Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 3
da kuma umarnin a birnin wanda dole mutum yabi ya yi biyayya a gare su. 74 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Akwai zaratan jarumai kuma jatartun mayaqan samari a wannan birni na hadhuzur waxanda suke kare garin daga dukkan wani mugun abu ko hari na bazata. Bayan ga albarka noma ta wannan birni akwai arziqi na ma’adanan qasa a qarqashin wani qaton tsauni dake tsakiyar wani qaton kogi a na samun zinare da murjani a wajen don haka kullum masu cinkin zinare a cikin ziyarta birnin suke daga ko ina cikin qasashen duniya. Lokacin da sarki Lafayis ya sami labarin wannan birni na madhuzar ya ji irin arziqin dake cikinsa sai ya ximauce, nan take yasa aka tara masa dakarunsa na yaqi suka kaxaita a cikin fadarsa inda ya dubi sarkin yaqinsa yace. 75 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI “Ya kai abu damrus wane sakamako ka samo mini bisa binciken da na ce ka yi a kan birnin madhuzar?” Sa’adda sarkin yaqi abu damrus ya ji wannan tambayar sai ya yi ajiyar dogon numfashi ya dubi sarki cikin alamun karayar zuciya yace. “Ya shugabana bisa binciken da na yi akwai manya qasashen kamar guda uku a nahiyar nasarawa waxanda suke baiwa birnin madhuzar kariya da dakarunsa na yaqi, idan muka ce za mu je mu yaqi birnin madhuzar ba zamu sami nasara ba, domin zamu tafi da gaba xayan mayaqan mu za a kawo dakarun da suka ninka namu sau xari, ka san kuwa sarkin yawa yafi sarkin qarfi don haka yanzu sai musan shawarar da za mu yanke”. Koda gama faxin haka sai fada ta yi tsi! Akwa kama kallon-kallo 76 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI juna aka rasa wanda zai ce qala da ganin haka sai sarki lafayis yayi murmushi yace. “Aje a fara shiri gobe za mu bar garin nan mu nufi birnin madhuzar kuma dakaru dubu xaya kacal nake so su yi mini rakiya”. Sarki lafayis na gama faxin hakan sai ya miqe tsaye ya fice daga cikin fadar ya nufi hanyar da zata kaishi cikin gidan sarauta. Sai da aka ga sarki ya qule an daina hangoshi sannan waziri ya dubi sarki yaqi yace “Me ka fahimta dangane da wannan hukunci da sarki ya yanke?” Sarkin yaqi ya yi murmushi yace. “Tabbas sarki ba zai yi yunqurin yaqar birnin madhuzar ba so yake mu je a matsayin fatake”. 77 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Koda jin haka sai hankalin gaba xayan ‘yan majalisar ya dugunzuma ba don komai ba sai saboda sun san halin sarki lafayis na iya yaudara akan tafarkin neman biyan buqatarsa akwai yayuwar ya je ma ya zauna a cikin birnin na madhuzar ya rinqa taimakonsa ya kwashe duk abin da yake so a garin ya sulale ya gudo kafin su Ankara. Na dai ‘yan majalisar suka yi ta kace na ce kowa na faxin albarkacin bakinsa. Lokacin da gari ya soma yin duhu sarki lafiyis na zaune a cikin babban falonsa yana nishaxi yana shan giya, ga waxansu kyawawan kuyangi su bakwai tsaye a gefe guda suna ta faman tiqa rawa sai ga sarkin yaqi abu Damrus ya shigo. 78 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Da isowarsa kusa da kujera da sarki lafayis ke zaune sai ya zube qasa ya gaisuwa, batare da ya xago kai ya dubi sarki ba, sai yace. “Ya shugabana an gama shirin tafiya kai ake jira kawai”. Koda jin haka sai sarki lafayis ya yi murmushi kuma ya miqe tsaye zumbur ya tafa hannayensa sau xaya take ‘yan matan dake rawa da waxanda suka fice daga falon shi kuwa sarki lafayis sai ya wuce gaba ya nufi hanyar fita daga falon yana mai cewa da sarkin yaqi mu je can bakin fadar. Dakarun Rakiyar na tsaitsaye bisa dawakai a gefe xaya kuma kuyangin sarki ne su goma gami da waxansu hadimai bakwai a kusa da dakarun kuma akwai raquma saba’in xauke da guzuri da kuma keken dokin sarki lafayis. 79 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Batare da vata lokaci ba sarki ya shiga cikin keken dokin nasa ya zauna,zamansa ke da wuya sai dakarun rakiyar suka rabu gida biyu, kaso xaya suka wuce gaban keken dokin sarki rabi kuma suka tsaya a bayan keken dokin ma’ana dai suka sa keken dokin a tsakiya. Nan take aka fara tafiya aka fice daga cikin birnin qisra gaba xaya sai da wannan zuga ta sarki lafayis ta shafe kwana uku cir! Tana keta dazuzzuka batare da sun haxu da wani mugun abu ba. A ranar kwana na uku ne suka yada zango a bakin wata qorama nan da nan aka kafa sansani aka haxa tantuna kuma aka kewaye sansanin da itatuwa yadda babu wata dabba ko mutum da zai iya shigo wa kai tsaye. A wannan lokkaci da aka kammala kafa sansanin farkon 80 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI yammaci ne don haka ana gama cin abinci sai sarki ya dubi sarkin yaqi yace. ‘Ka wakilceni akan komai ni yanzu ina sha’awar shiga daji domin yin farauta”. Koda jin haka sai hankalin kowa ya dugunzuma ainun, musamman sarkin yaqi don haka sai ya dubi sarki lafayis cikin alamun firgici yace. “Ya shugabana kusa ni cewa akwai abubuwa masu hatsari a cikin wannan dazuzzuka da muke bai kamata ka shiga yin farautana, kai kaxai”. Da jin haka sai sarki lafayis ya yi murmushi yace. ‘Na gama yanke hukunci duk wanda ya biyo ni a baya sai takobina yasha jininsa”. 81 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Koda gama faxin haka sai sarki lafiyas ya koma cikin tantinsa ya xauko makamansa na yaqi ya kunna kai izuwa cikin daji, kai tsaye batare da shakkar komai bah aka dai su sarki yaqi suka zubawa sarki lafayis idanu har ya qule aka daina hango shi. Haqiqa masu iya magana sunce jiki magayi ne kuma wanda bai ji bari ba zai ji woho. Lokacin da sarki lafayis yaci gaba da kutsawa cikin daji yana kallekalle da dube-dube sai jikinsa ya yi sanyi ba komai ne ya hadasa hakan ba face jin tsananin shirun da ya cika wannan daji da ya shigo inka xauke sautin takun sawayensa babu abinda mutum ke iya ji face sautin iskar da take kaxa ganyayen bishiyoyi da kuma rigar jikinsa. Duk da tsananin jarumtaka irin ta sarki lafayis sai da zuciyarsa ta 82 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI xan bugo da qarfi ya tambayi kansa cikin zuciya yace mene ne dalilin da ya hana mafarauta ko ‘yan fashi ratsowa cikin wannan dajin? Mene ne yasa babu dabbobin daji da manya tsuntsaye alhalin akwai ni’imar ruwa da tsirai haka dai sarki lafayis yaci gaba da yiwa kansa waxannan tambayoyin, batare da ya baiwa kansa amsa ba har sake kutsawa cikin dajin sosai bayan ya shafe tafiyar rabin sa’a adaidai wannan lokacin ne ya iso gaban wani qaramin kogi mai ruwa garai-garai gwanin ban sha’awa yana isowa gaban kogin sai ya hango waxansu manya kifaye,kimanin guda ashirin suna ta zullo gami da kai kawo a waje xaya. Koda ganin waxannan kifayen sai sarki lafayis ya ji ya kamu da tsananin sha’awarsu don haka sai ya fara tunanin hanyar da zai bi yayi su. 83 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Kawai sai ya je ya xauko wani dogon ice ya fiqe qarshensa ya rinqa kaiwa kifayen suka da ice domin ya kamo amma sai kifayen suka rinqa zullewa baya samun nasara cake su. Tsawon xan lokaci yana ta yin hakan amma ko kifi xaya ya kasa kamawa. Al’amarin da ya fusata shi kenan ya yi wurgi da icen hannunsa ya fara amfani da qarfin sihirinsa domin ya kamo kifayen gaba xaya, nan ma sai sihirin tsafi yaqi ya yi tasiri nan fa hankalinsa ya dugunzuma kuma ya kamu da tsananin mamaki gami da fushi, saboda wannan ne karo na farko a rayuwarsa daya jarabawa yin wani abu ya kasa. Mu haxu a cikin littafi na biyu daga Abdul’aziz Sani Madakin Gini. 84 HIKAYOYIN AL’AJABI  MADAKI RAI DA SO hankali kamar maciji wata baqar mota ta sulalo ta samu matsuguni a harabar farfajiyar asibitin, bayan ta samu matsuguni tsayin wasu mintina kafin qofar motar ta buxe a hankali, wani matashi xan kwalisa ya sako qafafunsa waje kafin a hankali shima ya qarasa fitowa. Fuskarsa tana sanye da wani baqin tabarau wanda ya taimaka wajen voye damuwar dake shimfixe akan fuskarsa. Kai tsaye ya wuce cikin asibitin, bai tsaya a ko ina ba sai qofar ofishin likita, ya tura haxi da sallama ya shiga. Wani dogo siriri kamar takanxa ya xago ya dube shi da motsatsiyar fuskarsa kamar an taka tunfafiya, ganin shigar Bashir ya saka bakinsa ya qara washe wa zuwa murmushi, kafin ya amsa sallamar da ya yi tare da miqa masa hannu suka gaisa cike da shauqin ganinsa. “Kamar kasan kai nake zaman jira” Ya faxa masa har lokacin hannun Bashir yana cikin nasa. 85 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI “Cinkoson ababen hawa ne ya hanani qarasowa akan lokaci” Ya faxa yana zama. Likitan ya gyaxa kai kamar qadangare sannan ya jawo wata takarda yana dubawa bayan wasu sakani ya xago qwayar idanunsa ya dubi Bashir yana xan yamutsa fuska, kamar ba zai yi magana ba. “Har yanzu dai abinda muke son samu bamu same shi ba” Ya xan yi shiru yana kallon fuskar Bashir sannan ya miqa siraran ‘yan yatsun hannunsa ya xauko biro yana juya shi a tsakanin tsintsiyar hannunsa sannan ya ci gaba da magana. “Yanzu ma kamar ko wane lokaci zan ci gaba da faxa maka cewar, yana da kyau ka sakawa zuciyarka dangana duk abinda Allah ya qaddara zai faru ya riga ya faru, ita mutuwa xaya ce kuma wanda ya mutu ba zai tava dawowa ba” Bashir ya xago a hankali ya dubi likitan sannan ya kauda kai zuwa gefe, idan da sabo wannan ba shi ne karo na farko da wannan motsatsen likitan ya ke faxa ma sa waxannan kalaman ba. “Likita ba zan iya cire son Zainab daga cikin raina ba” Ya faxa a taqaice, bayan xan shiru ya ci gaba da magana cikin kwantar da murya. 86 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI “Bana iya barci sai na kuna kaset xin bikin mu na kalla, haka nan dana tashi daga barci bama samun nutsuwa sai na xauko kundin hotunanta na kalla, sau nawa zan faxa maka ba zan tava iya daina tunaninta ba” Dogon likitan ya saukar da ajiyar zuciya. “Nima ba cewa na yi ka daina tunaninta ba, amman ka dubi irin halin daka shiga a rashinta, wannan ciwon naka dole sai ka daina sakawa ranka damuwa sannan za mu samu nasara akan samun lafiyarka” Bashir ya yi murmushi. “Ba zan tava daina tunanin matata zainab ba”. Ya faxa yana xan buga tebur xin da xan yatsansa. “Ni kaina nasan abu xaya ne zai saka na daina damuwa” Ya kalli idon likitan shima ya qura masa ido. “Mene shi?” Likitan ya tambaya jin shirun yana neman yin yawa. “Idan zaka iya bani maganin da zai dawo min da Zainab a raye” Cikin tsananin kaxuwa likitan ya dube shi baki buxe. 87 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Cike da damuwa Bashir ya baro wajen likitan ya na tafiya akan titi duk qwaqwalwarsa ta cika da tunani kala-kala shi kansa yasan tuqin kawai yake yi amman rabin hankalinsa baya kan titin. A haka ya zo daidai hanyar da zata kai shi unguwar Briged don haka sai ya saka sigina ya shiga daidai kwanar ‘yan kaji Mariya dake tafe hankalinta a tsananin tashe tafiya kawai take yi sam bata san wajen da take saka qafarta ba har ta hau tsakiyar titi sam bata sani ba. Kamar daga sama Bashir yaga ta faxo tsakiyar titi, cikin tsananin razana yaja wani birki amman duk da haka sai daya xan tava ta, Mariya ta xago kai ta dube shi, shima yana daga cikin motar ya dubeta. Kallon xaya daya yi mata yasan tana cikin tsananin tashin hankali, bata kuma bi ta kanshi ba sai ta yi gaba abinta. Bashir ya bita da kallo cike da mamaki, ko ita kuma me yake damunta? Yasan dai banza bata kai zomo kasuwa, da ganinta tana cikin tashin hankali. Bai kuma bi ta kanta ba ya sakawa motar giya ya soma tafiya yana yiwa Allah godiya da bai qaddara tsautsayin a kan shi yake ba. A haka 88 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI har ya qaraso inda ya nufa wajen malaminsa da yake ba shi taimako game da harkokin kasuwancin sa. A shagonsa ya same shi malam Yusuf matashin gardine xan kimanin shekara talatin, tun sanda matar Bashir ta rasu yake qoqari wajen yi masa rubutu yana ba shi duk a cikin qoqarin ganin ya mance da marigarya. Amman duk da wannan qoqarin da yake yi sam babu wani ci gaba, domin kullum ta Allah akwai wani abu na daban da Bashir xin yake zuwar masa da shi. A lokacin da Bashir xin ya qarasa qofar shagon ya samu waje ya yi fakin xin motar ya yi shiru yana kallon qofar shiga cikin shagon nan take wani tunani ya ziyarci zuciyarsa. Wata rana sun tava zuwa wajen malam Yusuf da Zainab saboda matsala aljanu da suke damunta tana yawan fama da wasu munanan mafarke-mafarke harma ta riqa zabura a cikin barci, sai kuma wani tsananin ciwon kai mara sauka daya adabeta. 89 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Hakan ya saka ya xaukota takanas ta kano ya kawota wajensa, lokacin da suka zo layin sai ta dubeshi cikin damuwa. “Ni bana son unguwar nan” Bashir ya dubeta da murmushi. “Me yasa?” Ta xan kalli gefe. “Shi kenan dai”. “Da kin faxi abinda yake ranki dai”. “Ni dai kawai mu koma gida, kaina ya daina ciwon” Suka qarasa cikin layin ya tsaya a qofar shiga shagon. “Sai da muka zo sannan za ki ce kin fasa, ki daure dai mu shiga kawai addu’a zai yi miki shi kenan” Zainab ta yi murmushi. “Mijina kenan, ai tunda na faxa maka ba zan shiga ba kasan ba zan tava shiga ba” Bashir ya xan yi shiru na taqin lokaci sannan ya ce mata. “To bari na shiga wajensa na fito”. “Dama hakan ya fi maka, ni dai ina nan zaune ina jiranka idan kuma ka daxe zaka dawo ka samu bana nan” Cikin sauri ya buxe motar ya fita. Ko daya shiga wajen malam Yusuf sai ya same shi a zaune yana zane-zane akan rairayi, 90 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI bayan sun gaisa sai ya dube shi ya yi murmushi tare da faxin. “Ina uwar gidan kuma?” Bashir ya dube shi cike da mamaki domin bai faxa masa cewar za su zo ba, ganin ya na yi masa kallon mamaki sai ya qara cewa da shi. “Ko ba kwana tayi tana ciwon kai ba?” Cikin sanyi jiki Bashir ya ba shi amsa. “Haka ne”. Sai ya qara yin murmushi ya ci gaba da zane-zanen shi sannan ya qara cewa da shi. “Yanzu ma da kuka zo ai cewa tayi dakai ba zata shigo nan ba, daman ai ba za su barta ta shigo ba” Bashir ya dube shi cikin kaxuwa. “Saboda me?” “Aljanun ne suka hanata…” Bashir ya saukar da ajiyar zuciya, bayan ya dawo daga duniyar tunanin daya shiga sannan a hankali ya buxe qofar motar ya zuro qafafunsa waje, ya jima a zaune qafarsa a qasa kafin ya fito daga cikin motar. Ya nufi qofar shiga cikin shagon yana zuwa ya qwanqwasa tare da yin sallama, daga 91 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI cikin shagon aka amsa masa tare da bashi izinin shiga cikin shagon, Bashir ya shiga tare da qara yin sallama ya samu Malam Yusuf a zaune akan wani buzu yana jan carbi. Ya miqa masa hannu suka gaisa fuskarsa cike da fara’a ya samu waje ya zauna, malam Yusuf ya qarasa janye sauran ‘ya ‘yan carbin da suka rage sannan ya ajiye carbin. “Malam Bashir ya qarin haquri?” “Haquri sai ma’aiki”. “Allah ya ji qansa”. “Allahuma amin” Suka yi shiru na taqin lokaci. “Ya kasuwar taka kuma?” Bashir ya gyara zama. “Kasuwa mun gode Allah, harkoki suna tafiya yadda ake so” Malam Yusuf ya jinjina kai. “Haka ake so” Ya xan yi shiru sannan ya kuma xauko carbinsa yana xan juyawa a hannunsa sannan ya ci gaba da magana. “Kana dai shan rubutun nan da nake bayarwa a kawo maka?” Bashir ya gyaxa kai. “Eh ina sha amman har yanzu ban daina ganin zainab ba, har yanzu duk lokacin dana shiga falon mu sai naganta a zaune tana yi mun 92 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI murmushi, haka ma idan na shiga wanka sai ta zo ta tayani, hakan nan tana zuwa ta tayani kwana” Malam Yusuf ya yi shiru kawai yana kallonsa cike da mamaki. “Duka marigayar kake gani tana yi maka waxannan abubuwan?” “Eh” Malam Yusuf ya yi murmushi, tare da dafa hannun Bashir. “Bashir wanda ya mutu ai ya riga ya mutu baya tava dawowa”. “Nasan da haka, amman wallahi Zainab nake gani”. Malam Yusuf ya kalle shi cikin tausayawa, sannan cikin kwantar da murya ya ce masa. “Bashir kana yin addu’o’in dana baka kuwa?”. “Wane kenan?” Shima ya mayar masa da tambayar. “Wacce da wacce na baka ma tukuna?”. “Dana kwanciya barci dana tashi daga barci dana fita daga gida dana shiga abin hawa dana saka kaya da…” Ya xaga masa hannu. 93 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI “Ya isa haka” Ya faxa yana sauke wani numfashi. “Amman kuma duk da haka baka daina gane-ganen marigaya ba?” “Shakka-babu” Malam Yusuf ya miqa hannu ya jawo wani allo dake xauke da rairayi ya xan soma zane-zane zuwa wani xan sakani sannan ya furza da wani huci ya xago kai ya dubi Bashir. “Kafin ka zo nan kun haxu da wata?” Bashir ya dubeshi cikin mamaki. “Ban haxu da wata mace ba”. Malam Yusuf ya yi murmushi, tare da ci gaba da zane-zanensa yana yin murmushi ya qara cewa da shi. “Tuna dai tabbas kun haxu da wata, kamar tana cikin tashin hankali…” Bashir ya katse masa magana cikin sauri. “Eh na kusa buge wata da mota, ga alama tana cikin tashin hankali”. Malam Yusuf ya dakata da dubansa. “Wannan ita ce maganin matsalar ka, ita zata saka mancewa da marigarya, sai dai matsalar xaya” Ya xago cikin jimami yana 94 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI kallon fuskar Bashir sannan ya ci gaba da magana. “Ta yi aure-aure har guda huxu”. “Huxu!” Cikin ruxani Bashir ya tambaya. “Eh” Ya tsuke fuska kamar an matse lemon tsami. “Bashir an camfata da cewar farar qafa gareta”. “Mene kuma farar qafa?” Ya tambaya cike da damuwa. Ya xan yi murmushin gefen fuska “Baka san abinda ake nufi da cewar mace tana da farar qafa ba?” Ya xauki carbinsa yaci gaba da ja. “Idan aka ce mace tana da farar qafa ma’ana duk wanda ta aura duk yawan dukiyarsa sai ya tsiyace ya koma kamar veran masalaci”. Cike da damuwa Bashir ya dube shi. “Malam mene maganin faruwar hakan?” “Abu xaya ne zai hana faruwar hakan, ace ka koma cikin mahaifiyarka”. Bashir ya yi mutuwar tsaye. Kadan kenan daga cikin littafi me suna RAI DA SO NEMI NAKA A KASUWA 95 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Domin neman qarin bayani tuntuvi lambar waya 09050063882 96 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3