Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
nan yadda ta baka shi kaima kaje ka jefar dashi ka hutawa kanka tonon silili. Kokuwa na tashi yayana na sanar dashi? To sai dai kuma haryanzu zuciyat nan nata kururuwa cikin kwakwalwata kai fa baka rabuwa da sakarci Wallahi mutumin da tuni mutanen unguwa sun gama zuzzuge kawun naka ana cewa yan iska ne ku yan shirin fim bakajin cewa idan yaganka da jariri zai iya tunanin ko naka ne aka kawo maka shi har gida dan bariki? Ai kawai ka dauki jaririn nan bakinka alaikum ka jefar dashi. Abinda yakama nayi kenan nace da kaina. Nasan dai yanzu babu jami'an tsaro akan tituna ballantana kuma mutane na mike tsaye cikin sauri ina mai fargabar kada gari ya waye min akamani da jariri dumu dumu ahannu. Wani zazzafan gumi yayi zarya tun daga kan doro wuyana har zuwa bayana. Kagafa hakane. Nace da kaina. Lallai kam mafita ta daya ce kawai na hanzarta na dauki jaririn nan na jefar dashi na huta in yaso daga baya na nemi uwarsa. Amma tabbas in har maganar ta fito fili to ko kawuna bai zargeni da komai ba sai mutanen sunyi ta yawo da zancen me yiwuwa ma wata rana yazama abin gori ga 'ya'yana. Akaro na farko tun bayan da akayi min kyautar jaririn sai naji sanyi sanyi araina. Kwakwalwata kuma tafara tunani sosai da sosai. Na nufi kofar dakin ahankali sannan na shiga falon. Na duba hanyar da zata kaika har bandaki saina girgiza kaina. Lallai budurwar tayi kyan dan maciji na wuce kai tsaye na nufi kofar da zata kaini har waje na budeta kadan. Sassanyar iskar dake ta faman watangarariya da kwayoyin ruwan dake zubowa adoron kasa daga sararin Subhanahu Wata'ala ta bugi fuskata yan sa'o'i kadan da suka wuce bazan iyayin maraba da iskar ba amma ayanzu saita zame min tamkar na'urar sanyaya daki alokacin zafi. Na juyo dakin cikin sauri na sunkuya abakin gadon sannan na tura hannuna na dauko katuwar rigar leda ta ruwa wacce azamanin danake tashe aharkar fim idan zamu tafi daukar shirin fim lokacin damina da ita nake fita. Koda na dauko rigar na karkadeta saina dorata akan rigar dake jikina sa'annan na fara balla maballin rigar bugun zuciyata yafara dawowa daidai ayanzu na sake sunkuya karkashin gadon akaro na biyu na dauko takalman ruwana nasa sannan na duba akwatin da mataccen jaririn ke ciki na tambayi kaina da cewa... To yanzu kuma ina zaka jefar da akwatin waje na farko daya fara zuwa zuciyata shine wani katon kango dake bayan gidan wani attajiri wanda ya saye ginin kwamnatin gidaje uku ya hadesu ya kera katon gida. Katon kango ne yadade ahaka an zagaye shi ba'a gina ko daki daya acikinsu ba. Lokacin damina kamar yanzu kangon cike yake da dogayen ciyayin tafasa da rai dore awani lokacin dan daya wuce zamanin muna yara acikin kangon muke bata lokaci muna wasan boyayyeniya idan mun taso daga makaranta. Bazan manta ba maciji ya taba cizon abokina Sani Ayuba acikin kangon. Nayi sauri na kawar da tunanin hakan daga zuciyata tabbas nan ya dace nakai akwatin. Na sunkiya ahankali na dauki akwatin mai tsaya wacce jaririn ke ciki na nufi kofar dakin cikin sauri. Koda na bude kofar dakin sainayi murmushin yake cikin duhun daren kamar awani fim din Daren mutuwa. Allah sarki jiya ba yau ba nace da kaina. Na dade akofar tsaye ina duban duhun daren ina tsammanin ko zanga wani dan motsi. Daga karshe dai sai...... ALAKAKAI-07 . Na dade a kofar tsaye ina duban duhun daren ina tsammanin ko zanga wani dan motsi daga karshe dai sai na saduda naga tsoro da fargaba basu amfana ta awannan lokacin sai kawai na jefa kafata waje na shige cikin ruwan ina mai Addu'ar Allah yasa duk wanda muka hadu dashi yayi kuskurena a matsayin jami'in tsaro. Naci gaba da tafiya ruwan saman dake zuba kamar da bakin indararo sai dukan bayan rigata yake fas fas. Duk dayake dai nayi sa'a duk kusan bangaren gidajen an dauke wutar lantarki amma Hakan bai bani kwarin gwiwar fitowa nayi tafiya kai tsaye cikin takama ba Ina tafiya ina bin inuwar bango kamar Kadangare wata sa'ar ko Walkiya akayi sai na rabe kadan kafin naci gaba da tafiya. Ina nan tafe lokaci guda kuma duk Addu'ar da Tazo bakina sai in karanta... Kwatsam sai nafara hango gidan attijirin tsakanina da gidan akwai yar tazara kafin ka kai ga kangon dake jikin gidan saikayi tafiya cikin wata yar farfajiya wacce babu gine gine a cikin ta sai ciyayi haka nan kuma anan filin wasan kwallon kafa na samarin Unguwar yake. Gabana ya fadi sa'ar dana hango fitilun lantarki naci a kofar gidan dakuma kan katangar reras dasu kamar taurari tabbas injin wutar lantarki ya kunna. Ganin hasken ne ya sani sauya shawara na kauce nabi wata yar siririyar hanya wacce ta ratsa ta cikin filin wasan kwallon kafar takuma bi ta bayan gidan attijirin zuwa cikin kangon da nake hari. A daidai lokacin ne to najiyo sautin abin da ya kusa sa akwatin dake hannuna ta subuce.... Ko shakka babu mutum ne abayana. Nayi mutuwar tsohuwa a tsaye tsoro da fargaba suka hanani juyawa. Wani abu ya dunguri dunduniyar takalmina na dauke numfashi cak ina kokarin zama gunki har yanzu wanda ke bayan nawa bai ce Dani uffan ba sannan ne to naji wani gurnani abayana marar dadin ji Gashin jikina ya mimmike tsaye kamar gashin bushiya tuni wani zazzabi zazzabi yafara kokarin rufeni nayi ta yan maza na juya a hankali na dubi bayana sai mukayi ido hudu da bawan Allah mai bakaken idanu kamar ifritu yana gurnani wani dankareren kare ne mai jajayen idanu da zako zakon hakora kamar tarko babu alamar farin gashi a jikinsa. Wani katon kare ne ya kwada min uban haushi WAWWAN Nayi tsallen gefe guda sai yakawo min sura santsi ya kwashe ni nafada cikin cabin ruwan nagama gigicewa maimakon na Jefar da jakar saima na sake mikewa tsaye da ita kankame a kirjina kai kace wasu makudan kudade ne aciki. Mukayi tsaye cirko cirko nida karen ya dube ni na dube shi saina juya da gudu karen kuwa yace da wa Allah ya hadashi bada ni ba. Tun kafin tafiya tayi nisa karen ya fara kawowa dunduniyata sura. Allah ya taimake ni da takalman ruwa a kafata akaro na biyu ne ya sami Nasarar farka rabin rigar ruwan dake jikina. . Wayyo Allah. Na kwalla ihu na manta da abun da ke dauke a hannuna na sake juyowa a firgice na kaiwa karen duka da jakar dake hannuna Saidai kuma dukan na matsoraci ne domin bai iya kwantar da ko da yar budurwa ba ballantana mahaukacin kare alokacin ne to TAFARU TA KARE. Wani abu mai kamar guduma ya sulalo ta cikin duhun daren ya daki tsakiyar kaina kafin na gama warwarewa sai wani abu kuma mai kamar katakon duka ya daki bayana naji kamar an soke ni da mashi. Wayyo Allah na kwalla ihu. Zakayi ihu ma sai agaba shege barawo. Me ka sato acikin akwatin? Wata kakkausar murya tace dani daga cikin duhun daren.... . ********* *********** ******** . Adaidai lokacin dana sulalewa zan fadi acikin cabalin ruwan ne sai wani busashshen hannu mai kamar iccen makera ya cafi kwalata ya dagoni sama da karfin tsiya ya girgizani. Me ka sato aciki Barawo? Aka sake tambayata akaro na biyu sannan sai busashshen hannun ya damki makwogorona. Idan baka fadi abinda ke cikin akwatin nan ba kasheka zanyi shege azzalumi kudin wa ka sato? Wallahi ba kudi bane.. Nace dashi cikin karaji. Uwarka ce to aciki? Shege Allah ya tona asirinka kananan barayin unguwa daman jira kakeyi afara ruwa saika biyo dare ka dauki wannan ka zari wancan kamar mayen karfe ko? Haryanzu ba'a daina tsuga uban ruwan saman ba na hadiye yawu da kyar ba karamin riko yayiwa makoshina ba dakyar nake numfashi gashi ya daga hancina sama ruwa sai shiga yakeyi kamar bututu. Busashshen hannun ya dada girgiza ni zuciyata sai harbawa takeyi Tam Tam kamar tamaula tsakanin hakarkarina akwatin kankame akirjina na san idan na sake ya bude akwatin kashina ya bude. Daureka zanyi yace dani yau Allah ya toni asirinka bazan buda akwatin daka sato ba amma da zarar gari ya karasa wayewa zan mika ka ga hukuma. Mutumin ya tura ni riki riki da akwatin ahannuna muka nufi katon gidan attajirin nan mai katanga dauke da fitilun lantarki burjuk kamar hasken rana. Mutumin yaci gaba da jana kamar mushe rabi ina tafiya rabi kuma kafata na jan kasa kamar kafar gawa. Wani lokacin idan aka kwantsama aradu mai karfin gaske sai mutumin ya dan dakata da jana yace. Shege dama ta fado maka azzalumi. Nayi mamakin ko wanene azzalumin tsakanina dashi. Bayan wasu yan tsirarrun mintuna muka kawo ga kofar gidan attajirin nan. Na dubi dankareren gidan kana na dubi yan mitsi mitsin kwayoyin ruwan dake ta zubowa bila adadin daga sararin Subhanahu Kamar hazo lokaci guda kuma na juyo akaro na farko nayiwa mutumin kyakkyawan kallo. Banyi kuskuren fasaltashi cikin zuciyata ba. Domin kamar dai yadda nayi tunaninsa haka nan yake saima abinda ya dadu kato, baki, jajayen idanu, fankaceciyar kafada, kamar kofar shagon kasuwa. Abin dayafi bani mamaki ga halittarsa shine duk da girman jikin nan nasa kansa dan kankanine haka kuma fuskarsa tsukakkiya ce fatar bakin siririya kama an tsaga wanda da tsinin wuka. Koda ya dada fizgata muka dada matsawa daf da kofar gidan sai tangamemiyar kofar ta bude wasu dogayen mutane suka fara fitowa daya bayan daya har suka zama su uku. Basu damu da ruwan da ake kwararawa ba. Mutanen uku duk Buzaye ne sirara masu dan rakeken wuya kamar kasan almakashi ka dauke. Kowannensu dauke da dakon katon rawani kamar mushen tunkiya rike da takobi tsirara. Wa Allah kuma ya hada ka dashi MAMUDA? Daya daga cikin masu gadin ya tambayi katon mutumin dake tike da wuyan rigata. Irin yan kananan barayin unguwannin nan ne dake damun unguwa da yan sace sace yanzu ma dubunsa ce ta cika na zagaya cikin ciyayin can sainaji DUNA yana haushi nakai masa agaji nakamo wannan karamin marar kunyar. Yana gama fadin haka saiya hankadani gaban buzayen da karfi na fadi ricaaa agabansu. . Wannan akwatin fa dake rungume akirjinsa? Buzun maigadin ya tambaya ban budata ba babu ruwana da abinda ya sato ku barshi kawai idan gari ya waye saimu mika shi ga jami'an tsaro domin irin kananan barayin nan annoba ce ga al'umma dan irin su ne idan suka rika sai su zama yan fashi da makai. Yasa kafa ya daki Duwawuna da karfin gaske na kwalla kara. Au dan dan wannan ma? Ai somin tabi ne kawai na baka ladan kamu ne saima gobe idan kaje hannun yan sanda kayi mai dalili Ya fashe da dariyar mugunta. Ku jefa min shi cikin dakin injin bada wuta yace da buzayen. To! Suka amsa baki daya sannan kowa daga cikinsu ya kama inda yafi rainawa ajikina sukayi sama dani kamar gadon kara suka nufi cikin gidan dani. Kada ma ku damu kanku da sai kun daure shi kudai ku kulle shi kawai aciki karamin barawo ne babu abinda zai iya yi. Suka karasa dani kofar wani dan daki dake manne ajikin bangon gabas na farfajiyar gidan dan dakin kusan duk akere yake da shuke shuken furannin alfarma haka nan duk farfajiyar gidan. Nayi bakin ciki domin duk da mummunan halin danake ciki basu barni na kashe kwarkwatan idanuna ba. Muna isa kofar dakin sai suka ajiyeni akasa biyu daga cikinsu suka rikeni yayinda dayan ya bude dakin jannaretan nan da nan karar injin dake cikin dakin gamida hayaki suka gauraye gurin. Anan zaka kwana in kuma kaso ma to kana iya sace injin gaba daya duk ribar kafa ce wai giwa ta taka kwado. Suka jefani cikin dakin kaina ya bugi jikin injin. Sannan na mirgina gefe guda ina murkususu. Masu gadin suka mako kofar garam!!! Sannan naji karar kwadon sun kulle dakin. . Na tashi zaune ahankali dodon kunnena kamar zai fice saboda karajin inji sannan kuma idanuna kamar zasu fito waje saboda hayakin injin dake shigo min. To amma fa duk wannan bai sa na jefar da akwatin dake rungume a kirjina ba ALAKAKAI-08 . Na tashi zaune ahankali dodon kunnena kamar zai fice saboda Karar injin sannan kuma idanuna kamar su fito waje saboda hayaƙi injin dake shigo min. Toh amma fa duk da irin wannan wahala baisa na jefar da akwatin dake rungume a kirjina ba na yunkura Dakyar sannan na nufi kofar kofar dan karamin dakin injin bada wutar lantarkin adaf da kofar dakin akwai wasu yan kananan tagogi ajere reras guda shida don haka ina Karasawa ga tagogin Saia tura hannuna ta cikin kofar daya daga cikin yan kananan tagogin hakan danayi shi ya bani damar shakar tsaftatacciyar iska sannan kuma sassanyar iskar ruwa ya bugi fuskata nan da nan naji na dan fara dawowa hayyacina akusa da kofar dakin daga hannun hagu akwai wai katon duro na mai. Na matsa kusa da durom din na ajiye akwatin akai na jingina dashi sannan kuma wani lokaci guda fuskata na cikin yar Jafar tagar ina shakar iskar tsaftatacciyar iskar ruwan Saman ahaka ko barcin gajiya ya dauke ni. Bansan iya sa'o'in dana share ina barci ba Nidai kwatsam ba zato ba tsammani sai ji na nayi nadaku da kasa. Sannan naji wani abu ya Fado min awannan sa'ar na tashi firgigit cikin tsoro sannan ne to na fuskanci ashe barci ne ya daukeni a tsaye harna ture durom jakar dana ajiye da kuma akwati. Na tashi tsaye da kyar jikina na rawa ga mamakina sai Naji gidan yayi tsit wannan shi ya tabbatar min da cewa an Dade da dauke ruwan saman acan wani bangare kuma na Unguwar nasu wani ladan mai zakin muryar gaske yana kwada kiran sallah asuba tayi nace a zuciyata kashina kuma ya bushe kenan. Na sake cewa a zuciyata Daman nasan da gari ya waye marasa imanin masu gadin nan zasu Mika ni hannun yan sanda shin anya kuwa haka zata yiwu? Yafa kamata ka motsa ko zaka samu hanyar tsira wata zuciya tace dani. Na nufi kofar dakin ahankali kafata kamar zata balle saboda ciwo nasa hannuna a jikin kofar na dan jijjigata sannan ne to naga kofar dakin......... Karshen abubuwan........ Ne. . Karfe da gilashi kuma gilashin dake daf da inda nake masakalin dan makullin yake a daya sakon. Nan da nan zuciyata tafara harbawa inama ace zan iya murde dan makullin na ce da kaina. Namika hannu naji hannun ya taba kwadon dakin kamar wasa sai kawai naji kwadon ga mamakina ya bude gumi yafara sarara agadon bayana sannan ne to wata zuciyar tace dani shashasha mai gadin bai balle kwadon ya shiga daidai ba. Nan da nan na murde kwadon na tura shi sama sai ya fadi can kasa Tim. Jikina kamar mazari na rawa na dauki akwatina sannan na tura kofar ahankali sai ta dan bude nayi shiru ina saurare ko zanji motsi shiru babu motsin komai sainaga hanya yakin bishiyoyin gidan da iska ke kadawa banyi mamakin jin shirun ba domin nasan hankalin masu gadin a kwance yake tunda dai a tunanin su ina nan a kulle abu na farko da ya fara zuwa zuciyata shine hanyar da zan bi na tsere to Saidai kuma tuni na tabbatarwa da kaina cewa bashi yiwuwa na tsere ta kofar da suka shigo dani idan nayi gangancin bi ta kofar to kamar na tura kaina ga halaka ne da gangan. . Tsakanina da inda dakin yake dakuma tangamemiyar kofar gidan yake akwai tazara don haka sai wata zuciya tace dani tunda dai kofar bata biyuwa me zai hana ka lallaba ta cikin duhun shuke shuken da suka kare dakin ka zagaya ta baya? Nan da nan sai na koma ina mai amincewa da shawarar zuciyata tunanin daya fara zuwa min shine na zagaya bayan gidan saina haura katangar indira cikin tsohon kangon dake makwabtaka da gidan wanda Daman tun farko anan nayi niyyar jefar da akwatin mai JARIRIN. Na tura kofar dakin ahankali sannan na fito waje. Sannan ahankali ina bin lungu lungu sako sako dake cikin shuke shuken har na kawo ga ginin gidan adaidai lokacin to naga yar siririyar hanyar data bi ta bayan ginin dakunan gidan har zuwa katangar arewa wacce itace ke makwabtaka da gidan. Fasalin ginin dakunan gidan irin Fasalin nan ne da zaka iya ginin dakunan su kadai ne a tsakiyar gidan batareda an jingina koda gini daya da katanga ba wannan shi ya baiwa rufanin damar yin yado ajikin katangar hakan nan kuma yan dukur dukur fitilun alfarmar suma suka kai kusurwar katangar kudu ta gidan abin gwanin ban sha'awa me yiwuwa hakan ce tasa akayi ginin tsakiyar gidan batareda an jingina shi da koda katanga daya ba. . Na lallaba ahankali kirjina na Dakan shida shida na bi yar siririyar katangar ta tsakanin shuke shuken na nufi katangar. A daidai lokacin ne to sainaga tagar daki ta bude nayi sauri na sunkuya acikin shuke shuken dake daf da tagar kadan ya rage tagar dakin ta buge min kai domin jikin ginin dakin nake bi bantaba zaton za'a bude tagar din ba haka nan shiyasa ni tunanin ko na koma da baya na sake hanya domin a baya na akwai jerin wasu tangagogin har guda biyar kafin nakai ga katangar danake hari. Bangama shawara ba sai na sake jin abin da yasa zuciyata harbawa da karfin gaske. Wata shakakkiyar muryar magidancin mutum tace..... Ke FADILA tashi munafuka INA KIKA JE DA DADDARE naji shiru na dan lokaci sai Naji an sake cewa Ke ba ke Nake yiwa magana ba? Shiru ba'a amsa ba can sai Naji an amsa BABA NI WALLAHI BABU INDA NAJE........ Jin muryar shi yasani mikewa zumbur kamar wanda aka sokawa kibiya na sake saurarawa dakyau To don iyayen ki ni zakiyiwa karya ina kallon ki fa jiya ana wannan ruwan kika fice dauke da akwati a hannun ki Ina Kika kai akwatin ina kuma kika ajiye motar da kika dauka? Wani abu mai Kamar gizo gizo ya biyo tun daga babban dan yatsana har zuwa bayana. Bab...... Don Allah tafara kuka na Mike tsaye ahankali na leka tagar dakin sannan ne to naji numfashina ya dauke ko shakka babu yarinyar data bani kyautar JARIRI NE . Tana zaune abakin gado ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta gashin kanta awarware wani katon mutum ne dattijo tsaye akanta sanye da babbar riga bana raba daya biyu mahifinta ne. Naci gaba da saurarensu jikina na rawa. Ina kika kai jaririn munafuka? Mutumin yace sannan ya matsa kusa da ita ya gaura mata mari tas ina kuka kai jaririn iye? Wato jefar dashi kukayi ko? To zakici gidanku.... Yau daga ke har shegiyar uwarki data bataki sai kun fice min daga gidana ke kuwa ahannun yanda zan mika ki. Kai Allah wadaran haihuwar irinku haihuwar bakin ciki. Adaidai lokacin ne to naji budewar kofar acan cikin dakin. Kada ka zageni. Wata sassanyar muryar mace tace duk abinda yafaru akan FADILA kai ka janyo ai sai da nace dakai kada ka riga sakarwa fadila kudi tun tana karama nayi nayi dakai ka ki kasai mata mota har guda uku don shagwaba har kasashen turai kake tafiya da ita tokuma shin ayanzu don.....idonta ya bude da iskanci har ta sami nasarar ba wa... DAN GWARZO shine kuma zaka zargeni ? Matar tayi shiru tana maida numfashi ai saida nace dakai a zubar da cikin ka ki yo kuma yanzu don ta haifi dan ta jefar shine zaka zo kahauta da duka ka dagata don Allah Alhaji kada ka kashe min 'ya ba fa taka bace kai kadai. Mutumin ya dubi matar a fusace yace. Allah wadaranki Wallahi nima kaddara ce tasa na aure ki rabon dai in sami wannan tsinanniyar yarinyar da zata janyo min abin kunya agari kema kafin na aure ki ciki nawa kikayi aka zubar? To kace ma fadilar ba 'yar ka bace mana. Matar tace a fusace nan da nan sai maigidan ya sake shake yarinyar yahauta da duka. Wayyo Allah baba na shiga uku fadila ta fada cikin kuka. Baki shiga uku ba ma tukunna sai ma na dora wuka a mokogoronki don ubanki. Ina kika jefar da jaririn. . Batare da na sake jiran komai ba sai kawai na dauki akwatin na koma... Da gudu ban damu da ko masu gadin zasu ganni su sake kamani ba. Ina zuwa saina nemi kofar shiga babban falon na tura kofa na shiga bayan nayi yan dube dube saina jiyo hayaniya awani daki. Hakan shi ya bani damar gane cewa shine dakin da nake nema. A ina kika jefar da jaririn? Ya sake tambayarta banyi watawata ba saina tura kofar na fada cikin dakin babu sallama. Gaba daya mutanen uku miji da mata dakuma 'ya suka juyo a firgice suka dubeni kamar wani Aljani. Kayi hakuri alhaji da shigowata babu sallama. Nace dashi. Zuwa nayi na ceci ran 'yarka domin ba sai ka dora wukar a makogoronta ba. Ga Jaririn nan bai yi nisa ba dazun nan tayi min kyauta dashi amatsayin kyakkyawan jaruminta na shekara. Nayi musu murmushin yake su kuma suka dubeni saroro kamar wadanda suke tunanin na tabu. Na ajiye akwatin agabansu sannan nace. Jaririnta yana cikin nan yana barci ni zan koma Alhaji saidai kuma don Allah kayiwa masu gadin nan magana domin su Barawo suka kamani jiya da daddare adakin injin dake baku wuta na kwana. Allah ne ma yasa zan raba wannan rikici shiyasa na fito. . Karya yake Wallahi baba shine ya sace jaririn wallahi shi ya sace min fadila tace. Yi min shiru munafuka mutumin ya buga mata tsawa na dubeta nayi murmushi sannan na lalubi aljihuna na dauko wasikar datayi min na mikawa mutumin nace. Duba min nan Alhaji shin wannan rubutuna ne ko nata? Ni sauri nakeyi domin muna da fim din da zamu fara idan an jima. Idan kuma kana bukatar karin bayani to saurareni da kyau. Mutumin ya amshi wasikar daga hannuna nikuma saina dubi Fadila itama ta dubeni nayi mata murmushi nace. Kadan ya rage ki kai labari yan mata to saidai kuma kyautar da kikayi min tayi girma dayawa. In banda abinci ina ke ina yi min kyautar Jariri? Ai tayi min yawa ina laifin ma ki bani Kyautar KWALBAR TURARE KO FULAWA Adaidai nan naji sautin sawun masu gadin suna ta guje guje atsakar gidan. Lafiya meye haka? Mutumin yace yana dubana nayi masa murmushi nace dashi kada ka damu masu gadinka ne suke nemana. Fadila ta daga kai idanunta cike da kwalla tace. HILAL nace Na'am FADILA Tace don Allah ka yafe ni. Na dubeta na tsawon dakiku sainaji tausayinta ya kamani saina dubeta da tattausan murmushi nace. Na yafe miki Fadila saiki nemi kuma gafara agurin Ubangijinki dakuma mahaifinki. Fadila ta fashe da kuka. Adaidai lokacin ne masu gadin suka kwankwasa kofa. Ku shigo nace dasu. Waya saka? Mutumin yace dani na dubeshi nayi masa murmushin ko in kula. . BABI NA HUDU 4 . Kusan minti guda muka share tsaye muna duban kofar kodayake fadila bata kallon kowa sai ni. Kofar dakin ta fara budewa ahankali kamar iskace ke turota sannan sai kakkausar muryar kartin nan tace. Salamu Alaikum....Alhaji mu shigo ne? Mahaifiyar fadila wacce ke tsaye rike da tsantsa tana huci kamar kububuwa. Mamuda ne? Shigo kai kadai. Maigadin yace bakinsa na rawa Garsakeken katon ya shigo dakin cikin sanda yana zuwa saiya dubeni ya rusuna agaban maigidansa yace. Kayi hakuri don Allah Alhaji Wallahi adakin injin bada wuta muka sashi ya gudo. Bari inyi waje dashi na hada shi da yan sanda. Yana gama fadi saiya yunkuro ya DAMKE NI............ ALAKAKAI-09 . Yana gama fada ya yunkro zai Damkeni... . Uhm Uhm mamuda kada ka taba shi. Maigidan yace cikin karaji. Mamuda yayi cak kamar ruwa ya cinye shi. Alhaji barawo ne... Kada ka damu mamuda jeka waje kaci gaba da aikinka kawai. Toh yallabai katon yace cikin girmamawa lokaci guda kuma ya nufi kofa. Af mamuda... Maigidan ya kira sunansa katon ya juyo cikin sauri na lura duk a rude yake me yiwuwa tunda yake gadi agidan bai taba shiga wannan dakin ba. Wannan maganar daga kai sai mu ka. Kafadawa abokan aikina ma bana so ta wuce tsakaninku. Kakuma kawo min akwatin daya bari adakin injin wutar. Katon ya gyada kai cikin fahimta sannan saiya dubeni. Kallon dayayi min na iya nufin komai. Nayi masa murmushi cikin sanda ya juya kamar yadda ya shigo ya sulale daga dakin. . Muka sake yin shiru na tsahon mintuna akaro na biyu mahaifin fadila na kallon tattausan kilishin dake dakin yayinda fadila ke kallon. Nikuwa idanuna na kallon mahaifiyar fadila wacce ta kurawa fadila idanu bata ko kiftawa. Azuciya na yarda da maganar mahaifin fadila dayace da mahaifiyarta tun farko itace ta bata fadila domin na lura da alamun damuwa karara a fuskarta dakuma kauna ga fadila yarta. Ku shiga daga ciki RASHIDA. Maigidan ya kira sunan matarsa akaro na farko. Nayi zaton zata hau masifa amma maimakon hakan saita dubi Fadila tace. Taho mu tafi. Fadila tayi min kallon gefe idanu tabi mahaifiyarta suka bi ta wata yar tsukakkiyar kofa suka shige ciki. Maigidan ya dubeni gamida sassauta yanayin dake fuskarsa yace. Zauna bawan Allah ya nuna min kujera araina sainaji na kaunace. Hakan shi yasa nayi biyayya na zauna batareda nayi jayayya ba. Ya danyi shiru gamida sakin wani tattausan tari kana sai ya dago kansa.. . Tun tana karama muke fama da ita kadarar yarinya ce ka ganta nan gashi da babu abinda ta rasa agidan nan na daga kayan alatu amma bata iya zama sai shegen yawo. Mahaifiyarta ce ta bata tun tana karama.... Yayi shiru akwai alamar takaici karara a fuskarsa. Na tausaya masa. Babu daman nayiwa yar cikina fada sai mahaifiyarta ta hauni da masifa. Haka kullum nake fama kwatsam ran nan sai muka fahimci yar banzar yarinyar tayi ciki mahaifiyarta tayita uzura min sai a zubar da cikin. Nikuma ina tuna mata yin hakan barna ce domin kisan kaine saimu bata goma biyar bata gyaru ba. Haka mukayi ta fama har zuwa ranar data haifu shine yanzu don tsabar rashin imani suka hada baki ita da mahaifiyarta suka kashe dan jaririn wata daya kawai da haihuwa....hawaye ya fara kwarara akan fuskarsa. Na yunkura akan kujerar cikin damuwa ni duk maganganun sun fara gundurata duk da dai basu shafeni ba ni abinda kawai nake so shine yabar ni na tafi dan na lura tuni har gari yafara haske. Duk da yake banga agogo ba ina kyautata tsammanin biyar na safe ta wuce. Fita fim dinsu Alhajiji ne araina. Alhaji.... Allah ya sawwake.. Nace dashi ina ganin in babu wani sauran abu to ni zan tafi alhaji domin kaga duk wannan abubuwan da kake fada bai kamata na sani ba domin sirrinku ne ku kadai bai shafe ni ba. Mutumin ya dago kai yana girgiza shi. Ya shafe ka bawan Allah. Awannan karon ni na dube shi cikin mamaki. Tayaya ya shafeni? Mutumin ya sunkuyar da kai na tsawon lokaci yana girgiza kai. Can saiya dago alamar damuwa a fuskarsa a fili. Ga mamakina sainaga ya mike tsaye ya nufo inda nake ya sunkuya akaina ya dafa kafadata yace. Bantaba neman alfarma agurin kowa ba tun da nake.... Amma yau zan fara. Abinda yace sai ya daga rudani. Ban fahimce ka ba. Ya daga girarsa sama kamar biri na lura karfin

Chapter 3 of 5