Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
sake kwankwasa kofar awannan karon da karfi. jin haka shiyasani tunanin komai bugun kofar kafadarsa ya jingina ajikin kofar yake kokarin balle kofar dakin. Nan da nan nayi wuf na zare sakatar dakin na janyo kofar da karfi. Sai naji sakayau kamar na janyo gadon kara babu abin da yabiyo baya. . Ashe dai ko agaske jarumi ne wata zazzakar murya tace dani Nayi sororo ina duban abin haushin dake tsaye akofar dakin cikin mamaki daya sani wangame baki fayau ina dubanta Atsaye abakin kofar sanye da bakar riga doguwa da jan lullubi jikinta na digar ruwan saman daya doke ta, wata mace ce ajin farko a jerin kyawawa. Shin ko na iya shigowa, sanyi nakeji gaskiya, gashi kuma duk kayana sun jike Na sake kallon katuwar akwatin mai taya dake hannunta na dama Nace Malama Lafiya? Daga ina kike Meya kawo ki gidana cikin wannan daren? Ta dubeni sannan ta jefeni da wani lallausan murmushin Allah kashemu dan dadi, tace Lafiya kalau HILAL ,daga wata nisan duniya na tawo domin kawai na ganka, na dade ina ganin finafinanka ina kaunarka raina na Begen ganinka. Shine naga bazan iya jurewa ba sai nazo naganka tun daga maiduguri Nake motar mu ce ta lalace ahanya shine mukayi dare yanzun ma direban motar ne yaga nayi dare shine na roke shi yakawoni nan , Tayi shiru tana dubana. Jarumi Hilal, Ina fatan yanzu dai ka gamsu Shin na iya shigowa, sanyi nakeji wallahi Hilal. Na matsa gefe guda ta shigo cikin dakin zuciyata cike da tunane tunane ta ajje akwatin atsakar dakin sannan tajuyo ta dubeni. In bazaka damu ba dan Allah nunamin inda bandaki yake so nake na shanya kayana duk sun jike jagaf. To ke kuma ki zauna dame Ina dubanta baki bude Tayi murmushi Sai na zauna aciki idan sun sha iska saina mai dasu jikina nafito, Sannan fa takura min idanu tana dubana ko kiftawa batayi Oh Hilal yau dai Allah ya nunamin kai wallahi kada kaga irin son danake ma duk cikin yan wasan hausa babu wanda nake kauna kamar ka zakayi mamaki idan nacema acan maiduguri akwai kawayena da suke kirana da suna HILAL tayi shiru tana dubana me yuyuwa koh dan ganin duk surutun da takeyi ban tanka mata ba Hilal yaya kake yimin irin wannan kallo ne, koh haryanzu baka amince dani ba? Bahaka bane malama amma abin dake bani mamaki shine zuwanki cikin wannan tala-tainin daren kuma...... Ta katseni. Nace dakai motar muce ta lalace, Haba Hilal nifa bakuwar kace. To naji na yarda amma kuma yaya akayi kika san gidana. Haba hilal Mutane nawane suke ziyartarka arana daga jihohi daban daban kawayena nawa ne suka zo gurinka ai kwatancen gidanku ba wuya tunda agidajen gwamnati kake ga kuma lamba daman kuma ance kai kadaine abangarenka daban amma kada ka zargeni agurin maziyartanka naji. Mukayi shuru muna duban juna sannan sai tasake cewa Nunamin bandakin Hilal kada mura ta kamani da wannan jikakken kayan jikin nawa. zo muje nace da ita na shiga gaba tana bina abaya Bandakin gidan acan baya babban falon yake saidai kuma zaka iya shiga bandakin tacikin falon akwai kofar dazata kaika ciki Ga kofar nan Nace da ita ina duban yala-yalan gashin kanta Hakika kyakkyawace ajin farko ta dubeni sannan ta sake jifana da murmushi ta shige bandakin ta rufo kofar gararamm a daidai lokacin ne toh aka saki wata aradu Rugugugu.. MASU KARATU KUYI HAKURI DA WASU YAN KURA KURAI DA ZAKU CI KARO DASU TUN DAGA NA DAYA ZUWA NAN DAMA GABA KADAN TAYANDA WASU SHAFUKAN ZAKU GA NA MAIMAITA SU KUMA HAKAN YAFARU NE SABODA WASU DALILAI NA KUSKUREN RUBUTU DANAYI TUN A FARKON LABARIN KUMA ZAIYI WAHALAR WARWAREWA SAI AKASHI NA 5 ZAREN LABARIN ZAI DAWO DAIDAI NAGODE. AMMA INA NEMAN AFUWAR KU . Na sake mikewa tsaye akaro na biyu naci gaba da safa da marwa cikin dakin. In har ba dauke ruwan akayi na bude tagar dakin ba zaiyi wuya in zan iya barci. Banda wannan kuma al'amuran da suka faru ma a yammacin ranar sun isa su hanani barci na daga kaina na dubi agogo karfe daya na dare daidai. . Sa'ar da muka baro kamfaninsu alhajiji (Sinad Production) sai Lauriyya tace saita rako ni har gida. Kiyi hakuri lauriyya kinsan yanzu ba kamar da bane sa'ar danake agidana yanzu kinga agidan yayana nake kare. Duk da yake dai bangarena daban ne to amma fa mutanen unguwa sun gama sa min ido dan sanin kanki ne duk yan fim yan isa aka daukesu ana son mune ana kuma kyamar mu. Lauriyya ta fahimci abinda nake nufi. Toh hilal sai gobe din kenan ma hadu. Kada ka manta fa da asussuba alhajiji yace zaku fita.... Na dubeta cikin murmushi ban taba sonta har cikin zuciyata ba kamar wannan ranar. Dan haka sa'ar dana fara zirga zirga acikin dakin inata lissafin dimbin basussukan da suke kaina sainayi mamakin irin tsabar son da lauriyya takeyimin. Kafin naci gaba da labarin nan danake baka bari in baka hoton lauriyya. Dakuma ranar da muka fara haduwa da ita domin lauriyya tana da matukar muhimmanci acikin labarin. . LAURIYYA doguwa ce launin kofi mararta ashafe siraran yan yatsun kafarta da na hannu gami da dan madaidaicin bakinta ma'abocin tattausan murmushi tare da taimakon dara daran fararen idanunta gamida dogon hancinta mai kamar kan biro su suka fallasa kyawun da ta gado daga kakanninta fulani mazauna Gongola. Haduwar mu da ita tsautsayi ce domin adaren wata juma'a ne nafito daga ofishina mukayi kicibis da ita dauke da jaka kallo daya nayi mata ta burgeni. Sannan naga zatayi daidai da budurwar da muke bukata acikin fim dina na DAREN MUTUWA. Kaine Hilal? Kwarai kuwa nine Wallahi daga gongola nake masauki nake nema. Hakanan a saukake don tsabar taren aradu da ka dakuma neman tsautsayi da rashin tunani sai kyawunta ya rufe min idanu na samar mata masauki batare da na binciki abinda ya rabo ta daga gida ba. Yan kwanaki kadan na fahimci ashe tanada ilmin boko mai dan tsayi domin har diploma ce da ita abangaren tsimi da tanadi. Haka nan tanada wayo da hikima hakan ce tasa na maida ita amatsayin sakatariya lokaci lokaci kuma nakan jefata a fina finai naso ace duk fim din da zan fito tare zamu fito to amma saboda acewarta. Bana son fuskata tayi yawa acikin fina finai sai kawai na kyaleta ban kuma tambayarta dalili ba. Har yanzun nan da nake safa da marwa cikin dakin bayan shekaru biyu cif cif da faruwar al'amarin ina tambayar kaina shin me ya raba lauriyya daga gaban iyayenta? Hakika lauriyya ta fara shiga raina sosai. Adacan sa'ar dana fara ganinta kyawunta ne kawai ke burgeni babu dadi ba ragi. To amma ayanzu abin ya wuce haka lauriyya ta zama jinin jikina abin tunaninaba dan komai ba kuwa sai don na fahimci ita kadai ke damuwa da fushina ita kadai ke farin ciki da karuwata ita kadaice komai ke sani dariya ta dauke min kewa aduk lokacin dana shiga damuwa. Gobe in Allah yaso saina tambayeta labarinta baki daya. Nayiwa kaina alkawarin hakan. . Haryanzu ruwan saman ake tafkawa kamar da bakin kwarya na sake nazarin sabon dakin dana dawo cikin takaici domin baikai ko rabin bandakin da nake wanka ba atsohon gidana dana sayar na biya bashi. Dakin danake ciki dan kankani ne kamar dai sauran dakunan da ake yiwa boyi boyi agidajen gwamnati kujeru uku ne kacal dakin ya iya dauka. Koda yake dai in ma zaici fiye da hakan ba samu zaiyi ba domin duk na sayar da kujeruna sama da talatin na biya bashi ayanzu kam in kadauke tsohon gadon katakon dake dakin katifar daya dana tsira da ita gamida talabijin daya mai kala da bidiyo da rediyon jin labarai mai gidan kaset daya dakin babu komai sai shegen zafi gamida manya manyan saurayen dake fizgar rigata ta baya ina kwacewa dakyar. Dakin danake zaune ayanzu an tanadae shi ne dan yaron gida dayake kawuna ma'aikacin gwamnati ne ya kuma san irin yadda mutane ke ta kawo min ziyara sai ya shawarce ni dana dawo nan na tare tunda da dai karayar arziki tazo min. . Nakoma bakin gadon na zauna sannan na cire rigar dake jikina na kwanta akan tsohon gadon inajin zazzafar iskar fankar dake busowa akan fuskata. Sannan kuma lokaci guda ina mai addu'ar allah sa adauke ruwan kona sami damar bude kofar nasha tsabtatacciyar iska. Ina nan kwance idanuna rufe zuciyata cike da zullumin basussukan da ake bina gamida tunanin Lauriyya ga kuma shegen zafi wannan shi ya hana barci ya daukeni. Nashiga cikin damuwa domin nasan gobe da asusussuba zan tashi domin tafiya sabon fim din da aka daukeni na Sinad production. Gashi kuma yanzu ba da ba. Domin banida ko jaki ballantana mota. Bansan sa'ar da barci ya daukeni ba adaren. Acikin barcin ne harna fara mafarki wai anata bubbuga min kofar dakin danake ciki kuma wai muryar lauriyyace ke kirana. Nayi firgigit na farka ina mitsitstsika idanuna sannan ne to ga mamakina sainaji ashe kuwa a gaske kofar dakin nawa ake ta bugawa....... ALAKAKAI-05 . Sannan ne to ga mamakina sainaji ashe kuwa da gaske kofar dakin nawa ake bubbugawa. Nayi fakare kamar zakara zuciyata na harbawa cikin mamakin ganin mafarkin nawa yazama Gaskiya. To saidai kuma buga kofar yasani cikin damuwa domin na lura haryanzu sheka uban ruwan ake kamar da bakin kwarya tabbas nasan ba lauriyya bace. Toh wanene ? Na tambayi kaina nadubi agogon dake jikin bangon dakin wanda ke dauke da hoton yan wasan da mukayi shirin flm din Daren mutuwa dasu. Karfe biyu da rabi na dare. Domin kuwa banga wanda zai buga min kofa ba cikin wannan uban daren sai ko barawo. Aka sake bugun kofar dakin Das Das Das kamar ana kugun kwarya da sullen kara. Nayi mamakin jin bugun kofar dakin babu karfi domin ko wanene ke bugun kofar to yana tausaya mata. Aka sake bugawa Raf Raf Raf har sau uku gumi yafara sartu a goshina hakika amafi yawan fina finan danake fitowa ni jarumi ne mai zafi marar tsoro to amma azahiri tsorone dani amar farar kura domin dan karamin yaro ma na iya tsoratani da bindigar wasan yara saboda tsorona. Me yiwuwa lauriyya ce.... Kai ba ita bace babu mamaki dai kawuna ne nace dakaina. To amma jikina baiyi amanna da kalaman zuciyata ba domin tun ranar dana tare agidan kawuna bai taba lekowa bangaren danake ba in son ganina yake saidai ya turo ayi kirana indai shine to tabbas ba lafiya ba. Can kuma sai wata zuciyar tace dani to ai kuwa idan shine kiran sunana zaiyi kai tsaye basai ya tsaya yanata kwankwashe kwankwashen kofar ba. Wannan shiyasa cikina ya dada durar ruwa jikina ya dauki bari nan da nan naji hakorana sun fada haduwa da juna kaf kaf kaf saboda tsoro. Najuya ahankali akan tsohon gadon na dubi yan tarkacen da suke dakin nace da kaina. In dan wannan ne sai na basu su tafi sun dauka jiya yau ce. Kawai wayannan barayi da rashin basira suke su basuda labarin na tsiyace ne ? Acikin fina finan danayi nasha arangama da barayi da yan fashi na doddoke su acikin sauki ina hura hanci wasu ma darakta yasa na kakkama su na daure. To amma duk wannan daban domin wasa ne yanzu kam shine azahiri domin gasu akofar dakina. Na lalubi aljihuna na dauko rubabbiyar naira goman da mai mashin yabani canji daman naira hamsin ce kadai ta rage a aljihuna sa'ar da zamu rabu da lauriyya na bata ashirin ta tafi gida nikuma na hawo acaba naira ashirin nakaraso gida da goma. Na zargi kaina saboda barin kofar gidan danayi a bude koda yake kusan ko yaushe ma ahaka take saboda abokai da maziyartan dake yawan zuwa gurina cikin dare wasu lokutan ma sai na dawo daga daukar fim cikin dare zan sami baki suna jirana. Amman ban taba samun bakin kusan karfe biyu na dare ba. Raf Raf akaci gaba da buga kofar na yunkura hantar cikina na rawa na nufi kofar dakin inata salati da sallallami. Wai wan....ne ? Nace muryata ashakre ban iya shaida ta ba amatsayin tawa, maimakon abani amsa sainaji an sake kwankwasawa. Wai wanene? Nasake kuga tambayar shiru ba amsa ba. Haushi yakamani saina tuna da fim din DAREN MUTUWA. Mun taba yin wani guri mai kamar wannan inda wasu barayi sukazo suna kokarin balla kofata nikuma nabari saida suka jingina da kofar suka gama bada karfinsu akanta sai na bude kofar da karfi suka zubo dakin kamar an handakosu nikuma na doddoke su. Yau ma zan maimaita nace cikin zuciyata saidai kuma sabanin wancan karon yanzu idan Allah yabani sa'a suka fado cikin dakin tsallake su zanyi na Gudu. Aka sake kwankwasa kofar awannan karon da karfi jin hakan shiyasani tunanin me yiwuwa mai bugun kofar jikinsa ya jingina akofar don haka cikin sauri saina zare sakata na janyo kofar da karfi sai naji sakayau kamar na janyo gadon kara babu abinda ya biyo baya. Ashe dai ko a gaske Jarumi ne. Wata zazzakar murya tace dani. Nayi sororo ina duban abin haushin dake tsaye akofar dakin cikin mamaki. Mace ce tsaye akofar dakin sanye da doguwar riga baka da jan lullubi akanta jikinta na digar ruwan saman daya daketa hakika ajin farko ce ajerin kyawawa. . ******** ********** ********** . Mun shafe kusan rabin minti muna tsaye muna duban juna haushi da fargaba da mamaki sun hanani magana. Shin ko na iya shigowa sanyi nakeji gaskiya kuma duk kayana ajike suke. Idanuna suka kai ga katuwar akwatin mai taya dake hannunta sai hakan ya tuno min da farkon haduwarmu da LAURIYYA. Malama ina fatan dai lafiya?.... Ma'ana daga ina kike cikin wannan uban daren? Kuma da wacce kika zo? Yar budurwar ta dubeni sa'annan t jefeni da lallausan murmushin Allah kasheni don dadi. Lafiya kalau Hilal tun daga wata nisan duniya nataho gareka domin kawai na ganka na dade ina ganin fina finanka ina kaunar araina da begen ganinka shne naga bazan iya jurewa ba sainazo na ganka da idanuna. Ta danyi shiru tana kokarin share ruwan dake sartu daga cikin gashinta zuwa fuskarta. Gashi dai cikin duhu muke tsaye dakin babu wuta amma duk dahaka fuskarta har sheki takeyi idan akayi Walkiya. Ko makaho ya lalubeta yasan Allah yayi halitta agurin. Tsarki ya tabbata ga mahaliccin kyawawa. Haryanzu dai baki gama amsa min tambayata ba nace da ita ina dubanta. Yar budurwa ta daga girar idanunta sama cikin rashin fahimta can kuma saita girgiza kai gamida wani alakaron murmushin. Oh kana nufin daga inda nake? Daga maiduguri nake motar mu ce ta baci ahanya shiyasa mukayi dare yanzun ma direban motar na roka Allah da Annabi shine yakawo ni har nan tayi shiru tana dubana. Jarumi Hilal ina fatan dai yanzu ka gamsu.....shin na iya shigowa? Sanyi nakeji Wallahi hilal akwai wani abu a tattare da ita dake damuna fiyeda yawan murmushinta gashi kuma ko ganina azahiri bata taba yi ba sai yanzu yanzu ma kuma acikin Duhu. . Na matsa gefe guda ta shigo cikin dakin zuciyata cike da tunane tunane. Ta ajiye akwatin sannan ta juyo ta dubeni. In baka damu ba don Allah nuna min bandaki yake so nake na shanya kayana duk sun jike jagaf. Gabana yafadi ras na bude baki cikin kaduwa nace Ki shanya kayanki? Na tambayeta adolance. Ta gyada kai. To ke kuma ki zauna dame? Tayi murmushi lokaci guda tasa hannu ta yane jikakkken lullubin dake kanta nan da nan siraran gashin kanta baki sidik suka zubo kan kafadarta koda walkiya ta hasko cikin dakin sainaji zuciyata na harbawa da sauri na dade banga gashi da kyawun nata ba. Saina zauna aciki idan sun sha iska na maida kayana nafito. Na sunkuyar dakaina kasa a rude kai yau na gamu da gamona. Nace cikin zuciyata koda na daga kaina sainaga ta kura min idanu kamar zata hadiye ni. Oh hilal yau dai Allah ya nuna min kai. Wallahi kada kaga irin son danakeyi maka duk cikin yan wasan hausa babu wanda nake kauna kamar ka zakayi mamaki idan nace ma acan maiduguri akwai kawayena da yawa da suke kirana da suna HILAL. Tayi shiru tana dubana me yiwuwa ko don ganin duk surutun da takeyi ban tanka mata bane. Hilal yaya kakeyi min irin wannan kallon ne haryanzu baka amince dani ba. Akaro na farko sainaga ta dan hade fuska amma duk da hakan saida idanunta suka nuna alamun murmushi. Bahaka bane malama abin da haryanzu ke rudani shine zuwanki cikin wannan talatainin dare kuma..... Ta katseni. Nace dakai motar muce ta lalace haba hilal nifa bakuwarka ce in kuma korata kakeyi shikenan bari natafi nagode. Ta yi nan tsaye bata dai motsa ba akaro na farko saina sassauta murya nace da ita a tausashe. Toh naji na yarda amma kuma yaya akayi kika san gidana? Yar budurwar ta dubi akwatin dake kwance atsakar dakin sannan ta dawo da dara daran idanunta kan fuskata. Hilal kaga in bakaji dadin zuwana ba simple ce kawai na fita saina fice ma daga daki ko a tasha na kwana da safe na koma garinmu yaya zaka sani agaba da irn wadannan tambayoyi kamar wani tsohon dan sanda. Ta harareni gamida murguda min baki ta danyi shiru tana maida numfashi. In banda abinka hilal mutane nawa ne suke zuwa ziyartarka arana daga jihohi daban daban ? Kawayena ma nawa ne suka zo gurin ka? Ai kwatancen gidan fitacce kamar ka ba wahala bane musamman agidaje irin wadannan na gwamnati kasan fa kowane gida yanada lamba...kodayake dai zuwana ne kawai baka so. Ta juya min baya tana kallon kofar dakin. Allah baki hakuri nace da ita a tausashe juyo mu fuskanci juna basai kin juya min baya ba yar budurwar ta juyo da faffadan murmushi. Lah hilal menene kuma na bata rai nifa ba fushi nayi ba ai ko ina fushi da mutane hilal kai ka wuce nayi fushi dakai idanunta suka kai ga agogon dake makale abangon dakin. Na dubeta nima karfe biyu da rabi na dare 2:30am . Lah wannan ai hotonku ne na fim din Daren Mutuwa. Budurwar tace cikin karaji sannan cikin hanzari ta matsa kusa da agogon ta kura masa idanu. Nikuwa hilal daman inason na tambayeka na dubeta cikin mamaki. Me zaki tambayeni? Yar budurwar ta dora dan yatsanta na hagu akan hoton ta nuna fuskar Lauriyya tace. Amma wannan yarinyar ko agaske ba'a fim ba budurwar kace ko? Naji gabana yafadi ras na girgiza kai. Kokusa kada kiyi tunanin haka fim ne kawai kinsan ku yan kallo kusan ko yaushe kuna da wannan kuskuren fahimtar. Irin kallon datakeyi mane a fim din na lura ya wuce na wasa..... Na dubeta akaro na farko sainayi mata murmushin yake..bakya rabuwa da kame kame baiwar Allah bakisan yan dirama bane yanzun nan sai suyi miki abu kiga kama da gaske nan kuwa karya suke. Bata juyo ta kalleni ba haryanzu kallon hoton take amma na lura da murmushinta ba zato ba tsammani saita juyo ta fuskance tace. Ai kuwa kyakkyawa ce. Mukayi shiru na tsahon lokaci muna duban juna. . Nuna min bandaki hilal kada mura ta kamani da wannan jikakkun kayan dake jikina. Zo muje nace da ita domin nagaji da jayayya. Nashiga gaba tana bina abaya kamar bawa da balarabe bandakin acan bayan falon yake saidai kuma zaka iya shiga bandakin ta cikin falon batareda k fita waje ba. Ga kofar nan nace da ita ina duban yala yalan gashin kanta. Hakika kyakkyawace ajin farko ta dubeni sannan ta sake jifana da murmushi ta shige bandakin gamida rufo kofar gararam da karfin gaske karar rufr kofar suka cakude da rugugin aradun nayi sauri na rufe kunnena. Akwai lokuta da dama da bana son sautin aradu domin ji nake kamar ni zata fadowa......... ALAKAKAI-06 . Domin ji nake kamar ni zata fadowa.. . Na juya ahankali na nufi dakin ina shiga saina janyo kofar dakin amma ban rufe ta gaba daya ba. Na zauna abakin gado nafara jujjuya batun wannan kyakkyawar budurwa mai ziyarar tsakar dare cikin zuciyata. Akwai wani abu atattare da ita dake bani tsoro na lura da ita ko kusa ko alama batada tsoro haka nan batada kunya kuma babu alamar bakunta ajikinta bugu da kari kuma acikin amsoshin tambayoyin danayi mata akwai amsa daya na tabbata karya takeyi. . Shin duka duka wata na nawa da tarewa awannan gidan da har maziryata na zasu kwatonta mata inda nake? Nidai a iya tunanina tun dana tare agidan bansamu wani maziyarci daga bakuwar jiha ba ina nan zaune ina jiran fitowarta na dubi agogo karfe uku saura kwata 2:45am nasan ni da sake samun wani isashshen barci kuma sai abinda hali yayi tunda dai nan sa sa'o'i biyu da motsi zamu fita sabon fim dinsu Alhajiji. Nayi murmushi sa'ar dana tuna yaudarar da Lauriyya tayiwa alhajiji kai wannan al'amari da daure kai yake nace da kaina saikayi mamakin yadda kudi da mata suke tsananin tasiri azuciyar Mazaje. Naji gabana yafadi sa'ar da wani tunani ya fado min nan da nan naji gumi ya fara sartu agoshina yanzu idan garin Allah ya waye wani kokuma kawuna yazo ya sameta adakin nan me zance dashi? Kirjina yafara dakan uku uku tuni nasan mutanen unguwa sun dade suna zuzzuga kawuna akan wai dole sai ya hanani harkar wasan kwaikwayo domin wai duk yan wasan kwaikwayo yan iska ne marasa mutunci da kyar nasamu na shawo kansa. To yanzu kuma bayan duk wannan idan yasami mace ta kwana adakina fa? Gumi yaci gaba da sartu akan goshina kaga dan samari wata zuciya tace dani abu mafi sauki shine data fito daga bandaki katafi da ita gidan kawunka ka kwankwasa masa kofa nasan in nayi masa dogon bayani yana iya fahimta sai su kwana tare da matarsa. Tunanina ya katse adaidai lokacin danaji wani abu kamar sautin mota wajen gidan na dubi agogo karfe uku harda kusan rabi 3:30am kai amma dai ta dade cikin bandakin nan kodana lissafa sainaga kusan sa'arta guda aciki na mike tsaye cikin sauri na nufi falon ina zuwa saina wuce kai tsaye zuwa kofar da zata kaini har bandakin ga mamakina sainaga kofar a bude. Gabana ya ya fadi na mtsa ahankali na kara kunnena ajikin kofar bandakin ko zanji motsi shiru sai sautin zubar ruwan sama akan kwanuka zuciyata na harbawa saina kwankwasa kofar bandakin. Malama haryanzu kina ciki? Shiru ta gaida kunnuwana. Malama ina kike ne? Na sake kiran sunanta to saidai kuma ni kaina nafara tunanin bazanji amsar komai ba. Na bude kofar bandakin ahankali sainaga WAYAM. Babu ita babu alamarta. Nan da nan na ruga aguje zuwa kofar gidan. Ina kike ne? Adaidai lokacin ne to naji sautin injin mota an tuka anbar gidan. Nakarasa aguje amma ni kaina nasan bazan taba samun motar ba na tsaya sororo ruwan saman na dukana ina hangen danjar motar tana daukar idona kamar gauta acikin rana. Sannu ahankali har na daina hangota. . BABI NA UKU 3 . Nadawo cikin dakin jikina na rawa kamar tsohuwar data sami kwarto karkashin gado. Na zauna jagwaf atsakar dakin kamar tsohuwar saniya na kurawa akwatin data bari danu sama da tambayoyi dari suka fara turereniya cikin zuciyata. Shin wacece ita? Daga ina take? Menene dalilin zuwanta? Yanzu kam dana tabbata TA GUDU na tabbata duk abinda ta fada abaya karya takeyi. Sannan babu zato babu tsammani saina tuno da akwatin datazo da ita. Na mike zumbur kamar an sokeni da kibiya na nufi inda akwatin take jikina na tsuma na daukota na dora akan gado sannan na fara kokarin budeta. Atunanina acikin akwatin ina iya samunwata shaida da zata sanar dani ita wacece. Allah ma ya taimakeni data bar akwatin nace cikin zuciyata. Na danna mabudan akwatin ina mai wasi wasin budurwar ga mamakina sainaga ta bude fayau. Na dubi cikin akwatin ina mai mamakin ganin babu komai ciki sai wani dan kyallen yadi fari lullube da wani abu. Jikina ya dauki rawa kamar mazari. Nasa hannuna kan farin kyallen sannan na janye farin kyallen. Numfashina ya kauracewa kirjina yawun bakina ya kafe kana yar autar cikina ta manne jikin hanjin cikina. Akwance male male akasan akwatin. DAN JARIRI NE. Sabuwar haihuwa kyakkyawa dashi kamar dan larabawa akusa dashi kuma takarda ce ko liketa ba'ayi ba ajikinta sakone a rubuce kamar haka........ . HILAL. Na dade ina ganin fina finanka kuma kana matukar burgeni hakan nema yasa begenka yafara mamaye zuciyata. Hakika tun danake arayuwata ban taba ganin jarumin danake kauna ba kamar kai ka iya shiri kwararrene kai mai burge yan kallo to saidai kuma katsam sai gashi acikin fim dinka na DAREN MUTUWA ka bani haushi kasa na tsaneka. Lokacin da ka dauki jaririn nan acikin fim din zaka jefa shi cikin rami sainaji kamar da gaske zaka jefa ciki. Baka dade ba da gama fim din sai nima na sami nawa jaririn abin dai kamar acikin dinka na daren mutuwa CIKIN SHEGE NE don haka sai naga abinda ya dace shine na sako shi cikin akwati na kawo maka shi tunda dai ka saba jefa jarira acikin rami me yiwuwa kana iya rabani da nawa abin kunyar ka taimaka ka Jefar min da shi. In kuma kana so to gashi nan nabaka shi kyauta a matsayin ka na kwararren jarumin fim din DAREN MUTUWA. Sai anjima kada ma ka nemeni domin bazaka taba samuna ba domin GARIN MU DA NISA.....! . NA ajiye takardar cikin akwatin jikina na rawa sannan na dubi jaririn dake kwance cikin akwatin sainaga kamar yanayi min dariyar kuda. Na dafe kirjinsa da tafin hannuna na girgiza kai cikin Kaduwa lallai kam kyauta ta musamman. Hakika kam nayi dace da kyautar kyakkyawan jariri in da ba don MATACCE BANE. . *********** ************ **************** . Idanuna suka fara zafi banyi mamaki domin gumin dake sartu akan fuskata kamar ruwa tuni yafara shigar min idanu. Nasake duban kyakkyawan jaririn dake kwance acikin akwatin na tsahon lokaci sannan sannu ahankali saina janyo farin kyallen na lullubeshi gami da rufe murfin akwatin ahankali kaikace tsoro nake kada na tashe shi daga barcin dayake. To saidaikuma nasan shi da farkawa sai ranar da aka busa kaho. Kafin na rufe akwatin saida na dauke wasikar da budurwar tasa aciki na tura ta cikin aljihuna sannan na mike tsaye ina muzurai ni kadai kamar tsararraren kwarto. Shin wace mata ce wannan? Shin danta ne? In kuma bana ta bane menene alakata da jaririn menene kuma dalilin dayasa ta rasa wanda zata kaiwa gawar jaririnin sai Ni? Kai wannan rashin imani na mutanen duniya da yawa yake. Haryanzu ba'adaina tsugu uban ruwan saman ba haka nan lokaci lokaci saikaji an ruguza aradu kamar ta tsaga dakin. Ama ni duk wannan ba ita bace agabana babban abinda yafi tayar min da hankali shine yaya zanyi da jaririn? Ka kirawo yan sanda wata zuciya ta shawarce ni. Acan kuma wani bangaren na zuciyata akace dani. Kai shashashan banza idan ka sake ka kirawo yan sanda ka kashe kanka daman tsammani zasuyi sato shi kayi ka rude shine ka kirasu. Basai kayi musu bayanin yadda budurwar ta kawo maka shi ba? Wata zuciyar ta sake kwabata in ka sake ka kira yan sanda ka karasa rusa kanka a harkar fim domin dole ne labari ya watsu abokan hamayyarka kuwa sun sami makamin da zasuyi ta yakarka har sai sun kai ka kasa. Can kuma sai wata zuciyar tace dani kai dan samari rufawa kanka asiri tun wuri ka dauki jaririn

Chapter 2 of 5