Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BAKUWAR DARE..... ©MrZaid™ *SADAUKARWA* Ga dukkan wadanda ibtila'in rayuwa ya taba fada masu 0️⃣1️⃣ Idan karfe sha biyun dare ta buga, duk inda hankalina yake yakan dawo gida. Koba komai ina son in tsaya daga zauren gidanmu in rika hango matashiyar dake giftawa ta gidan duk lokacin da karfe sha biyun dare ta buga. the Duk yadda nake jin bacci nakan dannewa zuciyata da tayi hakuri har sai sha biyun dare ta wuce kafin na kwanta baccin. Wata matashiya ce lamarinta ke daurin man kai, kullum ta kofar gidanmu take wucewa karfe sha biyun dare kamar yadda na fada a baya. Lallai ba fashi indai sha biyu tayi zanga wucewarta, tana sauri fuskarta dauke da tsantsar damuwa, bata ta6a wucewa ba kafin sha biyu, ko bayan sha biyun. Duk in zata wuce da takai kwanar karshe zata tsaya ta juyo kamar minti daya ko biyu tana kallon wajajen gidanmu sannan tayi gaba. Nasan dai bani take kallo ba, kamar yadda zuciyata ta sha faða man to taya ma za'ayi ta ganni?. Nida ke cikin gida kuma gidan rufe. Kamar kowace sha biyu yau ma na hakimce bakin zauren gidanmu ina jiran lokacin wucewarta. Kamar ance in dago idona na hango giftawar rabin jikinta ta wuce. Ma'anar kafarta daya har ta wuce saitin gidanmu, in banda rigarta da iska ke dauka, mawuyacin abune in ga giftawarta. Tayi tsaye in da ta saba tsayawa kafin ta shiga kwanar da takebi , madadin minti daya zuwa biyu sai gashi ta kwashe wajan mintuna goma tana tsaye. Zuciyata ta fara harbawa sakamakon hango hawaye da nayi a fuskarta, lallai yau rana ta 6aci kenan? Na tambayi kaina ina kara dubanta. Hasken farin watan daya mamaye gari ne, ya sani na kara ganinta sosai. Tabbas kuka takeyi, zuciyata ta fara tunanin bari in fita in taimaka mata. Wannan sharar fage ne 😉 In Labarin yasamu karbuwa Zan cigaba, Sh@r£ ✓ ßAKUWAR DARE (Rabon ayi) 0️⃣2️⃣ Ina nan tsaye ina dubanta har yanzu bata kauce daga inda take tsaye ba. Da'ace yau ne na saba ganinta tabbas zance wani ne take jira ya tafi yabar ta nan. Amma da yake ba yau na fara ganinta ba tabbas nasan babu wanda take jira akwai dai wani abu dake faruwa,wanda ba karamin al'amari bane. A ðan sanin da nayi mata kullum ba zata wuce mintuna biyu zuwa uku ba ta kauce daga kan wajan, amma abin mamaki har wajen mintuna sha biyar tana tsaye wajan, na lura da hakan ne sakamakon fitilar wayata dana haska naga rubutun lokaci ya fito man daro-daro karfe sha biyu da mintuna sha biyar. "Ka fita kaje wajanta kaji matsalarta wata kila ka taimake ta kaima wata rana Allah zai taimakeka". Naji wani bangare na zuciyata yana faða sa'adda na aza hannuna saman sakatar gidan, da niyyar buðewa cike da dukkan kuzari da kwanji. "Karka buðe, daga ganinta, ka sani koba mutum bace, wata kila irin mugayen nan ne masu jiran masu rabon tsautsayi ya kawo su kansu". Haka naji bangaren guda na zuciyata yana faða sa'adda nake kokarin janye hannuna daga niyyar buðe sakatar. Na sake lekowa a hankali kamar mai tsoron wani abu ina duban wajan, tana nan dai tsaye, amma ta ðan matsa daga inda take tsaye dazu. Akwai wata rana data ta6a wucewa na ayyana a raina cewa, sai na bita wata rana naga inda take zuwa koda kuwa bata san na biyo ta ba, amma da yake nasan duniyar nan abar tsoro ce sai na fidda wannan kudurin daga raina. "Kaje kayi taimako, macce ce zamanta a irin wannan lokacin waje yana da haðari sosai idan kanwarka ce ya zakaji?". Naji zuciyata ta kara shawarta ta akan na fita naje wajanta naji matsalarta. Ban san lokacin dana zare sakatar gidanmu ba na fito, na manta addu'a sam a raina, na tuna hakan ne sakamakon nasihar mahaifiyata kullum gareni "Ka rika addu'a a dukkan ayyukanka, koda neman aiki kake idan kana addu'a tabbas Allah zai dafa maka". Ban samu damar tsayawa addu'ar ba, sakamakon ganinta da nayi ta kara matsawa daga inda take tana dubana sakamakon ganina da tayi na fito daga gidan. Farin watan da ya haskaka gari ya haske mana fuskokinmu lokaci daya muka dubi juna, kallon cikin idon ta da nayyi ne yasa gabana, dukan Uku Uku, rass rass. Jiya Mun samu §haring 7 Hope yau musamu 14 ßAKUWAR DARE (Rabon ayi) ~DAYA~ Ina nan tsaye ina dubanta har yanzu bata kauce daga inda take tsaye ba. Da'ace yau ne na saba ganinta tabbas zance wani ne take jira ya tafi yabar ta nan. Amma da yake ba yau na fara ganinta ba tabbas nasan babu wanda take jira akwai dai wani abu dake faruwa,wanda ba karamin al'amari bane. A ðan sanin da nayi mata kullum ba zata wuce mintuna biyu zuwa uku ba ta kauce daga kan wajan, amma abin mamaki har wajen mintuna sha biyar tana tsaye wajan, na lura da hakan ne sakamakon fitilar wayata dana haska naga rubutun lokaci ya fito man daro-daro karfe sha biyu da mintuna sha biyar. "Ka fita kaje wajanta kaji matsalarta wata kila ka taimake ta kaima wata rana Allah zai taimakeka". Naji wani bangare na zuciyata yana faða sa'adda na aza hannuna saman sakatar gidan, da niyyar buðewa cike da dukkan kuzari da kwanji. "Karka buðe, daga ganinta ka sani koba mutum bace, wata kila irin mugayen nan ne masu jiran masu rabon tsautsayi ya kawo su kansu". Haka naji bangaren guda na zuciyata yana faða sa'adda nake kokarin janye hannuna daga niyyar buðe sakatar. Na sake lekowa a hankali kamar mai tsoron wani abu ina duban wajan, tana nan dai tsaye, amma ta ðan matsa daga inda take tsaye dazu. Akwai wata rana data ta6a wucewa na ayyana a raina cewa, sai na bita wata rana naga inda take zuwa koda kuwa bata san na biyo ta ba, amma da yake nasan duniyar nan abar tsoro ce sai na fidda wannan kudurin daga raina. "Kaje kayi taimako, macce ce zamanta a irin wannan lokacin waje yana da haðari sosai idan kanwarka ce ya zakaji?". Naji zuciyata ta kara shawarta ta akan na fita naje wajanta naji matsalarta. Ban san lokacin dana zare sakatar gidanmu ba na fito, na manta addu'a sam a raina, na tuna hakan ne sakamakon nasihar mahaifiyata kullum gareni "Ka rika addu'a a dukkan ayyukanka, koda neman aiki kake idan kana addu'a tabbas Allah zai dafa maka". Ban samu damar tsayawa addu'ar ba, sakamakon ganinta da nayi ta kara matsawa daga inda take tana dubana sakamakon ganina da tayi na fito daga gidan. Farin watan da ya haskaka gari ya haske mana fuskokinmu lokaci daya muka dubi juna. Khadeeja Almustapha BAKUWAR DARE Na Zaidu Ibrahim Barmo MrZaid UKU Ban san ina da irin wannan jarumtar ba a raina, sai da na ganni na fito daga cikin gidan ina dubanta. Tayi tsaye tana duban gefenta tamkar bata ganni ba. Kallon kallo kenan akuya da tsoron kura, na fada a zuciyata ina dubanta na kuma kasa karasawa kusa da'ita. Akwai fargaba sosai cikin zuciyata har yanzu, me ya fiddoni daga gida? Na tambayi kaina ina dubanta har yanzu. Ta juyo da fuskarta a hankali tana dubana, fuskarta da alamar tsantsar damuwa kamar yadda nake ganinta kullum. Har yanzu hasken farin wata na haska fuskokinmu ni da ita. Na daure sosai, zuciyata na tuna man irin tsautsayin da na sa kaina ko kuma zan sa kaina. Bata tafi ba tana tsaye wajan tana duban gefenta har yanzu, iskan dare dake kaðawa yana faman kaða doguwar rigarta, tamkar anyi iskan ne dan rigarta ita kaðai. Ta yafa ðan yalolon gyale, wanda nake tsammanin da kyar in ba kallabi bane lura da irin yadda gyalen yayi kama da tufafin da take sanye dasu sosai. Ban san sa'adda naji ina tafiya ina tunkarota ba cike da tsantsar jarumta, duk wata damuwa dake raina ta kauce, tamkar bani bane nake shakkar tunkararta. Sai da na kawo gaf da ita kamar zamuji numfashin juna sa'annan nayi tsaye ina jiran inji abinda zata furta, nasan dai duk yadda za'ai babu tsoro cikin zuciyarta, kamar yadda take shantake sha biyun dare tana biyo wannan hanyar lokacin da kafafu suka dauke. Ta juyo a hankali danjin tafiyar mutum a kusa da'ita tana dubana, idanuwanta sam babu alamar tsoro kamar yadda nayi tsammanin dama ba zataji tsoron ba. Ta fara kallona daga kafafuna kafin ta ðago dara-daran idanuwanta ta kalleni ga fuska. Akwai alamar mamakin ganina tsantsa a fuskarta, amma babu alamar tsorona sam a fuskarta. Idanuwanta wasu kala ba kamar sauran na mutanan dana saba gani ba, wata kila saboda dare ne shiyasa idanun nata suka zama haka, dama na ta6a jin wani abokina yace "Idan dare yayi wasu jama'ar abubuwan halittarsu na canzawa" Nasan ita ma tana cikin irin waðannan mutanan, na tuna hakan a raina sa'adda ta dinga kallona kamar tana nazarin wani abu a tare dani. Har yanzu idanuwanta na kaina tana kallona, duk jarumtata da kwarjini na sai naji sun yaye zuciyata na faman buga fat-fat kamar wani abu zai fito daga ciki. "Sunana Taslim" Naji ta faða sa'adda iskar karshen sunan ya daki kunnena, tare da fitar sanyayyar muryarta kamar sarewa. Na bita da idanu ina dubanta har yanzu da tsantsar mamakinta a fuskata, karfe sha biyu da rabi naga agogon waya ta ya nuna. Ma'ana har na kwashe mintuna sha biyar a waje ina dubanta. Cikin lalube-lalube na cafko maganar da ban san sa'adda nayi ta ba nace, "Me ya kawo ki nan da daddare kuma ke wacece?" Ta kara matsowa kusa dani tana dubana tun daga kafafuna har zuwa kaina. Da alama akwai wani abu na musamman da take nazarta game dani, kuma zai iya yiyuwa sirrin zuciyarta ne ita kaðai. "Me kikeyi da dare haka baki tafi gida ba?". Na sake tambayarta kaina ka'sa sakamakon kwarjini da idanuwanta sukai man yanzu, sakamakon dazu da nake kallonta lafiya lau, duk kuwa da canji launin idanu irin nata. "Menene damuwarka da abinda nakeyi da dare? ta faða tana dubana da alama kuma ranta a 6ace tayi maganar. Nayi kasake wajan mintuna biyu zuwa uku bance komai ba, sa'annan na sake dubanta cikin rage sautin murya nace, "Bai kamata ace macce ta fito karfe sha biyun dare ba a irin wannan zamanin da muke ciki da duniya ta lalace, kai koda namiji ne ka gani a irin wannan lokacin sai dai in yana wani aiki ne zai fito amma ba dai ga banza ba". Na takaita maganar ina duban fuskarta ba dan na gama faði mata abinda zan faðin ba. "Kayi kokari" Naji ta faða tana sakin fuskarta ba kamar dazu ba, da ta haðe rai kamar wadda ta cizi bedi. Na lura da'ita sosai a wannan tsayuwar tamu idan tayi murmushi fuskarta tafi wannan farin watan daya haskamu kyau da ado. Amma idan ta 6ata rai sai inga kamar duk duniyar nan babu mai muni kamarta, wata kila saboda kasancewarta bakar fata mai kuma faðin fuska shiyasa. Naga ta ðan matsa kaðan daga inda take, tana duban sashin hanyar da ta saba bi idan ta gama kallon gidajen dake layin namu, kamar tana jiran wani yazo yanayin kallon da tayiwa wajan. "Ko kina jiran wani ne?" "A'a. Ta mai do man amsar kamar tana jiran tambayar dama. Daga ganinta baka cika son surutu ba, maganarta kawai zata nuna hakan komai tana bada amsarshi a takaice "Sannunka Hafiz" Naji ta kira sunana kai tsaye kamar dama ta sanni. Zamu cigaba Hafiz Koza AdamußAKUWAR DARE ~HUDU~ In banda ina ganinta da siffar mutane da tuni na zube wajan, abin mamaki ne koda da rana mutum ya kira sunanka baka sanshi ba balantana da dare irin wannan lokaci karfe sha biyun dare. "Kayi mamaki ko?" ta sake faða tana dubana fuskarta dauke da alamar tambaya. "dole inyi mamaki gaskiya musamman da naji kin kira sunana alhalin ban sanki ba". Tayi far! Da idanuwanta tana duban wani haske daya haskemu lokaci daya daga sai tin gidanmu, "Zan wuce sai gobe kenan lokacin tafiyata yayi". Ta fada tana dubana lokacin har ta fara tafiya. "Saboda me zaki tafi yanzu?" naji bakina ya furta yana tambayarta. "Kawai lokacin tafiyar tawa ne yayi zamu sake haduwa wani lokacin hafiz" ta karashe maganar da kiran sunana kamar yadda ta kira ðazun, ban ankara ba ta shiga lungun da ta saba bi tayi tafiyarta. Ta jefeni da wani ni'imtaccen murmushi wanda ban taba ganin irinshi ba tunda nake a duniya, sai dai na duba ban ganta ba tayi tafiyarta. Na juyo da baya jikina ba kwari domin komawa gida, akwai abubuwa da yawa da naso na tambayeta amma ban samu wannan damar ba, ban san kome yasa tace lokacin tafiyarta yayi ba. Ina zata? Na tambayi kaina ina jin haushin abubuwa da yawa da ban sani ba game da ita. Naso jin tarihinta da abinda ke fiddota da daddare amma nasan duk yadda za'ai zamu sake haðewa koba yau ba, nasan ba yau ne farko ba, ba kuma yau ne karshe ba. Ta kira sunana kai tsaye wannan na nuna cewa, ta sanni kenan duk yadda za'ai. "Sunana Taslim" Maganarta ta fado man a rai sa'adda nake kokarin tuna inda nasan sunan, amma babu abinda kwakwalwa ta ta tuna game da hakan. Nasan dai wani suna ne can daban, wanda ban ta6a ji ba a duniyata da kuma rayuwata, al'amuranta akwai rikitarwa na fada a fili sa'adda na shiga gidan nasa sakata din kyauren na shige dakina na kwanta. Duk juyi daya da zanyi sai ta faðo man ga rai, shiyasa sam! Ban samu baccin kirki ba ranar, daga mafarkinta sai tunanin al'amuranta masu matukar rikitarwa, nasan tabbas da karamar kwakwalwa gareni da yanzu na rikice game da lamarin nan. "lokacin tafiyata yayi sai wani lokacin hafiz". Maganarta ta karshe ta faðo man ga rai sa'adda na juya daga kwanciyar da nayi. Wa zan tambaya taslim ko labarinta? Na tambata duk wadanda na sani basu san ta ba, ba su kuma san wacece wata taslim ba, lallai ta cancanta da sunan da zuciyata ke kiranta "BAKUWAR DARE". Idan kuwa hakane kenan tana nufin duk lokacin da zamu hadu sai da da dare, daren ma sai karfe sha biyu kamar yadda na saba ganinta kullum tana wucewa. Hafiz Koza AdamußAKUWAR DARE ~BIYAR~ Idan kuwa da dare zamu dinga haduwa na tabbata wata rana za'a samu matsala, dan kuwa 'yan banga ko wasu masu yawo da dare dan duba gari idan suka ganmu wajan ban san yadda zamu kwashe dasu ba. Da haka wani nannauyan barci ya sace ni wanda ya kaini akalla wajan awanni biyar zuwa shida, ban farka ba sai karfe takwas na safe har da wasu 'yan mintuka. Abubuwan da suka faru jiya suka rinka faðo man ga rai, kamar mafarki kamar gaske, da'ace taslim bata faði man sunanta na gaskiya ba, to da tabbas nasan mafarki ne kawai wanda bazai taba tabbata ba. Akwai abubuwa da yawa da suka cika man zuciya, ko badan wannan al'amarin ba dama ni abu kadan ke damuna ga zuciya balantana irin wannan na rikitarwa. Ta shigo duniyata da rayuwata lokaci daya, na bibiye ta dan tausaya mata, amma sam ita bata gane abinda ya kawoni wajanta ba, in baccin tausayinta da nakeji da yanzu na fiddata daga dukkan rayuwata. Na kwashe satittika ina ganinta bazan taba mance ranar farko dana fara ganinta ba na fito yin sallar dare lokacin ana zafi, ina kwanciya waje. Bazan taba mantawa da ranar ba bayan na gama sallar na kwanta ne kafin bacci ya daukeni sai gata. Tana tafe tana sauri, fuskarta da alamar damuwa sosai kamar yadda naganta jiya da farko, gashin kanta ya barbazo a waje wanda shine abu na farko daya fara tsoratani game da'ita da dukkan al'amuranta. Sa'adda takai kwanar karshe da zata shiga sai naga ta tsaya tana kalon wajen gidanmu minti daya zuwa biyu sa'annan tayi wucewarta. Tun daga wannan lokacin kullum sai na lura ashe bata wucewa sai karfe sha biyu daidai. Ban taba faði wa kowa wannan al'amarin ba kamar yadda na barwa zuciyata a matsayin sirri. Kowane dan'adam yana da sirri a rayuwarshi dan haka na barwa zuciyata wannan al'amarin a matsayin sirrinta da kuma ni kaina, Abu daya ne na kasa ganewa game da taslim shine, shin mutum ce ko aljana ce, har yanzu da nake wannan zancen banga alamar taslim mutum ce ba. In banda sunanta data fada man ban tambayeta ba, da yanzu ina nan da fargabar abubuwa da yawa a raina game da'ita. Sada Bin Suleiman Usman ßAKUWAR DARE ~SHIDDA~ Haka abubuwa da yawa suka dinga giftawa ga raina game da al'amuran wannan baiwar Allah data fado rayuwata, lallai taslim ta zamo wata daban a cikin mutane, idan mutum din ce. Karfe sha biyun dare ko namiji kaga yana yawo wannan lokacin mawuyaci ne in karamin abu ya fiddoshi daga gida, musamman dai yadda duniya ta lalace kamar yadda na jiya da dare sa'adda nake tambayarta abinda ya fiddota daga gida. Kar in jaku da nisa bari in fada maku yadda muka kare yau nida bakuwar tawa. Kamar yadda ta saba wucewa kowane daren duniya, yau ma batayi fashin wucewa ba, tabbas nasan zata zo ba fashi dan haka tunda wuri na kammala duk wasu ayyukana wadanda nasan zasu bata man lokaci ban kammala ba, ciki kuwa hada wanke tarin kayan dana dade ban wanke ba. Nayi tsaye daga kofar shagona ina kallon waje yau bata kyauren gida nake tsammanin jiranta ba, ta kofar shago na tsaya ina tsammanin zuwanta, yawanci fargabar dake raina ta gushe ba kamar jiya ba, duk da dai har yanzu ina jin tsoronta kadan. Fu! Naji sahun wucewar takalminta bata ko tsaya kallon sai tin shagona ba, shirun da gari yayi ne yasani jin takun takalmin nata tamkar tana gudu. Na bude sakatar a hankali na zuru kaina ina lekenta, tana sanye da doguwar riga kamar jiya amma yau ba baka bace fara ce, sanye da 'yar karamar hijabi iya kafada. Tana tafiya tana hadawa da sauri-sauri kamar zata shige lungun da ta saba shiga sai kuma ta juyo tana duban wajen gidanmu inda take kallo kullum. Ganin na samu wannan damar ne yasa na fito da sauri dan zuwa wajanta, koba komai zuciyata cike take da son sanin wacece ita?. Nima kamar in hada da sauri-saurin har nazo wajanta, nayi shiru bance komai ba. "Malam Hafiz" Naji ta kira sunana kai tsaye kamar yadda ta fada jiya, fuskarta da alamar murmushi da kuma jindadin lokacin, ba kamar jiya ba sa'adda na ganta ta haðe rai kuma tana cikin tsananin damuwa. "Sannunki taslim" Na fada ina duban wasu manyan zobuna dake hannunta na dama, in banda farin watan dake akwai to da tabbas hasken zobunan kaðai ya isa mu dinga ganin fuskokin junanmu. Tayi shiru bata ce komai ba tana daga kai alamar ta amsa, "Da alama bata cika yawan son magana ba kamar dai jiyan" Naji zuciyata ta fada cikin ka'guwa da son jin abinda zai fito daga bakinta. "Jiya muna labarinmu sai lokacin tafiyata yayi, kuma idan lokacin tafiyata yayi bana iya kara ko minti daya ne saboda gudun wata matsala". Ta gama maganar tana murza zobunan dake hannunta. "Wace matsala ce?". Na tambayeta ina duban fuskarta cike da alamar tambaya. Abdulhamid Muhammad Sani MatazußAKUWAR DARE ~BAKWAI~ "Idan na kara minti daya za'a iya samun matsalar da zanyi wata daya ban fita daga cikinta ba". Ta gama maganar tana duban hannun rigarta, abubuwa da yawa suka ziyarci zuciyata lokaci daya game da lamuranta. "Sunanki kawai kika fada man jiya baki fada man abubuwa da yawa game da ke ba, kamar labarinki da sauran abubuwa dai". Na fada ina dubanta. Kamar an tsikareta ta juyo da sauri tana dubana fuskarta da alamar mamaki tace, "Nasan duk 'yan gidanku kaga dai nasan Mariya nasan anti Zainab Nasan Hassan da husaina, bayan nan nasan Abdulmajid wanda ya rasu, da kuma Abdulmajid wanda yake raye, nasan Alh babba wanda shine babba a duk 'yan uwanku, nasan kanwarshi Barira wadda take abuja tana auren sanata, nasan anti amarya wannan mai bala'in son kallon fina-finan indiya, nasan autanta yasir mai yawan san lemon viju". Ta gama lissafa sunayen tana dariya, yayinda tabar kwalwa ta da tunani irin na rudaddu, "Kenan duk kinsan wadannan mutanan?". Na fada ina dubanta cike da mamaki har zuwa wannan lokacin dariyar take kamar wani abu ya faru. "Kwarai kuwa kana mamaki ko dan bakaji na lissafa kai abubuwan da kafi so ba?. Ta jefeni da maganar tana dubana, tun kafin nace komai taci gaba da cewa, "Kai mutum ne mai son wasa da dariya raha da barkwanci, shiyasa wata kawata take ceman kana burgeta sosai, saboda duk unguwarku babu matashi kamarka mai son wasa da raha kamar ka. Ta kara kasheni da mamakin maganganunta masu matukar rudarwa, yanzun ma bance komai ba taci gaba da cewa, "Kana da son tsafta da mutane masu tsafta, kana da son karatun litattafan hausa na ban al'ajabi irin wadanda suka shimfida zamaninsu tun kafin kazo duniya, ma'ana kai mutum ne mai son jin labarin ban al'ajabi da rikitarwa irin wanda baka taba ji ba". Ta gama maganar tana tafiya da alama yau ðin ma tafiya zatayi bata fada man labarinta ba. "Sai haduwa ta gaba kenan malam hafiz" ta fada tana tafiyarta bata ko damu da irin abinda zan fada mata ba. Duk maganganun dake bakina dole in riqe su sai haduwa ta gaba, saboda na tabbata duk maganar da zan mata ba zata tsaya ba dole ne ta tafi tunda lokacin tafiyar tata yayi. "Sai goben to kenan?". Naji bakina ya furta ina dubanta zuciyata cunkushe da damuwa da maganganu da yawa bakina fal! Amma ta tafi bazan samu damar fadinsu ba sai gobe idan mun hadu. Goben ma ba wai tabbacin fada mata maganar gareni ba sai in lokacinta ya barmu, ina tunanin har ta kule na daina ganinta tayi nisa daga wajan kenan. Na juyo ba kuzari jikina, kamar wanda akaiwa bugun tsiya, na tunkaro gida ina tunanin lamuran taslim wadda take neman jefani a rudani kullum. Jiya ta kira sunana kai tsaye, yau kuma ta fada man sunayen 'yan uwana gaba daya harda Alhaji babba wanda shine babba a zuri'armu na raye, ta fada man halayen anti amarya da danta, ta kuma fadi man nawa halayen wasu. Gobe bansan abinda zata ce man idan muka hadu. Sharif Medouki ßAKUWAR DARE ~TAKWAS~ Idan har zataci gaba da lissafa man abubuwan dake faruwa a rayuwata, nasan tabbas wata rana zata fada man maganar da zata tarwatsa man kai, koba komai ita ðin wata mutum ce ta musamman ga rayuwata kamar yadda zuciyata ke fada man. Jiya muka fara haduwa gaba-da-gaba amma ta fadi sunana kai tsaye ba shamaki wannan na nuna cewa, ta sanni duk yadda akai sani kuma ba karami ba, musamman in nayi lura da kalamanta na yau da ta lissafa sunayen 'yan gidanmu wai har abdulmajid daya rasu ta sani. Lallai wannan tasan rayuwata sosai, na fada ina jinjina al'amarinta cikin raina sa'adda na kwanta, kamar ana jiran zamana naga an maido wutar lantarki, wannan yasa na tashi na sa kwamfuta dita ga wutar dan tun jiya ta dauke. Sa'adda ta samu kamar mintuna goma zuwa sha biyar ne na kunnata domin hawa yanar gizo da duk 'yan kwanakin nan ban leka ba, nasan zan tadda sakunan jama'a da yawa dan kuwa nasan wadanda muka saba wasan zolaya dasu sakonninsu na nan fal! Da

Chapter 1 of 3