Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KASUWAR RAYUKA Littafi Na Daya (1) PART {A} A WANI Zamani can baya mai tsawo da ya shude,lokacin da ake kan tsakiyar cinikin bayi,sa'adda sarakuna ke mulkin KAMA KARYA,MULKIN ZALUNCI,a zamanin da mutum bashi da wani yanci na kansa face ya kasance sarki ko mashahurin attajiri ko kuma gawurataccen Boka ko Jarumi.Indai mutum bai taka wannan matsayi ba'ana sarrafashi tamkar dabba ba dan adam ba.A wannan lokaci kaf duniya babu kasar da tafi BIRNIN KISRA Daukaka a harkar CINIKIN BAYI,domin basu da wata sana'a wacce tafita.Sarkin dake mulkin Birnin Kisra {DR ROKED} Awannan lokaci ya kasance gawurtaccen sadauki kuma gagarumin mayaki mai TARWATSA MAZA a FILI FAM,ana kiransa da suna SARKI UZAIMA IBINI SARZAF.Sarki Uzaima shine da kansa yake kwasar dakarunsa na yaki kamar mutum dubu uku su tafi FARAUTAR BAYI,kuma indai zai fita farautar bayi baya kai hari a yankin kasarsa ko kasashen dake makoftaka da kasarsa,yakan tafi wata nahiyar ne gaba daya kuma mafi akasarin tafiye tafiyen nasa yana yinsu ne akan TEKU.Duk sa'adda sarki Uzaima ya fita farautar bayi baya dawowa gida da kasa da bayi dubu goma,kuma shi baya kamo yara ko tsofaffi sai matasan SAMARI da 'YAN MATA masu jini a jika.Duk garin da yaje yakan sauka a bayan garin ne ya aikawa da sarkinsu wasika.A cikin wasikar sai ya bukaci a bashi bayi dubu goma cikin salama,idan kuwa aka ki sai ya fakawa garin da yaki ya kama duk wanda ya gadama a matsayin bawa koda kuwa sarkin garin ne da kansa.Kasuwar cinikin bayi ta birnin Kisra tana cine bayan duk karshen mako biyu.A duk wannan rana attajirai da sarakai suna zuwa birnin na kisra daga kowanne bangare na duniya domin siyen bayi saboda babu irin kalar bawan da mutum bazai samu ba.A wannan rana sarki Uzaima yana samun kazaman kudade masu dimbin yawan dashi kansa yana mamaki.Saida sarki Uzaima ya shekara ashirin akan KARAGAR MULKI yana wannan sana'a ta tara arziki wanda har takai cewa yama rasa abinda zaiyi da kudin.Sau bakwai yana sawa ana rushe fadarsa ana gina sabuwa,ya zamana cewa duk duniya babu wata fada data kai tasa kyawu da kawa.Sarki Uzaima ya tara gonaki,gidaje,dabbobi da rumfunoni a kasuwa ba adadi wanda shi kansa baisan iyakar adadinsu ba.Wani iko na Allah sarki Uzaima ya kasance mutum mai matukar koshin lafiya domin tunda ya hau karagar mulki bai taba yin cutar datasa ya kwanta ba koda tsawon yini daya saidai dan gajeren zazzabi ko ciwon kai.Sarki Uzaima yana da matar aure guda daya jal.Wata kyakkyawar mace mai suna Suhaira wacce tun yana da shekara ashirin da daya akayi musu auren saurayi da budurwa tun zamanin mahaifinsa.A yanzu Suhaira ta shekara goma sha hudu da auren sarki Uzaima amma ko bari bata taba yi ba.Sarki Uzaima yana da kwarkwarori guda ashirin da daya,kuyangi da bayi mata kuwa gasu nan birjik amma dayarsu bata taba samun ciki dashi ba.Duk wannan irin ni'ima da Allah ya baiwa Sarki Uzaima ta mulki,jarumta,d ukiya,daula,mata da ingantacciyar lafiya sai ta zama ta banza,domin duk sa'adda ya tuna cewa bashi da magaji sai ya shiga daki ya kulle kansa yayi ta kuka har sai ya gaji da kukan barci ya sace shi bai sani ba.Allah shine mai iko!Gashi dai duk wata daukaka ta duniya an baiwa sarki Uzaima amma sai aka hanashi haihuwa dimin a nuna masa cewa shima fa ba kowa bane face bawan Allah.Bokaye da likitoci barkatai sun tabbatarwa da sarki Uzaima cewa lafiyarsa kalai kuma zai iya haihuwa amma babu wanda yasan yaushe ne zai samu haihuwar,kuma babu wanda yasan macen da zata sami wannan sa'a ta haihu dashi.A tsawon shekaru ashirin da sarki Uzaima ya kwashe yana kai hare hare izuwa kasashen ketare bai taba zuwa garin daya kasa samo nasara ba,kuma bai taba yin gumurzu da wani jarumi ya sami nasarar koda lakutar jikinsa ba bare ace gashi anyi masa wani babban rauni saboda tsabar KARFINSA,JARUMTAKARSA DA SA'ARSA.A ranar da sarki Uzaima ya cika shekara arba'in cif a duniya ne ya zamana cewa ya sami shekaru ashirin akan karagar mulki,bisa wannan dalili yasa aka shirya gagarumar walima ta musamman,kuma ya gayyaci gaba dayan sarakunan dake nahiyarsa domin suzo su tayashi murnar cika shekarunsa na haihuwa arba'in da kuma cikar shekara ashirin akan KARAGAR MULKI.Baya ga wannan Walima kuma saiya shirya gagarumar gasa ta yki akan cewa duk jarumin daya sami nasarar yi masa rauni ko ya kaishi kasa to ya fadi duk abinda yake so walau dukiya ko wata kadara tasa zai bashi.Lokacin da wannan labari ya bazu a nahiyar,sai sadaukai,jarumai da mayaka sukayi ta tururuwa izuwa cikin birnin kisra domin shiga wannan gasa duk da cewa da yawansu sun firgita da al'amarin sarki Uzaima,sun san cewa babu wanda ya taba samun galaba akansa amma saboda kwadayin ladan da sukaji za'a baiwa mutane sukayi kundunbalar shiga wannan gasa. ¤ ¤ ¤ DR KABEER LAWAL UMAR ROKED A YAMMA da Birnin Kisra akwai wata karamar kasa da ake kira da NURUL AMSAR.Sarki dake mulkin wannan kasa ya kasance adali,kuma tsoho ne tukuf! Har ma takai cewa ya kwanta CUTAR AJALI saboda tsufan nasa.Shi dai wannan sarki ana kiransa da suna SA'AD IBINI HUSEIN.Saboda birnin Nurul Ansar tana makoftaka da birnin Kisra sai ta sami kariya daga sharrin mahara da yan FARAUTAR BAYI.Don haka akwai cikakken kwanciyar hankali da zaman lafiya a birnin.Kuma Allah ya albarkaci birnin da arzikin noma,kuma sannan sarki Sa'ad yana matukar biyayya ga sarki Uzaima,hakan yasa duk shekara yake aika masa da kyautar amfanin gona mai yawan gaske da kuyangi.Bisa wannan dalili ne ko kadan sarki Uzaima bai taba sa ido akan kasar Nurul Ansar ba,kai har ma zuba dakarunsa yayi akan bodar birnin domin su basu tsaro daga yan kawo harin sumame.Sarki Sa'ad yana da matan aure shida,amma kuma 'yarsa guda daya ce jal!A duniya wata kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance mai suna ARYALA.A Duniya babu abinda sarki Sa'adda ke SO da KAUNA sama da gimbiya Aryala,amma tunda aka haifi Aryala aka boyeta saboda tsananin Kyawunta.Kai!Hatta Barori da hadiman gidan sarautar babu wanda ya taba ganin fuskar Gimbiya Aryala bare ya tsegunta irin kyawunta saboda kullum ana rufe fuskarta ne da wata bakar Hula wacce idanunta,bakinta da hancinta kadai ake iya gani,kuma mahaifinta ne ya bada wannan umarni saboda wani sirri da bokansa ya gaya masa.Lokacin da Aryala ta fara tasowa sai Sarki Sa'adda yaga ashe Allah yayi mata baiwa ta sadaukantaka,domin tun tana shekara shida a duniya take iya dagashi sama ta fyada da kasa a lokacin da yake koya mata kokawa. Doctor kabeer kemagana Koda gain wannan al'amari na ban mamaki sai sarki Sa'ad ya sake killace Gimbiya Aryala aka dauketa ita da mahaifiyarta aka kaisu can wani gidan sarki dake can bayan gari.In banda dakarun dake gadin gidan babu kowa a cikinsa face Aryala da mahaifiyarta.Anan ne kuma sarki Sa'adda ya rinka zuwa da kansa yana koyawa gimbiya Aryala yaki.A sannan ne fa ya sake ganin abin al'ajabi daya shallake tunaninsa.Ba komai ya gani ba face yadda a kwana uku kacal Aryala ta lakanci sarrafa takobi fiye dashi.A cikin sati uku kuwa sai gashi tana baiwa kanta horon yakin da ba'a taba koya mata ba,sai gashi har tashi sama take kamar tsuntsuwa tana kaiwa iska SARA DA SUKA.haka dai Gimbiya Aryala da mahaifiyarta ZALIMA suka cigaba da rayuwa a cikin wannan gida na bayan gari su biyu kacal tsawon shekara goma sha biyu.A tsawon wannan lokaci Aryala bata da wani aiki wanda yafi baiwa kanta horon yaki da kuma fita daji farauta a sirrance ba tare da dakarun gidan sin sami ba.Daidai da rana daya Gimbiya Aryala bata taba cire hular fuskarta ba ta kalli kanta a madubi bare taga kamanninta.Bata cire wannan hula face idan zatayi wanka ko zatayi barci,saboda dokace sarki ya kafa mata.Gimbiya Aryala ta kasance tana tsananin son sarki Sa'ad don haka tana matukar biyayya a gareshi saboda haka bata yarda ta sabawa umarninsa.Duk sa'adda Gimbiya Aryala ta tuna cewa itafa yar sarki ce kuma mai jiran gado,amma gashi an kawota wani gida dake cikin kungurmin daji an ajiyeta tare da mahaifiyarta tsawon shekaru goma sha biyu ba tare datasan dalili ba,kuma sannan an kafa mata dokar rufe fuskarta a koyaushe har yakai cewa ita kanta batasan kamannin kanta ba.An nisantata da jama'a,bata ma san yadda ake tafiyar da al'amarin rayuwa ba face abinda mahaifiyarta ta koya mata,sai tayi kuka na takaici da bakin ciki a duk sa'dda ta zauna tana tunani akan wannan lamari na rayuwarta.Abu daya ne yake sa zuciyarta tayi sanyi a duk sa'adda ta kasance a cikin wannan hali,kuma ba komai bane face duk sa'adda ta tafi farauta daji tayi gumurzu da wata dabbar mai hadari ta kasheta sai ta tsinci kanta a cikin dimbin farin ciki,tayi murna bisa ganin jarumtakar da Allah ya bata.A duk lokacin da Gimbiya Aryala ta tambayi mahaifiyarta dalilin da yasa aka killacesu a cikin wannan gida dake daji aka hanasu rayuwa a cikin gari da gidan sarauta sai kawai taga hawaye ya zubowa mahaifiyarta Zalima,sannan tace da ita kiyi hakuri yake 'yata lokaci yana nan zuwa da zamu koma cikin gari kuma a sannan ne zaki gaji mahaifinki ki haukan KARAGAR MULKINSA!!!Duk sa'adda Gimbiya Aryala taki wannan batu daga bakin mahaifiyarta Zalima sai ta kamu da tsananin mamaki,ta dubeta tace,saboda me bazamu koma yanzu ba?Yake Ummina ki tuna fa cewa yanzu mahaifina ya tsufa tukuf,kuma gashi yana yawan yin rashin lafiya,har ta kai cewa yanzu sau biyu rak yake iya kawo mana ziyara gidan nan,shin bakya tsoron AJALI zai iya riskarsa muna nan bamu sani ba?Yake mahaifiyata keda kanki kinsan irin tsananin son da nake yiwa Abbana,don haka ko zai mutu inason ya mutu akan kafaduna ina rungume dashi.Koda Gimbiya Aryala tazo nan a zancenta sai hawaye ya zubo mata daga idanunta.Itama mahaifiyarta Zalima ta kamu da tsananin tausayinta ta kama zubar da hawayen suka rungume juna suna masu ci gaba da kukan. Toh ai shikenan Nima tsananin jin tausayin su yasa na tsaya ina jimami. .... Dafatan yayi kuma zakuyi liking da commenting kamar yadda kuka saba.. Sannan zan cigaba kaman yadda na saba Insha Allah. ............ ... By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOOKASUWAR RAYUKA Littafi na Daya (1) Part B. Suka rungume juna suna masu ci gaba da kukan.Tun daga wannan rana sai da sarki sa'ad ya shafe sati biyu cur!bai kawowa su Gimbiya Aryala ziyara ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalinsu kenan,kawai sai Gimbiya Aryala ya mike tsaye ta kama shiri zata fita.Cikin firgici mahaifiyarta Zalima ta sha gabanta tace,ina zakije?Koda jin wannnan tambaya sai hawaye ya zubowa Gimbiya Aryala tace,ya za'ayi naci gaba da zama tsawon sati biyu ba tare danaga Abbana ba?Bamu san halin da yake ciki ba a yanzu yana raye ko baya raye bamu sani ba.Dole ne yanzu naje cikin gari na shiga har fada domin nasan abinda ake ciki. KABEER LAWAL UMAR ROKED Gimbiya Aryala na gama fadin hakan sai ta juya ta nufi bakin kofa da nufin taje inda bargar dawakai take ta kama daya ta hau.Koda ganin haka sai Zalima ta ruga tasha gabanta ta rungumeta kuma ta fashe da kuka tana mai rokonta akan ta kara hakuri lallai sarki bazai barsu haka ba.Nan fa gardama ta karke a tsakaninsu,Gimbiya Aryala nacewa sai ta tafi,ita kuma Zalima tana riketa tare da rokonta akan ta hakura da zuwa.Suna cikin wannan hali ne kwatsam!Sai akaji haniniyar doki a kofar gidan alamar cewa manzo yazo daga fada.A Guje Zalima da Gimbiya Aryala suka ruga izuwa kofar gidan,suna zuwa kuwa sai sukaga ashe wani hadimin sarki ne na jikinsa yazo.Take hadimin ya sauko daga kan dokinsa,koda yazo gaban gimbiya Aryala sai ya zube bisa guiwoyinsa yayi mata gaisuwa irin wacce ake yiwa sarki.Duk da cewa fuskar gimbiya Aryala a rufe take saida Hadimin yaga alamun tsananin tsoro akan fuskarta domin ja tayi da baya a firgice tana mai dafe kirjinta ta dubi hadimin tace,meya faru ga Abbana?Hadimin yayi murmushi sannan yace sarki nanan a raye,amma yana kwance cikin jinya,kuma shine ua aikoni gareku yanzu. Sarki yace a shaida muku cewa yaune ranar dazaiyi murabus ya baki KARAGAR MULKINSA don haka sai ku shirya mu tafi.Koda jin wannan batu sai Gimbiya Aryala da mahaifiyarta Zalima suka kamu da tsananin farinciki gami da mamaki.Nan da nan cikin kankanin lokaci Zalima da Gimbiya Aryala suka yi shiri suka debi yan kayan dasuke bukata suka hau dawakai biyu,hadimin yayi musu jagora suka durfafi hanyar dazata kaisu cikin gari.Tunda suka fara wannan tafiya sai Gimbiya Aryala ta tsinci kanta a cikin tsananin farin ciki don haka sai ta rinka kalle kallen daji tana ta murmushi cikin annashuwa.Koda suka iso kofar gari kuma taga yadda gaba dayan garin ya sauya da sabbabin gine gine sai hawaye ya zubo mata saboda rabon data taka kasar garin yau shekara goma sha biyu kenan.Kawai sai Gimbiya Aryala ta sauko daga kan dokinta ta debi kasa da hannayenta biyu ta shinshinata sannan tayi ihu cikin murna. DOCTOR KABEER LAWAL UMAR ROKED Al'amarin daya firgita hadimin sarki kenan,yayi sauri ya tsaida dokinsa ya sauko ya kama Gimbiya Aryala ya tasheta tsaye da sauri ya dubeta yace,haba ya shugabata,ayau fa zaki zama sarauniyarmu yaya zaki rinka yin abu na kaskanci irin haka?Koda jin wannan batu sai Zalima ta dubi Hadimin ta bushe da dariya tace,yakai SHUBARU ka kyale 'yata tayi farin cikinta ta more domin tana begen birninta ne.Nan dai Shubaru ya kamawa Gimbiya Aryala Dokinta ta sake hawa suka cigaba da tafiya suka kunna kai izuwa cikin garin.Har suka isa gidan sarautar babu wanda ya gane ko su waye.Kai tsaye aka wuce dasu Gimbiya Aryala izuwa fadar sarki.Al'amarin daya basu mamaki kenan har Gimbiya Aryala ta dubi hadimi Shubaru cikin mamaki da rashin fahimta tace saboda me zaka nufi fada damu maimakon ka kaimu turakar sarki muga halin da yake ciki?Hadimi Shubaru yace,ai sarki yana fada yana jiranku.Gama fadin hakan keda wuya kuwa sai suka iso bakin kofar fadar aka bude musu suka shiga.Suna shiga suke iske fadar a cike makil da fadawa da kuma mutanen gari babu masakar tsinke.Take suka hango sarki Sa'd zaune akan karagar mulki yana rike da sandarsa ta mulki.Kallo daya Gimbiya Aryala da Zalima suka yiwa sarki Sa'ad suka gane cewa yana jin jiki,kawai karfin hali yayi harma ya iya fitowa fadar ya zauna.Koda jama'a sukaga matar sarki Zalima da 'yarta Gimbiya Aryala sun durfafi inda sarki sa'ad ke zauna sai suka cika da tsananin mamaki saboda jama'a da yawa sun zata cewa Zalima ta mutu tun shekaru goma sha biyu bayan ta tafi garinsu gaida iyayenta.Wannan itace jita jitar da akayi ta yadawa har ma ana cewa jaririyarta data haifa ma ta mutu.A wannan lokaci Gimbiya Aryala tana sanye da wata doguwar riga ce ta talakawa wacce mahaifiyarta ce ta dinkata da hannunta,kuma takalmin dake kafarta mana fate ne kalar na talakawa.Duk da cewa fuskar Gimbiya Aryala a rufe take,amma kyawun siffar jikinta sai daya dimauta gaba daya mutanen dake fadar musamman mazaje.Koda sarki sa'ad ya hango matarsa Zalima tare da 'yarsa Gimbiya Aryala sun shigo cikin fadar,sai fuskarsa ta fadada da murmushi,kawai sai akaga sarki sa'ad ya yunkura cikin matukar karfin hali ya mike tsaye sannan ya taka matattakalar dake gabansa ya sauko kasa daga kan tudun da Kargar Mulkinsa take yazo ya tare su Zalima duk su biyun sai suka fada kan kirjinsa suka rungumeshi suna kuka.Take shima sarki sa'ad zuciyarsa ta karaya har hawaye ya zubo masa.Al'amarin daya kara baiwa kowa mamaki kenan.Bayan sarki sa'ad ya dan jima kankame dasu Gimbiya Aryala,daga can saiya janye jikinsa daga cikin nasun sannan ya fuskanci jama'a yace,yaku jama'ar birnin nurul ansar da yawanku kun san kowace ce wannan a hannuna na hagu.To ga wadanda basu santa ba ina mai sanar dasu cewa wannan itace matata guda daya jal a duniya wato Zalima wacce ake ta yada rade radin cewa ta mutu a can garin su kimanin shekaru goma sha biyu da suka gabata baya.Wannan budurwa kuwa da kuke gani a hannu na na dama ba wata bace face 'yata guda daya jal tilo a duniya,wato gimbiya Aryala. ... .... By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO KASUWÀR RAYUKA!!! Littafi na Dàya (1). Part C Wannan budurwa kuwa da kuka gani a hannuna na dama ba wata bace face 'yata guda daya jal tilo a duniya,wato Gimbiya Aryala.Koda sarki sa'ad yazo nan a zancensa sai gaba dayan mutanen dake fadar suka mike tsaye cikin tsananin mamaki suka kurawa Gimbiya Aryala Idanu.Nan take sarki yasa hannu ya cire hular dake kan fuskar gimbiya Aryala,jama'a sukayi arba da tsananin kyawun fuskarta tata,ai hatta yan'uwanta mata dimaucewa sukayi saboda tsananin kyawunta.Nan take sarki sa'ad ya kama hannun gimbiya Aryala yajata izuwa kan karagarsa ta mulki yaje ya zaunar da ita sannan ya cire KAMBUN SARAUTARsa na danyen zinare da lu'u lu'u dake kansa ya dora mata akanta,sannan ya mike mata sandarsa ta mulki ta karba.Kawai sai ya zube kasa a gabanta yayi gaisuwa mai nuna MUBAYA'A.Koda ganin haka sai gaba dayan jama'ar dake cikin fadar suka zube kasa gaban Gimbiya Aryala suna masu jadda mubaya'arsu kamar yadda sukaga sarki sa'ad yayi suna cewa cikin hadin baki munyi MUBAYA'A a gareki ya sarauniyarmu!!! KABEER LAWAL UMAR ROKED Nan fa suka yi ta fadan hakan har muryoyinsu suka cika birnin gaba daya,jama'ar dake cikin gari ma da basu zo fadar ba a wannan lokaci saida suka jiyo,kuma labari ya riskesu da gaggawa cewa ai 'yar sarki sa'ad na nan a raye bata mutu ba,kuma gata nan ma a fada har yayi murabus ya dorata akan karagar Mulkin Birnin tare dayi mata mubaya'a.Nanfa Jama'a suka rude da shewa kuma akayi ta tururuwa zuwa fadar domin su wadanda basu ganta ba su ganta su ma kuma suyi mubaya'a a gareta.A takaice dai a wannan rana akayi bikin nadin gimbiya Aryala akan karagar mulki akayi ta shagali.Makada da mawaka sukayi ta bidirinsu,abinci da abinsha kuwa akayi ta wadakarsu.Saida aka raba dare ana wannan shagali sannan jama'a suka watse suka tafi izuwa gidajensu cikin farin ciki kowa na tofa albarkacin bakinsa.A wannan lokaci ne sarki sa'ad ya tura aka kirawo gimbiya Aryala da mahaifiyarta Zalima daga cikin gidan sarautar suka kadaita a cikin turakarsa.Saida gaba dayan hadiman sarki suka fice daga cikin turakar aka kullo kofofi da tagogin turakar gaba daya,ya zamana cewa saura su uku kacal!A cikin turakar,sannan sarki sa'ad ya mike zaune da kyar daga kan gadon da yake kwance yana mai yin wani irin tari mai zafi,ya dubi gimbiya Aryala yace,yake 'yata na sani cewa na jefa rayuwarki data mahaifiyarki a cikin kunci da matsi bisa tsarewar danayi muku a can gidana na bayan gari har tsawon shekaru goma sha biyu ba tare da kunsan dalilin yin hakan ba?To ku sani cewa yanzu ne zan gaya muku dalilin da yasa nayi muku hakan.Da farko dai inason yanzu kije gaban wancan madubi ki dubi fuskarki da siffar jikinki domin yaune ranar farko dazaki kalli kanki a cikin madubi kiga baiwar da kike da ita.Cikin sanyin jiki da alamun tsananin tsoro gimbiya Aryala ta mike tsaye ta nufi inda madubin turakar yake.Koda ta tsaya a gaban madubin ta kalli fuskarta da jikinta taga irin tsananin kyan da Allah ya bata,sai hawaye ya zubo mata ta juya da dubi sarki sa'ad tace yakai mahaifina,shin dama yanzu irin wannan ce baiwar danake da ita amma ka boyewa jama'armu ni har tsawin shekaru goma sha biyu? Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa sarki sa'ad yace,yake 'yata ki sani cewa tun daga ranar dana daukeku keda mahaifiyarki nakai ku wannan gida nawa na bayan gari na killace ku,kullum saina yi kuka saboda tsantsar bakin cikin rabuwa da ku,kuma da bakim cikin rashim ganin wannan kyakyawar fuskar Taki.Tun kafin na haifeki wani bokana ya taba bani labari cewa za'a haifa mini kyakkyawar 'yar da babu kamar a kaf wannan nahiya gaba daya,amma idan har ban boye ta ba har tsawon shekaru goma sha biyu ba to za'a rabani da ita ta karfin tsiya kuma bazata ta taba gadon karagar mulkina ba.To bisa wannan dalili ne yasa na boyeku a wannan gida har tsawon wadannan shekaru,yanzu ina fadan zaku gafarceni keda mahaifiyarki bisa wannan babban laifi dana aikata muku,ni akaran kaina banayi bane don na cuceku sai domin na kyautata rayuwarku gaba daya dagani harku,musamman ma ke Gimbiya.Koda sarki sa'adda yazo nan a zancensa sai hawaye ya sake zubowa gimbiya Aryala da mahaifiyarta Zalima suka rungume sarki kuma suka kara fashewa da kukan murna gaba dayansu. ADMIN ROKED Gimbiya Aryala tace,yakai Abbana nima ka gafarceni bisa damuwar dana shiga a dalilin wannan gata dakayi mana bisa rashin sani ba,inda nasan cewa gata kayi mini domin ka tserar da rayuwata don na gajeka daban damu ba daidai da rana daya,maimakon hakan zai zamo kowanne lokaci ina cikin farin ciki mara misaltuwa.Koda jin wannan batu sai sarki sa'ad yayi guntun murmushi a lokacin da tari ya sarkeshi kamar zai mutu,idanunsa sun zazzaro sun fara juyewa har gudan jini ya subuto daga cikin bakinsa.Al'amarin daya firgita gimbiya Aryala da mahaifiyarta Zalima kenan,suka dimauce da matsanancin tashin hankali ga firgici.Zalima ta yunkura domin ta ruga ta kirawo likita,amma sai sarki sa'ad yayi sauri cikin dauriya ya riko hannunta ya dakatar da ita tare da dubanta a lokacin da idanuwansa suka kada sukayi jajur tamakar garwashin wuta,ya bude bakinsa dakyar cikin dauriya yace,yake matata kiyi sani cewa bakin alkalami ya riga ya bushe,babu tantama ko jayayya mutuwa zanyi,don haka babu wani magani da zai iya warkar mini da wannan ciwo nawa,kawai saidai jiran lokaci.Inason ku saurara da kyau kuji abinda zan gaya muke keda gimbiya Aryala.Yayi shiru yana mayar da numfashi sannan ya dawo da dubansa ga gimbiya Aryala yace,yake 'yata ki sani cewa bincike ya tabbatar da cewa baza kiyi aure ba har izuwa lokacin da zaki gushe,amma kuma zaki haifi 'da namiji wanda zai sami daukakar da babu mai kamarta a wannan zamani.Ki kasance mai hakuri bisa duk irin kaddarar da zata sameki,kuma ki rungumi danki hannu bibbiyu kada ki tsaneshi ko ki tsani ubansa da yayi sanadin zuwansa duniya.Koda sarki Sa'ad yazo nan a zancensa sai hawayen takaici ya zubowa Gimbiya Aryala ta dubeshi tace,ya kai Abbana yanzu kenan ni zan haifi dan da bata hanyar aure aka sameshi ba? Ai wannan babban abin kunya ne kuma abin gori ga wannan masarauta tamu wanda bazai taba gushewa ba har abanda?Sa'adda sarki sa'ad yaji wannan batu sai ya girgiza kai yace,a matsayinki na jarumar dazatayi abin al'ajabin da babu wani jarumi daya taba yi a wannan nahiya,to ina tabbatar miki babu wani abu na kunya ko gari dazai kasance a gareki.Koda gama fadin hakan sai sarki sa'ad ya zura hannu a karkashin matashin kan gadonsa ya dauko wata wasika ya mikawa gimbiya Aryala.Nan take gimbiya Aryala ta karbi wasikar ta warwareta ta karanceta tsaf,cikin tsananin mamaki ta dago kanta bayan takai karshen wasikar ta dubi sarki tace haba yakai Abbana yaya zakace nayi shiri na tafi izuwa birnin kisra na wakilceka a gaiyatar da sarki uzaima yayi maka alhalin kana cikin wannan hali na rashin lafiya.Sarki sa'ad ya numfasa yace zuwanki wannan gaiyata shine zai daukaka darajarki a duniya don haka bani da wani buri da yafi kije ki halarci wannan taro.Kamar yadda kika gani a cikin wannan wasikar akwai GASAR JARUMTAKA wacce sarki uzaima ya shirya akan cewa duk jarumin daya kaishi kas ko yayi masa rauni zai bashi duk abinda yakeso,inaso ki shiga wannan gasa kema a fafata dake.Koda jin haka sai idanun Gimbiya Aryala dana mahaifiyarta Zalima suka zazzaro suka dubi sarki sa'ad cikin firgici da mamaki.Gimbiya Aryala ta budi baki tace yakai Abbana saboda me zakace na shiga wannan gasa tayin gumurzu da sarki uzaima alhalin tun ina yarinya karama nake jin labarin irin gagarumar jarumtakarsa?Ance fa tunda yake bai taba zuwa kasa ba a filin fama,ta yaya nidana kasance ban taba yin yaki da mutane ba zakace naje na tareshi har mu fafata.Sarki sa'ad ya daga hannunsa da kyar ya dora akan kafadar gimbiya Aryala yace yake 'yata kiyi sani cewa matsoraci baya zama gwani har abada.Don haka kada ki yarda har abada zuciyarki ta karaya bisa duk abinda kika sa a gabanki.Daga Yau na umarceki da ki zama MACE MAI KAMAR MAZA,domin hakan ne kadai zaisa wannan MASARAUTA tamu ta wannan gari namu yacigaba da wanzuwa a doron kasa.Inason ki fara shirin wannan tafiya dun daga daren yau domin gobe da sassafe zaki tafi izuwa birnin Kisra.Zaki tafi tare da dakaru dubu uku kacal,wadanda zasuyi miki rakiya,kuma akan keken dokin masarauta zaki tafi dauke da tutar birninmu a matsayinki na sabuwar sarauniyarmu.Kada ki boye fuskarki ko kyanki kuma ki saki ranki cewa kin fita yakin kare mutuncin masarautarmu ne da rayuwar jama'ar kasarmu .... ..... By AL MUSTAPHA Isah Inkiya #MUSTINDOO #PRABHAS kuhuta lfy KASUWAR RAYUKA!!! Littafi na Daya (1) Part D Kin fita yakin kare mutuncin masarautarmu ne da rayuwar jama'ar kasarmu.Koda jin wannan batu sai gimbiya Aryala taji dukkan wani tsoro yakau daga cikin zuciyarta kuma taji cewar zata iya sallama rayuwarta don kare lafiyar karagarta ta mulki da kuma jama'arta,don haka saita rungume sarki sa'ad tana mai zubar da hawaye tace,yakai Abbana nayi maka alkawari cewa lallai daga yau na kau da dukkan tsoro daga cikin raina bisa duk abinda nasa a gabana kuma zanyi wannan tafiya cikin burin samun nasara.Abinda zan rokeka guda daya ne jal,inason ka rayu har naje na dawo daga wannan tafiya

Chapter 1 of 4