Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ABOKAN GABA MUKHTAR I. KWALISA 08069524699 G imbiya Lusa tana gaba akan ingaraman dokinta ta yi shiga ta bajinta cikin sulke da aka yi masa ado da koren qyalqyali. Daga nesa idan ka kalleta sai ka xauka wani barde ne mai qarfin dantse amma idan ta matso kusa sai kaga ashe mace ce. Sai tauri a duniyar sadaukai idan suka ganta suna saurin rainata, amma abinda ba su sani ba shi ne da mutum ya raina Gimbiya Lusa ya xauketa ba wani abu ba gwara ya sha guba da za ta hallakar da shi a sa’o’I uku domin Gimbiya lusa ta fi guba saurin kisa. Ita xaya take faman kaiwa da komowa a cikin duniya tana ta faman farauce rayukan sadaukai da jarumai tun daga lokacin da aka bata labarin cewar wani sadauki zai bayyana ya sace ruhin mahaifinta wato sarkin aljanu mai girman daraja sarki Gamsu. A duk duniya babu wanda gimbiya lusa take matuqar qauna kamar mahaifinta sarkin aljanu gamsu duk da zamtowar ita ba aljana bace ta kasance mutum bil’adama amma mahaifinta aljani ne. Gimbiya lusa ta kasace mace ma’abociyar kyau da a faxin duniya babu tamkarta a zamanin. Ta kasance doguwar mace mai yalwar jiki ba wai sosai ba tana da faffaxaar fuska mai xauke da fararen idanuwa. Tafi iya murmushi fiye da komai. A duk lokacin daka ganota daga nesa gani za ka yi har wani xaukar idanu take yi, tana da qirar jarumta tana da ruwan tausayi, kyawunta yafi jarumtakarta. A yanzu Gimbiya lusa tana tsaye a gaban wani saurayin namiji mai cike da yalwar kyawu da cikar zati, mai kwarjinin fuska da jarumta. Wannan saurayin da yake tsaye a gabanta shi kaxai ne jarumin da ya yi saura wanda bata farauce ransa ba, a cikin mutanen da take tsammanin za su iya zuwa har fadar sarkin aljanu domin sato ruhinsa. A duk jaruman da su ka yi gwagwaarmaya da ita wannan shi ne kaxai jarumin da kwarjinsa ya cika mata fuska. Suka jima a tsaye suna kallon junansu, a hankali ya dubeta yace mata. “Tun da nake a rayuwata ban tava ganin mace da kyawunta ya girgiza mun ruhi ba sai ke… na yi matuqar baqin ciki da kika zamo mace mai yin hidima ga aljanu, kike farauce rayukan ‘yan uwanki mutane akan kare ruhin wani tsohon aljani don gudun sace shi”.Ya yi maganar yana mai dubanta kafin ya ci gaba da magana cikin isa da izza. “Kar ki mance duniya tana da yawa kuma qaddara ta riga fata” Gimbiya lusa ta yi murmushi kafin ta mayar masa da martani cikin wani irin sautin murya. “Ina da tabbacin idan na farauce rayuwarka zan kawo qarshen matsalar dake shirin faruwa ga mahaifina zai zamo cikin walwala da nishaxi, don haka yanzu zan kawo qarshen numfashinka kamar yadda na aikata ga sauran jarumai ‘yan uwanka” Da muryar jarumta tace masa. Cike da jimami yace mata “Duniya ta zamo mafaka ta mutane daban-daban ina fatan baki mance da yanki baqar fata ba?” Yana mai tsareta da idanu. Ta yi murmushi. “Baqar fata ba su da wayewar da har za su san amfanin ruhin mahaifina a garesu, mutanen da ba su fahimci kansu ba, taya za su fahimci amfanin wani abu” Ya girgiza kai. “Xan hakin daka raina shi ke tsone maka ido”. suka yi shiru su duka suna kallon juna na tsawon lokaci daga bisani ya qara dubanta sannan cikin isa da taqama yace mata. “Lallai ina mai tabbatar miki ruhina yafi qarfin ki farauce shi don ba za ki tava samun nasara akai na ba”. Maganarshi ta zamto tamkar wuta ya watsa mata, ta dube shi da qunar rai da tafarshashiyar zuciya tace masa. “Babu wani jarumi a duniya da ba zan sami nasara akan shi ba, domin na farauce rayukan sadaukai irinka waxanda suka fika jarumta da nuna bajinta a duniya, don haka kaima lallai ina baka tabbacin zan kawo qarshen numfashinka ka zamto kamar ba a yi ka ba”.Gimbiya Lusa ta tabbatar masa. Ya girgiza kanshi sannan lokaci xaya ya gyara ruqon da ya yiwa takobinshi ya kalleta sosai a hankali yace mata. “Bana buqatar ki zamto abokiyar gabata” Ya yi shiru yana kallonta a hankali ya kuma ce mata. “Kinyi gaggawa wurin yarda da cewar wani aljani ne mahaifinki,bayan aljani bai isa ya haifi halitta kamar ki kyakkyawa mai kyawun fuska da kyawun idanu da kyawun shataccen baki ja”. “Bana buqatar yawan surutu don haka ka shirya tarata gani nan tafe zuwa gareka” ta ce masa cikin tsawar murya, sannan lokaci xaya tayi xauki zuwa gareshi shima ya taso ma ta lokci xaya suka gamu da juna a tsakiyar fili, su ka kaiwa junansu sara da takubbansu, makamansu suka gamu wuri xaya, qarar haxuwar makaman ta cika wurin suka gauraye wuri xaya suka soma qoqarin farautar rayuwar juna, suka dinga kai sara ga junansu. Gimbiya Lusa t sami sadaukin ba yadda ta tsammace shi ba. Lokaci xaya suka yi jina-jina duk jikinsu idan ka duba jikinsu ya yi kaca-kaca da ciwuka. Haa suka ci gaba da saran juna kafin daga bisani suka yanke jiki suka faxi suka yi kare-jini-biri-jini. “Ba za ki tava samun nasara a kaina ba, domin ina son ki sani Ubangiji da nake bautawa, wato Ubangijin da ya yi horo da bin addinin musulunci wanda shi ne ya hanaki samun nasara a kaina” Ya tabbatar mata. Gimbiya Lusa ta girgiza kanta cike da gamsuwa domin ta tabbata bata samu nasara ba ga wannan jarumin. Ta xago kanta a hankali ta dube shi taga yadda jini yake malalowa daga jikin raunukan da tayi msa. A hankali itama ta dubi jikinta taga yadda itama jini yake ta faman xuba daga jikinta ta girgiza kanta. ‘Babu makawa ba za ta iya samun nasara ba akan wannan jarumin sai dai su yi Mutuwar kasko, tun da suka yi kare-jini-biri-jini” Gimbiya Lusa ta zuba masa idanuwa tana kallonsa shima ya zuba mata idanuwa yana kallonta. Kowa ya ajiye makamin shi a gefe xaya. Wannan ita ce rana ta farko da Gimbiya Lusa ta tava ganin jarumin da jarumtarsa ta birgeta, wannan rana ita ce rana ta farko da Gimbiya Lusa ta ji tana son wani sadauki mutum kamarta a cikin ranta. Amma ta fidda rai, raunukan da yake a jikinta da jikinshi ba za su barsu su ci gaba da rayuwa ba. Ta lumshe idanuwanta sunan shi ya dawo mata a cikin zuciyarta. “Ansar”. A dai-dai lokacin da ta furta hakan a cikin ranta, a dai-dai lokacin wani mummmunan aljani mafi girma ya sauka a gabanta, yana sauka ya suretaa da hannunsa ya juya ya yi sama da ita a guje, tamkar an harba kibiya. Gimbiya Lusa ta buxe idanuwanta a hankali ta kuma kallon Ansar da yake kwance a wurin. Ta mayar da idanuwanta ta lumshe su. Ungulaye suka ci gba da yin shawagi, suna jiran Ansar ya qarasa mutuwa su sami damar yin kalaci da namanshi. NAHIYAR BAQAR FATA Nahiya ce data yi fice ta kuma shahara wajen siye da siyarwa ta bayi. Don haka baqar fata ba shi da wata daraja a wajen larabawa da nasarawa, domin suna masa kallon ba shi da wani amfani idan ba bautarwa ba. Farsu ya kasance baqar fata mai kaifin basira da dabara. Ya zamto jarumi mai yawan bajinta, farsu ya kasance bawa ne ga bokanya Namsu wacce ta kasance baqar fatar bokanya data shahara a fagen sihiri, don haka a cikin tsafinta ta gano amfanin ruhin sarkin aljanu Gamsu a gareta. Domin ya bayyanar mata matuqar tana son ta mulki duniyar bokanci ya zamo duk duniya babu kamarta to sai ta mallaki ruhin sarkin aljanu hakan yasa ta bazama duniyar tsafi da bincike akan yadda zata mallaki ruhin, amma sai ta gano qarfi sihirin tsafi ba zai tava sakawa ta mallake shi ba. Haka ma tsananin jarumta. Wanan lamarin ya matuqar tayarwa da bokanya Namsu hankali ta rasa meye yake mata daxi, tayi ta nazari ta rasa samun mafita. Sai daga baya tayi tunanin tura bawanta Farsu yaje ya gwada sato mata shi. Tunda shi Farsu gwani ne wajen iya sata kamar sidabaru haka yake iya sace abu. Tana gama tunanin ta nufi inda yake ta same shi a zaune yana gyara makaminsa. Ta dube shi ido cikin ido. Farsu ya yi gaggawar zubewa a gabanta domin girmamawa Bokanya Namsu a hankali ta soma yi masa magana. “Lokaci ya yi daya kamaya ka yi mun bauta ta qarshe daya kamata na ‘yanta ka” Ta saurara tana kallonsa sannan ta ci gaba da magana. “Samun nasaraka a wannan karon tamkar ka sami ‘yanci ne, don haka wannan damace gareka ta barin qangi na bauta” Ta basa tabbaci. Farsu ya xago idanu yana duban bokanya Namsu, wannan shi ne zance mafi daxin ji daya tava ji daga bakinta a iya zamanshi a qarqashinta. Don haka cike da qwarin gwiwa yace mata. “Wannan wane irin aikine haka?” Bokanya Namsu tayi murmushi domin ganin tarkonta ya kamar kurciya, a hankali tace masa “Ruhin sarkin aljanu Gamsu nake son ka sato mun”. Maganar ta zo masa a bazata ya sauke wani gwauron numfashi kafin yace mata. “Zan sato miki shi matuqar zan samu ‘yanci na kuvuta daga qangin bauta” Ya tabbatar mata. Ta dube shi cike da jin daxi tace masa. “Wannan itace bauta ta qarshe da za ka yi mun a rayuwarka, don haka idan ka sami nasara ka zamto kuvutacce, ‘yantace. Yanzu zan haxaka da aljanin da zai xaukeka ya kaika har cikin fadar sarkin aljanu Gamsu” Ta kammala maganar tana dubanshi kafin ta qara cewa da shi. “Ko kan da wata buqatar ta yin shiri?” Ya girgiza kai gami da faxin. “Bana buqatar yin ko wanne shiri ya shugabar bokaye”. Bokanya Namsu ta yi dariya jin sunan daya kirata, take ta shafi xamararta kamar qiftawar ido wata jibgegeyar halitta ta bayyana mai tsananin girma da tsananin muni. Tana da dogon wuya kamar raqumin dawa da manya-manya kunuwa farakam-farakam sun lanqwasa kamar alamar tambaya(?) yana da fuka-fukai kimanin guda ashirin da bakwi. Bokanya Namsu ta dube shi tace masa. “Maza ka xauki bawana Farsu ka kai shi fadar sarkin aljanu Gamsu” Take aljanin ya girgiza kai cike da girmamawa, Bokanya Namsu ta dubi Farsu tace masa “Idan ka shirya kuna iya tafiya”. Farsu ya dubi bayan aljanin ya dubi kayan makamansa ya sunkuya ya xebesu ya naxesu a cikin wata rigar fatarsa da yake amfani da ita a lokacin tsananin sanyi, ya daka tsalle ya haye bayan aljanin kafin yace masa. “Muna iya tafiya”. Bokanya Namsu ta dube shi gami da xauko wani makami ta cilla mishi kafin tace masa. “Ga wannan zai taimake ka” Farsu ya zuba mata ido yana dubanta, a daidai lokacin aljanin ya buxe fuka-fukanshi ya soma tashi cikin sararin samaniya suka luluqa suka nutse a cikin gajimare. Haka suka xaui tsawon wata xaya da sati xaya suna tafiya sannan suka qaraso fadar sarkin aljanu Gamsu, wanda tun daga nesa farsu ya ga rundunar aljanu tsaitsaye cikin shirin yaqi ko ina ka duba sune. An qawata fadar da ado mai jan hankali da zane-zane abubuwa masu matuqar kyau da ban sha’awa. A hankali aljanin ya yo qasa-qasa ya shiga ciki fadar, ga matuqar mamakin farsu sai yaga babu wani aljani daya damu da shi, ko wanne sabgogin gabanshi yake yi a haka suka dangana har cikin fadar, wanda a can ciki ne suka samu wasu zaratan aljanu tsaitsaye suna ta faman muzurai ko wanne aljani yana cikin shiga irin ta yaqi irin wacce farsu bai tava ganin irinta ba. A zaue akan wata kujera ta farin qarfe wani dattijon aljani ne xan kimanin shekara dubu takwas yana zaune cikin isa da taqama. Aljanin daya xauko shi ya sauke shi, kafin ya matsa zuwa ga sarkin aljanu ya faxi ya yi gaisuwa, sarkin aljanu ya dubi Farsu dake zaune a bayan aljanin xan tsurut! Da shi kamar ruwan aski yace masa. “Kai bil’adama mai ya kawo ka cikin babbar fadar duniya ta sarkin aljanu Gamsu?” Farsu ya sauko daga bayan aljanin ya dubi sarkin aljanu Gamsu cike da girmamawa sannan ya zube a gabanshi ya yi gaisuwa a hankali yace masa. “Ya mai darja mai girman daraja wanda sarakunan mutane suke shayi, kayi sani cewar na zo ne gareka domin ganewa idanuna wani abu da ake gayaa mani ban aminta ba wanda aka ce duk duniya kai kaxai ne a duniyar mutum da aljan kake da ikon haka” sarkin aljanu gamsu ya dubi Farsu da duban nutsuwa sannan yace masa. ‘Wannan wane abune haka da har duniyar mutane suke girmamani dominsa? Na kuma zamto ni kaxai ne mai iko da shi?” Ya tambayi farsu yana duban shi da idanunsa farsu ya sunkuyar da kansa qasa domin gudun kar sarkin aljanu ya gano qaryar da yake shirin yi masa sannan yace masa. “An ce a duk duniya mutum da aljan kai xaya ne ruhinka yake a cikin kwlba, ma’ana kana iya cireshi daga jikinka idan ka so ka kan ajiye shi a gefe xaya gangar jikinka ta zamo babu ruhi ka zamto tamkar matacce har sai an mayar da ruhin. Don haka na zo domin ganewa idanuwana wannan abin mamakin, wanda ya gagari duniyar sarakunan mutane” Sarki aljanu Gamsu ya dubi farsu da idanunshi da duban nutsuwa ya xauki tsawon lokaci yana dubanshi daga bisani ya nisa a hankali yace masa. “Ina fatan kana da masaniyar domin ‘yarta Gimbiya Lusa ta samu labarin cewar wani jarumi zai zo domin sace ruhina shi yasa ta sauka duniyar mutane domin halaka duk wani jarumi?’ Ya tambaye shi yana tsare shi da idanuwanshi, farsu ya kuma sunkuayar da kansa cikin ladabi sannan yace masa. “Ni ban zamto jarumi ba, face na shahara a wajen zuwa ganin duk wani abun mamaki da bajinta wanda hakan shi yasa da na samu labarin irin wannan bajinta taka ta cire ruhina daga jikinka ya sani na taho domin na ganewa idanuwana. In fatan zan sami biyan buqatar ta a nuna mun wannan abin mamakin” Farsu yace masa. Sarin aljanu Gamsu ya dube shi ya yi murmushi wani turiri ya fita ta cikin qofofin kunuwanshi, sannan a hankali ya cewa farsu. “Tun kafin sarakunan mutane su farka daga bacci mu muka rigaya muka je inda zamu. Don haka bajintata ta yi nisa a duniya ta kuma gagari duk wani bil’adama sai mu gagararun aljanu.don haka zan nuna maka ruhina domin na san ko kayi yunqurin guduwa ba za ka iya kai labari ba, domin rundunar aljanu tafi qarfin duk wani bil’adama” Sarki aljanu Gamsu ya tabbatar masa sannan ya ci gaba da ce masa. “Kayi sani cewar ruhina ya zamto a cikin kwalbar tsafi wanda idan babu shi a jikina zan zamto tamkar matacce har sai an dawo mun da shi jikina an saka mun shi a qirjina yadda yake, don haka ka yi sani cewar za ka zamto xan Adam na farko daya soma ganinsa wanda a duk faxin duniya babu wani mutum ko aljani daya tava ganinsa sai kai, amma idan ka gansa hukunci na gareka shi ne zan halakaka” Da murmushin mugunta ya faxa. Farsu ya yi shiru yana kallon tsohon aljanin da yake gabanshi mai kama da siffar bididigin kwaxo sannan da murya jarumtaka yace masa. “Na amince matuqar burina zai cika na ganin wannan babbar bajinta da wani mahaluki bai tava yinta ba. Kuma na tabbatar zan zama mutum na farko da duniya zata riqa tunawa da shi a matsayin wanda ya tava ganin wannan ruhin naka” Ya kammala maganar yana mai duban fuskar sarkin Aljanu wanda yake dubanshi da haxaxxiyar fuskar data tattare kamar busashiyar fata sannan ya yi dariya yace. “Haka nake son naga mutum ya zamto mai zuciyar jarumta da rashin tsoro, don haka maza ka shirya ganin ruhina yanzu nan” Yace masa yana dubanshi sannan a hankali ya miqe tsaye ya yi wata irin girgiza da ta haddasa tashin wata maxaukakiyar guguwa. A sannu a hankali guguwar ta soma yayewa sannan wasu fuka-fukai suka fito a jikin shi daga bisani suka soma bubuxewa a tsakiyar qirjinshi wata kwalba ta bayyana. Ya dubi Farsu sannan yace “Matso ka ga ruhina”. Cikin jarumta ya tunkareshi ya qarasa gabanshi ya tsaya yana zubawa ruhin na shi da yake cikin kwalba idanu yana kallonshi cike da mamaki. A hankali ruhin yake motsi a cikin kwalba. Cikin tsananin zafin nama na bazata Farsu ya miqa hannu ya cafi ruhin sannan ya fisgoshi daga cikin inda yake. Sarkin aljanu Gamsu ya qwarara wata qara a razane, sannan lokaci xaya ya soma bushewa yana komawa kamar busashen karmami, a haka ya gama bushewa ya zama kamar gunki. Farsu ya dubi ruhin dake hannunsa ya dubi busashiyar gangar jikin sarkin aljanu Gamsu yace masa “Baka san hikimar mutane bane shi yasa ka yi gaggawar amincewa da ni”. Yana gama maganar ya buxe jakarsa da ya yi xamara da ita ya cilla ruhin a ciki sannan ya juya. A lokacin rundunar aljanun da suke a fadar suka zaburo masa domin amsar ruhin sarki aljanu Gamsu. Farsu ya zare takobinsa ya jinjina ta a hannunsa ya dubi yawan rundunar aljannun ya lumshe idanunshi ya buxe ya kuma gyara riqon da ya yi wa takobinsa. Adadin rundunar suka matso ganin sun kusa zuwa gareshi ya sa shima ya nufe su a guje suka gamu a wuri xaya, kasuwar yaqi ta soma ci rayuka suka soma salwanta, mutuwa ta soma shawagi tana farauce rayuka, jini ya soma fantsama kawuna suka dinga yawo a sama kamar tsintsaye makamai suka riqa zubewa qasa daga hannun mariqansu. Yawan adadin rundunar aljanun ya dinga raguwa domin irin yadda Farsu yake farauce ruhinsu yaqi ya ci gaba da tsawaita a garesu mutuwa ta ci gaba da shawagi a tsakaninsu duk wurin daya saka gaba sai dai kaga matattu suna zubowa qasa a haka ya ci gaba da yaqarsu suma suna qara danno shi. Haka suka xauki tsawon kwanaki biyu suna wannan gwagwarmaya shi bai saduda ya gaji ba suma ba su qare ba, yaqi ya ci gaba da gudana mutuwa ta ci gaba da shawagi tana xauke rayukansu. Can bayan tsawon lokaci a lokacin gajiya ta soma kama Farsu ya soma sauya salon yaqin a zuciyarshi yana mai tunanin abinda ya kamata ya yi a lokacin ne bai yi aune ba wata qara gami da walqiya ta cika cikin fadar, sannan lokaci xaya wani baqin aljani mai girman gami da mummunar siffa ya bayyana da ganinsa sai duk rundunar aljanun suka tunzura suka razana suka zubar da makamansu suka ruga a guje. Ya juya ya dubi Farsu ba tare daya ce masa komai ba ya miqa hannu xaya ya damqoshi ya buxe fuka-fukanshi ya tashi sama da shi suka fice daga cikin fadar sarkin aljanu Gamsu. Farsu ya leqo qasa da idanunshi ya dubi gawarwakin aljanun da suke kwance fululu. ** A hankali Gimbiya Lusa ta saka hannu ta xauko jakarta ta buxeta ta xauko wani garin magani ta buxe bakinta ta zazzagashi tana gama haxiye maganin take taji qarfi a jikinta, lokaci guda ta yi murmushi ta yunqura ta tashi ta dubi aljanin daya xaukota cikin murya qasa-qasa tace masa. “Waye ya aiko ka ka tafi da ni?” aljanin ya ci gaba da karkaxa fuka-fukanshi sannan ya bata amsa da cewar “Ni bawan mahaifinki ne sarkin aljanu Gamsu, a yanzu na baro wani bil’adama yana yaqar jama’armu bayan ya sace ruhin mahaifinki” Wannan maganar ta zo wa Gimbiya Luna a bazata, tun data samu wannan labarin ta fita take yaqar duk wani sadauki da take tsammanin zai iya zuwa ya sace ruhin mahaifinta amman ashe qaddara ta riga fata, bata san lokacin data kwarara wani irin ihu ba, take idanunta suka kaxa suka yi ja, saboda tsananin fusata cikin damuwa tace wa aljanin. ‘Qara gaggawa domin mu samu mu qarasa gareshi domin na yi gagawar sadashi da ajalinsa” Aljanin ya qara qarfin karkaxa fuka-fukansa suka tunkari fadar sarkin aljanu Gamsu. A lokacin da rana ta kusa faxuwa Suka qaraso fadar tun daga nesa Gimbiya Lusa ta riqa hango gawarwakin aljanu a kwankwance bila adadi, suka qaraso cikin fadar Gimbiya Lusa ta dubi gawarwakin aljanun dake kwance a cikin jini wani baqin ciki ya lulluve mata rai. Wannan shi ne karon farko da wani ya tava shigowa cikin fadar sarkin aljanu Gamsu ya yi nasara ga rundunarshi. Ta mayar da dubanta ga karagar sarkin aljanu Gamsu, ta gano gangar jikinshi a zaune a kan karagar babu ruhi a jikinsa, da gudu ta nufi wajen da yake taje gabansa ta tsaya tana kallonshi hawaye yana kwaranya daga cikin idanunta. Takaici da baqin ciki ya cika mata cikin zuciyarta, hawayen ta ya ci gaba da kwaranya daga cikin idanunta, ta ci gaba da kallon gangar jikin sarkin aljanu Gamsu. A rayuwarta ta duniya babu wani mahaluki da taji tana matuqar qaunarsa kamar mahaifinta sarkin aljanu Gamsu ta yi matuqar mamaki yadda ta shaqu da shi kamar yadda mafiya yawan lokuta take matuqar mamakin yadda kamanin halitarsu suka bambanta, sau tari tana iya lokutan da take kallon surata a jikin madubi, sannan ta dubi ta kuyanginta ‘yan matan aljanu sai taga akwai matuqar bambanci sosai da su, domin ita tsarin jikinta jiki ne mai santsi babu gashi sai farar fatarta da take faman sheqi da xaukar idanuwa. Qafafunta suna tattare da ‘yan yatsu su kuma dukansu suna da kofato tamkar na dawakai, tsarin surasu bai yi kama ba sam. Sau tari idan sun so sukan sauya kamanin halittarsu daga kyawawa zuwa munana, amma ita bata iya sauya kamani kamar yadda suke sauyawa. A lokacin tana da quruciya ta sha tambayar mahaifinta sarki aljanu Gamsu ko mai yasa kamaninta suka bambanta da na su kamanin? Mafi yawan lokuta yakan dubeta sannan yace mata. “Akwai lokacin da za ki gamu da wasu halita waxanda zubin halitarku iri xaya ne” Wannan maganar ya tabbatarwa Gimbiya Lusa bambanci da take gani a bayyane yake. Lokacin farko data soma shigowa cikin bil’adama data ga jinsi mai irin nata sai mamaki ya cikata, ta kuma haqiqance a cikin ranta wannan zubin halitar sune jinsinta sune ‘yan uwanta amma da yake ba buqatar sanin asalinta da halittarta ne ya fito da ita ba don haka bata mayar da hankali kan haka ba. A lokacin ta fito ne domin nemo sadaukin da aka bata labarin zai zo ya sace ruhin mahaifinta. Duk data samu nasara kashe sadaukai, amman nasara bata yi mata amfani ba, ta gama farauce rayukan jaruman wanda suka yi suna suka sami xaukaka a duniya amma wani baqar fata wanda ba a saka shi a cikin lisaffin jaruman duniya ya zo ya sace ruhin. Wannan shi ne anyi ba a yi ba! Ta rufe qofa da varawo. Duk abubuwan da suke ta faman zuwar wa Gimbiya Lusa a rai, suka gama zuwar mata, ta dubi makamanta da kayan yaqinta bata buqatar sauya wasu ta mayar da dubanta ga sarkin aljanu Gamsu da yake zaune babu ruhi a jikinsa taji damuwarta ta qaru da fusatar zuciya tace “Halaka ta tabbata a gareka maqasqancin bawa, tabbas gani nan zuwa gareka domin farauce ranka” Da xaga murya tace, a lokaci xaya ta dubi aljanin daya xakota tace masa/ “Ka xaukeni bisa gaggawa ka kani domin riskar ABOKIN GABA domin mu yi GABA DA GABA da shi” Tana gama maganarta tayi tsalle ta haye bayansa shi kuma aljanin ya buxe fuka-fukansa ya tashi da ita sararin samaniya. Gimbiya Lusa ta jiyo ta dubi gangar jikin sarki Gamsu lokaci xaya tana jin hawaye suna kwaranyo mata, a hankali ta kai hannunta ta shafi takobinta. ‘Zan ladaftar da kai BAQAR FATA’ tace a ranta. SADAUKI ANSAR Yana kwance cikin tagaiyara da fidda rai daga tsammanin ci gaba da rayuwa, domin irin raunikan da suke jikinsa. Lokaci zuwa lokaci ya kan xan tuna cewar wannan shi ne yaqi xaya a duniya da suka tava kare jini-biri-biri-jini da abokin gabarshi. A irin jarumtar da yake da ita babu wani sadauki da ya tava xaukar sa’a xaya a gabanshi ba tare da ya farauce ranshi ba. Amman sai gashi mace ta wanzu tsawon wasu lokuta a gabanshi suna xauki ba daxi. Wannan abun mamaki ne ga sadauki mai sadaukantaka kamar Ansar wannan baqon abu ne a gareshi da bai tava tsammanin faruwarshi ba. A hankali ya xaga idanunshi ya dubi ungulayen da suke ta faman shawagi a sararin samaniya suna jiran ya hallaka domin su samu suyi kalaci da namanshi. A hankali ya buxe bakinshi ya soma faxin “Allah kai ne ubangiji xaya wanda ya halicci komai, kai muke bautawa, Allah kar ka wulaqanta gangar jikina na zamto na hallaka na zamto abincin ungulaye, Allah ka suturta gangar jikina”. Ya gama addu’ar tashi yana mai lumshe idanunshi a lokacin ya ji saukar wani

Chapter 1 of 3