Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MUN JI MUN GANI Cigaban Sirrinsu Na Maje elhajeej Typing by Shuraih Usman Ebook creator Shuraih 99% Ebook publish by http://hausaebooks.cf . Zaku iya downloading wasu ebook namu ta hanyar dannan wannan adireshin yanar gizo gizon http://shuraih.waphall.com . "Habib daman kai muka kama jiya da daddare" Kaman daga sama naji muryan sageer daga bayana ina juyowa kuwa naci karo dashi, Sanye da kakin yan sanda ya tsaya ajikin karafan da suke manne da kofar cell din a ak kulle ni aciki. Sageer abokinane. Munyi secondry tare dashi har takaimu ga ga jami'a "Sageer" cikin mamaki nafada . "Ina katsaya jiya har kakai dare haka" Sageer yafada yana duban fuskana cikin mamaki shima. Anan dai na ware mai bakin jaka Tun daga haduwata da farida har jiya dana bisu har cikin villa guest inn , Na tafi sanar da iyayenta al'amarin ya kasance akaina . Lokacin danake fadamasa labarin tattara hankalin sa yayi gareni bayan na idar sai yayi jugum, kana ya nufi wata durowar tulin takardu dake jingine a ofishin, yafara lalube-lalube har sai daya zakulo wata jarida,sannan ya bude inda yake son budowa , kana ya ajiye min agabana . Wanda hakan na nufin yana bukatar na karanta "A GHOST WAS MY HUSBAND FOR SIX YEARS WE HAD TWO CHILDRENS" (Na auri fatalwa har tsawon shekaru shida,mun kuma haifi 'ya'ya biyu tare) Abin da idona yai karo dashi kenan ,lokacin dana fara karanta jaridar.cikin sauri na juya bayan jaridar. Jaridace mai suna Glow,fitowa ta goma shatakwas , da ake wallafawa a ikeja dake jihar lagos , akwatin gidanwaya 10352. Matar da al'amarin ya faru gareta ga hotonta nan balo- balo ajikin jaridar . "Lokacin dana karanta kabarin ban gaskata ba, sai yanzu da ya faru gareka ,karanta kaji abin dake kunshe cikin labarin ,daidaine da abin daya faru gareka ," Sageer yafada yayin da hankalina ke kan hoton matar da al'amarin yafaru gareta . *Shuraih usman* (Labarin yana shafin ishirin da tara na jaridar kuma agurguje abin dake kunshe da labarin shine: Maimunat haruna ta hadu da cletus ne a wajen wata liyafa ,tun daga ranar taji ta kamar ta hadeyi shi saboda masifarsonsa da taji tanayi. Kota ina ya kwanta mata azuciyarta ,saboda kyakkyawane ya kuma iya kwalliya . A kasancewar da su kayi tare ta fahimci cewar batare da iyayensa ya keba , yakuma rabu da iyayensa lokaci mai tsawo baya kuma son komawa wajensu . A tunaninta idan tarabu dashi bazata kara haduwa da namijin da zai shiga zuciyarta kamarshiba , bata kuma tunanin rabuwa da shi . Saboda tarairayarta daso da kauna dayakeyi. A takaice dai har takaisu gayin auren shekara shida , suka kuma samu yaya biyu junior da betty. Sannan ne tarinka matsanta masa akan dole sai sun ziyarci danginsa ,da kyar da jibin goshi ya amince. Jihar filato nan suka nufa wata ranar litinin,suna zuwa wani waje sai ya tsiyar da motar, ya kwatanta mata gidan yace ta karasa yana tafe . Babu irin magiyar da batayi masa ba don sutafi tare , yalallameta akan taje shima yana tafe . Mahaifiyarsa tana fitowa ta shaidata saboda kama da sukayi da mijinta da kuma yayan dasuka haifa. Ita kanta mahaifiyarsa sai ta kurawa yayan ido don ganin sunyi kama da danta . Tana shiga gidAn taga hotunansa tun yana saurayi ,sannan ne tafadawa iyayensa tare dashi suke. Dukkansu sai suka rinka kallonta kamar daga wata duniyar ta zo,ita kanta sai data tsargu akwai wani abu dake shirin faruwa. Kafin wani lokaci makwabta sun taru agidan ,don gaiyatarsu da iyayensa suka yi ,anan ne suka bata tabbacin shekarun wanda ta ce shine mijinta ,goma shadaya da shekawa barzahu. (Lallai kam) *Mr: Shuraih 99%* ******* ********* ******* "Nasir! nakirawo sunansa lokacin ina tsayar da motar a kofar gidansu,shikuma yana shirin shiga gidan . Galala ya kura min ido ,tamkar fatalwa yake gani . Har na rufe kofar motar naje wajensa kallona yake yi, kamar ni, shi kansa kamanninsa sun birkita. Shakka-babu al'amarn akwai rikitarwa ya tabbata farida ta mutu sun kuma binneta ,sanna kiri-kiri ba mafarki yayi ba ya kara ganinta. "Habib! Yakirawo sunana cikin sanyayyiyar murya . Na rike hannunsa muka nufi inda na ajiye motar dana zo da ita ,gindin wata bishiyar mangwaro dake nesa kadan da kofar gidansu nasir. "Naseer! Danazo muku da labarin na gamu da farida ,ta kwatanta min nan gidan ,na kuma bata zobe kin gaskata ni kukayi. Kaine kadai ka yarda dani,yayin dana tsinci zobena akan kabarinta. Yanzu naji matukar dadi da kuka ganta kai da meenat , me kuma zaka ce yanzu game da wannan al'amari" Dukkanmu muka yi shiru na wasu lokuta . "Babu abinda zan iya cewa game da wannan al'amarin habib. Ni dai nasan tabbas ya ta farida ta mutu shekaru uku da suka shude , kuma tabbas na kara ganinta a kano" (Wasa mafarin aiki*Mr: shuraih 99%*) "Ranar alhamis da muka ga farida nida kai da kuma meenat ,kashegari ranar juma'a na kara ganinta tare da matar dana tambayeka ,kace baka santaba . Wacce muka gansu tare da faridar. Nayi kokari na bisu naga masaukinsu (Villa Guest Inn),dana bincika sai naga kusin kwana daya suka biya . Abin ya faru ne karfe ukun dare , nayi yunkurin sanar daku a tarauni jami'an tsaro suka cafkeni,na kwana a can sai yau na fito. Ko gida banjeba na koma villa guest inn din na tarar sun tafi . Ina zuwa ma'aikacin dana tambaya ya gane ni,ya kuma nuna min 'yar karamar jakarsu da suka manta ,wacce ya tsinta a dakin dasuka kwana kaga jakar(nafada lokacin dana dauko jakar daga aljihuna na nuna masa ). Kyawawan zararrika ne masu kyan launi guda tkwas aciki. Irin wanda na gani a hannun farida lokaci na farko dana fara ganinta. Sai kuma wani dan karamin kati an rubuta [BBH] ajiki. Shine na galla masa karyar dama farida ce ta aikoni na karbar mata jakar. Baiyi min gardama baya ni. Nakoma tarauni sulaiman ya sanar dani kun dawo gida .shine na biyo bayanku. *MR:Shuraih 99%* Kuma duba wannan jaridar kagani(na buda mota na dauko masa jaridar sageer na mika masa.). Wannan matar maimunat ta auri mutumin da shekarunsa goma shadaya da rasuwa,sunkuma haifi 'yaya biyu" "Shin yanzu ina mijin nata?" Yafada bayan ya gama karantawa . "Har yanzu bata kara ganinsa ba ,sai dai 'yayan dasuka haifa " Ina rufe baki sai mahaifiyarsu rike da hannun meenat suka fito dga gidan ,wani mutum yana biye dasu abaya . Basai aniyimin bayanin kowayeba nan take na fahimci mahaifinsu ne. Meenat na ganina sai ta kyankyame jikin mahaifiyarta ,yayinda ita kuma mahaifiyar take yi min wani irin kallo dake nuni da bata bukatan kara ganina kusa da iyalinta. Kai tsaye sai mahaifinsu ya nufo wajena. "Bana bukatar kara ganinka a kofar gidannan har abada , yaya kake nema kazauta mun ahalina (iyali munce yarmu ta mutu kace ba ta mutu ba , to ina ruwanka da ita !koa kai ka haife mana ita ! Idan nakara ganinka akofar gidna sai dai kuliya ta rabamu" Wlh abokina ne ya takurani saina Rakashi wajen budurwarsa. Amma gobe JLAHADI11 ~ 4 ~ '99Arayuwata ban taba haduwa da yamacen da cikin kankanin lokaci hasken sonta yahaskaka ruhina da har nake tunanin idan na rasata, son wata ya macen ba zai kara samun sarari a zuciyata irin fareeda ba.Babban abin dayake firgitani shine rashin sanin ta-ka-maiman shin farida mutumce,aljanace ko kuma fatalwa ! Shin dagaske ta mutu ko kuma tana da rai"Idan har farida ce ta ajiye zoben dana bata akan kabarin,farida bata mutu ba.Idan kuma tana darai menene dalilin kauracewA iyayenta ,bayan tasan inda suke ?Anaya babu hadin bakin farida ?Idan kuMa da hadin bakinta takunkumin ala-ka-kai, da'aka gindaya wa rayuwarta fa?Shin menene hadin farida da wannan mummunar matar?Kwata-kwata na gama tsarguwa ,da al'amuran wannan matar.Tun lokacin dana dawo daga kaduna ina zaune afalon gidan ahmad .zuciyata fal da tunane-tunane.Ita kanta fatima tazo ta zauna mu yi hira ,kamar yadda muka saba kafin inhadu da farida .Amma ganin cewar babu abinda zai iya janye hankalina daga tunanin da nakeyi,sai ta kyaleni.*MR:shuraih 99%*"Munce yarmu ta mutu ,kace bata mutu ba , to ina ruwanka daita!" Natuno da maganar mahaifin farida ,na tuna lokacin da jikina kamar ba laka ,natuka motata na bar kofar gidan."Idan nakara ganinka a kofar gidana ,sai dai kulliya ta rabamu ...."Shi kansa nasir bai so maganganun da mahaifinsa ya fada min ba .Ina ganin lokacin da hawaye suka zubo daga idanunsa,yayin dana shiga motata zan tafi.Shin yaya za'ayi na fatattaki saon farida daga zuciyata ?""Shakka- babu"Naji mauryar mace tafada adaidai lokacin dana ke tsaye a gaban dogon mudubin ina duba kwalliyar danayi tun kafin na waiga na san ko wacece ,domin na kasance da haka ta ke kirana ,kawas yaYata ce fatima ,tana kuma yawan barkwanci"Habiba " na kirawo sunanta lokacin dana waiga ita da kawayanta ne su uku dukkaninsu muka gaggaisa.*Mr:shuraih 99%*"Kinsan mene dalilin daYasa nake kiransa da shakka babu?"Ta tambayi daya daga cikin kawayenta."Yawancin duk maganar dazai yi sai ya fadi shakka babu. Yanzu daza a fasa cikinsa shakka babu ce taf aciki.idan kuma ka yi musu yanzu yanzunanmuje asibitin, nabiya a fedeka"Tafada tan yimini kallon zolaya.Idan nace zan daka ta habiba , bami lokaci zatayi,Kuma ni abin dake gabana shine halartar wasan kwallon kafar daza a gudanar tsakanin nigeria da kasar ireland.Azagaye na byu na gasar cin kofin matasa(NIGERIA'99) ko Allah zai kara hadani da farida a yanzu ma hotonta ne rike a hannuna ."Kai,kai,kai! Sagwai-sagwai, irn wannan luntsimemiyar ya sai kace ita tayi kanta "Habiba tafada lokacin da wuf ta fizge hoton farida dake hannuna .Tana fizge hoton sai naji kamar daddaureni tayi.domin babu inda zan iya motsawa sai ta bani hoton .Kuma babu yadda za'a yi tabani ba tare data bata min rai ba.*mr:shuraih 99%*"Sumaza burinsu kawai ace budurwasu kyakyawace ko kuma yar gidan masu hannu da shunice, sun manta da fadar masana sirrin mata cewa mata sirrine ,ba tukwane bane ballantana akwankwasa agane ta kwarai ,sai ka ga macen da maza ke yiwa kallon hadarin kaji ,ita ce kuma zasu samu nutusuwa da gamsuwa daga gareta "Habiba ke fada yayin da dukkansu ke kallon hoton.Duk dacewar ita ma kyakyawace ,na fahimci kishin kyan farida atattare da maganarta."To ,shin su mazan basa tunanin cewar ,idan kyakyawa da yar mai kudi kawai suke hange.suma matan akidatsu zata'iya komawa ,kyawawan samari da yayan masu kudi kawai zasu rika soyayya dasu .Su kuma munanan mazan da yayan talakawan ,sai suyi yaya?su rataye kawunansu?"Daya daga ciknsu tafada."Habiba ! Don Allah ia rokonki dAki taimaka ki bani hoton nan, ba nawa bane ,budurwar wani abokinace suka samu sabani a tsakaninsu,duk ta mayar masa da hotunansa ,shine ita ma take bukatar ya dawo mata da nata .Jiya ya dawo mata da nata wannan ne kadai ya manta,shine ya bani sako na mayar mata da abinta"*MR:shuraih 99%*Nafada cikin sanyayyiyar murya , kuma nayi mata karya ne saboda idan ta san nawane, zata dade tana jamin rai .tayi far da idanuwanta ,ta dan rausaya jikinta kana kuma tayi tattausan murmushi.."Allah sarki habib! Ina ma ace koda yaushe zaka kasance cikin wannan maganar da katafi da imanin mata.Domin bakaji inda ka narkar min da zuciya ta ba"Ba wai dadin yabon ne banji ba ,domin yamace takan so namiji ya yabata ,kamar yadda kowanne namiji ke son mace ta yabe shi.Sai dai buri da doki son kara haduwa da farida yafi min komai a rayuwata ."Eh wallahi abin tausayi .ko bahijjah"Daya daga kawayenta tafada ,yayin datake kallonta kusa da da ita."Don Allah habiba bashi hotonsa"ita ma dayar tafada.A daidai wannan lokaci fatima ta shigo falon.*Mr:shuraih 99%*"Fatima shin wannan budurwan habib ce ,ko kuma da gaske budurwar abokinsane ?"Habiba ta tambaya yayin datake nunawa fatima hoton."Bai baki labarin wacece ke jikin hoton ba,cikin mamaki habiba ta bukata.A nutse fatima ta labarta musu komai ,bayan sun zazzauna .Dukkaninsu sai suka tattara hankalinsu ga hoton farida ,suna masu cike da matukar mamaki."Habib na taba samun irin wannan labarin ,amma kin gaskata shi nayi,habiba tafada.Kanin mahaifiyata Anas, shine ya sanar dani labarin abokinsa ,da shima ya hadu da wata yarinya a marhaba cinema.A lokacin ana ruwan sama ,ita kuma ta fake awani waje tana ta rawar dari.Ganin haka yasa ya cire kwat din jikinsa ya bata tasa,Bayan ya je wajenta sunyi hira ,ta kuma kwatan ta mai gidansu .Suka rabu akan kashe gari zai je gidansu,kuma idan yaje ya karbo kwat dinsa .Karfe taran safiya yamai a kofar gidansu dake madobi,kamar yadda ta kwatanta mai. Da suka bashi tabbacin ta dade da mutuwa ,kin yarda yayi. Kamar yadda yafaru ga habib,shi ma sai ya tsinci kwat dinsa akan kabarinta da aka kai shi don gamsar da shi ce war ta mutu. Da zakayi kokarin samun Anas ,zai yi matukar taimaka maka, ka fahimci hakikanin al'amarin. Domin ya kasance mai yawaita bincike akan abubuwan da suka shafi taurari da kuma abinda ya shafi aljanu(Ostrologist) kasan shi,shima ya sanka. ******** *********** ******** A daidai lokacin da dan'acaban dana ke kai zai gifta makarantar 'yan mata ta shekara sai na hange shi daf da makarantar tsaye suna tattaunawa da wani abokinsa. Na umarci dan-acaban yakaini inda suke, na biya shi yatafi. "Habib yakira sunana yayindana mika masa hannu muka gaisa da shi da abokinsa. Nafada masa cewar dama wajensa zani.kai tsaye yace mu wuce gidansa a umguwar yakasai yake da zama. "Habib yanaga kana ramewa kamar wanda ke hadiyar Allura? Koduk ayyukane ? Domin na sanku daywan zirga zirga" Yafada bayan mun zauna a falon gidansa. *Mr: Shuraih 99%* Yafada lokacin dayake rike da hannuna ,nayi rungumiyar ajiyar zuciya,sannan na mika masa hoton farida . "Tabarakallahu fi Ahsanil khaliqin(hakika ubangiji shine mafificin tsara halitta kuma ta tsaru), hakika yarnan ta halittu habib" Yafada yayin da idanuwansa ke kan hoton. "Kuma dalilintane rayuwata ke cikin jidali" "Wai kana nufin tafi karfinka" yabukat. "ranar asbar 3/4/99 ranar da kasar kwastarika tayi wasa da nigeria a legas,na hadu da ita ta kwatantamin gidansu akaduna kashegari ranar lahadi 4/4/99 na bita gidansu,iyayanta suka bani kwararan hujjojin da suka gamsar dani shakka-babu shekarunta uku da mutuwa,na kuma tsinci zoben dana bata akan kabarinta ,kana sau biyar ina sake ganinta a wurare daban daban" Yayi shiru na wasu lokuta ,bayan yafita tsakar gida yadaga kansa yakalli sararin samaniya. "ALLAHU - AKBAR! ALLAHU - AKBAR!! ALLAHU - AKBAR!!!" Yafada harsau uku sannan yadawo da hankalinsa gareni,ya kuma dafa kafadana. "Habeeb! IN HUWA HAZA SIRIHUN AZIM! Wannan sihirine babba . Kafin na war ware maka sirrin komai dalla dalla , ina mai sanar dakai faduwace dai tazo daidai da zama kuma kayan falke ne sika tsinke a gindin kaba". "Mekake nufi anas?" "Ina nufin gobe zamuyi wata tafiya ,tafiyar dazat budewa rayu warka sabuwan kofa ,kuma itace tafiyar dazata warkar da lalulurar dake addaban rayuwarka". "Anas fahimtar dani abinda kake nufi" "Faridar da iyayenta suka tabbatar maka da hujjojin mutuwarta,ita ce dai faridar daka hadu daita a lagos ,itace faridar daka bawa zobe ,haka kuma itace faridar daka hadu da ita a wurare daban daban" Cikin kaguwa da birkita na rike hannuwansa . "Shin anas kana nufin faridar dana hadu da ita mutumce mai rai " "(LA - SHAKK FI HAZAL AMRI) BABU - SHAKKA ACIKIN WANNAN AL'AMARIN K LITININ 12 ~ 4 ~ 99Jama'a ne makil atattare wajen kaman duk al'umman kauyen ne suka hallara a wajen.Duk sunyi da'ira kana kuma sun tattara hankalinsu ga wani abu dake wakana a wajen.Kallo daya zakayi musu ka fahimci duk abin da suke kallo bakaramin jan hankalinsu yakeyiba .Haka-zalika suna matukar jin dadin kallon.Daga inda muke ina jiyo tashin sautikan muryoyin jama'ar wajen gauraye da kuma sautin kidan ganguna.Na kare fuskata da tafin hannuna daga hasken ranar dake dimama kwanyata ,duk da cewar da yamma muka sauka a garin,har yanzu akwai ragowar zafi atattare da ranar."Habeeb! Wannan shine garin bidda,karamar hukuma ce (local government) dake karkashin jihar nigar.TAFIYA MABUDIN ILMI, wannan tafiyar,tafiyace da zata mayar maka da fari ya koma baki, ka kuma yarda da hakan, bayan ba hakan bane .Duk abinda kagani ya kuma dada ka da kasa , rubuta domin zakaci karo da dimbin abubuwan da zasu kara girgiza tunaninka"Anan yafada lokacin daya rike hannuna muka nufi wajen taron al'ummar.*mr : Shuraih 99%*Rike da hannuna ya rinka kutsa taron .Kuma duk wanda muka ba'a son ransaba,Sabida wasu tsaki suka rinka yi,yayin da wasu suka ringa guna-guni da yarensu,wanda ba fahimtar abin dasuke fada nakeyiba .Wanda hakan ne yakara tabbatar mini suna kin duk wani abin da zai janye hankalinsu daga abin da suke kallo.Sai daya kasance muna ganin wainar da'ake tayawa atsakiyar taron sannan muka tsaya.Sakamakon don jama'ar wajen sun zagi mutum dun kawo musu cikas ga abin da suke kallo basuyi laifi ba .Wasu mutane ne guda biyu kowanne rike da takobi a hannunsa ,daga su sai bantai,gabadaya fuskokinsu sunyi faca-faca da jini.Gajeran ciki baki mai dankwalelen hanci,ya kaftawa kuncin dogon mai zungureriyar keya sara da takobi ahannusa.Kai tsaye takobin ya ratsA kuncin, fata ce kadai tarike tsokar jini ya rinka tsattsafowa daga tafkeken raunin.Kiri-kiri wanda aka sara din ya tallafa tsokar, ya mayar da ita inda aka sarota. Kamar a shirin film din al'mara,sai tsokar ta koma ta like tamkar dama ba a sari wajen ba ,jini kadai ya rage a wajen.*mr:shuraih 99%*Bayan ya like kuncin nasa, sai shima ya sari kunnen dogon mai zungureriyar keyar.Shi ma fata da jijiya ne kadai suka hana kunnen faduwa kasa.Kamar yadda dan uwansa yayi shima ya mayar ya kuma like.Wannan rikitaccen al'amari danake gani ayanzu shakka babu bashine na farko dana fara ganin irinsa ba.A shekarar daza a rantsar da zababben gwamna na farar hula na jihar kano alhaji kabiru ibrahim gaya,naga wannan wasa mai suna (SHANCI)Idan ma ka ziyarci balare cikin ajingi ko falali bangaren sumaila ,ko kuma fala wajen rano da kibiya,duk maguzawa suna irin wannan wasan .Bayan su fice daga tsakiyar taron sai mai zungureruyar keyar ya dawo fes babu alamar jini.Ya nufi inda wasu gingima gingiman akwatunan katako suke irin wadanna zaka rinka gani a wajen masu wasa da miciji.Ya buda daya daga ciki ya dauko kwalba babu komai a cikinta,sannan ya kara debo kwayaye guda uku,kiri -kiri a gabanmu ya ringa saka kwayayen daya bayan daya har sai da duk yasaka su cikin kwalbar.Abin mamaki shine ba wai kwaiba,hatta tsakuwar da bata kai rabin- rabin kwai ba baza samu damar shiga kalbar ba.Saboda kankantar karamin bakin kwalban $Mr:$huraih 99%Ya nunawa mutane tabbas ga kwayayen cikin kwalbar,ya kara buda akwatin ya dauko wata zurmukekiyar kayar beguwa,ita ma yadaga yanuna mana sannan ya rinka zurata cikin hancinsa sai da ta kule dif.Sannan kuma ya zarota.Bayan wannan sai yadauko jarida ya warwareta muna kallo kana ya kanannade kamar yadda akeyin gurguru."BE"yafada yana yafito wani yaro,duk da ban taba jin kalmar ba , nafahimci(zo)yake nufi.Ya bawa yaron ruwa yakuma umarceshi daya dura ruwa cikin jaridar.duk dacewar ruwan daidai da dis ba digaba .Bayan mutane sun dauka wannan ne abin mamakin,daya warware jaridar babu komai cikinta,Da kuma ya kara nada jaridar ,sai ya rinka zubo da ruwan .Ya yagi takardar ya sa abakinsa,sai ya ringa fitar da sababbin Allurai da rezozi daga bakinsa .Duk irin wannan abubuwa yan bori da masu wasa da majizai sukan yi ire irensu(ru'ido).Daga karshe bayan yayi abubuwan al'ajabi da dama .sai kuma tsam ! Aka nemeshi sama da kasa aka rasa .Daga shi har akwatunan nsa zuwa masu kade-kaden sun bace Ganin jam'a sun fara kama gabansu ,anas baice dani uffan ba ,yawuce gaba ina biye dashi a baya ,muka rinka shiga cikin unguwar ,har sai da muka je wani gida ginin gargajiya,sannan muka tsaya . Bamu dade da tsayawa ba wata budurwa, dauke da tulu tazo zata shiga gidan. Kallo daya nayi mata,naga kamannin mai zungureriyar keyar nan tattare da ita ,kana na fahimci nan ne gidansu. "Okun".tafadawa anas ,shima yafada mata wasu abubuwa da yaren ,ni dai kawai okun na rike ,wanda sai daga baya na fahimci(sannu da zuwa take nufi) ta kura min ido yayin da suke magana da anas,bayan ta shiga tafadawa masa wani cikin yaren,sai takara kura min ido,kana ta koma gida . Bata dade da komawa ba sai mai zungureriyar keyar yafito. Bakamar dazu ba ya sauya kayan jikinsa,ban kuma yi mamakin ganinsa a nan ba , don ya bace a gabana . Duk wanda ke zaune a kasar Hausa,yana da labarin layar zana. Mr:shuraih 99% "Anas! Yafada lokacin suka gaisa Kana nima yamiko hannu muka gaisa . Bayan ya kawo mana tabarma mun zauna ,yakuma kara kawo mana gasassun zabi biyu da kindirmo. "Dandash ! Wannan abokinane sunansa habib ,habib abokinane sunansa dandash, yayi matukar taimaka min lokacinda nake zaune a nan" anas yafada. "Dandash! Wannan tafiyar don kai mkayita kuma abin da ketafe damu shine: Nan anas ya labarta masa rikitaccen al'amarin daya faru gareni cikin nutsuwa. Dandash yayi shiru kamar mai yin tunani ,sannan yayi dan murmushi ,ya matso da bakinsa kusa da fuskata. "(Kemina farida tsuwna a ciga ganwa tsu wastu ma an)KAI MA ZAKA MUTU KUMA ACIGABA DA GANINKA A WATA DUNIYAR,KAMAR YADDA YAFARU AKAN FARIDA. (Sarih yan yin gaina).WANNAN YANA DAGA CIKIN SIRRINMU". ********** *********** ******** SIRRINSU shi ne abin da yau za'anuna maka" Anas yafada bayan dandash ya shiga gida . Har yanzu kwalkwalwata arude take , zanmutu kuma acigaba da ganina ? Shekaru uku da suka shude, farida ta mutu ta kuma dawo. Nima yanzu hakan na neman kasancewa a gareni. A daidai wannan lokaci dandash ya leko ,yayi mana umarnin mushiga daga cikin gidan. Har muka shiga muka zauna a wani kebabben muhalli a razane nake . Na mutu a kuma cigaba da ganina ? Bawai gani na da za arikayi bayan na mutune ke girgizani ba, irin mutuwar dazanyi din. "Habib ! Kafin na cika maka alkawarin dana yi maka,bari na fara nuna maka wasu kwararrun hujjoji, don zama matashiya ga yunkurin daidaita tunaninka dana ke shirin yi" Dandash yafada yayin daya kwanto wani guru dake daure akugunsa . Mr:Shuraih 99% "Rike wannan" yamiko min gurun. "Mene ne wannan " yabukata lokacin dana ke rike da gurun. "Guru ne"na amsa masa. "Yar dashi akasa" ya umarceni. Cikin halin kidimewa na tashi zan cika bujena da iska ,yayin dana iyar da gurun,ya rikide ya koma maciji yana tafiya a kasa. "Kada ka tsorata, kamashi!"Dandash yakara umartata . Ba don na amince anas bazai kawo ni inda za a cuceniba ,da ba zan kama ba. Ina kamawa atsorace sai ga gurun rike a hannuna ,ya karba ya kara daurawa a kugunsa. "Tabani"ya umarceni . "Wakake tabawa?" Yatambayeni lokacinda hannuna ketaba jikinsa. "Kainake tabawa "na amsa masa. Kamar walkiya sai nemarsa nayi na rasa. "Kana ganina ?"Muryarsa daga wani waje ta bayyana . "Bana ganinka " "Kalli saman bishiyar dake kusa da kai"muryarsa ta kara fitowa. Ina kallon saman bishiyar sai na ganshi zaune akan reshe. Kamar dai walkiya sai yakara bacewa ,ban ankaraba sai ji nayi yana girgizani, yayin dana tattara hankalina kan bishiyar. Yana zaune inda yake dazu. Agabanmu yahada kiraruwa ya kunna Wuta,ya dauki wani dan karamin sanda ya nannadeshi da tsumma ya jika shi kananzir. Yana sa shi a wutar takama jikin tsumman da ci. Mr Shuraih 99% "Cire rigarka"ya umarceni. Banyi musa ba na cire. "Kai sharifine"? Ya tambayeni. "Ni ba sharifi bane " Kafin narufe bakina yafara goggogamin wutar ajikina . Shakka babu al'amarin da mamaki,kiri-kiri ga wutar tana taba fatata,amma babu wani alaman tsafi ballantana na kone. Bayan yakashe wutar na mayar darigana sai ya zauna kusa dani. "Kodon gaba, idan kaga mutum ya kirawo dabbobi suna hira,ko kaga mutum ya shiga tulu, ko kaga mutum ya shiga ta bakin jaka ya fito ta farjinta,ko kaga mutum ya mayar da cikinsa gefensa ko kuma bayansa ko kaga mutum yadaki bishiya mai rai a gabanka ta bushe ,kokaga mutum yayiwa turmi ko dutse kaho,su kuma tsotso jini, kokaga mutum yana zuko ruwa daga hannunsa yana fesarwa,har ruwan ya taru dayawa,ka kuma rinka ganin kifaye suna ninkaya acikin ruwan. Ko kuma kaga mutum ya ajiye kwano babu komi aciki,take agabanka abinci yazo,ko anuna maka akwati babu komai aciki take agabanka tacika da kayayyaki iri daban daban, Ko kaga kan mutum sun zama barkatai , koirn wanda nayi maka yanzu a takaice muna kiransa sihirin damfara,akasar hausa kuwa rufa ido."Alokacin da mutumin da al'amuransa ya shafemu ke aiwatar da wani abu,ko yake fada ko kuma yake tunawa ,alokacin muke sani. Habib! Koda wasa kada kayi sha'awar wannan shirmee da mukeyi. Duk wanda keyin shirka ,kafadawa kowa baya cikin da kwancoyar hankali, Ba ya kuma samun sanyin zuciya. Zaka sameshi mara imani da tausayi ,haka kuma gasu da cutar rayuwar al'umma domin duk wani sihiri idan kaji yadda ake hada shi,ka san aiki ne na shaidanu . Kuma babu wani amfanarwa tattare da

Chapter 1 of 2