abu a kusa
da shi ya yi saurin buxe idanunshi ya dubi abinda
ya sauka a kusa da shi. Wani farin aljani ne mai
kyawun siffa daga cikin jinsi aljanu dudud
shekarunsa ba za su gaza xari uku zuwa huxu ba,
wannan aljanin ya zamto mai ganiyar quruciya a
jikin shi kuma mai ji da sadaukantaka.
Yana sauka ya dubi sadauki Ansar yace
masa “Ungulaye ba za su ci gangar jikinka ba
domin ranar mutuwarka ba yi ba” Yana gama
faxar hakan ya yi gaggawar xauko wata buta ya
zubawa sadauki Ansar wani ruwan da yake cikin
butar a gangar jikinsa nan da nan sadauki Ansar ya
soma jin qarfin jikinshi ya soma dawowa jikinshi.
Bayan wucewar awanni uku sadauki
Ansar ya ji duk wata gajiya da wajen da yake masa
ciwo ya daina, ya zamto tamkar wani abu bai tava
samunshi ba, ya dubi farin aljaninan da duban
girmamawa sannan a hankali yace masa.
“Godiya gareka da ka zamto ka
taimakaeni ka kuvutar da rayuwata” Sadaukin
Ansar yace masa. Shi kuma ya dubi Ansar a
hankali yace masa “Sunana aljani zammaru na
zamto xaya daga cikin ‘yan qabilar bamu shammat,
kuma na zamto daga cikin jinsi aljanu mabiya
addinin musulunci na zo ne domin na taimakeka
na kuvutar da kai daga halaka, domin duniya tana
buqatarka idan ka halaka za a rasa jarumin da zai
sasanta rigimar da zata mamaye duka duniya ta
sace ruhin sarkin aljanu gamsu” Sadauki Ansar ya
dubi Aljani zammaru da matuqar mamaki sannan
yace masa.
“Ta ya zan sasanta rigimar da dominta
aka so hallakani? Ni musulmine babu ruwana da
abinda ya shafi kafirai” Ya tabbatar masa.
Aljani zammaru ya yi murmushi sannan
yace “Akwai matsala babba tun da aka sato ruhin
sarki aljanu Gamsu matsalar ita ce sarkin aljanu
Gamsu ya zamto adalin sarki mai taimakon
talakawa mai kare addinin musulman aljanu duk
da cewar ya zamto shi ba ma’abocin musulunci
bane, hakan yasa a lokacin da aka sace ruhin na
shi duk wani musulmin aljani ya shiga cikin
fargaba da tsoro domin sun san za su soma samun
tursasawa daga sauran azzaluman sarakunan aljanu,
shi yasa na zo gareka domin neman ka taimaki
musulmai ‘yan uwanka a sassanta a dawowa da
adalin sarki ruhinsa ko ma ci gaba da ibada a cikin
kwanciyar hankali ba tare da zullumi ba”.
Sadauki Anwar ya yi shiru na tsawon
wani lokaci yana tunani daga bisani ya xago da
kanshi ya dubi aljani zammaru yace masa.
“Na yadda zan nemo wannan ruhin duk
inda yake domin mayarwa da sarkin aljanu Gamsu
koda hakan yana nufin sai an gabza yaqi, da izinin
Allah nasara tana gareni” Ya kammala maganar
yana dubansa kafin ya qara da cewar “Yanzu ina
za mu riski wanda ya sace wannan ruhin?” Aljani
zammaruu ya dube shi sannan ya bashi amsa da
cewar.
“Wata bokanya ce baqar fata, ta saka
wani hatsabibin bawanta shima baqar fata ya sato
wannan ruhin, domin haka za mu iya riskarsa a
hanya kafin ya qarasa zuwa gareta” Sadauki Ansar
ya girgiza kanshi cikin gamsuwa sannan yace wa
aljani zammaru “Za mu iya yin gaggawa domin
zuwa riskarsa” Yana gama maganar ya yi tsalle ya
haye bayan aljani zammaru lokaci xaya shima ya
buxe fuka-fukanshi ya tashi da shi sararin
samaniya.
Suka bi bayan baqar fata bawa Farsu
daya sace ruhin sarkin aljanu Gamsu.
BAQAR FATA BAWA FARSU
Yana zaune a bayan aljani a ranshi yana
jinjina irin girman siffa da muni da wannan aljanin
yake da shi. Suka zo tsakiyar wani teku mai girma
da faxi, tun da farsu yake a rayuwarsa bai tava
ganin teku mai girma tamkar wannan ba. A
hankali ya leqo da kanshi yana kallon ruwan tekun
yana cike da al’ajabi.
A dai-dai lokacin da suka zo dai-dai
tsakiyar tekun a lokacin tamkar walqiya su
Gimbiya Lusa suka bayyana a gabansu.
Aljanin da yake xauke da Farsu ya dakata
da tafiya da yake yi cike da tsoro da fargaba.
Ganin ya dakata yasa Farsu ya dawo da hankalinsa
gabansa idanunsa suka gane masa su ya girgiza
kansa cike da jimami. A hankali su Gimbiya Lusa
suka matso daf da juna ta miqe tsaye daga kan
aljanin da take kai, tana zuwa dai-dai inda aljanin
da Farsu uake kai ta daka wani tsalle ta dawo
kanshi.
Farsu ya yi gaggawar miqewa domin
ganin ganin abinda ya faru, suka tsaya suna
kallon-kallo da shi da Gimbiya Lusa. Cikin
tsananin hasala tace masa.
“Na zo domin amsar ruhin mahaifina
sarkin aljanu Gamsu wanda ka sace” farsu ya
dubeta a fusace shima yace mata “Amman kin
yaudari kanki ‘yar budurwa da kike kiran aljani
mahaifinki, kin tava ganin aljani ya haifi mutum?
Sannan saboda tsananin ganganci shi ne za ki
sadaukar da rayuwarki domin ki halaka kika
biyoni domin amsar ruhin” Ya saurara kafin ya
qara da cewar.
“Yar kyakkyawar budurwa duk kyawun
surarki hakan ba zai hanani saka takobi na a
tsakiyar siririn wuyanki na raba kanki da
kyakkyawan gangar jikinki” Ya gama magana
yana mata wani shu’umin murmushi.
“Kai baqar fata gafalalle kayi sani cewar
ni ce Gimbiya Lusa mai maganin duk wani xan
iska! Dan haka ka bani ruhin da ka sato cikin
ruwan sanyi ya fiye maka kafin wannan
mummunar baqar fuskar taka ta gamu da azabar
kaifin takobina wacce bata san komai ba sai shan
jinin sadaukai ma su ji da jarumtaka da taurin kai”
Cikin murya tsawa-tsawa tace masa.
Farsu ya dubeta a fusace cikin daka tsawa
yace da ita “Ahir! Xinki da dubana ki gayamun
irin waxannan kalaman bana tunanin akwai wani
jarumi da zai iya tsoratani da jarumtakarsa ko
kalamansa na kurari na baki, balle ke mace mai
raunin jarumtaka” Gimbiya Lusa ta girgiza kanta
cikin tsananin takaici ta sassauta murya tamkar
mai yi masa raxa tace da shi cikin fushi.
“Ka yaudari kanka da har kake tunanin
gwara na amshi ruhin da tsananin jarumtaka, a
yanzu ne za ka san cewar ka yi gagarumin kuskure
kuma zaka rabe tsakanin aya da tsakuwa, domin
yanzu zan farauce ranka na kuma cilla wannan
mummunar gawar taka cikin teku” Tana gama
faxa masa ta zare takobinta lokaci xaya ta dubeshi
tace “Yau zamu yi gaba da gaba da kai domin
sanin bambanci a bayyane yake”. Ta sake yin
murmushi.
“Ni da kai ABOKAN GABA ne, don
haka mu kan iya soma farautar rayukan junanmu”
Tana gama maganar ta kai masa wani wawan sara
da zumar tsinke zaren da yake sarqe da ruhin cikin
zafin nama ya kaucewa saran sannan ya wuce tare
da wani hucin iska mai qarfi.
Farsu ya dubeta ya girgiza kanshi, sannan
ya gyara riqon takobinsa. Suka yi xauki kan
junansu lokaci xaya suka gauraya da mummunan
artabu a wuri xaya suna musayar kai sara da
suka.qara gami da tartsatsin haxuwar makamansu
ya karaxe sararin saman tekun. Ko wannensu ya
himmatu domin ganin ya samu nasara akan abokin
gabansa. Gimbiya Lusa ta samu Farus ba yanda ta
yi tsamaninsa ba, domin ta same shi dakakken
namiji mai tsananin jarumtaka, turjiya gami da
zafin nama. Haka shima Farsu ya sami Gimbiya
Lusa cikakiyar jaruma mai qarfin damtse da zafin
nama wajen kai sara da kare kanta. Jarumar da tafi
jarumai da dama qwarewa da sanin salo-salo na
yaqi.
Haka suka ci gaba da mummunan
gwamza yaqi mai tsananin ban mamaki a
tsakaninsu, suka wanzu wajen kaiwa junansu
miyagun sara da suka da niyar farauce ran juna.
Bayan sun xaki dogon lokaci suna wannan
fafatawar a lokacin wani abu ya sauka a
tsakaninsu.
Jin saukar abin shi ne ya tilasta musu
dakatawa da yin yaqin su duka suka dubi abun. A
lokacin idanun Farsu ya sauka akan Bokanya
Namsu uwar gidanshi da ta saka shi aikin idan ya
sami nasara zata ‘yanta shi. Ganinta ya saka ya ji
wani daxi ya lulluve shi. Bokanya Namsu tace
masa cikin sassauta murya.
“Maza miqo mun ruhin naga ko wannan
qaramar qwaruwar zata iya amsa a wajena, kai
yanzu ka kammala aikinka ka gama yi mun bauta
don haka na ‘yanta ka” Waxannan kalaman sun
matuqar qayatar da zuciyar Farsu. Don haka cikin
gaggawa ya miqa hannu ya xauko ruhin daga cikin
inda ya adana shi ya dubi Bokanya Namsu itama
ta dubi Ruhin.
Gambiya Lusa ta dubi ruhin mahaifinta
sarkin Aljanu Gamsu. Ba su yi aune ba sai jin dirar
wani abu suka kuma ji Yif! Kamar an sauke
nannauyan dutse cikin gaggawa suka kai kallonsu
idanun Farsu ya kuma ganin wata Bokanya Namsu
a tsaye ya dubeta cikin tsananin mamaki yanzu sun
zama su biyu ma su kama iri xaya sak kamar an
tsaga kara.
“Wace ce kenan ta gaskiyar?” Ya
tambayi kansa kamar amsar tambayarsa ya ji ance
masa.
“Ni ce uwar gidanka Bokanya Namsu”
Da kakkausar murya tace masa.
Xayar itama ta matso gareshi tace masa
“Ni ce uwar gidanka Bokanya Namsu”.
Farsu ya zuba musu idanu yana kallonsu
cikin ruxani ya kasa tantance wace ce ta gaskiyar
wace ce ta qarya.
A lokacin aljani Zammnaru ya qaraso
shima xauke da sadauki Ansar a bayansa shima ya
bi ruhin da kallo ya mayar da kallonsa ga Gimbiya
Lusa sanna ya haske mata fuska da murmushi
lokaci guda kuma cikin tsananin zafin nama ya
zare takobi ya kaiwa farsu sara a hannun da yake
xauke da Ruhin sarkin Aljanu Gamsu take ruhin
ya zame daga hannunsa ya yi qasan teku.
Farsu ya juya ya dube shi ya kuma dubi
Gimbiya Lusa yace mata “To kyakkyawa ruhin
mahaifinki ya faxa cikin teku, ko za ki biyoni
cikin tekun mu ci gaba da fafatawa” Yana gama
maganar ya sulmiyo daga kan aljanin ya biyo
ruhin daya sulmiyo qasan teku.
Gimbiya Lusa ta girgiza kanta tunda take
a rayuwarta ba ta tava ganin hatsabibin mutum
kamar wannan baqar fatar ba. Itama ta daka tsalle
ta biyo bayanshi.
Ganin haka ne ya sa sadauki Ansar shima
ya sulmiyo ya yo qasa shima ya biyo bayan Ruhin
sarkin Aljanu Gamsu da ya yo qasan taiku.
A cikin tekun sarauniyar aljanun cikin
ruwa ta tara mayaqanta suna tsaye suna sauraren
qarasowar ruhin sarkin aljanu Gamsu. Tun kamin
shekaru xari uku Bokanta ya faxa mata cewar
Ruhin zai faxo a nan wurin tun lokacin ta zauna
zaman jiran faxowarsa.
Ruhin ya faxa cikin ruwan tekun ya
zamto tamkar an cilla wani nannauyan dutse mai
nauyi lokaci xaya ya yi qasan teku. Sarauniyar
aljanun cikin ruwa tana zaune akan karagarta tana
jiran faxowar ruhin. Tsayin shekara xari uku
kenan tana zaune zaman jiran faxowarsa. A
lokacin da bata yi aune ba taji faxowar abu akanta
tayi gagawar buxe idanunta ta dubi abin da
idanunta suka gane mata abinda ta jima tana zaune
zaman jira tsawon shekaru, tabbas Ruhin sarkin
aljanu Gamsu ne wani daxi ya mamaye cikin
zuciyarta da gaggawa ta miqe cikin azama ta miqa
hannunta ta xauki ruhin ta zuba masa idanu tana
kallonsa.
Ta juya cikin gaggawa ta xagashi sama a
gaban idanun jama’arta cikin xaga murya tace
musu “Abinda muka jima muna zaman jiran shi
yau mun same shi” Duka hankalin dakarun ya
tattara akanta suka zuba mata idanuwa suna kallon
ruhin sarkin aljanu Gamsu da yake riqe a hannunta
sannan lokaci xaya suka ruxe da shewa da
kururuwa suna ma su xaga makamansu sama.
A lokacin Bawa Farsu ya faxo tsakiyar
wurin ya miqe tsaye da matuwar mamaki domin a
tsammaninsa zai yi nutsu a cikin ruwa ya yi qasan
tekun amma ga matuqar mamakinsa sai ya ga ya
faxo tsakiyar wani fili mai yanyame da dakarun
aljanu cikin shirin yaqi. Ya zuba musu idanu yana
kallonsu suma suka zubo masa idanu aka soma
kallon-kallo a tsakaninsu kamar akuya da kura.
A lokacin suma su Gimbiya Lusa suka
faxo tsakiyar wurin suka miqe tsaye suka zubawa
wurin idanu cike da matuqar mamaki. Sarauniyar
aljanun cikin ruwa ta dube su cikin mamaki lokaci
xaya yanayin fuskarta ya sauya daga farin ciki
zuwa vacin rai ta dubi Ruhin sarkin aljanu Gamsu
da yake hannunta ta yi murmushi sannan ta buxe
wata jaka da take xaure a gefen qugunta ta saka
Ruhin a ciki ta mayar ta rufe kafin ta mayar da
dubanta zuwa ga su Farsu dake tsaye carko-carko
kamar wasu zakaru cikin murya tsawa-tsawa tace
musu.
“Kai baqar fata wanne irin shisshigine ya
kawoka cikin fadata” Farsu ya dubeta cikin
nutsuwa kafin ya bata amsa. “Ni ne baqar fata
Farsu na zo ne domin amsar Ruhin da yake
hannunki domin bai dace da ke ba” Maganarshi ta
zamto tamkar sukar kibiya a cikin zuciyar
sarauniyar aljanun cikin ruwa, ta yi zaman shekara
xari uku tana jiran abu yau ta same shi sannan
wasu za su ce sun zo domin su rabata da shi? Ta
dube shi sheqeqe.
“Babu makawa duk duniya babu wani
wanda yake da jarumtar da zai iya amsar wannan
Ruhin daga hannuna, idan kuma akwai jarumi to
yana iya gwadawa” Cikin izza ta faxa.
Gimbiya Lusa ta dubeta sannan cikin
xaga murya tace mata “Na yi zaton mutane ne
kawai suke son sace ruhin mahaifina sarkin aljanu
Gamsu, ashe ba haka bane a cikin duniyar aljanu
ma akwai masu buqatar shi, don haka ina mai
tabbatar miki cewar za ki zamto aljana ta farko da
zan soma sadarwa zuwa ga ajalinta” Jin haka yasa
sarauniyar aljanun cikin ruwa ta yi dariya sannan
ta nunata da yatsa tace mata.
“Duniya ta daxe da wayewa Gimbiya
Lusa don haka na gaba ya yi gaba” Gimbniya Lusa
itama ta xaga hannu ta nunata. “Babu makawa zan
dawo da na gaba baya, domin duk tsohon da bai ji
kunyar hawa jaki ba to shima jaki ba zai ji kunyar
kayar da shi ba. Da mai jini a jika shi ne wanda
zamani yake tafiya da shi, don haka ke mai tashe
ce ni kuma mai zamani, saboda haka za ki bani ta
lumana ko kuwa sai kin ga jinin sadaukanki yana
malala tamkar magunar ruwa” Maganar ta zamto
tamkar ta watsawa sarauniyar aljanun cikin ruwa
wuta a zuciyarta cike da fusata ta dubeta.
“Lallai za ki yi nadamar wannan furucin
naki, domin sai na ladaftar dake bisa kuskuren da
kika yi” Tana rufe baki ta dubi yawan dakarunta
da suke mamaye da wajen cikin isa da qasaita tace
mu musu “Maza ku yi mun maganin waxannan
qananin halitar” tana rufe bakinta dakarun suka
zaburo a fusace makamansu a zare za su yi
sukuwar sallah akan su.
Hausa qarasowa zuwa garesu
suna
tsaye suna kallonsu, sai da ya zamto baifi sauran
taku goma ba sannan Ansar ya daka musu tsawa,
wanda hakan ya haddasa musu tsawa waj e xaya
lokaci guda yace wa sarauniyar aljanun cikin
ruwa.
“Kin yi babban kuskure wurin turo
dakarunki domin su yaqe mu, don haka ki saurara
kiga yadda za mu qare da su kafin mu qaraso
gareki” Yana gama maganar ya zare takobinsa
sannan cikin azama ta bazata ya yi xauki garesu,
ganin tahowarsa yasa suma dakarun suka kuma
zaburowa suka gamu a tsakiya kasuwar yaqi da
saye da sayarwa rayuka ta soma ci mutuwa ta
soma shawagi tana farauce ruhin aljanun cikin
ruwa.
Masifa irin ta yaqi ta dunga sauka a
wurin kai sara da kai suka ya yawaita zubar jini da
malalarsa ya wanzu a wurin qasan tekun ya
hautsine wanda hakan yasa ruwan tekun ya soma
tambal-tambal tamkar zai malalo cikin duniya.
Bawa Farsu ya zamo tamkar wata annoba ta wuta
a cikin tsakiyar gonar auduga domin duk wurin da
ya sa kai sai dfai ka ga kawuna suna yawo a sama
tamkar tsuntsaye, jikuna suna zubewa qasa babu
kawuna haka itama Gimbiya Lusa ta wanzu tana
saukar musu da azabar yaqi.
Kafin wani lokaci sun yiwa rundunar
fata-fata sai tsirarun xaixaikun dakarun suka rage
ganin sun zama tsiraru ya saka sauran suka yadda
makamansu suka yi mubaya’a. ganin haka ya sa
ran sarauniyar aljanun cikin ruwa ya matuqar
dugunzuma ta dube su cikin tsawa tace musu
“Qasqanci ya tabbata a gareku halaka ta zama dole
a gareku” Tana gama maganar ta zare takobinta
dake xaure a xamarata sannan lokaci xaya ta
tunkaresu da zumar ta yaqe su ganin irin wannan
tahowar da ta yi ya sa bawa Farsu ya taryeta tun
kafin ta qaraso suka yi wata muguwar haxuwa
takubbansu suka gamu a wuri xaya, wata qara mai
qarfi ta cika wurin sannan wata wuta ta buga ta yi
sama, suka soma musayar sara da suka a
tsakaninsu zuwa tsawon lokaci, ganin lokaci yana
tafiya a banza ya sa bawa Farsu ya tunzura ya qara
qaimi wurin kai sara da suka gareta can ya xauki
numnfashinta ya kai mata wani kaitattacen sara a
wuya da zumar tsinke mata kai.
Ganin tahowar saran ya sa sarauniyar
aljanun cikin ruwa yin qoqarin kaucewa domin kar
saran ya sameta amman ta makara domin sai da
saran ya sameta kaxan a wuyanta. Ba don wata
sarqa da take rateye a wuyanta ba wacce saran ya
tsaya akanta, amman banda haka da saran ya yi
tasiri akanta da tuni wani labarin ake yi ba nata ba.
Sarqa ta zamo daga wuyanta ta sulmiyo ta yo qasa.
Bawa Farsu ya ga tahowarta ya miqa hannunsa ya
taryota ya riqeta a cikin tafin hannunsa ya yi
zamiya yana kallonta.
Ita ma ta dube shi na wani lokaci, a
tsawon rayuwarta yau ita ce ranar farko da wani
sadauki ya tava wanzuwa a gabanta tsawon lokaci
har ya ke qoqarin samun nasara akanta, a
rayuwarta bata xaukar wani tsawon lokaci suna
fafatawa da wani sadauki, sai ta farauce rayuwarsa
amma ga mamakinta sai ga baqar fata ya zamar
mata ciwon ido. Suka zubawa junansu idanu suna
kallon juna bawa Farsu ya dubi sarauniyar aljanun
cikin ruwa ya dubi sarqa da take riqe a hannunsa
ya xagata sama ya nuna mata ita ta bi sarqa da
kallo cike da mamaki da baqin cikin ganin ya
qwace ta daga gareta annurin da ya yi saura akan
fuskarta ya soma narkewa daga kan fuskarta. Tana
gama kallon sarqa da Bawa Farsu ya xaga mata
akan fuskarta sai ta juya ta dubi hanya sosai
sannan tace masa “Wannan sarqa da ka xagata
akan idanuna dole na gudu tunda ka xagata na
ganta da idanuna, domin sirrin tsafin dake jikinta,
amman ba don haka ba da yau sai na halakar da
ruhinka, don haka ka jirani a haxuwa ta gaba da za
mu yi”. Tana qarasa faxar haka ta dubi hanya ya
falfala da wani azababben gudu kafin su farga har
ta vace musu daga gani.
Bawa Farsu ya bi sarqa da kallo cike da
mamaki ya juya ta zuwa ga su Gimbiya Lusa da
sadauki Ansar ya fuskance su sosai yana kallonsu
cike da mamaki ita kuma sarqa sai qyalqyali take
tana xaukar idanu Gimbiya Lusa ta miqa hannu
zata amsa Bawa Farsu yace mata.
“Dakata” Ga matuqar mamakinsa sai
yaga ta qame tamkar gunki ya dubeta sosai ya yi
murmushi ya nuna sadauki Ansar da ita shima
yace masa “Qame!” Take Ansar ya maqale shi ma
tamkar busashen itace. Bawa Farsu ya dube shi a
qame kamar busasun itatuwa ya qyalqyale da
dariya cike da gamsuwa ya matsa gaban Gimbiya
Lusa ya shafi fuskarta a hankali yace mata.
“Qaramar mara kunya”.
**
Bokanya Namsu ta dubu xayar da take
tsaye a kusa da ita da duban matuqar mamaki mai
matuqar yawa domin ganin matuqar kama da su
ka yi da junansu. Ta yi murmushi akan faffaxar
fuskarta sannan cikin murya fushi tace.
“Ka yi mana asara biyu, dukkanmu mun
rasa abin don haka kakan iya dawowa sufaffarka ta
ainahi kafin na halakaka bisa wannan zunibin da
ka aikata mun” tana gama maganar tana duban
xayar da ke tsaye a gabanta, aka yi wata dariya
mai xauke da isgilanci sannan cikin taqama aka ce
mata “BOKA SHARBANGA shi kaxai ne wanda
ya kamata ya mallaki ruhin sarkin Aljanu Gamsu
domin na fi kowa sanin muhimmancinsa a duniyar
mutane, domin haka kafin ki halakani ni yanzu zan
salwantar da ruhinki domin ke kaxaice bokanya da
za ki iya bani matsala a cikin lamarina’.
Ya gama maganar yana mai yin wata
girgiza tamkar tsuntswa nan take duk kayan da
suke sanye a jikinsa suka zube a qasa, ya komo
ainahin surarshi ta ainahi, wato namiji basamuden
qato mai mummunan kama ya dubi Bokaya
Namsu ya yi murmushi.
Ta dubeshi itama cikin tsananin fushi mai
tarin yawa tace masa.
“A yau bokanya xaya a tsakiyar mazaje
zata daka maka gumba a hannunka, ta nuna maka
cewar akwai bambanci tsakanin aya da tsakuwa”
Ta gama maganar tata tana mai miqa
hannunta cikin gashin kanta ta zaro wani xan
guntun itace ta cilla masa shi, take wuta ta kama
itacen ta soma ci ganga-ganga lokaci xaya aljanin
da suke kai ya kurma wani ihu mai tunzura zuciya
sannan lokaci xaya wutar ya narkashi ya narke
tamkar ruwa, ya riqa xiga yana zagwanyewa
lokaci guda wutar ta doshi Boka sharbanga.
Bokanya Namsu ta miqe ta yi sama tamkar
wata tsuntsuwa ta tsaya akan iska ta bi wutar da
kallo tana da tabbacin ta gama halaka boka
sharbanga.
Wutar tana zuwa wurin da boka sharbanga
yake tsaye ya narke ya zama ruwa wutar ta ratsa ta
cikinsa, wuta da ruwa suka bada wata qara sannan
lokaci xaya wutar ta mutu boka sharbanga ya yi
dariya yana kallonta yace mata.
“Ke qaramar mara kunya maza bisa kanki”
Yana rufe bakinsa ya yi wata fitar burtu ya tasar
mata yana zuwa kusa da ita suka sake tashi a sama
kamar tsuntsaye, nan take ya buxe qirjinsa suka
taso suka qaxa qirji da qirji nan take suka yi baya
kamar an watsa yakuwa a cikin teku, suka sake
tasowa juna a guje suka yi suka yiwa juna karo
kamar raguna suka yi baya taga-taga.
Wajen da suka yi gware take ya fashe jini
ya soma zuba boka sharbanga ya miqa hannunsa
sama take wata takobi ta bayyana ya yi xauki akan
bokanya Namsu kafin ya qarasa gareta itama ta
miqa hannu cikin iska, lokaci guda wata takobi ta
bayyana a hannunta itama tayi xauki kansa suka yi
wata gamuwa mai muni suka soma kaiwa junansu
sara da suka ko wanne yana qoqarin farauce
rayuwar xan uwansa duk wanda ya sari wani a
cikinsu sai dai kaji kamar wani qarfe da qarfe ne
suka gamu a waje guda.
Haka suka tafiyar da tsawon lokaci suna
faman fafatawa a tsakaninsu ba tare da wani a
cikinsu ya sami nasara akan xan uwansa ba, can
suna cikin wannan gumurzun sai Boka sharbanga
ya faki numfashin bokanya Namsu ya zaro wata
farar hoda daga cikin jakarsa ta bokanci ya watsa
mata.
Hodar tana sauka a jikinta nan take ta soma
jin jikinta duk ya saki, ta saki makamin da yake
hannunta sannan lokaci guda ta zube a qasa, ya
dubeta a wulaqance sannan ya qyalqyale da
dariya.
“Wanda ya fiki himma ya riga ya sha kanki,
don haka yanzunnan zan halaka ki”. Yana gama
maganar shi ya buxe jakar bokancinsa ya xauko
wata wuqa da aka yi da qashin haqarqarin mutum
ua xago da idanunshi ya kalleta gami da
qyaqyacewa da dariya kafin ya sake cewa da ita.
“Duk duniya babu wani mai sihiri da
wannan wuqar ba zata huda shi ba, don haka
yanzunnan zan halakar da ruhinki, ki zamto
tamkar ba a tava yinki na doron qasa ba” Yana
gama maganar tashi lokaci xaya ya xaga wuqar a
sama ya dubi qirjinta daidai inda zai luma wuqar
sannan yace mata.
“Sai wata rana ABOKIYAR GABATA,
Bokanya Namsu” Yana gama maganar ya nufi
qirjinta cikin sauri da zumar soka wuqar a gaban
qirjinta.
**
Sarauniyar aljanun cikin ruwa ta wanzu
tsawon lokaci tana tafiya babu qaqautawa ita da
kanta tana da masaniyar duk duniya babu wani
mahaluki da yake da gaggawar da zai iya biyo
bayanta har ya cimmata don haka ganin ta yi nisa
da wurin su bawa Farsu sai ta rage gaggawar da
take yi ta samu wuri ta tsaya.
A hankali ta miqa hannunta ta shafi
wuyanta cike da takaici da baqin ciki domin rasa
sarqarta da ta yi. Duk duniya babu abinda tafi
qauna a rayuwarta kamar sarqa domin duk wani
sirri nata ya ta’allaqa a jikinta. Duk abubuwan duk
abubuwan ba su ne vacin ranta ba, babban vacin
ranta na rashin samun damar buxe jakar da ta saka
ruhin sarkin aljanu Gamsu wanda dole sai ta yi
amfani da sarqa ta zata buxe jakar. Wannan abun
shi ne abu mai muni da sarauniyar aljanun cikin
ruwa ta tava cin karo da shi a tsawon shekarunta
da ta yi a duniya.
Ta xaga kanta sama ta soma qoqarin tunani
da zumar ta tunano hanyar da zata bi domin ganin
ta samo mafita akan abinda ya dameta.
Abubuwa da yawa suka yi ta zuwar mata
cikin ranta, amma duk ba su haska mata tunanin
yadda zata dawo da sarqarta ba. Haka sa’o’i masu
dama suka wuce tana faman tunane-tunane bayan
tsawon lokaci wata dabara ta faxo mata, wannan
dabarar ba qaramun faranta mata rai tayi ba,
domin ta yi imani itace hanya guda da zata dawo
da sarqarta gareta cikin ruwan sanyi.
Don haka cikin gaggawa ta miqe tsaye ta
lalubi gefen qungunta ta xauko wani madubin tsafi
ta dubi kanta a ciki ta yi murmushi sannu a hankali
ta soma karanto wasu xalasimai na tsafi tana
duban kanta a jikin madubin, bata xauki wani
lokaci a haka ba take kamaninta suka soma juyewa
zuwa na bil’adama.
A hankali ta juya kama zuwa ga surar mace
baqar fata mai kyawun gaske, yadda duk wani
namiji idan ya kalleta sai ya yi mafarkin kyawunta,
ta dubi kanta a jikin madubin har sheqi take yi
tamkar ta shafa shuni a jikin fatarta, ga manyan
fararen idanu da jan shacin bakinta tayi wa kanta
tattausan murmushi a hankali tace.
“Wannan surar Gimbiya Zailu na aro, duk
duniyar baqaqe babu mai kyawunta zan yaudari
baqar fatar nan na amshi sarqata daga hannunsa
kafin na halakar da ruhinsa ya zamto na shafe shi
daga doron qasa” Ta qarasa magana tana
qyaqyacewa da dariya kafin lokaci guda ta nufi
wajen teku ta wajen da tana da tabbacin tanan su
Bawa Farsu za su fito.
Iska teku ta ci gaba da kaxawa a hankali.
**
Tsawon lokaci suka xauka a tsaye a wurin
bawa farsu yana kallonsu yana yi musu dariya.
Kafin ya miqa hannu ya xauki sadauki Ansar ya
mayar da shi can wani wuri yua ajiye shi, ya
xauko wasu sassa na gawarwaki halittun da suka
yi yaqi da su ya xoxxora masa a jikinsa. Ya dawo
itama Gimbiya Lusa ya zuba mata idanu yana
kallonta ya qare mata kallo a hankali.
Ban tava tsayawa na qare miki kallo ba sai
yau, ashe daman haka kike da tsantsar kyau, ya
saurara yana dubanta ya dubi idanunta da suke a
buxe manya da su, farare qal. “Tunda nake a
rayuwata ban tava ganin kyawawan qwayar
idanuwa kamar naki ba, surarki zata xauki
hankalin sarakuna da attajirai ma su ji da kansu”
Ya kammala maganar yana dubanta. Ya juya ga
sadauki Ansar yace masa “Ka koma yadda kake”
Yana faxar haka sai sadauki Ansar ya ci
gaba da motsi kamar yadda ya ke a baya, ya tsaya
yana duban kansa cike da mamaki ya mayar da
kallonsa ga Bawa Farsu yaga yadda ya tsaya a
gaban Gimbiya Lusa cikin tsawa yace masa.
“Meye haka? Maza ka matsa daga wajenta”
Ya juyo yana dubansa fuskarsa xauke da
murmushi.
“Kana da alaqa da ita ne?” Ya jefa masa
tambayar sadauki Ansar shima ya tsare sa da ido.
“Wanne sihiri ka samo kake aikatawa a
gare mu, don haka ina mai sanar maka lallai kayi
gaggawar rabuwa da shi, idan kuma ba haka