna saka after dress dina milk tace bari inje inga kalar shi,da kike rawar kafa akan shi,dame yafi Yayana."


Murmushi nayi nace.
"Rabin kafar shi bai kamaba ai Ya Taufiq na musamman ne."
Uhmm banda riya dai muje inganshi."
Haka muka fita ita kuma bakar rigace jikinta.
Har bakin motar muka tsaya duk yanda yaso mu shiga ciki kiyawa nayi dan ni banga wanda zan shiga cikin motar shiba hankalina a kwance kamar Ya Taufiq ba."
Ganin munki shiga hakan yasa ya hakura muka gaisa nan yafara jan Fatash da fira yana cewa.




_Yar Mutan Kankia ce❣️_





Share
Pls
❣️


*BAKIN JININA YAJAMAN😭*


*NA*

_Yar Mutan Kankia❣️_

*_TRUE LIFE STORY!_*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.*_


S2/E25&26



"Fatima manya duk da bantaba ganin kiba,raina yabani kece Fatash din Minal ya Makarantar.?"
"Alhmdullh,ya kake.?"
Lfy lau,ya karatu."
Alhmdullh."
Atakaice take bashi amsa tana kallan shi akaikaice nidai saidai inyi murmushin gefen baki maganar shi ta katse mani dariyar da nikema Fatash.


"Gimbiyata kinyi kyau fa ya makaranta.?"
"Lafiya lau alhmdullh,
Ya hanya.?"
Alhmdullh,kinji dadin danaji ganin kyakkwar fuskar ki,gaskia Fatima kawar nan taki mai kyauce."

Aikuwa masha Allahu gata nan kamar tsada."
Gaskia kam bakiyi kuskure ba dan hartafi tsadar kyau da usuli."

Murmushi nayi nace,uhmm kudai akeji nikam ya kawata Allah yasa baku basu citta."
Wane mutun aikodan gimbiya an daga masu kafa bare kuna Husna ai tadaban ce."

Allah yasa hakane,da naji dadi kuwa.?"
"Kiji dadinki gimbiya ta."
Duba agogon hannuna nayi nace,lokaci yayi zan koma daki."

Haba daga fara magana sai kice zaki tafi."
Sorry almost 30mint fa kaga nakara dayawa ai."
Hakane nagode maki gimbiya ta."
Uhmmm ba komai.
Juyawa nayi zamu tafi yace.
"Fatima bissimillah mana."
Komawa tayi nikam nai tafiya ta,ina daga mashi hannu shima waving dina yayi na shige hostel.


banfi minti biyar da zama ba saiga Fatash nikiniki da katuwar leda,da kallo nabita danfarar da ita tayi gabana tace.
"Ga abarki,ga kudi duk yace abaki."
Kikadai amsa."
Nace mata


"Mtssw kema kinsan banda kwadai matsa mani yai minti nawa yana bugawa dani da wani bakin shi,wai dan Allah kikulaman da gimbiya ta minene minene,yan yan yan Ohh ya cika kilbibi."

Murmushi nayi ina mamakin adawar da Fatash kema Ahmad har haka bude ledar nayi su Ice cream drinks sai kaji dasu biscuits,kudi kuwa 10k ne.

Bude wata jikka nayi inda na aje kudin JJ na jefasu nace ko sisi bazan taba ba."

Uhmmm ke kika sani cewar Fatash.
Kwanciya ta nayi ina murmushi nasan yau na kule kawar tawa, Husna nakira mukaci gaba da waya.

Muna gamawa saiga kiran JJ ya shigo kamar in buga ihu na dauka.
"Waye yazo wajen ki yau.?"
Kamarya wace tambaya ce wannan."
Okay tambayata kike kenan.?"
Aini naga ina daki tambayar tabani mamaki ne."
Kibar mamaki saboda abinda nikeso nike bibiya akan mi zaki shiga damuwa."
Waye yazo wajen ki mai fararen kaya?"
Dan Allah JJ mubar issue din nan."

Look beauty kinasan in mashi illane waye shi.?"
Yaya nane."
Oh daman gidan ku kinada yaya kenan i think kece babba ko sai Ahmad ina kika samu wa haka bansani ba.?"

Mamaki yagama kasheni da lamarin JJ wani irin bibiya yake mani har haka mi hakan ke nufi ohni Amina.

Azahiri cewa nayi Yayan Husna ne."
Halifa,ko Salisu ciki wane kike nufi,look Amina kada ki mani wasa da hankali,kada ki kuskura ki yaudareni dan wlh ban yafiya zan iya komai akanki,saurayin kine ko.?"
Aaa Cousin dina ne Yayan Husna dan yar mamarta,sako ya kawo mani."


"Exellent mind ur self beauty i will call u later."
Katse kiran nayi ina al'ajabi a raina,dafani Fatash tayi a tsorace na kalleta.
"Duk da bansan mi ake cemaki ba amman ga dukkan alamu kina cikin firgici wanene wannan kuma mi yake nema a wajen ki.?"
Sauke ajiyar zuciya nayi na kirkiro murmushin munafunci nace.

Ya Aliyu ne Cousin din Umaima cikin gari yake,shine ya ganni da Ahmad wai zagaya gida,shine na samu na kare kaina."

Kamar da gaske yaushe kikafara karya Minal?"
Serious trust me."
Okay is okay Allah ya kyauta saiki kiyaye gaba."
Insha Allah."


*******Mama Pov


A Caranci kuwa su Mama ne gidan Anty Hafsat sai hidima sukeyi yau zasuyi aikin dibilan da cincin duk yan uwa sunje kowa yana jiran a fiddo flawa afara aiki abin mamaki sai ta bada tiya takwas da rabin man ulga sai siga tiya biyu tace aje ayi aiki,daga Mama har Anty Mubara kallan mamaki sukema yar uwar tasu,haka suka fara aiki da kyal aka cika botikin dibilan na cincin kuwa ko rabi bai kaiba,siga kuwa baijiba Anty Mubara taja Mama tace.


"Haba Anty Khadija akanmi zamu sama Anty Hafsat ido komai tabada kadan kamar anroko,jibifa kiga yanda tabada suger ga filawar ko isa baiba,gaskia nidai magana zan mata wlh,ina buhun filawar da kika kawo da mai banda suger mu ai yar'mu mukace taima hidima bawai ta saida ba bari inje gunta."

Aaa Mubaraka,karkije ki barta ni zansa akara mata daga gidana akai mata gidanta bansan rikici."

Wlh Anty sai naje Allah."
Tafiyar ta tayi ta kira Anty tai mata magana kamar jira tafara fada.
"Toh sa'idinawa ai daman nasan haka zakice aiku daman badai kuima mutun abu dan Allah ba sai kun masa gori,mi ruwanki da abinda Khadija tabani inma saidawa nayi Mubara mi ruwanki kodai kinga kinzama tsarata shiyasa zaki gaya mani son ranki?toh bude kunnen ki da kyau kijini na saida buhun filawa da jarkar mai kuma na saida ne dan biyama kaina bukata,atamfofi na siyo da zan saka a koren dangin miji,ai daman su zasu cinye garar to kwara su daura zani da suci sujuye masai."


Toh yanzun idan bamu gaya maki gaskia ba Anty wazai gaya maki.?"
Dallah tsaya Mubara banson gaskiar ki,ni ba sakara bace,nawa kike."

Yi hakuri karambanina ya jaman amman kisani anata zaginki komai kin bada kadan badan Allah bai rufa maki asiriba."


"Yo duk uban da baifasaba yaci uwar shi nace kinajina."
Naji Anty Allah ya kyauta."

"Gaba ba,indai yanzun ne angama tunda nafadi ta cikina saura gaban kuma aiman inyi tas da mutun kowaye shi."
Shikenan Allah yasa mugama hidimar mu lafiya."
Ameen."

Koda takoma wajen Mama batace mata komai ba,ta dauki hijab dinta sai gida kare yasha taba.

Itadai Mama haka ta dinga bi a hankali wani a hantareta wani kuma ai dadi da ita,amman a inda zata wahalu kenan.


"""""Tunda daga lokacin bankara bari ko ganina JJ ya sakeyi ba ko waya ya kirani sai ince ban lafiya daina zuwa Lecturen shi nayi kwata kwata aganina ta hakane kawai zan samu ya rabu dani.

Saidai duk sanda zai tambayeni dalilin kin zuwa Class sai ince ban lafiya haka naitayi mashi alaye dan Allah yasani natsani JJ tsana mafi muni arayuwata.

Shiko Ya Taufiq tunda ya maidomu makaranta bamu sake waya ba duk da jibine zamuje suna dan har dinki saida Mama ta aiko mana nida Fatash wanda zamusa da suna.
Nida Fatash kuwa bamu da aiki sai zuzuta sunan twins din Ya Tariq kai kace wani gaggarumin bikine za'ayi.
Yanda mukejin sunan a ranmu.

Ranar suna kuwa Usama yazo daukar mu,kayan da Mama ta dinka mana muka dauka sai wata less pich,kala biyu muka dauka sai doguwar riga daya,fita mukayi muna isa muka gaidashi,bamu jimaba muka tafi.

Muna isa gidan direct dakin da muka kwana nan muka aje kayan mu,sannan mukaje wajen Anty Aisha lokacin ana mata kunshi,tasha uban kitso dayake da sassafe ne mukaje ko goma batayi ba,nan fa mukace munasan lallai,ana ida mata aka fara zana mani sannan akaima Fatash sai sha biyu daidai na wanke nawa itako Fatima saida yakai karfe ɗaya sannan ta wanke,wanka nayi na sanya atamfar da Mama ta dinka mana nayi kwalliya ina gama shirya Fatash itama ta shiga wanka.

Waya tace tahau ruri Ya Taufiq ne yakirani har kyarma nike in daga Allah yasani nayi missing dinshi araina,ina dauka yace.
"My Happiness ina waje inajiranki."
Murmushi nayi nace gani nan zuwa.
Zaunawa nayi wai dole sai naja Class irin yan

Please Login or Register in order to submit comment