Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
tana can bayan window na parlo, a hankali suka tako suka iso parlon Anum dake durƙushe ta leƙa ta hangosu, sai da tayi dariya mai isarta kafin tace "rawa zakuyi sannan kuyi a hankali karku bige ɗan autanmu" Dady ya maimaita "rawa kuma? nida ko rawa banayi za'acamin wani inyi rawa, gaskiya bazan iya ba, badan dare ba wlhi da barin gidannan zamuyi ya kalli momy yace "Aljanu ne suka saukar mana a gida ya kamata mu bar gidannan" "Zakuyi abinda muka ce ne ko sai mun fito muku a siffar mu?" Dady yana turo baki yace "zamuyi, momy ma tayi harara tana kumbure-kumbure kai kace yarinya tace "yifa mukeyi" Dady ya fara rawa shida momy sai wani sunkuyar da kai yakeyi, acan jikin window ɗin aka sake cewa "girki a cikin minti goma shinkafa da miya shawara ta rage gareku sai ku shiga kicin" Momy tace "damu suke" Dady yace "ke muda aka samu yin rawa taya za'a sakamu yin girki?" Wani rudududu sukaji ai da gudu suka wuce kitchen Dady ya kalli momy kana ya haye kujerar tare da rafka tagumi, momy tace "minti goma fa aka bamu"...! Drop your comments domin samun cigaba. Tabbas akwai cakwakiya a ciki muje zuwa.. Page3 Shiru ne ya ratsa gidan, hakan ya bawa Dady damar yin magana, "momyn Jannat inaga fa mutanen nan sun tafi tashi mu koma ɗakina dan wlhi bazani ɗakinki ba" Jikin momy na rawa tace "Dadyn Jannat karfa mu tafi su kuma dawowa" hannunta ya kamo kana yace "Allah ya fisu nikam nayi nan, tunda baki kunna gas ba zomu wuce, ina zamukai uban abincin da sukace a girka?" suna tafe suna waige har suka wuce hanyar ɗakin jannat, momy tace "Dadyn Jannat Please barin je in duba ko tana lafiya" hararta yayi sbda abin ta cikin ɗakin Jannat ɗin ya fara, kafin yace "babu inda zaki ga dukkan alamu garin yawace-yawacenta ne ta kwaso Aljanu gobe insha Allah zan nemi malamin da zai zo yayi mata ruqiya da sassafe zan fice" Dady ya faɗa yana buɗe door na ɗakinsa. Koda suka shiga ɗakin har yanzu shida momy a tsorace suke daga abu yayi ɓurum sai su miƙe a zabure, tsabar tsoro ko kayan basu cire ba haka suka kwanta, Acan ɗakin Jannat Anum ta fito daga toilet tana dafe ciki, Jannat dake kwance wari ya addabeta sannan ta kasa tashi ta kawar da ledar cikin faɗa tace "haba Anum bayan fitsari kuma harda kashi kinsan kin cutar dani sosai kuwa?" ƙarasowa gaban drowar Anum tayi kafin ta kalli Jannat ɗin sannan tace "dan Allah kiyi haƙuri na tsorata ne sosai, yanzu zan fita dashi" Anum ɗin tayi magana kamar zatayi kuka, Jannat na kwance ta fitar da kashin zuwa toilet ta juye kana ta kora ruwa ya tafi, ledar kuma ta buɗe ƙofar waje ta wurga ta katanga kana ta dawo ciki tasa omo ta goge sannan ta ɗauki room freshener ta fesa kana tazo zata kwanta, "Kinyi sallah?" Jannat ta tambayeta, a'a banyi ba naga kema bakiyi ba" banayi ne" Jannat ta bata amsa a taƙaice, toilet taje tayo alwalah kana ta fara haramar yin Sallah dan har ta shimfiɗa sallahya komai nata irin na maza sometimes kuma takanyi abu irin na mata, "mai yasa bazakisa hijab ba?" Anum ta juyo da kallonta ga Jannat tana yamutsa fuska tace "yana shaƙemin wuya" "Kince kinason ki zamo mace akan me zaki dinga abubuwan maza, ki ɗauki hijab ɗina kisa" Badan taso ba ta ɗauki hijab tasa a kaikaice sannan ta tada sallahar, magriba da isha'i tayi, bayan ta idar ta ɗaga hannunta sama tana roƙon Allah ta jima a gurin daga ƙarshe ta miƙe ta ninke sallahya da hijab ɗin ta haye gado, can gefe ta kwanta tare da takure jikinta, itakam Jannat ta riga da tayi barci, sam Anum ta kasa barci babbar damuwarta Arshi da kuma idan gari ya waye wane babin zata kama, sannan a wane irin hali Arshi ɗin take?" sosai zuciyarta ta tsinke ta ƙaddarawa zuciyarta bazata sake samun farinciki ba, ta juya ta kalli Jannat da sai barcinta takeyi, a zuciyarta tace "Allah sarki zaman mutunci ne ya haɗani da ita tun ina makarantar primary kafin in shiga secondary na fara fuskantar tsangwama da tsana" wasu zafafan hawaye suka samu nasarar zubowa a idanunta, ta sanya hannu ta share, tana cikin tunin barci yayi gaba da ita, Ƙarfe 4:am Jannat ta farka, kana ta miƙe zaune tare da jingina kanta da jikin gado, tunanin mafita da zasu fuskanta ne ya faɗo mata, tabbas tasan ba ƙaramin ganganci tayi ba, na shigo da Anum cikin gidannan hankali a tashe take ta saƙa da warwara sbda ta fara tunanin idan har ta samawa Anum Aiki a gidan ƴar uwar momy wataran idan momy taje ko sistern nata tazo zata labarta mata cewar itace ta kawo mata mai aiki, can kuma Jannat ta tura yatsanta ɗaya a baki sbda tanada burin ingantawa Anum rayuwa duk da itama a karkashin iyayenta take, mahaifinta yanada arziƙi amma bawai yana sakar mata bane, 5k ta tambaya sai tayi masa dogon bayani, hakan yasa wasu lokutan take zama sisi bata magani, juyin da Anum tayi ne yasa Jannat tashin ta cikin sanyin murya tace "Anum yanzu fa ba lokacin barci bane ki tashi mu fara shawarar inda zamu ɓullowa lamarin zuwanki gidan aiki idan kuma gidanku zaki koma Tom, saboda wlhi ina cikin wani hali ko da wanne lokaci su momy suna iya shigowa, tunda Kinga jiya hankalinsu ya tashi" "Anty Jannat nafi son zuwa gidan Aikin saboda in cika burina na komawa mace sannan inci gaba da karatu kamar kowa" Anum ta faɗa tana kallon Jannat ɗin. "Shikenan ana kiran sallahar Asbha ki shirya zan baki Naira ɗari wlhi bani da kuɗi, ki hau Adai-daita zuwa anguwarku nikuma anjima zan zo gidanku sai muyi magana" Anum tayiwa Jannat ɗin godiya, Anum ɗin ta sakko daga kan bed tare da shiga toilet, alwalah kawai tayi ta fito sannan ta ɗauki hijabi ta kabbara sallah, lokacin da ta zauna zaman yin adu'oi aka fara kiraye-kirayen sallaha, Har tayi sallah ta idar idon Jannat a kanta, tasan yanzu Dady bai dawo daga masallaci ba, ta miƙawa Anum Naira ɗari tace "muje in rakaki amma ki tabbatar kin saka hijabi ki tafi dashi na baki kyauta" godiya ta sake yiwa Jannat ɗin kafin suka fito harabar gidan, sai a lokacin ma Lado mai gadi yake yin Sallah, ta buɗewa Anum ta fice sannan ta rufe ƙofar kana ta tsaya tana jiran ya idar da sallah, tana tsaye yayi sallama sannan yayi adu'oinsa ya shafa, yana shirin naɗe dardumarsa tace "Lado idan har naji labarin ka gayawa wani fitar ƙawata da na raka yanzu wlhi zaka fuskanci mummun hukunci tunda kai ka iya munafurci" Ta faɗa tana nuna shi da yatsanta, jikinsa na rawa tabbas yasan barazanar kora takeyi masa, yace "insha Allah babu wanda zai ji" ta wuce ba tare da ta ƙara bi ta kansa ba. Cikin sanɗa ta wuce ɗakinta tare da kullo ƙofa ta haye gado sannan taja blanket ta rufa har kanta, A hankali momy ta turo ƙofa tare da yin sallama, momyn ta tsaya daga bakin ƙofa sabda a zahiri tsoron Jannat ɗin takeji, "Jannat kinyi sallah kuwa?" "Eh nayi" Jannat ɗin ta faɗa tana daga cikin blanket. Duk da tsoron Jannat ɗin da takeji bai hanata cewa "tashi mu shiga kitchen yau da asbha tafiya ta kama dadynki da wuri zai fita yana dawowa daga masallaci" Jannat ta zuro ƙafafunta ƙasa kafin ta miƙe tana turo baki, momy ta jinjina kai kana tace "wato wuyanki ya isa yanka ko? daga ki tayani aiki sau turo baki, na ma mance ina kwana?" Jannat ta sunkuyar da kanta ƙasa kafin tace "good morning momy" Kallon banza ta watsa mata kafin tace "wuce muje" Kai tsaye suka wuce kitchen suka fara hada hadar haɗa abin karyawa, momy take bata labarin abinda ya faru jiya, a maimakon Jannat ɗin ta jajanta musu sai kawai ta fashe da dariya harda tafa hannu, abin ya matuƙar bawa momy mamaki, Dady ya shigo lokacin gari ya fara haske, har ƙasa Jannat ta durƙusa ta gaishe shi kafin ta ɗago sukaci gaba da aiki, bayan ya amsa ya wuce bedroom ɗinsa, ƙarfe 8:am suka kammala komai da komai, lokacin Dady ya fito sanye da riga t-shirt fara da baƙin wandon jeans, Jannat taje tayi brush ta dawo dining suka fara karyawa bayan momy ta zubawa kowa. A hankali take tafiya har ta iso bakin titi, cikin sa'a tana tare wani mai napep ya tsaya, ta shiga tare da gaya mata anguwar da zai kaita, suna tafe tana ta tunani duk da dai ma tunanin nata bai wuce akan abu biyu ba, suna isowa ta fito kana ta miƙa masa kuɗinsa sannan ta fara tafiya har ta iso ƙofar gidansu, gidane da zamu iya kiransa da gida na masu ƙaramin ƙarfi dan su Anum ba wasu masu hali bane, sai Ummu tayi sana'ar siyarda kamu take samun kuɗin da zasu ci su sha, bakinta ɗauke da sallama Anum ta tura ƙofar galan galan ɗin gidansu, tana tafe tana tunanin koyaya Arshi ta kwana, sallama tasake yi kafin ta tura ƙofar ɗakin da suke kwana, juyowa tayi ta kalli ƙofar ɗakin Ummu ga mamakinta taga takalmi a gurin, fasa shiga ɗakin nasu tayi ta dawo da baya zuwa ɗakin Ummun, ta yaye labule tare da yin sallama, jin Muryar Anum yasa Ummu toshe kunnuwanta, cikin tsananin ɓacin rai da tsantsar tsana tace "mai ya dawo dake nan gidan ban riga da na sallameki ba? akan halittar nan taki mutane suka daina shigomin gida har cewa akeyi wai kina tsorata mutane, to yanzu hankalinki ya kwanta sun daina zuwa mun zauna bamu da cin yau bare na gobe" Ummu takai ƙarshen maganar tana miƙewa tsaye, "Haba Ummu wai shin ba Allah bane ya baki anty Anum ba?" Arshi tayi maganar tana zarewa Ummu idanu, "Allah ne ya bani ita nace bana sonta ko ana dole ne?" Arshi tayi wani irin gurnani kamar zaki kana ta taho da gudu tayi ciki da Ummu, ta kamo hannayenta ta kamo ƙafafuwanta ta haɗesu guri ɗaya kafin tace "ko kin ƙi ko kinzo anty Anum jininki ce babu inda za'ayi ki sauyata, Arshi tayi maganar cikin ƙaraji, zuciyar Anum na dukan uku-uku damuwarta kar Arshi ta yi kisan kai, duk da hawayen dake zubowa a idanunta jikinta na kyarma bai hanata ƙarasa shiga cikin ɗakin Ummun ba, ta sanya hannunta ana Arshi cikin Muryar kuka tace "ki rabu da ita koba komai taci darajar uwa a gurinmu" tabbas Ummu ta maguzu dan bakinnan yayi ƙato, dama gashi lafcece Arshi ta fice a ɗakin tana kamo hannun Anum, can ɗakinsu suka wuce, ta zauna akan tabarma kasancewar itace arziƙinsu a ɗakin sai katifa wace duk ta yayyage ga kuɗin cizo shima yana zuba shagalinsa, "anty Anum mai zai hana mu samawa kanmu mafita mubar gidannan" "Arshi Gara ma ke nikam duk inda naje guduna zasu dinga yi kekam matsalarki ɗaya ce, idan akayi miki maganin Aljanun kanki komai zai zo da sauƙi" rai a ɓace Arshi tace "anty Anum Please stop saying that bani da larurar komai, idan zaki yarda ki yarda Ummu bata sonmu" Muryar Ummun suka tsinkayo tana daga tsaye ta riƙe ƙugu tace "iya Anum nace tabar gidanan Arshi idan kika fita ba da yawona ba, Anum da abin yaso bata dariya duk da tana cikin takaici tace "wai Ummu ya akayi kika dawo daga wancan gidan bayan kince babu uban da ya isa?" Ummu tayi shiru batace komai ba, tana daga tsaye Arshi tace "Ummu tunda dai bakyason anty Anum nima zan tafi Kinga sai ki zauna ke kaɗai, "wato Allah ya kawo mu zamanin da ɗan cikinka sai ya gaya maka magana son ransa? duk kuyi zanyi maganinku, kekuma Arshi ki tashi ki shirya naji labarin wani mai maganin iskoki dan wlhi naci gaba da zama dake a cikin wannan gidan zuwa gaba kasheni kawai zakiyi" Ummu ta faɗa tana harar Anum. "Nikam babu inda zani" Arshi ta faɗa tana turo baki, Ummu na tafiya Arshi tace "kinga dole mu samowa kanmu mafita, naji labarin wai Ummu zatayi aure, wlhi tallahi idan tayi sai na saka mijin fitsari a wando, sun daɗe suna tattauna halin rayuwa, daga ƙarshe Anum ta miƙe tsaye, "ina zaki?" "Zan yi wanka in sauya kaya saboda anty Jannat tace zata rakani wani gida in fara aiki" Anum ta faɗa tana juya baya tare da samun zani ta ɗaura a ƙirjinta, Arshi na daga zaune tace " Wai labarin yayi muku kuwa? Dan Allah kuyi following account ɗina arewabook Drop your comments Shin wane ƙalubale zata fuskanta a gurin aiki, gafa maganar auren Ummu Arshi zata barta tasha ruwa kuwa? Page4 Shigarta wanka bayan ta cire zanin jikinta zuciyarta ta sake tsinkewa sbda ƙarewa halittar jikinta kallo da ta dinga yi, duk da cewa bawai baƙon abu bane a gurinta amma takanji rashin daɗin ganin halittarta a hakan, abinda ya sata daɗewa a wanka kenan dan har takai tsawon one hour tana wankan, itada ba ma'abociyar daɗewa a wanka ba, ta ɗaura zani taji Arshi na cewa "anty Anum kiyi sauri ki fito Anty Jannat tazo" Da sauri ta wanke sosan wankan kana ta fito tana washe baki, Ummu dake can ɗaki tana jiyo sallamar Jannat ɗin amma bata amsa ba. "Oyoyo antyna ta kaina" Anum ta faɗa tana washe haƙora, "Oyoyo ƙanwata da fatan kin shirya saboda time ɗin tafiyata school yayi, sbda kar in saɓa alƙawari ne yasa nace barin biyo idan na ajiye ki sai in wuce" Jannat ta faɗa tana yi mata murmushi, Arshi tace "anty Jannat ki ƙaraso ciki kafin ta shirya, nima zan biku" Cikin tausasa murya Jannat tace "kiyi haƙuri Arshi babbar matsalata Anum idan har ta samu mafaka insha Allah kema kamar kin samu ne" Arshi ta narke fuska kamar mai shirin yin kuka. Ɗakin su Anum ɗin Jannat ta shiga, a gurguje Anum ta shafa mai sannan ta ɗauko powder zata shafa, Jannat ta dakatar da ita tare da cewa "karki shafa sa kaya sannan muga wane za'ayi" duk cikin kayanta riga da wando ne na maza sai hula P/cap shi take sawa, sbda tun tana ƙarama haka Ummun take sanya mata, ta ɗauko wani ƙaton wando zata sanya Jannat ta ƙwace tare da cewa "karki manta a matsayin cikakkiyar budurwa zakije ba a namiji ba, mai yasa kayan maza zasu shigo ciki?" Anum ta shagwaɓe fuska kafin tace "bani da kayan da zasu dace" Jannat ta kalli Arshi kana tace"miƙomin ledar da nazo da ita" Arshi ɗin ta ɗauko ta kawo gaban Jannat, kasancewarta ƙwararriya ta fannin makeup batayi ƙasa a guwaiwa ba, ta fara fito da kayan kwalliya, sai da ta fara shaving ɗin gemun Anum ɗin sannan ta sanya cum ta gyara mata gashin kanta kafin ta fara tsara inda kwalliyar zata kasance, sun shafe tsawon lokaci anata gyaran fuska kafin daga ƙarshe ta ɓula mata kunne tasa mata ɗan kunne mai barima, sosai Anum tayi kyau, dan haka take kunnenta ko ɓuli babu, abin sai yai matuƙar burgeta duk da cewar taji zafin yin hakan, "Bamu da isasshen lokaci Anum har yanayin tafiyarki dole ki sauya saboda yawanci kinayin abu kamar na maza, sannan ki rage gwada wa abu ƙarfinki, magana ma ki dinga dai-daita wa, Saboda gudun kar mu fuskanci matsala" Jannat ta faɗa tana buɗe ledar ta ciro riga da skirt na atamfa mai kyau, ta miƙawa Anum, Anum ta jujuyasu tare da cewa "anty Jannat a jikina zan saka?" "Eh sakawa zakiyi idan har Allah ya bamu nasara zan gayawa Ƙanwar momyn cewar duk kwana uku zaki dinga dawowa gida" "Tom amma anty Jannat idan nasa kayannan kunyar tafiya dasu zan dinga ji" Cikin jin haushi Jannat ta watsa mata daƙuwa kafin tace"ana ga yaƙi kina ga ƙura, kinsan dai na gaya miki zan wuce school ko akan rashin zuwa da banayi malaminmu zai iya kiran Dady, idan kuma zaki bari inje in dawo idan na dawo sai in biyo tanan" Arshi dai tana kallonsu sosai tausayin Anum ɗin ya kamata, babu damuwa zan jiraki tunda ai bazaki daɗeba ko?" "Eh ba daɗewa zanyi ba, naso ace ma mu wuce hospital daga nan sbda mu samu wasu bayanai a kanki" "Shikenan babu damuwa Allah ya dawo dake lafiya" Anum ta faɗa cike da nuna kulawa. THAILAND Yangon Zaune suke a cikin wani hadaɗen parlo mai kyau sosai, parlon ya kasance madaidaici, yana ɗauke da tausasan kujeru guda uku, dukkansu masu zaman mutum ɗaɗɗaya ne, color na kujerun light blue ne, yayinda samansu yake kewaye da adon katako mai kyau, fentin jikin bangon fari ne, sannan kayan kallo da su fridge da sauransu, ɗakuna uku ne a gidan, bedroom biyu sai kitchen kowanne bedroom da toilet a cikinsa, acan parlo wasu kyawawan samari ne a zaune ko wanne fuskarsa babu walwalah dukkansu farare ne hakan shizai tabbatar muku da cewar haifaffun garinne, Masha Allah kaf cikinsu basu da wani makusa duk da cewar suɗin abokan juna ne, ɗaya daga cikin su mai suna Khair yace "ya kamata Ku hanzarta kunsan yau weekend su Leeela basa free idan har Allah ya bamu nasara sai mu taho da yaran" Aman ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa kafin yace "tabbas bamu da wani enough time ku hanzarta" Bahi da sai yanzu yayi magana, murya a sanyaye yace "ni am ready ku nake jira" su biyun suka miƙe shima ya miƙe, dukkansu suka haɗa hannu alamar sunyiwa Juna alƙawarin babu wata matsala kana suka fito tare da kulle gidan, a inda suka tsara tun farko hakan ne ya kasance ko wanne zai hau tasa motar saboda tsaro, hakan yabawa Bahi damar kiran Leeela, ringing ɗaya Leela ɗin ya ɗaga, time ɗin yana tare da ƴan mata sai wani iyayi sukeyi masa, "oga su Aman fa basu daddara da gargaɗin da kayi musu ba, yanzu haka dukkanmu muna hanyar zuwa ɗibo ƴan matan ne" Cikin sauri Leela ya mike tsaye zuciyarsa na zafi yace "har akwai wani wanda zai tsallake min layin da na zana, inaaa!.." Yai maganar yana watsar da ƴan matan dake a kusa dashi, cikin zafin nama ya shiga wani ɗaki wanda ya kasance yana cike da makamai, ko me ya ɗauka oho ya fito ya ƙarasa ciki, kafin ya danna wasu numbobi a wayar tafi da gidanka, ringing ɗaya aka ɗaga cikin ɓacin rai yace "Raja kaje titin Haiphong cikin sauri akwai wasu motoci guda uku da zasuyi parking a gurin yanzu yanzu ka kawomin su nan" daga can ɓangaren Raja yace "an gama mai gida" Cikin shiri ya fito daga gida, Raja baƙi ne sosai daga ganin yanayin fuskarsa zaka tabbatar da babu mutunci. Suna cikin tafiya dukkansu ukun kafin su ƙarasa titin Haiphong ɗin motar Khair ta lalace, dama shi da Aman kusan a tare suke tafiya, shikam Bahi yayi nisa sosai, Aman ya fito cikin sauri tare da riƙe hannun Khair kafin yace "khair ga dukkan alamu Bahi bashi da gaskiya zomu juya komai zai iya faruwa damu anan" Hankali a tashe Aman yake magana, hakan kuma bai hana Khair durƙusawa a gaban motarsa ba, ya fara duba abinda yake bashi matsala, Aman ya kamo masa hannu Khair ɗin yana jan Aman, Aman yana jan khair, cikin zafin nama Khair ya mari Arman kafin yace "tabbas baka da hankali, mai yasa abokinmu aminin mu zaka dinga yi masa mummunan zato, Bahi bazai iya yarda a haɗa baki dashi.... Ƙarar Harbin bindigar da sukaji ne yasa ko wanne dai-daita nutsuwarsa, Arman yaja Khair suka gudu, saboda sun fara ƙure musu gudu, suna gudun har suka iso gurin motar Aman suka shiga cikin gaggawa ko rufe murfin motar basuyi ba, Arman ya fara driving, abin mamaki babu Bahi babu alamarsa, sukuma su Aman sunata gudu mutanen na binsu, mutanen Leeela suka dinga sakar musu bindiga har suka sace musu taya ɗaya, sosai tsoro ya kamasu tunda dai basu da wani makami da zasu kare kansu gashi kuma mutanen sunzo har gabansu, suka durƙusa a gurin kowannensu ya ɗaga hannu sama, cikin wata mummunar murya Raja yace "mai yasa zaku shiga hannun oga bayan kunsan bazaku iya dashi ba?" yai Maganar yana hanɓare Aman, wayar Khair ta fara ringing cikin tsoro ya kalli aljihunsa hannunsa na a sama, Raja ya sanya hannu ya ciro wayar kana ya kara a kunne, cikin ƙaraji yake cewa "wayeee!!" Nice kakarsa da fatan dai yana nan ƙalau ko?, yau ne birthday ɗinsa har mun shirya nida ƙanwarsa ina fatan zaka sanar masa" Raja ya daka mata tsawa cikin ƙaraji yace "keeee kaka, ba kaka kike ba ko kakus ne, jikanki ya shiga hannun Iyalan Leeela da fatan zaki cigaba da murnar shagalin bikin birthday ɗinsa" Hannun granny na rawa ta miƙawa Arya wayar hannun granny yana karkarwa, da sauri Arya ta tallafi granny tare da kallon ƙasan ƙafafunta tace "granny lafiya naga kamar fitsari kikeyi?" idanun granny sun kakkafe tace "ba dole ba, tun daga nan na fara jiyo jiniyar sojoji sun garƙame Khair, nima Gara in mutu kawai" Cikin kiɗima Arya tace "yimin bayani wani abun ne ya faru?" Wata uwar tusa da granny ta saki ne yasa Arya sake hannun granny tare da matsawa can gefe rai a ɓace tace "baki gayamin abinda ke faruwa ba, sannan kin cikawa mutane ciki da guba anya granny ba haka kikayi a yarintarki ba?" Da sauri granny ta buɗe ido, ta ɗorasu a na Arya, a zuciyarta tace "inafama da wani baƙincikin ta sake cusamin wani" tsabar takaici granny ta kasa furta koda kalma ɗaya, tana zaune a gurin ta dinga banko tusa mai wari, Arya kam guduwa tayi sbda cikinta ya fara rikicewa, da gudu ta nufi toilet ta fara tsuga gudawa har tana riƙe cikinta, sosai ta haɗa gumi sbda abin babu sauƙi, tana fama da kashi granny ta leƙo cikin rage murya tace "Arya ki fito zan shiga ina tunanin abincin da nayi mana jiya shine ya lalata mana ciki" sam Arya bata jinta bare tasan da ita takeyi, murya a narke granny ta sake cewa "Arya fito zanyi a ƙasa kinsan ba pant na saka ba" wata uwar tusa granny ta sake sakewa wacce tasa Arya ɓarowa daga gurin kashin, da rarrafe ta fice cikinta na murɗawa, idanuwan granny sunyi ƙulu ƙulu ta haye gurin kashin tare da zakin zawo ɓirrrrrr a hankali ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido, ta daɗe tana tsigawa dan har wani irin gumi takeyi gashi sam jikinta babu wani ƙwari, da ƙyar ta sakko tare da kunna ruwa a pampo ta ɗauki buta ta tara murya kamar an sanyata magana dole take cewa "oh wannan Arya ɗin haka ta fice ko kashin bata wanke ba, inda take ma bazan dosa ba" granny tayi maganar tana dafe kwankwaso, a duƙe ta fice waje bayan ta kora kashin ya wuce, ta jingina da jikin bango, kira ya sake shigowa, wayar na ajiye saman kujera, da sauri granny takai hannu ta amsa kiran cikin marairaice murya tace "waye dan Allah ku sakarmin jikana shi kaɗai nake dashi" Khair yana kuka taji muryarsa yana cewa "granny ki sakamu a adu'a yanzu haka gidansu Leeela zamu wuuuu..." Granny bata tsaya jin ƙarashen zancen ba ta zube a gurin ko numfashi batayi, Arya da ta koma ɗakinta ta watsa ruwa ta fito ta samu granny a kwance a gurin, ta kira sunanta yakai sau uku amma shiru bata amsa ba, hakan ya sake tabbatar mata da suma tayi, da sauri ta buɗe fridge ta ɗauko ruwa mai ƙanƙara ta tsiyaye a fuskar granny tana daga tsaye, a zabure granny ta miƙe tare da cakumo wuyan Arya tana cewa "Leeela ka sakarmin jikana kokuma inzo in gwada maka wasan dambe wanda nayishi tare da kakanka" Arya ta waro idanu sam har yanzu bata fahimci inda granny ɗin ta dosa ba, sai wasu abubuwa takeyi kamar mai taɓin hankali, "shaƙe mata wuyan da granny ta sake yi a karo na biyu ne yasa ta fincike hannunta cikin rashin sa'a granny ta zube akan markaɗaɗen Attahiru dake a hannun Arya zata shiga kitchen samawa kanta abinci, sbda kashin da tayi cikinta ya zazzage, ihu granny ta kurma, cewa takeyi babu wando ku taimaka babu wando, Arya ɗauko min Vaseline in shafa ko pipi zeyi min sauƙi, ai duk kece muguwa mai hali irin na uwarta, nace Miki babu wando ki kawomin koda sabulu ne in

Chapter 2 of 7