Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
yawa. Kamar ana jiran in hau naga sallama da bakuwar lamba daga kasar nijer, wannan yasa na gane lallai ba daga nan gida nijeriya bane, makwaftanmu ne nijer. Anyi rubutu daro-daro kamar haka "Assalamu Alaikum daga masoyiyarka" Nayi dariya ina duban lambar kamar bazan mai da ba, ganin wadda tayiman sallamar bata sama, kuma dai na daure na maida sallamar da cewa, "Amin wa alaikis salam 'yar uwa". Tunda tace man masoyi bai kamata nima na biye mata nace mata masoyiya ba,dalilina kuwa shine, ban san ko wacece ba. Dan haka na maida mata da kalmar 'yar uwa, nasan koba komai zataji daðin kalmar zata kuma yi maraba da'ita. "Ya gida ya aiki ya cakudaddun al'amuran dake faruwa dakai kwana biyu" Shine sakon da naga an maido man da sauri sa'adda na tura tawa amsar da 'yan mintunan da basu wuce uku zuwa hudu ba. Wannan ya tabbatar man da cewa tana "online" kenan ta dai koma "offline" ne. Na shanye kamar banji komai a raina ba na sake rubuta mata sakon kar ta kwana akan cewa, "cakudaddun al'amura kuma a ina?". Ina gama rubutawa na maida sannan na bude hoton data ðora. "HAFIZ" Naga an rubuta da manyan baki ga wani bakin hoto, anyi rubutun da launin kala fara, ga bakin waje marar zanen komai. "Dankari!. Na fada a fili ina duban na'urar sadarwar tawa sa'adda naga ta takarkare tana faman rubutu da alama yanzun nan zata mai do man amsa kamar yadda nake tsammani. "Nasan ko yanzu kana fargaba amma a sannu zaka gane komai, kuma ka fahimci komai". "Ko kece taslim?" Na mai da mata amsa ban lura da sakon ta ba, sai da na lura kwarai sai naga ashe ta turo man sako sa'adda nake kan yi mata 'typing'. "bani bace" Kawai aka rubuta sannan aka dire daga saman yanar gizon, ta 6ace kenan na fada a fili cikie da tsantsar mamaki, yanzun ma kamar bazan mai da ba kuma dai na sake rubuta mata cewa, "Duk yadda za'ai kuna da alaqa da taslim ðin, ko kece kawarta da take bani labarin ina burgeta?". Na tura sakon nasan dai amsar ba yanzu ba, ina turawa na jawo murfin kwamfutar zan kashe kenan sai ga sakon ta kamar haka "A'a sam babu hada komai ba wai kare da gudun layya". Nayi jugum! Kafin na sake rubuta mata cewa, "Amma tayaya kika san wasu abubuwa dake faruwa dani, alhalin daga ni sai zuciya ta". Na mai da mata amsar kai tsaye yanzun ma bata sama, na lura koma wacece kamar tsuntsuwa take, yanzu tana nan anjima bata nan. Khadeeja AlmustaphaßAKUWAR DARE TARA "Bani bace taslim ban ma ta6a jin mai wannan sunan ba tunda nake a duniya". Shine sakon daya shigo cikin kwafutar tawa sa'adda nake kokarin rufe ta da niyar kwantawa dan kuwa zuwa yanzu bacci ne fal a idanuna, amma duk da haka sai da na mai da mata da cewa, "Na dauka kece ai". Na tura sannan na rufe kwafuta din na kwanta, ban wuce minti uku zuwa hudu ba bacci yayi awon gaba dani. Yau ma kamar jiya sai da nayi mafarkinta a baccina, wannan kuwa bai rasa nasaba da tunaninta dana dauka na sa a zuciyata. Bayan ganinta dana fara yi inajin tsoro, yanzu har so nake na ganta kusa dani mu dinga labarin duniya tana dariya, cikin abubuwan da suka fidda man shakkunta daga cikin raina hada murmushinta,wanda shine abu na farko dake burge ni game da'ita ya kuma sani saurin tuno ta. Tunda nake ganin 'yam mata ban taba ganin wadda takai ta iya murmushi ba, in ba dan da dare nake ganinta ba zan iya cewa ban taba ganin wadda takai ta iya ado ba, duk da cewa manyan riguna take sawa amma sunayi mata kyau sosai. Washe gari tunda safe na tashi nayi wanka na nufi makaranta sakamakon ina da darasin safe, dan haka na nufi inda nake samun motar makaranta kullum dan tafiya. Sa'adda na karasa wajan tuni motar ta cika ana neman mutum daya ko biyu, dan haka na hanzarta ganin motar zata tashi, na nemi kujerar baya da ta rage na zauna. Na bude dan littafin dake hannuna ina duba wasu abubuwa da mukai makarantar kafin muje hutun karshen mako. "Taslim kin gama assignment din ranar juma'a kuwa, dan kinsan yau fa litinin yace zai ansa". Naji muryar wata mace dake gefena ta faða tana duban ta kusa da'ita. Da sauri nakai duba wajan dan ganin wace taslim ðin ce, itama wannan tana sanye da doguwar riga ruwan madara, ta sa 'yar fingilallar hijabi iya kafadu. Tsawonta bazai wuce taslim din dana sani ba, sai dai ba zan iya shaida fuskarta kai tsaye ba, wannan farace mai matsaikaicin jiki, taslim din dana sani ban sani ba baka ce ko fara, ban kuma taba lura da yanayin jikinta ba balle nagane yadda take. Ta juyo da fara'arta tana baiwa waccan data yi mata tambayar amsa "Na kammala tun jiya ai dan ma wani uzuri ya dan tsaidani". Nayi kasa'ke ina dubanta cike da tsantsar mamaki sai kuma naji dayar tace, "Anti binta ta nijer zata zo bikin gidanmu sati mai zuwa". Naji gabana ya faði dam kodai wannan ce bakuwata taslim, naji sunan iri daya, na kuma ji suna labarin nijer. Ban ankara ba sai da naji kowa yana sauka daga motar lokacin dana sauko nayi niyyar in bibiyi wannan taslim din, amma har ta shige wani sashi na makarantar lokacin ne na dinga zare-zaren idanu dan hangota. Ita da kawar tata ba wadda nagani ma'ana duk inda suke suna tare, sauran dalibai dake cikin motar na juya ina kallo dan ganin ko tana nan bata fito ba, amma wayam! Bata nan. Na nufi ajin da zamuyi darasin yau zuciyata cike da tunanin lallai duk yadda za'ai sai na sake ganin taslim ðin nan ko nan gaba na kuwa bibiyi rayuwarta dan banbance tsakanin wannan taslim ðin da waccan. Hafiz Koza AdamußAKUWAR DARE GOMA Ban fita daga makaranta ba sai wajajen karfe hudu na yamma, na dawo gida jikina cike da kasala da gajiya, ga yunwa inaji da sauri na nufi wajan mahaifiyata dan jin ko ta aje man abincin rana. Bayan na anso abincin ne na shiga shagona na zauna ina cin abincin. Abubuwa dai da yawa gasu nan birjik rayuwa na ta ðebowa tana zubawa,naji wannan tunanin yazo man a rai ina duban tsohuwar katifata dake jingine tamkar an dasa ta wajan. Bayan kujiba-kujiba ta waje yanzu abun harya fito waje kenan?, na tambayi kaina ina nazarin wasu abubuwan. Taslim ta makaranta daban, binta ta nijer daban, ga kuma original din taslim din dake tayani hira da daddare. Akwai abubuwan nazari sosai, tsakanin mutanan nan da suke neman hanani tunanin abinda zanyi, da kuma hanani karatu. Dan kuwa duk karshen mako din nan babu karatun da nayi, hasalima ko littafi ban karanta ba. Bayan na gama nayi kwance saman katifar ina kallon silin dakin tamkar mai nazartar wani abu game da silin, sai yanzu na samu damar kallon saman dakina har nayi nazarin wasu abubuwa da dakin yayi, yayi datti, kayan kallona dake aje tamkar katon madubi suna nan birjik! Rabona da karewa dakin kallo irin wannan tun kafin bakuwata bata ziyarce ni ba. 12-00pm Yau ma kamar kullum nayi la6e ina jiran wucewarta, bari in dawo baya daku kadan daku nasan wasun ku zasu dinga mamakin cewa, ko babu aikin da nakeyi?. Wannan ba abin mamaki bane musamman idan kuka fidda lokacin makaranta dina, yawanci lokutana duk ina cinyesu ne a makarantar, wannan yasa bani da wata rikakkiyar sana'a da nakeyi yanzu. Har sha biyu da rabi bata wuce ba, wannan ya tabbatar man da cewa, mawuyaci ne idan zata wuce yau, to amma me zai hana wucewa ma?. Duk tsawon satittikan da nake ganinta bata ta6a fashin wucewa ba ko fashin lokaci. Ganin ba zata zo ba yasa ni kwantawa na jawo kwamfuta dita domin hawa yanar gizo da kuma fidda wani assignment da aka bani yau a makaranta. Ina bude data sakon bakuwar lambar nan ce ta jiya na fara cin karo da'ita, "Ban san wata taslim ba, ban kuma san wata mai wannan sunan ba kamar dai yadda na fada maka jiya". Ta maido man amsar tana wajan awa uku da turo sakon, "Na dauka 'yar uwarki ce ai". Na tura mata nima. Nan take naga ta fara kokarin mai do man da amsar "A'a". Shine kawai abinda ta rubuta, tun kafin in sake rubuta komai ta kara turo wani sakon kamar haka- "Akwai fa wata kullaliya mai wuyar kullewa da ganewa". Banyi mamaki ba nadai yi nazarin rubutun na wasu 'yan sakanni sa'annan na mai da mata da nawa rubutun, kamar abin bai bani mamaki ba nace- "Kulalliya kuma ta mi?" "Ta wasu al'amura kalilan" "kenan ma" "Eh kai dai ka dinga nazari" "Bayan wanda nakeyi kuma" "Eh ya kamata ka kara gaskiya" "Karin amfanin me zai yi man?" "Zai kara saka sanin abubuwan rayuwa wadanda suke fuskantarka baka sani ba, sai da safe". Daga nan ta sauka ban samu damar kara ce mata komai ba sakamakon barcin da naji nima yana shirin fin karfin idanuwana. Yau dai kam taslim batazo ba ban kuma san abinda ya hanata zuwa ba. Kamal Y. Iyantama ßAKUWAR DARE SHA DAYA Ba karamin abu bane zai hanata zuwa, amma dai duk da haka yau din bata zo ba, na tabbata daren gobe zamu hadu da'ita. Washe gari banje makaranta da safe ba saboda ranar gaba daya banda lakca. Wannan yasa tun safe ina zaune gida ba inda naje sai ma abokina Aliyu fafa da ya kawo man ziyara. Mun dade muna labari dashi inda muka dinga ta6o al'amuran rayuwa wadanda suka faru damu tun bayan rabuwarmu. Abokina ne sosai rabonmu dashi tun sa'adda muka gama sakandiri shi ya tafi neman kudi birnin ikko, ni kuma na zauna a gida ina karatu kuma ina buga-buga. "Yanzu wace sana'a kake a ikko?" Na tambayeshi sa'adda ya jawo kwamfuta dita dake gefe yana niyyar kunnawa. "Kasan ikko yanzu sai dai buga-bugar babu wata sana'a da zaka ce ka tsaya gareta ita kadai, in hakane zaka dade 'yan canji basu shigo ka ba". Ya gama fadin maganar sa'adda yake kokarin shiga yanar gizo ga kwamfuta din. "Kaine ai da son duniya aliyu, nace maka ka tsaya kayi karatunka, amma sauran abokanka sun zigeka sun hure maka kunnuwa ban san yadda zanyi dakai ba". Nayi dariya ina kallonshi sa'adda na gama maganar ina jiran abinda zai fada. "Kai karatun nan fa na boko haka yake, bawai son shi ne bane banayi ba a'a ka gama karatun ma aikin yi ya gagareka, wani dan gidan mai kudi na can gida kwance za'a sai da mashi takardun karatunka, shikenan wahalarka ta tashi banza, ga kuma rashin adalci irin na manyanmu in kai ba dan gidan wani babba bane mawuyaci ne ma ko kallon takardunka ayi". Lokacin baya wani ya ta6a ceman yaga abokina aliyu yana shaye-shaye a ikko, kamar zan gasgata na kuma karyata maganar, na dauka maganganun da zai yi man yanzu irin na mashaya ne, amma sai na samu sabanin hakan, Akwai gaskiya a cikin maganganunshi, amma fa ba duka ba. Ganin na rasa amsar da zan sake jefo mashi yasa nace mashi, "Amma dai idan kayi karatun ai zaka ga amfaninshi ko gaba, ka samu ko difloma ce kayi Aliyu tunda dai takardunka sunyi kyau yadda ake so". Na fadi mashi ina dubanshi "Ashe kana da 'yan nijar a soshiyal midiya?" Aliyun ya fada yana dubana. "Meka gani?" Kai tsaye ya bani amsa da cewa, "Ai ina bude kwamfuta din sakon da ya fara shigowa kenan da lambar nijar". "Bani in gani yau kuma da wace tazo" Na fada ina kallon Aliyu. "Yau bakuda lakca kenan sai da yamma wata kila mu hadu dakin karatu idan kazo, ka gaida man abokinka aliyu". Shine sakon da ta turo, wata kyakkyawar ajiyar zuciya na aje ina duban aliyu. Khadeeja AlmustaphaßAKUWAR DARE SHA BIYU Mamaki tsantsa ne a fuskar aliyu sa'adda yaga rubutun da'aka rubuto, saboda ni kaina bansan da zuwan aliyun ba sai da na ganshi. "Wacece wannan?" Aliyu ya tambayeni yana dubana fuskarsa cike da tsantsar mamaki da al'ajabin abin. "Ina 'yar nijar tasan da zuwana, kai bama ita ba inajin ko kai baka san da zuwana ba sai da kaganni". Aliyu ya fada tun kafin na sake cewa komai, kallo daya nayiwa fuskarsa na hango tsantsar mamakin da yayi. Nan na kwashe labarin dukkan abinda yake faruwa dani na fadi wa aliyu ban boye masa komai ba, ban taba boye masa wani al'amari game dani ba, nasha kin fadin wani abu daya shafeni a gidanmu amma in fadi wa aliyu. Cikin labarin na tattaro har labarin bakuwata tun daga ranar da muka fara haduwa har zuwa rabuwarmu ta kwana dayan nan. "Abokina bakayi gamo kuwa ba?". Ya tambayeni cike da mamakin al'amarin yana dubana, akwai alamar razana kadan a fuskarsa. "Ni kaina ban sani ba, wata kila gamon nayi rayuwa mai jajibe-jajibe ta kwaso wani abin ta lika man". "Kai da kake da hanyar rabuwa da'ita kawai kabar yadda kuna haduwa da daddaren mana". Yace, yana kallona akwai alamar zai iya furta wata maganar bayan wannan da yayi. "Sunanta taslim, kuna haduwa da dare, kaga wata taslim din kuma a makaranta, an maka magana da lambar nijar kuma kaji suna labarin nijar, karshe ka bari ta su6uce maka. Wannan ba karamin ganganci bane kayi hafiz, kamata yayi ka tsaya ka binciki rayuwarta sosai kaga da abinda tazo maka, kaga kai kanka bakada tabbacin mutum ce ko aljana?". Na daga kaina alamar hakane ina duban tarin takardun dake aje cikin dakin tamkar wani firofesa wanda yayi malanta ya gama. "Taslim" Naji aliyu ya furta sunan yana dubana, cike da mamaki ga fuskarsa har yanzu. "Zan tayaka wannan aikin inajin ba naka bane kai kadai, dan kuwa fuskantarshi kai kadai babban kalubale ne gareka" Aliyu ya gama maganar fuskarsa cike da karsashi da kwanjin iyawa, zai iya zuciyata ta bani sa'adda na kalleshi sosai, ba alamar tsoro ko fargaba a fuskarshi, ba mamaki wata kila har zuciyarshi haka abun yake. "Na dawo nan da zama har sai mun ga karshen al'amarin nan hafiz" Ya sake fada yana dafa kafaduna cikin azama da ðaura niyya. "Zaka iya abokina?" Na furta a hankali ina dubanshi kamar bani son wani yaji maganar. "Zan iya" ya fada har yanzu kalamansa da kwanji na iyawa da kuma tabbaci. Naji dadi a raina koba komai wata kila aliyu zai zama wani jigo a rayuwata da zai taimakeni nan gaba ko yanzu Abdulhamid Muhammad Sani MatazußAKUWAR DARE SHA UKU Koba komai zuwan aliyu yayi man dadin dana dade ban ji ba, na farko dai sanadiyyarshi na koma karatu koda ban so ba, dan kuwa koda nayi barci sai yazo ya tadani ya tursasani nayi karatun dan dole. Wannan abun yayi man dadi sosai a raina musamman da yanzu jarabawar karshen zangon karatu ke fuskantomu. Idan dare yayi zamu nufi wajen yawanmu ba zamu dawo ba sai wajan karfe daya na dare ko sha biyu, manufar yin hakan ga Aliyu dan kar in dinga ganin baquwata taslim tana kara sani rudani, dan kuwa yasan ba karamin rusa man karatu zatayi ba, yanzu ma ya aka kare bisa ga nan gaba. Har yanzu ina son ganin taslim a raina amma bani fadi gaban aliyu, Zuciyata na bani akwai wasu al'amura na musamman game da rayuwarta, koda ba mutum bace taslim zata kasance mai tausayi ba azzaluma ba. Naji bakina yana kwararo mata kalaman yabawa da shauqi, wadanda ni kaina banyi tsammanin ina da su adane cikin bakin nawa ba. Babban kuskure ne zanyi in dinga tunanin irin wannan lokacin, amma sam! Tunaninta kullum kara dawowa man yake a zuciya sabo dal! . Na san da wannan dama dole ta kasance, dan kuwa ba abin mamaki bane, tunanin taslim dole ya zamar man wani abu na musamman dake shirin fin karatuna muhimmanci. Da'ace ban taba ganinta ba, da yanzu duk wadannan al'amuran basu faru ba, da yanzu ba'a taba labarin wata taslim ba, ni kaina da yanzu ina nan hankali kwance ba damuwar komai a raina, ina tunanin jarabawa da kuma sakamakon da zai fito idan an kammala jarabawar. To amma da yake rayuwa ce, mai kwashe-kwashe ta kara kwasoni ta kawowa taslim ta zuba, tamkar dai kwallo a raga sai yadda 'yan wasa sukayi da'ita. Aliyu ya zama wani jigo sosai a rayuwata kamar yadda na fada dazu a baya, duk yadda yaga na fara damuwa yanzun nan zaka jishi ya dauko man labarin 'yan film din indiya yana bani ko kuma labarin jarumta irin wanda ya son ina so fiye da komai. Koda ban fadi maku a baya ba ya zama dole na fadi maku yanzu, duk duniyar nan babu abinda nake son ji ko gani irin labarun jarumta, musamman ma wanda akwai tausayi cikin ransu Khadeeja AlmustaphaßAKUWAR DARE SHA HUDU A hankali kwanaki sukai ta wucewa rayuwa na tafiya ga wanda ya hankalta, an kwashe fiye da mako daya ban sake ganin taslim ba, hatta taslim din makaranta ban sake haduwa da'ita ba. Hatta 'yar nijar dake yi man magana a yanar gizo ta bari wannan na nufin sun fita daga rayuwata kenan?. Na tambayi kaina sa'adda nake kwance wajan karfe sha daya da rabi na dare ina tunanin duniya. Jarabawar dake fuskantomu itace babban abinda ke cikin raina yanzu fiye da komai, naji dadin yadda na rage tunanin taslim a zuciyata, koba komai hakan zai bani damar yin karatuna hankali kwance ba kamar can baya ba. Idan taslim bata fado rayuwata ba kuma, da duk wannan labarin ma bai faru ba, hasalima kila da banga amfanin saqa maku wannan labarin ba. Kamar ance in dago kaina na leqo ta 'yar hudar dana saba leqenta idan zata wuce, na hango ta tana fuskanto wajan tana tafiya a hankali kamar tana tausayin ka'sa tana sanye da wata doguwar rigar kamar kullum, amma wannan ruwan ja ce sai wasu dogayen takalmi masu tsini da ta saka, hasken wutar nefa ya haskake fuskarta sosai yadda har na nesa na iya hangota, amma ta dade fuskarta da niqab duk tsiyar mutum ba zai iya ganin fuskar tata ba. Na dinga tashin aliyu daga barci akan ya tashi ya ga taslim, amma ina bacci ya riga yaci karfinshi duk inna tadashi sai ya koma ya kwanta kamar sabuwar gawa. Naso ace aliyu ya tashi muje wajan taslim tare koba komai wata qila ya fini kwarjinin magana wajanta. Haka na fita nasan dai dole sai ta tsaya inda ta saba tsayawa kafin ta wuce daga layin gaba daya. Tana tsaye wajan dai kamar yadda nayi tsammani, iskan dake kaðawa yana faman wasa da gashin kanta daga wannan sashen zuwa wannan. Fuskarta ta ka'ra annuri sosai sakamakon murmushi da naga tana yi man, "Kin hadu sosai" na fada tun kafin na ida karasowa kusa da'ita hasken zobunan dake 'yan yatsunta suka haske idanuna lokaci daya. Haskensu tamkar 'yar karamar fitilar haskawa, har yanzu tana nan tsaye wajan tana kallona tana murmushi irin na tausayi ko jimami. Zuciyata cike da tambayoyi masu yawa gareta, ina fatan Allah yasa dai kar sai mun fara hira tace man lokacin tafiyarta yayi. "Sannu malam hafiz" ta fada sa'adda na kawo gaf da'ita. "Yauwa sannu taslim" Nima na fada ina dubanta. "ba wata kara" ta fada jin na fadi sunanta kai tsaye. Nayi murmushi sa'annan nace, "Na dauka iyakar sunan kenan ai ban zata akwai wani kari gaba ba". Na gama maganar ina dariya ina dubanta. Ban sani ba yau sam! Banajin wata shakka game da'ita, tunda ina daga ido ina dubanta, "Sunan kenan fa ko ina" Naji ta fada a hankali kamar bata son wani yaji maganar, cikin tausasawa. "Kinsan wata taslim a makarantarmu dan Allah?" Na jefo mata tambayar ina dubanta?. "Ban san ta ba" Naji ta fada kamar tana jiran maganar sannan ta hade rai tana duban wani sashin na wajan. "Kamar baki so tambayar ba ko?" na fada mata ina dubanta duk da bani take kallo ba. Sada Bin Suleiman UsmanßAKUWAR DARE SHA BIYAR "Ban san wata taslim ba duk duniyar nan ba in ba ni kadai ba". Ta fada tana duban daya sashin na inda muke kamar tana nazartar wani abu. "Na dauka kin santa ma ai?". Na sake fada ina dukar da kaina kasa. "A'a gaskiya ban santa ba ni hasalima ban san ko wacece ba". Tun kafin na sake cewa komai taci gaba da cewa, "Kana mamakin ni mutum ce ko aljana ko?" Na juyo da tsantsar mamakin maganarta ina dubanta, koba komai anzo gabar da nake son ji game da ita da dukkan rayuwarta. "Hakane" Kawai na furta bansan ma na fadi hakan ba saboda mamaki, sai daga baya nake tambayar kaina wai maganar waje nayi ta ko cikin zuciya?. "Hafiz kenan" ta fada a hankali tana dubana har yanzu fuskarta da alamar bacin rai ba kamar sa'adda tazo da farko ba. "Karfe nawa?" Na duba agogon dake hannuna karfe sha biyu da mintuna arba'in har da hudu. "Zan tafi hafiz, amma haduwarmu ta gaba zaka san taslim da dukkan wani abu daya shige maka duhu game da taslim, wata kila hakan zai zamo wata warwara gareka". Tun kafin nace komai ta yi tafiyarta bata ko juyo inda nake ba. Duk lokacin da muke tare idan tace zata tafi, tofa shikenan ba zan sake wata maganar ba, dan kuwa da tace zata tafi ba zata kara tsayawa saurarar wata magana daga gareni ba zatayi tafiyarta. Sa'adda na shigo cikin shagona na tarar da aliyu yana ta barcinsa harda munshari bai san abinda yake faruwa ba, wai nan shine wanda zai taimakaman game da lamuran taslim. Gata nan tazo tayi tafiyarta baka san ma tazo ba na fada ina dubanshi sa'adda yake barcin kamar zan makeshi saboda wani haushin shi da naji ya diro man lokaci daya. A hankali ya fara mirtsike idanuwansa daga barcin sakamakon karar bidiyo da na kunna. "Baka kwanta ba hafiz?" ya fada sa'adda yake kokarin mikewa daga kwanciyar da yayi. "Tazo har ta tafi". Kawai na fada ina kokarin canza wani kaset daga bidiyon. Ya mike da sauri daga kwancen da yake yana dubana sosai "Tsakaninka da Allah wai hafiz?". "Karya zan maka ne?" nima na fada ina dubanshi har yanzu da haushinshi cikin raina. "Ya kuka kare yau?" ya tambaya yana dubana. Na dubeshi nace, "Nan fa na dinga tada ka daga baccin nan amma kaki tashi sai yanzu zaka dinga tambaya ta abinda ya faru?". Ganin yayi shiru yasa naci gaba da cewa, "Tace man haduwarmu ta gaba zata bani labarin rayuwarta gaba daya, zata fada man wacece ita da kuma dukkan wani abu wanda ya shige man duhu game da al'amuranta. "Yaushe kukai da'ita zata dawo?" Aliyu ya fada cikin kagara yana duban kasasuwan dana aje gabana. "Zuwanta ba wai tabbas gareshi ba, kamar yadda na shafe kwanaki ina tsimayin zuwanta amma bata zo ba, amma nasan duk sadda muka hadun zata bani labarin rayuwar tata kamar yadda tayi man alkawari. Kamal Muhammad Lawal Dambu BAKUWAR DARE SHA SHIDDA Ba abin mamaki bane kuma ka ganta goben tazo wucewa. Na fadi ma aliyu sa'adda bacci ya fara fisgar idanuwana ina lumshe ido a hankali. "Allah ya kaimu idan tazo goben tare dani za'a kar'kare komai". Ya fada cikin kwanji da nuna iyawa da kuma tabbaci, da yawa salon maganar aliyu yana yinta ne cikin tsantsar jarumta da kuma gwanancewa. "Sunana taslim" Naji sunanta ya fado man ga rai sa'adda mukayi haduwar farko da'ita, tana sanye da doguwar rigarta fuskarta dauke da tsantsar damuwa, ba karamin abin mamaki bane da kuma wawanci kaga mace karfe sha biyun dare tana tafiya, ka kuma biyota kana tambayarta inda zataje alhalin babu alamar tsorata a fuskarta. Wannan ne abinda ya fado man ga rai a dai-dai wannan lokacin har naji barci na shirin kauracewa idanuwana. Aliyu bai sake cewa komai ba, nima ban sake ce mashi wani abu ba, madadin shirun sai na shiga nazartar kalaman taslim a zuciyata tun daga haduwarmu ta farko yanzun da nake baku wannan labarin. "Alhaji babba" duk abubuwan mamakin da take fadaman kullum babu abinda yafi daure man kai, bisa ga maganar alhaji babba da ta taba kawoman, ko aljani ba kowa ne zakaji yana labarin alhaji babba ba, in ma suna labarin mutane kenan ma. Madadin haka sai ga taslim zake-zake tana bani labarin rayuwata gaba daya, har da labarin gidan alhaji babba. **** Washe gari tunda safe nayi saukon zuwa tarbar motar makaranta dan kuwa darasinmu tun karfe bakwai da rabi na safe ne yau. Dan haka ban tsaya cin komai gida ba na kwararo hanyar da muke tarbar motar makaranta. Sa'adda naje wajan fasinjoji sun cika ana neman mutum daya, dan haka ina hawa suka tada motar. "Taslim" Naji an kira sunan yau ma sa'adda kaina yake duqe ina karanta littafin da zamuyi bitarshi yau, da alama itama darasin safe sukeyi yau a ajin nasu. Nakai wajan minti daya zuwa biyu ban dago kaina ba ina nazarin sunan kafin na dago kaina na kara duban taslm din makaranta. "Baki ji yadda muka kwashe da malamin Ilmin kimiyya rannan ba?"?. Ta tsaya da maganar tana jiran taji abinda taslim din zata ce. Na dago kaina ina dubansu suna gabana, tsawon kujerun ba zai sani hango fuskokinsu ba, amma inajin muryoyinsu tamkar gabana sukeyin hirar. "Wani malami ne ya matsa man da naci nikuma, shiyasa naso a barni inyi karatuna a nijer can makarantar da'aka fara samar man da farko kafin wannan kwalejin". Wadda aka ambata da taslim itace tayi maganar,

Chapter 2 of 3