su suka gama raina shi. Har kananan yaran su, idan sun tattare ragowa abinci sai su hada masa haka zasu dinga cin karo da gashi majina duk aciki babu yadda suka iya haka zasuci.
Wata rana ya fahimci matarsa na da ciki. Wannan labari ya cika shi da farin ciki. Ya yi alwashin iri-iri akan dan da za a haifa. Duk kasalancinsa a ibada, wannan karon ya dage da tashin dare, salloli akan lokaci, addu’ar Allah ya bashi ɗa wanda zai haskaka a dangi da duniya. Matarsa ta fahimci wannan nacinsa ba don yana da ilimi ba, sai don zuciya. Ta yi amfani da iliminta da salon kissa, inda ta dinga koya masa yadda zai bautawa Allah tare da bashi shawarar ya shiga makarantar yaƙi da jahilci.
Cikin ikon Allah, ashe shi ma mutum ne na musamman — kwakwalwarsa tamkar ta computer. Duk kuwa da ya manyanta, yanzu kam yana iya karatu da rubutu, sannan bangaren Arabic ya kan iya hada baki da biya wasu surori. Matarsa ta kan taimaka masa wajen addu’ar cikar burinsa.
A ƙarshe Allah ya sauketa lafiya, sai dai mace ta haifa. Wannan ya sa ta ji burin mijinta bai cika ba. Amma ga mamakinta sai taga farin ciki yake sosai.
Ya zauna kusa da ita yana dubanta da kallon tsanaki.
“Baiwar Allah, me ke faruwa ne?”
Ta danyi murmushi.
“Naso na cika maka burinka wajen haihuwar namiji, sai gashi na haifa maka mace. Naga kuma baka damu ba, farin ciki kawai kakeyi.”
Ya ce:
“Hakika ina da burin samun ɗa namiji, amma nasani duk abinda namiji zai iya yi, mace ma zata iya. Kalli fa yarinyata — ban taɓa ganin jaririya mai kyawunta ba. Jinake ajikina, itace komai nawa. Jinake kowa zai yi alfahari da ita. Wannan ita ce tamkar da goma. Na shayin mafarkin wata yarinya mai kama da yar Larabawa tana zaune cikin dubban jama’a, kowa na tafa mata yana yi mata kirari. Kina haihuwar mace, na tabbatar wannan ta cikin mafarkin itace.”
Kawai sai jaririya ta fara murmushi kamar ta ji me ake cewa.
“Kingani tana murmushi. Kalli ruwan kyawu. Na sani wannan ba zata yi irin yacca nayi ba — zaki bata tarbiya irin taki, ko?”
Ta ce:
“Mijina, da izinin Allah wannan yarinya kowa zai yi alfahari da ita. Rayuwarta zata haskaka, ko da kuwa bayan raina ne. Insha Allah baza ta taɓe ba.”
Ya ce:
“To yanzu gaya min, wata yo?”
Ta kalli jaririyar.
“Bakinta irin nawa, idanunta mankya-mankya kamar naka, farace tas kamar kai, halayenta iri—”
Ya ce da sauri:
“Irin taki.”
Suka sa dariya gaba ɗaya. Daga nan ya raɗa mata suna Nana Aisha, amma za,a dinga kiranta Ikhalas.
Tunda aka haifeta suke samun albarka. Wasu ma saboda kyawunta suke kawo musu kyauta. A takaice sai da aka yanka raguna uku.
Ikhalas tana shekara biyu da rabi aka saka ta makaranta. Idan aka tashi, ana yi mata lesson na musamman. Makaranta ce mai tsada, makocinsu ne ya dauki nauyin ta. Duk wani buri Ibrahim ya dora akan ta.
Tana ƙarama iyayenta suka tabbatar da addu’arsu ta karbu. Tana da kokari, nutsuwa, turanci a bakinta tamkar a England aka haifeta. Ta zama abar alfahari a makarantar Abul Anwar Computable School. Yanayinta ya saje da yaran masu kudi saboda makocinsu duk abinda ya siya ma ‘ya’yansa sai ya siya mata.
Ta gama primary tana shekara takwas, yar karama ce amma magana bata dame ta, ba ta da surutun yara. Ga takura da Ibrahim ya yi mata da karatu — baya taba barinta ta huta. Kwakwalwarta ta gama horuwa, mamanta har ta kan tausaya mata.
Suna shirin shiga secondary school sai Allah yayi wa makocinsu rasuwa. Ibrahim yayi kuka kamar zai mutu. Wannan ne yasa Ikhalas ta koma makarantar gwamnati.
A wannan lokacin suka hadu da Rahama suka shaku. Ita ce kadai da Ibrahim ya amince da alakarta da Ikhalas — amma bai sani ba Rahama ce ke kokarin rusa masa burinsa, ta hanyar karfafa Ikhalas akan wanda basu san waye ba — wato Zaruk. Zaruk ne Ikhalas ke mutuwar kauna tamkar ranta.
Har yanzu ta kasa bayyana wa iyayenta abin da ya faru da wayarta. Tunda ya kyalla ido kan hotunanta, bai da tunanin da ya wuce ta. Ya shiga laluben lambobin wayarsa, har ya hango My Number a contact dinta. Ya mike a dokance, ya shiga kiran ta.
Suna zaune ita da Rahama cike da alhini, sai karamar handset dinta ta soma ringing. Ta duba fuskar wayar, taga lambarta. Ta dubi Rahama cike da mugun farin ciki, rudewar farin ciki ya hana ta furta sunan Rahman. Muryarta na rawa har da kwalla:
“Kingani? Ana kirana da layina… Allah na gode maka.”
Rahama ta ce:
“Bangane ba, kamar yaya?”
“A layina ake kirana.”
“To kiyi sauri ki amsa.”
Ikhalas ta dauki wayar, ta kara kunne.
“Hi mai kyau, shin baki damu da wayarki bane? Koda bashi da tsada, abubuwan dake ciki zasu zama masu tsada — musamman hotunan tauraruwar ilimi kamar ki.”
Ta dubi Rahama, amma ta kasa cewa komai. Rahama ta karbi wayar.
“Kina jina ko? Idan kina bukatar wayarki, gobe da misalin karfe goma na safe mu hadu a Tahir Hotel sai ki karba.”
Idanun Rahman suka fito — hakan yasa Ikhalas ta tsorata. Ta girgiza kai alamar baza ta je ba.
“Kayi hakuri, ba’a barina fita ko ina.”
Ta cire wayar a kunne tana tambayar Rahama:
“Ina ne Tahir Hotel?”
Kalmar hotel ta zame mata kamar harshen wuta a kunne. Zuciyarta na harbawa. Rahama ta lallashe ta, amma muryar mutumin daga can ta kara tsananta mata tsoro:
“Zan maishe ki mujiyar jama’a. Zan karya miki mutuncinki idan kika ki zuwa — musamman idan na yi amfani da kyawawan hotunanki dake cikin wayar.”
Hawaye suka zubo mata. Ta kasa jurewa.
“To… zan zo. Amma me yasa sai a can zan karɓa?”
Wayar ta katse. Ta rage numfashi tana kallon Rahama, idonta cike da tambayoyi da tsoro.
Rahama ta ce:
“Ki kwantar da hankalinki, Ikhalas. Allah ba zai tozarta ki ba. Amma ki ji tsoron mutum idan zuciyarsa ta mutu — irin wannan zai iya yin duk abin da zai bata miki suna.
Na san kina jin haushin jin cewa ki tafi hotel, amma ki fahimci ba duk wanda yake cikin hotel yake aikata mugunta ba. Amma a gaskiya, wannan zamanin mutane sun fi daukar hotel a matsayin ramin zunubi. Idan aka ji an ganki a can, koda babu komai, za a yi miki hukunci ba tare da sauraronki ba.
Sau nawa kika ji labarin an dauki hoton mace tsirara? Sau nawa kika ga an baza video ana yi mata dariya? Wani lokacin ma hakan don kazantar da suna ake yi, ba don wani abu ba.
Idan hakan ya same ki babu mafita — kimarki zata zube gaba daya. Iyaye ma zasu iya cewa, ‘Ashe wannan ce asalin halinta.’ Wannan shi ne abin da zuciyata ke tsoron ki fada ciki. Ba wai lalata jiki kawai ake yi ba — suna ma ana lalawa har ya kasa gyaruwa.”
[18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_
_BY_
*BILKISU H MUHD*
Phone 08031307884
Page 9
*MARUBUCIYAR*
ILLAR SABO
RASHIN RABO
YA YI SAKE
ZAFIN HAWAYE NA
BAKIN KAZAFI
WAYA FI SONTA
GORO DA SANKARA
JINI BIYU
DACEWA
KAUNA CE
BAYAN KUSKURE
MATSALAR KAUNA
TARAIRAYA
DAKE NA DACE
AKWAI BANBANCI
BAKIN KAZAFI
MULKIN MALLAKA
IZZATU
BAYAN KUSKURE
KA AURE NI
KYAUTAR ZUCIYA
*sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA DA SO zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.*
makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake. Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba.
Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻
Wattpad:👇🏻
@bilkishmuhd
Arewa Book:👇🏻
bilkisuhmuhd
WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t
WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o
FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT
BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t
------------------💥
Ikhlass na fitowa, amma ƙafafunta tamkar an ɗaura musu sarƙa. Zuciyarta tana bugawa kamar ana dukan ganga a cikin ƙirjinta. Hawaye sun gaji da saukowa, amma ba su gajiya da yin zafi a idanuwanta. Kunnenta yana maimaita kalaman da ta ji daga mutumin nan, kalaman da idan suka tabbata — Abu zai ɗaure rai, fushin da ba zai gushe ba har abada ba.
Wannan abin ba ƙaramin kunya zai bata a idon mutane ba. Kafin ta gama tunanin yadda zata iya tserewa daga wannan jarrabawar, saƙon nan ya shigo. Hannunta na rawa, ta duba — address. Saƙon ya ɗauke da umarni mai sanyi amma mai tsini: "nan da awa ɗaya kacal. Idan baki zo ba, ki kashe waya ki saurari abin da zai biyo baya."
Wata gagarumar damuwa ta kulle mata ƙwaƙwalwa. Ta san yau Asabar ce, babu makaranta. Wace ƙarya zata yi?
Ta shiga kai-koma a ɗaki, zuciyarta ta rikice kamar wutar lantarki da aka saki a tsakar ruwa. Daga can sitting room, ta ji muryar Abu da Ammi na hira. Hanyar tsira ta fado mata.
Ta yi wanka, ta fito, ta shafa mai kaɗan, babu hoda. Ta ɗauko uniform ɗinta, wanda tun jiya ta goge, ta saka. Gabanta na harbawa, ta fito.
---
"Lu’ulu’u, yau Asabar ne fa," Abu ya ce da mamaki.
"Nasani, Abu… amma an ce muzo saboda mun kusa fara jarrabawa," ta amsa tana boye rawar murya.
Abu ya ciro kuɗi daga aljihunsa, ya miƙa mata. Ammi ta haɗe fuska.
"Me ya sa baki sanar da ni ba?"
"Na manta ne…" ta ce da sanyin murya.
"A irin wannan lokaci kuma? makaranta?" Ammi ta sake tambaya, idonta na neman zurfafawa cikin sirrinta.
Kafafunta suka yi sanyi, ta san idan Ammi ta matsa tambaya, zata iya gano gaskiya. Ta yi shiru kawai.
"Allah ya bada sa’a," Ammi ta ce, bata ji daɗi ba.
Ta fice da sauri kamar wadda mai shirin tashi sama.
---
Adai-daita ya tsaya gabanta, fiye da biyar in suka tambaye ta inda za ta,sai ta kasa furtawa. Sai wani sabon saƙo ya shigo: "Lokacinki na ƙarewa." Nan ta tilasta kanta ta faɗin address.
Tunda ta shiga napep, hawaye suka fara gudu. Direban yana kallonta ta gefe, kamar yana tambayar kansa, "Ina yarinyar nan ke nufa haka?"
"Mun iso. Ki bani hakkina kafin wani ya zo ya ce na ɗauke masa ‘ya ," direban ya faɗa yana murmushin ɓoyayyen damuwa.
Zuciyarta ta ce kawai: Allahumma ajirni fi musibati…
---
Ta tsaya a bakin hotel, jikinta na rawa. Idanunta sun cika da hawaye, zuciya na bugun bala’i. Da sassarfa ta shiga ciki, ta yi karo da wani mutum tsaye gabanta.
"Kece mai amsar waya?"
Ta ɗaga kai, amma ta kasa magana.
"Kije daki mai lamba goma sha ɗaya. Oga na can yana jiranki."
Numfashinta ya kulle, jikinta na rawa.
"Kiyi sauri kafin ki jawo wa kanki matsala," ya ƙara faɗa yana nuna hanya.
Ta tafi a hankali, tana waiwaye. Ta isa kofar ɗakin 11, ta rintse idanu, hannunta na rawa.
---
Sai kawai aka murɗa key, ƙofar ta buɗe. Wani kallo mai nauyi ya sauka kanta.
"Shigo," muryarsa ta fito mai sanyi amma mai ɗauke da guba.
Ya zauna yana kallonta, yana jin duk jikinsa na tsigar sha’awa da mamaki. Singlet ce a jikinsa da gajeren wando, Ta kame idonta, ta shiga maimaita addu’a a ranta.
"Kinga, shige ciki ki bani wayata, sai ki karɓi taki," ya faɗa.
Ta shige sum-sum. Ya nuna mata kujerar zama, amma ta ki. Sai kawai ya daka mata tsawa, ta tsinci kanta da zama. Gumi ya gangaro daga gashinta zuwa fuskarta.
"Naga kina gumi kamar wadda ta gudu daga fanfalaki. Sha ruwa."
Ta girgiza kai.
Sai kawai ya ɗaga muryarsa, ta tsorata ta da sauri ta karɓi robar ruwan. Bai tsaya nan ba ya ɗauki lemon, ya buɗe ya mika mata. Cikin firgici ta karɓa, ta sha har sai da kwalin ya ƙare.
Yana ta kallonta, idanunsa sun sauya launi. Ya fara tambayarta:
"Sunan ki?"
"Ikhlas."
"Wace makaranta kike zuwa? Ajin ki nawa?"
Tana amsa masa a fusge, zuciyarta na juyawa. Murmushin mugunta ya bayyana a fuskarsa. A hankali ya cire hijab da dankwali, ya fara laluben rigarta. Amma a tsakar wannan sha’awa, wata zuciya ta shige masa — ina ma ace ita matata ce…
Ya tsaya cak, zuciyarsa na bugawa. Amma kalaman kakarsa suka katse masa nufin da zai aikata. Wani kira ya shigo wayarsa Grany yagani a rubuce.
"Oh, kakahhh… me zan yi miki kuma?"
Wayar ta katse ba tare da ya daga ba. Sai can ta sake ruri, afusace ya ratsa ya kara a kunne.
"Ina bin sahunka ban ganka ba, na tsorata da abin da ka fada dazu. Na kasa samun nutsuwa saboda na san halinka. To ka ji, wallahi ka keta mutuncin yarinyar nan, ba zan taba yafe maka ba — kai da iyayen da suka yi sanadin zuwanka duniya. Sai la’anar Allah ta tabbata a gare ka, azzalumi! Daga kanta zaka ga aya. Kuma ma, ko yatsanta ka taba, ina rokon Ubangiji ya yi gaggawar saka mata ta inda zaka kasa fita har abada. Sai Allah ya jarrabe ka akan wannan!”
"Ya isa haka!!"
"Haba, irin wannan jafai haka, kamar ba jinin kiba?"
Ta ja tsaki, ta kashe wayar. Duk tantirancinsa, yana tsoron bakin kakarsa. Tun kafin ya taso, ya riga ya canfata da cewa tana da kambun baka — duk ikirarin da ta yi, yawanci yana tabbata. Muguwa ce shiyasa kullum zaka ganta a kan buzu, gaba daya bata da lokacin bacci, hannunta kullum rike da carbi.
Ya koma falon cikin dakin yana ta zarya. Kalaman kaka ne suka dinga yi masa yawo a kwakwalwa, yayin da idanunsa ke haska masa halittar Ikhlas.
Ya sauke ajiyar zuciya.
Yadda yake jin ta a ransa ya kasa tantancewa — tsananin sha’awa ne, ko kuma takaicin sumbatun kaka?
Ya fara sumbatu kamar wani tababbe, yana maimaita kalmomi da ba shi da tabbacin ma’anarsu, kamar zuciyarsa na rikici tsakanin son wani abu da tsoron la’anar da aka jefa masa.
A’a, ban taɓa jin mace ta shiga zuciyata ta ratsa kowace jijiyata irin haka ba. Na gode wa Allah da ban keta mata haddi ba… amma inajin kamar an ajiye ni a hannunta ta hanyar da ba zan iya guduwa ba. Daga can ƙasan zuciyata, akwai wani ƙauna mai zurfi da dole sai na kare rayuwata da ita dole sai ita ce matata.
Sai dai gaba ɗaya na tsani kaina. Me yasa na bi wannan hanyar? Da wane ido zan sake dubanta? Yaya zan haɗa ido da ita? Zuciyata na ƙuna kamar wuta, zuciyata na harbawa da ciwo, amma har yanzu ina jin wani irin ƙarfin sha’awar ta a cikina. Wannan ji mai haɗa tsoro da farin ciki ya mamaye ni, har numfashina ya fara nauyi.
---
A gefe guda, Ikhlass ta motsa a hankali. Idanunta suka buɗe cikin kasala, amma ciwon kai ya daki ƙwaƙwalwarta kamar guduma. Tana yunƙurin tashi, sai ta ga hijabinta da dankwalinta a gefe, uniform ɗinta a cunkushe. Wani irin ƙara mai haɗe da kuka ya kuɓce mata. Da gudu ta fice, ba tare da ta ɗauki hijabi ko takalmi ba.
Tafiyarta cike take da girgiza ƙasa da bugun ƙafa, kowa na kallonta da mamaki. Ita wacce kullum ake gani cikin mutunci da kunya, yau tana gudu a haka.
Shi kuma daga nesa ya hange ta. Zuciyarsa ta doki ƙirji da ƙarfin da bai taɓa ji ba. Ya kira mai tsaron ƙofar da gaggawa, hannunsa na rawa.
“Dakatar da ita… don Allah, ka dakatar da wannan yarinyar!”
Kafin ya fito, mai gadin ya riga ya nufo shi.
“Tana ina?!” ya tambaya da muryar da ke girgiza zuciya.
“Sorry oga… mota ce ta bugeta,” mai gadin ya faɗa da lalatacciyar Hausan sa, ya wuce.
“What…!” Kalmomin suka makale a makogwaro. Idonsa ya fara juyawa da tsoro, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi. Ya gangaro daga bene da gudu, kowa na kallonsa amma ba wanda ya iya tambayarsa.
A waje, ya tarar da taron mutane. Jini yana kwance a titi. Zuciyarsa ta yi nauyi kamar an ɗora dutse a kai.
“Ina yarinyar da ta yi hatsari?” ya tare wani saurayi.
“‘Yan sanda sun ɗauke ta. Na tabbata asibiti za su kai ta Allah dai yasa bata mutuba ,dan wannan sai wani ikon Allah,” saurayin ya ce, ya wuce.
Wannan shine last free page mai son cigaba ya tuntuɓe ni a wannan numbar -08031307884
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels