Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
biyani albashi ba indai zan kasance a kusa da ita ina ganin wannan kyakkyawar surar tata zan iya cigaba dayi mata bauta har izuwa karshen rayuwata"Koda sarauniya Aryala taga jarumi damzur ya sunkuyar da kansa kas ya kasa cigaba da kallonta sai ta taso daga kan kujerar da take zaune ta tako har inda yake tsaye ta kama hannunsa.Take yaji gaba dayan tsigar jikinsa ta tashi,amma sai yayi ta maza ya kame.Sarauniya Aryala taja jarumi Damzur izuwa kan wannan kujera da take zaune ta zaunar dashi kuma tasa aka zuba ruwan inibi a cikin kofunan zinare guda biyu masu daraja aka kawo musu.Kawai sai ta dauki kofi daya ta mikawa jarumi Damzur itama ta dauki daya kofin ta kurbi ruwan inibin sau daya sannan ta umarceshi da shima yasha.Ba tare da fargabar komai ba kuwa jarumi Damzur ya kurbi ruwan inibin har sau biyu.Sarauniya Aryala ta dubeshi cikin murmushi tace,yakai Babban jarumi abin dogaro na kuma abin alfahari na kayi sani cewa daya yau na baka izini na bani shawara bisa duk abinda kake ganin zai amfaneni ko zai taimaki masarautata.Kan a da izinin kawo mini ziyara a kowanne lokaci walau safiya,dare ko rana.Maza ka sanar dani sabon al'amarin daya taso yanzu.Koda jarumi Damzur yaji wannan jawabi na sarauniya Aryala sai ya kara kamuwa da tsananin farinciki bisa amincin data bashi ba tare da fargaba ko shayin zai iya cutar da ita ba.Jarumi Damzur yayi gyaran murya ba tare daya dago kansa ba ya sake duban sarauniya Aryala ba sannan yace ya shugabata sarki uzaima ne ya canja tsarin walimar daya shirya tare da sarakai.Yanzu yace zaiyi walimar ne tare da sarakai da kuma jaruman gasa a daren yau.Yanzun nan wani manzonsa yazo ya isar da wannan sako a garemu.Koda jin wannan batu sai sarauniya Aryala ta kyalkyale da dariya tace,to saime kuma?ai babu wani abin damuwa ni hakan ma yafi mini dadi.Zanyi shiga ta mace jaruma,kuma zan halarci wannan walimar da matsayi biyu,ma'ana nice wakiliyar sarki sa'ad a matsayin 'yarsa,kuma nice jarumar gasa daga birnin nurul ansar,kuma kaine mai take mini baya a duk inda nasa kafata.Koda sarauniya Aryala tazo nan a jawabinta sai idanun jarumi Damzur suka zazzaro ya dubeta cikin alamun matukar tsoro yace,ya shugabat sarki uzaima ya sanni fa sosai,yana ganina zai shaidani.Sarauniya Aryala tayi murmushi tace,ai hakan nakeso ta kasance,idan yaga cewa jarumin daya kasa kaishi kas ne mai tsaron lafiya bazai yi mini kallon raini ba kuma bazai hanani shiga gasar jarumtaka dashi ba.Amma idan ya ganni ni kadai kyawuna ne zai ribaceshi kuma ya kamu da tsananin sona yadda bazai iya barina na shiga gasar jarumtakar ba.Koda jin wannan batu sai jarumi Damzur ya sake dago kai ya dubi sarauniya Aryala a karo na biyu cikin murmushi yace,ya shugabata na rantse da gemun ubana ban taba ganin mace mai basira da hangen nesa kamarki ba.Kina zartar da al'amuranki kamar wacce take samun wahayi daga ubangijinta.Sar auniya Aryala tayi murmushi tace,shin bakayi mamakin jarumtakata da kyawuna ba sai mamakin basirata.? Wannan shine abinda yasa na aminta dakai saboda kwakwalwarka tana da tunani mai kyau,kuma tana yanke hukunci mai kyau a lokacin daya dace.Na sallameka ka tafi izuwa dakinka domin ka huce gajiyar tafiya sai idan lokacin tafiya wajen walima yayi kazo mu tafi.Inason kafin kazo kayi gagarumar shiga ta yaki mai kwarjinin gaske saboda ana son idan mutum yana da kyau to ya kara da wanka.Koda jin haka sai jarumi Damzur yayi murmushi gami da godiya yace,an gama ya shugabata.Kawai sai ya mike tsaye ya fice daga cikin turakar .ΔKΔAΔEEΔRΔΔ ΔΔΔ Wani Babban daki mai fadi da tsawon gaske a cikin gidan sarautar wanda zai iya cin mutum dubu goma wanda aka kawatashi da kujeru da tebura na alfarma. Zan dakata anan: . By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO KASUWAR RAYUKA!!! Littafi na Biyu (2) Part B Wani babban daki mai fadi da tsawon gaske,a cikin gidan sarautar wanda zai iya cin mutum dubu goma wanda aka kawatashi da kujeru da tebura na alfarma,sannan an zuba fitulu masu hasken gaske birjik!Ba adadi kai kace rana ce alhalin dare yayi.Akan kowanne dogon tebur na dakin an zuba kayan ciye ciye da shaye shaye iri iri har da wanda ma mutum bai taba gani ba.Nama kuwa tsakanin kaji,zabi,agwagi,talo talo,rago,saniy a,rakumi da sauran tsuntsaye kala kala babu wanda babu a wajen.Wani naman gasasshe ne wani soyayya da kuma dafaffe wato farfesu.'Ya'yan itatuwa kuwa dangin su inibi,lemo,ayaba,tuffa,baure,f asa dabur babu irin nau'in da babu.Cikin kankanin lokaci wannan daki ya cika da sarakuna da jaruman gasa suka kama ciye ciye da shaye shaye.Acan gefe daya kuwa wadansu kyawawan 'yan mata ne su goma sha biyu a cikin shiga iri daya suna sanye da wata riga mai siffar tsuntsun dawisu suna ta faman tika rawa don debewa baki kewa,makada sunayi musu kida mai taushi a cikin bushin wata sarewa mai zakin gaske da taushi.Komai rashin son kidan mutum idan yaji wannan bai san sa'adda zai kama rausayawa ba.Sarki Uzaima ne ya fara halartar wannan dakin walima,kuma tunda ya shige yaje ya zauna a gaban wani katon tebur dake can sama bisa wani gini mai tudu dauke da mattakala inda duk wanda ya shigo cikin dakin shi zai fara hangowa.Duk sarkin daya shigo sai a kaishi can inda sarki Uzaima ke zaune su gaisa,dama akwai kujeru da zai zauna an tanada a kewayen inda sarki Uzaima yake.Tunda aka fara shigowa cikin dakin sarki Uzaima ya kasa ya tsare,ma'ana yasa idanunsa akan bakin kofar shigowa kawai jira yake yaga mace jaruma ta shigo yaga kalarta da siffarta,kuma sannan yasa ido yaga yadda sarki sa'ad na birnin nurul ansar zai shigo tunda bashi lafiya wata kila saidai a daukoshi akan karaga.Saida gaba dayan sarakai da jaruman gasa suka gama shigowa amma sarki sa'ad baiga shigowar sarki sa'ad da bakuwar jarumar da zata fafata gasar jarumtaka wacce tazo daga birnin sarki sa'ad din,wato birnin nurul ansar.Al'amarin dayai matukar bashi mamaki kenan ya fara tunanin ko ciwon sarki sa'ad ne ya tsananta shi yasa basu shigo ba.Har sarki Uzaima ya kirawo wani hadimi nasa zai turashi izuwa can masaukin sarki sa'ad domin ya gano halin da ake ciki,kawai sai jama'a sukaji an buga tambari na musamman irin wanda ba'a taba jin mai dadin sautinsa ba.Kwatsam!Sai ga Sarauniya Aryala ta shigo cikin dakin taron.A wannan lokaci sarauniya Aryala ta caba ado na gasken gaske.Tana sanye da wata koriyar riga doguwa wacce akayi ta da siffar fure.Rigar ta dame jikinta dukkan surorin jikinta sun bayyana a fili.Gashin kanta an tattareshi an daure a baya da wani abun ado mai siffar kwaron malam buda mana littafi,shima kalar kore ne.Kai!Hatta sarka,dan kunne da awarwaron dake hannunta na zinare koraye ne,haka ma takalmin dake kafarta duk koraye ne.Hakika shigar tayi mata tsananin kyau,kuma sai kyawunta da kyawun surar jikinta suka kara haskaka kyan nata.Jarumi Damzur na biye da ita a baya cikin gagarumar shigar kayan yaki,kuma shima garkuwarsa,kufen takobinsa da duk launin abinda ke jikinsa kore ne abin gwanin ban sha'awa.Da shigowar sarauniya Aryala da jarumi Damzur cikin wannan dakin walima sai gaba dayan jama'ar dake cikin dakin taron suka mike tsaye cikin kaduwa da tsananin mamaki,ciki kuwa har dashi kansa sarki Uzaima din.Sai gashi kowa ya kame kamar gunki ko gifta idanu babu mai yi sai kace gumaka ne,kuma dukkaninsu sarauniya Aryala suka kurawa idanu.Ba komai ne ya janyo hakan ba face ganin tsananin kyawunta da kuma ganin badakaren dake tsaron lafiyarta.Abinda ya kara daurewa sarakunan da jaruman gasar kai shine ganin yadda sarauniya Aryala tasa damara a kugunta gami da wadansu takubba da TAGWAYEN MASU guda biyu a kuibin cinyoyinta alamar cewa itama tana cikin JARUMAN GASA.Kallon farko da sarki Uzaima yayiwa sarauniya Aryala yaji nan take ya kamu da tsananin sonta da sha'awarta,kuma ya aiyana a zuciyarsa cewa ko sama da kasa zasu hade sai ya mallaki wannan kyakkyawar budurwar a matsayin matarsa ta aure.A wannan lokaci bokan sarki uzaima wanda ake kira ZARDASH IBINI ULAIMA na zaune a daf dashi akan wata kujera.Koda boka zardash yayi arba da sarauniya Aryala sai zuciyarsa ta buga da karfi a lokacin dayaga wani irin haske a goshinta.Nan take yai sauri ya dauko madubinsa na tsafi ya shafeshi take madubi ya disashe ya zama bakikkirin.Cikin tsananin firgici da matukar mamaki boka zardash ya yiwa sarki uzaima rada a kunne yace,ya shugabana wannan ce kadai macen da zata tara da ita ka sami haihuwa a duk duniya.Koda jin wannan batu sai sarki uzaima ya dimauce,bai san sa'adda ya yunkura cikin farin ciki da nufin yaje ya taryo sarauniya Aryala,amma sai bok zardash yai sauri ya riko hannunsa ya zaunar dashi akan karagarsa ya dubeshi yace,haba ya shugabana,kada ka janyi mana abin kunya mana.A matsayinka na shugaban sarakunan wannan nahiya bai kamata ka rude ba don kaga wannan kyakyawar sura.Koda jin wannan batu sai sarki uzaima ya dubi boka zardash cikin yake yace,ai kuwa bai kamata kaga laifina ba tunda wannan ce macen dana dade ina jira a tsawon shekaruna akan KARAGAR MULKI.Kuma babu wani 'da namiji dazai ga wannan kyakyawar sura ba tare daya kamu da tsananin sonta ba da sha'awarta a lokaci guda.Kafin boka zardash ya budi baki ya sake cewa wani abu tuni sarauniya Aryala har ta iso gabansu.Kawai sai jarumi Damzur da ita suka risina a gareshi sukayi gaisuwa sannan jarumi Damzur ya budi baki yace,yakai sarkin sarakuna ina mai farincikin gabatar ma ka da sabuwar sarauniyar birnin nurul ansar,wato Gimbiya Aryala Ibini Sarki sa'ad mai mulkin birnin nurul ansar a baya kafin yayi MUBAYA'A ya dorata a matsayin sabuwar sarauniyar dazata mulki birnin iya tsawon rayuwarta.Sannan kuma abu na biyu itace jarumar jarumai ta birnin nurul ansar wacce tazo birninka domin ta shiga GASAR GUMURZU dakai don jarraba sa'arta akanka.Koda jin wannan batu sai gaba dayan jama'ar dake cikin dakin walimar suka sake kamuwa da tsananin mamaki musamman ma sarakunan,domin babu wanda ya taba sanin cewa sarki sa'ad mai mulkin birnin nurul ansar yana da zukekiyar 'ya haka ba.Shi kuwa sarki Uzaima mamaki biyu ne ya turnukeshi.Mamakin farko shine,na ganin sarauniya Aryala ne bisa ganin tsananin kyawunta da kuma matsayin data samu na zama sabuwar sarauniyar birnin nurul ansar a cikin kankanin lokaci ba tare da labarin hakan yazo gareshi ba.Mamaki na biyu kuma shine ganin jarumi Damzur a tare da ita a matsayin mai kare lafiyarta.Take sarki Uzaima ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace,"ta yaya akayi sarauniya Aryala ta mayar da wannan tsohon dan fashi,kuma gawurtaccen jarumi mai tsaron lafiyarta alhalin ni kaina na kasa kaishi kasa kuma na kasa kamashi na daure?Nanfa sarki uzaima ya kasa baiwa kansa amsar wannan tambaya.To waishin ita sarauniya Aryala wacce irin hatsabibiyace mai tataka da har zata mallaki jarumi Damzur kuma har da zata shiga gasar gumurzun dani ba tare da shakkar komai ba a matsayinta na karamar yarinya kuma 'ya mace? Sarki Uzaima na cikin yin wannan tunani ne sarauniya Aryala ta matso daf dashi fuskarta a murtuke ta dubeshi tace ko bani da matsayin dazaka sa a bani wurin zama ne shi yasa ka barni a tsaye?Koda jin wannan tambaya sai sarki uzaima yayi murmushi tare da girgiza kai yace,kinda da babban matsayin daya wuce duk wani bako dake cikin wannan daki,don haka zo muje na baki wajen zama.Nan take ya shiga gaba yayi mata jagora da kansa har izuwa inda aka tanadarwa mahaifinta sarki sa'ad mai mulkin birnin nurul ansar.Dama an ware wata kasaitacciyar kujera dabam a gefe daya ita kadai.Koda jarumi Damzur yaga sarki uzaima na neman hada kafada da sarauniya Aryala sai yai sauri ya shiga tsakaninsu,har suka isa gaban kujerar,sarauniya Aryala ta zauna akai.Gaba dayan sarakai da jaruman dake cikin wannan dakin walima har izuwa wannan lokaci babu wanda yake cikin hayyacinsa sosai saboda tuni sarauniya Aryala ta birkita tunaninsu da nutsuwarsu kuma sun dimauce bisa ganin tsananin kyawunta.Saida sarauniya Aryala ta zauna akan kujerarta sannan sarki Uzaima ya juya ya koma izuwa inda kujerarsa take,amma yana waigenta har yana tuntube kamar zai fadi. ........... .... Al Mustapha isa nake Inkiya #MUSTINDOO KASUWAR RAYUKA!!! Littafi na Biyu (2) Part C Amma yana waigenta har yana tuntube kamar zai fadi.Ita kanta sarauniya Aryala bata san sa'adda dariya ta kwace mata ba,amma sai tayi sauri ta guntse bakinta da hannayenta biyu ta sunkui da kanta kasa.Kowa dake cikin wannnan dakin baiyi mamakin rudewar da sarki uzaima yayi ba bisa ganin tsananin kyawun sarauniya Aryala da kuma kyawun surarta,saboda da yawansu ma sun fara zubar da hawayen takaici saboda sunsan cewa wutsiyar rakumi ta yiwa yaro nisa.Kuma babu mai iya mallakar wannan sarauniya face mai tsananin sa'a da rabo bisa ganin yanayin shirinta da kuma jin izzarta tunda gashi shi kansa sarki uzaima magana take yi masa da kakkaifan harshe ba tare da shakkar komai ba,kuma ko kadan babu annuri akan fuskarta.Har sarki Uzaima ya dawo kan kujerarsa ya zauna bai daina waigen sarauniya Aryala ba,kuma ko kunya baiji ba ya rinka yawan kallonta kai da ka gani kasan cewa ya dimauce harma yana neman ya fita daga hayyacinsa.Haka dai aka cigaba da walima babu wanda keda sukuni a cikin dakin.Duk sa'adda sarauniya Aryala ta dago kai sai taga kowa ita yake kallo in badon ma akwai wadannan yan mata da suke ta faman tika rawa ba da bazata iya zama ba tunda ita kadaice 'ya mace.Shi kuwa sarki uzaima sai ya kasa zama dam akan kujerarsa yayi ta mutsu mutsu da waige waige kuma ya kasa cigaba da shan komai in banda waige waige babu abinda yakeyi.Take yaji cewa babu abinda yake so face ya mike tsaye yaje ya zauna a gaban sarauniya Aryala domin su tattauna maganganu masu muhimmanci.Maganar farko da yakeson ya gabatar a gareta itace batun ta bashi soyayyarta suyi aure.Magana ta biyu kuma itace yana son ta janye batun shiga wannan gasa ta jarumtaka dashi.Ba wani abu bane yasa sarki uzaima ya kasa mikewa yaje wajenta domin suyi wannan magana ba face sai duk sa'adda ya waigo suka hada ido sai yaga ta murtuke fuska tana harararsa ko kadan babu annuri a tare da ita.Al'amarin dayai matukar bashi mamaki kenan,kuma ya fusatashi yace a cikin ransa"Yaya ma ina sarki mai cikakken iko haka wanda ake tsoro a wannan nahiya gaba daya amma yau 'ya mace guda daya zata yimin kwarjini da har zan kasa aiwatar da abinda zuciyata ta raya min a kanta?Koda yake tunda boka zardash yace itace kadai macen dazan sami haihuwa da ita lallai zan lallabata har na samu nasarar siye zuciyarta,amma fa hakurina yana da iyaka,idan ta kaini makura zata aureni bisa dole ko don na sami magaji.Haka dai sarki Uzaima yayita zancen zuci har aka gama wannan Walima bai iya komawa inda sarauniya Aryala ke zaune ba bare ya gabatar mata da bukatunsa biyu,haka kuma bai dandana komai ba a bakinsa na abincin walimar.Itama sarauniya Aryala ko ruwa mukurwa daya bata sha ba a dakin walimar saboda tsorone ya kamata ta fara tunanin kada asa mata wani abu a cikin abinda zata ci ko wanda zatasha ya cutar da ita ko ya zamo sanadin da zata fita daga cikin hayyacinta har a sami damar yi mata wani abun.Sarauniya Aryala bata sami nutsuwa da kwanciyar hankali ba har saida ta taga an kammala walimar ta tafi izuwa masaukinta take ta kwanta akan gado.Kwanciyarta keda wuya sai taji zuciyarta ta buga da karfi,ba komai ne ya janyo hakan ba face tunowa da maganar mahaifinta sarki sa'ad lokacin da yake cewa da ita zata sami haihuwa amma bata hanyar aure ba.Kawai sai sarauniya Aryala taji hawaye ya zubo mata,take tace a cikin ranta"Ai kuwa dole ne na dauki matakin nisantar kowanne 'da namiji don ba zata taba yarda wani ya sanni 'ya mace ba muddin ina numfashi,kuma ina cikin hayyacina da lafiyata.Duk yadda zanyi na canja wannan kaddara dake kaina sainayi bazan bari wani 'da namiji ya sanni ba face ya zama mijina na aure"Koda gama aiyana hakan sai sarauniya Aryala ta mike tsaye zumbur ta fito daga cikin kuryar dakin da take kwance ta iske kuyanginta zaune a falo suna hira.Kawai sai ta dubesu tace,aje a gayawa jarumi Damzru da Barde Husam su kara matakan tsaro a kewayen wannan masauki nata ko tsuntsu kada a bari ya kusanceshi.Nan take daya daga cikin kuyangin taje ta sanar dasu jarumi Damzur wannan sako.Koda jin hakan sai jarumi Damzur da Husam suka dubi junansu cikin alamun tsananin mamaki domin basu ga wani tsaro da zasu kara ba tunda gaba dayan dakin kewaye yake da dakaru gabas da yamma kudu da arewa,duk abinda yazo ko ta sama ne zai gita sai an ganshi an harboshi da kibiya.Lokacin da sarauniya Aryala ta koma cikin kuryar dakin nata saita dauko tagwayen masunta ta kwanta akan gado rike dasu bayan ta tabbatar da cewar ta kulle kofar dakin da dukkan tagoginsa.Tana rike da masunta tacigaba da sake saken zuciya har barci ua saceta bata sani ba. ΔΔΔ ΔΔΔ ΔΔΔ AL'AMARIN Sarki Uzaima kuwa lokacin da aka kammala walima ya isa turakarsa ya kwanta domin yayi barci sai idanunsa suka bushe,ya zamana cewa da zarar ya rufe idanun nasa babu abinda yake gani sai kyakkyawar fuskar sarauniya Aryala.Koda ya shafe sama da sa'a uku a cikin wannan hali sai ransa ya baci,kawai sai ya mike tsaye zumbur ya sauya tufafin jikinsa ya kure adaka sannan ya dauko turare mafi kamshi ya shafe jikinsa ya fice daga cikin turakarsa.Yana fitowa sai dakarun dake tsaron lafiyarsa suka take masa baya ya tunkari hanyar zata kaishi masaukin sarauniya Aryala.Gaba daya hadimin gidan sarautar saida suka cika da dumbin mamaki saboda tsawon shekaru ashirin da hawansa karagar mulki ba'a taba ganin yaci ado ba haka kuma bai taba fitowa daga cikin turakarsa ba a tsakiyar dare irin haka sai yau.Kai tsaye sarki uzaima yaciga da tunkarar masaukin sarauniya Aryala har ya iso kofar gidan da take.Da iso warsa dakarunsa na take masa baya suka iske jarumi Damzur da Barde Husam tsaye a kofar gidan sun rike kugu,sauran dakarunsu kuwa sun kewaye gidan gaba daya wasun su ma akan katangar gidan suke a zaune.Koda ganin sarki uzaima a wannan lokaci sai mamaki ya kama su jarumi Damzur.Cikin hanzari barde Husam ya tari su sarki Uzaima ya risina a gareshi ya kwashi gaisuwa yace,ya shugabana lafiya kazo garemu a cikin wannan dare haka?Koda jin wannan tambaya sai sarki uzaima yayi murmushi sannan yace aje a gayawa sarauniyarku cewa lallai inason na gana da ita a yanzu domin ina da wata muhimmiyar magana da nakeson mu tattauna da ita.Dajin haka sai barde Husam ya sake risina yace,zamuyi kamar yadda ka bukata ya shugabana.Nan take barde Husam ya juya ya shige cikin gidan.Jim kadai sai ga Husam ya dawo da saurinsa.Da zuwansa ya dubi sarki Uzaima yace,ya shugabana ai sarauniyarmu tayi barci,kuma ta baiwa kuyanginta sakon cewa ko waye yazo wajenta kada a tasheta daga barci,mu kanmu ta bamu umarnin cewa kada a bar wani abu ma ya kusanci wannan gida koda tsuntsu ne yazo giftawa ta sama to a gaggauta harboshi.Ya shugabana ina ganin cewa zaifi kya ka hakura ka tafi saida safe ka sami damar ganawa da ita.Koda jin wannan batu sai ran sarki Uzaima ya baci cikin alamun fishi ya dakawa barde Husam tsawa yace wacece sarauniyar taku har da zata kafa mini doka a cikin gidan sarautata wacce ban isa na karyata ba?Ina mai umartarka daka koma da gaggawa ka tashi sarauniyarku daga barci domin sarki sarakuna ne keson ya gana da ita yanzu,in ba haka ba kuwa yanzun nan takobina zata sama mini hanya izuwa cikin wannan gida da karfin tsiya.Koda jin wannan batu sai jarumi Damzur ya zare takobinsa yasha gaban sarki uzaima yace,idan har hakan zata faru to saidai bana raye.Cikin tsananin fishi sarki Uzaima ya zare takobin wani badakare dake gefensa ya yunkura da nufin ya afkawa Jarumi Damzur,kawai sai yaji an daka masa tsawa.Cikin mamaki da tsananin fishi sarki Uzaima ya juya domin yaga wanda yayi masa wannan tsawa,kawai sai yaga ashe.....ne. .... .... By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO KASUWAR RAYUKA!!! Littafi na Biyu (2) Part D Cikin mamaki da tsananin fishi sarki uzaima ya juya domin yaga wanda yayi masa wannan tsawa,kawai sai yaga ashe boka Zardash ne.Boka zardash ya karaso wajen sarki uzaima ya kama hannunsa ya jashi gefe daya sukayi kus kus.Bisa mamaki sai akaga sarki uzaima ya juya ya koma baya izuwa cikin gidan sarautar tasa.Ai kuwa sai dakarunsa suka bishi da sauri yana tafe yana huci da ciza lebe tamkar zakin daya ratso daji a fusace yana neman abinda zai ci a lokacin da yake cikin tsananin yunwa.Kashe gari da sassafe jama'a suka fara taruwa a filin gidan sarautar inda za'ayi gasar jarumtaka.Nan da nan filin gasar ya cika ya batse da mutane ya zamana cewa duk inda mutum ya hanga baya ganin komai face kawunan bil'adama fululul kai kace kwari ne ba mutane ba.Jaruman gasar kuwa su dariya biyu da casa'in da tara ne suka iya hallara a cikin filin gasar.Har tsawon ADMIN ROKED KEMAGANA wannan lokaci sarki uzaima da sarauniya Aryala basu iso filin gasar ba,su kadai ake jira su fito filin gasar a fara gabatar da GASAR JARUMTAKA! # ΔΔΔRΔΔΔOΔΔΔKΔΔΔEΔΔΔDΔΔΔ LOKACIN da Sarauniya Aryala ta gama shiri ta sanya sulke a jikinta kuma ta daura damararta ta zuba TAGWAYEN MASUNTA a jikinta sai ta fito daga cikin dakinta.Tana isowa ta iske su Jarumi Damzur a tsaitsaye cikin kaguwar jiranta.Sarauniya Aryala ta dubi Jarumi Damzur da Barde Humas cikin murmushi tace,na sani cewa mun makara,amma kada ku damu wannan itace IZZAH irin ta jarumin daya yarda da kansa.Yanzu ne zamu iya zuwa FILIN GASAR JARUMTAKA!Tana gama fadin hakan sai ta wuce gaba faga cikin falon.Cikin sauri su Jarumi Damzur suka bita a baya suka nufi hanyar da zata kaisu filin gasar.Sarauniya Aryala suka iso filin gasar,jama'a na hangota aka rude da shewa tamkar dama can an saba ganin jarumtakarta.Na nfa makada da mawaka suka shiga yimata kirari suna kodata.A wannnan rana matan da sukazo kallon wannan gasa sun ninka maza yawa sau hudu,saboda tuni labarin sarauniya Aryala ya baza ko ina a cikin birni da kauyukan kasar harma da kasashen dake makoftaka da birnin kisra.Da yawan matan da sukazo sun zone kawai domin suga iyakar kyawun sarauniya Aryala da ake ta zuzutawa musamman ma maza da suke yabonta da kurantata koda a gaban matansu ne.Wasu kuma daga cikin matan da sukazo sunzo ne kawai saboda dasu kara mata kwarin guiwa a matsayinta na 'yar uwarsu mace,kuma 'ya mace ta farko a nahiyar da zatayi gasar gumurzu da sarki Uzaima.Lokacin da su sarauniya Aryala suka shigo filin gasar,ta hanga inda kujerar sarki uzaima take,taga baya nan sai ranta ya sosu,domin ba haka taso ba.So tayi ace ya rigata zuwa filin gasar,ya zamana cewa ya zauna ya jira isowarta.Haka dai sarauniya Aryala taje inda jaruman gasar suke ta tsaya,amma sai aka dakatar da dukkanin dakarunta daga waje,Jarumi Damzur kadai aka bari yayi mata rakiya.Saida sarauniya Aryala da jaruman gasa suka shafe kusan rabin sa'a a tsaye suna jira sannan akaji an buga tambarin sarki.Kafin ma aga sarki filin ya rude da shewa gami da tafi da kuma bugun ganguna,kirari da jinjina ninkin wanda aka yiwa sarauniya Aryala sau uku.Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da sukacewa,KOWA A GIDANSA SARKI NE!A wannan lokaci sarauniya Aryala ta fahimci cewa mutanen birnin kisra suna matukar son sarkinsu,domin mazansu da matansu jinjina suka kama yiwa sarki uzaima suna ihun farincikin ganinsa.Kai tsaye sarki Uzaima ya shigo filin gasar fuskarsa cike da annuri yana tafiya cikin izza ta kaisata har ya iso cikin tsakiyar filin gasar.Kawai sai ya tsaya a gaban jaruman gasar ya fuskancesu a lokacin da yake kokarin kirgasu.Koda ya hada idanu da sarauniya Aryala sai yayi mata murmushi,ita kuwa saita murtuke fuskarta tamkar taga babban makiyinta a duniya.Al'amarin dayai matukar bashi mamaki kenan kuma ya sosa masa rai.Lokacin da sarki Uzaima ya gama kirga jaruma gasar yaga su dari uku ne cif har dashi kansa,kuma ya kare musu kallo ya tabbatar da cewa zakwakurai ne wadanda dole ne ayi fama dasu sai ya dubi alkalin gasar yace,inaso a raba jaruma gasar nan gida uku domin abin kunya ne a gareni nayi yaki dasu daya bayan daya.Inason nayi yaki da mutane dari dari sau uku ADMIN KABEER ROKED KEMAGANA alokaci guda,amma banda jaruma mace,ita a wareta sai a karshe zan fafata da ita.Koda jin wannan batu sai filin gasar ya sake rudewa da shewa aka cigaba da yiwa sarki uzaima kirari da jinjina.Itama sarauniya Aryala farin cikin ne ya kamata da taji cewar ita dashi ne kadai zasu fafata,amma fa data dubi sarki uzaima da kyau taga ashe yafi jarumi Damzur cika da haiba da kuma kira ta sadaukantaka,take ta aiyana a ranta cewa,inda ace sarki uzaima da jarumi Damzur sun taba shafe sa'o'i masu yawa sun fafatawa da dole ne sarki Uzaima yayi nasarar akan jarumi Damzur saboda da ganinsa zai zama mai tsananin juriya da dauriya.Ba tare da bata wani lokaci ba aka raba dakarun gasa izuwa kaso uku,wato dari dari guda biyu,sai kuma mutum casa'in da tara,cikon darin ce sarauniya Aryala aka wareta a gefe daya.Ba tare da bata wani lokaci ba aka buga tambarin fara gasa take jaruman gasa kashi na farko su dari suka zare takubbansu suka fuskanci sarki uzaima.Kafin suyi wani yunkuri tuni sarki uzaima ya zare zabgegiyar takobinsa ya kwarara karkarfan ihu mai matukar firgitarwa,sann an ya ruga da gudu izuwa kansu.Da karfin tsiya ya kutsa ta tsakiyarsu yana kai musu mugun SARA DA SUKA suma suna kai masa .. By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO #PRABHAS KASUWAR RAYUKA Littafi na 2 Part E .******** posting By AL MUSTAPHA Isah .MUKAFTA@@@@@ ££££££ Da karfin tsiya ya kutsa ta tsakiyarsu yana mai kai musu mugun SARA DA SUKA suma suna kai masa.Amma kafin yakai karshen su saida ya sami nasarar yankar kowannensu,suka rinka zubewa kasa suna ihu a lokacin da jininsu ke tsartuwa daga jikinsu,amma suko lakutar jikinsa ba sami wanda yayi ba.Koda ganin wannan gagarumar jarumtaka da sarki Uzaima yayi sai filin gasar ya sake rudewa da shewa a karo na uku, ADMIN Al Mustapha KEMAGANA shewar ta cika birnin gaba daya da amsa kuwwa har izuwa cikin daji.Faruwar hakan ce tasa ragowar kasa biyu na jaruman su dari da casa'in da tara suka firgice ainun,kawai sai suka zubar da makamansu suka fice daga cikin filin gasar,alamar cewar sun jante daga gasar bazasu iya ba.Ai kuwa sai filin gasar ya sake rudewa da shewa fiye da karon farko dana biyu.Filin gasar ya rage saura sarauniya Aryala da sarki Uzaima kacal a tsaye.Kawai sai filin yayi tsit!Tamkar mutuwa ta gifta a lokacin da sarki Uzaima da sarauniya Aryala suka fara kallon kallo.Sai a yanzu ne sarki Uzaima ya lura da yanayin siffar baragen jikin sarauniya Aryala,ya gane cewa lallai akwai jinin sadaukantaka a tare da ita,kuma yana kallon cikin kwayar idon nata ya gane cewa zuciyarta a kekashe take babu alamar tsoro.Nan take ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace,"Yaya ni da MANYAN MAZAJE kuma GWARZAYEN SADAUKAI ke shakkar yin GABA DA GABA dani,amma yau gashi wai 'ya mace 'yar shekara goma sha ce ta tsaya a gabana zata yakeni ba tare da wata alama ta fargaba ko tsoro ba.Tabbas na gamsu cewa wannan ce macen dazan iya haihuwa da ita.Bari na fara jarraba iyakar jarumtakarta na gani.Gama aiyana hakan keda wuya sai sarki uzaima ya daga takobinsa sama ya yafito sarauniya Aryala da hannu yana maiyi mata nuni yana mai yi mata kira irin na raini.Maimakon sarauniya Aryala ta ruga izuwa gareshi kawai sai akaga ta dako tsalle a sama daga inda take tsaye tamkar daga cikin baka aka harbota.A saman ta zare takobinta ta kawo masa wawan sara da nufin ta tsarge kansa gida biyu.Cikin tsananin zafin nama sarki uzaima ya daga takobinsa sama ya kare saran,amma saboda nauyin saran nata saida ya dan durkusa kasa bisa guiwarsa guda sannan ya mike tsaye zumbur suka kacame da masifaffen azababben yaki mai tsananin muni da tayar da hankali.Ya zamana cewa suna kaiwa junansu SARA DA SUKA cikin mugun bakin zafin nama,juriya,jarumtaka da bajinta ta ban al'ajabi irin wanda idanuwa basu taba gani ko kunnuwa suji labari.Nanfa jama'ar dake wajen suka rude da ihu da shewa gamo da tafi,kowa yana mai tsananin mamaki bisa ganin irin jarumtakar da sarauniya Aryala keyi.A wannan lokaci ne sarki Uzaima ya gane cewa lallai sarauniya Aryala ba kanwar-lasa bace,kuma jarumtakarta ta musamman ce wacce ta wuce yadda yake zato ko tsammani.Nan take zuciyarsa ta fara aiyana masa cewa lallai babu yadda za'ayi ace akwai wata 'ya mace BASADAUKIYA mai tsantsar jarumtaka da bajinta gami da bakin zafin nama irin sarauniya Aryala,saidai idan wani sihirin tsafi gareta mai karfin gaske,domin al'amarin nata ya zama tamkar almara a gareshi. TSAKANIN SARKI UZAIMA DA SARAUNIYA ARYALA WAYE ZAI SAMI NASARA A WANNAN AZABABBEN YAKI NA GASAR JARUMTAKA DA SUKE FAFATAWA? YAUSHE SARAUNIYA ARYALA ZATA HAIFI YARON DAZA'A SAMESHI BATA HANYAR AURE BA KUMA WAYE MAHAIFINSA? IDAN YARON YAZO DUNIYA WACCE IRIN DAUKAKA ZAI SAMU KAMAR YADDA KAKANSA,WATO SARKI SA'AD MAHAIFIN SARAUNIYA ARYALA NA BIRNIN NURUL ANSAR YA FADA? SHIN SARKI UZAIMA ZAI SAMU NASARAR CIKA BURINSA NA AUREN SARAUNIYA ARYALA HAR YA SAMU MAGAJI DA ITA KAMAR YADDA BOKANSA ZARDASH YA SANAR DASHI? YAUSHE SARAUNIYA ARYALA ZATA CIKA BURIKAN DAKE CIKIN ZUCIYARTA? Mu hadu a littafin KASUWAR RAYUKA (3) don jin cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari. Alhamdulillah!!! Godiya ga Allah madaukakin Sarki Daya bamu ikon kammala wannan littafi. Dama kamar yadda na fada muku 1&2 ne kadai ya fito 3 bai fito ba,gashi dai mun kammala 1&2,sai muyi jiran fitowar 3&4 da sauransu. AL MUSTAPHA Isah nee Inkiya #MUSTINDOO

Chapter 3 of 4