Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels JARUMAN DUNIYA Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp Number 08137237071 A wani zamani can baya mai tsawo daya shude,lokacin da jahilci yayi katutu a zukatan bil'adama, karfi da jarumtaka suka zamo jari,rashin tausayi da adalci yayi kaura da zukatan mutane. A lokacin an yi wata nahiya a yankin ƙasashen larabawa mai suna mufrad. Nahiyar mufard tayi kaurin suna a fagen yake-yake,zalunci da sihiri, Duk sarkin daya fi dan uwansa karfin runduna ko na sihiri sai ya yake sa ya mamaye kasar sa ta dawo izuwa karkashin mulkin sa. Akwai manyan kasashe guda biyu da su kayi fice anahiyar. Ƙasa ta farko ana kiran ta da suna madinatul-husuf,sarki Baddadul-arus shi ne ke rike da kambun mulkin ta. Sarki Baddadul-arus yakasance garjejepn kato mai kirar samudawan farko yana da matukar jarumtaka dadin dadawa kuma yakasance mashahurin matsafi. Yana da wata kyakkyawar ya guda ɗaya mai su na uzaima, uzaima ta taso cikin gata da kwanciyar hankali kuma ta kasance basadaukiya mace maikamar maza. Duk lokacin da sarki Baddadhl-arus zai kai farmaki wata kasa shi da yarsa uzaima kadai suke yakar garin su yiwa sarkin JUYIN MULKI. A rayuwar sarki Baddadul-arus babu abinda yake so sama da wannan ya tashi, bisa wannan dalili ne yasanya duk inda zashi baya rabuwa da ita face kwanciyar barci. Ƙasa ta biyu kuwa ana kiranta da suna Darul-kushur,sarki Himras ne ke mulkin ta,sarki Himras ya kasance gwarzon mayaƙi mai tarwatsa maza afilin daga, ya shahara ainun a sanin ɗalasiman tsafi da tarin dukiya. Yana da ɗa guda ɗaya mai suna muzaifar, Yarima muzaifar ya kasance kyakkyawan gaske kuma gwarzon duniya, Domin shi kaɗai ya na iya baje gari guda ya ci su da yaƙi batare da wani ya taimaka mashi ba. Saboda matuƙar jarumtakar shi yasa wasu suke ganin cewa yafi mahaifinshi sarki Himras ƙarfin damtse Gaba ɗaya jama'ar birnin Darul-kushur suna matukar tsoran yarima muzaifar kasancewar shi azzalumi maras tausayi. A ƙasar Darul-kushur akwai ƙananan sarakuna guda bakwai dukkanin su suna karkashin mulkin sarki Himras, Duk shekara sarakun kan biya Himras harajin da yakai dinare miliyan takwas da dubu ɗari biyar gaba ɗaya sarakunan sarki himras ne yayi musu juyin mulki ta karfin tsiya. *** Gaba ɗaya wadannan sarakuna biyu, sarki Himras da sarki Baddadhl-arus sun kasance abokan gabar juna, A kan hakan sun gwabza yaƙi sau arba'in da biyu amma ɗayan su baya samun nasara sai dai ayi ragas! Burin dayansu shi ne ya yiwa abokin gabarsa juyin mulki ya zamana shine sarkin sarakunan nahiyar baki daya. Saboda tsananin gabar dake tsakanin sarakunan biyu, babu wanda ɗan kasar shi ya isa ya shiga ƙasar ɗayan face hukuncin kisa ya tabbata akanshi. Gimbiya uzaima da yarima muzaifar suna matuƙar gaba da juna wacce ta huce ta haifansu. Lokacin da sarakunan biyu su ka fahimci cewa bazasu iya kawar da juna da karfin runduna ba sai dukkanin su su ka nutsa cikin halarar tsafin su domin su gano hanyar da ɗayansu zai iya mallakar nahiya. A rana guda sarakunan su ka gano mafitar, sai dai mafitar nada matukar wahalar gaske. Abin da sarakunan su ka gano shine ɗayan su bazai samu nasarar kawar da abokin gabar sa ba face ya mallaki wadansu abubuwa masu wahalar gaske waɗanda nemo su dai dai yake da buɗe taskar ANNOBA DARI. Da farko dai sarakunan zasu mallaki wata salƙar tsafi dake ajiye a wani tsohon ƙabari abirnin rum, shi dai ƙabarin an gina shi ne a cikin wani ɗaki yau shekaru ɗari tara babu wanda ya taɓa shiga inda ƙabarin yake. Asalin ƙabarin na wani hatsabibin boka ne da ya yi mulki a birnin na Rum. Idan mutum ya mallaki wannan sarƙa da ita zai yi amfani wajen tashin wani boka a birnin kisra. wannan boka shi ne kadai yasan dokoki da ƙa'idojin tafiyar da sarakunan zasu yi, wannan boka ana kiran shi da suna sharubu, a yanzu haka ya shekara ɗari bakwai da mutuwa. Abu na biyu da sarakunan zasu mallaka shi ne, SIHIRTACCEN KUNDI dake ajiye a cikin wata tsohuwar rijiya a can fadar boka zammar da zamanin shu ya shuɗe a can baya. Abu na ƙarshe da sarakunan zasu mallaka ita ce wata sihirtacciyar takobi da akewa laƙabi da TAKOBI SIHIRI, Takobin tana ajiya ne a fadar sarkin bokayen duniya na uku. Baza a samu damar shiga fadar ba face an karanta waɗansu ɗalasiman tsafi dake cikin wancan SIHIRTACCEN KUNDI. Takobin tana ɗauke da wadan su sirrika guda hudu. sirri na farko shine idan mutum yana tare da ita babu wani tsafi dazai yi tasiri akan shi. Sirri na biyu shine dukkan abin da ka sara da takobin walau mutum ko aljan nan take zai zagwanye ya narke. Sirri na uku idan mutun ya mallake ta zai zamo abin tsoro a cikin yan uwanshi mutane kuma zai iya sarrafa ta yadda ya ga dama. Bokayen duniya sunyi ittifaƙin cewa a kaf sarakunan aljanu na duniya ba a taɓa yin hatsabibi kamar boka Ayyamul-layal ba, domin shi kaɗai ne ya taɓa yaƙar rabin sarakunan duniya su ka dawo ƙarƙashin mulkinshi. Bai kai ga yaƙar sauran ba rai ya yi halin shi sakamakon gwanbza yaƙi da yayi da wani jarumi ma'abocin addinin musulunci. Kafin mutum ya isa fadar boka Ayyamul- layal sai ya ketare waɗansu miyagun dazuzzuka guda tara. Har yau har gobe bokaye sun gaza gano adadin musibun dake tattare da dazuzzukan. lokacin da sarakunan biyu su kaga gagarumin aikin dake gaban su na ɗaukoTAKOBIN SIHIRI sai hankalansu ya dugunzuma ainun domin suna ganin ajali zai iya riskar su kafin su cika burin su amma da suka tuna irin gabar da ke tsakanin su sai kowanne ya yi aniyar shiga duniya mallako takobin. *** Wata rana daga cikin ranakun da yarima muzaifar kan zagayawa cikin gari domin yin nisaɗi da walwala. Yana tafe akan ingarman doki shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro, waɗansu irin samudawan dakaru masu jajayen tufafi na take mashi baya. kallo ɗaya za ka yi musu kasance cewa sun cika ZARATAN MAYAKA masu dakakkiyar zuciya, gaba ɗaya dakarun su na ɗauke da miyagun makamai masu barazana ga duk wata halitta mai numfashi. Lokacin da yarima muzaifar da waɗannan dakaru su ka cigaba da tafiya a cikin babbar birnin Darul-kushur, sai ya zamana cewa duk inda jama'a suka hangosu sai kaga sun tarwatse tamkar sun ga mutuwarsu, Masu kasuwanci ba a barsu a baya ba domin tattare hajar su su ke yi suna cika wandunansu da iska saboda tashin hankali. Idan kuwa har su yarima da dakarun sa suka riska mutum bai gudu ba, Nan take dakarun zasu gabzawa mutum duka da kulaken dake hannunsu take zai faɗi ƙasa matacce ko shurawa bazai yi ba. Sai da yarima da dakarun suka shafe sa'a uku suna tafiya babu sassauci, Ana cikin wannan tafiya ne yarima muzaifar ya fahimci cewa dokinshi yana bukatar ya sha ruwa, koda gama ayyana hakan sai yarima ya hangi wata hijiya nesa kaɗan da inda suke ga jama'a nan A wajen wasu na shayar da dabbobin su wasu suna ɗauraye tufafinsu. Nan take yarima yasakarwa dokinshi linzami ya durfafi rijiyar. Ai kuwa koda mutanen dake wajen suka hango su yarima sai suka cika wandon su da iska su ka bar wajen tamkar sun hango mutuwarsu, kafin kiftawar ido babu kowa a wajen sai wata budurwa da wani tsoho tukuf ne basu gudu ba. Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa yarima kai kenan kuma ya bashi mamaki, Domin tun da yake fitowa rangadi hakan bai taɓa faruwa ba. Shin wannan budurwa mai take taƙama da shi da har zata gan shi bata razana ba. Abin da yafi Ɗaure yarima muzaifar kai shi ne tufafin dake jikin budurwar sun kasance tsofaffi tukuf!, saboda tsufan su har waɗanda ke jikin tsohon sun fi nata Tsafta kuma budurwar bata tare da wani makami ajikinta da za tayi taƙama da shi. Dakarun dake bayan yarima kuwa sai zuciyar su ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone jikkunansu su ka kama tsuma, kawai umarni suke jira su afkawa budurwar. Da isowar su yarima bakin rijiyar sai kawai yaga budurwar taci gaba da ɗebe ruwa Guga tana zubawa a salkarta batare da ta waigo ta dube shi ba, sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata kone, har dakarun dake bayanshi sun yunƙura zasu afkawa budurwar sai kawai yarima ya rike linzamin dokinshi ya sauko ƙasa, ya taka da kafafunshi har izuwa inda budurwar take ya dube ta yana mai dakamata tsawa yace. "wace ce ke da bazaki girmamani kamar yadda jama'a ke girma ma ni ba? Ba tare da budurwar ta ba shi amsar tambayar ba, kawai taci gaba da ɗebe ruwan tana zuba acikin salkarta. Al,amarin daya ƙara fusata yarima muzaifar kenan bisa ganin cewa ya mace wacce ba kowa ba, tana wulaƙantashi a matsayinshi na hamshaƙin BASARAKE kuma GWARZON DUNIYA. cikin fushi yarima ya kai mata wawan naushi a gefan kuncinta na hagu da nufin bazar da ita a kasa. Cikin gwanin ta kyakkyawar budurwar ta sunkuya hannun yarima ya naushi iska. Nan take su kacame da azababban yaƙi suka wanzu suna kaiwa juna naushi da bugu hannu da ƙafa cikin matukar zafin nama JURIYA DA BAJINTA, A wasu lokutan sai kaga budurwar ta daka tsalle ta raba kafafunta biyu akan rijiyar tana cigaba da kaiwa yarima muzaifar naushi da bugu cikin zafin nama naban al'ajabi. Duk wannan artabu da ake fafatawa tsakanin yarima muzaifar da kyakkyawar budurwar daga can nesa mutane sun buɗe tagoginsu suna kallon abinda ke faruwa. Koda su ka ga irin masifaffan yakin da a ke yi sai suka cika da marukar mamaki. Abin da ya basu mamakin shi ne wai ace yau yarima ne ke fafata yaƙi da ya mace. Nan take su ka raya a zuckatansu cewa an ya kuwa wannan jaruma ba gimbiya uzaima ba ce yar sarki Baddadul arus tayo badda kama domin ta yaki yarima muzaifar?. Amsar tambayoyin da su ka kasa bawa kansu kenan kawai su ka zuba idanu domin su ga abinda zai faru. Koda yarima yaga an shafe sa'a ɗaya ba tare da ya samu nasara akan budurwar ba, sai kawai ya canza salon fadanshi, inda ya dunga daka tsalle yana kaiwa budurwar naushi da bugu hannu da ƙafa. Wohoho! tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da su ka ce "idan kaga ki gudu to fa sa gudu ne bai zoba." kuma haƙiƙa idan gwani ya haɗu da gwani dola ne ƙananan jarumai su zamo yan kallo. To hakanne ya faru da dakarun birnin domin ana cikin wannan yaƙi ne su ka rugo izuwa wajen ɗauke da miyagun makamai. ko da suka ga irin baƙin artabun da ake yi sai suka koma gefe guda suka zuba idanu. Ana cikin wannan yaƙi ne wani tunani ya fadowa yarima muzaifar, Tunanin kuwa shine "wai wannan wata irin hatsabibiyar jaruma ce yau ya haɗu da ita wacce take nema ta kunya tashi a gaban jama'a, lallai fa wannan shi ne masu iya magana ke cewa "Gaba da gabanta aljani ya taka wuta". ko da gama tunanin hakan sai yarima ya yiwa dakarunshi inkiya ta wutsiyar ido dake nuni da basu umarni. Kamar dakarun jira suke sai kawai su ka ɗaga makamansu sama suna ihu da kururuwa mai firgitarwa su ka yunkura izuwa kan wannan tsoho makaho mahaifin budurwar domin su hallakashi. ko da ya rage bai fi saura taku shida su afka masa ba, kwatsam! bazato babu tsammani sai makahon ya dako wawan tsalle daga inda yake sannan ya sanya kirjinshi ya daki kirjin ɗaya daga cikin dakarun da dukkan karfinshi saboda karfin dukan sai da badakaren yayi sama tamkar an janyeshi da kugiya sannan daga bisani ya faɗo ƙasa tim! tamkar an jefar da bijimin sa. Ko da ganin hakan sai sauran dakarun su ka firgice bisa ganin yadda tsohon makaho yayi wannan bajinta haka lallai akwai alamar tambaya ?. kawai sai suka afkawa ma shi da azababban yaki suka shiga kai ma shi sara da suka da makamansu gami da bugu da kulakensu. Shi kuwa ya wanzu yana kare hare-haren su da sandar da yake dogarawa tare da mayar da martani cikin Matuƙar JURIYA DA BAJINTA taban al'ajabi. Da ace mutum yana wajen lokacin da ake fafata wannan yaƙi sai ya rantse yace tsohon yakasance mai idanu ba makawo ba. kallo ɗaya mutum zai yi ma shi ya fahimci cewa a lokacin da yake samartaka ya cika GWARZON DUNIYA, mai karfi na Allah ya isa koda cewar ya tsufa akwai alamun sadaukantaka a tare dashi. kaico! nanfa makahon ya zamewa dakarun alaƙaƙai kuma kadangaren bakin tulu suka rasa yadda zasu yi dashi ya wanzu yana mako su daga kan dawakansu su na yin MUGUWAR HALLAKA. Koda yarima muzaifar ya kyallara idanu, yaga halin da dakarunshk ke ciki sai zuciyarshi ta harzuƙa fiye da ko yaushe. kawai sai ya shammaci budurwar ya gabza ma ta wawan naushi afuska a lokacin data raba kafafunta biyu akan bakin rijiyar. Ai kuwa sai kafarta ta zame ta fada cikin rijiyar amma sai ta tokare da wani dutse sannan ta maidawa yarima martanin naushin a lokacin da ya daka tsalle ya dira abakin rijiyar. Nan take ƙafafun yarima su ka zame ya afka cikin rijiyar, Amma saboda gwaninta irin ta JARUMAN DUNIYA sai ya ƙi yarda ya kai ƙarshen rijiyar ya rarraba kafafunshi a tsakanin rijiyar su ka cigaba da kaiwa juna naushi da bugu a hakan cikin juriya da nacin tsiya. Tabbas yau yarima muzaifar yayi gamo da mace mai kamar maza kuma BASADAUKIYA UWAR SADAUKAI. Sai da rabin sa'a ta shuɗe su na kaiwa juna naushi da bugu, Duk sa'adda ɗayan su ya naushi ɗan uwanshi sai kaga ya gwara kan shi da jikin rijiyar kuma yayi kasa lu! zai afka rijiyar amma sai kaga ya turje ya mayar da martani. Babu abin da zai bawa mutum mamaki ga jaruman biyu face yadda su ka shafe lokaci mai tsawo su na artabu ta hanyar yiwa juna lugudan naushi amma ko kaɗan babu alamun gajiya a tare dasu. Ana cikin wannan yaƙi ne Budurwar ta shammaci yarima muzaifar ta gabza masa naushi a fuska kanshi ya gwaru da jikin rijiyar, ya tsage jini yayi tsartuwa saboda tsananin zafin da yarima ya ji bai san sa'adda ya tsandara ihu ba kafafunshi suka zame ya afka ciki. koda samun wannan gagarumar nasara sai kyakkyawar budurwar ta sunkuyar da kanta ƙasa tana mai kallon yarima dake kwance tsamo-tsamo acikin ruwan, tana mai yi ma shi murmushi mai taushi. Sannan ta shiga kama bangon rijiyar tana yo sama kamar yadda kadangare yake tafiya a jikin garu. koda fitowar kyakkyawar budurwar daga cikin rijiyar. Dakarun dake yaƙi da mahaifinta su kayi arba da ita sai dukkaninsu su ka dakatar da yaƙin su ka ja da baya a tsora ce. kyakkyawar budurwar ta tsugunna ƙasa ta ɗauki salkar ruwanta ta rayata a gadon bayanta sannan ta je ta kama hannun mahaifinta suka juya su ka tafi gaba ɗaya dakarun dake wajen su ka bisu da kallo cike da matukar mamaki da al,ajabi. Ana cikin wannan hali ne yarima muzaifar ya fito daga cikin rijiyar jikinshi ya jiƙe sharkaf da ruwa ga kanshi ya tsage jini yana zuba. koda dakarun su kayi arba da halin da yarima yake ciki sai hankulansu yayi mummunan tashi kuma a ka ra sa wanda zai tare sa. Shi kuwa yarima sai ya kura kyakkyawar budurwar idanu batare da yayi yunƙurin komai ba, kawai sai a ka ga budurwar ta tsaya cak sannan ta waigo tare da yiwa junan su lallausan murmushi a lokaci guda su duka biyun su kaji sun kamu da matuƙar soyayyar junan su. kyakkyawar budurwar ta ɗauke dubanta daga na yarima su ka ci gaba da tafiya sai dai su yarima su ka daina hango su. jiki a sanyaye yarima ya je ya kama linzamin dokinshi yayi gaba, Sauran dakarun su ka mara ma shi baya suna masu zaburar dawakansu. Tun da aka fara wannan tafiya har aka iso gidan sarauta yarima bai ce kalaba. ***** Fada ce ƙasaitacciya da aka ƙawata ta da kayan alatun jin dadin rayuwar duniya, Duk isar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin wannan fada dola ne ya zamo cikekken ɗan kauye kuma ya rai na kanshi. Zaune a bisa karagar mulkin, sarki Baddadul-arus ne. Sarki Baddadul-arus yakasance garjejen kato mai kama da giwa yana da ɗan mitsitsin kai da katon ciki tamkar an kifa ƙwarya a habarshi yana da ɗan mitsitsin gemu fari rol! da tsawon shi bai huce kamu ɗaya ba. A gefen hannunshi na dama gimbiya uzaima ce, zaune a bisa wata kayatacciyar kujera ta alfarma ta na sanye da tsaleliyar alkyabba mai fatsi-fatsi, shigar tayi matukar fito da kyawun surar jikin ta. Haƙiƙa duk inda kyawu yake gimbiya uzaima ta cika kyakkyawa domin ko gasar kyau Za ayi zata iya zamowa ta daya. A wannan lokaci gaba ɗaya mutanen fadar babu abinda su ke kallo face satar kallon gimbiya uzaima, kai bama maza hatta 'yan uwanta mata idan su kayi arba da ita sai kaga sun wan game bakunan su suna dalalar da yawu, saboda yadda kyawun ta ya burgesu. Gaba ɗaya fadar tayi tsit! tamkar mutuwa ta gifta, Daga can sai gimbiya ta katse shirun daya wanzu ta dubi mahaifinta sannan ta buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai daɗi tamkar sarewa tace "ya Abbana wai yaushe ne zamu tafiya nemo abubuwa guda uku domin mallakar TAKOBIN SIHIRI ?, Tabbas na ƙagu naga anyi wannan tafiya domin na sake yin ido biyu da abokin gaba ta yarima muzaifar domin ayi ta takare. Koda jin wannan tambaya daga bakin uzaima sai sarki Baddadul-arus ya bushe da dariyar mugunta har da kyakyatawa sannan daga bisani ya dubi uzaima yace "ya yata mafi soyuwa agareni kiyi sani cewa bakomai ne ya hanamu tafiya nemo abubuwa uku ba domin mallakar TAKOBIN SIHIRI ba sai domin akwai wani sauran birni guda daya da nake so na cinye shi da yaƙi, dazarar na kammala zamu fara shirye -shiryen tafiya, ina fatan kin gamsu da wannan bayani. Uzaima ta gyaɗa kai alamar gamsuwa sannan ta buɗi baki a karo na biyu tace,

Chapter 1 of 2