Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
domin idanunka suga arzikin dazan zo dashi gami da nasarar dana samo.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sarki sa'ad ya rungume sarauniya Aryala yana maiyi mata godiya gami dasa mata albarka.Kashe gari kuwa tun kafin alfijir ya keto aka gama shirin dakarun daza suyiwa sarauniya Aryala rakiya izuwa birnin kisra kuma aka shirya guzuri gami da bayi da kuyangi da zasu yi mata hidama.Kamar yadda sarki sa'ad ya fada haka aka shirya wato a cikin keken dokin masarautar sarauniya Aryala ta tafi birnin kisra don amsa gaiyatar sarki Uzaima.Nan fa suka kama tafiya suna masu ratsa dazuzzuka,birane da kauyuka da garuruwa har tsawon kwana goma sha daya ba tare dasun hadu da wani mugun abu ba.A ranar kwana na goma sha dayan ne da yammaci kafin rana ta fadi suka yada zango a wani daji a bakin wata fadama.Tun kafin a yada zango ne shugaban dakarun wani Barde da ake kira Husam ya dubi sarauniya Aryala yace,ya shugabata wannan daji da muka yada zango a cikinsa daji ne mai hadari ana yawan yin fashi a cikinsa kuma yan fashin dake cikinsa suna da yawan gaske zasu iya ninka adadinmu sau goma.Koda jin wannan batu sai sarauniya Aryala tayi murmushi yace,yakai Husam ka kwantar da hankalinka kuma na umarceka kai da dakarunka duk kuje ku kwanta kuyi barcinku ni zanyi gadin kowa. ADMIN KE MAGANA Koda jin haka sai Husam ya zube kasa bisa guiwarsa guda daya kansa na sunkuye yace,ki gafarcemu ya shugabata ai bamu isa muje mu kwanta ba ke kiyi gadinmu muna matsayin bayinki.Cikin fishi sarauniya Aryala ta dakawa Husam tsawa tace idan ma bazaku iya barci ba to kawai ku zuba ido kuga yadda zanyi da duk masu tsautsayin da suka kawo mana hari.Wannan umarni ne na baku bawai rokonku nayi ba.Koda jin haka sai hankalin barde Husam ya dugunzuma ainun saboda shidai bai taba ganin sarauniya Aryala tyi yaki ba bare yasan irin jarumtakarta kuma yasan cewa idan lafiyarta ta tabu ko rayuwarta ta salwanta shida duk dakarunsa basu isa su koma gida ba,in kuwa suka koma sai sarki sa'ad yasa an kashesu idan baiga 'yarsa ba saidai idan sun iske baya raye.Cikin alamun tsananin damuwa da sanyi jiki barde Husam ya mike tsaye ya koma gefe daya.Sarauniya Aryala ta fito daga cikin keken dokin nata sannan ta dubi gabas da yamma kudu da arewa na dajin ta gama nazarinsa,sai ta dubi Barde Husam tace ka raba yaranka biyu kaso daya suje su saro itatiwa masu tsawo su katange sansani namu suyi mana kofa ta shiga da fita.Daya kason kuma suka kama aiki kafin cikar sa'a biyu da rabi sun kammala.Sarauniya Aryala ta sake duban barde Husam tace,yanzu kuma ina son kasa a kafa mutum mutumi na dakaru a cikin kowacce kusurwa na sansanin nan masu yawa kuma a kunna fitilun itace da yawa su haskake ko ina.Inason gaba dayanku ku fice daga cikin sansanin ku barni ni kadai a cikinsa.Koda jin haka sai idanun barde Husam suka zazzaro ya dubi gimbiya Aryala cikin kaduwa da firgici yace,haba ya shugabata ai wannan ganganci ne kuma sai da rai ne.Sarauniya Aryala ta sake dakawa Barde Husam tsawa tace,idan ka sake nuna mini karayarka ko ka sabawa umarnina zan sallameka ka koma gida. ADMIN DR KABEER LAWAL UMAR ROKED Cikin rawar murya Husam ya zube kasa yana mai cewa tuba nake ya shugabata.Nan da nan cikin hanzari aka aikata duk abinda sarauniya Aryala ta bayar da umarni ya zamana cewa gaba dayan dakarun da hadiman sarauniya Aryala suka fice daga cikin sansanin aka barta ita kadai a cikin tantinta,su kuma su Husam sai suka je nesa kadan da sansanin suka kwanta a cikin wata duhuwa mai kwazazzabai wacce baza'a taba tunanin cewa mutum zai shiga wajen ba,suka zuba ido suna kallon can inda sansanin yake cikin tsananin tsoro da fargaba aka rasa mutum daya wanda zai iya runtsawa har yayi barci.Har dare ya fara rabawa shiru ba'a ji motsin komai ba,kuma ba'a ga komai ba.Ba tare da fargabar komai ba kuwa sarauniya Aryala ta shiga cikin tantinta ta kwanta ta kama barci abindata harda minshari tamkar tana cikin gidan sarautarta.Kwat sam! Ba zato ba tsammani sai su Barde Husam suka jiyo wani irin takun sawaye mai karfi mai ban tsoro wanda mutum bazai iya tantacewa kona mutane ne kona dabbabo kuma akwai alamun cewa sawayen suna guda ne.Cikin kankanin lokaci saiga wadansu dakarun sumame su dayawa ba adadi wasunsu akan dawakai suke wasu kuma akan giwaye suka dukkaninsu suna dauke mugayen makaman yaki.Tunda Barde Husam ke fita yaki gami da yawace ywacen da yayi a duniya bai taba ganin yan fashi masu kwarjini da kayan aiki kamar wadannan ba.Cikin tsananin tsoro Barde Husam da sauran dakarunsa suka sake kwanciya a cikin duhuwar da suka kwanta suna masu dade buya.Ta gabansu wannan runduna ta yan fashi suka wuce sukaje suka yiwa sansanin KAWANYA.Ko shugaban yan fashin yaga ashe dakarun mutum mutumi ne zagaye da sansanin sai ransa ya baci ya budi baki da nufin ya baiwa dakarun nasa umarnin su bazama neman inda su Husam suka buya kawai sai yaga sarauniya Aryala ta fito daga cikin tantinta,kawai sai ta gyara tsayuwarta tana mai rike da kugunta cikin gadara ta dubi shugaban yan fashin nan ta daka masa tsawa tace,kai kuma waye har dazaka zo ka katse mini barcina a cikin wannan dare da karar sawayen ababan hawanku?Ka debo gayyar wadansu banzayen dakaru naka matsoratan banza da basa iya kawo hari ido na ganin ido sai dare ya raba....Kafin sarauniya Aryala ta gama ruge bakinta tuni shugaban yan fashin ya fusata ainun ya tari numfashinta yana mai daka mata tsawa yace,ke kuma wace daga cikin masu fada aji a wannan zamani har da zaki dubemu kiyi mana rashin kunya.Waishin ma ke kike takama dashi har da zaki fito ke kadai ki fuskanci wannan runduna tamu.Sarauniya Aryala ta dubeshi cikin gadara tace,nice sarauniya Aryala ibini sa'ad dan hussein mai mulkin birnin Nurul Ansar kafin yayi mubaya'a ya nadani a matsayin sabuwar sarauniyar birnin nurul ansar.Ina gaggauta shawartakarka da kayi gaggawar janye wadanann kananun dakarun naka ku bace mini da gani in ba haka ba kuwa daga yau kun daina yin wannan mumunar sana'a taku ta fashi da zalunci.Koda sarauniya Aryala tazo nan a zancenta sai shugaban yan fashin ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yace,waishin ke yanzu a tunaninki da haukani kina ganin cewa dabarar da kikayi ta boye dakarunki a wani wurin zatasa ki kubuta daga sharrinmu?To idan baki sani ba ki sani cewa gaba daya dajin nan ma a kewaye yake da yarana babu ta inda zaku iya guduwa ku tsira,kuma koda tsohon mahaifinki da dukkan sauran dakarun birninku zasu kawo muku dauki bazasu iya tsira daga dandanon mutuwar da zamu shayar daku ba...Sarauniya Aryala ta katse shi ta hanyar daka masa tsawa tace,kai wulakantacce mahaifina da dakarun birninmu sunfi karfinku,nidin nan da kuke gani na isheku ba sai dakaruna sun taimaka mini ba,idan kuma kuna shakka to GA FILI GA MAI DOKI ku gwada ku gani sai ku tantance tsakanin AYA DA TSAKUWA.Koda Sarauniya Aryala tazo nan a zancenta sai ta zaro tagwayen masu daga gadon bayanta ta gyara tsayuwarta tana jiran taga ta inda za'a fara kawo mata hari.Koda ganin gaka sai shugaban yan fashin ya bushe da dariyar mugunta a karo na biyu sannan ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya yana mai kutsawa ta cikin tsakiyar dakarunsa tamkar tafiya zasuyi,amma saiyaja linzamin dokin nasa ya tsaya cak yace ina maharbana?Na umarceku dakuyi ta sakar mata ruwan kibiyoyi har sai jikinta ya cika da kibiyoyin da babu masakar tsinke.Koda jin wannan umarni sai maharban kibbau suka zaro kibiyoyinsu daga cikin kwanson kibiyoyin dake rataye a gadon bayansu suka dana akan zaren kwarin suka fara sakarwa sarauniya Ayala hari cikin sauri da zafin nama.Nanfa dubunnan kibiyoyi sukayi kan sarauniya Aryala a guje zasu cake a jikinta. Ganin ruwan kibiyoyin da aka harbo mata yasa na tsaya cak. na rasa abinyi naje na taimaka mata ne ko na tsaya naci gaba da daukar rahoto ..... By AL MUSTAPHA Isah KASUWAR RAYUKA!!! Littafi na Daya (1) Part E. Nan fa dubunnan kibiyoyi sukayi kan sarauniyar Aryala a guje zasu cake a jikinta.Cikin tsananin zafin nama sarauniya Aryala ta daka tsalle sama ta rinka kade kibiyoyin da masun hannunta kuma ta nufo inda shugaban yan fashin yake a sama.Nanfa su Barde Husam dake labe a cikin duhuwa suka hango duk abinda ke faruwa suka cika da tsantar mamakin sarauniya Aryala bisa ganin irin wannan gagarumar jarumtaka da bajinta da takeyi domin duk ruwan kibiyoyin da ake harba mata ko guda daya bata shiga jikinta ba.Kawai sai gani akayi sarauniya Aryala ta daki kirjin shugaban yan fashin da kafarta guda.Duk da cewa shugaban yan fashin ya kasance narkeken katon gaske sai gashi ya hantsilo kasa daga kan dokinsa. ADMIN #MUSTINDOO KE MAGANA Ita kuwa sarauniya Aryala maimakon ta duro kasa sai ta taka gadon bayan dokin shugaban yan fashin tayi sama,a saman kuma ta rinka kawai dakarunsa sara da suka ta rinka shawagi a kansu tamkar tsuntsuwa mai fuka fukai sai gashi tana ragargazarsu suna zubowa kasa daga kan dawakansu tamkar ana sassabe a gona.Cikin tsananin fishi shugaban yan fashin ma ya mike tsaye zumbur ya daka tsalle sama ya tareta suka ruguntsume da masifaffen yaki,sai gashi sarauniya Aryala tana yin yakin bangare biyu,ma'ana tana yakar dakarun kuma tana yakar shugabansu,kuma ko sau daya bata bari kafarta ta taba turba ba saidai kaga tana taka kan dakarunda gadon bayan dawakansu saboda tsananin zafin namanta da jarumtakarta.Babu abinda yafi daurewa su Barde Husam da sauran dakarunsa kai sama da yadda sarauniya Aryala ke sarrafa jikinta a sama tana wurkilashi tamkar ta kasance mazari abin burgawa da hannu ko filfiluwa abar wasan yara.Duk da cewa shima shugaban yan fashin ya kasance gawurtaccen jarumi mai tsananin karfin damtse,jarumtaka,naci da iya yaki,sai gashi ya kasa koda lakutar jikin sarauniya Aryala,itama kuma ta kasa cutar dashi,domin duk harin data kawo masa walau da makami ko da hannayenta koda kafarta yana iya karewa,saidai inda gizon ke sakar shine cigaba take da yiwa dakarunsa sarki ya hana dawa tsaiwa domin girbar kawunansu take kawai,saidai kaga jini na feshi da fallatsi ta cikin dungulmin wuya,gangar jiki na subutowa kasa daga kan doki.A cikin abinda bai wuce rabin sa'a ba sai gashi sarauniya Aryala ta kashe sama da dakaru dubu bakwai.Kaico!Wuya mai sa dole!Kuma Sa Gudu Maganin Ki Gudu!! Koda dakarun yan fashin nan sukaga irin mummunar barnar da sarauniya Aryala keyi musu ta zama tamkar GUGUWAR ANNOBA mai saukar da mutuwa a tsakiyarsu,ko kuma shaidaniya mai karar da dangi,sai suka firgita suka fara zubar da makamansu suna ranta ana kare!Koda ganin haka sai shugaban yan fashin ya fusata ainun,ya daka musu karkarfar tsawa yana mai umartarsu da lallai su daina guduwa su tsaya,amma ina kamar ma kara tunzurasu yakeyi domin maimakon su tsaya sai kara karfin gudun suke yi don tsira da rayukansu.Al'amarin daya kara fusata shugaban yan fashin kenan ainun,kawai sai ya daina yaki da sarauniya Aryala ya tayata ragargazar yaran nasa dake neman gudu.Koda sarauniya Aryala taga shugaban yan fashin ya kama sara da sukan yaransa sai ta sauko kasa ta dira bisa dokinta ta zuba masa idanu sai gashi dakarun nasa sun kara kaimin guduwa daga filin yakin kafin kace me duk sun arce babu dayansu a wajen face gawarwakin yan uwansu saishi shugaban nasu shi kadai a tsaye yana haki da huci tamkar mesa yana mai fuskanta sarauniya Aryala suna kallon juna.Abinda daya batawa shugaban yan fashin rai shine yau kusan shekaru ashirin da daya kenan yana jagorantar wannan runduna ta yanfashi a wannan daji bai taba ganin rashin sa'a ba irin ta wannan rana,domin komai yawan dakaru ko ayari na fatake sai sun tarwatsa su sun kwashe dukiyoyinsu amma sai gashi yarinya karama wacce batafi shekara goma sha ba ta ragargajesu ita kadai ta tarwatsasu.Al'amarin dayai matukar bashi mamaki kenan har ya fara tunanin cewa anya kuwa wannan jarumar budurwar mutum ce ba Aljana bace?Abu na farko dai gata da kuruciya amma sai masifaffiyar jarumtaka da bajinta da kuma tsantsar iya yaki.Kawai sai wata zuciyar tace dashi ai kuwa ko aljanar ce yau sai yaga abinda ya turewa buzu nadi,tunda shima ya yarda da kansa a fannin jarumtaka,bajinta da iya yaki da kuma karfin sihirin tsafi,duk da cewa a lokacin daya fara gumurzu da sarauniya Aryala akwai wani abu dayai matukar bashi mamaki.Ba wani abu bane ya bashi mamakin ba face sihirin tsafi baya tasiri akan sarauniya Aryala kumababu alamar cewa tana amfani da tsafi a cikin jarumtakarta.Bayan anyi kallon kallo na tsawon yan dakiku masu yawa tsakanin wannan shugaban yan fashi da sarauniya Aryala sai lokaci guda duk su biyun suka sake rugawa izuwa kan juna kamar hadin baki suna haduwa suka sake kacamewa da masifaffen azababben yaki mai tsananin ban tsoro tamkar zasu cinye junansu.Ita kanta sarauniya Aryala sai taji tana matukar mamakin jarumtakar data keyi a wannan rana a matsayin gumurzunta na farko da bil'adam,saboda ita dai bata saba yin gumurzu da mutane ba sai dabbobi,dodanni da aljanu a cikin daji tana tarwatsasu tamkar an baje kayan koli a kasuwa.Saida Sarauniya Aryala da shugaban yan fashin suka shafe dakika dari hudu da sittin da uku suna kaiwa junansu sara da suka gami da naushi da bugun juna cikin bakin zafin nama da gagarumar jarumtaka sannan sarauniya Aryala ta sami nasarar yi masa barin makauniya a fuska da kafarta ta dama a lokacin da tayi wata irin katantanwa a samansa cikin shammace.Saboda karfin dukan fuskar tasa datayi saida yai sama da baya shima yayi katantanwa sau bakwai a saman sannan ya fado kasa tim!.A lokacin da hakorinsa guda na sama yayi fitar burgu daga cikin bakinsa tare da wani gudan jini ....... ....... ........ Abun mamaki mace take suburbudar namji haka to ai shikenan mukafta Naku har Kullun AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO #PRABHAS saida safe KASUWAR RAYUKA!!! Littafi na Daya (1) Part F. A lokacin da hakorinsa guda na sama yayi fitar burgu daga cikin bakinsa tare da wani gudan jini.Saboda tsananin jigatar da yayi a lokacin dayaji kansa yai masa nauyi tamkar an dora masa dakon katon dutse sai ya kasa mikewa tsaye ya kife a kasa da rub da ciki.Kawai sai sarauniya Aryala ta dunkule hannayenta cikin hammatarta ta zuba masa idanu tana maiyin murmushin farinciki bisa ganin nasarar data samu.Cikin tsananin takaici da bakin ciki shugaban yan fashin ya yunkura ya mike tsaye ya kwarara uban ihu kamar zai sake rugawa gareta su cigaba da yakin,kawai sai ya durkusa kasa bisa guiwoyinsa a lokacin da hawaye ya zubo masa ya dubeta yace,yake wannan jaruma mai ban al'ajabi na rantse da darajar iyayena kece jaruma ta farko data taba kaini kasa a filin fama.Kisani cewa hatta sarki Uzaima na birnin kisra sau uku muna fafata kazamin gumurzu ni dashi a wannan daji har sama da tsawon sa'a uku amma bai taba kaini kas ba,nima kuma ban taba kaishi kas ba saidai a karshe mu hakura da yakar juna kowa ya kama gabansa,amma yau gashi ke kin kaini kas,har ma kin fitar da jini daga jikina kin janyo min asarar hakorina guda.Na rantse da darajar iyayena da kakannina tunda har kika karya lagona daga yau na zama bawanki,ina mai rokonki daki karbeni a matsayin shugaban dakarunki mai tsaron lafiyarki,domin daga yau na daina sata da fashi ke nan har abada.A daidai wannan lokaci ne Barde Husam da sauran dakarun sarauniya Aryala suka ruga daga inda suke boye a cikin duhuwa sukazo bayan sarauniya Aryala suka tsaitsaya.Barde Husam ya yiwa sarauniya Aryala rada a kunne yace,ya shugabata kada ki yarda da wannan tsohon azzalumin dan fashi wanda ya shafe kusan shekaru ashirin yana hana mutane sakat a wannan daji,in banda sarki Uzaima babu wani mahaluki daya taba ratsawa ta cikin wannan daji lafiya ba tare daya rasa dukiyarsa da lafiyarsa ba.Sa'adda sarauniya Aryala taji wannan batu na shugaban dakarunta wato Barde Husam sai tayi murmushi sannan ta dubeshi tace,kuskure ne a ki karbar tuban mai laifi,domin yin hakan zaisa a tunzura shi ya cigaba da aikata laifin daya saba yi.Tana gama fadin hakan sai ta dubi shugaban yan fashin tace,menene sunanka?Shugaban yan fashin yace sunana DAMZUR BIN AUKAS.Sarauniya Aryala tayi masa dan guntun murmushi sannan tace,na karbi bukatarka amma bisa sharadi guda. KABEER LAWAL UMAR ROKED Sharadin kuwa shine idan kaci amanata ko kuma ka cutar da mutum daya daga cikin jama'ata ba tare da izinina ba zan kasheka.Ka sani cewa ni mutum ce mai iya zuba idanu akan mutum kamar yadda uwa ke kula da jaririnta.Koda gama fadin hakan sai sarauniya Aryala ta dubi barde Husam tace a baiwa jarumi Damzur bin Aukas tufafi irin na dakarunmu ya sanya daga yau ya zama mai tsaron lafiyata.Cikin tsananin firgici barde Husam ya kwalalo idanu kuma ya wangame baki ya kasa cewa komai.Jikinsa na tsuma yaje ya dauko tufafi irin wanda ke sanye a jikinsa,wato dakarunsu ya kawowa jarumi Damzur,shi kuwa jarumi Damzur sai ya karbi tufafin yana mai tsananin murna.Nan take yasa hannu ya yage rigar jikinsa yayi jifa da ita ya sanya wannan tufafi da aka bashi yaje ya tsaya a bayan sarauniya Aryala yana muzurai da kalle kalle don tsaron lafiyarta,kai kace dama can shine mai tsaron lafiyarta ta.Sarauniya Aryala ta dubeshi cikin murmushi tace,tabbas aikin dana baka ya dace dakai.A cigaba da tafiya.Tana gama fadin hakan sai ta nufi keken dokinta ta shiga ta zauna.A guje Jarumi Damzur ya ruga ya kamo dokinsa ya hau yazo daf da keken dokin sarauniya Aryala ya tsaya a bangaren damanta.Shi kuwa barde Husam sai ya koma bangaren hagunta aka fara tafiya.Ana cikin tafiyar ne sarauniya Aryala ta leko da kanta ta cikin tagar keken dokin bangaren hagu ta dubi barde Husam tace,daga yau Damzur ne shugabanku gaba daya kuma shine zai rinka baku horo na yaki,don haka albashinsa ya ninka na kowa sau uku.Koda jarumi Damzur yaji wannan albishir a cikin kunnensa sai ya kurma ihun farinciki yayi godiya ga sarauniya Aryala kuma ya shiga yi mata kirari yana mai cewa:"Ga sarauniyar Duniya mai haska kowa!Kece mace mai kamar maza!Kece tauraruwar wannan zamani!Kece shugabar kyawawan wannan zamani!Kece jarumar jarumai!Ko dubu ta taru albarka!Kece shugabar attajiran duniya mai kyautar ban mamaki!Kece mai ladabtar da barawo yayi tuban dole...!!!Koda Jarumi Damzur yazo nan a kirarinsa sai dariya ta kwacewa kowa a cikin tawagar aka kama kyakyatawa. MAI ZAI FARU IDAN SU SARAUNUYA ARYALA SUKA KARASA BIRNIN KISRA DOMIN WAKILTAR MAHAIFINTA SARKI SA'AD WAJEN GAYYATAR DA SARKI UZAIMA YAYI MASA NA MURNAR CIKAR SHEKARUNSA ASHIRIN AKAN MULKI? WA ZAI LASHE GASAR JARUMTAKA DA SARKI YASA WADDA ZA'A GABATAR RANAR BIKIN MURNAR? SHIN SARAUNIYA ARYALA ZATA DAWO TA TARAR DA MAHAIFINTA SARKI SA'AD A RAYE? YAUSHE SARAUNIYA ARYALA ZATA SAMU CIKI BA TARE DA AURE BA HAR TA HAIFI DAN DAZAI SAMU DAUKAKA A DUNIYA.? Mu hadu A KASUWAR RAYUKA kashi na biyu(2) don jin cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari. ...... ..... Naku Har Kullun AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO #PRABHAS kuhuta lfy KASUWAR RAYUKA!!! Littafi na Biyu (2) Part A. LOKACIN da tawagar Sarauniya Aryala suka cigaba da tafiya suna ratsa dajijjika,kowannensu ka kalleshi zakaga alamun kwanciyar hankali da annashuwa gami da nutsuwa a tare dashi.Haka suka cigaba da tafiya cikin nutsuwa har aka shafe yan kwanaki aka iso birnin Kisra,ba'a sake haduwa da wani tsautsayi ko wani mugun abu ba.Duk da cewa birnin Nurul Ansar gari ne dan babba,kuma kwatacce,amma da shigowar sarauniya Aryala sai ta gane cewa ruwa ba sa'an kwando bane,saboda birnin kisra ya ninka birninsu na nurul ansar sau uku a girma,ginuwa a kawatuwa.Batun arziki kuwa da tarin al'umma sai taga kamar a dauko kwayar hatsi guda daya jal!A karata a kusa da buhun maiwa, DR ROKED KEMAGANA wato dai a takaice bambancin dake tsakaninsu a baiyane yake.Da shigowarsu cikin birnin Kisra suka gane cewa lallai akwai babban taro da akeyi a birnin,domin garin ya cika ya batse da al'umma ba masakar tsinke,duk inda mutum ya hanga baya ganin komai sai dandazon kawunan bil'adam rututu.Kai!Hatta hanyar wucewa ma da karfin tsiya dakaru ke buda jama'a sannan ake samu a wuce.Nanfa sarauniya Aryala ta rinka ganin tawaga tawaga ta sarakai suna ta biyo bayan tasu,wasu kuwa ma tuni suna gabansu.Da yake ita tana cikin keken doki ne,kuma dakarunta na dauke da tutar birnin nurul ansar sai aka zata cewa sarki sa'ad ne yazo da kansa duk da cewa ansan cewa yana kwance cikin halin rashin lafiya.Haka dai aka cigaba da tafiya aka ratsa ta tsakiyar kasuwar birnin kisra.Koda sarauniya Aryala taga yadda girman kasuwar yake cike da rumfuna ga yan kasuwa sun baje kayyakinsu tuli ba adadi,kuma ga fatake ana ta cinikayya sai taji batada wani buri a duniya wanda yafi ta habaka kasuwancin birninta yakai koda rabin na wannan birnin ne."Ta yaya zan iya cimma burina?Amsar data kasa baiwa kanta kenan.Nan dai gaba dayan tawagogin sarakunan suka iso kofar gidan sarautar birnin kisra.Koda sarauniya Aryala ta leko da fuskarta kadan ta dubi kofar gidan sarautar wacce ita kanta anyi tane da zallan karfen lu'u lu'u gata katuwa mai tsawo da fadi saita gyada kai cikin alamun takaici tace,ashe dai ni da a kauye nake ban sani ba?Ai kuwa idanunta na kaiwa kan ginin masarautar sai ta dimauce kuma ta cika da tsananin mamaki,saboda ganin irin aljannar duniyar da aka shirya.Tace a ranta,lallai ashe ma mu miskinai ne ba sarakai ba akan sarki Uzaima!Duk sarkin daya iso kofar gidan sarautar birnin kisra sai fadawan sarki uzaima su tareshi suyi masa barka da zuwa kuma sai ya fito daga cikin keken dokinsa ya gaisa da manyan fadawan sarki uzaima sannan a bashi takarda da alkalami ya rubuta sunansa,kuma ya buga hatiminsa,sannan ne za'ayi masa jagora izuwa masaukinsa dake cikin gidan sarautar.Haka aka cigaba da saukar sarakuna har akazo kan sarauniya Aryala amma ita da akazo kanta sai taki fitowa daga cikin keken dokin,dama tun kafin su iso ta baiwa jarumi Damzur umarnin ya wakilceta a komai.Shidai jarumi Damzur mutum ne mai matukar kwarjini da cika idanu,don haka mutane ma basa iya hada ido dashi sau biyu.Da isowar keken dokin sarauniya Aryala gaban kofar da fadawan sarki uzaima ke tsaitsaye sai jarumi Damzur yai sauri ya sauko daga kan dokinsa yazo gaban fadawan ya tsaya ya mika musu dannu don su gaisa.Cikin kaduwa da mamaki gaba dayan fadawan suka dan ja da baya kadan a tsorace,sannan daya daga cikinsu yayi karfin hali ya dubi jarumi Damzur yace,me yasa sarkin naka bai fito ba daga cikin keken dokinsa baya wakiltoka alhalin ba haka dukkan sauran sarakunan da suka fi sarkin naka daukaka da girman masarauta sukayi ba?Cikin daurewar fuskar da alamun fishi jarumi Damzur yace,waye a nahiyar nan baisan cewa sarki sa'ad na birnin nurul ansar yana cikin halon rashin lafiya ba?Ku bani takarda nasa hannu na buga hatiminsa,umarnin daya bani kenan,don haka bazai iya fitowa ba da kansa.Koda jin wannan batu sai bafaden da ke rike da takardar ya matso da sauri gaban jarumi Damzur jikinsa na tsuma ya bashi ya rubuta sunan sarki sa'ad kuma ya buga hatiminsa.Ba tare da bata wani lokaci ba aka basu dan jagora wanda zai kaisu izuwa masaukinsu aka bude musu kofa suka shige cikin gidan sarautar.Nanfa gaba dayan jama'ar dake cikin kofar gidan sarautar sukabi Jarumi Damzur da kallo saboda gaba dayan dakarun sarakunan da suka shigo birnin babu wani badakare mai girmansa,kwarjininsa da kirarsa ta jarumtaka.Da yawa daga cikin irin mutanen da suka taba ratsawa ta cikin dajin da yake fashi suka tsira da rayuwarsu sai suka kura masa idanu suna son su tuno a inda suka sanshi,amma sai suka kasa tunowa saboda tsananin kwarjininsa da tsoron hada idanu dashi.Bayan an gama saukar dukkanin sarakunan da suka shigo birnin kisra da kuma dukkanin jarumai da sadaukan da sukazo domin su shiga GASAR JARUMTAKA daza suyi da sarki Uzaima,an gama rubuta sunan kowa da hatiminsa da sunan kasarsa,sai aka kaiwa sarki Uzaima takardar ya fara dubawa.Takardun a ware suke,ta jarumai da sadaukai daban,ta attajirai ma daban,haka ta sarakuna,don haka ana kai masa wadannan takardu takardar sarakan ya fara dubawa,koda yayi kicibus da sunan sarki sa'ad na birnin nurul ansar sai ya cika da tsananin mamaki saboda yana da labarin halin da yake ciki na tsananin rashin lafiya wanda yakai matsayin saidai a kwantar dashi a tayar dashi baya iya yiwa kansa komai saidai ayi masa.Cikin mamaki sarki Uzaima ya dubi fadawansa yace,shin da gaske sarki sa'ad da kansa ya halarci wannan gaiyata wata? DOCTOR KABEER NE Wazirin sarki uzaima yayi gyaran murya yace,ya shugabana mu dai munga keken dokinsa amma wani babban badakarensa ne ya wakilceshi ya rubuta sunansa da suna Birninsa sannan ya buga hatiminsa,amma mu bamu ganshi da idanunmu ba tunda ance yana cikin keken doki a kwance bazai iya fitowa na yazo ya rubuta da kansa ba saboda halin rashin lafiyar da yake ciki.Sarki Uzaima yayi ajiyar numfashi cikin matukar mamaki sannan yace,ai mutumin da yake cikin halin rashin lafiyar da saidai a kwantar a tayar bai kamata ace ya halarci wannan taro ba.Koda gama fadin hakan sai sarki Uzaima ya ajiye takardar sunayen sarakunan ya karbi ta jarumai ya fara dubawa.Kwatsam!Yna cikin dubawa sai yayi kicibus da sunan JARUMA ARYALA daga birnin nurul ansar.Cikin tsananin mamaki sarki uzaima ya sake karantasunan domin a zatonsa ko idanunsa basu gane masa daidai ba.Abinda ya bashi mamaki kuma ya daure masa kai shine a cikin sunayen gaba dayan jaruman gasar kusan mutum dari uku da doriya sunan mace ko daya babu sai wannan jaruma mai suna Aryala ita kadai.Sannan kuma bai taba jin labarin cewa akwai wata jaruma mai wannan suna ba a cikin birnin nurul ansar.To wai shin ma yaushe ne wannan bakuwar jaruma ta wanzu har da zata shiga wannan gasa?Amsar da sarki Uzaima ya kasa baiwa kansa kenan.Nan fa ya fada kogon tunani.Nan take dabara ta fado masa kawai saiya dubi wazirinsa yace,na sauya tsarin walimar dana shirya ta gobe,a daren yau nakeson a gabatar da wannan walima ta murnar cikar shekarun haihuwata arba'in da kuma cikar shekaruna ashirin akan KARAGAR MULKI.Maimakon gayyatar sarakuna kadai izuwa dakin walima inason a shiga har da gaba dayan JARUMAN GASA,kuma inason a shiga dasu din ne bisa tsarin daya bayan daya domin na gamsu da idanuna kafin a fara walimar.Koda jin wannan batu sai waziri da sauran fadawan suka cika da mamaki babu mai ikon tankawa koyin tambaya da jayayya akan wannan umarni,kawai sai waziri ya sake risina yace,an gama ya shugabana.Nan take aka tashi manzanni suka tafi izuwa masaukin bakin suna isar da wannan sabon sakon gaiyatar walima na sarki uzaima a daren yau. ΔRΔOΔKΔEΔDΔ SARAUNIYA ARYALA tana zaune a can cikin turakar masaukin da aka bata tare da kuyanginta ta kishingida akan wata doguwar kujera ta alfarma anayi mata gyaran gashi saiga wata kuyangarta ta shigo da sauri.Da zuwanta gaban sarauniya Aryala sai ta zube kasa tace,ya shugabata jarumi Damzur ne ya iso kofar dakin nan yace a gaya miki cewa wani sabon al'amari ya taso daga sarki uzaima a yanzu yanzun nan.A wannan lokaci sarauniya Aryala tana sanye da wata riga ce mai shara shara wacce ta bayyana komai na surar jikinta don haka sai tasa aka miko mata mayafi ta daurashi kamar zani sannan ta dubi wannan kuyanga tace,jeki kice da Damzur ya shigo.Cikin mamaki gaba dayan kuyangin suka dubi Sarauniya Aryala suna masu zazzaro idanuwansu.Wacce ta kawo rahoton zuwan Damzur dama itace shugabarsu ana kiranta da suna HIMAILA.Kuyanga Himaila ta dubi sarauniya Aryala cikin alamun tsoro da fargaba tace,haba ya shugaba saboda me zaki aminta da jarumi Damzur haka har ki amince masa shigowa cikin turarki?Koda jin wannan tambaya sai sarauniya Aryala tayi murmushi tace,idan kana son ka sami damar sarrafa jarumi yadda kakeso kuma ka sami yardarsa dole ne ka fara bashi amincinka da yardarka.Ina bukatar amincin jarumi Damzur domin na cika wadansu burika na rayuwata duk da cewa ya zama bawa na.Bamu san abinda ke karkashin zuciyarsa ba,babu mamaki nan gaba ya bultuce mini ko yaci amanata,amma idan na jashi a jikina hakan zai iya karya zuciyarsa ua fasa aiwatar da mugun nufinsa a kaina idan ma shi yayi niyya a zuciyar tasa.Maza kije ki shigo dashi yanzun nan kamar yadda na umarceki.Kuyanga Himaila ta sake risina tace an gama.Ta juya ta fice daga cikin turakar,zuwa can sai gata ta dawo tare da jarumi Damzur yana biye da ita a baya.Koda Jarumi Damzur yayi arba da sarauniya Aryala yaga wani bangare na saman kirjinta,kuma yaga kyakkyawan gashin kanta mai tsananin haske,baki da kyalkali wanda aka tajeshi ya zuba izuwa kasan kwankwasonta sai ya dimauce jikinsa ya kama tsuma.Cikin sauri ya sunkui da kansa kasa a lokacin da zuciyarsa ta raya masa cewa"Aini ko sarauniya Aryala bazata

Chapter 2 of 4