Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 3
ba zan amshe shi da qarfin tsiya na lalatashi” Kalamansa ya baiwa bawa Farsu dariya ya fuskance shi sosai sannan yace masa. “Bana jin akwai wani sadauki da zai iya amsar wannan abun daga hannuna da zunzurutun jarumtaka don haka idan kana ganin cewar za ka iya to ga fili ga mai doki, daga ni sai kai sai kuma Gimbiya Lusa” Ya gama maganar yana mai dubanta “Ci gaba da rayuwarki” yana rufe bakinsa itama ta dawo yadda take ta dubi kanta cike da mamaki, ta mayar da kallonta ga sadauki Ansar cikin mamaki ta tambaye shi. “Kaima abinda ya faru da ni ya sameka?” ya gyaxa kai. “Ga wanda ya aikata mana sihirin tsafi, kuma yanzu nan zan ladaftar da shi akan wannan laifin daya aikata mana. Domin zan amshi sihirin na lalata shi”. Gimbiya Lusa ta juya ta dubi Bawa Farsu a fusace tace masa gwara tun cikin ruwan sanyi ka bamu sihirin da ka aikata akanmu mu lalatashi domin idan ba haka ba zamu amshe shi da qarfin tsiya, sannan mu mayar da shi kanka” Bawa farsu ya dubeta ya yi murmushi kafin yace mata. “Ba irin mu ake yiwa barazana ba domin mun sha jarumtaka a nono, mun zama dutsen dake cikin ruwa bamu san ana rana ba. Saboda haka duk wanda yake ganin zai iya amsa da qarfin damtse to ga fili ga mai doki” Ya gama magana yana dubansu. Sadauki Anwar ya miqa hannunsa ya zaro takubinsa ya riqeta sosai a hannunsa ya dubi Bawa Farsu ganin haka shima ya zare nasa makamin ya dubi sadauki Anwar suka fuskanci juna ko wanne a cikinsu yana jujjuya makaminsa. Tsawon lokaci suna tsaye carko-carko kamar zakaru kafin daga bisani Anwar ya yi xauki ga bawa Farsu da zumar ya yi tafiyar guguwa da shi,ganin tahowarsa ya saka shima bawa Farsu ya tare shi suka yi wata qazamar gamuwa data girgiza qasan tekun, makamansu suka bayar da wata maxaukakiyar qara, su ka yi zamiya suka kuma juyowa suka gauraya suka soma musayar sara da suka a tsakaninsu. A haka suka xauki tsawon lokaci suna faman fafatawa bayan tsawon wani lokaci sannan bawa Farsu ya sauya salon yaqinsa nan take ya takura Sadauki Ansar duk da irin tsananin jarumtar da yake da ita. Wannan shi ne salon yaqi xaya da aka tava sauya masa a tsawon rayuwarshi ta duniya bai san ta yadda zai qare kanshi ba a ‘yan lokuta kaxan bawa Farsu ya gajiyar da shi ainun! Ganin abinda yake shirin faruwa ya sa Gimbiya Lusa itama ta zare makaminta ta yi xauki akansa da wata irin zuciya mai kama da dutse, jin motsinta ya saka ya yi saurin juyawa tana zuwa ta kai masa wani sara a kaikace cikin zafin nama ya kaucewa saran, nan suka soma kai sara da suka ya zamana su biyu wato Gimbiya Lusa da sadauki Ansar sun rufarwa Bawa Farsu a tsakiya. Qura ta turniqe a wurin babu abunda zaka dunga juyowa sai qarar haxuwar makamansu da gilmawar kai sara da suka a tsakaninsu walqiya da motsin wucewar makamansu ya karaxe ilahirin wurin. Kai komo da sintiri suka rika yi a wajen ko wanne a cikinsu yana burin ganin ya samu galaba akan xan uwansa. Su Gimbiya Lusa suka kasa samun nasara akan Bawa Farsu haka shima ya kasa samun nasara akan su, har suka gaji dukansu suka zame qasa a jigace numfashinsu yana fita da sauri da sauri. A daidai lokacin wani aljani ya keto qasa ya fito ya tsaya a gaban Gimbiya Lusa ya yi gaisuwa a gareta ta dubeshi sannan ta ce masa cikin muryar gajiya “Maza ka xauke mu ka fitar da mu gavar teku” Bata gama rufe bakinta ba ya sunkuya ya xaukesu ya ajiye su a bayansa sannan lokaci xaya ya vace daga wurin. Ilahirin wajen ya zamto tamkar wata halitta mai rai bata tava wanzuwa ba, babu komai a wurin da ya yi saura, sai gawarwakin matattun dakarun sarauniyar aljanun cikin ruwa. ** Bokanya Namsu tana kwance ta na kallon tsinin wuqar boka sharbanga ta tunkaro qirjinta ta ta lumshe idanunta tana da tabbacin yau itace ranar mutuwarta, domin babu wani mahaluki da zai iya zuwa domin ya ceci rayuwarta daga halakar da take ciki. Duk da runtse idanunta da tayi hakan bai hanata ganin kakkaifar wuqar boka sharbanga ba, haka ya sa ta yi gaggawar buxe idanunta a lokacin ya nufo qirjinta da wuqar da zumar ya soka mata Bokanya Namsu ta runtse idanunta karo na biyu wannan karon ta fi tsorata fiye da kowanne lokaci. Kafin kaifin wuqar ya qarasa qirjin bokanya Namsu, wata kibiya ta qaraso ta samu matsuguni a hannun Boka Sharbanga ya qwala wata razananniyar qara da amonta ya watsu ko ina da ina na illahirin sararin samaniyar tekun. Hakan ya sa Bokanya Namsu ta yi gaggawar buxe idanunta domin ganin abunda ya sa Boka Sharbanga qwala ihu. Tana buxewa ta ga Boka Sharbanga ya yi tsalle gefe xaya yana qoqarin zare kibiyar da ta samu matsuguni a jikin hannunsa. A lokacin wani saurayin aljani ya qaraso wurin wata budurwa mai kyawun fuska ta sako daga kansa ta tsaya gaban Boka Sharbanga ta tsaya a hannunta riqe da wata kwari da baka qirar mutanen nahiyar baqaqen fata. Wannan budurwa dake tsaye akan Boka Sharbanga itama baqar fata ce kamar Bokanya Namsu, sai dai ita yarince xanya domin du-du-du shekarunta ba su fi goma sha tara ba, tana da qirar cika na mace ta tattare gashinta a wuri xaya, tana sanye da kayan yaqi koraye, waxanda suka matuqar yi mata kyawu a bayanta tana rataye da wata takobi mai koren mariqi da aka yi mata ado da farin qyalqyali, akwai alamomin jarumtaka a jikinta. Ta sunkuya ta buxe gefen takalminta ta xauko wata hoda ta watsata a jikin Bokanya Namsu nan take ta ji duk kuzarinta da ta rasa ya dawo, cikin sauri ta miqe ta tsaya gaban budurwa tana dubanta, a lokacin Boka Sharbanga ya zare kibiyar daga hannunsa ya miqe tsaye a fusace ya dubi budurwa da fushin murya yace mata. “Wacce ce ke da har kika aikata wannan laifin a gareni?” Budurwa ta dubeshi fuska da fuska kana ta ba shi amsa da cewar. “Ni ce Sultan”. Boka sharbanga ya zuba mata idanu cikin tsananin mamaki, yana da labarinya ya santa a matsayin jaruma mai tsananin jarumtaka duk wajen dataje a rayuwarta sai anyi tsananin zubar da jini, bata zuwa wani waje ba tare da wani ya mutu ba, wannan shi ne abinda kawai ya sani akanta. Ya juma yana kallonta, sannan cikin xaukar numfashi ya shammaceta ya yi wuf! Ya zare takobinsa ya afka mata suka gauraya a wuri xaya suka soma musayar kai wa juna sara da suka mutuwa ta soma shawagi a tsakaninsu musayar kai sara da suka ya karaxe wurin suka xauki tsawon lokaci suna fafatawa. Ganin lokaci yana tafiya ya sa Sultan ta sauya salon fafatawar bayan wasu ‘yan lokuta ta xauki numfashin Boka Sharbanga ta tafka masa wani nagartaccen sara a dokin wuya ta tsinke masa kai gangar jikin ta zube a wurin kan ya faxa cikin teku. Ta juya ta dubi Bokanya Namsu cikin kwantar da murya tace mata. “Ni ce ‘yarki Sultum”. Bokanya Namsu ta rungumeta cike da farin ciki da jin daxi a yau burinta ya cika ‘yarta ta zamto jaruma mai ji da jarumtaka ga tsafi daga gada a gareta, wannan ranace da take fatan zuwanta take xaukin zuwanta, ga shi ta ganta suka juma a rungume da juna daga bisani suka rabu a hankali Bokanya Namsu ta ce mata “Ya aka yi kika san ina nan?” Sultum ta dubeta da murmushi sannan tace mata. “Wani madubi na tsafi na samo a hannun wani boka da muka yi yaqi da shi a duk lokacin da na buqaci zuwa wurin mutum ina ambatar sunan shi sai na duba jikin madubin zanga inda yake, to da na so dawowa gida wurinki shi ne na ambaci sunanki sai na ganoki kuna fafatawa da boka sharbanga shi ne na yi gaggawar tahowa gareki, domin kawo miki xauki domin nasan halinsa gwani ne wajen iya yaudara” Ta gama faxa mata tana mai fitowa da madubin ta nunawa Bokanya Namsu ta amshi madubin tana nazarinsa lokaci xaya ta yi murmushi “Ina fatan baki halaka Bokan da kika amso wannan madubin ba?” Sultum ta dubi mahaifiyarta cike da mamaki sannan ta bata amsa da cewar “Ina mai fargabar ce miki Bokan ba zai tava halaka ba, har sai wa’adinsa ya yi domin na sameshi tsayayen jarumi mai jarumtaka wayeyye a fannin sihiri na sirri ya karantu ya yi nisa a tsafi da sanin alqaluman tsafi, ya mallaka min shi domin ya yaba da jarumtakata”. Bokanya Namsu ta yi ajiyar zuciya lokaci xaya ta yi murmushi. Sultum ta dube shi cike da mamaki ta qara cewa da ita “Ko kin san shi ne?” Bokanya Namsu ta dubeta ta sake yin murmushi kafin ta bata amsa da cewar “Shi ne mahaifinki ba domin yasan ke ‘yarsa bace da ba zai tava mallaka miki wannan madubin tsafin ba, ya yi hakane kuma domin duk inda kike ya kasance yana kallonki irin wannan madubin guda uku ya haxa ya xauki biyu ya mallaka min xaya kafin mu rabu da shi” Ta gama faxa mata hakan tana mai xauko mata nata madubin Sultan ta saka hannunta ta amsa ta yi nazarinsa ba shi da bambanci da nata ta girgiza kanta. Bokanya Namsu ta dubi wanda ya ke riqe a hannunta a hankali tace “Ina son sanin inda bawa Farsu yake” Tana gama rufe bakinta sai bakin gavar tekun ta bayyana a jikin madubin sannan hoton aljanin da ya xaukosu ya bayyana shi ma kai tsaye ya nufi gabashin tekun da su. Ta mayar da madubin ga ‘yarta kafin tace mata “Mu nufi bakin gavar tekun ta hanyar gabas”A hankali suka nufi bakin gavar wajen da su gimbiya lusa suka nufa. ** Nahiyar yamma maso kudu ita ce mahaxa da ta tattara taron baqa fata wanda adadinsu ba zai qidudugu ba, amman duk bayi ne qasar Margas ta zamto fitattaciyar qasa da ta ke yankin. Domin ta zama qasa da mutanen cikinta suka gwanance wurin sana’ar kamun kifi wato ma sunta ne, sai kuma saye da siyar da baya hakan yasa qasar ta zamto mahaxa ta nahiyar yammaci. Ko wacce safiya jama’ar qasar sukan fito bakin tekun garin su yi kamun kifi amman banda ranar juma’a da asabar wannan ranakun ba sa zuwa kamun kifaye. Sarauniya Zultum itace ke mulkin qasar, ta hau mulkin qasar kimanin shekaru uku da suka gabata a lokacin shekarunta ba su gaza sha takwas ba, a rayuwar sarauniya Zultum babu abinda yake birgeta tamkar ganin mutum ya nuna wata bajinta ta ban mamaki, wannan dalilin ya saka duk shekara a qasar take saka gasar kamun kifi duk wanda ya kama wanda ya fi na kowa girma to za a yi masa kyauta mai qayatarwa talakawan qasarta suna matuqar jin daxin wannan gasar da sarauniya Zultum ta ke sawa. A wannan shekarar gasar ta sauya salo domin sarauniya Zultum ta fito da kanta ita ma zata yi kallon gasar savanin sauran lokutan baya sai dai ta tura wakilai kuma ta yi alqawarin cewar zata auri duk wanda ya samu nasara a gasar amma zata faxa masa sharuxan sadakinta wanda ta tabbatar ba qaramin namiji ne zai samu nasara a gasar ba har ya aureta. Wannan kalamin nata ya sa masoyanta suka dunga varkowa daga duniya mafiya yawansu ‘ya ‘yan sarakai ne sai tsarukansu ‘ya ‘yan attajirai da talakawa domin daman masoyanta sun daxe suna jiran su ji sharuxan aurenta. ‘Ya ‘yan sarakuna da attajirai suka yi ta neman sa’a a wurin bokaye da masu sihiri domin su samu su shiga cikin tekun ba tare da wata matsala ba kuma sa’a ta tabbata a garesu. Habaru ya kasance saurayi matashi mai tsananin taqadiranci da rashin jin magana a kullum sai Habaru ya janyowa iyayenshi magana, ba a kawo qararsa gida wajen iyayenshi a rana ba a kawo qara sau saba’in ko ma fiye da haka domin duk wurin da ya je sai an kawo qarashi. Baban Habaru wani tsohon masunci ne da sana’ar sa bata magance masa komai game da talaucin da suke ciki. Habaru bai wani tsaya ya mayar da hankali ya koyi sana’ar babanshi ba ga kuma tsufa sosai ya kama shi. A yayin da shi kuma Habaru kullum tunaninsa ta yaya zai mallaki dukiya ta wata hanyar, domin shi dai ya yi duba sosai ya ga cewar a duk masu sana’ar kamun kifi bai tava ganin wanda ya yi kuxi da sana’ar ba. A lokacin da labarin gasar sarauniya ya zo masa sai shima ya ji cewar ya kamata ya shiga domin ko banza idan ya samu nasara zai samu damar auren sarauniya shima ya shiga cikin ma su mulki, ya kasance ana kaxa masa tambari tare da kirarin. Sai Habaru xan tsohon masunci, talaka mai qashin arziqi. Wannan tunanin da ya yi shi ya ja hankalinsa ya je ya bayar da sunansa a cikin masu shiga gasar. A lokacin da labari da labari ya watsu cewar Habaru ya shiga gasar auren sarauniya sai jama’a da dama suka riqa yin addu’a Allah yasa ya mutu a wurin gasar domin sun gaji da irin taqadirancinsa. Mahaifin Habaru yasan babu wani abu da xansa zai iya kuma lokaci ya qure balle ya koya masa dabaru na kamun kifi don haka ya kirashi domin ya yi masa nasiha. Da Habaru ya samu mahaifinsa sai ya samu wuri ya zauna ya yi shiru yana kallonsa mahaifinsa ya dubeshi a hankali yace masa. “Abubuwa biyu zan gaya maka” Ya yi shiru yana kallonsa sannan ya ci gaba da cewar “Na farko ka saka a ranka cewar nasara Allah shi ne yake bayarwa ga wanda ya so” Ya kuma yin shiru karo na biyu yana dubansa kafin ya ci gaba da magana “Na biyu ka yi addu’a a koda yaushe domin Allah yana taimakon bawansa” Ya sake saurarawa kafin ya ci gaba da magana “Waxannan abubuwan su kaxai zan gaya maka daga su babu wani abu da zan iya yi maka sai fatan alheri xana”. Habaru ya yi shiru yana kallon fuskar mahaifinsa wadda ta tattare domin tsufa da ya kamashi, wannan shi ne karo na farko da mahaifinsa ya gaya masa wani abu da zai amfaneshi a rayuwarsa. Domin abunda Habaru ya xauka game da mahaifinsa a baya babu abinda zai iya faxa masa.babu kuma wani abu da zai tsinana masa sai talauci da ya yi masa qabe-qabe a rayuwarsa. Habaru ya tashi a kasalance ya koma xakinsa ya zauna ya yi shiru yana tunanin abubuwa da dama da suka zo masa kai da kuma waxanda suka tunkaro rayuwarshi. A zahiri yana da masaniyar cewar ba shi da wata dabara ko qwarewa da zata taimaki rayuwarshi har ya kai ga samun nasara, ba shi da wata mafita kawai dai zai jarraba sa’arsa a sana’ar da iyayensa suka gada. Habaru ya tashi a hankali ya je ya yo alwala ya yi sallah ya xaga hannunsa sama ya soma roqon Allah akan ya ba shi nasara game da gasar daya shiga. A haka ya tafiyar da lokacinsa. Rana ta xaga bakin teku ya cika maqil da mutane kowa yana jiran ya ga yadda gasar zata kasance da kuma ganin wanda zai samu nasarar zama wanda zai auri sarauniya zultum. Duk waxanda suka shiga cikin gasar sun gama halarta a wurin suna juran zuwan sarauniya Zultum domin soma gudanar da gasae duk wanda ka duba za ka samu ya shirinsa wasu sun rataya kayan tsatsubarsu a wuyansu wasu kuma a ciki, wasu a baki kowa ka kalla akwai irin shirinsa.. Xan Boka Margadasy ya fi kowa qwarin gwiwar samun nasara tana gareshi domin mahaifinsa ya ba shi wata sanda da ya riqeta a hannunsa wanda da zarar lokacin fitowa ya yi idan ya fito zata rikixa ta zama qatoton kifi da babu wanda zai kama kamarsa domin babanshi mashahurin matsafi ne da shahararshi ta kai ko ina. A haka lokaci ya yi sarauniya zultum ta qaraso wurin ta samu wuri ta zauna a cikin tanti da aka tanadar mata, daga wajen da take zaune tana kallon duk abinda yake faruwa ‘yan takara suka gabato gabanta suka yi gaisuwa ta girmamawa ta dunga kallonsu xaya bayan xaya a haka suka kammala zuwa daga nan aka bada damar shiga cikin teku domin soma gabatar da gasa. Makaxa da mawaqa suka soma kaxawa masu gasar kixa suna kambama gwanayensu da kalamai da suke qara musu qwarin gwiwa a haka har suka qarasa zuwa ga bakin teku kowa ya gama shirinsa sanna aka soma shiha cikin ruwa domin fara gudanar da gasar. Habaru ya juma a tsaye a wurin yana addu’a domin neman samun nasara a wajen ubangiji daga nan ya yi tsalle ya faxa cikin teku ya nutse ya yi qasan ruwan domin laluben kifin da zai kamo. A hankali lokacin ya tafi waxanda suka shiga cikin gasar suka soma fitowa xan Voka margadasu ne ya fara fitowa daga cikin tekun janye da wani murgujejejn kifi daya baiwa kowa mamaki domin a tarihi ba a tava ganin wani wanda ya kamo tamkarshi ba tun daga lokacin kowa ya saduda ya yarda cewar lallai shi ne mai nasara a gasar babu wani da zai iya kamo wanda ya fi nashi. Sarauniya zultum tana zaune tana kallon duk abubuwan da suke tafiya duk wanda ya fito sai ya fito da kifin da bai yi ko da rabin na shi ba da zarar ya qyallara idanu ya ga sihirtaccen kifin da xan Boka Margadasu ya fito da shi sai ya yarda nashi domin yana da tabbacin ba zai kai labari ba. Xan Boka ya yi ta qyalqyala musu dariyar mugunta yana mai alfahari da yiwa kansa kirari gami da ambaton nasaba a haka kowa ya gama fitowa ya kasance sauran Habaru can bayan tsawon wani lokaci sannan Habaru ya fito yana janye da wani abu da qyar domin matuqar nauyi da ya yi masa idanuwan kowa ya koma kanshi. Habaru ya fito daga cikin ruwan yana janye da wani murgujejen kifi wanda ya ninka na xan Boka Margadasu sau biyu, domin yana ganin na shi shima ya tsorata da ganinsa domin tunda yake a rayuwarshi bai tava tsammanin wani xan Adam zai iya kamo kifi kamar wannan ba. Jama’a duk aka bar kallon sihirtaccen kifin da xan boka Margadusu ya kamo aka koma kallon na Habaru sarauniya Zultum da kanta ta tashi ta je ta taryo Habaru da kanta ta yi masa jinjina bisa nasara daya samu. Mafarkin da Habaru ya yi ya kusa zama gaskiya. Washe gari Habaru ya zo fada cikin kayan alfarma fadawa suna take masa baya, ya zube gaban sarauniya ya yi gaisuwa ya sunkuyar da kansa yana jiran ya ji abinda za a yanke masa a matsayin sadakin auren sarauniya zultum bayan wucewar wasu ‘yan lokuta sannan ta nisa gami da faxin “A yau na tsayar da mijin aurena, sannan kuma a yau zan yanka masa sadakin aurena ko a yanzu ya samo ya kawo mun shi za a xaura mana aure” Ta xan yi shiru kafin ta ci gaba da magana cikin nutsuwa “Ka yi sani cewar a lokacin da mahaifinmu ya haifemu mun kasance ‘yan biyu mahaifiyarmu ta haifa. Duka mu biyun kamarmu xata babu wani bambanci wata rana sai wani aljani ya sace xaya daga cikinmu domin tsabar son rai nasa wannan abun ya matuqar qonawa mahaifinmu rai wanda sanadin wannan baqin cikin shi ya zama ajalinsa, ita kuma mahaifiyata tun lokacin take fama da baqin cikin abun kullum tana cikin kuka. Saboda haka wannan ‘yar uwar tawa nake son ka nemo mun wacce a yanzu haka tana cikin wannan duniyar tamu wannan shi ne sadakin aurena” Ta xan yi shiru sannan ta qara da cewar. “Kamarmu xaya sunanta Gimbiya Lusa”. Habaru ya yi shiru yana jinjina lamarin a ranshi, a rayuwarshi wannan shi ne karo na farko da zai aikata aikin wahala ya sunkuya yace mata. “Insha Allahu zan nemo miki ita” Fadawa suka yi kabbara domin qarfafa masa gwiwa. Washe gari Habaru ya gama shirinsa ya fita mahaifinshi ya rakasa har bakin qofar gari ya xauko wata takobi ya ba shi suka yi sallama da juna. ** Su gimbiya Lusa suka sauka a daidai gavar teku suka yi shiru suna duban-duba suna tunanin abinda ya kamata su yi, suka soma shawarwarin hanyar da ya kamata su bi. Suna cikin shawara ne bawa Farsy ya hango mace a kwance a gefen gavar tekun ga alama ruwa ne ya ciyota da sauri ya nufi wurin ya qarasa ya janyota ya fito da ita ya dubeta a nutse ya ganta baqar fata kyakkyawa wacce idanuwanshi ba su tava ganin mai kyawunta ba ya zuba mata idanu yana kallonta cike da mamakin irin kyawu da ya gani tana da shi, a haka su Gimbiya Lusa suka qaraso suka sameshi. Gimbiya lusa ta tsuguna a gabanta ta saka hannunta ta danna qirjinta take ta soma aman ruwan data sha, zuwa wani xan lokaci ta farfaxo ta zuba musu idanu tana kallonsu har zuwa wasu ‘yan sakani kafin tace mata “Na gode da taimakon da kika mun”. Bawa farsu ya yi murmushi a hankali yace mata “Ba komai dolen mu ai mu taimaki kyakkyawa kamarki” Ya gama maganar yana mai wasa da sarqa tsafin dake hannunsa. Ta kalleta kafin ta sake cewa “Wannan sarqa tana da kyau, ta matarka ce?” Ya dubeta ya dubi sarqa ya bata amsa da cewar. “Ba ta matata bace, ni bani da mata” Ta yi murmushi tare da qara kashe murya tace masa. “Na ga tana da kyau za a iya bani na ganta?” Bawa Farsu ya kalleta ya kalli sarqa ya xanyi shiru na wasu ‘yan sakani tamkar ba zai bata ba daga bisani ya miqa mata ta miqa hannu zata amsa sai Gimbiya Lusa ta yi sauri riqe hannunsa su duka suka mayar da kallonsu gareta a hankali tace da bawa Farsu “Kar ka yarda da ita mayaudariya ce”. Maganar ta tsaya wa bawa faru a rai ya juya ya kalli fuskar budurwa kyawun fuskarta ya mamaye masa rai ya juya ya dubi Gimbiya lusa yace mata. “Ba mayaudariya bace sai dai kece mayaudariya” Yana gama gaya mata ya juya ya miqa mata sarqa a hankali yace mata “Ga ta ki gani ki dawo mun da kayata” Tana saka hannu ta amsa ta dubeta a tsanake sannan ta dubi bawa farsu ta qyalqyale da dariya ya dubeta a tsorace dariyar ta janyo hankalinsu. Suka zuba mata idanu suna kallonsu ga mamakinsu sai suka ga ta miqe ta yi wata girgiza take kamaninta suka sauya zuwa na sarauniyar aljanun cikin ruwa ta xaga sarqa akan idanunsu kafin tace musu. “Ta tafi kuma ta dawo, don haka yanzu zan halakar da ruhinku gaba xayanku” Tana gama maganar bawa Farsu ya zare takobinsa da sauri ya kai mata sara, tayi tsalle gefe xaya saran ya wuce ta yi tsalle akan iska ta koma can gefe nesa kaxan da su, ta dube su ta yi nuni da hannunta zuwa ga wani wuri nan da nan wuta ta kama itatuwan da suke dajin ta nufi wurin da suke da zumar halakar da ruhinsu. Sarauniyar aljanun cikin ruwa ta qyalqyale da dariya. Bawa farsu ya dubi sihirtaciyar wutar data yo kansu tana cinye duk abinda ta samu, sai ya juya ya dubi su Gimbiya Lusa yace musu. “Duk wanda zai iya yakan iya biyoni” Yana gama maganar ya nufi wurin da wutar take tahowa a guje takobinsa a zare. Gimbiya Lusa ta bishi da kallo a hankali ta juya ta dubi sadauki Ansar tace masa. “Wannan baqar fatar ba qaramun hatsabibi bane, ban tava ganin mutum kamarshi a”> Wutar ta ci gaba da nufosu da zumar halakar da su… Alhamdulillahi masha Allah. Sauran labarin zai zo muku a cikin littafin ABOKAN GABA 3 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3