Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 3
bayan nan bata sake cewa, komai ba sai dayar ta amsa da cewa, "Ina mamaki sosai gaskiya da al'amuran mutanen makarantar nan gaba daya fa. Har yanzu taslim din batace komai ba, tana zaune tana latsa wata faskekiyar waya dake dake hannunta, akwai alamar zatayi magana amma kuma abinda take son fada din kamar zai mata wahalar fadi. Muttaka A HassanBAKUWAR DARE SHA BAKWAI. Batayi maganar ba kamar yadda dama nima nayi tsammanin ba zatace komai ðin ba. Daga haka har motar tazo daidai inda take aje dukkan daliban. Ina fitowa na samu gindin wata itaciya nayi tsaye ina jiran fitowarsu, lokaci daya suka fito daga motar suna rike da hannuwan juna, fuskar taslim din da niqab dayar kuma fuskarta bude, wannan yasa naji damuwa ta taru ta tsaya man ga zuciya lokaci daya. Na farko dai naso ganin fuskarta, saboda koba komai idan muka hadu yau da daddare zan tantance waccan taslim din, da kuma wannan taslim din, wata kila na samu wani banbanci a tsakaninsu. Naji zuciyata ta fara tunanin tafiya na bisu koba komai wata kila na gano wani abu game da'ita. Banyi wasa da wannan damar ba nabi bayansu sa'adda suke tafe suna arerewa suna wasa da dariya, fuskokinsu cike da farin ciki, har yanzu suna riqe da hannuwan junansu, kana ganinsu kaga kawayen da suke son junansu. Na biyosu da sauri ina hadawa da gudu-gudu sauri-sauri dan na cin masu, "Sannunku dai". Na fada sa'adda nakai gab! Dasu kamar zan bangaje daya daga cikinsu. "Yauwa sannu dai malam" dayar ta fada tana dubana. Yayinda taslim din tayi gaba bata ma tsaya jin abinda zamu ce ba, bata kuma ce komai ba. ganin tayi gaba yasa dayar ta dube ta tace, "Ya zaki tafi taslim?". Bata ce mata komai ba illa tafiyarta da taci gaba dayi bata ko kara juyowa wajanmu ba". Muka gaisa da dayar sama-sama yayinda tace man suna sauri zasu shiga darasi yanzu, amma idan aka fito zamu hadu". Nayi mata godiya ganin ta damu dani,alhalin a zuciyata ba wajanta nazo ba, amma nasan koba komai zansan wani abu game da wannan taslim din ta dalilinta. Nayi sauri nufar namu ajin nasan yanzu malaminmu ya shigo ajin, dan kuwa general ne zamuyi yau. Na zauna kenan ina sauraren darasin malamin na hango su can kasa, Zaune wajan mata suna bude litattafansu ashe muna haduwa wajan general dasu na fada ina dubansu cikin mamaki. Har yanzu tana sanye da niqab dinta kamar sabuwar malamar addini, dayar ta tattara hankalinta wajan duba wasu tarin "hand out" dake gefensu tana dubawa. Yayinda taslim din take zaune tana duban malamin da yake mana darasin, tamkar ita kadai ce ake koya mawa saboda tsananin natsuwar da tayi tana sauraren darasin. Kamal Muhammad Lawal DambuBAKUWAR DARE @Zaidu Ibrahim Barmo ~SHA TAKWAS~ Malamin ya dubemu gaba daya sa'annan yaje fo tambaya yana kallon dukkan daliban dake cikin ajin daya bayan daya. Yaya farkon halittar dan'adam take?, itace tambayar da yayi yana dubanmu, an kwashe sama da mintuna uku zuwa hudu babu wanda ya bada amsar tambayar, illa dai-daiku dake bada amsar amma ba daidai ba, yawanci cikinsu irin 'yan iskan daliban nan ne dake abu dan ayi dariya, so wannan ba wani abin mamaki bane ga daliban dake rayuwa a jami'a koba komai makarance da ta hada mutane kala-kala har iskokai ba zaka rasa ba, balantana mutane da sukazo daga jahohin kasar nan mabanbanta. "Ba zaku iya bane?" malamin ya tambaya yana dubanmu lokaci daya kuma yana niyyar tattara litattafansa ya fita. Madadin su bashi amsar wadanda suka sani sai suka fake da cewa, "time up sir". Ma'ana lokacin fitarsa yayi, yayi tsaye yana duban daliban, lokacin ne ajin yayi shiru tamkar mutuwa ta gifta. Can na hangota ta miqe da niqab dinta har yanzu tana masu bayanin abinda malamin ya tambaya. Tayi bayani sosai akan farkon halittar dan'adam, duk wanda yake cikin ajin ya gamsu da bayanan da tayi, tayi maganganunta cikin natsuwa yadda za'a gane sosai. Ta gama bayanin malamin yana mata tafi shi kanshi abin ya burgeshi sosai matuka, yanayin fuskarshi ne kawai zai nuna hakan. Ya dubi tarin jama'ar dake cikin ajin yace, "Kun bani kunya wallahi banga amfanin tarin mazan nan ba, yana nuna inda muke zaune, ko baku karatun addini ne?. Kafin kowa yace komai ya dora da cewa, "Abin kunya 'ya mace guda daya tayi bayanin da maza sama da dari biyu suka kasa yi, inajin daga yau na gama daukarku darasina. Ya fita da tarin litattafan dake hannunsa ransa a bace. Dukkan daliban suka miqe sukayo waje wadansu suka tafi dakunan baccinsu, wadansu suka nufi wasu wajajen daban, yayinda wasu sukayi zaune basu fita daga ajin ba. Sa'adda na fito na dinga wurga ido ko zan ganta amma shiru banga wulginta ba. Wannan yasa na nufi "School bus" da sauri da naga tana niyyar tashi. ** *** *** **** Lokaci daya matasan dake kofar gidanmu sukayo kaina sa'adda na karaso kofar gidan. Fuskokinsu dauke da fara'a da alama duk yadda za'ai abin arziki ya kawo su, sukayi man sallama muka gaisa sannan dayan ya gabatar man da kansa da cewa, shi bako ne daga nijar an bashi sako wajena. "Daga wajan wa?" na tambayeshi ina dubanshi fuskata dauke da alamomin tambaya. Waccan dayan yayi murmushi yace, ba ko gaisuwa abokina. Na sha'afa da gaisuwar sakamakon gajiya dake tattare dani, da kuma maganar da suka tarbeni da'ita. Dole ne inji ba'asin wanda ya aiko su wajena kafin mu gaisa. "Ku shigo daga ciki" Sa'adda nake kokarin bude shagona na fada. Suka taho tare kamar suna jira, bayan sun zauna mun gaisa ne nake basu hakurin rashin gaisuwar da banyi masu da farko ba,sakamakon dawowa da nayi a gajiye tun safe ina makaranta. "Ba komai wallahi ba damuwa" suka fada tare su duka biyun. "Munzo nan garin ne wajan wani aiki ga sako nan daga bintu ta nijer tace a kawo maka, wannan dayan daka gani yayanta ne". "Bintu bintu bintu!!" Na dinga maimaita sunan ina so in tuno inda na santa. "Oh! Bintu wadda muke yanar gizo da'ita? "Eh itace" dayan yayi saurin amsawa yana miqo man takardar hannunsa. "Gashi tace a baka zata shigo nijeriya nan da wata daya wajan wani biki da za'ayi". Suka mike tare ina dubansu, "Sauri muke sai wani lokacin idan Allah ya sake hadamu suka fada suna niyyar fita daga dakin. Khadeeja Almustapha An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3