akan wannan ƙazamar talakan zakace naje nayi driving bayan kasan banason......."
Ɗaga mata hannu yayi ya dubi Anam yace “Ɗauko hijjab ɗinki Kharimatu" da sauri ta miƙe domin shiga ta ɗauko hijjab ɗin jiri ya ɗebeta ji kakeyi tik ta zube a ƙasa ya isa da gudu ya ɗagota ya fice da ita yasata a mota suka fita suna zuwa aka bata gado tsoron kira yake ya faɗa yasan masifar Granny Indai tasan dalili to ba Salma ba shi kansa ya kaɗe har ganyensa.
Ganin lkc na tafiya gashi yanada taro 9:30am yasashi yin shahadar kiran wayar Mama Yabi ta ɗaga suka gaisa ya faɗa mata abinda ke faruwa aikam ta ruɗe tace “bansan yaushe Kharimatu zatayi hankali ba kawai saboda sakarci taje zata illata kanta ganinan"
Ajiyar zuciya yayi ganin ya ɗorata ta ɗoru yaci gaba da zama gurin Anam tare da zubanta ido yanda take kwance da drip a hannunta baccin wahala ya ɗauketa kanta sanye da hula fuskarta wasai ga ɗaurin dressing ɗin da akayi mata jiya a hankali ya gangaro zuwa gangar jikinta yana ƙare mata kallo tunda yake baitaɓa tsayawa ya ƙarewa Anam kallo ba sai Yau Nazeer abokinsa yana yawan faɗa masa wato Aliyu babyn nan ta gdanka Anam tana matuƙar burgeni ɓoyayyen kyaunta yana ruɗani bantaɓa gajiya da kallonta ba nikam da zan samu dama zanso abani wannan yarinya matsayin mata nasan zanji daɗin hakan" taɓe baki yayi ya miƙe yana ƙare mata kallo yace “kai kasan wani ɓoyayyen kyau Nazeer Ni bayyananne na sani".......
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi kan ₦300 kacal tura ta acc 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta whattsAp number 09013718241_
*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?
~Paid book~
Oum Hairan
7-8
Kiciɓis sukayi da Mama a ƙofar shiga ɗakin suka gaisa ta shige ciki ta zubawa ƴartata ido cike da tausayi ƙarasawa tayi gabanta ta riƙo hannunta daidai lkcn data buɗe idonta tace mata “sannu Kharimatu ashe haka tsautsayi ya faru dake kema kin cika gaugawa ki rinƙa bin abubuwa a hankali kinji" lumshe idonta tayi tanajin ɗacin abinda ya faru da ita a ranta Aliyu ya shigo da sallamarsa a ƙasan maqoshi ya ajiye ruwa da magunguna yace da Mama “tunda kinzo zanje office inada Meeting zuwa tara da rabi" kuɗi ya zaro ya ajiye a gefen gadon tayi masa gdy ya fice a ɗakin batare dako inda Anam take ya kalla ba.
Bayan fitarsa Mama ta haɗa mata shayi me kauri da madarar daya kawo ta zauna tana bata tanaci daƙyar abincin ɗaci yakeyi mata a baki hakadai ta rinƙa turawa harta ƙoshi jefi² suke yar hirarsu da Mama Anam ta kasa jurewa ta faɗawa Mama asalin abinda yaji mata ciwo har ya haifar mata da zazzaɓin sosai Mama taji babu daɗi amma a fili sai tace “babu komai akwai Allah da talaka da mai arziƙi duka wanda yayi su son abinsa yakeyi saboda haka komai yayi farko zaiyi ƙarshe"
Ba haka Anam tasoba domin zuwa lkcn hƙrnta da zama a gdan Salma ya ƙare burinta kawai barin gdan saidai batada wata hanya ta barin gdan dole saida shahalewar Mama, yini sukayi a asibitin da yamma Aliyu ya dawo shida Granny tanata zubawa Anam sannu likitan yazo ya sallameta yayi Hamdala domin bayaso asirinsu ya tonu yafiso ayi a lulluɓe mgnr ɗebe kayan sukayi suka zuba a mota bayan sun shiga Granny tace “Ali wannan yarinyar gda zata wucce gurin uwarta idan ta warke ta dawo wannan kasaltacciyar matar taka me shegen son jiki ba ƙyaleta zatayi ta warke ba"
Bayason jan maganar dole ya amince saboda gudun tujarar Granny suka wucce Ɗan ladi nab Sidi zuciyar Mama da Anam wasai suna zuwa ya zubesu ya juya ya nufi gdansa. A falon ya tarar da Salma taci uwar kwalliya ta harɗe tana kallo tanacin donnut ya dubi yaran yagansu da kayan islamiyya yace “ya haka Salma gobe babu makaranta ne?" Ɗagowa tayi tace “kayan naji suna tsamin gumi shine nabarsu idan kun dawo waccen yarinyar ta wanke" jinjina kai yayi lallai Salma batada imani wato wadda aka sallamo a asibiti take tsammanin tayi mata wanki lallai Granny tanada hangen nesa.
Samansa ya haye yayi wanka ya fito ya zauna a dinning ya buɗe abinci ya faraci baici na kirki ba ya miƙe ya nufi waje ya zauna a kujerun dake cikin flowers na gdan yana duba jarida
Bai koma cikin gdan ba sai bayan yayi sallah Magrib da isha sannan ya shiga ya nufi saman ya shiga ɗakinsa ya sake watsa ruwa ya kwanta shiru yana jiran Salma har dare ya tsala yaja tsaki ya juya lamarin Salma ta fannin kula da shimfiɗarsa yana bashi tsoro kullum ita cikin uzuri take yau aiki gobe ciwon mara jibi zubar jini idan bataga damaba sai su shafe satittika a haka babu ruwanta shikuma ga miskilanci Indai bata kawo kanta ba ya daina kiranta.
Wayewar garin ta shirya tsaf tana mita ta shirya yaran suka fice suka tafi aiki sukuma yaran aka wucce dasu makaranta a mota take tambayarsa wai meye ya hana Anam dawowa? A gajarce yace “ganin dama" daga haka tayi masa shiru shima yayi mata ya ajeta a ma'aikatarsu ya wucce Campanynsu.
Kwanakin da Anam tayi tare da Mahaifiyarta abin gwanin daɗi ji takeyi kamar karta koma.
Ranar data cika sati tana ɗakin Granny sunata shirmensu Suka tsinkayo sallamar Aliyu saida gabanta ya faɗi ya shigo ɗakin idanunsa na kanta hakanan ya riski kansa da wata muguwar faɗuwar gaba lkcn da ya sauke idanunsa akanta cikin sati gudan da baya ganinta sai yaga gabaɗaya ta canza masa tayi wani haske fuskarta tayi fiyau da ita, janye gashinta tayi daga hannun Granny da take daure matashi tana ranƙwashinta tana cewa “ni banda tsiya Allah yayi miki yalwar suma ki rinƙa neman lalatata da shirme idan tayi fushi ta kaɗe ai naga da uwar da zakiyawa mijin da kishiyar gwalli"
Turo baki tayi tace “tabdi lallai ma Granny nikam ki dainamin fatan kishiya wlh ko sunan banson ji" ba Granny ba hatta Aliyu saida ya zare tabarau ɗin idanunsa ya kalleta tayi ƙasa da kai ganin irin kallon da yakeyi mata yasata jan mayafinta ta fice sumsum har taje bakin ƙofa yace “ki shirya zamu tafi gdan babu kowa Salma ta tafi Ziyarar aiki Sokoto sai yara"
Amsawa tayi cikin ladabi duk da bataso hakan ba amma ya zatayi ta fice ta nufi cikin ta ishe Hajiya Muniba a parlour tayi mata sannu da gda ta amsa mata a yatsine ta wucce ta tarar Mama hatta haɗe mata kayanta dauka kawai tayi tana hawaye ta fita daidai lkcn da yake fitowa a sashin Granny ya shiga gdan bai jima ba ya fito ya shiga motar itama ta shiga suka wucce.
Yaran sai murna sukeyi ta dawo itakuma tana ƙunci sarai Aliyu ya lura bataso dawowar ba daga yanayinta baisan dalili ba duk sai yaji ya tsargi kansa da takura mata to amma ya zaiyi zaman gda daga shi sai yara bazai yiwu ba itakuma Salma yanayin aikinta yana yawan sasu yawo.
Kayanta ta ɗauka ta shige ciki yabita da kallo shi kansa baisan meye yake kallo a jikinta ba amma tabbas yasani ba tun yau ba wani abu yana burgeshi game da yarinyar a hankali batare daya sani ba ya kira sunanta taja ta tsaya cikin fargaba tare da juyowa shikansa baisan dalilin kiran ba yace “am ki dafamin coffee ki kawomin ɗakina" saida taji wani ras da yace ɗakinsa domin a tarihin zamanta na gdan batajin ta taɓa shiga ɗakinsa yananan bai bata dama ba har marinta saida yayi akan aikenta ma da Salma takeyi tun lkcn ta daina gigin zuwar masa ɗaki........
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi kan ₦300 kacal tura ta acc 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta whattsAp number 09013718241_
*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?
Paid book
Oum Hairan
9-10
Shiga tayi ta aje kayan ta fito ta nufi kitchen yaran suka biyo ta musamman Farooq yana ce mata “nifa yunwa nake ji daddy indomie kawai ya bamu" jinjina kai tayi ta kunnan kan Gas biyu ɗaya ta doransa coffee ɗaya ta ɗora abinci ta riga gama dafa masa coffee ɗin ta ɗauka ta nufi ɗakin nasa ta ƙwanƙwasa yana zaune ya zuba uban tagumi baisan abinda zuciyarsa take shirin aikatawa ba amma tabbas tana tunzurashi ya aikata wani abu saidai shi kansa yanajin faɗuwar gaba idan ya tuna abin mai wahalar yuwuwa ne bayan haka ma zuciyarsa kamar ba adala bace a cikin sati guda tunanin nan ya fara bijiro masa wanda ya ɗarsu domin nemawa yaransa mafita shin tayaya ma Anam zata amince da wannan shirin nasa? In itan ta amince mahaifiyarta da mahaifansa zasu yarda? Musamman ma Hajiya Muniba.
Ya jinjina wannan lamari yafi a ƙirga kafin ya ankare da taɓa ƙofar da akeyi yabata izinin shigowa ta buɗe ta shigo da sallama a bakinta amma kanta a ƙasa yake ta ajiye masa flat ɗin data jero kofunan ta miƙe zata fita yace “am bakiji ba...." Tsayawa tayi tare da juyowa ta koma ta tsugunna tace “Na'am" zubanta ido yayi ya kuma kasa cewa da ita komi har saida ta gaji tace “Abinci na ɗorawa su Farooq zai iya ƙonewa"
Numfashi ya sauke ya bata izinin tashi ta miƙe ta fita ta koma kitchen ɗin ta tace shinkafar data ɗora ta zuba musu miyar data dumama ta ɗauka suka fito Parlourn tana bawa jannat Muwaddat da Farooq sunaci yanda yaran sukecin abincin zai tabbatar maka da gaske yunwa sukeji.
Sunci abincin sosai ta gyara gurin ta jasu ɗakinsu ta kwantar dasu bayan tayi musu wanka itama tayi tayi sallar Magrib da isha da bata samu tayi ba ta kwanta a cikinsu tana rungume da Jannat tayi musu Addu'a bacci ya ɗaukesu dukkansu.
Fitowa yayi domin duba yaran ya buɗe ɗakin ya shiga tare da kai hannu ya kunna glub gabansa ya fadi ganinta kwance tsakiyar yaran ya daɗe tsaye yana kallonta luguden zuciyarsa na ƙaruwa a kallo na zahiri baya hango wani abu dake burgeshi ga Anam Amma ya fahimci zuciyarsa ta jima da sanya masa wasu alamomi masu neman fassara.
Juyawa yayi ya fice zucciyar tasa cike da tunanin ta inda zai fara aikinsa tabbas lkc yayi da ya kamata ya samawa yarinyar yanci wanda ya farajin ɗarsuwar dacewar sa daga tausayi, ya ɓata dogon lkc yana tunanin rikicin da yake shirin ɓallowa kansa da Anam Amma zuciyarsa taƙi karaya a ƙarshe wayarsa ya ɗauka ya turawa abokinsa Nazeer cewar gobe su haɗu a office yanason su tattauna. Hakance ta faru washegarin kamar yanda Anam ta tashi da wuri haka shima ya tashi lkcn daya fito tana kitchen tana haɗa abin karin safe tana goye da Jannat da tayima wanka ta juyo ta ganshi tsaye a ƙofar kitchen ɗin ta sunkuyar da kanta tare da gaisheshi cikin ladabi ya amsata yace “ina sauri ne" daga kai tayi tare da ɗaukar kayan data gama dasu takai dinning ta dawo ta gyara kitchen ɗin ta shirya yaran ta miƙawa driver su ya tafi kaisu makaranta hakan yabata damar sake kwanciya.
*********
Duban juna sukeyi da Nazeer kowa yana sauke numfashi inda Nazeer yake goge zuffa ya ɗago cikin tsananin mamakin abokin nasa yace “ƴar aikin gdanka kakeji kanaso kuma so na aure? To ya kuma zakayi da masifaffiyar matarka me baƙin kishin masifa?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya aje biron da yake wasa dashi a hannunsa yace “abinda nakasa samun amsarsa kenan am ni Ina ganin idan harsu Hajiya sun amince bazai zama matsala ba asanya rana gajeriys cikin sirri zanyi ƙoƙarin nema mata gida ƙarami nasata a ciki kafin komai ya daidaita bansan meye yake damun mata ba sun gaza ta ɓangarori da dama na auratayya amma daga lkcn da namiji yayi niyyar ɗauko musu wacce zata tayasu sai suyi tsalle suce basusan zancen ba duba dai Nazeer kaga rayuwar gdana nasani duk da cewar Salma Bata cikin matan da zaayima tambarin ƙazanta Amma fah da taimakon Anam kullum kaje gdannan Anam Bata tsaye bata zaune itace kula da yara gda da masu gda to inda zata iya ɗaukar wannan aikin meye yasa bazan gayyato ta tazo ta tayamu rayuwar har abada ba? Am Bama wannan ba Nazeer duk da cewar Ni bana cikin jinsi na maza masu takura ko yawan buqata hasali ma ta wannan fannin inada rauni amma fah a hakan duk lkcn dana buƙaci Salma sai ta kawomin uzuri kuma fah duk da haka cewa takeyi Ni ragone"
Shafa ƙeya Nazeer yayi yace “hakane
saidai kasan tunanin mata ya bambanta da namu sukan a ɓangarensu wannan babban abin kunya ne zaka aikata tabbas za'ayi surutu Bama iyakar surutu ba harda abinda yafi surutu to amma dake ka shirya saika fita da qwanjinka idan rabone sai kaga ka dauka"
Miƙewa sukayi tare suka fita sun jima jikin mota suna ƙara tattaunawa sannan sukayi musabaha suka rabu kowa ya shiga motarsa lkcn da yaje gda bai iske kowa ba a parlour ɗakinsa ya shiga ya cire kayansa ya watsa ruwa ya sanya jallabiya ya sauko ƙasan ɗakin Anam ya nufa ya ƙwanƙwasa ta miƙe a gyaran wardrobe ɗin da takeyi ta buɗe yana tsaye da cup a hannunsa ya zubanta idanunsa masu kama da wanda kejin bacci ta sunkuya cikin nutsuwa tace “barka da dawowa" lumshe idonsa yayi yanajin muryarta na ratsa sassan jikinsa yace “ina yaran nan?" Sunkuyar dakai tayi tace “dake juma'a ce Zeeze tazo ta ɗaukesu wai Aunty Salma tace tazo ta ɗaukesu suyi weekend acan"
Jinjina kai yayi yace “ina buƙatar abinci" yana faɗin haka yayi gaba ta koma ciki ta ɗauka hijjab ɗinta ta fito ta shiga kitchen ta haɗo masa abincin ta kawo masa ta miƙe zata tafi yace “bakiji ba" tsayawa tayi yace “ki haɗa kizo ki zauna inason mgn dake ne" dawowa tayi ta zauna ta fara haɗa masa a zahiri zakace wayar hannunsa yake kallo amma Anam ya zubawa idanu yana nazarinta sanyin yanayinta yafi komai burgeshi a ƴan kwanakin nan mika masa flat ɗin tayi cikin natsuwa yasa hannu ya karba tare da saukowa ƙasa ya zauna ya tanƙwashe ƙafarsa yanacin abincin yana satar kallonta, duk ta tsargu so take ya sallameta ta tafi gashi taga alamun bashi da niyyar bata izinin tafiya.
“Ranar da naje ɗaukoki a gda naji kinyi mgn lkcn da Granny take Miki faɗan gyara gashi kince ta daina yi miki fatan kishiya ko zan iya sanin dalilinki?"
Kanta na ƙasa ta ɗago ta sake sunkuyar dakai bazata iya jurewa irin kallon da yakeyi mata ba hakan yasa duk ta takura
Alamu yaga na bazatayi mgn ba yasashi cewa “ok amma zaki iya auren me mata?" Ɗagowa tayi da mugun sauri tare da girgiza masa kai ba tare da ta san tana girgiza masan ba kafeta yayi da idanunsa cike da faduwar gaba yace “why?" Maimakon ta bashi amsa sai kawai yaga ta fara share hawaye ya sake zubanta ido yace “talk me mana" ƙasa tayi da idanunta tace “ni kawai banaso ne saboda bazan iya fitina da tashin hankali ba kuma...kuma...." Shiru tayi
Tana qorarin haɗiye mgnr yace “kuma me?" Sake jan zuciya tayi tace “idan bakada galihu Gara ka samu mijinka kai ɗaya kada kaje ka shiga inda za'a ke maka gori" da sauri ya dubeta yace “gorin me?" Shiru tayi masa alamun tagaji da tambayar yayi murmushi ya matso gabanta yakai hannunsa kamar zai kamo nata tayi saurin janyewa cike da tsoro kawar da hannunsa yayi yace “yanzu idan ya kasance wani mutum me daraja da yasan ƙimarki yasan mutuncinki ya fito yace yanason aurenki sai ya kasance yanada mata da yara amma yace bazai hadaku gda ɗaya ba zai ware miki mazauninki daban shin zaki iya amincewa da hakan ko har yanzu baki gamsu ba?"
Shiru tayi gabanta na faɗuwa yayi murmushi yace “life hakanne zai faru wato akwai wani da yayimin mgn akanki kuma na yaba da nutsuwarsa so sai naga dacewar neman jin ra'ayinki game da hakan kafin a shigar da mgnr ga Mama so me kike gani akai yacemin bai buƙatar jan lkc a shirye yake kuma da gaske yakeyi"
Tunda ya kawo mgnr wanin gabanta ke faɗuwa wani tsoro yana shigar ta ta ɗago tana girgiza masa kai tace “Yallaɓai nikam banason auren me mata inajin tsoron kishiya amma idan ka yaba da nutsuwarsa banida ja zan roƙi Allah ya sanyamin dangana ya ciremin tsoron a zuciyata" murmushi yayi yace “good haka nakeso kije ki kwanta saida safe" kamar me jiran ya bata umarni ta miƙe ta nufi ɗakinta yabita da kallo yana murmushi yarinyar akwai nutsuwa shi mamakin ta inda ta samu wannan tarbiyyar yakeyi duk da kasancewar uwarta batada sauƙi wajen tarbiyya amma yawanci irin yaran nan da suka taso a wahalce zaka samesu basu cika nutsuwa ba tabbas idan yayi nasarar mallakar ta zai samu cikakkiyar kwanciyar hankali........
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi kan ₦300 kacal tura ta acc 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241_
*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?
~Paid book~
Oum Hairan
Free 11-12
_promo ya sauka💃🏼_ _Littafaina biyu da nakeyi yanzu haka YAFI ZAMAN AURE da ME YA JAMIN? A baya regular na kowanne 300 ne VIP 600 so yanzu abun ya canza idan ki/ka nason duka biyun regular zakiyi subscribe da ₦400 ne VIP kuma duka biyun zaki biya ₦700 ne wannan ya faru ne sakamakon wani dalili wanda garabasar zata ƙare daga ashirin ga watannan ne so ku hanzarta biyan naku maimakon ₦900 vip 2 books ya koma ₦700 regular 2 books ya koma ₦400 tabbas sai me rabo._
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafai ta hanyar biyan kuɗinku ta 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241_
_____________________________
Tunda ta shiga ɗakin take kaiwa da komowa ƙirjinta sai bugawa yakeyi Allah ya jarabceta da mugun tsoron kishiya itakam batason kishiya badon komai ba sai don gudun fitina musamman yanda zamani ya zama kawai suna marnege na rayuwarsu ita da mahaifiyarta aje a illata akan namiji......
Zama tayi a gefen gadon ta ɗaga hannunta sama tace “ya Allah ka zama gatana a duk inda ka sanya rayuwata tabbas kaine sarki mafi iya hukunci ga bayinsa kaine mafi cikakken zaɓi da iko" tana faɗin haka ta kwanta ta lumshe idanunta maganganun da sukayi da Aliyu suna dawo mata bata bawa sanin mutumin da yake bata lbr muhimmanci ba saboda haka ta gyara kwanciya taja bargo ta ƙudundune baccinta me daɗi na kwanciyar hankali ya ɗauke ta gobe zata huta babu yara babu matar gdan sai megidan shikam ba fitowa yakeyi ba weekend sai 12:00pm hakan yasa taji a ranta zata sarara na 2 days.
Washegari sai takwas tayi wanka ta fito ta gyara parlourn ta nufi kitchen ta ɗora break sai bayan ta gama ta fahimci ashe Aliyun baya gdan ta jere a dinning ta nufi ɗakinta ta zauna taci nata hankali kwance bayan ta gama tayi wanke² ta sake gyara inda ta ɓata ta kuma kwanciya bacci ya ɗauketa sai azahar ta farka tayi sallah ta wucce kitchen shiru babu Aliyu babu labarinsa haka ta ɗauki abincin safen ta kaiwa masu gadi sannan tayi wani.
Ta gama girkin kenan taji tsayawar motarsa ta ɗauki hijjab ɗinta ta zura ya shigo ta fito a kitchen ɗin ta durƙusa tace “barka da shigowa yallaɓai" wata gwauruwar ajiyar zuciya ta dubeshi da sauri yayi mata murmushi batare da yace komai ba ya nufi saman saida yaje step na ƙarshe sannan yace “ki kawomin coffee da abinci nasha wahala yau garinku sunada tsaurin Al'ada" “garinmu kuma?" Ta faɗa a zucci tare da juyawa ta shiga kitchen ta haɗo masa duk abinda tasan zashi buƙata ta nufi saman tayi knowking yabata izinin shiga yana zaune a parlourn nasa daga shi sai boxes ko arziƙin riga bashida sai suma da tayima ƙirjinsa riga tayi saurin ɗauke idonta cike da faduwar gaba ta aje kayan jikinta na rawa ta juya zata fita yace “Kharimatuh" tsayawa tayi ba tare data juyoba yana numfashi yace.
“Dole takunki ya canza ki kula da kanki sosai kuma kiyi hƙr da duk abinda ka iya faɗowa rayuwarki a wannan lokacin ki sani keɗin ba Kharimatun da bace yanzun akwai wani gingimemen nauyi akanki wanda idan kikayi wasarairai dashi tabbas Ubangiji ka iya azabtar dake da haƙƙinsa ba kowanne irin nauyi aka ɗora miki ba face igiyar aure......."
A mugun firgice kuma a kiɗime ta juyo jikinta da bakinta na ɓari tace “au....aure...." Murmushi yayi mata yace “Yeah aure Kharimatu tabbas yau cikin iko na Ubangiji kin tabbata matar Barrister Aliyu Ma'aruf Gusau......" Batasan sanda ƙafafunta suka zubar da ita a tsakiyar ɗakin ba cikin sarƙewar Harshe take furta “Innanillahi wa Inna ilaihirraji'un" kasa sake furta kowacce kalma tayi saboda tsabar birgici da tashin hankali inda shikuma yaja butar coffee ɗinsa ya tsiyaya yakai bakinsa ya lumshe idanunsa ya sake kurɓa sannan ya sauke yace “tabbas kamar yanda abin ya daki zuciyarki ya daki zuciyar kowa ma daya sani musamman Hajiyata da Mama da ƙanne na bansan lkcn da hakan ta faru ba bansan meye ya janyo ba nidai a daren jiya naje na sanar da Granny yanda mukayi dake domin nasan itace kaɗai zata goyamin baya sannan zatasa kowa taga dama yayi ko baiyi niyya ba bayan na taho a daren ta shigar da mgnr ga Dad so shima baija ba yaji daɗi sosai yace idan an sanar da Mama sai aje a nemamin aurenkin.
Aikam a lkcn Granny ta kira mama da Hajiyata ta sanar dasu dukkansu sunso suyi tsalle wai bazai yuwu Salmah ta raineki kuma ki aure mata miji ba zaman bazai taɓa daɗi ba saida Granny ta hau kan Hajiya sannan ta hƙr tace itafa ba ƙinki takeyi ba kawai dai tana jiye miki abinda kaje yazo ne, Itako Mama Yabi ƙin amincewa tayi saida taga ran Granny ya ɓaci sannan ta aminta so da safennan Dad ya kirani yace nazo nakai Mama Guru sanda naje hatta tafi sai yace muje nida Baba Labaran da Nazeer dashi haka muka tafi bansan meye za'ayi ba saida mukaje suke faɗamin an sanar da kakanki ne a daren jiya yace azo da sadaki da kuɗin turare al'ada dai taku ta barebari zai ɗaura aure gobe.
Wannsn ne ya kawo aka ɗaura aure na dake a yau Kharimatu....."
Kuka ta rushe dashi me gunji cikin kukan take cewa “nikam banyi marhabun da wannan auren ba wannan wanne irin rashin yanci ne wlh ban yarda ba ban amince ba banason auren nan don Allah Daddy Farooq ka rufamin asiri kada Aunty Salma taji ta kasheni wlh taci alwashin duk matar data auri mijinta saita kasheta a gabana tasha furta wannan kalmar meye yasa Ni zan jefa kaina......
*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?
~Paid book~
Oum Hairan
Free 13-14
_promo ya sauka saura kwana biyu rak👌🏻💃🏼_ _Littafaina biyu da nakeyi yanzu haka YAFI ZAMAN AURE da ME YA JAMIN? A baya regular na kowanne 300 ne VIP 600 so yanzu abun ya canza idan ki/ka nason duka biyun regular zakiyi subscribe da ₦400 ne VIP kuma duka biyun zaki biya ₦700 ne wannan ya faru ne sakamakon wani dalili wanda garabasar zata ƙare daga ashirin ga watannan ne so ku hanzarta biyan naku maimakon ₦900 vip 2 books ya koma ₦700 regular 2 books ya koma ₦400 tabbas sai me rabo, saura kwana biyu rak👌🏻💃🏼._
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafai ta hanyar biyan kuɗinku ta 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241_
_Ƴan Niger kuyi mgn ta wannan number domin biyan naku 94775574_
_____________________________
*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?
~Paid book~
Oum Hairan
Free 15-16
_promo ya sauka saura kwana ɗaya rak👌🏻💃🏼_ _Littafaina biyu da nakeyi yanzu haka YAFI ZAMAN AURE da ME YA JAMIN? A baya regular na kowanne 300 ne VIP 600 so yanzu abun ya canza idan ki/ka nason duka biyun regular zakiyi subscribe da ₦400 ne VIP kuma duka biyun zaki biya ₦700 ne wannan ya faru ne sakamakon wani dalili wanda garabasar zata ƙare daga ashirin ga watannan ne so ku hanzarta biyan naku maimakon ₦900 vip 2 books ya koma ₦700 regular 2 books ya koma ₦400 tabbas sai me rabo, saura kwana ɗaya rak👌🏻💃🏼._
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafai ta hanyar biyan kuɗinku ta 0255526235 Gtbank ko kati MTN