Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ALAKAKAI Nazir Adam Salih Made by Shuraih Usman Daga http://fb.com/hausaebooks ALAKAKAI-01 . DAYA 1 Wata ranar lahadi aka tashi da gagarumin hadari wanda yakan firgita birrai. Kodayake a safiyar ranar ba'a tashi da alamun hadarin ba. Sararin samaniyar tarwai yake babu alamar gajimare ko kankani wannan shi ya baiwa rana lasisin ci gaba da dumama rufin gidaje da kayuwan bani adama tun daga karfe goma na safiyar har zuwa karfe daya na ranar. Abin bai zowa mutane a bazata ba musamman ma wadanda suka sha miya da yawa domin sun dade da yin amannar cewa duk sa'ar da zafi ya tsananta alokacin damuna to hadari ne ke son haduwa. Haka kuwa akayi babu zato ba tsammani sai hadarin ya fara haduwa sahu sahu sannu ahankali har ya dakushe hasken ranar ba'a dade ba sai iska gamida feshin tsattsafar ruwa nan da nan jama'a suka fara tserere akan tituna domin su sami gurin fakewa acikinsu harda Ni wanda rabona da ofishina tun karfe tara na safe da wani mutum yazo karbar bashinsa na gudu. . Wannan bashine karo na farko ba dana fara tserewa masu bina bashi kusan watanni tara kenan da harkar fim ta juya min baya tun fitowar fim dina na DAREN MUTUWA shikenan sai mutane suka dau karan tsana suka dora min. Iskar hadarin ta fara tsananta dan haka sai nayi sallama da mai shagon dinkin da nake boye aciki tun safe nace dashi. ISYAKU zan koma ofishina. Isyaku tela ya dubeni cikin damuwa daman yasan irin matsanancin halin danake ciki Gara ka tafi gida Hilal domin komawarka ofis ayanzu ganganci ne... Na dubeshi gamida murmushin yake kada ka damu isyaku leka waje ka gani hadari ne bakikirin ga iska.. Nasan dai mutum yanzu in ba maye bane dole ne ai yabar ofishin..... Kuma bugu da karawa ma dole ne na koma ofishin domin na sallami sakatariyata LAURIYYA dan nasan ko kudin mota bata dashi...... Abincin rana ma bansan yadda zatayi ba.. Isyaku ya dubeni cikin mamaki. Kana nufin haryanzu Lauriyya tana tare dakai? Na gyada masa kai kwarai kuwa ai tattaraba ce uwar alkawari ita kadai ta rage a yarana duk sun barni sai ita kadai... Isyaku ya dan yi murmushi yana dubana. Itama akwai dalili.. Na dube shi cikin mamaki dalili... Kamar yaya ban fahimce ka ba isyaku yayi atishawa sannan yace Haba Hilal har sau nawa kake so in maimaita ma cewa Lauriyya sonka take. Nayi saurin girgiza kai A'a bari bari isyaku kada kayi min mummunan fahimta na yarda ni dan fim ne amma zakayi mamaki idan nace dakai tunda nake ban taba soyayya ba da wata yar fim. . Kakkarfar iskar hadarin dake ta hankoron dauke rufin dakunan masu rangwamen gata ta bugo kofar shagon telan da karfin gaske Isyaku yasa kafa ya tokareta. Baka fahimce ni ba Hilal ko kuma ince kasan gaskiya ka ke takewa ai ko makaho ya laluba yasan lauriyya tana mutuwar sonka. . ******* ********* ************ . Lokacin dana baro shagon telolin saina tsallaka titi na nufi ofishina cikin sauri da kyar nake ganin gabana saboda kakkafar iskar ma'abociyar kara dake ta bulbule min idanu. Kura ta turnuke ko ina haka nan garin yayi jajur duhu ya lullube ko ina kai kace karfe shida da rabi na yamma tayi duk kuwa da cewa karfe daya ne na rana. Cikin sauri na nufi ofishin inata waige waige domin haryanzu jikina na bani cewa akwai sauran masu bina bashi cikin ofishin suna jirana. Tun kafin na karasa ofishin na fara hange hange da rabe rabe sannu ahankali har na isa kofar ofishin wacce ke rufe tana duban bakin titi. Nayi tsaye a kofar ofishin kusan minti guda nayi kasake kamar barawo ina saurare ko zan ji surutai ko hayaniya shiru banji komai ba na dan dada matsawa kadan na kara kunnuwana ajikin katuwar kofar nayi ajiyar zuciya sannan sainayi shahada na daga hannuna zan tura kofar kenan sai kawai naga an bude daga ciki. Sannu da zuwa hilal yi maka ka shigo daga ciki yanzu yanzun nan EMEKA yatafi tun sha daya yaketa jiranka nace dashi katafi kaduna... Amma yaki yadda Kirjina na dakan uku uku cikin sauri na shige ofishin. Lauriyya ta mayar da kofar ofishin cikin gaggawa ta rufe sannan saita jingina bayanta ajikin kofar ta kura min idanu bata ko kiftawa. Na nufi cikin ofishin ahankali hannayena cikin aljihunan wandona zuciyata na kuna nayi kokarin nazarin ofishin amma saboda duhun hadarin bana iya ganin komai cikin ofishin. Lauriyya ta fahimci haka cikin sauri ta nufi makunnar lantarki ta kunna nan da nan dakin ya gauraye da haske. Lauriyya tayi tsaye jikin makunnar lantarkin tana kallona ina kallonta. Akwai alamar tausayi karara a fuskarta banda wannan kuma naso na hangi kwalla acikin kwayar idanunta. Cikin sauri na dauke kaina gefe guda sannan nafara nazarin ofishin..... Da a da dan wani lokaci can daya shude babu wani ofishin darakta na fim daya kai koda rabinsa a tsaruwa amma koda na tsaya ayanzu ina nazarin ofishin sainaji kamar na fashe masa da kuka lallai ruwa ya daki babban zakara. Saidai hakuri Hilal haka duniya take rawar yan mata lauriyya ce ke magana abayana cikin wata rarraunar murya. Naji abinda ta fada to saidai kuma ban iya juyowa na kalleta ba ballantana ma na tanka mata. . Zuciyata da tunanina suka koma baya kadan wani dan shudaddan zamani.... Sa'ar danake tauraron jarumai na wasan fina finan hausa. Na rufe fuskata da tafukan hannuna sannan nafara tunanin sa'ar dana shigo harkar fim da kafar dama cikin watanni ukun farko da shigata harkar na fito cikin fina finai sama da shirin wadanda duk nine jarumi acikinsu sannu ahankali sai sunana yayi tambari duk inda ka zagaya babu sunan wanda ake fade sai HILAL. Duk inda na zagaya yara da manya basa barina na huta sun yita bina kenan abaya kungiya-kungiya kamar uban garke idan naje sayayya kasuwa ba'a karbar kudina haka nan da zarar an kyalla ido na ganni saikaga anata rububin ganina kowa na gayyata dana zo nayi siyayya ta a rumfarsa duk kuwa da cewa ba kudina zasu karba ba. Na mallaki abubuwa da dama a shekarata ta farko da shiga harkar fim wanda adacan wani lokaci ban taba mafarkin mallakarsa ba akwana kusa motoci uku na hawa kayan sawa na kwalisa sama da kala dari uku da goma sha takwas agogunan sarka ashirin na fata goma takalma sittin safa kuwa da singileti duk wacce nasa sau uku bana kara amfani da ita sai wata sabuwar. Sannu ahankali samari suka fara kwaikwayon yadda nake direshin duk abinda nayi koda sakarci ne sai ya burgesu saikaga sun zamo masu kwaikwayona. . Ashekarar ne na bude katon ofishina wanda aka kawata shi da kyale kyale gami da manya manyan kujeru masu numfashi da taushi kamar ada da sau da yawa idan muka sauki baki indai har zasu shafe mintuna goma suna zaune sai an sami wanda ya bingire da barci saboda dadi. Duniya ta dawo min sabuwa ina da yara dake aiki akarkashina sama da mutum ashirin suna kuma jin maganata fiye data iyayen da suka haifesu wasu suna bina sau da kafa ne wai don kawai suna so na sa su kokuma nayi musu hanya su shiga shirin fim yayinda wasu kuma suke yi min biyayya don kawai kaunata da sukeyi. Nazama kamar sarki acikin fadawa duk abinda nake so shi za'ayi batareda bata lokaci ba. Da ace yarana awannan lokacin suna da iko da fitsari da numfashi ma su zasuyi min. Muna nan ahaka har shekaru biyu suka shude Kwatsam ran nan sai duniyar data dagani sama ina shanawa tafara yin kasa kasa dani sannu ahankali ta damfara ni da kasa. Abin yafara ne a yammacin wata ranar lahadi sa'ar danake karbar kudaden sabon fim dina RAGAS daya fito. Shagon farko danaje sai akace dani wai fim din baya tafiya nayi mamaki domin tunda kamfanina yake fim ba'a taba samun wanda bai shiga ba. Me ya faru da fim din? Na tambayai wani dillalin kasa kasan fim din. Eh to kasan dai mutane yadda suke ba'a iya musu inajin dai gajiya sukayi dakai.... Kuma sunata korafi akan cewa wa fina finanka na kwanan babu labari mai kyau. Tun daga ranar ne al'amura suka dagule min abin kamar sa hannu komai na taba sai ya lalace gashi dai nagama kashewa fim din Ragas kudi... Na ranto kudin jama'a duk na lafta saboda a tunanina zaiyi bala'in karbuwa saigashi cikin ikon Ubangiji saidata kawo ko kashi daya bisa goma na kudin fim din basu komo ba. Rayuwata tsananta kaina ya dauki zafi rikici goma da ashirin ga tarin bashi fal akaina gashi kuma ya furodusoshin ma da suke daukana na fito musu a matsayin jarumi duk sun gujeni ba'a dade ba duk yarana suka watse suka barni daga ni sai yar amana LAURIYYA. . Koda na daga fuskata sa'ar danake tunanin na dubeta saina tuno da kalamanta saa'ar da gari yayi mana zafi bazan taba mantawa da ranar ba. Ranar wata laraba da yamma bayan sama da mutane goma sun zo tambayata bashin su. Hilal.. Ina da shawara in zaka yarda. Lauriyya tace dani na dago kai na dubeta. Fadi shawararki lauriyya...indai mai amsuwace ai na dauka.. Tunda dai ko banza dai ke kadai kika rafe atare dani.. Wallahi lauriyya ayanzu kin wuce sakatariya agurina saidai ko in Yar Uwa. Lauriyya ta dan matso daf dani duk da yake duk ranmu abace yake to amma na lura da alamun jin dadin abinda nace karara a fuskarta na sani ba tun lokacin ba har zuwa yanzu Lauriyya sona takeyi to amma ta rasa yadda zata fito ta fada min. Hilal... Ni ina ganin a shawara da ace kullum mutane suyita binka suna tambayarka bashi... Suna muzanta ka kamar barawo gara in kana ganin babu damuwa ka daga dan kadarorin daka mallaka kasa su akasuwa in yaso saika biya mutane bashin su... Ko banza dai ina ganin ai tsira da mutunci yafi tsira da kudi. Hakan data fada saina fahimci tabbas ta fadi gaskiya ba'afi sati daya da bada shawarar ba na sayar da motocina guda uku gidana kai da duk wani abu danake ganin zai iya kawo min wasu dunkulallun kudi saida na sayar dasu. Acikin makonne na biya jama'a da dama basussukansu ni kuma nakoma gidan yayana inda daman tun farko acan nake kafin na samu abin duniya UNGULU TA KOMA GIDANTA NA TSAMIYA . To saidai kuma abin bakin ciki duk da kadarorina dana sayar basu isa biyan bashin da ake bina ba. Gashi kuma haryanzu babu wani labari daga gurin masu shirya fina finai wadanda ada suke ta bina agindi agindi suna rokona danazo na fito musu a fim yanzu da sun hangoni sai su fara buya domin duk labari ya ishesu acikin kankanin lokaci kamar wutar daji cewa wai kasuwar fim ta daina yi dani......... Wannan duk wani Abune daya shude Abaya. . ALAKAKAI 02 . Wannan duk wani abune daya shude abaya . Hilal aka kira sunana abaya na juya firgigit Lauriyya ce har yanzu tsaye ajikin makunnar lantarkin tana kallona idanunta sunyi rau-rau kamar zata fashe da kuka. Tunanin me kakeyi Hilal? Ta tambayeni bakinta na rawa na juyo ahankali hannayenta harde da juna makale abayanta. Kikace Emaka yazo nemana? Lauriyya ta gyada min kai bata yadda ta bude bakinta ba ina tsammanin da tayi magana alokacin fashewa zatayi da kuka. Sauran cikon kudin kwalin kaset din daya buga mana yazo karba nace da ita batareda na iya hada ido da ita ba. Ban da shima su shafi'i sunzo wai karbar kudin kayan kwastum... Haladu da sabo da ma duk sunzo maganar cikon kudinsu... Tsahon lokaci babu wanda ya sake cewa kala nida ita can bayan wasu yan dakiku sai lauriyya ta matso daf da inda nake tsaye inata faman karatun wasikar jaki ta dafa kafadata tace dani. Juyo ka dubeni hilal... Ina da shawarar da nake tsammanin me yiwuwa ta zama mafita agareka. Adaidai lokacin aka saki wata katuwar aradu data girgiza ofishin sannan wata walkiya mai tsananin haske ta harko cikin ofishin duk kuwa da kwan lantar dake ci. . ***** ******* ****** ****** *** . Na zurawa lauriyya idanu ina kallonta sannan kamar wani sahorami domin bansan me zance da ita ba ganin bance da ita komai ba sai ta dafa kafada na sannan ta sunkuyo da kanta tace dani. Ka gafarce ni hilal ba wani abu ne yasa nake tare dakai ba haryanzu sai don...... Ta kasa karasawa tausayinta yakamani haryanzu iska ake ta ketawa awaje saikuma sautin yan kananan kwayoyin ruwan da iska ke ta alakoro dasu akan rufin gidaje kafin isashshen ruwan ya karaso. Cigaba lauriyya.... Ke nake sauraro nace da ita a sanyaye lauriyya tayi dan jim na yan dakiku kana saitace cikin karyayyyiyar murya. Kau.....narka ce ta rike ni har zuwa wannan lokaci ina tare dakai.... Duk abinda ya same ka kamar ni ya shafa ne domin lokacin danazo garin nan kai ka karbeni ka mutuntani ka maida ni mutum. Banida cewa akan abinda tace dan haka sai nayi shiru ina sauraron abinda zataci gaba da cewa. Hilal.....abinda nake kokarin baka shawara akai shine me zai hana muje kamfanin fina finan su ALHAJIJI me yiwuwa...... Bata karasa ba sakamakon sauyin yanayin data gani karara a fuskarta. Haba lauriyya wace irin magana kikeyi ina ni ina wani Alhajiji kuma? Lauriyya ta dada matsowa gareni kamar zata kankameni. Hilal ka saurari abinda nake son fada ma dan Allah nsan dole bazakaji dadi ba domin zan saka yin abinda baka so ba. Ta dan saurara. Duk acikin yan shirin fim shi kadai ne nasan baya bakin ciki dakai.... Shiyasa tun jiya nake tunanin me zai hana muje mu gani ko zai samo ma wani fim din ajefaka aciki koda a mataimakin jarumi ne saikaga kadan samu wani abu ka rage bashin dake kanka. Tayi shiru tana dubana. Nayi dim na yan dakiku ina jujjuya kalamanta acikin zuciyata. Lauriyya abinda nake so ki lura dashi shine mutumin nan fa babu irin nacin da baiyi min ba sa'ar da nake kan ganiyar tashe na akan nazo nayi masa jarumi a finafinansa amma naki... Ke din nan da kanki sau nawa yana bugo waya ina cewa kice dashi bana nan....? Duk da haka dai hilal..... Haka nan zaka daure muje ai durkusawa wada ba gajiyawa bane ni nasan ba zai wulakanta ka ba tunda dai koda ada din ma ai ba fitowa kayi kiri kiri kace dashi bazakayi masa fim din ba. Na girgiza kai sa'ar danaji tayi shiru. Lauriyya ban ki shawarar ki ba amma abinda kamar wuya wai gurguwa da auren nesa ina ta faman nuna miki Annabi kina runtse idanu abinda nake so ki gane shine tuni labari ya watsu aduk fadin duniyar fina finan hausa cewa kamfaninmu ya fadi bama wani tasiri akasuwar fim shiyasa kikaga fa kowa ya gujeni an daina rububin sa ni a fim domin ana ganin nazama asara. To in dai kuwa hakane wacce irin hauka ce ta hau kan alhajiji da kike tsammanin zai sani cikin fim dinsa in janyo masa asara sa'ar danayi shiru saina lura tuni hawaye ya fara sartu akan kumatun lauriyya. . Daina cewa zaka janyo masa asara Hilal....abin da nake so ka gane shine ba kaine ka daina tashe ba kamfaninmu ne ya karye ya daina tashe amma ni nasan ita duk duniyar nan basu yarda ba ni nayi imani da cewa kana nan akan HILAL dinka jarumin jarumai. Kukanta yafara bayyana a fili. Nayi sauri na rike hannayenta nace da ita a sanyaye. Daina kuka lauriyya shikenan na yarda zamuje to amma kuma wani hanzari ba gudu ba. Lauriyya ta dago kai tana share hawaye cikin rashin fahimta. Yanzu idan mukaje bamu dace ba kinsan fa labari zai watsu aduniyar fina finan hausa cewa tsohon jarumin jarumai yafara tallan kansa..... Wacce illa kike tsammanin hakan zata janyowa durkusashshen kamfaninmu? Lauriyya ta bata fuska tace. Hilal so dai kakeyi saika bata min rai ko? Da dai bana son na fada amma yanzu ka takura ni saina fada? Na dubeta cikin mamaki me zaki fada? Lauriyya ta harareni gamida murmushin yake tace. Alhajiji yana mutuwar kaunata nice dai ban bashi hadin kai ba. Ni nasan ko yana so ko baya so dolene idan nayi masa magana yasaka acikin sabon fim din zaiyi. Tana gama fadin hakan saita kama hannuna ta fara jana kamar wani karamin yaro. Zo mu tafi dan Allah kada afara ruwa. Nabita abaya sumi sumi kamar tunkiya muka shiga cikin iskar damina. Jarumin jarumai Na kira kaina da kaina sannan sai na saki daddadan murmushi. Lauriyya ta lura Murmushin me kake? Na girgiza kaina nace babu komai.... Kece kawai kika burgeni, . ****** ********* ************* . Sa'ar da muka isa kamfanin fina finai na alhajiji sainaga toge abaya abjikin wani kantin kayan karau nace da lauriyya Jeki kuyi magana dashi ni bazan karasa ba... Lauriyya ta dubeni zatace wani abu saikuma ta fasa me yiwuwa itama ta lura da taron yan alabaku mu samun fim dake tare birjik akofar kamfanin duk kuwa da uwar iskar da ake ketawa. Lauriyya ta rike hannuna tace. Toh shikenan hilal jirani anan naje na dawo ta lura da fuskata haryanzu a murtuke take cikin damuwa. Kada ka damu hilal komai zai zama daidai in Allah ya yarda. Kaidai ka jirani. Tana gama fadin hakan saita matsa hannuna sannan ta jefeni da wani boyayyen murmushi mai kunshe da dubban manufofi ta juya tana rausaya ta nufi cikin kamfanin. . Na duba agogona bayana na jingine da itacen wayar lantarki dake daf da kantin na cika da mamaki sa'ar danaga tuni har mintuna goma sha uku sun shude da shigar lauriyya cikin kamfanin. Adaidai lokacin da damuwata ta fara tsananta saina hangi lauriyya ta fito alhajiji kuma yana biye da ita cikin fara'a akwai alamun farin ciki karara a fuskarsa me ywuwa na murnar zanyiwa kamfaninsa fim ne. Sa'ar da kuma na tuna da cewa nifa ayanzu ta kare min sai nafara tunanin to me yiwuwa ganin lauriyya ta nemi alfarma agurinsa ne yasashi murna. Ina nan tsaye har suka iso gareni. Yallabai! Yallabai!! Alhajiji yace dani cikin wata murya mai sautin amon alburushi sannan ya cafki hannuna kamar zai tsaga minsu saboda riko. Alhajiji kato ne baki mai katon ciki da dogon gemu babu gashin baki fuskarsa cikakkiya ce a mulmule kamar kwallon kafa duk sa'ar da yayi dariya saikaga ya zama tamkar mutum mutumi wannan ce tasa dayawa daga cikin shakiyan jaruman fina finan hausa suke so suga yayi dariya dan kawai su sha dariya. Wata shekara an taba fitowa dashi cikin wani shirin fim na abin dariya amatsayin dan daudu. . Saika rabe kuma daga nan Hilal ai SINAD PRODUCTION kamar gidan kace. Ya dubi lauriyya cikin murmushi itama kuma ta dubeni da murmushin yaudara ta kifta min idanu. Mu shiga daga ciki Hilal.... Wallahi nayi farin ciki da ganinka domin kaya ya tsinke agindin kaba daman yanzun nan nake kokarin buga ma waya saiga Lauriyya domin akwai wani babban fim dinmu na shekara da za'a fita gobe kai nake so ka fito a jarumi sunansa. MUTUWA DA FARINTA TAKE TAKE! Sa'ar da na dubeshi na dubi Lauriyya sainaji kamar na fashe da dariya domin ko shakka banayi nasan karya yakeyi dayace wai ni yayi niyyar sawa amatsayin jarumin tun farko kamata yayi a sanar dani tun satin daya gaba tabbas Lauriyya ce ta yaudaro shi. ALAKAKAI 03 . BABI NA BIYU Daga inda nake zaune ina iya jiyo sautin zubar ruwan saman akan kwanukan gidajen jama'a. . Na muskuta ahankali sannan na mike tsaye na nufi tagar dakin na dan janye gilashin tagar feshin ruwan saman gami da sansanyar iskar ruwan suka bugi fuskata. Nayi sauri na rufe tagar sannan nakoma na zauna akan kujerar ina nazarin dakin. shin wai yaushe za'a dauke ruwan nan ne. iskar dake cikin dakin ta fara karanci, hakan shiyasa fankar dake juyawa ta kasa yin maganin zafin dake addabata, gashi kuma idan nabude tagar dakin ruwa yajikani. Nasake mikewa tsaye naci gaba da safa da marwa hakika indai har ba dauke ruwan nan akayiba to da kyar zan iya barci. Gashi kuma tuni karfe dayan dare ta gota. Dakin danake ciki matsakaicine kamar dai sauran gidajen gwamnatin dake gurin. kujeru ukune kacal adakin kamar aya gami da tsohon gadon katakon dake dakon katuwar sabuwar katifar dana saya kwanaki biyu da suka wuce. daga bangaren arewa na dakin akwai talabijin mai kala da bidiyo asamanta. sannan kuma asaman bidiyon fulawace ta roba acikin kofin tangaran Amatsayina na TAURARON JARUMAN WASANNIN FINA-FINAN HAUSA dole ne naga nayi kokarin kawata dakin danake kwana koh don taren bakin dake tafaman sintirin kawomin ziyarce-ziyarce dare da rana. Yawan bakin da suke kawomin ziyara ne yasa kawuna ya waremin bangare guda agidan ya sanya katanga tsakanina dashi domin nasamu damar ganawa da bakina, tunda dai haryanzu banyi aure ba Na koma bakin gadon na zauna sannan na cire rigata na kwanta, inajin zazzafar iskar da fankar dakin ke busawa akan fuskata sannan kuma lokaci guda ina mai adu'ar Allah yasa a dauke ruwan saman koh na bude kofar dakin nasha iska. Na rufe idanuna amma barci ya kasa daukata gashi kuma gobe tashin asuba zanyi domin awashegarin ne zamu fara sabon fim din kamfanin SINAD PRODUCTION mai suna MUTUWA DA MAFARINTA TAKE TAFE, amatsayina na jarumin fim din dole ne nasamu isashen bacci domin na sami nutsuwar yin abin da daraktana yace nayi, toh sai gashi kuma zafi na neman hanani barci. toh ashe abun daban saniba shine bayan zafin dake addabata akwai wani al'amari daban dazasu kawo wa shirin fim din nawa matsala. . Ban san sa'ar da barci ya daukeniba acikin barcin ne nayi mafarki wai ana ta bubbuga kofar dakin danake ciki nayi firgigit na farka ina mutsutstsuka idanuna sannan ne to naji ana buga kofar dakin danake kwance nayi shiru cikin mamaki ganin mafarkin nawa ya zama gaskiya sannan kuma nayi mamakin shin wanene ke buga min kofata cikin wannan talatainin dare. Nadubi agogon dake makale ajikin bangon dakin wanda ke dauke da hoton yan wasan da muka shirya wasan fim din DAREN MUTUWA dasu karfe biyu da rabi na dare Tsoro ya kamani domin kuwa banga wanda zai bugamin daki ba cikin wannan daren sai koh BARAWO Aka sake bubbuga kofar dakin Das Das kamar ana bugun kwarya da sillan kara Nayi mamakin jin bugun kofar dakin babu karfi domin kowane ne ke buga kofar dakin hakika yana tausayamata aka sake bugawa raf raf raf har sau uku. Gumi yafara kwararowa kan fuskata hakika acikin mafiya yawan finafinan danake fitowa ni jarumine mai zafi marar tsoro to amma fa azahiri tsoro ne dani kamar farar kura dan karamin yaro ma yana iya tsoratani da bindigar wasan yara saboda tsorona. ALAKAKAI-04 . Me yuwuwa kawuna ne nace da kaina to amma kuma ban yadda da kalaman da zuciyata keyiba domin nasan tun da kawuna ya ware min bangarena daban bai taba koda lekowa ba idan kuwa shine to nasan tabbas ba lafiya ba to amma kuma idan shine ai kiran sunana zaiyi gami da kwankwasa dakin, jikina ya sake daukar bari na juya a hankali na dubi 'yan kayan dake dakin indai dan wannan ne sai nabasu su tafi. Acikin fina finan danayi nasha arangama da barayi da yan fashi na daddakesu wasu kuma kamasu nake in daure to amma wannan daban wasane, yanzu kuma shine zahiri tunda gasu akofar dakina, Na zargi kaina saboda barin kofar gidan danayi abude,ko da yake daman kuma kullum ahaka take kwana saboda maziyarta da abokan arziki dasuke yawan zuwa gurina da daddare to amma ba karfe biyu da rabin dare irin wannan ba........... Raf Raf Raf aka ci gaba da kwankwasa kofar Na yunkura hantar cikina na rawa na nufi kofar dakin, ina ta salati da salalallami. Wai.....wai wane ne? Nace muryata ashake ban iya shaida muryar amatsayin tawa ba. Maimakon abani amsar sai naji an sake kwankwasawa, Wa......Nene? Na sake kuma tambayar shiru ba abani amsa ba haushi ya kamani sannan sai na tuno da fim din DAREN MUTUWA Muntaba wani sin mai kamar wannan inda barayi suka zo suna kokarin balla kofata nikuma na bari sai da suka gama jingina ajikin kofar sannan na bude suka zubo cikin dakin kamar an hankadosu nikuma nabisu na daddakesu. To yau ma zan kwatanta. Nace cikin zuciyata Saidai kuma wannan karon inhar Allah yabani sa'a suka zubo cikin dakin to tsallakewa zanyi na gudu. . Aka

Chapter 1 of 5