Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
cewar Ikhalas. ....................... 💥 Ammi ce ta bata labarin abin da ya faru a inda itama ta gaya mata maganar da ta jiyo ana yi a waje " Amman Ammi mai yasa Abu ya ke haka ne baya tsoron bakin mutane, idan baya so sai ya karɓa ko su Baffa hamza sai ya baiwa" Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya," ni na ce ke kanki kin fi kowa sanin halinsa? sai nuna isa gashi bai isa ɗinba" Ikhalas taji kalamen Ammi sunyi mata tsauri sai ta dingajin babu dadi aganinta bai kamata ta fito da irin wannan maganar agabanta ba kawai ta barshi aranta tunda ita din y'ace. motsin shigowar da suka ji ne yasa su yin shiru. --------------------------------------- "Ai in Allah ya yadda sai Ikhlas ta mutu inyaso muga ta ƙarya" Salisu ya fada. baffa Hamza ne ya dakatar da shi gun tsinkeshi da wani azababben mari ya dafe kunci yana huci baffa Hamza yace"dan uban ka ƙanwar taka ka ke yiwa fatan mutuwa? ita ɗin mai tayi maka kawai sabida halin ubanta?" Cikin ƙunci yace"Amman Abba abin nasa ne akwai ban haushi, ya sani mu ba unguwar mu ɗaya da baban sukari ba, yasani mu ba, bamu za'ayi ba, ya san kuma da hakan amman tsabar baƙin hali da son nuna fariya ya....." "Ba zaka yi mani shiru ba ko? ko kai baka taɓa cin abinci bane?" " Toh amman Abba ko yanzu babu wanda ya karya a cikin mu" "Ba zaka yi mani shuru ba ko!!?" gyaɗa kansa yayi, Fuuuu yayi waje yana faman ƙunƙuni. "An faɗa in Allah ya yadda ƙwaƙwalwar ta sai ta zama ta jakai" "Abban su Salisu dole fa yaji babu daɗi, kai ban san me yasa baka ganin laifin su ba" "Banda ke da abun ki Dija kowa fa arziƙin shi yake ci, muma fa mun haifa wataran zamu ci albarkacin yaran mu, baki sani ba ƙila ma a kwai shugaban ƙasa a cikin yaran naki" ya faɗa yana murmushi. Banza tayi masa ta shige ciki ita bata taɓa ganin marar zuciya irin baban Salisu ba. ........................ 💥 Haj Hauwa ce durƙushe a gaban malam tana faman kuka"yanzu malam babu yadda za'a yi in samu haihuwa?" Malam ya maida hankali a kan ƙasar da ke gaban sa ya ɗanyi zane zanen sa ya ɗago kai ya dube ta" gaskiya mijin ki ba mai haihuwa bane" Ta jinjina kai cikin tashin hankali " to malam menene abin yi?" ya ɗanyi shuru yana shafar ƙasar dake gaban sa, sannan ya ɗago yace"kawai dai a sake sabon ta soyayyar  yaron ki a zuciyar sa" "Toh malam kodai a kashe shi?" Da sauri malamin ya ɗago yana duban ta" ai mutuwa sai lokaci yayi, kuma mu babu kisa a tsarin aikin mu idan lalle sai kisan kike so sai dai ki nemi wani" Jikin ta ne yayi sanyi duk sai taji ta muzanta " to shikenan a sabunta soyayyar yaron nawa a zuciyarsa in yaso ya zamto sai yadda mukayi da shi" bundle din ƴan dubu dubu ta ajiye masa suka yi sallama.   ---------------------------------------                 Alhaji Ashir (Baban sikari) shahararren attajiri ne wanda bashi da burin da ya wuce ya farantawa mabuƙata, kullum yana jin cewar an bashi arziƙin ne kawai domin ya taimakawa marasa ƙarfi, har matasa ne dashi waɗan da ya wakilta a kan duk wanda yake cikin unguwar tasu idan bashi da shi a gaya masa, ya sayi motoci irin bus bus ɗin nan dan kai  yara makaranta, waɗanda ya ɗauki nauyin karatun su ba zasu lissafu ba, Alhaji Ashir ɗan kwangila ne sannan yana da manyan kantina a kasuwar kwari, ana juya masa kuɗaɗen shi. Dattijo ne shi ɗan kimanin shekara sittin, yana da mata guda ɗaya, a halin yanzu matarsa ta fari Allah yayi mata rasuwa, sai hauwa wadda i tace ke zaune da shi da yaron ta ƙwaya ɗaya wanda ta haifa a wani gidan wato Nazir, tun yana ɗan shekara goma sha huɗu ta kawo shi gidan, yanzu haka shekarunsa ashirin da takwas, taƙadari ne na gasken gaske, sai dai a gaban baban sukari babu mutumin kirki irin shi, baban sukari ya riƙi Nazir tamkar ɗan cikin sa ƙaton shago ya mallaka masa a  kasuwar kwari, sai dai Nazir da haj hauwa basu da buri illa ya danƙa ragamar dukkan harkokin shi a hannun sa, sun bi malamai sun bi bokaye har sun gaji, duk lokacin da baban sukari ke fidda zakka ji suke yi tamkar za suyi hauka, yanzu burin hauwa ta yaya zata sami haihuwa da shi ko dan taci gadon shi, wannan kenan. Cikin mamaki ta kalli ƙawar tata sannan tace"Lalle haj hauwa yau na tabbatar da baki da hankali, yo idan kika saka aka kashe shi dame zaki ƙaru? ai gwara kisaka ayi masa asirin da zai zamo shi ba'a mace ba, shi ba'a raye ba, yanzu fa da zaran ya mutu waɗanda ma baki taɓa gani ba zasu yunƙura suce ɗan'uwan su ne, kuma dole ne a raba gadon dasu" Hajiya hauwa ta saki ajiyar zuciya, cikin damuwa tace"haka ne aminiya, yanzu meye abin yi?" " Abin yi kawai mubi a hankali zamu sami wanda zaiyi mana aiki a kansa, kudi zaki bani naje India kinsan ance sheɗanun bokaye sunfi yawa a can" Wata uwar shewa suka saka tare da tafawa wannan kenan. -----------------------------------💥      America Babban birnin Amurka shine Washington, D.C. Shi ne cibiyar gwamnati ta Tarayyar Amurka, inda Aso Villa na Amurka wato White House, Majalisa (Capitol Hill), da Kotun Koli (Supreme Court) suke. Georgetown Wannan tsohuwar unguwa ce mai tarihi da kudi. Tana cike da gidaje masu tsada, shaguna masu kyau, manyan restaurants, da manyan mutanen kasa. Akwai celebrities da diplomats da manyan ‘yan kasuwa da ke zaune a nan. The Four Seasons Hotel Washington, D.C. Yana cikin Georgetown. Wannan hotel din yana da matakin duniya, yana karbar shugabanni, celebrities, da ‘yan kasuwa. Farashin ɗakin dare ɗaya yana iya haura $1000 . A hotel  din wani katon Holl ne wanda ya gama kayatuwa da kayan alatu da wasu irin kujeru na alfarma ga yadda holl din yayi shuru zaka tabbatar da cewar abinda ake tattauna akai yana da matukar mahinmanci. Wani matashi wanda bazai wuce shekaru ashirin da takwas ba sanye da white shirt da Black jeans yayi aski low cut mai tsafta sanye yake da Rolex agogo a sandar hannunsa da kuma tabarau rayban sai dan karamin zoben gold a yatsan sa takalmin kafarsa Fendi shoes sai Hermes belt dake daure a kugunshi. Zaruk kenan yong billions wanda ake ji dashi a wannan zamanin manyan kusoshi ke neman hada hannu dashi ayanzu haka iya da hannun jari a campanunuwa irinsu Apple Inc. (AAPL) Kamfani mafi girma a duniya bisa kasuwar daraja (market capitalization). Yana kera iPhone, iPad, Mac, da sauran kayayyakin zamani. Saka hannun jari a Apple yana da daraja saboda yana da ƙarfi sosai a kasuwa. Microsoft (MSFT) Shahararren kamfani na fasahar zamani. Yana da software irin su Windows da Microsoft Office, da kuma Azure (cloud computing). Amazon (AMZN) Babban kamfani na e-commerce (sayayya ta yanar gizo). Hakanan yana da Amazon Web Services (AWS) – babban kamfani na girgijen ajiya. Wanda ke kawo riba sosai. Nvidia (NVDA) Kamfani mai ƙera kwakwalwan kwamfuta da ake amfani da su wajen AI, da wasanni (gaming). Hannun jarinsa ya haɓaka sosai a cikin shekarun baya-bayan nan saboda tasirin AI. Inda Zaruk ke zaune da wasu irin speakers jere agabansa yana magana kadai zai tabbatar da cewa shidin wani babban kusane da ake ji dashi Ya dade yana jawabi cikin muryarsa mai ƙarfi da kwarjini, lokacin daya gama jawabin gaba daya aka dauki tafi . Wadanda suke baki agun kasan cewar yaune ganinsu da shi na farko yayi mutukar birgesu tambaye suke wai waye shi sabida gaba daya shi din bai kaisu haske ba amman fatarshi tafi tasu kwanciya da kyau gashi da tsayi wanda bai wuce misali ba siffa mai kyau  alamar kulawa da lafiya. Tafiya da tsayuwa irin ta jarumi Gaskiya da aminci: baya yaudara, kuma abin dogara ne. yana da hangen nesa da sanin me yake nema. yana da Sauƙin kai ba mai girman kai ko wulaƙanci ga mutane ba. yana da Kiyaye magana da alkawari: idan ya ce zai yi, to sai ya yi. yana nuna damuwa da jinƙai ga na kusa da shi. Kyakkyawa ne na gaske . bayan kowa ya gama jawabinsa  taro ya watse sai dai shi kasan cewarsa musulmi sai da shi da tsitarin musulmen dake gun sukayi addu,o'insu kafin su watse. gashi dai ba'a ƙasar musulunci ya taso ba amman yana ibada tamkar yau zai bar duniya, haka kuma mutum  ne mai  son ibada, abin da zai baka mamakin a kan Zaruk kaf gidan shine kaɗai musulmi, sunyi iya yinsu akan ya koma Christian amman fir yaƙi, kasancewar su a turai kowa na bin ra'ayin sa ne, kafin mahaifinsa John ya mutu ya gargaɗi dangin sa cewar kada wanda ya kuskura ya tilasta shi a barshi a musuluncin sa, dan haka kowa ya sa masa ido, wannan banbancin addinin baisa sun ƙyamace shi ba, suna mutuƙar ƙaunar sa, za kayi mamakin idan kaga Zaruk na yin hausa tamkar ya girma cikin garin Kano, hakan ta samo asali ne ta dalilin gidansu amininsa wanda ya kasance kaf ya kare rayuwarsa a cikin gidansu, kwanciyar bacci ne kawai ke raba su da gidan sai dai yanzu gaba ɗaya sun koma Nigeria, lokacin da uban gidan su ya mutu wato John mahaifin Zaruk a dalilin yadda suka riƙe Zaruk ya sanya John ya mallaka  masa dukiya mai tarin yawa  har kawo yanzu Alhaji Auwal, Zaruk dinne ya zamo mai gidan sa, arzikin da Zaruk ya gada a wajen John bashi da iyaka, abun birgewar shine baka taɓa sanin waye shi  ko a suturar da yake sawa  inba sanin ta kansu kayi ba sai ka zaci mai saukin kudi ne sabida rashin hayaniyar kayan wani fannin ya kan saka na matsakaicin kuɗi. --------------------------------------------- Babban Gida Gini mai hawa   da launuka masu natsuwa (fari, grey, da duhu-blue).kewaye da babban haraba Gidaje Na Cikin Gida (Guest Villas) Domin ma aikata da baki da kuma abokai. Swimming Pool mai kyan gani da haske da tsakar dare. Ga Private Garden: Lambu da shuke-shuke masu tsada, kamar orchids da bonsai trees. Garage na Supercars: Ferrari, Lamborghini, da Mercedes Maybach suna a tsare. Cikin Gida (Interior) Babban Falo (Living Room): Mai fadi, design na zamani (minimalist + luxury), da LED lights masu canza launi. Glass Walls: Ganuwar gilashi da ke nuna lambu ko pool. Library + Office: Wurin da yake karatu da gudanar da business. Kitchen na zamani: Inda shi kansa zai iya dafa wani abu idan yana so Home Cinema:  ta kallo fim. Idan ya gayyaci abokai Fitness Room / Gym: Don ya nuna jikinsa yana aiki, lafiyayye ne. Balcony mai View: Wurin da zai dinga kallon taurari idan yana jin damuwa tayi masa yawa. Sanye yake da White Shirt + Dark Jeans Yana tsaye a gaban gilas din falo yana kallon ruwan sama da tunanin mushinta. Ikhalas na waya da Zaruk a ɓoye, ta gefe guda kuma tace baban sikari yana birgeta, Iklhas yane😅 Yaya zata kaya tsakanin Baban sikari da kuma matarsa Hajiya hauwa? shin tana yin nasara a kansa domin su samu gadon dukiyar sa? Tafiyar tamu me tsawo ce kawai ku antayo mu tafi tare💃🏻💃🏻💃🏻 Bilkisu H Muhd✍🏻 [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 4 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 Haba mommy wannan ta,adin yayi yawa ai bashine ƙaruna ba wanda yafi kowa kudi da a kullim shi bashi da magana sai na ya taimaki jama'a ,wai kinji makudan kudin da yabayar wai wasu malamai zasu tafi can Kan dutse da'awa,amman mu idan mukace muna son kudi sai an tambayi abinda zamuyi dasu kodan ni bashi ya haife niba ai inda ace ni dansa ne komai zai sakar mini shago fa daya ya bani mai naci aciki Mai na bawa mutane na ga jamila na dauke da ciki ni dai gaskiya nagaji kawai ki sama mana mafita"haba Nazir kadinga kasa da murya mana kofa yaushe zai iya shigowa,ni nafison mubishi a sannu mutun ne shi mai wayo idan na nuna ina son abinsa bazai sake gaya mini sirrin shiba kaga yana yawan gaya mini inda kadarorinshi suke idan mukace zamuyi wani yunkuri zamu rasa abubuwa da dama idan muka dan jinkir ta dazaran ya gama gaya mini inda dukkan kadarorinshi suke komeye sai muyi mishi sallama suka jiwo daga harabar gidan " yanake jin murya kamar ta rakiya ta dan leka ta taga aikuwa da gudu ta kwasa kamar wata karamar yarinya suka rungume juna har suna huwaɗuwa haj Hauwa ta ruko hannun rakiya cancan kuryar daki take shirin kaita zasu wuce kawai Nazir ya bisu da kallo babu sannu ballan tana gaisuwa shifa duk wata kawa ta mahaifiyar ta to tazo ne ta yagi rabonta.    acan cikin daki atsakiyar gado tana zaune dafi'an gabanta kayan ciye-ciye ne kala kala,kai kana kallon rakiya zaka tabbatar da tsohuwar kilakice babu digon kunya a idanunta. Kaf haj Hauwa ta gama shaida mata abinda ke faruwa da kuma wanda take shirinyi. "Tabdijan lalle bakima da hankali to duk abinda kika tsara beyiba hajiyata kawai harka zamu bude haj Hauwa ta gyara zama " banfahimta ba " badai baya haihuwa ba to zamu samo mishi yaro awaje dole ki dana bariki bama sai na koya miki ba tunda an taba danawa,kawai sake lale zakiyi ki koma ruwa zabura tayi cike da mamaki" haba rakiya tsofai tsofai dani,kuma fa karki mance ina da saurayin ɗa  bandama ban haihu da wuri ba da yanzu ina da guda uku kafinshi"tsaya tukunnan saratu badai kina jinin al'ada ba" inayi amman wani fannin nakanyi wata biyu zuwa uku kafin nayi" kinga koma kin daina zamu dawo dashi ki samo yaro a manna mishi" a,a rakiya ina ganin wannan hanyar bamai bullewa bace mutuminan yafasan baya haihuwa"to ba yana da sani ba, yasani idan Allah yaga dama zai iya juya lamarinsa ke kodama ya gane dole ya yadda nasani kodan tsira da mutuncinsa, haj Hauwa ta dinga jinjina kai alamar zancen ya shigeta,ammanfa sai kin bude bakin aljihu idan da kuruciya ke za'ake biya idan kuma kin zama iya ke zaki biya,kuma biya mai kyau dazaran komai ya kankama yanzu zaki ga kin zama yarinya,amman kuma sai fa kina hadawa da gyara naga yanzu duk kin sukurkuce kamar bakeba dan yaro bazai baki hadin kai kina tsaminnan ba jibeki kin sanya kaya mai kyau harda su janbaki sai dai gashi sai wani bashi'bashi kikeyi ga tsami nasan awannan hamamin danake ji kin kai sati bakiyi wankaba,"a,a ke Kuma banson cin fuska" kinsanni tin da bana barin abu aciki batare da na amayar ba nasani yadda kike wannan warin na tabbata pant din dake jikinki ba karamin doyi yake ba Kuma--tayi saurin katseta "waike rakiya kin mance wacece ni " yo koma wacece kedai kinsan ba,a bakin komai nake ganinki ba sabida tun muna fita da dan bantai muke tare kinsan ke ba komai bace face matsiya ciya wadda bata da cin yau mune ma muke taimakawa gidan ku da guntattakin abincin da yaran gidan mu sukaci suka rage"haba rakiya wannan cin fuskar yayi yawa,ko kin mance ni mamanku take rikewa nake rakata gun kwaraten ta yawan ma danakeyi ada ai ita ta sanyani a hanya" Kinga to mubar zance haka muyi abinda ke gabanmu haj Hauwa sai cika da batsewa take" haba tawan saki rai mana muyi shawarar yadda zamu ci arziki mubarshi amazaunin sa" hehehe mubarshi fa kika ce ai shi wannan arzikin sai mun cinyeshi tas ko kale bazamu bariba suka kwashe da dariya tare da tafawa" shegiyas ashe har yanzu bakin halin nanan. ------------------------------------ Karfe goma Sha daya da rabi na dare ikhlas ce keta faman Kai komo idanunta a rintse rike da littafi a hannu da alama tana son tabbatar da cewar haddar da take kokarin yi ya zauna mata akanta  sai dai ga mamaki ta wannan karon haddar taki zama innillahi wa'inna ilaihim raju'un wannan shine karo na farko da hakan ta faru da ita wayyo Allah wai meke shirin faruwa da ita ne? ta koma ta zauna gaba daya tunanin zaruk ya hanata sukuni.    kwance da ammi agado  yadan bude ido ahankali sabida sautin karatun ikhlas da yaji da sauri ya diro daga gado ya kinkimi flast din shayi sai yajishi babu nauyi alamar Babu komi aciki ya ja tsaki.     Ammi tadan dago Kai.     "Indai shayi ne na shanye". "amman dai kinsan ikhlas zata bukata ko" yafada cike da takaici. "shikenan sai naki Sha sabida bukatar ikhlas. Ta koma ta kwanta taja bargo ta rufe kai. Mikewa yayi ya dauki flast din ya shiga kitchen ya kunna gas ya dora wani tea din baibar gunba sai da shayi ya kammalu ya juye cikin flast sannan ya nufi dakinta. Ita kam ikhlass tasake mikewa tana zagawa cikin karatu tare da sake rintse i cikin rashin sani ta bangaji abban nata har sai da flast din ya kusa faduwa da sauri ta bude idanunta. " Sannu Abu bansan ka shigoba. Yayi murmushi Mai tattare da  kulawa. " Sannu da himma ikhlas,mamanki ta ce ta kawo miki nescafe din naki ko? " Eh. Ya ajiye flast din dake rike a hannunsa " kifa dinga amfani da nescefe shi zai taimaka miki wajen karatun ki baza kiji bacci ba. Ta dan jinjina kai alamar to. " Zanje na wanke uniform Inna gama sai na Sha tea din. Yayi murmushi . "Sai dai kijira nefa kuma sukawo wuta kiyi gugan ,na wankesu tun dazu. Ya juya ya fita ta koma ta zauna agefen gado kaunar Abu na kara ratsa zuciyar ta,duk yadda yake takure ta amman yadda yake nuna mata kulawa tanaji babu Wanda ya kaita sa,an samun uba. Acan karkashin zuciyar ta tausayawa kanta takeyi da ta yadda ta sake soyayyar wanda bata sani ba ya hudata, ta yadda koda mai abban ta zayyi bata jin zata iya rayuwa batare da shi ba. Wannan kenan. Ahankali ta ware idanunta yayin da hasken rana ya dallare mata idanu abu biyu ne ya fado mata makarar yin sallar asuba sai gugan uniform . "Subhanallahi, Tayi saurin dirowa daga gado zata fita ta hangi uniform din nata a kan dirowa. Ta kada Kai cikin murmushi tasan wannan aikin Abu ne,ta fada bathroom tayi wanka tare da dauro alwala ta haukan dadduma tayi sallah bayan ta idar ta zauna ta rasa addu, ar da za tayi kamar yadda Ammi tace a duk lokacin da tayi sallah ta dinga rokawa kanta samun miji na gari, jitakeyi aranta Zaruk din miji ne na gari tsintar kanta tayi da fadin Allah ka sassauta zuciyar Abu ya amince mini zaruk ya zamo abokin rayuwa ta,ta yaya, wani bangare daga cikin zuciyar ta tayi mata wannan tambayar ras taji gabata ya buga da sauri ta kwautar da wannan tunanin muryar Ammi taji tana kwala mata kira da sauri ta mike.   Alhaji Ibrahim zaune a darning table suna karyawa ikhlas ta fito cikin Shirin makaranta ta durkusa har kasa ta gaidasu ta koma ta zauna agaggwuce ta fara cin abincin  Wanda taci baikai ya kawoba ta sunkuci Jakarta zata fice. "Abu sai na dawo,ammi natafi. da sauri Ammi ta dauko raguwar break din nata ta juye mata cikin wata yar karamar roba Mai murfi ta zuge jakar ta  Wanda ke goye abayanta ta zira aciki. Gudu gudu sauri sauri ikhlas ta fice a gidan. Alhaji Ibrahim yana kokarin yiwa Ammi magana Handset din Sa ya shiga ruri yayi saurin dauka yadade suna musayar magana daganan ya aje wayar cike da farin ciki. Tunda ya fara wayar ammi ta kafeshi da ido ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ya aje wayar tana kallonsa. "Yarki fa likafa nata ci gaba,yanzu haka ansanya sunanta agasar da za,ayi acan  abuja  sannan idan har ikhlass tazo koda ta biyar ne  za,a  a fita kasar London kafinma mu je candin sai munje mun sauke farali anyi mana alkawarim zamu sake komawa mu sauke farali lalle lu'ulu'una kyauta ce daga Allah. "Amman baka ganin idan wannan abin yayi yawa za,a dinga jin tsoron dosanta da sunan aure. Wani irin zabura yayi. "Ke kina da hankali kuwa,tabbas na yadda baki San ciwon kanki ba,aini kiga nayiwa lu'ulu'una aure sai naga ta taka kololuwar matsayi a ilimi. Ammi ta katseshi da fadin " Kana son kace koda mijii yazo bazatayi aure ba? "Kinga jinan, wallahi ko dan gidan dangwatai ne ya zo neman aurenta sai na cika burina kan na aurar da ita gareshi in bazai jira ba ya kara gaba,ni nafison ta Sami arziki na kashin kanta ba na mijin ta Wanda ko yaushe zai dingayi mata gori ba ita kadai fa na mallaka sai na baiwa kowa kunya akanta bazata yi irin rayuwar danayi ba muddin ina raye sai ta zama a bar kwatance. Ammi kawai jinjina Kai takeyi cike da takaici. "Amman yakamata ka sani tuni ubangiji ya gama tsara mata rayuwar ta. Kafin ya yi magana ta mike tabar gun dan ta tabbatar ta baro rigima muddin bata dan kwaice daga gun ba.   Bayan an tashi a makaranta ta dade tsaye tana Jiran napep duk Wanda ta tsare sai yace ba nan zaiyi ba Iphone dinta ya soma ringing ta dubi fuskar wayar. "Wayyo Allah Abu ne.. Ta ratsa Kore tare da kafe wayar a kunne. "Ina kika tsaya kusan awa guda da tashi?. "Abu mota nake jira har yanzu bansamo ba Amman insha Allah yanzu zan karaso. "To shikenan sai kin dawo. Ta maida wayar cikin jaka ta soma tafiya cikin hanzari wani dattijo Mai napep ya hangeta har ya wuce ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita ya dawo da baya yayi parking hadi da dan leko da Kai . "Ina zakije? Kamar zatayi kuka. "Sharada. "Bisimillah,shigo muje. Tunda ta shiga napep take ta faman sake sake. "Munzo sharadan. Tayi firgigita tana kokarin dauko masa kudi dari biyar ta mika masa ta sauka zata tafi. "Tsaya ki karbi canjinki. "Kaje kawai . "Nagode sosai. Sai da yaja babur din ta gane bai kaiga inda takeson tsayawa ba duk taji ba dadi tabbas yau zatasha tafiyar ƙafa gashi tabashi dukkan kudin ballantana ta sake shiga wani,kwanar mai kwaikwa zuwa masallacin juma,a na sharada akwai tazara yazatayi? Wata tsohuwa ta hanga rike da uban kullin kaya har rankwafawa ta danyi tafe take dakyar tausayi ya kamata tuni ta mance da tata matsalar. BILKISU H MUHD,✍️ [18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_              _BY_ *BILKISU H MUHD* Phone 08031307884 Page 3 *MARUBUCIYAR* ILLAR SABO RASHIN RABO YA YI SAKE ZAFIN HAWAYE NA BAKIN KAZAFI WAYA FI SONTA GORO DA SANKARA JINI BIYU DACEWA KAUNA CE BAYAN KUSKURE MATSALAR KAUNA TARAIRAYA DAKE NA DACE AKWAI BANBANCI BAKIN KAZAFI MULKIN MALLAKA IZZATU BAYAN KUSKURE KA AURE NI KYAUTAR ZUCIYA *sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.* makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba. Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻 Wattpad:👇🏻 @bilkishmuhd Arewa Book:👇🏻 bilkisuhmuhd WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻 https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t ------------------💥 Tunda ya rasa mahaifi sa yake ji shi tamkar wanda aka dauke shi daga cikin inuwa aka maida shi tsakiyar kwalleriyar rana, Amman bai san mai yasa ba haduwarsa da Aisha ya sauya komi, itace wacca ruhinsa

Chapter 2 of 5