wayar, dan indai ahaka zasuyi wayarnan bazai fahimci komaiba, ajiye wayar yayi yatashi ya shige bathroom.
Da kallo k'asa-k'asa kawai na iya binsa, amma nakasa ko kwakwkwaran numfashi.
Daga can kuwa Nuren kwashewa yayi da dariya saboda tuno wani Abu, (to su Nuren dai dama bariki sune manyantađ€Ł), dariya yakeyi iya iyawa yana dukan kansa, daya fara tsagaitawa saiya kuma saka wata, saida yayi ta ishesa sannan ya daina, ya rik'e ha6a yana fad'in âoh ni su brother ansan takan tsiya, ina ganinsa lab-lab Ashe d'anba sauk'ine, toma uwar miye na d'agamin wayar tunda yasan yafara sauka a networkđ€Ł, yakuma saka dariya saikace wani sabon kamu.đŹ
Galadima kam ruwa ya sakarma kansa kawai, ya dafe bango da hannu biyu ruwan na kwarara saman kansa, sai faman taune lips yakeyi shi kad'ai, yayi da zuciyarsa ke sak'awa da kwancewa, saida ya ji k'arfi-k'arfi sannan ya kashe shower d'in yaja bathrobe d'in ya saka yana faman sauke 6oyayyar ajiyar zuciya.
Inda yabarta anan ya fito ya isketa, kallo d'aya yamata ya d'aukekai, bakin gadon ya zauna yana goge kansa da k'aramin towel, yajawo wayar da d'ayan hannun ya danna kiran Nuren.
Bugu d'aya Nuren d'in ya d'aga, da k'yar yasamu ya danne dariyarsa, âbrother wai miya farune naji muryarka haka? nifa ka tadamin hankaliâ.
âBa komai, shin kajene?â.
Nuren ya toshe bakinsa gudun kar dariya ta kufce masa, Sameer d'an rainin wayone ALLAH, wai babu komai, to naji babu komai aje a haka.
âwai kana jina kuwa?â. Galadima yafad'a.
âOh sorry brother network nayin wasa, gani a gidan, amma bankai ga shiga inda takebaneâ.
âok tom kaje, amma kabar wayar a kunne, inason naji komaiâ.
Nuren yace âtoâ.
Da sallama ya shiga d'akin, sai wani ciccin magani yake.
Farhat dake zaune bakin gadon d'akin ta zabga tagumi ta d'ago kai tana kallonsa, yayin da wasu hawaye ke shirin zubo mata.
Kujera guda d'aya dake d'akin ya jawo ya zauna.
Farhat ta share hawayen kumatunta, murya a sanyaye tace, âyayana dan ALLAH kayi hak'uri, wlhy ina missing d'in families d'ina da karatuna, dan ALLAH idan kasheni zakayi ka kasheni kawai na hutama rayuwa ma ni gaba d'ayaâ.
Murmushi Nuren yayi, idonsa a kanta yace, âbazan kashekiba Farhat, dan bakimin komaiba, kamar yanda na sanarmiki mahaifinkine yaja miki, ki kwantar da hankalinki, insha ALLAH zaki koma gidanku kwana kusa, yanzuma dukba wannanba, wata tambaya nazo yimiki, ALLAH yasa zaki bani had'in kai?â.
Kanta ta jinjina masa tana kuma share sauran hawayen, âinsha ALLAH inhar nasani zan fad'a makaâ.
âgood girl â. âcewar Nuren yana gyara zamaâ.
âFarhat nasan kinsan duk yaran Abbanki ko?, ina nufin masu masa hidima a office ko a gida?â.
âEh nasan mafi yawansu, dan ina zuwa wajensa a Office, kuma wasu acikinsu sukanzo gidanmaâ.
âMasha ALLAH, kokin san SD?â.
âSD!?â.
âeh shiâ.
âgaskiya a yaran Abbana dana sani babu wani mai suna SDâ.
âokay, amma ko wani mai Something sunan dazai iya kasancewa full name bazaki iya hasasowa ba?â.
Shiru tayi ta lula duniyar nazari, shidai Nuren ya zauna mata idanu yana kuma jinjina ma ubangiji akan yin k'yak'yk'yawar hallita, dan Farhat black beauty ce masha ALLAH.
A jiyar zuciya ta sauke, âyaya inaga kamar dai akwai wani Sagir dauda dana Sani, amma bansan aikin da yake a k'ark'ashin Abbanmu ba, sai kuma ya Shareffudden k'anin Aunty Umma, sai Steven Danielâ.
âshi Steven d'in wanene shi a gidanku, itama Aunty Umman haka?â.
âDriver d'insu Mom ne, shike kaisu anguwa, ita kuma Aunty Umma matar Abbanmu ce ai, itace amaryarsaâ.
âUhyimâ. Nuren yafad'a yana jinjina kai.
âDan ALLAH yayana in tambayeka mana?â.
âina saurarenkiâ.
âlaifin mi Abbana yamuku hakane?â.
murmushi Nuren yayi, âkarki damu nangaba kad'an komai zai wuce, kuma bashi yay laifinba, wanine yayi na kusa dashiâ.
âto ALLAH yasa Ku kamashi, amma dan ALLAH karkuma Abbana komaiâ.
âinsha ALLAH babieâ.
Murmushi Farhat tayi, Nuren kuma ya mik'e tsaye idonsa a kanta. âbabu dai wata Matsala ko?â.
Cikin shagwa6ar data saba tace, âplease ko TV ka samin, banajin dad'in zaman hakananâ.
âAm sorry to say dear, har kibar gidannan dokace, babu television, babu phones, amma way not nakawo miki irin Hausa novels d'innan danaga mata na karantawa?â.
Idonta ya cika da kwalla, âayya yayana wlhy ban iya karatun hausaba sosai, yana bani wahalaâ.
Ido yad'an zaro waje, yace, âsaboda mi? Keba bahaushiya bacene?â.
âbahausa manaâ. âtafad'a cikin turo bani irinnan ta6ararruâ.
Baki ya ta6e yana kama hanyar fita, âzaki cigaba da kad'aicinki ashe kuwaâ.
Ganin zai fice da sauri tace, âplease ka siyo zan fara koya toâ.
âit's betterâ. âyafad'a yana ficewarsaâ.
Saman gadon ta fad'a ta fashe da kuma mai ban tausayi.
Duk abinda ke faruwa Galadima najin komai ta waya, Munaya ma na zauna a sofa har yanzu tana satar kallonsa, amma batajin miyake saurare da ya nutsu haka.
Cire wayar yafara k'ok'arin yi ya jiyo muryar Nuren na fad'in âhello brother kana jina?â.
Galadima yace, âehâ.
âokay duk kaji aimi ta fad'a ko?â.
âduk najiku, saika samin ido akan duk d'unsu, a bincikomin komai daya shafesuâ.
âindai wannanne insha ALLAH angama, amma ni a ganina banda wannan Shareffuden d'in datace, domin babu wani kamanni a cikin nashi sunan, ballema tace k'anin step mom nataneâ.
âHumm Nuredeen kenan, shifa mak'iyi ba'a rainashi, mutane da yawa sukan d'auki cinnaka ba komaiba, amma idan yacijesu sukan ji cizon har a ransu, dan haka karka ta6a d'aukar mage mafi sauk'i akan kare, itama idan taga nama citakeyiâ.
âwannan gaskiyane brother, ALLAH yabamu sa'aâ.
âamin ya rabbi, naji kuna maganar buks da ita, kaje ka samo mata dukkan Wanda take buk'ata, har English novels d'in, sannan ak'ara tanadar mata dukkan abinci mai k'yau datake soâ.
âinsha ALLAH angon Munayaâ.
Girgiza kai kawai Galadima yayi ya yanke wayar.
Kallon Munaya yayi suka had'a ido, saita janye cikeda basarwa. Shima tashi yayi ya koma gaban mirror, duk uzirinsa yayi ya gama sannan yamatsa ga wardrobe ya ciro kayan dayake buk'ata.
Ganin haka Munaya tazame ta kwanta cikin kujerar yandama bazata gansaba.
Baki kawai ya ta6e yacigaba da saka kayansa.
Bayan yagama yamatsa kusada ita, âtashi ki canja kaya ki rakani wani wajeâ.
Fuska Munaya tad'an yatsina, kamar zatace wani Abu saikuma ta yunk'ura zata tashi kawai, hannunta ya kama ya taimaka mata ta tashi zaune. fita yayi abinsa. Hakan yasata fahimtar zai jirata a falo kenan.
https://2gnblog.blogspot.com/
Bata 6ata lokaciba ta canja kayanta da atanfa skt da riga, takawo after dress ta saka sannan ta nad'a Vail d'in rigar, d'as ta fito itada cikinta, kamar ka saceta ka gudu abinka.
Tunda ta fito ya zuba mata idanu, ko k'yaftawa bayayi, saida yaga tana gabda k'arasowa garesa ya basar yana mik'ewa. Gaba yayi tabisa abaya, yandama yake taka steps d'in benen dolene ya birgeka, duk takunsa nakan idonta, yayinda itama take binsa daki-daki a hankali.
Babu kowa a falon, dan haka suka fice basu nemi kowanba.
A mota yana tuk'i da sauraren karatu itakuma tana latsa waya suna charts a families group d'insu. Sai murmushi take zubawa, duk abinda take yana kallonta ta gefen ido. Sun isa wani k'aton shagon saida kayan babies, duk abinda kake buk'ata zaka sameshi indai na yarane daga 1year zuwa 15. Itadai mamaki ya ishi Munaya, miye nawani kawota nan? yabari a haihun mana ma.
Tarba ta musamman aka musu, hakan ya tabbatar ma Munaya yasan mai shagon kenan, dan yanda aketa girmamasu sai abin ke bata mamaki. gashi indiyanci sukeyi bata fahimtar maganganunsu. Itadai tana zaune hankalinta ya rabu gida biyu, wajensu Galadima da kuma wasu mata biyu da yaransu uku dabazasu wuce 7-7years ba, yaran k'yawawa masha ALLAH, ga wayo.
Galadima ya juyo zai mata magana saiya lura da inda ta zubama idanu, shima shagala yay a kallon yaran, iyayensu na za6ar kaya amma su suna tibirewa sai Wanda sukeso za'a d'auka. Munaya sai zuba murmushi takeyi, dan suntafi da imaninta, shima murmusawa yayi yana lasar lips, kafin ya d'auke kansa ya maida ga Wanda suke maganar.
Zuwa can gardama ta hark'ume tsakanin yaran akan wani game da iyayen ke dubawa maybe zasu saya musu ne. Kuma games d'in suna kusada Munaya ne, d'aya a cikin yaran ya d'akko yazo wajen Munaya yana tambayarta wai âAunty wannan yafi dad'i aidai ko?â.
Munaya bata fahimceshiba, dan yayi maganane da yaren dabata ji, dan haka saitayi murmushi ta tambayesa yanajin English?.
Yaron ya d'aga mata kai alamar eh.
Ta kuma murmusawa, duk abinda ke faruwa a idon Galadima ne.
Da turanci munaya tace, âyarona kai kata6a irin wannan game d'inne?â.
Murmushi yamata shima, yace âaunty akwai dad'i ma sosai, ranar saida na cinye kharan a gidansu maâ.
âda gaske?â. munaya tafad'a tana dafa kafad'arsa.
Kansa ya d'aga mata, cike da d'oki yace, âAunty na koya miki?â.
Munaya ta d'aga masa kai.
Game d'in ya d'ora a cinyarta, ya danna wasu Number, sai kuma ya zubasu cikin d'aya, duk suka shige. Cikin mamaki munaya tace âmikenan to?â.
Shima dariyarsu ta yara yayi, yace âAunty ai wayo na miki, Abu guda d'ayane, amma sainayi ammafani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacalâ.
Sosai abun ya birge munaya, tayi dariya har hak'oranta na bayyana, jawo yaron tayi a jikinta ta rungume.
Iyayensa dake tsaye suna kallonsu tun d'azun duk sukayi dariya suma, sannan suka matsa kusada munaya suna bata hannu alamar gaisuwa. itama ta mik'a musu suka gaisa, d'aya tace sunanta Radha, d'ayar kuma tace Anjali, munaya ta fad'a musu nata suna itama, sannan takamo hannun saran yaran tana tambayarsu suma, d'aya yace vanish, d'ayan kuma Anjun, duk kumatunsu ta sumbata tana sakama rayuwarsu albarka.
Wadda tace sunanta Radha tace âkiyi hak'uri da surutun Vishnu shi baya gajiyane ko kad'anâ.
Munaya tace babu komai.
Daganan sukai gaba, munaya tana binsu da kallo tana murmushi, yaran sai waigenta suke suna d'aga mata hannu.
Sunje wajen biyan kud'i akace subar kud'insu inji mai shagon, da mamaki suka tambayi wanene? Mikuma yasa ya barmusu.
Mai kar6ar kud'i ya murmusawa yana fad'in mijin matarcan da kuka gaisane mai shagon ai.
Munaya batasan mike faruwaba taga sun dawo, godiya suka shiga yimata, ta tambayesu akan me?.
Suka bata amsa da cewar mijinta bai kar6i kud'in kayansu ba. Murmushi tayi, k'asan ranta tana mamakin dama shagon na Galadima ne?.
Sun katse mata tunani da tambayar kozasu samu number ta, babu musu tabasu sukayi sallama suka tafi.
Maida kallonta tayi ga Galadima dake zaune yanata latse-latsen laptop tamkar baisan mike faruwaba, da alama yana duba kayane ko wani Abu, dan time to time Wanda yake gefensa yakan nuna masa wani yanki na kayan dake shagon, shikuma ya waiga ya kalla, idan bai hango sosaiba saiya kalla ta cikin Computer d'in dake tareda cctv cameras d'in shagon.
Munaya tace kai mutuminnan akwai son kud'in tsiya, kai komai kana saidawa, wata zuciya tace idan bai nemi kud'iba dame zai kula da mahaifinsa?. âhakane kumaâ. ta fad'a a fili tana sauke ajiyar zuciya.
Kusan mintuna 15 saitaga ya taso ya nufota. Zama yay kujerar kusa da ita yana fad'in âsorry friend na barki ke kad'ai. kin gaji mu tafi ko?â.
Munaya tad'an yamutsa fuska tace âba sosaibaâ.
Ya d'an murmusa, âok tunda baki gajiba kozaki d'an mana taimako ni da abin cikin kwan?â.
Hararsa tad'anyi, itafa haushin wannan abin cikin kwan dayake fad'a takeji.
Hannu yasa ya dafe bakinsa yana fad'in âmaida wuk'arâ.
A tare suka dinga zagayawa cikin shagon, dayake babbane sosai, kayan yarane kuma zalla a wajen, komai bibbiyu take d'auka, baice komaiba, dan yasan dai bai wuce tana had'awa da cikin 'Yar uwarta Munubiya bane. Sund'an d'iba kaya babu laifi, yabada ATM d'insa aka d'auka harda na wad'ancan matan, yaran shagonne suka kai musu har cikin mota.
Yanzuma haka suka taho tamkar kurame.
Kowa da abinda yake sak'awa....
Danja data tsayar damune yasakashi juyowa yad'an kalleni, ganin hankalina nakan wasu yara 'yan makaranta dake mota yace, âdama haka kike da son yara?â.
Juyowa nayi Na kalleshi, amma saiya d'auke kai tamkar bashine yay maganarba ma.
Nima maida kaina nayi ga yaran, a kuma time d'inne muka sami damar barin wajen.
Saida muka fara tafiya nabashi amsa da âyalla6ai kenan, waye zaice baison yaro, a duniya babu abinda yafi k'uruciya dad'iâ.
Kad'an ya juyo yad'an kalleni yana fad'in âreally?â.
Nima kallon nasa nayi ina fad'in âna tabbata amsarnan kowama zai baka idan ka tambayesaâ.
Bai kalleniba yanzun kam, hankalinsa naga tuk'insa, yace, âALLAH ya kawoka duniya lafiya abin cikin kwanâ.
âshiru namasa bance uffanbaâ.
Har muka isa gida kuma babu Wanda ya sake magana a cikinmu. Saida yay parking motar a harabar gidan sannan ya juyo gareni, ina niyyar bud'ewa Na fita ya ruk'o hannuna. kallonsa nayi da mamaki, yawani ci magani irin babu raininnan, kamar zanyi magana saikuma nayi shiru muka zubama juna ido, kowannenmu zuciyarsa Na bugawa da sauri-sauri. Cikin k'asaitarnan tasa yace, âAddu'a nayi amma jan aji yahanaki amsamin da aminâ.
Ni dariyama ya bani wai jan aji, hakanne yasakani murmusawa kad'an ina k'ok'arin janye idona daga cikin nasa, amma saiya hanani hakan, nace, âna amsa ai, bakaji bane kawaiâ.
âaiba kurma kika aurabaâ.
Uhm wannan aure ana tak'ama dashi, Na fad'a a raina, a fili kuma nace, âa zuciya Na amsaâ.
âk'arya haramun, banji wannan sak'onba a tawa zuciyarâ.
Da mamaki Na waro idanu waje ina fad'in âban fahimceka baâ.
Lips d'insa yad'an ciza da hak'ora yana matsoda fuskarsa dab da tawa, gashi ya sark'eni da idanu nakasa matsawa, d'an yatsansa ya d'ora saitin zuciyata, muryarsa k'asa-k'asa tamkar mai rad'a yace, âzuciyoyi aminan juna sukan kar6i sak'on juna alokacinda d'aya ya aikashi ga d'aya, karki jahilci kanki har yanzu akwai sauran damaâ.....
Yana gama fad'a ya saki hannuna, tareda bud'e motar ya fice.
Galala nabisa da kallo tamkar wata sokuwa, nakasa motsi nakasa fassara zantukansa da ma'anarsu.
Tsawon mintunan dahar bayin gidan sungama kwashe kayan da mukazo dasu ban fitoba, bud'ewa naji anyi, hannunsa kawai ya mik'omin alamar nakama Na fito. tamkar sokuwa haka Na d'ora hannun cikin nasa, ya kamoni ahankali Na fito, maimakon ya sakeni saiya jawoni Na shige jikinsa, ya d'ora kansa a dokin wuyana, cikin kunnena yace âwasu bayanan basa buk'atar fassara, ayanda sukazo ahaka ake barinsu, karki zurfafa tunani, dan yana kawo ciwon kai da hana Hutuâ.
Ya d'ago kaina tareda janye jikinsa yana d'agamin gira da salute d'ina, ya juya zuwa cikin gida.
Binsa kawai nakeyi a baya tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki.
A falo muka iske duka ahalin gidan, har Momma dazata kwana yau a gida, Abba ne kawai babu, muduka sun birgemu, Dan hira suke ta nishad'i da girmama juna.
Dagani harshi gaishesu mukayi, Sauban da Samha dasuka k'arasa da kayanda da bayi suka shigo dasu suka sakko daga samanmu suna mana sannu da zuwa.
Ni kad'ai Na amsa, Galadima hannu kawai ya d'aga musu.
Momma tace, âkuje ku huta manaâ.
mik'ewa mukayi duk a kunyace, ina gaba a yanzu yana baya, suduka da kallon sha'awa suka bimu, dad'i da farinciki Na ratsa zukatansu, innarmu harda kwalla suka cika idonta, Wanda ita kad'ai tasan fasaarar kayanta.
â
â
â
â
â
â
â
Da daddare Galadima Na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda Munaya ke zaune a tsakkiyar gado tana karatun wani English novel na Galadima, buk d'in love story ne dan haka taketa faman zabga murmushi, lokaci-lokaci yakan d'ago ido ya kalleta, saboda idan tayi murmushi yakan jiyo sautinsa.
Maida kansa yayi, yacigaba da aikinsa dayakeyi akan numbers d'in layin Abba na sirri, kwatsam sai maganar yaron d'azu na shago mai suna Vishnu ta fad'o masa a rai.
*_Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'aya ne, amma sainayi amfani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal._*
Saida yakuma maimaita maganar kusan sau uku a ransa, kafin ya kalli Munaya da dukkan hankalinta ke kan Novel,
âFriend!â.
Ya kirata a nutse.
Da âna'amâ Na amsa ina kallonsa, saikuma Na janye saboda wandon jikinsa baiko rufe masa cinyaba, sai k'aramar riga mara hannu.
Yace, âmikika fahimta ga zancen abokinki na shago?â.
âabokina? waye abokina?â.
Tasowa yayi dagashi har laptop d'in da coffee d'insa ya hawo gadon, nima saina tashi zaune sosai.
Ya zauna ta gefe tareda ajiye mug d'in hannunsa a drowa d'in gefen gadon, laptop d'in kuma a saman gadon d'ayan gefensa. hannu ya mik'amin alamar nazo.
Ban musa masaba Na matso, ya kamoni ya sakani a jikinsa, dan tsakkiyar k'afafunsa ya sakani, saina zame Na kwanta na d'ora kaina a cinyarsa, (dama wajen lak'ewa nake nemađ€Ș).
Ya kar6i buk d'in hannuna ya ajiye gefe, ya d'ora hannunsa a saman cikina.
Kuma maimaita masa tambayar nayi.
Ya shafa sajensa yana cije lips, âmiyasa wataran kike da basarwaâ..
âni d'in?â. ânafad'a ina nuna kaina da kallonsaâ.
Bai bani amsaba yace âina nufin yaron d'azunâ.
âOh sorryâ. nafad'a ina gyara kwanciyat.
Nace, âwai Vishnu? â.
Kansa ya d'aga min
âto amma wace maganace tasa? tazama abin nazari yalla6ai?â.
âgameâ.
âgame! game!â nashiga fad'a ina k'ok'arin tunanowa.
âokay, wai yanda yafad'i yaci game d'in?â.
âUhhmâ. ya fad'a a tak'aice..
Nikuma saina murmusa, âto dukda dai bansan ma'anar d'aukar maganar da muhimmanciba amma anawa tunanin yana nufin _abinnan mabanbantane, amma saiyayi amfani dasu cikin Abu d'aya, kuma sukai masa aiki iri d'aya, sannan duk shi kad'ai ya sarrafasu akan Abu d'aya bawai yayi tarayyar da wasu mutane da yawa bane ko aikinsa had'aka,_ wannan itace fahimta ta ga zancen nasaâ.
Lumshe ido Galadima yayi, ya duk'o a hankali ya mannamin Sumba mai k'au a goshi. Sannan ya d'akko novel d'in ya damk'amin a hannu, yajawo laptop d'insa yacigaba da aikinsa.
Kallon mamaki kawai na zuba masa, kokad'an ban fahimci muhallin maganar tasaba da son fashin bak'i.
Batareda ya kalleni ba, idonsa akan system d'insa yace, âkallonfa?â.
Janye idona nayi ina ta6e baki.
Shima saiya ta6e nasa alamar yaganni kenan. karatuna nacigaba shima yacigaba da aikinsa yana shan coffee time to time.
Yayi aiki mai tsawo kafin yasaki wani murmushi da ajiyar zuciya, ya kalli munaya da barci ya kwashe, fuskarta ya shafa yana kuma sakin wani murmushin, âtabbas gaskiya Vishnu ya fad'a, mutum d'ayane ke amfani da Numbers daban-daban wajen kiran Abba munaya, duk wadda yagama da ita bazai sakeba, tagama aikinta, a wannan karon lallai kunyi aiki da basira, wadda harta birkita tunanin Sameer, kuna kiran Abba da mabanbanta Numbers wad'anda kunrigada kun gama shirya matakan da kowacce number bazata sake aikiba, shima kansa ya d'auka mutane daban-dabanne ke kiransa. O ALLAH wannan shine bada k'afa, to ai inkunsan wata bakusan wataba kuma, Muhammad Sameer ruwane, idan bakasha yanzuba zakasha anjima, idan kak'i kuma k'ishirwa ta kasheka. Inhar tarkon dazan d'ana zai d'annu dai-dai, tabbas zan cafke kurayen daji mai duhuwa a wannan karonâ. âYa k'are maganar da jan hancin munaya yana kuma sumbatar goshintaâ.
Kwanciya ya gyara mata sosai, ya ja bargo ya lullu6a mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala, kamar yanda ya saba ya raya wannan dare da nafilfili da godiyar ALLAH, kafin yazo ya kwanta gefen munaya zuciyarsa na cike da annashuwa da farinciki, kaikace komai yayi done ne.
Addu'a ya musu sannan yasakata jikinsa barci ya Lula dashi shima.
Nima mai d'aukar rahoto bara
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 47 Chapter of 90