Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 2
shi sai cutarwa. Habib! Ka san menene ke tsorata ni fiye da komai?" Yafada yayin dayayi shiru,ni kaina sai na tausaya masa. "Aduk lokacin da mai sihiri ya mutu,jeka ka tona kabarinsa idan har kana da karfin yin hakan. Abin da zaka gani ciki ba zaisa kayi sha'awar kasancewa cikin wannan hali ba. Habib! Ni kaina ina son na daina sai dai ina!shaidan yayi alkawarin batar da duk wanda baifi karfin zuciyarsa ba" Ya samu dakiku biyar kawai ya kurawa kwalbar ido,tamkar yana mamakin ganinta a hannunsa. "Ka taya ni addu'a habib" Lokacin daya fada hawaye ne a idanuwansa,amma yana rufe bakinsa sai ya kafa kwalbar giyar a bakinsa ,yaci gaba da zazzaga ruwan a tumbinsa . Tun daga lokacin bai kara cewa uffan ba ,haka zalika ni ma bance masa komai ba . Har sai lokacin da anas ya idar da sallar ya karaso inda muke. "Yanzu dandash mene ne abun yi ?" Ya bukata. Batare da dandash yayi magana ba ya buda jakarsa ya fito da wani sumulmulen farin dutse ya dora shi a hannun hagunsa,kana sannu a hankali yafara. Shashshafa dutsen da hannun damansa. Bai dade yana yin hakan ba sai mukaji yanayin magana da farko ba mu samu fahimci meke faruwa ba ,sai da muka ga ya tattara hankalinsa ga ruwan,sannan nima na kalla. Cikin sauri na dauke idona a razane nan da nan bugun zuciya ta ya tsananta,cikin kankanin lokaci gumi ya rinka keto min,take jikina ya rinka tsima kamar mazari,ba na son kallon abinda na gani . Fuskar mummunar matar dana gansu, tare da fareeda ce ta bayyana akan ruwan. "Yaya sunanki?". Dandash ya bukata . Taki yin magana . Yakara tambayarta shiru,sai ya matsa dutsen dake hannunsa. "Sunana G-A-R-M-O-D-A!" Tafada cikin shakakkiyar muryA. "Ina farida" wannan karonma taki magana ,shima sai ya kara matsa dutsen. "Tana taredamu" alokacinne na fahimci ta hanyar matsa dutsen ne ya ke tirsasa ta take magana . Kamar yarda masu yin (ruqiyya) ke tirsasa aljanu suyi magana ta hanyar karanta Alqur'ani. "Bamu labarin komai" dandash ya bukata. "Shugabanmu ne yakawota,kuma yafi sonta fiye da kowacce macen dake tare damu. Shine da zaiyi tafiya ya bani umarnin kula da ita,cewar duk inda zani kafata kafarta. @mr:shuraih 99% Nikuma dama aikinane dukinda ake gagarimin taro indai na mata ,zan rika bi ina dauko kyawawa daga ciki. Ina kawowa shugabanmu. Sanin cewar kyawawan mata zasu halarci wasan kwallon kafar da za agudanar, (nigeria 99) shine na tafi da ita . A lokacin danake kokarin dauke wata kyakkyawan yarinya,shine habib yahadu da ita ,sukayi hira yabata zobe,ta kuma kwatanta masa gidansu. Zoben daya bata shine na mayar,kan kabarin da jama'a ke tunanin gawar farida na ciki. Nayi hakanne don kawar da zarginsa Idan yagani kada ya dauka farida mutunce, alokacin dayake kan hanyarsa ta zuwa gidansu na tura da zoben. Ganin bai hakura ba yana neman bayyano sirrin shine naso na zautashi ta hanyar baiyana cikin haske siffar fareeda ,yayinda yake tsaye akan kabarinta karo na biyu. Addu'ar dayayi itace ta zamar masa garkuwa ,daga wannan sharrin dana tasamma yi masa" Alokacin dana ji wannan batu , nayi matukar mamaki da tuni na zama zararre. Anan kuma na kara fahimtar,wannan hira da dandash keyi da Garmoda,taso tayi daidai da wani abu da turawa keyi wa mutumin da yayi wani abu kwata kwatakuma ya manta. Idan anso ya tuna sai ayimasa wani abu da suke kira (hypno analysis) @mr:shuraih 99% "Wanene shugaban naku? Ta yaya kuke daukar mace ? Me kuma yakeyi da matan?" Dandash ya katse min tunanina . Wannan tabyar da yayi .rufe bakinsa keda wuya,kamar walkiya ta baiyana ta bace ,sai kwatsam !ganinmu mukayi a wani irin gida ,yayin da ruwan yayi ambaliyar ba-zata da mu. A razane na kalli anas da shima tuni ya rude ,dandash kuwa ya fice daga hayyacinsa . A sannane na fahimci Garmoda ta yiwa dandash ,abinda baiyi tsammani ba. Kuma da dukkan alamu a Fadar shugabansu muke . Can sai wani jibgegen kato kamar wanda yahada dangantaka da samudawa ,kyawawan matan zagaye da shi ya nufo wajenmu. Farin kyalle ne daure a jibgegen kansa,anyi daran rubutu da bakin fenti BARBUSHE. 9"Aaaah!"Nafada yayin da jibgegiyar kafarsa ta dira a timbina .Yakara tallafo fuskata ya gabza min mari,wannan karon kasa yin ihu nayi.Ya cakumo kwalar rigata da jibgegen hannunsa har sai d fuskata tazo daf da tasa.Ya kura min ido da jibga-jibgan idanuwansa,masu kama da garwashin wuta.Bazan iya hada ido da shiba ,kawai sai na rufe idanuwana .Ina jin zazzafan numfashinsa na bugun fuskata.Ban dade da rufe idanuwana ba sai jin bugu. Nayi a kirjina ,"Uuhhh!" Cikin halin jin matsanancin radadi nayi kug.Alokaci guda kuma ya cillar dani .Matukar zogin danaji yayin dana gwaru da bangon dakin shi yatabbatmin kasusuwan bayana sun kakkarye.Das! Jibgegiyar kafarsa tayi dirar ungulu a kwanyata .Nazata raina ne ke shirin ficewar daga jikina ,A lokacin dawasu irin taurari suka ziyarci ganina .Sai daga bayane na fahimci ashe suma nayi.Cikin halin matsanancin ciwo da azabbabben radadin dake azabtar da duk wata gaba dake jikina .Kwalkwalta kamar ta tarwatso daga cikin kokon kaina,saboda masifaffen zogi.Da kyar da jibin goshi nadan bude idanuwana.@mr:shuraih 99%A halin jina jina naga Anas da kuma dandash ,shine ya tabbatar min suma sun sha dan karen bugu kamar yadda nasha.Na lura da yadda jininmu ya fantsamu nan da can ajikin bangon dakin."Nhmm....". Cikin halim yar karamar murya mai cike da tausayi ,shima anas ya farfado.Bayan ya bude idanuwansa ya fahimci halin da muke ciki,sai yadaga hannuwansa,yafa ra Addu'a. .A duk halin da bawa yasamu kansa babu abu mafi alkhairi gare shi irn fadawa ubangiji bukatunsa nikaina sai na fara Addu'a.Bayan mun gama addu'a sai dandash shima ya farfado.Duk dani kaina a galabaice nake sai na da tausaya masa ,yayin dana kalli galabaitacciyar fuskarsa .Ya kalle ni kana Anas,sannan ya umarcemu da mu matsa kusa da shi.Bayan ya kwanto wata doguwar siririyar fata daga kugunsa.Sai yakara mayar da fatar kugunsA ya daura sau daya ,sannan ya rike hannun anas dake bangaren hagunsa ya kure da jelar fatar.Ni maya kama hannuna da daya jelar fatar ya daure tamau.Kawai mu dai munzuba masa ido ne ,domin munsan akwai al'amarin dayake shirin aiwatarwa.A daidai wannan lokacin sai kofa tabude.Barbushe da aka rubuta balo-balo da bakin fenti dake daure a jibgegen kansa shine ya shigo dakin .Kamar lokacin farko,wannan karon ma kyawawan mata ne hagunsa da damansa,daban kirga adadinsu ba.Bayan ya shigo dakin sai kuma garmoda ta shigo,kallo daya zakayi wa mummunar fuskarta kasan arazane take.A bayanta sanye da bakin kwat da siket din dana fara ganinta dasu a rayuwarta .farida ce.@mr : shuraih 99%Shiru ya mamaye dakin tamkar mutuce ta ratsa ,in ka dauke zuciyata dake barazanar faso kirjina ,don matsanciyar bugun da takeyi.Na kalleta sama da kasa ,naga shakka babu farida ce,saina ji wani irin ni'imtaccen sanyin soyayyarta ya keta zuciyata.Wanda har na manta da ciwon da zogin dake addabata.Tunda ta shigo dakin babu wanda ta kalla,kawai dai ta sunkuyar da kanta ,ta tattara hankalinta ga kyakkyawan zaren da ke hannunta,kamar lokacin farko da muka hadu.Dana lura da hannuwan sauran matan,duk akwai irin wannan zaren,kuma irinsa ne suka manta a villa guest inn.Jibgagen katon yakalli dandash da anas,sannan ya dawo da hankalinsa gareni.Ganin ina kallon farida yasa yayi mini wani irin kallo,wanda fal kallon yake da matsanancin kuna ,kasancewar yana son farida fiye da komai,kamar yadda garmoda ta fada.Dukkaninmu muka yi jugum, kamar berayen da kyanwa ta ritsa.Ganin na dauke kaina sai ya mayar da hankalinsa ga garmoda .Babu abinda ke bani mamki da shi irin tun daya fizgo mu zuwa fadarsa, har zuwa yanzu ban ga motsa bakinsaa ba ,ballantana yayi magana.Cikin kankanin lokaci gaemoda ta fice daga hayyacinta ,yayinda kai tsaye barbushe ke kallon cikin idanuwanta.Jikinta gabadaya ya rinka kakkarwa,kamar wacce ake gasawa da wuta .Tun tana dan daurewa dan kada tafadi kasa,Amma ina !sai data yanke jiki tafadi kasa wanwar . Akwai wani lokaci dana taba ganin wata kyanwa ta kura wa kadangare ido,kadangaren makale yake ajikin katangan wata kango,inda. Babu yadda za ayi magennan ta riskeshi,kuma dan motsawa kadan zaiyi ya gujewa magen ta daina ganinsa .Amma cikin wani hukunci na ubangiji kadangren ya kasa zuwa ko ina,kawai sai ya tsaya yana ta makyarkyata ,har sai daya fado magen ta dauka .To shine yayi daidai da abin da abin danake gani yanzu¤¤¤¤ Kiri kiri a idonmu ,garmoda ta fadi tana makyarkyata ,kana ganin yaddda mummunar fuskarta ke ya mutsewa cikin kunci,kasan ranta ne ke shirin barinn jikinta.Wani abu daya dada girgiza tunanina shi ne narkewa da ta ringa yi tamkar yadda dalma ke narkwa a kan wuta.Ina ganin lokacin da anas ya makalkale jikin dandash, yayin daya dauke idonsa daga kallon abin al'ajabin dake faruwa.Wannan shine yayi daidai da lokacin da garmoda tazo min da siffar farida yayin danake tsaye akan kabarin farida.Shakka babu wannan sihirine mabaiyani.A daidai wannan lokaci sai dandash ya tube hukar dake kansa,yaciro wani kambu dake damtsen hannunsa na dama yasaka acikin hular,cikin halin saurin baki ya ringa fadan wasu yamutsasstsun kalmomi yana yawu akambun dake cikin hulat.Basai wani ya fassar min meyake shirin aiwatarawa ba,sihiri zai yi ahankali sai hayaki yafara tashi daga cikin hular.Dana mayar da hankalina ga barbushe ,yana nan yadda yake tsaye akan garmoda dake narkewa cikin haske.Kamar daukewar wutar lantarki, babu wani abu da yayi saura daga gareta ta narke .babu ita sannan babu wata shaidan da zata tabbatar dazu ta tsaya awajen.Bazan iya tuna hakikanin yadda al'amarin yafaru ba ,ni dai kawai abinda zan iya tunawa naga hayaki na fita daga cikin hular dandash ,lokacin daya cilla ta daki fuskar farida .Cikin abin da baifi dakika ba gabada dakin ya turnike da hayaki,tamkar ilahirin gidan ne ke shirin gobarewa."Alelujah" jibgegiyar muryar barbushe mai kaman fashewar nakiya ya gauraye ilahirin dakin ,yayin dayayi wata irin faduwar bazata .Kamar daukarsa akayi aka fyada da kasa .Sai tsintar kaina nayi har yanzu hannuna daure tamau ,ga dandahs da kuma anas dukkaninmu ya janye mu daga fadar barbushe zuwa tsibirn dazu.Babban taimakon da muka samu abakin gaba muke.Cikin abin da baifi dakiku uku ba ,muka fito waje haryanzu jakar fatar dandash da kuma kwalaben giyarsa guda biyu na nan a wajen.Daya ya shanye ,daya kuma akwai ragowar 'yar kadan.@mr:shuraih 99%Ba sai dandash yayi bayanin halin dayake cikiba kallonsa kawai zakayi ka fahimci ya fimu jigata .Don sai da muka taimaka wajen fito dashi daga ruwan.Yayi yunkurin kwance mana hannayenmu amma sai ya kasa.Ganin abin daya ke nufi sai muka kwance hannayenmu.Anas na kwance hannunsa sai ya durkusa akan gwiwowinsa ya fuskanci gabas ,kana yadaga hannayensa sama alamar rokon Allah yakeyi .Cikin karfin hali dandash ya yafito ni, alamar na kai kunnena bakinsa."KASHE KANTA ZATA YI" .da kyar maganar ta fito daga bakinsa ,yayin daya yi min nuni da hannunsa.Ina kallon abin dayake nuna min sai hangar farida nayi ta jike sharkaf alamar ita ma ruwan ta fado,kamar yadda muma muka fado.Sai dai ita har ta riga ta fita kuma ta rufa aguje,kamar wacce ke shirin tashi sama."KASHE KANTA ZATA YI". Maganar ta kara daidai tuwa a kwalkwalwata."Farida" muryata ta cika dajin cikin tsohion daren lokacin da raina kamar zai fita don gudun hana ta yunkurin kashe kanta,da take shirin aiwatarwa.Domin sai daga bayane na fahimci wani tangamemen ramine ,dake nesa kadan daga inda take ,shikuma ta ke shirin fadawa.Gudu take yi,Gudu nakeyi.Tana dada kusantar ramin,ina dada kusantarta.A daidai lokacin da take shirn taka takun karshe ,wanda daga shi sai мυη ~ ĵι~ мυη ~ gαηι ¢ιgαвαη ѕιяяιηѕυ ωαяηιηg : вα'α кαяαηтα Ļιттαƒιηηαη đα đαđđαяє ѕαвσđα gυĵєωα мυgαуєη мαƒαякαι αυтнσυя: мαĵє єĻ нαĵĵ ωяιттєη : ѕнυяαιн υѕмαη ¢нαρтєя : 10 Kiri kiri a idonmu ,garmoda ta fadi tana makyarkyata ,kana ganin yaddda mummunar fuskarta ke ya mutsewa cikin kunci,kasan ranta ne ke shirin barinn jikinta. Wani abu daya dada girgiza tunanina shi ne narkewa da ta ringa yi tamkar yadda dalma ke narkwa a kan wuta. Ina ganin lokacin da anas ya makalkale jikin dandash, yayin daya dauke idonsa daga kallon abin al'ajabin dake faruwa. Wannan shine yayi daidai da lokacin da garmoda tazo min da siffar farida yayin danake tsaye akan kabarin farida. Shakka babu wannan sihirine mabaiyani. A daidai wannan lokaci sai dandash ya tube hukar dake kansa,yaciro wani kambu dake damtsen hannunsa na dama yasaka acikin hular,cikin halin saurin baki ya ringa fadan wasu yamutsasstsun kalmomi yana yawu akambun dake cikin hulat. Basai wani ya fassar min meyake shirin aiwatarawa ba,sihiri zai yi ahankali sai hayaki yafara tashi daga cikin hular. Dana mayar da hankalina ga barbushe ,yana nan yadda yake tsaye akan garmoda dake narkewa cikin haske. Kamar daukewar wutar lantarki, babu wani abu da yayi saura daga gareta ta narke .babu ita sannan babu wata shaidan da zata tabbatar dazu ta tsaya awajen. Bazan iya tuna hakikanin yadda al'amarin yafaru ba ,ni dai kawai abinda zan iya tunawa naga hayaki na fita daga cikin hular dandash ,lokacin daya cilla ta daki fuskar farida . Cikin abin da baifi dakika ba gabada dakin ya turnike da hayaki,tamkar ilahirin gidan ne ke shirin gobarewa. "Alelujah" jibgegiyar muryar barbushe mai kaman fashewar nakiya ya gauraye ilahirin dakin ,yayin dayayi wata irin faduwar bazata . Kamar daukarsa akayi aka fyada da kasa . Sai tsintar kaina nayi har yanzu hannuna daure tamau ,ga dandahs da kuma anas dukkaninmu ya janye mu daga fadar barbushe zuwa tsibirn dazu. Babban taimakon da muka samu abakin gaba muke. Cikin abin da baifi dakiku uku ba ,muka fito waje haryanzu jakar fatar dandash da kuma kwalaben giyarsa guda biyu na nan a wajen. Daya ya shanye ,daya kuma akwai ragowar 'yar kadan. @mr:shuraih 99% Ba sai dandash yayi bayanin halin dayake cikiba kallonsa kawai zakayi ka fahimci ya fimu jigata . Don sai da muka taimaka wajen fito dashi daga ruwan. Yayi yunkurin kwance mana hannayenmu amma sai ya kasa. Ganin abin daya ke nufi sai muka kwance hannayenmu. Anas na kwance hannunsa sai ya durkusa akan gwiwowinsa ya fuskanci gabas ,kana yadaga hannayensa sama alamar rokon Allah yakeyi . Cikin karfin hali dandash ya yafito ni, alamar na kai kunnena bakinsa. "KASHE KANTA ZATA YI" .da kyar maganar ta fito daga bakinsa ,yayin daya yi min nuni da hannunsa. Ina kallon abin dayake nuna min sai hangar farida nayi ta jike sharkaf alamar ita ma ruwan ta fado,kamar yadda muma muka fado. Sai dai ita har ta riga ta fita kuma ta rufa aguje,kamar wacce ke shirin tashi sama. "KASHE KANTA ZATA YI". Maganar ta kara daidai tuwa a kwalkwalwata. "Farida" muryata ta cika dajin cikin tsohion daren lokacin da raina kamar zai fita don gudun hana ta yunkurin kashe kanta,da take shirin aiwatarwa. Domin sai daga bayane na fahimci wani tangamemen ramine ,dake nesa kadan daga inda take ,shikuma ta ke shirin fadawa. Gudu take yi,Gudu nakeyi. Tana dada kusantar ramin,ina dada kusantarta. A daidai lokacin da take shirn taka takun karshe ,wanda daga shi sai.................... Zanci gabaPart 11 Last page Tana dada kusantar ramin,ina dada kusantarta. A daidai lokacin da take shirn taka takun karshe ,wanda daga shi sai ramin adai dai lokacinne hannuna yayi nasarar kamota . LAST PAGE ERROR . Jama'a dayake kunsan wannan littafi tsohon ajiya ne , toh yanzu dai karashen littafin ya yage Amma ga abun da karashen fallen littafin ya kunsa ******* Mun yi nasarar tseratar da Farida da kuma karya Asirin da Barbushe yai mata, Daga nan sai dandash yayi sihiri muka bace a cikin dokar dajin nan muka bayyana a gida ***** Jaridan Dankari jaridace ta mijin yayana Ahmad, a jaridan tayi suna da karbuwa sosai a wajen al'umma inda mutane suke jiran fitowarta duk sati . Wannan karon Jaridan na dauke da firgitaccen labari wanda mutane da dama bazasu taba yarda da shi ba, a shafin Farko na jaridar an sanya hotona dana farida cikin manyan launi, a saman hoton an rubuta (......) Na manta abun da aka rubuta friends . Wannan yasa jaridan na wannan satin ta samu karbuwa sosai mutane da dama da suka sanni suka runga zuwa wajena muna gaisawa suna yimin barka , ****** Yan sanda sun samu nasarar kama barbushe da dukkan mukarrabansa ma'abota tsafi ******** Tangamemen falone mai madaidaicin girma, iyayen farida da iyayena suna zazzaune akan wasu dogayen kujeru masu matsakaicin tsayi, a gefe daya kuwa Anas,Dandash da insfekta Sagir suna zazzaune suma akan kujera mai mazauna uku, ni kuma ina zaune akan kafet din tsakar dakin fuskana na kallon kafet din, Mahaifin farida ne ya fara bude taron da Addu'a sannan ni na tashi na fara kawo labarin tun farkon haduwana da farida , har ta kwatanta mani gidansu, da zuwana gidan da nayi aka tabbatarmani ta dade da mutuwa da sake ganinta dana ke a wurare dabam dabam, Har zuwa lokacin da na hadu da anas muka je garin su dandash , Dandash ya mike ya fara bayani, akan mutuwan sihiri, da yadda ma'abota tsafi suke sanya mutum yayi doguwan suma bayan an bizneshi suje kabarinsa su ciroshi su maye gurbinsa da wani abun daban , ** Godiya sosai mahaifan farida sukai mani, Bada dadewa ba aka sanya Ranar Aurena da farida, *** Abubuwa sun daidaita yanzu dandash ya musulunta, Bayan haka da mukaje muka tone kabarin Farida sai muka tarar da tarin itacen giginya ne a ciki . Alhamdulillah MAJE EL HAJEEJ HOTORO 1999 . Anan muka kawo karshen littafin MUN JI MUN GANI cigaban SIRRINSU, Ya Allah duk wasu kurakuren dana tafka cikin littafin Allah ka gafarta mani , JIN JINA GA Ilyas ishak gundutse Muhammad Maiyi ninko Yarima a gangariya Sadeeq Shehu Shareef, Matukar jinjinawa gareku na jmiri da jiran Postin dina ILYAS ISHAK GUNDUTSE MUHAMMAD MAIYO NINKO SHAMSU A BAITI ALHASSAN ADAMU ALA Usman Ubale SafUs Rano Shaheedah Fahat Ma'aji Da sauransu . FATAN ALKHAIRI GA AHALIN Taskar Gidan Littafi Tsangayar marubuta . Littafin da zan kawo maku na gaba shine AJALI daga Gidan Littafi . Littafin yazo maku ne daga shafin http://hausaebooks.cf A kowani yanayi, ko wane lokaci zaku iya shiga shafin don dauko wasu littatafan masu kayatarwa An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 2 of 2