kifa tsabar sauri, ta ƙaraso gurinsa murya na rawa tace...
"Barka da isowa Alhaji" sai da ya ƙare mata kallo kafin yace "barka" kasancewarsa mai ƙaramin jiki yasa yawan shekarunsa ɓuya, sbda a ƙalla zaiyi shekaru hamsin a duniya, fari ne amma ba can ba, sannan yanada cikar zati da kwarjini gami da isa tare da tsaurarawa,
Har ta miƙe zata juya ya kirata da Cold voice ɗinsa, jikinta na rawa ta dawo ta tsuguna kafin tace "gani" ƙafafunsa suna saman table ya jingina kansa da kujera ya ɗan matso kusa kafin ya ɗaga hannu ya watsa mata Mari, da sauri ta miƙe ita ba kuka ba ita ba jimami ba, tana tsaye kanta a sunkuye yace "a gidanku haka kike yiwa mahaifinki ko dama baki samu ingantacciyar tarbiyya bane?"
Da sauri ta ɗago idanuwanta ta kalleshi, kafin ta juyar da kai gefe, a zuciyarta tana maimaita "da mahaifina yana da rai ko kallo baka isheni ba, duk da shiɗin talaka ne" ta faɗi hakan kusan sau uku, tsinkayo tsawar da ya daka mata da tayi ne yasa tai saurin barin gurin ta dawo kitchen, "sannu da Aiki Hajiya" Anum ta faɗa hawaye na shirin zubowa a idanunta, "yauwa sannu amma Anum banji daɗin abinda kikayiwa Dad ba yanzu ya kirani yake gayamin bakisan waye dad ba ko?"
"Hajiya kiyi haƙuri insha Allah hakan bazata sake faruwa ba"
Jumayma da Arshi suka fito,
📢kasancewar sunan Arshi yazo ɗaya da na ƙanwar Anum zamu dinga kiranta da sunan da Dad yake kiranta dashi, Little Hajo, sunan yayarsa kenan Hajo.
Dariyarsu da yaji ne yasa shi saurin ɗago kansa tare da faɗaɗa fara'arsa cike da nuna kulawa ya ware musu hannayensa alamar su taho, da gudu suka taho har suna rige rige, yana dariya yace "Jumayma kekam bakya girma" Little Hajo ta kamo hannunsa kafin tace "Dad munyi missing ɗinka amma dai bazaka ƙara komawa ba ko?" janyota yayi kana ya ɗorata a saman cinyarsa cike da nuna kulawa yace "idan kikace kar in koma zan zauna my Little" dariya tayi wanda yasa point ɗin dake kumatunta loɓawa kafin tace "Dad an kawo sabuwar ƴar aiki ka ganta?"
Sai a lokacin Jumayma dake gefen Dad ɗin tayi magana, "Dad Please ka ce ta koma gidansu nikam bana sonta"
"Big girl menene dalilin da yasa bakya sonta tayi miki wani abunne" Jumayma ta turo baki tare da gyaɗa kai alamar a'a,
"Idan har naga zata takura muku dole ta koma inda ta fito"
Dad ya faɗa yana mikewa tsaye, "Dad bakasha kunun ba ga ƙosan nan" Jumayma ta faɗa tana kallonsa, "eh kusha kawai"
Ya faɗa yana wucewa ciki,
Dad wani irin mutum ne, wanda idan har yayi faɗa akan abu to bazai cishi ba komi muƙaminsa kuma komai sonsa da abin.
Kai tsaye ɗakinsa ya wuce, mom kuma sun kammala komai dan ƙosan ma Jumayma ta bawa ta kawo ta ajiye masa, iya Anum ce a kitchen ɗin, itama da ta kammala ta dawo ɗakin da yake a mazaunin nata, ta zabga tagumi, tunani takeyi anya zamanta zai ɗore a wannan gidan kuwa?"
Tayi nisa a tunani taji an hankaɗo labule, cikin isa da gadara take cewa "ki tashi ki soyamin bread and egg yanzu yanzu" sam bata ma ɗauki murya ba, dan bata san wace a tsaye a kanta ba, sai da ta ɗago da idanunta ta kalleta kafin tace "dan Allah kiyi haƙuri wlhi na gaji, akwai ragowar wanda aka soyawa Alhaji a kitchen nasan zai isheki"
Little Hajo ta wani galla mata harara tare da nunata da yatsa, bata dai ce mata komai ba, ta fice, da kuka ta ƙarasa bedroom ɗin mom ta samu mom ɗin tana sallahar magriba, cikin shagoɓa ta fice fuuu tare da wucewa bedroom ɗin dad, yana tsaye ya sanya farar jallabiya yana ɓalle botir na gaban rigarsa ta rungumeshi murya kamar zatayi kuka tace "Dad kayi wa ƴar aiki magana inason cin bredi da ƙwai taƙi soyamin nidai Dad shi zanci" da sauri ya fito fuu zai wuce, ganin mom a tsaye ta rungume hannaye tana jifansa da murmushi yasa shi tahowa gurinta, cikin faɗa yake cewa "kiyi gaggawar korar waccar yarinyar, matsawar bazata yi mana biyayya ba ta yiwa ƴayana wlhi bazata zauna min a gida ba" tunda ya fara maganar mom take rungume dashi har ya kammala, ta janyo hannunsa suka dawo ɗakinta, wani haɗaɗen ƙamshi yayiwa hancinsa sallama, "kayi sallah ne?"
"Eh nayi isha'i nake jira" Dad ya faɗa yana kashe mata ido, tasani bai ci abinda Anum ta kawo masa ba, dan haka wanda ta kawo ɗakinta ta bashi da kanta har sai da ya ƙoshi, sam bata yi masa maganar Anum ba, tafison zuwa safiya su tattauna akanta, "Dad idan kayi sallah ka kwanta ka huta kasha hanya" mom ta faɗa cike da nuna kulawa" wane irin Hutu zanyi bayan gaki" yau a gunki zan warware gajiya hajiyata"
Little Hajo dake saman bed ɗin dad tana jiran dawowarsa sannan taji hukuncin da ya yanke akan Anum, har barci ya fara ɗaukarta bai dawo ɗakin nasa ba, tun tana barcin tana buɗe ido har mai ƙarfin yayi gaba da ita,
Tunda Jannat ta gargaɗeta akan yin Sallah da hijab, bata saɓa alƙawarin da tayiwa Jannat ɗin ba, a tsakanin 2days har ta fara sabawa, bayan ta idar da sallahar isha'i ta ɗaga hannunta sama tare da fashewa da kuka ta fara gayawa Ubangiji halin da take ciki tare da rokonsa ya kawo mata mafita, sannan ta shafa adu'ar hawaye na bin kumatunta, tunowa da tozarcin da take fuskanta a gurin mahaifiyarta yasa ta sake ƙarfafawa kanta guwaiwa, tasan a halin yanzu Allah gatanta Jannat gatanta sannan wannan gidan da take aiki shima gatanta, babban abin da yake damunta bai wuce ace mahaifiyarka wace ta ɗauki cikinka ta jure laulayi da naƙuda da raino amma daga baya ta nuna bata ƙaunarka dama hakan tana faruwa?"
Sai da tayi kuka mai isarta kafin ta dafe kanta dake tsananin sara mata, idanunta sunyi jajir ta miƙe tsaye ta cire hijab tare da ninke sallahya ta haye gado bayan ta ajiye su a mazauninsu,
Bataji sallamarta ba shigowarta kawai taji cikin masifa take cewa "tashi ki haɗamin tea" Anum ta ɗago jajayen idanunta da sam bata wani iya buɗesu sosai saboda tsabar ciwo da kanta yakeyi mata har wani duhu take gani, kafin ta riƙe kan nata sanan tace "dan Allah kuyi haƙuri Kinga yanzu ina fama da ciwon kai ne, akwai ruwan zafi a flaks ɗazu Hajiya ta sani na dafa harda su na'ana a ciki" Jumayma dake tsaye ta riƙe ƙugu tace "ke kalleni ubanwa kike gayawa haka? ta sake yin maganar cikin ɗaga murya, "Nace ubanwa kike gayawa haka, dama Hutu kikazo yi? gida babu AC da lallausar katifa ko? to bazan je in haɗa da kaina ba, idan bazakije ki haɗamin ba ki barshi tunda ni kina ganin damata zan isar da saƙon ga Dad"
Anum ta miƙe jiki karkarwa kafin ta dafe kanta ta raɓa ta gefen Jumayma ta wuce, koda ta shiga kitchen ɗin, dole sai da ta sake ɗora wani ruwan shayin sbda flaks ɗin ma baya kitchen, tana cikin dafawa tana tunani, ruwan yana tafasa ta tsumbula hannu, da sauri ta cire tare da matsar ƙwalla tana yarfe hannu, Ta juye a cup kenan Jannat ta shigo tana ce mata, "idan kin gama dafawa ki shanye time ɗin barcina yayi"
Tana faɗar haka ta juya tabar gurin.
Zuciyar Anum na yi mata ƙuna, ta jingina da bango tare da ƙarewa shayin da ta dafa ta juyeshi a cup kallo, ta jima a tsaye tana kallonsa, daga ƙarshe ta rufe da murfin cup ɗin ta barshi a gurin dan ko kuɗi za'a bata bazata iya kaishi bakinta ba, sai da ta tabbatar da ta kashe komai wanda yake aiki da wutar lantarki kafin ta koma ɗakinta ta turo ƙofa dan bata saka key ba, duk da sanyin AC dake ratsa fatar jikinta bai hanata jin zufa na damuna ba, ta yakice ɗankwalin kanta kanta wanda ya kasance babu gashi irin na maza ya bayyana, sannan ta cire riga da skirt a taƙaice dai tayi zigidir, alamun shigowar da taji za'ayi ne yasa ta....!
Afuwan masoya makaranta littafin NISAN KIWO jiya ban samu damar yi muku posting ba kuyi haƙuri.
Me kuke tunani shin waye yazo ɗakin Anum sannan a wane hali zai ganta?
# Anum
# Jumayma
#Dad
#Little Hajo
Waye gwaninku?
Kar a manta ayi following ɗina arewabook momislam11
Ga wanda sukeson number wayata ga tan kuyi saving 08141799224 nima kuyimin magana inyi taku sannan zanyi adding ɗinku a group wanda nake posting.
Page10
Janyo ƙaton hijabin da Jannat ta bata tayi, cikin sauri ta sanya ta tare da zubawa ƙofa ido,
"Anum kinci abinci kuwa naga kamar bakici komai ba"
Mom ta tambayeta yayin da take ƙarasowa cikin ɗakin,
"Eh naci Hajiya"
Anum ta mayar mata da amsar kanta a ƙasa, mom ta ƙarasa shigowa tana cewa "yauwa dama ina son in gargaɗeki game da Dad, gobe insha Allah zai zo ya tambaye ki akan ki koma aiki gidan wansa, gaskiya wanda mugu ne walhi idan kika kuskura kikaje zaki gwammace kiɗa da karatu dan bashi da tausayi, Anum ta ɗago jajayen idanuwanta kafin ta ɗorasu a fuskar mom, a ranta tace "kenan har ya zarce Alhaji a mugunta?" da sauri tace "Hajiya in Allah ya yarda bazan jeba, har mom ta juya zata fice, Anum tace "sai dai Hajiya ina tsoron sake haɗa fuska dashi"
Mom tayi murmushi batace mata komai ba ta fice.
Har gari ya waye kaf ɗinsu babu wanda yasan anyi sallahar Asbha, sabda basu samu damar yin barci da wuri ba, can tsakar gida tun kafin gari yayi haske ta share ko ina tare da kafa kujera ta zauna, da kaganta zaka san babu lafiya, tana sanye da atamfa ɗinkin riga da zani kasancewar ɗankwalin wadatacce ne yasa ta kafa ɗauri, a zaune take amma hankalinta sam baya jikinta, idanuwanta sun wani juye ita kanta bata san halin da take ciki ba,
Ƙarfe 7:am mijin Ummu Auwalu ya fito daga ɗakin Ummu yana hamma, kallo ɗaya tayi masa kana ta kawar da kanta gefe, cikin wata iriyar murya mai sanya wanda ya saurareta shiga ruɗu da tsananin firgici, "Kai Auwalu yalo ina zakaje zo ka fara yin tsallen kwaɗo" mijin Ummu ya zaro ido tare da cewa "ke Arwa kike ko Arshi? in banda fitsara da tacewar rashin kunya ina mijin mahaifiyarki inda kara ai ni mahaifinki ne, amma kike rainani"
Yana gama faɗar maganar ya fara tafiya kenan ya sule ya faɗi a gurin timm, Arshi na zaune sam Bama shi take kallo ba, ya miƙe daƙyar zai fara tafiya ya sake jin murya irin ta ɗazu wacce Arshi ɗin tayi masa, "idan har kana son zaman lafiya dole kayi tsallen kwaɗo saboda ka saɓawa Allah, lokaci ya ƙure a safiyar yau aljanu miliyan biyu ne suka je ƙasar Makka suka dawo kai kana barcin asara, tunda yaji ance Aljanu ai ya fice da uban gudu ko takalmi babu, yana gudun yana cewa "wlhi gamo nayi jama'a ku taimaka min nayi gamo da mutanen ɓoye"
Yayi gudu wanda idan da kuɗi zai bawa mai Adai-daita sai ya biya ɗari da hamsin in few minutes yayi tafiyar da bai san yayita ba, dai-dai shagon abokinsa ya yada zango, tunda ya hangoshi a furgice ya fito a shagon nasa cikin tuhuma yake cewa "Auwalu mai ya faru, kai da ya kamata ace kana gida gurin amaryarka?"
"Wace amarya ina cikin gararin rayuwa, tun daga gida nake ta tafiya da uban gudu na rasa inda zan dosa ne kawai nayo nan"
"Kardai kace min baka da kuɗin mashin?"
"A'a Hayatu inada kuɗi wlhi masifa ce ta koroni"
Hayatu mai shago ya kamo hannun Auwalu suka shiga shagon nasa, ya ƙarewa Auwalu kallo kafin yace "tabbas fuskarka ta nuna alamun kana cikin tashin hankali amma bani labari meye matsalar?"
Auwalu ya numfasa kafin yace "wato yarinyar matar da na aura gidan Aljanu gareta dan har cewa takeyi wai aljanu miliyan ne sukaje inane ma tace" kai koma dai menene wlhi yau idan na koma gida dole ta zaɓi ɗaya, ko zama dani ko tasan inda zatayi da wannan ƴar Tata mai ruwan Aljanu"
Hayatu mai shago ya tuntsure da dariya tare da buga tebur kana yace "wato kace Allah ya haɗaka da ƙarfen ƙafa, ni tunda Allah ya haɗa aurena da Zainabu lutiya wlhi na kasa tsinana abin arziƙi, na rasa ya akeyi ko nayi ciniki a shago sai na tattaro kuɗin na kawo mata wannan ja'iba tayi yawa, kai Auwalu Gara kai sau dubu"
Hayatu ya ƙare maganar cikin jimami da tausayin kansa,
Tunowa da maganar sallah yasa shi cewa "Hayatu ko sallah banyi ba, nikam na shiga uku"
Hayatu ya zaro ido tare da kallon Auwalu kafin yace "yanzu ai lokacin yin sallahar walha ne"
Auwalu ya miƙe tare da wucewa inda butoci suke ya ɗauka tare da nufar banɗakin dake raɓe da shagon, sai da yayi alwalah kana ya dawo shagon ya karɓi sallahya kana ya kabbara sallah, koda ya idar bai tashi a gurin ba, ya daɗe yana zaune har gyangyaɗi ya fara, Hayatu ya taɓoshi tare da cewa "mutumina ya kamata ka koma gida fa"
"Eh wlhi kam dan ko Abin karin kumallo ban bar musu ba"
Auwalu ya faɗa yana shafa kansa, zai sake magana wayarsa tayi ringing, ya zura hannunsa a aljihu ya Ciro wayar tare da duba waye mai kiran nasa, ganin sunan Ummu yasa shi ɗagawa da sauri "Alhajin Allah lafiya kuwa daga zuwa yin alwalah har yanzu baka dawo ba?"
Ummu tai maganar tana sake danna saƙata a ɗakinta dan Arshi ta kafa ta tsare wai sai dai Ummu ta haura ta katanga ta kawo mata Anum,
Tunda Ummu taji haka ta danna saƙata a ƙofa dama lekowa tayi, kiran Auwalu da tayi neman agaji take dan idan Aljanun Arshi suka tashi ko gangar cochi albarka gurin dokuwa,
Har yanzu tana nan zaune a tsakar gidan, hannunta riƙe da shimfiɗeɗiyar bulala sai karkaɗa ƙafafu takeyi.
Iya nera Ɗari ne a aljihunsa, da ƙafa ya dawo daga shagon Hayatu, amma ya ciyo bashin Madara ƴar ɗari da milo, ya biya gurin mai ƙosai ya siyo na ɗari, a ƙafa ya dawo gida, yana tafe yana cewa "ina tunanin akwai ragowar sugan jiya da bredi ya ishemu shan shayi,
Yana tafe yana lissafin kuɗin abincin rana har Allah ya kawoshi ƙofar gidan, sai da ya gyara wuyan rigarsa sannan ya shigo gidan da sallama, kafin ya ƙarasa shiga gidan ya ciro wayarsa dake ruri a aljihu ya kara a kunne, yana tafe yana waya, cikin rashin tsammani yaji saukar bulala a bayansa, ware idanu ya shiga yi ko zai ga wanda yai hakan, tana zaune ta hakimce akan kujera gashi shi kuma yana tsaye a ƙofar ɗakin Ummu, ita kuma tana zaune a saitin ƙofar ɗakinta dan tana kallonsa duk da tsakaninsa da inda take zaune akwai rata, "bani abinda ke hannunka" Arshi ta faɗa cikin wata iriyar murya wacce tayi daban da ta ɗazu a taƙaice ma Muryar tafi kamanni da na jarirai, hankali a tashe jikinsa na rawa ya miƙa mata, ta miƙe tsaye tare da ajiye ƙosan akan kujera, yana tsaye yana kallonta ta zazzage madara da milo akan ƙosan kana ta koma ta zauna tare da nunashi da bulala, tsananin tsoro ya sanyashi sakin fitsari cikin daga murya yace "dan Allah Hajiya ki buɗe ina cikin gararin rayuwa" Ummu dake manne a jikin ƙofa tace "aiko idan baka koma inda ta fito ba, zuwa anjima sai ka sauya kamanni" Auwalu ya zame a gurin babu numfashi, bayan ta gama cin ƙosan ta koma ɗakinta tana kwashewa da dariya, ta window Ummu ta ɗan leƙo tare da yaye labule, ganin ba kowa yasa ta leƙa Auwalu ko ya tafi, ga mamakinta sai taji gurnanin mutum, sosai ta tsorata ta buɗe ƙofa, tare da tahowa gurinsa da gudu, cikin Muryar kuka take cewa "dan Allah ka tashi karka mutu na roƙeka, tana maganar hawaye nabin kumatunta, atishawar Arshi da taji ne yasa ta yin hamdala tasan mutanen kan nata sun tafi, cikin ɗaga murya tace "Arshi dan Allah kizo Kinga abinda kika janyomin ko?" Arshi ta fito a ɗakinta tana mutsike ido, "menayi?" Arshi ta tambaya dan bata ma san tayi ba,
"Insha Allah yau ɗinnan zamu tafi gidan magani ko kinƙi ko kinso wlhi wataran kashemu aljanunki zasuyi"
Arshi ta taɓe baki, kafin tace "Ummu nifa ban gane abinda kike nufi ba, wane aljanu?"
Ummu ta harareta kana tace "bani ruwa a buta" Arshi ta kawo mata, ta yayyafawa Auwalu ya mike zumbur tana cewa "wlhi dole a cikin biyu ayi ɗaya"
Ummu ta riƙe baki tare da fara jera masa sannu, Arshi ma sannu tayi masa ya watsa mata harara tare da kawar da kai gefe, a fusace ya wuce ɗakin Ummu cike da masifa yafara magana "Na dai gaya miki, yaufa kwana ɗaya da auranmu har mun fara fuskantar masifu nikam bazan iya zama da wannan yarinyar ba, kisan nayi da ita" yai maganar in seriously"
Cikin firgici Ummu tace "Auwalu ita kenan min fa ina kakeso in kaita?"
"Akwai wani abokina da matarsa take gallaza masa, tanayin Tuwon siyarwa ni bance tayi tallah ba, ko aikin abincin ta dinga tayata amma bazata dinga kwana mana a gida ba"
Har yanzu Ummu bata aminta da shawarsa ba, suna tsaka da magana akayo sallama, Ummu na daga ɗaki ta amsa sallamar tare da mikewa ta fito, Anty Hadiza ta gani a tsaye, Ummu ta washe baki tare da cewa "oyoyo mutuniyar kirki jiya na gama maganarki shiga nan ina zuwa"
Anty Hadiza tai sallama a ɗakin Arshi, Arshi ta amsa tare da washe baki, Anty Hadiza tace "Masha Allah Arshi anata girma ina Anum?"
"Tayi tafiya"
Arshi ta faɗa a takaice.
Ummu ko na can ɗaki Auwalu nayi maga gargaɗin Arshi, Ummu tace masa "idan muka dai-daita da Hadiza sai su tafi tare amma bazan iya bada Arshi zuwa aikatau ba"
Ummu ta fito tana cewa "Hadiza kiyi haƙuri gani nan zuwa"
Ummu ta shigo suka gaisa Hadiza take tambayarta ya bayan rabuwa?
Hadiza tace "uhm ni Bama wannan ya kawoni ba, labari naji ashe bayan tafiyarmu ƙasar waje kin karɓi key na gidanmu kin shiga ciki, to wlhi Alhaji yayi ajiyar kuɗi a lokar bedroom ɗinsa dubu ɗari bakwai an nemi dubu hamsin an rasa, kuma mutanen anguwa sunce babu wanda ya shiga gidan idan ba ke ba, dan haka ki fito masa da kuɗinsa, bari kiji recording ɗin maganarsa da nayi.
"Idan bata bata baki kuɗin ba, kice hukuma ce zata rabani da ita, idan bata taɓa kwana a bayan kanta ba yau zataje ko kaffara bazanyi ba sai ta biyani kuɗina"
Ummu ta waro ido tare da kallon wayar Anty Hadiza kafin tace"wato ya mayar dani ɓarauniya ko? Ubanme zanci da kuɗin wani ba nawa ba, to ko sisi ban gani ba bare in taɓa, na ɗauka zancen arziƙi ne ya kawoki ashe sharri kikazo ki laƙaba min" Hadiza ta mike cike da rashin mutunci, kafin ta nuna Ummu da yatsa tace "zaki amsa kira a station ki jira dawowata"
Hadiza ta ɗauki jakarta ta wuce fuuuu tabar ɗakin.
Hadiza na fita Arshi ta kalli Ummu kafin tace "Ummu idan kece kika ɗaukar musu kuɗi kiyi gaggawar basu dan nashiga ban ɗauka ba bata fidda ɓarawo, Ummu ta zaro ido kana tace "dan ubanki kema zargina kikeyi? daga naje shan AC da fanka shine abin zargi?" Ummu ta ƙarashe maganar kamar zata rufe Arshi da duka, "babu abinda suka isa suyi wanda Allah beyishi ba, ina nan daram babu inda zani" Ummu tai maganar tana shewa, Auwalu da ya shiga wanka ya fito yana sanye da jallabiya ya buɗe labulen ɗakin Arshi sai da ya karewa Arshi ɗin kallo yaga idanun nata ba irin na ɗazu ba, sannan yace "wai meke faruwa ne? Cikin masifa Ummu tace "yo Kai kuma meye naka banda gulma da tsegumi me kazo ji....!
Page11
Ina miƙa saƙon godiyata ga masoyana jiki Alhmdulilah Nagode sosai.
"Allah ya baki haƙuri naji kamar cewa akayi kuɗi ya ɓata"
Auwalu ya faɗa yana juyawa zuwa ɗakin Ummu,
"Da ka tsaya mana, in banda gulma da kinibibi mitsw"
Ummu tai tsaki tare da washe baki kamar ba itace ta gama masifa ba, "Arshi dan Allah ki amince da zuwa gidan Hadiza kwata-kwata aikin da zakiyi na wata biyu ne, Kinga an biyasu dubu hamsin ɗinsu kafin su miƙamu ga hukuma, gara muyi komai cikin rufin asiri"
"Ummu naji zanje amma da sharaɗin dole Anum ta dawo gidannan"
Arshi ta faɗa tana jinjina kai alamar maganar fa da gaske take yi,
Jikin Ummu na rawa tace "indai Anum ce kamar ta dawo an gama nayi miki alƙawari kedai kawai ki shirya ranar da zaki dawo ranar zansa Jannat ta kawo Anum ɗin" Arshi ta janyo jakar kayanta ta fara zaɓar wanda zataje dashi gidan anty Hadiza, wata ƴar ƙaramar jaka ta ɗauka wacce zata ci kaya kamar kala goma, sannan ta zuge zip ɗin bayan ta gama shiryawa, tana daga tsaye tace "Ummu yunwa nake ji ƙarfe 10:am ko karin kumallo banyi ba"
"Yo nima me nasa a bakina? ya fice tun tuni ya dawo hannu rabbana"
Cikin ɗaga murya Ummu tace "Auwalu ina abin karyarwar da kace zaka kawo?"
Yana leƙowa ta labule sukayi ido biyu da Arshi yaga idanunta na bashi tsoro cikin rawar murya yace "naajeee...najeee" Ummu ta fito a ɗakin tare da riƙe ƙugu kafin tace "turr da wannan rayuwa tun ba'aje ko ina ba ciyar dani yana neman gagarar ka? To wlhi ko kaƙi ko kaso sana'a zan kama yi wacce zan tsira da mutunci na"
Gabaki ɗaya bakinsa ya rufe kamar an ɗaureshi sam ya kasa bata amsa kwata-kwata, sai kallonta da yake yi, a cikin ransa kuma mamakin maganganun da ta gaggaya masa yakeyi, Ummu ta kunto bakin zaninta ta miƙawa Arshi ɗari biyar, kana tace "ki siyo mana katin Mtn na ɗari sannan ki karɓo kamu na ɗari suga na ɗari sai ƙosai shima na ɗari, yanzu zan haɗa gawayi insa ruwa kafin ki dawo Arshi kiyi sauri" Ummu ta faɗa tana harar Auwalu.
Hijab ɗinta ta ɗauka ta fice, kai tsaye ta sissiyo abubuwan da Ummu ta gaya mata, bata wani jima ba ta dawo lokacin wutar ta kama har Ummu ta ɗora ƴar tukunya,
"Ɗauko wayata a ɗaki kisa katinnan zan kirawo Hadiza yanzu" Ummu ta faɗa tana yiwa Arshi nuni da hannu.
Bayan ta sanya katin ta miƙawa Ummu tare da danna number Anty Hadiza, Ringing ɗaya zuwa biyu ta ɗaga kasancewar tanada number Ummu, "Nace ga Arshi nan zata zo tayi miki aiki na wata biyu a madadin kuɗinku ayi haƙuri nidai ba ni na ɗauki wannan kudi da ake zargina dashi ba, ko da yake nashiga ban ɗauka ba ai bata fidda ɓarawo"
Ummu ta faɗa tana karyar da murya,
Sai da Hadizan ta ɗau tsawon lokaci kafin tace "wlhi kin taimaki kanki, gashi nan breakfast yakeyi na shigo na sameshi ya gama shiryawa barin gaya masa abinda yace sai ki shirya" ta katse kiran.
Alhaji Kasim kenan, babban ɗan kasuwa wanda duniya tasan da zamansa, ba a iya nan ya tsaya ba, kasuwanci har a ƙasashen Turai yana taɓawa, ya kawo kayan su Nigeria sannan ya ɗibi na Nigeria wanda sukeso ya kai musu,
Zaune yake a saman lallausar kujara mai zaman mutum biyu, Anty Hadiza tana gefensa, cike da nuna kulawa tace "Yaya maganar ɗazu ce da ka turani gidan matar nan da tazo ta tare mana a gida bayan tafiyarmu London, tace wai yanzu zata turo yarinyarta.."
Alhaji Kasim ya dakatar da ita, kafin yace"zata turo yarinyarta me zatayi mana?"
"Aiki a madadin kuɗin nikuma na nuna amincewata tunda basu da halin nemo kuɗin bare su biya"
Anty Hadiza ta faɗa tana shafo gemunsa.
"Shikenan amman dai kinsan bana son hayaniya ko, idan har zata kiyaye ace mata tazo"
Sai da anty Hadiza tayi masa kiss kafin ta danna number Ummu tace "arshi ɗin tazo"
Ummu tace tana nan tahowa,
Sai da Arshi ɗan tayi karin kumallo kafin ta sake wanka dan gwana ce ta fannin tsafta kana ta sanya hijab sannan ta fito hannunta riƙe da jaka tace "Ummu na tafi"
"Ummu na ɗora ruwan wanka tace "ai ban baki kuɗin Adai-daita ba, dan Allah Arshi karki nuna musu halinki daga kinji ranki ya ɓaci ki ambaci sunan Allah ki samu ki kammala wannan aikin cikin kwanciyar hankali arshi ki taimakeni kinji?"
Gyaɗa kai tayi