Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ban saniba?"

Sake bata fuska tayi ta zame daga rikon da yayi mata, fita tayi gaba daya daga cikin dakin tanufi falo tana tafiya tana kokarin zuge zip din rigarta, tana zama mami na shigowa,

Sannu da zuwa tayi mata ta karbi kayan dake hannunta, kinkimar kayan da mamin tazo dashi hafsat tayi takai cikin dakin mami tafito lokacin har yusleem yafito yana zaune kusa da mamin,

Ko kallonshi batayi ba tawuce tazauna, dan kallonta yayi ya rausayar dakai alamun ban hakuri, dauke kanta tayi taki kallonshi,

"Mami dan Allah kibawa yarinyar nan hakuri naga sai fushi take dani daga yimata wasa....." Tajiyo yusleem yana fadawa mami,

"Ahh fushi kuma?" Mami ta tambaya, juyawa tayi ga hafsa,

"Hafsa meya faru??"

Murmushi hafsa tayi cikeda jin kunya tace, "Allah mami ni babu komai ba fushi nakeba"

"Wallahi mami karya take yi fada mukayi saboda wai kawai nayi mata wasa nace zata rakani zance wurin budurwata..."

Jin abinda yace yasa mami yin murmushi tatashi ta wuce kitchen wurin kuku tabarsu afalon saboda ta fahimci maganarsu ce ba tataba,

Ganin mami tafita yasa yusleem kallonta yana gyarawa hularshi karinta,

"Wallahi Allah hafsa wasa nake yimiki, wallahi ni banida wata budurwa kin san dai bazan rantse miki akan karya ba.."

Jin abinda yace yasata sakin ranta kadan amma bawai dan ta huceba sai dai ko babu komai zuciyarta ta danyi sanyi domin ta tabbatar da gaskiyar abinda yafada tunda har ya rantse mata,

Tashi yayi yafita saboda jin batayi masa magana ba, tunda yatafi bata kara jin motsinshi ba har karfe 2 narana, suna zaune suna cin abinci taji yakira mami awaya,

"To shikenan bari mugama sai tazo, ehh tana nan zuwa" mami tafada sannan takatse wayar tajuya tana kallon hafsa,

"Yusleem ne wai idan kin gama kije ki karbo mana kayan tsarabarmu, kiji wani kinibibi tun dasafe bai bamu ba sai yanzu..."

Murmushi hafsa tayi saboda tagano wayonshi kawai son ganinta yake shine ya bullo tanan,

Saida mami tasake tuna mata bayan sun gama cin abincin sannan ta tashi tatafi, baya cikin falo dan haka tawuce ciki, akan gado ta hangoshi zaune yana daddanna wayarshi,

"Mami tace kana kirana, gani.."

"Zo..."

Karasawa tayi gaban gadon ta tsaya batare data kalleshiba tun bayan kallon farko da tayi masa saboda daga shi sai gajeren wando da farar vest iya shaddar da yasaka kawai yacire,

Hannunshi ya mika ya kamo nata ya fisgota da karfi, babu zato tajita tafada kanshi, matseta yayi yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi, sam baya gajiya da lalubarta dan haka nan take yafara,

Duk da tana dan fushi dashi amma hakan baisata juya masa baya ba,soyayya ya nuna mata sosai ita har mamakinshi ma tayi,

"Baby wallahi bana gajiya dake,kefa kina gajiya dani...?"

Shiru tayi masa ta dauke kanta cikeda kunya,

Hancinshi yagoga ajikin nata,

"Uhm...?"

Shirun tasake yimasa, hancinta yaja tareda lakuce mata shi yana murmushi,


"Bacci nake son ki dan tayani baby zuwa anjima sai kitafi wurin mamin ko?"

Bai jira amsarta ba ya rungumeta tsam tsam ajikinshi yana shafa sumar kanta wacce tasha gyaran saloon......



*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[1:54PM, 2/22/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*




*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_



*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_



_DEDICATED TO MISS XOXO_


*Fatan alkhairi gareki mamuh Gee,shafin yau sadaukarwa ne agareki....*



*50*



***Saida hafsat ta tabbatar da cewar yusleem yayi bacci sannan ta zare jikinta ta fice, cikin sa'a lokacin da tashiga falon babu kowa mami tana cikin dakinta tana hutawa, ita dinma nata dakin tawuce ta kwanta,

Bata samu zarafin tashiba sai misalin karfe 3 na yamma, wanka tashiga, bata wani jima sosai ba tafito daure da zani daurin kirji sam bata san yusleem yashigo ba sai ganinshi tayi tsaye gaban mudubi yana jingine,

Ji tayi kamar ta juya ta koma amma saita daure duk da tasan yau tsokanar da zata sha awurinshi mai yawace,

Kallo yabita dashi tun daga kan gashinta wanda ke jike jalaf da ruwa har izuwa dukkan jikinta,

"Su hafsat haka aka girma?" Taji yafada cikin sigar tsokana, rabuwa tayi dashi taje zata dauki mai, rike hannunta yayi bayan ta dauki man suka koma gefen gado,

"Wai wankan me kikayi?"

Shiru tayi masa ta lukuto man zata fara shafawa ya kwace daga hannunta ya lukuta zai shafa mata,

"Babyn mami kinaji ina tambayarki shine kikayi min shiru?"

Bata fuska tayi,

"To me kakeso ince maka?"

"Ai ke kikasan abinda zakice min nidai kawai tambayarki nayi nace wankan da kikayi na menene?"

Kunyace ta kamata amma tasan idan bata bashi amsa daidai da tambayarshi ba yau tsuyeta zaiyi yasata agaba yayita tsokanarta domin yusleem ya iya tsokana,

Daga kan wuyanta yafara shafa mata man zuwa kafadarta,

"Kodai bashida suna?" Yasake tambayarta cikin tsokana,

"Da akwai mana" tabashi amsa tana rike daurin zanin dake jikinta,

"To wanne irine?"

"Irin wanda kayi...."

Murmushi yayi ya matsa kusa da ita,

"Waya fada miki ni nayi wanka?"

"Allah kaima kayi, kalli fa kasake kaya da ai ba wadannan bane ajikinta..." Takarasa maganar tana nuna brown t shirt din dake jikinsa da bakin trouser,

Hannunta yarike,

"To tunda kince haka shikenan nayarda yanzu bari sai musake yin wani tare"

Girgiza masa kai tayi,

"Why?" Yace da ita yana matsa tafin hannunta, zare hannunta tayi ta lakuci man zata ci gaba da shafawa ya hanata,

"Bari mana inkarasa shafa miki..."

Lakutowa yakuma yi yana kallonta, "oya to kunce zanin"
Ki tayi ta girgiza kai, "ni basai ansa anan ba"

"Inji wa? So kike kiyi fururu..."

"Ehh"

"A'a to ni bana so"

Da wayo da wayo yasamu yayi kasa da zanin, kunyace ta lullubeta gaba daya saboda hakan bai taba faruwa ba sai yau, ita yau gaba daya takasa gane kan yusleem domin yahanata sakat,

Sam gaba daya ma shi yamanta da cewar wai mai yake shafa mata domin tuni yagama shagala da abinda yake yi,

Ganin lamarin yana neman yin nisa yasata kokarin dakatar dashi,

"Dan Allah yaya yusleem kabari"

Batare da ya iya bude idanuwanshi ba ya shafo fuskarta,

"Haba baby...."

"Nidai Allah kabari"

Shiru yayi mata,dakyar tasamu ta kwace jikinta daga gareshi,

Zanin taja ta daura tana zumburo baki, murmushi yayi ya kishingida agefen gadon yana fitar da numfashi ahankali,

"Yau sau uku kina bata min jikina"

Yi tayi kamar bataji abinda yace ba saboda nauyin da maganar tayi mata,

"Yanzu sai kinsa nasake alwala bayan nayi alwalata ta sallar la'asar"

Tashi yayi yafita bayan yaja hancinta, saida tasake komawa tayi alwala sannan tafito tazo takarasa shiryawa, riga da skirt na leshi ruwan kwai tasaka sannan tayi salla tafita bayan tagyara fuskarta,

Mami da yusleem tahango zaune, shi yana cin abinci yayinda ita kuma mamin ke karanta jarida wanda yazama dabi'arta domin kullum saita tura ansiyo mata,

Ruwan sanyi ta dauko acikin fridge ta zauna akan kujera, yusleem ta kalla wanda ya kafeta da ido yana kallonta yana cin abincin dake gabanshi,

"Su yaya yusleem jaraba, ashe kai dinma jarababbe ne ban saniba" tafada acikin ranta domin gani tayi yasake kayan dake jikinsa maimaikon bakin wando yanzu blue ne ajikinsa kuma ta tabbata wannan kallon da yadameta dashi kari yake nema,

Idanuwanshi ya lumshe mata sannan yabude su akanta, kawar da kanta tayi tamayar kan tv,

"Yawwa ni ina tsarabar tamune naji shiru ba ace gataba bayan kuma tunda rana naji ance aje akarbo" mami tafada tana murmushi,

Daga shi har ita sai lokacin ma suka tuna da maganar domin har sun manta ma da makasudin zuwanta dakin nashi saboda shagalinsu kawai suka sha,

"Mami zan baku dazunne ban ganiba amma bari ingama sai inje indubo"

"To adubo akawo mana" inji mami,

"Wallahi mami kinga wacce ta sa namanta wurinma da na ajiye" yayi maganar yana nunata da spoon din da yake cin abinci.

"A'a wallahi mami babu ruwana" tafada tana harararshi, murmushi mami tayi tace,

"Rabu dashi hafsa ai nasan ba dagaske yakeba.."

Ajiye filet din dayake cin abinci yayi yamike yafita babu jimawa sai gashi yadawo dauke da wasu yan madaidaitan gold case guda biyu wadanda basu da girma, mikawa mami yayi yazauna akusa da ita,

Karba tayi fuskarta dauke da murmushi tasoma dubawa, wasu hadaddun Indian gold ne kanana ba manya canba sai faman walwali suke suna daukar ido,

"Mami ga tsarabarku..."

"Ai kuwa gashi munsha tsaraba, kai da kaje neman lafiya shine harda su tsarabar daham?"

"Babu komai mami dama da niyyar siyo muku natafi shiyasa ma natafi da kudin.."

"Cancadi, Allah yakara lafiya yayi albarka, hafsa matso kigani"

Tashi hafsa tayi taje wurin mami nan ta mika mata sarkokin da earrings dinsu da dan karamin ring aciki, bin sarkokin da kallo hafsa tayi nan taga guda daya harda wani dan siririn rubutu anrubuta harafin H ajiki,daga gani itace tata,

"Wow...., yaya yusleem mun gode madalla Allah yakara lafiya da arziki mai amfani"

"Amin hafsa, idan kin gama murnar gani kitashi muje unguwar mudawo" yace da ita yana kashe mata ido,

Mikawa mami tata tayi ita kuma tanufi cikin daki da tata,

Tana tsaye gaban mirror tana kokarin saka sarkar sai gashi yashigo, hannu yasa yakarbe daga hannunta ya saka mata dan kunnen sannan ya sa mata sarkar a wuyanta, hannu yakai yashafi wuyan nata,

"Kinyi kyau sosai, sarkar ta amsheki"

Murmushi tayi har hakoranta suka bayyana,

"Nagode yaya yusleem"

"Shirya kizo muje mugaida su ummi mudawo"

Juyawa tayi ta kalleshi, "kace ai zamuje gidansu maman amir sannan idan mun fito ina son naje gidan kawata amina"

"A'a banda wadannan su kyaje su daga baya"

Rakwarkwabe fuska tayi, "dan Allah yayana..."

Murmushi yayi, "naki"

"Haba sweetheart"

Dariya yayi yajuya zai fita,

"Yau harda su canja min suna saboda za akware ni ko? To naki wayon"

Kafin tabashi amsa har yafice daga cikin dakin murmushi tayi ta gyara fuskarta tasaka hijabinta tafita bayan ta fesa turare,

Atsaye ta iskeshi afalo yana jingine ajikin bango yana yin game awayarshi,

Bedroom din mami ta leka tayi mata sallama ta fito, har lokacin yana tsaye kamar yadda tabarshi yana yin game din,

"Yaya yusleem muje to"

Shiru taji yayi dan haka ta leka screen din wayar nan taga game din angry birds yake yi,

Pause yasa ya kalleta, "muje,banso ne wannan game din na fadi"

"Kawo incigaba da yimaka"

Hanata yayi tarike hannunshi,har suka fita daga cikin falon bata iya karbar wayar daga hannunshi ba, saida suka shiga cikin mota sannan yabata,

Gidansu hafsat suka fara zuwa,ba karamin dadin ganinsu Ummi tajiba dan haka ta karbesu da murnarta, tunda hafsa taga yanayin gidan ta fahimci cewar canji yasamu ai kuwa tunaninta yabata gaskiya domin koda suka shiga cikin daki ummin ke fada mata cewar kayan mahaifinsu da customs suka rike ansakosu sun fito yanzu haka mahaifin nasu yana can wurin hada hadar kasuwancinsa, murnar awurin hafsat kamar zatayi me domin babban farin cikinta shine taga su Ummi cikin walwala,nan ta nunawa ummi itama sarkar gold din da yusleem ya siyo mata, ummi albarka tasa tareda yimusu fatan alkhairi,

Sun dan jima agidan Ummi sannan suka yimata sallama suka fito, gidan hayarsu nada suka hara,gidan nanan kamar yadda yake ada matan gidan gasu nan zazzaune suna hira kowacce tana girkinta nadare akofar dakinta, hafsat ce tashiga ita kadai, duk cikin matan gidan babu wanda yaganeta har saida tayi musu bayanin cewar sune masu waccan dakin dake rufe, da gudu Maman amir tafito tazo ta rungumeta suka shiga daki,

Daga gani babu tambaya Maman amir tasan hafsat hutu da jin dadi yasamu domin gaba daya ta sauya fatarta ta goge,

Fitowa tayi bayan sun gama gaisawa da Maman amir tafita wurin yusleem yashigo suka shiga dakinsu nada wanda suka zauna aciki, rungumeta tabaya yayi yana bin dakin da kallo yana tuno abubuwa da dama tsakaninshi da ita wadanda suka faru acikin dakin,

"Yaya yusleem ya zamuyi da wadannan kayanne?"

"Kibarwa kawarki su"

"Nima haka nace araina amma fa banda keken sakata domin tsakanina dashi amanace"

Murmushi yayi yasaketa yaje ya ciro mata shi daga cikin shirgi, sallama suka yiwa su Maman amir bayan sun fada mata cewar sun bar mata komai nasu dake cikin dakin,

Gidan amina kawarta yakaita acanma tayi sallar magrib domin lokacin salla yayi, daga nan kuma suka wuce gida, lokacin da sukaje gida sun tarar da mami suna zaune suna hira da khadija, yusleem ko shiga baiyiba yawuce part dinsu khalifa yayinda ita kuma hafsa takarasa wurin khadija,nan suka shantake sai wurin 8 sannan khadija tatafi gida.

Daren yau kam duk da hafsa bata son zuwa part dinsu khalifa saida yusleem yakaita, kallo ya kunna musu a laptop dinshi daga karshe anan tayi bacci dan haka acan suka kwana saida asuba sannan ta tuna a inda take, kokarin guduwa tayi domin komawa part din mami amma ya hanata saboda akwai bukatar da yake bukata.

Sai da karfe 8 sannan tasamu tagudu takoma part din mami danma tayi sa'a mamin bata fitoba, nan tasake kwanciya tasha baccinta saida 11 tayi sannan tatashi tayi wanka tashirya tana shirin fitowa gogan yashigo yasha wani farin lallausan yadi mai kyau,

Harde hannuwanshi yayi yana kallonta,

"Yaya yusleem ina kwana?"

"Kin tashi lafiya?"

"Lafiya lau"

Hannunta Yakama yana kallonta,karan hancinta yaja,

"Dama zuwa nayi infada miki wata muhimmiyar magana mai muhimmanci dan haka ina son ki nutsu ki saurareni kuma ki fahimceni...!"



*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[3:09PM, 2/23/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat_



*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*



_DEDICATED TO MISS XOXO_




*51*




***Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi,

"Ina sauraronka ya yusleem"

"Hakuri zan baki akan rashin baki hakkinki da banayi wannan yana faruwane bisa umarnin da likita yabani saboda har yanzu akwai sauran bacteria atare dani so idan nace zan baki hakkinki to zan iya cutar dake ta hanyar maidaki victim, shiyasa nake mai baki hakuri da kikara dan bani lokaci har zuwa time din da zan koma Cairo naga likita nasan insha Allah lokacin komai yazama normal ina dawowa abinda zan fara yi shine insauke hakkinki inbaki kayanki..."

Juya masa baya tayi cikeda kunya tana murmushi saboda ita dataji yace zasuyi magana a tunaninta wata muhimmiyar magana ce ashe wai wannan zai sanar da ita,

Rungumeta ta baya yayi hancinsa yana shakar daddadan kamshinta,

"Banji kince komai ba Nana hafsa"


Jin tayi shiru yace,

"Uhm?"

"To yaya yusleem me zance? Ni wallahi nazaci wata muhimmiyar magana zaka fada ashe wannan zakace.."

"Wannan ba muhimmiya bace? Wannan maganar ai ni aganina tafi kowacce magana da zan fada miki ayanzu"

"Ni bahaka bane gaskiya"

Murmushi yayi ya juyo da ita,

"Tsakaninki da Allah bakya son inbaki hakkinki?"

Zame jikinta tayi zata fita daga cikin dakin yasake rikota,

"Ai babu inda zakije sai kin amsa min tambayar da nayi miki"

"Kai yaya yusleem, nifa yunwa nakeji"

"Ehh zakice min ko a'a"

"To ehh"

"Ohh dagaske bakya so din kenan ko? Shikenan to bari Indaina wahalar da kaina na sai nasamu lafiya, basai nakoma Cairo dinba sai kawai inzauna muci gaba da zamanmu haka"

Dasauri ta dago ta kalleshi bayan ta zaro idanuwa,

"Haba ya yusleem, haka zaka yita zama da cuta ajikinka?"

Murmushi yayi yaja hancinta,

"Dama ashe karya kike ba gaskiya kika fada ba"

"Nifa ba wannan nake nufiba"

"Ai nariga da nagane wayonki"

"Allah ya yusleem ni bahaka nake nufi ba"

"To naji, ke bakya bukatata kenan?"

Kwacewa tayi daga jikinshi tajuya tana bubbuga kafa, "nidai Allah yaya yusleem kabari"

"Shikenan nabari amma gaskiya ni kullum acikin bukatarki nake"

Hannayenta tasa tarufe fuskarta taki juyowa,

"Tunda ni ba a bukatata bari natafi.."

Juyawa yayi zai fita tabi bayanshi,

Tea tahada masa sannan tazuba mishi sauran kayan soye soyen wanda aka tanada dan karin kumallo,

Har yagama karyawa mami bata fito ba, kallon hafsa yayi,

"Nabar hulata adakinki, jeki dauko min"

Tashi tayi tanufi cikin dakin taje ta dauko hular tadawo,

Hannu ya mika zai karba ta hanashi,

"Zan gwada sa makane ingani ko na iya"

"Tom gwada ingani..."

Wayarshi yazaro saboda jin yar tsuwwarta daga cikin aljihunsa, ganin alh musa mori ne yasashi saurin dagawa, saka masa hular tayi tazaro turaren data boyo tasoma fesa masa ajikinshi, hannunta yarike bayan tagama fesa masa turaren yajata kan cinyarshi, kokarin kissing dinta yake duk da bai gama yin wayar ba, kanta ta ajiye akan kafadarshi tana shafa kasumbarshi, hannun yarike yakai bakinshi,

Zumbur ta mike daga kan cinyarshi saboda jiyo maganar mami da tayi tana kokarin fitowa daga bedroom wanda da alama waya take yi,

Akan kujera tazauna itama mami tazo ta zauna har lokacin bata gama wayarba, saida yusleem yajira tagama sannan yagaidata yafita yana yiwa hafsa wani kallo, "adawo lafiya" tafada ahankali wanda shi kadaine yaji, binshi da kallo hafsa tayi har yafice daga cikin falon.

Acikin mota yazauna yana kallon fuskarshi tajikin mirror, hular da hafsa tasaka mishi yake kallo domin ba karamin kyau yayi ba, tada motar yayi fuskarshi kunshe da murmushi har yaje gidan alh musa,

Kamar jiya yauma hafsa yar gidan alh musa tana tsaye asaman upstairs awani dan corridor tana jiran ganin zuwan yusleem cikin sa'a kuwa saiga motarshi ta kunno kai, murmushi tayi lokacin da taga yafito daga cikin motar yana duba agogon dake daure a hannunshi,

"Fine boy" tafada ahankali tana kallonshi, bata iya dauke idonta daga kanshiba har saida taga kulewarshi sannan ta nufi hanyar saukowa.

Kamar jiya yauma yusleem afalon alh musa ya sameshi yazauna bayan sun gaisa, tashi alh musan yayi yashiga ciki yabar yusleem zaune afalon,

Hafsa ce tashigo dauke da wani kyakkyawan faranti sai fitinannen kamshine ke fita daga jikinta,

Doguwar riga tasa ja mai gajeren hannu tayafa dan karamin bakin mayafi akanta,

Agaban yusleem ta ajiye abincin,

"Ina kwana...?"

"Lafiya lau, yagida"

"Alhamdulillah,bismillah ga abinci"

"Alhamdulillah"

"Haba dai, dan Allah kaci ko babu yawa, please" ta karashe maganar kamar zatayi kuka,

"Ok to nagode"

Juyawa tayi tafita baiyi niyyar cin komai ba amma yahada coffee yasha yana gamawa alh musa na fitowa dan haka babu bata lokaci suka dunguma suka fita.


Karfe 8 nadare suka dawo domin daga yau sun gama zagayen da yakamata suyi saboda duk inda ya dace suje sunje kuma yusleem zai fara fita aiki nanda sati mai zuwa domin alh musa ya gabatar dashi,


Gaba daya hankalin yusleem yayi gida saboda yau wuni guda baiga hafsanshi ba dan haka suna dawowa yaso tafiya gida amma alh musa yahana yace sai sunyi dinner haka ya zauna ba don yasoba, hafsa ce takawo abincin yanzu blue din doguwar rigace ajikinta da dan mayafi, tuwon semo miyar ogu ta kawo musu,

Filet ta dauka ta zuzzuba musu sannan tafita, kadan yusleem yaci yayiwa alh musa sallama yafita,

Abin mamaki koda yaje motarshi saiyaga tayoyin gaba daya sun sace babu iska motar tayi kasa, tsayawa yayi yana duban motar cikeda mamaki,

"Ya yusleem lafiya kuwa?" Yajiyo zazzakar muryarta daga bayanshi,juyawa yayi ya kalleta,

"Lafiya lau, tayoyin motar ne suka sace..."

"Ayya to yanzu ya za ayi? Gashi dare yayi balle inkira maka bakanike dinmu.."

"Ah babu damuwa bari kawai zanje insamu keke napep so gobe sai nazo da bakanike"

"A'a kabari inyi dropping dinka mana ko kuma inbaka motata sai katafi da ita gobe ka Kawo min"

"Karki damu babu komai"

"A'a wallahi gaskiya bazaka hau keke napep ba da daren nan,ka karbi motata dan Allah katafi da ita, haba mana ya yusleem yaushe da ajinka da komai zaka wani tafi a keke napep..."

Tsayawa yayi yana kallonta yanda ta tubure sai yatafi da motarta, shi abinma dayafi bashi mamaki yanda akayi ta rike sunanshi tamau abakinta tamkar itace ta rada mushi ga wata shagwaba da take yimasa,

"Ya yusleem please say something.."

"Am ina ganin basai na karbi mot...

"Please ya yusleem don't say bazaka karbi motata ba, please ban son wani abu yafaru dakai"

Daga mata kai yayi alamun takawo key din, juyawa tayi zuwa cikin gida mintuna kadan sai gata tafito, yana tsaye yana bin tangamemen tsakar gidan da kallo wanda ya wadatu da shuke shuke da hasken fitilu kamar rana,

"Gashi" ta mika masa tareda dan rissinawa, karba yayi yana jiran ta nuna mishi motar,

"Ga motar can, the last one din"

Parking space din yaje wanda ke dankare da lafiyayyun motoci hadaddu, takarshen ya bude kamar yadda tafada, ash colour ce motar kirar Mercedes Benz mai bakaken glass,shiga yayi yabawa motar wuta ya fito, tana tsaye tana kallonshi har yazo saitinta, kasa yayi da tintac glass din yaleko,

"Nagode sai goben, thank you"

"Don't mention it, Allah yakaimu"

Sai da taga fitarshi daga cikin gidan sannan tanufi ciki cikeda murna domin dama tana neman hanyar da zata samu tayi magana dashi sai gashi tasamu cikin sauki....








*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[8:24PM, 2/25/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*




*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_



_DEDICATED TO MISS XOXO_


_Fatan alkhairi ga kawata Billy Galadanchi ina mutukar yinki..._




*52*



***K'arfe 8:30 yusleem yashiga cikin gidansu daidai lokacin da yashiga yahango hafsat itada khadija suna tsaye jikin motar khadijan suna hira,

Fitowa yayi hannunshi rikeda robar ruwa, jikinshi gaba daya ya kamu da daddadan kamshin dake cikin motar Hafsat domin wani irin fitinannen kamshi ne shi ba turaren wuta ba shi ba perfume spray ba,

Ganin yusleem yasa hafsa jin mamaki domin a iya saninta yanzu basuda mota irin wannan,

Wani kallo khadija tabishi dashi lokacin da yazo daidai kusa dasu, gaisheshi tayi ya amsa batare da yatsaya ba bare ya kalli inda take, dan jijjiga kai tayi tana mamakin takamarshi domin har yanzu wannan jijji da kan nashi yana nan bai sauka ba saima karuwa da yasake yi,

Sallama sukayi tatafi ita kuma hafsat tawuce ciki, a bakin kofa taganshi tsaye da alama ita yake jira, tana zuwa kusa dashi taji ya rungumeta, kissing dinta yafara yi,

"Ya yusleem daga dawowa?"

"Ehh mana barka da dawowa nake baki ko bakya so?"

Murmushi tayi tarufe fuskarta, hannunshi yasakala a kugunta yana fuskantarta,

"Yau wuni guda ban gankiba, ke amma babu ruwanki ko, ko ma damuwa bakiyi ba"

"To ai nasan duk acikin aikine, naganka ma da sabuwar mota tawaye?"

Shiru yayi yarasa amsar da zai bata domin yasan idan yafada mata gaskiyar abinda yafaru kila za a iya samun matsala,

"Uhm yaya yusleem?" Tafada tana wasa da clips din dake jikin rigarshi,

"Motar gidan alh musa ce na aro saboda ta mamin da naje da ita tayoyinta sun sace.."

Murmushi yaga tayi tareda jan dogon hancinshi abinda bata taba yiba,

"Ban yarda dakaiba" shine abinda tace tareda kokarin tafiya, sake kankameta yayi yana sinsina wuyanta,

"Duniya tazo karshe tunda gashi hafsa tafara karyata ni"

Dariya ce tazo mata saboda jin abinda yace

"Ni ban isa inkaryata yaya yusleem ba, yanzu ni duk bama wannan ba zo muje kayi wanka sai kafito kaci abinci"

Jin abinda tace yasashi dan murmusawa,

"Yawwa Nana hafsa na, zo muje tare to"

Tana makale ajikinshi suka nufi part din su Abdul, suna zuwa balcony yayi sama da ita yabude part din suka shiga, har cikin bedroom yaje da ita ahaka, asaman gado ya ajiyeta tareda binta,

"Gaskiya wata yarinya tafara nauyi, mami tana bata abinci tana koshi"

Murmushi tayi tashafo kanshi wanda ke kwance bisa kirjinta,

"Kuma kaga ko rabinka banyi ba fa"

"Ahh karya kike da ace akwai scale da angwada"

"To agwada"

"To agwada mana" yafada tareda dago kanshi yana kallon fuskarta,

"Tayaya?" Ta tambayeshi,

"Zamuje agwada kibari sai nasamu lokaci, yanzu tashi ki hada min ruwan wankan..."

Tayar da ita zaune yayi tashiga cikin bathroom shikuma yasoma cire agogon hannunshi, fitowa tayi tasameshi tsaye yana jiranta bayan tahada mishi ruwan,

"Sauranki cire wannan.." Yayi maganar yana nuna mata kayan jikinshi, kunya taji ta kamata domin bata taba cire mishi kayaba amma saita daure, clips din rigarshi tasoma cirewa nan taji ya matseta ajikinshi har suna jiyo bugun zuciyar junansu,

"Yaya yusleem easy mana.."

Sassauta rikon da yai mata yayi,cire mishi kayan tayi tabarshi da na ciki kadai.

Ahankali taji yafara zuge zip din dake jikin rigarta,saurin kallonshi tayi,

"Lafiya?"

Langabar da kanshi yayi,

"Tare zamuyi dan Allah karkice a'a"


Kasa tayi da kanta nan ya kinkimeta yayi cikin bathroom din da ita, duk jinta tayi atakure saboda sam bata shiryawa wankan ba shiyasa abin yazo mata kwatsam,

Dadewar da sukayi acikin bathroom din ba kadan bace daga karshe dai shine yarigata fitowa yazo yatsaya agaban mudubi yafara goge sumar kanshi da dan karamin towel,

Yana cikin shafa turare yahangota tana fitowa,sunkuyar da kanshi yayi yana murmushi yaci gaba da bulbulawa jikinshi turare domin shi arayuwarsa yana tsananin son kamshi ko nawane zai iya kashewa ya siyi turare komai tsadarshi,

Ji tayi gaba daya dakin ya kaure da kamshin turarukan da yake shafawa wanda yawancinsu oil ne masu karfi,

Ta gefenshi tabi ta dauki turaren zata shafa,

"To kinga ai na taimaka miki kinyi wanka yanzu kina zuwa sai dai kawai kisa kayan bacci ki kwanta"

Turo baki tayi tana harararshi, kunnenshi guda daya ya kama,

"Nadauki laifin, yi hakuri..."

Murmushi tayi batace komaiba har ta gama shiryawa tasa kayanta, koriyar t shirt yasa da boxer, ba karamin kyau taga yayiba wanda harta shagala tana kallonsa bata saniba, hure mata ido yayi da bakinshi,

"Ko wankan bai isheki ba akara wani?"

Makale kafada tayi,

"Kyau kamin"

"Kema haka"

"Nagode"

Murmushi yayi bai bata amsaba illa kama hannunta da

2 Comments On ALWASHI
avatar
aliyu-1-5-2

1 year ago

Reply

I appreciate it

avatar
aliyu-1-5-2

1 year ago

Reply

I appreciate it

Please Login or Register in order to submit comment