fada gadon tana kuka lallai tai kuskuren rike namiji garkuwa tun ba'aje ko inaba ma yanai mata gori fuuu ya fice yabar dakin.
Kanwata
Na F.A.Ya'u
Saida ya fita yadan xauna sannan hankalinsa ya bashi tabvas bai kyauta mataba abinda yai mata ya fara dawo masa kukanta na ratsa kwanyarsa.
Ahankula ya shiga dakin har yanxu kukan take tausayinta yakara kamashi inda take yaje yadagota haba tawan kukan ya isa haka atakaice adaren suka shirya yai tai mata dadin baki da alkawarirrika kala kala har yasamu ta aminta da batun auran ida yavama kudin hado lefe komai biyu yace ta siyo.
Ita da fadya yawanci ke fita wani sa inma fadyar ke xaba dan xatonta kayan hai huwa take hadawa tunda cikinta wata bakwai.
Kanwata
Na F.A.Ya'u
Angama komai dai dai yau fara na xaune farhan ya shigo rike da ibi lpy naga kamar kana cikin damuwa kedai bari na rasa yadda xanyi inma fadya mganar auran haryaufa batasan da batunba baba yace dole sena fada mt da kaina tai dariya kabarmin komai ta karbi ibi din ta mike ina xuwa tai dakin da fadyar take tana xaune tana chat ta kwace wayar gami da mika mata ibi din mene karanta afirgice ta mike baxai yuwuba wai wace fadyar ke mana da sauri xai waje ta rukota gami da zaunarta haba fadya maine haka bansanki da waytaba.
Wallahi baxai yiwuba ni na taba cemuku inasan farhan ne ni wallahi baxan aureshuba ai wannan tauye hakkine ke ba wanda kike so aka vakiba nima muhd nakeso haba kekuwa amaryarmu kikalli tsukeken mijina kice baki sansa ai fade kike to shi so anfada miki kyaune ni wallahi baxai yuwuba ina ganin mutunciki ki yi kokari mudore ayadda muke.
Dakuka tasamu ummanta haba umma anmin adalci kenan basai atambayi ra'ayina ba jafin xartarwa abbanta dake uwar daka ya leko sannu isasshiya dake kedin baxawarace ko duk yadda fadya xatai kan mgnar auren tasha ruwa tayi kowa yaki saurararta ala dole ta hakura..
Andaura aure inda fadya itama xata xauna cikin gidan sabon gurin da'aka yanka mata saidai tace ita gaskiya baxata xauna asabon gurinba tabarma yayarta kotadan samu saukin rashin mutuncin mutan gidan duda ba wai xata bar gidan bane tadai yu nesa da kadan dasu seta fito xata gansu haka kuwa akai.
Duk inda xaman lpy yakai sunayi ita da yayarta fara watansu uku da aure fara ta haifo diyarta mace taci sunan umman farhan marigayiya.
Kanwata
Na F.A.Ya'u.
Fadya ankammala karatu dan yanxu aikima take xamansu lpy fara bata taba nuna kyashi wajen aikin gida ba koda yakasance kuwa girkin fadyarne indai tana aiki haka take xagewa tai abinta.
Hakan yasanya itama fadya ko kadan bata kyashin kashe kudinta kan fara da yayanta dan ita har yanxu haihuwar shuru sunje asibiti ance ba wata matsala bace likacine baiba fadya ta toshe kunnenta ga duk wani abu da ake fadi agidan nasu kan fara tamata asiri bama ta nuna tasan da batun.
Albashinta na farko uku ta rabshi tai musu sayayya da daya daya ta aje daya kuma ta rarrabama yan uwa kusan rabin siyayyar ta fara da yaranta ce itakanta tasan fadya nasanta da xuciya daya take santa.
Cikin shekara fadya ta tara isasshen kudi tasai dan jaramin fili kan kace maine ta fara gini.
Kwanci tashi va wuya gida ya kannalu tsaf komai ta xuba dan jiyama sukaje ita da yayarta suka gani aiko fara sai yabon gidan take .
Umma so nake na baima fara gidan nan da na gina nasan kona baima yaya baxai karbaba inaso takoma can dan wallahi na gaji da abinda ake mata agidannan dako kin kyauta to kin fada mata a'a inaso inji mai xakice to Allah yasa albarka ta ce amin umma bari naje nasameta.
Tana xaune malan karami na sukuwa abayanta tace dan rikici kana nan kana damun ummankako yai dariya gami da xuwa ya fada jikinta ina takwarar tawa ta fice daxu baban ya daukesu ita da hajiya karama suka fice.
Daman wajenki naxo towo Allah yasa lpy tai dariya lpy kalau ta mika mata mukullai me xan dasu karbi mana ta karba gidan da mukaje jiya ne so nake nanda sati xaki koma hhh xadai mu koma ah aikinganshi gidan mace daya aiko ba'ayi haka ba saidai ke ki koma aiko wallahi baxan koma va towo haba kanwis maye na saurin rantsuwa to kin fadama yaya a'a umma xata fada masa godiya kam sai tashi tai tabar dakin dan tayi tayi tai shuru taki.
Shima farhan dakyar ya amince da batun komawar saida umma tai tabashi baki ya amince.
Kanwata
Na F.A.Ya'u
Cikin ikon Allah auransu yanada shekara biyar fara nada yaya hudu maryam wato hajiya karama malan karami sai sagira wato fadya sai dan karamin mai sunan babanta suke kiransa da Abi yayin da fadya keda shekara hudu cif da aure haryau ba bayani.
Cikin ikon Allah ance mahakurci mawadaci itama fadya saigata da nata cikin duk wani mai san fadya ya tayata murna.
Yaya na'am kanwis daman wata shawarace inajinki mai xaisa tunda aikin gwamnati yaki ka koma kasuwa yai dariya kumafa kinkawo shawara ban taba tunanin hakaba tosaidai kinga albashina bazai isa jariba tundabkina kallon yadda muke kaiwa dakyar yake kaimu wata to mai xai hana inbaka ina baxai yuwuba haba yaya wai dan Allah yaushe xaka yadda mun xama daya saidai ai dawajewa kiban bashi to shikenan na amince yai dariya to nagode Allah yasa da alkairi.
Cikin fadya ya tsufa sosai haihuwa koyau ko gobe yayin da kasuwancin farhan kullun sai bunkasa yake fiye da tunani dan harya biya fadya kudinta danma saida sukaso rigima dan cewatai baxata karba ba yasai filinsa a jan bilo haryafara gini danma yadan tsaya savida haihuwarnan.
Fara ba yadda bataiba kan fadya ta dawo suxauna dan su kula da ita tace ita ina tafisan xama gata ga ummanta haka suka hakura suka kyaleta.
Kanwata
Na F.A.Ya'u
Ciwon datakeji ya fuce tunaninta duda cikin darene haka ta tashi hajiya karama dake yaran suk suna guda anma barmata hajiya karama ta tashi dudu yarinyar ba wayo gareta sosaiba ta bata fitila maxa jeki ki kiramin umma da sauri ta fice dan vata da tsoro taje tana buga dakin waye nice anti ce tace na kiraki afirgice suka bude kofar tana ina tana daki takira kanwar fadyar maxa kuje ku kwanta keda hajiya karama tai dakin fadyar yanayin datake ciki ya wuce tunanin umma dole adaren suka wuce asibiti adaren su farhan suka xo asibitin.
Sai gefin asiba tasauka tasa wuya sosai dan harjini aka kara mata yaranta biyu haka ta haifosu lafiyayyu mace da na miji kowa kagani fakinsa wai.
Fara ce xaune gefen gadon tana rike da baby macen ke hotonki kawai kika dire tai dariya haka aketa cewa wallahi kamarku ta baci.
Umma daman inasan infada miki dan Allah in antashi sakama yarannan suna namijin asa masa sunan baba sulaiman wato baban farhan na gaskiya umma tai dariya ke ko kunya bakyaji yayan farine fa tai dariya umma kenan dan miko min su ban daukesuba datsu cikina na ciwo bakyajin kunya atso aganki dasu a hannu fara ta mike haba umma yanxufa andene wannan abin ta miko mata su umma ta mike badaniba axoganni agabana ake wannan rashin kunyar sukai dariya vaki daya fadya ta dago facen tana shafa kanta tabvas kamarmu daya ta mikawa fara duk subiyun tace rikesu naga ta rike nabar mikisi kirikesu har amana tai dariya kanwarmu kenan Allah sun dace dake da kika rike kamar naki tai dariya ai kayanki nawane dan haka yayanki nawa ko bakice kin banva tai dariya bacci nakeji vari nadan huta kafin cikina yakuma murdawa.
Baccin da bata farka ba kenan dan har wajen magariba in anxi dubiya saidai aga yara mai jego na bacci saida nurse mai xagajen yanma taxo taga anya kuwa tana da rai taje takira doctor aiko ba irin duban da basuyi mata va anman ina babu Allah ya karbi abarsa fara kam tai kuka kuka mai isarta duk wani da yasan fadya saida yai kuka musanman in aka kalli danyun jariran da ta bari dake anan take aiki a asibitin sukansu saida sukai kuka dan sun saba mace ce da kullum take maida komai ba komai ba komai akai mata.
Farhan kasa saka hannu yai gurin sakata akabari dakyar aka samu yasata xaman dirshan yai agun kabarin yana kuka dakyar da nasiha suka samu yataso yabar gun bayqn bakwai fara ta debi jariran suka dawo gida dan ita xata shayar dasu tunda daman awatannan xata yaye danta kawai saita barma umma svashi.
Kanwata
Na F.A.Ya'u
Mutuwar nan ta daki fara sosai dan takasa sakinta musanman inta kalli yaran tausayinsu sai ya cikata.
Ummi ce ta shigo da gudi da gwalan gwalantunta na yara momi kinga karami ko ta cafeta yana kokarin dukanta haba yaya kaifa babba ne mai taima ba itace ta cinye nata cake din ta hada da nawaba yi hakuri kaga kai vabvabe kaida xaka dinga siyo mata inka girma ni tabdi ya fice itama ta diro tabi bayansa da dan gudunta tai dariya yaro kenan yanxu kuma seta gansu tare.
Farhan yagama gidansa inda gidannan iya haduwa gidan ya hadu duk yadda yai dasu umma atare tare dasu suka ki dan haka nasu bangaren haka ya gyare musu shi inkana bangarensu baxaka taba tunanin awanna gidan kasar kake ba.
Dakyar da nasiha farhan ya ke ma babansa abubuwa duk kuwa abunda yake masa vaya gani dan matarsa kullun cikin xugashi rake kan wai yana fifitashi akan wani haka kawaima sai yaxo yaita bala'i wai sun mallake masa da sudai vasa ce nasa uffan dan sanin halinsa duda kuwa duk abinda farhan yai musu shi yake masa anman baya gani.
Koda ya tashi kai abban maka tare da baban nasa da daya kanin baban ya hada anman sai cewa yai wannan cun fuskane danmai baxai fara biya masa shi dayaba dan nuna musu shidinne ya haifeshi shidai vai ce masa komai ba sai hakuri da yai ta vashi.
Kanwata
Na F.A.Ya'u
Dakyar farhan yasha kan fara da nasiha kala kala kan ta daure taje ta nemi gafarar iyayanta dan haka yau ta shirya tsaf itada yan biyunta sai karami kayansu iri daya dan sauran yaran suna can vabban gida gun umma tace itama abarmata su dan kannen fadya sunyi aure namijin kuma yana makaranta.
Kai tsaye gidansu ta wuce komai na gidan ya sauya mata bakamar yadda ta barshi ba kamar ansake gyarashi ganinta a mota tsaf maigadi ya bude mata ta shiga matar ta karbetacikin fara'a da sakin fuska suka gaisa ina matar gidan ai nice ta xaro ido ke kuma eh mun sayi gidan ne sheka biyu da ta wuce ok ko xan iya sanin inda masu gidan suka koma ehto ban saniba gaskiya saidai ki tambayi mai gadi ok to xan tambayeshi na gode ta mike tavar falon.
A farfajiya ta suka hadu take tambayarsa eh yanxu suna dorayi ko xaka min kwatance nan yai mata kwatance ako vata koma gida ba ta wuce can.
Bata sha wuyava ta gano gidan dan lokon bamai wuya bane gidanma bata sha wuyaba tagano gidan da sallama ta shiga umnanta ba wanke wanke ta amsa da gami da saurin dagowa kamar miryar fara nice momi taxaro ido gami da bankawa daki fara dagaske kece ko mafarki nake nice umna but dad dinki yace kin mutu sai hawaye mutuwa umma wallahi van mutuba ki fito miyi mgn nan ta fito jiki na bari mum ki nutsu kitamaka ki tsaya ki saurareni ta xauna kwanaki kimanin shekaru biyu da xamu taso babanki ya gano komai yaje dan neman afuwarki ya tadda a gidan naku anyi mutuwa akace matar farhan ta rasu tare aka kai gawar dashi yaxo ya fadan tai shuru mum vani na rasuba kanwata nan sukai ra hirar yaushe gamo.
Dad ne ya shigo fara na bayi tana alwala maman fara ta fito rike da karami towo ina kika samu yaro tai dariya jikanka ne jikana kuma ya kamo hannun yaron ya sunanka sunana Hamza anman karami ake cemin a kace takwara bane yai dariya kaima karami ake cema eh amman kai vabbane kai wannan yaro da wayo kake ummi ce ta fito tana kuka ina mominta dan ita vata cuka sabiba irin yarannan ne nasu nacun uwa ah ashe yaran da yawa ya kamota tako kara tsanyara kuka fara ta futo da sauri ta dauketa to yar rigima takwantar da kai a girjinta tana saukarda ajiyar xuciya dad ya xaro idi wanake gani kamar fara nice dad yakalli mum tai masa murmushi jeka masallaci kadawo sai kaji komai.
Koda ya dawo ta fada masa yadda sukai yace ikon Allah rabon tun alokacin baxamu gana bane tace dad mai yadawo dakunan naje can kunsaida sai hawaye kuskurena ne bakomai ba haba dad mai yajawo kuka kayi hakuri in mgnta ko xuwana ya bata maka rai ko kusa basu suka batanba sai tuna abinda dan uwana yamin.
Kanwata
Na F.A.Ya'u
Tun bayan mukai mgnar auranki kika bujire tun lokacin naji tsanarki haka kawai banasan ganinki na rasa mai yasa sai bayan da akai auren yaya yaxo duk wata harkata ya shiga tsimdim dafarko komai normal dan nama manta dake yayinda a hankula inna kaka tafara canja min ko naje gunta bata shiga sabgata gai suwata ma tadena amsawa na rasa mai nai mata ahankula komai nawa ta dena karba saima ta hada kayanta ta koma gidan yaya.
Ban fiskanci komaiba saida aka gama cuta ta domin ina gida akaxo wai ansaida gidan nace kamar ya aka ban takarda naga sa hannun yaya naje nasameshi sai na taddashi a kujerata a gun aiki wai ai daman yai alkawari kuma alkawarinsa ya cika domin tun muna yara anfi sona agida komai ni shi kuma abin na masa ciwo angirma na fishi arxiki gashi har yanxu ummanmu tafison yata kan nasa shiyasa yaci burin sai ya rabani da komai dan inji bakin cikin da yakeji aduk sanda aka fifitani shiyasa yafara da rabani da diyata uwata da dukiyata aranar nai kuka nai kuka kamar mai haka yasa akamun korar kare yace jibima innaxo ansaida kamfanin itako inna kaka badamar ganinta dan yace kar abarni na shigar masa gida tsanata yasa aka sanya a xuciyarta ki yafemin komai ba lefina vane lefin asirine duda kuwa asirima na tadda hali tasa kuka dad nice xan nemi gafararka ni nakasa maka biyayya watakil danayi yaya salim ya aureni da duk hakan bata faruba.
Sai tara tabar gidan tabar musu karami dan yan biyu basa yadda da kowa sai ita sai vabansu in yan wulakancin suka motsa ko shi basa kulashi suna manne daita.
Kanwata
NaF.A.Ya'u
Washe gari fara ta aiko da mota dan su mum dinta suxo suga gidanta aiko tunda aka shawo lokon suke gwala la idanu dan kam duk lokon babu karamin gida basuga gidan da yai dai dai da farhanba ga mamakinsu gidan da yafi kowanne aka nufa dasu basu kara tsindima cikin mamakiba saida sukaga fara tsaye tana jiransu.
Dadi kasa shuru yai saida ya tambaya anya kuwa nanne fara tai dariya nanne mana das shima yajira baku isoba yace bara yaje ya dauko yara dan kugansu acan babban gida.
Basu dade da xamaba ya iso aikon farhanne saidai duk ya sauya kana kallonsa xakasan kudi sun xauna yakara kyau yai yar giba dai dai shi nan yagaidasu cike da ladabi dad yai tabashi hakuri yace aishi bai taba rike shiba.
Koda suka dawo gida cike da alkairi iri iri dad yace lallai ikon Allah sai kallo mum tace aini naga haka mutum ba'a bakin komai yakeba kedai bari naga ishara yanxu mukuma akiramu mai tace ai nikam batun yauba nadaukarma kaina alkawarin dena cin xarafin talaka yai dariya to muma cin ina kudin aimuma daya muke arxiki daga Allah kigadai yaronnan lokacin da nake cin mutuncinsa waxai ce xaiyi koda keke ne nasa segashi koda ace inada kudin vaxan kama kafa dashiba kinajifa har gwala gwalai yake da shagonsu a saudia da Dubai haka naji sudai haka sukai da danasaninsu kala kala.
Duk wani nauyi na su dad farhan keyi dan yanxu ya saimusu gida anan rijiyar xaki daman wanda suke ciki na dorayi na haya ne abubuwa sun fara komawa dai dai dan kasuwancinsa ma farhan ya sanya masa hannu ya kara masa jari ya fara far fadowa abu daya ya dameshi shine inna kanasu.
Kanwata
Na F.A.Ya'u
Shawarar da Fara ta kawo suka bi duk juma'a ana dafa abinci abaima almajirai sauka kuwa asati sai ai sau uku ko hudu addu'a ba kama hannun yaro kan Allah ya karya abinda akaima inna na farraku ita da dad.
Akace wanda ya kama addu'a baya danasani domin kuwa inna kaka yau ta tubure fada ita sai ankaita gurin danta yaya yanaji yana gani yadauketa har gidan kanin nasa dan yasan inda yake aiko anan ya sauketa ko gidan bai shigaba yajuya dan sunyi da matarsa akan yana kaita yaxo su koma gurin boka dan wani abin ita ke dorashi akai duda shima da bakar xuciyarsa.
Akan hanyarsu ta xuwa sikai hatsari nan take matar ta mace asibiti aka kira wayar hamxa bai bata lokaciba ya xo ganin halin da yayan nasa ke ciki ne ya daga masa hankali shi yai masa komai kafin yaje ya tawo da inna kaka da mum saida yaga komai normal yadauki gawar umma amarya sai gidan acan aka hadata aka kaita inka dauke yayanta ba wanda ya damu dan murnama suke sun rabu da masifa musanman ma sauran kishiyoyinta abinda kawai ya damesu kawai lpyar mai gidan.
Inna kaka na gefe yana kuka ya ruko hannunta inna ki taimaka kisa kanina ya yafemin itama tana kuka mune sanadi da tun farko muka dasa maka tsanar sa ta nuna banbanci mu muka kasa danne xuciyarmu.
Nikam tun farko ban rikeka ba lefina nadauka nagode kanina farama haka ya nemi gafarar ta tace ita tuni ta yafe masa.
Jinyarsa gaba daya inna kaka ce tai kulawa ta musanman take bashi duda tasan abune daxai gogeba tun farko sunyi kuskure na nuna ban vanci tsakanin yayan nasu.
Kanwata
Na F.A.Ya'u
Jiki kam yai sauki ansallami shi ya koma gida kullum inya xauna bashi da aiki sai rokar kanin nasa afuwa.
Kinsan me sai ka fada kasu wanci na na Malay nakesan xuwa sabida wasu abu buwa da suka taso kuma akalla xanyi watanni yakike gani tai dariya sai innemo maka yar yarinya ka aura katafi da abarka kwasha amarci yai dariya kinfiye xaulaya da gaske fa nake to ya xamuyi da yaranmu daman hutu suke suna babban gida karami yana gunsu dad se mu tafi da yan biyu sune daman dai matsala tai dariya to Allah ya nuna mn.
Duk wani shirinsu sun kammala angama komai fara taje duk tai sallama da yan uwa abinda ya vata mamaki shine dataje babban gida kowa sai nan nan ake da ita kamar ba itaba ce wadda suka dauki karan tsana suka dorama va abinda vata saniba shine duk abinda farhan ke musu yakance injita.
Baban yara na'am inajinki yako batun masallacinnan eh an gama inaso kafin mu tafi afara sallah yawwa na gode ranar da xa'a su tafi ta tace masa nasadaukar da masallacin ga kanwarmu yai dariya Allah yasa da alkairi danshi baisan iya abinda yai sadaukarwa ga kanwarsa mai sansa ba duda kasantuwar yayansu yara ne anman sun dorasu kan insunyi sallah ko kiran sallah suka jiyo su musu addu'a suyima umma fadya abin har ya xame musu jiki dai dai da yan biyu sun iya.
Harfilin jirgi aka raka su anata daga musu hannu tana rike da ummi yayinda farhan han ke rike da abi saida sukaga dagawar jirgin sannan suka watse.
Nima anan nake cewa Allah yakaisu lpy yabar so da kauna dan banda kudin binsu balle inkawo muku rayuwarsu a Malaysia.
Alhamdulillah Allah abin godiya da ya bani ikon kammala wannan littafi fatana ya amfanar.
Wani abu da nake san agane.
Banyi dan cin mutunciba ko bata sunan wani sai dan nishadan tarwa fadakarwa.
Wani abu game da labarin da nake san a fuskanta.
Mutum baya xama mutum har sai ya girmama mutum dan uwansa duk yadda kakejin kafi wannan mutumin bakasan irin baiwarsa ba bakasan yadda xata kaya maka ba akarshen rayuwarka.
Biyayya ga iyaye dolene komai sukai maka indai harkana san cigaban farin cikinka kamar yadda fara bata samu farin ciki mai dorewaba saida iyayanta suka yafe mata.
Gareku iyaye nuna ban banci tsakanin yayanku kan jawo musu kin juna da tabarbarewar xumunci ko kafisan daya daure kabar abin aranka treat them equal.
Manta alkairi ga wanda akaima bai xamto halin dana gariba kamar yadda fara ta kasa mantawa da karamci mutuncin fadya ga rayuwarta.
Godiya
Godiya ga duk wani ko wata da yabada lokacinsa wajen karanta wannan littafi fatan duk wani kuskure da'aka gani xa'amin afuwa dan adam axijine.
Taku har'abada
Fatima Aminu Ya'u
F.A.Ya'u
09028287218
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if