Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
tava sirrinki,sirrin kuma shi ne za ki iya mayar da akwatin nan ta zama xan qarami guri da zaki xaure shi a qugunki ya kasance dare da rana yana jikin ki, duk sa’adda kika kaxaita a cikin xakinki ya zamana cewa kina son ki karanta littafin al’ajabi sai ki kwance 35 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI gurin ki ajiye shi a gabanki ki xiga masa jini. Take gurin zai zama kawai sai ke kaxai kuma akwatin zata buxe kanta ki xauko littafin ki karanta da zarar kin kammala kin mayar da littafin cikin akwatin za ki ga ta rufe kanta, kuma ta sake rikixewa ta zama qaramin gurin. Haka za ki yi ta yi har ki samu nasarar kammala karanta littafi a cikin kwanaki xari uku a da sittin ki sani cewa daga yau ba ni da sauran alaqa da ke koda wannan littafi domin dama nib a waiwar kakanki ce na fi shekara saba’in ina yi masa bauta bai ‘yanta ni ba albashir xin ‘yanta shi ne na kare wanna littafi har izuwa lokacin da hannunki zai kai kansa, gashi kuwa yanzu lokacin ya yi. Da wannan furuci nake yi miki bankwana yanzu nan zan tafi izuwa 36 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI can qarshen duniya vangaren bangon arewa zan qarasa sauran rayuwata tare da mijina wanda tun da aka raba mu tsawon shekaru yake zaune yana faman sharar kuka, idan na koma gare shin a sami ‘yancina babu wani boka da ya isa ya sake tsare ni na yi masa bauta, kuma har izuwa qarshen rayuwata bazan sake rabuwa da mijina ba, daidai da tsawon kwana xaya”. Koda gama faxin hakan sai Aljana jarisa ta yunqura zata tashi sama, amma sai Nasmirat ta yi wuf ta roqo fukafukinta guda xaya tace “Ya za ki tafi baki gaya mini yadda zan mayar da wannan akwati xan qaramin guru ba?” Koda jin wannan tambaya sai aljana jarisa ta qyalqyale da dariya tace “Ai na gaya miki tun xazu tun da dai yanzu kece kaxai a cikin wannan kogon dutse babu wata halitta mai 37 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI raid a ke ganinki ko sauraronki,kawai ki buxe littafin ki karanta labarai bakwai kina kammala wa sai ki mayar da littafin cikin akwatin ki rufe za ki ga akwatin da kanta ta rikixe ta zama gurun. Gama faxin hakan ke da wuya sai aljana jarisa ta buxe fukafukanta ta yi sama tana ta qyalqyala dariya farin ciki kuma ta buxe muryarta da qarfi tana faxin na sami ‘yanci na samu ‘yanci. Kafin cikin daqiqa biyar aljana jarisa ta luluqa a cikin gajimare ta vace vat tamkar bata tava wanzuwa ba a wajen. Koda ganin abinda ya faru sai Nasmirat ta dubi gabas da yamma kudu da arewa a cikin kogon dutsen kuma ta kasa kunnuwa har sai data tabbatar da cewar babu wnai mahaluki mai rai a cikin kogon sannan ta buxe 38 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI littafin na hikayoyin aljabi ya fara karanta labarin farko. Koda ta ji irin tsananin daxin labarin da kuma abubuwan al’ajabin dake cikinsa sai ta ji cewa ai idan kwana zata yi a tsaye tana karanta shi ba zata gaji ba. Nan da nan a cikin daqiqa kaxan ta gama karanta labaru bakwai. Tana gama karanta labari na bakwai sai littafin ya rufe kansa, Nasmirat ta yunqura da nufin ta sake buxe littafin domin ta ci gaba da karanta shi amma sai ta ji littafin ya vame! Tamkar qusa aka kafe shi. Nan fa ta dage iya qarfinta domin ta buxe amma sai ta kasa, bisa dole ta haqura ta mayar da littafin cikin akwatin. Faruwa haka keda wuya sai farar akwatin ta rufe kanta sannan ta qanqance ta zama guru xaya xan 39 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI qarami cikin farin ciki Nasmirat ta xauko gurun sannan ta xaure shi a qugunta sannna ta ruga da gudu ta fice daga cikin kogon dutsen. Daga wannan rana kullum da daddare sai Nasmirat ta shiga cikin wani shago kasuwa wanda babu wani a cikinsa ta kulle kanta ta kwance wannan guru daga qugunta ta ajiye shi a gabanta sannan tasa zabira ta xan yanki xanyatsanta ta xigawa gurin jini. Take yake zama wannan farar akwatin ya buxe ita kuma sai ta xauko littafi hikayoyin al’ajabi ta karance labarai bakwai a cikinsa. Tana gamawa sai ta mayar da littafin cikin akwatin kuwa sai ta zama guru, Nasmirat ta xauke abinta tax aura shi a qugunta. 40 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI BABI NA HUXU Yau kwana bakwai ke nan Nasmirat tana yin wannan abun cikin sirri ba tare da kowa ya gani ba, ko ya ji hatta mahaifinta nata kuwa amma kawai ranar daya tava hannunta ya ji alamun yanka ya tambaye ta yadda aka yi ta sami wannan raunika sai tace da shi ai ta je aikin aikatau ne a wani gidan attajiri aka sata ferayar kabewa shi ne ta samu wannan raunika. Koda jin haka sai makaho marhat yayi ajiyar zuciya, cikin alamun rashin gamsuwa amma sai ya yi shiru bai sake tanka mata ba. 41 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI A wanna rana ta bakwai ne aka je aka xauko Nasmirat da mahaifinta aka kai su cikin wannan qerarren gida da shirin cewa kashe gari za a yi bikin aurenta da sarki Ram. A can gidan sarki Ram kuwa tuni an fara shirye-shiryen bikin aurensa ana ta shirya abinci da za a ci gobe manya baqi kuwa tuni sun fara hallara daga sauran qasashen makwabtaka birni da qauye, hadimai,barori da kuyangi kuwa sai kai kawo suke yi suna ta yin ayyuka nag yare-gyare ado da shirya qawa a wurare da yake na cikin gidan sarautar. Su kuwa matan sarki Ram su goma sha xaya sun taru gaba xayansu a cikin xakin uwargidansu suna shiryawa kansu wata ‘yar qaramar walima sai ciye-ciye da shaye-shaye suke yi, suna ta qyalqyala dariya 42 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI mugunta suna cewa za su ga yanda wannan budurwa zata iya tsallake kaifin takobin sarki Ram yaya suma suka kasance matan sarki na tsawon shekaru sun haqura da zuwa turakarsa sai kamar budurwa yar shekara sha takwas ce zata iya da shi? Me ta sani a rayuwar duniya ma bare ta bashi labarum da za su kwantar masa da hankali su hana shi hauka. A can vangaren turakar sarki kuma a wannan rana wani abin mamaki ne ya faru, domin a ranar gaba xaya ciwon sarki bai tashi ba ko sau xaya ba, kuma sai ya kasance a cikin tsananin farin ciki ya yi ta rabon kuxi da kayayyaki ya zamana cewa babu abinda yake son a faxa masa face a ambaci sunan amaryarsa Nasmirat, shi kansa Boka Aulad makusancin sarki Ram sai da ya yi 43 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI matuqar mamakin yadda aka yi sarki Ram bai yi cutarsa ta hauka ba a wannan rana, kuma har sai da dare ya raba sarki Ram bai daina nishaxi da farin ciki ba, babu shiri a lokacin Boka Aulad yasa aka baiwa sarki Ram maganin barci yasha sannan ya vingire akan gado ya kama sharar barci hard a minshari rabon da sarki Ram ya sami irin wannan barci mai nauyi tun kafin ya haxu da lalurar wannan cuta. Kashe gari kuwa da sassafe aka fara shagalin biki gaba xaya birnin ya ruxe da kaxe-kaxe gami da bushebushe sarakuna da ‘ya ‘yansu attajirai da masu faxa aji suka yi ta tururwa izuwa cikin birnin suna rinqa shiga gidan sarautar,masana tarihin birnin said a suka tabbatar da cewa ba a tava yin gagarumin taro da ya kai na bikin auren sarki Ram da Nasmirat ba, 44 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI tun daga farkon kafuwar qasar kuwa izuwa yanzu. Bisa al’adar auren a qasar Hindu a wannan lokacin dole ne ango da amarya su tsaya a gaban masoyansu ‘yan uwansu da dukkan zuri’arsu a kwara musu ruwan madarar shanu akansu sannan kowannensu ya zo gaban gunkin da suke bautawa ya yi sujjada ya dangwali wani jan zabibi da xanyatsansa na hagu yayi fashin goshi a kansa da goshin gunkin, sannan kuma ango ya shafawa amaryarsa jan zabibin akan goshinta, hakan na faruwa sun tabbata miji da mata kuma sun sami albarkar gunki. Bayan taro y agama cika, duk inda mutum ya hanga gabas da yamma kudu da arewa sai dai yaga kowannan bil’adama rubutu batutu babu masaka tsinke, a cikin tsakiyar filin gidan sarautar ne aka yi wannan 45 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI gangami sai ga sarki Ram tare da amaryarsa sun fito daga cikin gidan sarautar sun fito daga cikin gidan sarauta. Dukkaninsu sun cava ado na gaban kwatance suna tafiya a kan wani jan kishi wanda ya nufo wajen da gunki yake, dakaru da kuyangi na take musu baya. Koda ganin fitowar sarki da amaryarsa sai mutane suka ruxe da shewa suka kama yi musu jinjina gami da kirari. Sai da sarki Ram da amaryasa Nasmirat suka yi taku sittin sannan suka iso gaban gunki suka tsaya tsayuwarsu keda wuya sai aka zo da madarar guda biyu a cikin gorar ruwa aka kwararaa sarki da Nasmirat a kansu suka jiqe sharkaf kaico, kaji wata al’adar banza duk wannan 46 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI kwalliya da ma’auratan suka yi an vatata. Nan take sarki Ram ya dangwali jan zabibi ya yiwa kan fashin goshin kuma ya yiwa gunki ya koma gefe xaya ya tsaya. Ita ma Nasmirat sai ta dangwali zabibin ta shafawa kanta a goshin. Koda ta durfafi gunki da nufin ta shafa masa zabibin akan goshinsa sai kawai aka ji an zabga wata irin tsawa mai qarfin gaske mai tsananin ban tsoro wacce ta razana kowa alhalin babu alamar hadari a garin. Ita kanta Nasmirat bata san sa’adda ta faxi qas saboda tsananin firgita da tayi, amma sai ta miqe tsaye zumbur taje ta shafawa gunki zabibin sannnan ta shafawa kanta. Koda ganin haka sai murna ta kama sarki Ram don haka sai shima ya 47 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI dangwali zabibin ya shafawa Nasmirat a goshinta suka rungume juna a lokacin da jama’a suka kaure da shewa gami da tafi alamar aure ya tabbata a lokacin da jama’a suka kaure da wannan shewa ana ta murna gaba xaya bokayen qasar kuwa hankalinsu a dugunzume yake bisa wannan muguwar tsawa da aka tafka. A lokacin da Nasimarat ta je zata shafawa abin bautarsu zabibi a goshi. Hakan bai tava faruwa ba kuma yana yi musu nuni ne da cewa lallai akwai wani babban sauyi da yake shirin zuwa, amma ta hannu wannan budurwa amarya sarki. Nan da nan Bokayen suka bar filin gidan sarautar gaba xayansu suka tafi izuwa can wani xakin bauta dake bayan gari suka kulle qofarsa. 48 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI 49 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI BABI NA BIYAR Boka Aulad shi ne shugabansu don haka sai ya dube su gaba xayansu yace da su “Abin da nake so da ku shi ne kowannenku yayi mana bincike yanzu a cikin madubin tsafinsa ya gano mana ma’anar wannan tsawa mai ban tsoro da aka tafka sakamakon zuwan Nasmirat gaban abin bautarmu da nufin shafa masa zabibi bisa al’adar aure. Koda jin wannan umarni sai gaba xaya bokayen suka fiddo madubinsu na tsafi suka duqufa shima Boka Aulad xin ba a barshi a baya ba sai ya taya su jim kaxan sai kowa ya xago kai suka rinqa kallon-kallo a junansu cikin matuqar al’ajabi aka rasa wanda zai ce qala har shi kansa Boka Aulad xin. 50 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Daga can sai boka Aulad ya dube su yace. “Na sani cewa duk abu guda muka gani a cikin bincikenmu don haka ba sai na tambayi xayanku ba. Tabbas wannan bil al’ajabi ne baba kuma abin tsoro don haka ya zama wajibi musan matakan da zamu xauka, wannan tsawa da aka tafka ashe ba komai bace face gargaxi a gare mu gaba xayan mutanen Hindu cewar mai girma abin bautarmu bai yi amana da wannan auren ba na sarki saboda ita wannan yarinya Nasmirat tana da wani babban sirri wanda nan gaba zata kai ga samun babban matsayi da xaukaka a birninmu. Ga dukkan alamu ma sai ta mulke mu ta zama sarauniyarmu idan kuma hakan ta faru, mun tafka babban abin kunya da ba a tava yin kamarsa ba. 51 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Ko ina a duniya ace ‘yar almajiri mara cikaken asali ta zama sarauniyar mu ya zama dole mu hana sarki yin taraiya da wannan amarya tasa a wannan daren na yau, kuma musan hanyar da za mu bi mu hallakata a sirrance batare da kowa ya sani ba”. Koda boka Aulad ya zo nan a zancensa sai babban Boka na birnin Kashmir ya miqe tsaye ya dube shi cikin alamun girmamawa kuma ya risina masa yace “Ya shugabana to yanzu ya za mu yi da wannan cuta ta sarki tunda ka san cewa abu ne mawuyanci mu sake samun budurwar da zata iya sai da ranta ta aure shi?” Koda jin wannan tambaya sai Boka Aulad ya ja numfashi ya ajiye sannan yace “Ai har abada jarumai basa qarewa a cikin duniya sai mu lalubo wata, ina son ku barni mini 52 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI komai a hannuna zan san abin da zan yi. A yau xin nan zan kawar da wannan amarya ta sarki cire silin gashi daga cikin tandun mai yafi wannan aikin sauqi a wajena, tunda kun sani cewa babu wani mahaluki daya fini samun aminci a wajen sarki”. Koda jin wannan batun sai farin ciki ya lulluve dukanin bokayen suka kama yiwa Boka Aulad jinjina cikin farin ciki gami da samun nutsuwa. A can filin gidan sarauta kuwa bayan an gama xaura aure sarakai da manya baqi suna zuwa su taya shi murna, kuma suna bashi kyaututtuka a lokacin da amaryarsa ke tsaye daf da shi, sai ya lura babu boka Aulad a filin gaba xaya. Koda ya sake hangawa ko ina sai yaga ashe gaba xaya bokayen qasar ma basa nan, nan take hankalin 53 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI sarki Ram ya dugunzuma ainun ya aiyana a cikin ransa cewar lallai Boka Aulad yaci amanarsa kuma akwai wata maqarqashiya da yake shirin tafka masa, shi da sauran bokayen. Nan take sarki Ram ya kirawo sarkin yaqinsa yace da shi, maza kasa a rakani izuwa turakata kuma daga yau kada a sake barin kowa ya shigo inda nake ko a inda amaryata take koda kuwa Boka Aulad ne, kai kaxai na yarda da ka shigo turakar mu yi magana. Sarkin yaqi ya risina ya ce “An gama ya shugabana”. Nan take sarki Ram ya kama hannun amaryasa Nasmirat suka nufi cikin gidan sarauta dakaru sama da miliyan xaya na mutane da aljanu na take masa baya. A daidai wannan lokacin ne Bola Aulad da sauran bokayen suka 54 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI dawo filin fadar koda Boka Aulad ya hango sarki da amaryarsa za su shige cikin gidan sarautar sai ya rugo da gudu ya nufi inda sarki ya ke da nufin ya shiga. Kwatsam sai Boka Aulad yaga sarkin yaqi ya sha gabansa cikin fushi Boka Aulad ya dube shi yace “Wane irin shirme ne haka zaka zo kasha gabana alhalin kasan cewa sarki baya son na gusa daga kusa da shi daidai da tsawon rabin sa’a”. Koda jin haka sai sarkin yaqi ya yi xan guntun murmushi yace. “Ai wannan da ne, yanzu nan sarki ya bani umarnin cewa kada na sake barin kowa ya je inda yake, koda kuwa kai ne”. Koda jin haka sai ran Boka Aulad ya vaci ainun ya dakawa sarkin yaqi tsawa yace “Wai shin ni kakan ka 55 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI ne har da zaka zo mini da maganar wasa”. Da jin haka sai sarkin yaqi ya turvune fuskarsa yace “Na tava yi maka wasa ne? ko kuwa zan yi wa sarki qarya ne saboda kawai biyan wata buqata tawa? Inda sarki bai sauya ra’ayinsa ba ai babu yadda za a yi ya tafi ya barka. Ni ina ganin sarki yana zarginka da wani laifi don haka kasan hanyar da zaka bi ka gyara tsakaninka da shi”. Koda sarkin yaqi ya zo nan a zancensa sai hankali Boka Aulad ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe ya dubi sarkin yaqi cikin alamun matuqar damuwa yace. “Dole ne naga sarki yanzu domin na hana shi Tarawa da wannan amaryar tasa domin kuwa akwai babbar matsala, abin da nake so da 56 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI kai shi ne ka yi min jagora izuwa ga sarki yanzu nan kafin lokaci ya qure”. Sarkin yaqi ya girgiza kai yace. “Ba zan iya ba, domin ni ma idan na kaika gare shi zan iya rasa matsayina gaba xaya”. Koda jin haka sai Boka Aulad ya dakawa sarkin yaqi tsawa, a karo na biyu yace. ‘Shin ka manta ne cewa ni da kai duk munyi rantsuwa da girman abin bautarmu cewa zamu sallama rayuwarmu da komai na mu domin mu kare wannan gidan sarauta na mu da qasar gaba xaya. Na rantse da girman iyayena idan ban hana sarki taraiya da wannan amarya tasa ba sai mulkin ya suvuce masa gaba xaya domin ita amaryarce zata haye karagarsa kuma ajalinsa a hannunta yake, ta yaya muna ji muna gani za mu bar ‘yar almajiri mara 57 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI cikakken asali zata zo ta karvi mulkin qasar nan dare xaya? Sa’adda Boka Aulad ya zo nan a zancensa sai hankalin sarkin yaqi ya dugunzuma ainun ya yi shiru yana tunani da nazari har izuwa tsawon yan daqiqu ya rasa abin da zai ce daga can sai ya xago kai ya dubi Boka Aulad yace. “Tabbas dole ne na baka haxin kai xari bisa xari domin ganin mun ceci rayuwar sarki da kuma darajar qasar nan ta kowane hali, amma ka sani cewa tsalle xaya shi ke jefa mutum a cikin rijiya, gaggawa a cikin wannan al’amari a gare ni yana da matuqar haxari, ka tuna cewa kai fa boka ne wanda babu kamarsa a qasar nan don haka ka yi amfani da qarfin sihirinka wajen magance wannan matsala”. 58 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Boka Aulad ya yi ajiyar zuciya cikin alamun takaici yace “Ai in da zan iya yin hakan da tuni na yi ba sai na tuntuve ka ba, ai idan ka ji makaho yace a yi wasan jifa to lallai ya taka hoge, ka tuna cewa duk faxin qasar nan ba a sami budurwa da ta amince za ta auri sarki ba a cikin wannan larura tasa face Nasmirat kasan kuma lallai akwai abinda ta taka. Bisa wannan binciken da na yi a kanta na gano cewa akwai wani babban sihirin tsafi a jikinta wanda duk wanda ya tunkareta da nufin ya hallakata mutuwa zai yi, maganinta kawai shi ne sarki ya fasa aurenta kuma ya nisanta da ita. Tun da ba zamu iya tava Nasmirat ba ai za mu iya raba sarki da ita, ni yanzu ba ni da sauran aminci sarki kai kuwa kana da shi, ka yi amfani da wannan dama a yau xin nan 59 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI kafin sarki ya shiga xakin amaryarsa kasa a sace shi a sirrance mu fitar da daga cikin gidan sarautar gaba xaya, mu kaishi can gidana na bayan gari mu voye shi. A sannan ne zamu yi tunanin hanyar da zamu bi mu fitar da Nasmirat daga cikin gidan sarautar gaba xaya a cikin ruwan sanyi”. Lokacin da Boka Aulad ya zo nan a zancensa sai hankalin sarkin yaqi ya qara dugunzuma ya shiga cikin halin wasi-wasi,zullumi, fargaba da zargi kawai sai ya xago kai ya dubi Boka Aulad cikin alamun rashin yadda yace. “Duk waxannan abubuwan da ka shirya mini yanzu sunyi kama da hanyoyin da ake bi a shirya juyin mulki, da wace hujja zan yi amfani na gamsu cewa ba juyin mulki kake shirin yiwa sarki ba?” 60 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Boka Aulad ya dakawa sarkin yaqi tsawa a karo na uku yace “Yau shekara ta arba’in ina bauta a wannan gidan na sarauta na yi bauta ga mahaifin sarki Ram da kakansa duk tsawon waxannan shekarun ba a tava kamani da laifin cin amanarsu ba, duk abinda nake nema na jin daxi duniya ina da shi a can fada ta ina da dukiya mai tsananin yawan da ban san iyakar adadin yawanta ba, ina da matan aure guda tamanin da xaya, ina da ‘ya ‘ya arba’in da biyu fadata ta ginu kuma ta qawatu fiye da wannan wacce muke ciki ina da fadawa kuyangi,barori da dakarun tsaro waxanda suka ninka na wannan fadar sau uku, a kan wane dalili zan yi sha’awar wannan fada ko karagar cikinta?”. Koda sarkin yaqi ya ji waxannan tambayoyi da Boka Aulad ya yi masa sai jikinsa ya yi sanyi 61 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI matuqa ya rasa abin da zai ce daga can sai ya xaga kai ya dubi Boka Aulad yace. “Kafin dare yayi akai amarya xakin angonta zan san abin da zan yi akai kuma zan nemeka na sanar da kai komai”. Koda jin haka sai Boka Aulad yayi doguwar ajiyar zuciya, sannan yace “Lallai ka tabbatar da cewa ka yi duk motsinka kafin a kai amarya xakin sarki”. Koda gama faxin haka sai Boka Aulad ya juya ya yafito wani hadiminsa da hannu take hadimin ya janyo dokin Boka Aulad da sauri ya kawo masa. Cikin alamun fushi Boka Aulad ya kama dokin nasa yah aye ya zabureshi da gudu ya nufi hanyar fita daga cikin gidan sarautar gaba xaya, aikuwa sai wasu dakarun Boka Aulad 62 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI kimanin su arba’in bisa dawakai suka rufa masa baya. Koda jama’ar gari suka ga Boka Aulad ya fice daga ciki gidan sarautar gaba xaya sai suka cika da tsananin mamaki saboda an san cewa dare da rana yana tare da sarki baya yarda ya yi nisanta da shi,shi ma sarkin haka fa aka fara tsegumi, kowa ya riqa faxin albarkacin bakinsa. 63 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI BABI NA SHIDA Al’amarin sarki Ram kuwa lokacin daya kama hannun amaryarsa Nasmirat ya yaja ta izuwa cikin gidan sarauta bai zame ko ina ba sai cikin wani babban falo wanda girmansa ya kai na fadar gidan sarautar. Babu komai a cikin wannan falo face kujeru da tebura na cin abinci birjik da yawa iya ganin mutum. Suna shigowa cikin wannan babban falon sai suka yi arba da gaba xayan sarakunan nahiyar waxanda suka zo taya sarki Ram murna wannan aure nas kowane sarki yana tare da matarsa a zaune ga kayan ciye-ciye dana shaye-shaye, iri-iri babu adadi akan teburin amma a saboda girmama 64 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI sarki Ram ko ruwansha babu wanda ya xauka ya kai bakinsa sai ya iso tukuna. Koda sarakuna da matayensu suka ga sarki Ram tare da amaryarsa sun shigo cikin falon sai gaba xayansu suka miqe tsaye suna kama yi masa tafi ya yin da waxannan sarakunan suka yi arba da amaryar Nasmirat a cikin gagarumin ado da aka cava mata sai dukkaninsu suka ximauce bisa ganin irin tsananin kyawun da Allah ya bata. Nan fa wasun su suka fara munafunci da tsegumi ga ‘yan uwansu sarakuna. Sarkin birnin kirishna ne ya dubi sarkin birnin lamras ya yi masa raxa a kunne yace “Tabbas banga laifin sarki Ram ba da ya auri wannan yarinyar ‘yar almajiri saboda ko ni ne ba zan bari ta wuce ni ba”. 65 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Koda jin haka sai sarki lamras ya yi murmushi yace “Amma ba don kyaunta ya aure ta ba an ce saboda kawai zata iya bashi labaru ne masu daxi waxanda za su sa hankalinsa ya kwanta ya daina hauka da shirme, abin tambaya a nan shi ne a ina wannan yarinya zata iya samo labarai masu daxi, kuma masu ban al’ajabin da za su iya saita wannan mahaukacin sarki?” Koda gama faxin hakan sai ga sarki Ram tare da amaryarsa sun iso daf da sarki lamras,kawai sai sarki Ram ya dubi sarki Lamras yace. “Na yi murna da ganinka a wannan biki a zatona ba zaka zo ba saboda laifin da na yi maka sa’adda muka haxu a bikin naxin sarautar birnin sin”. 66 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Koda jin haka sai sarki lamras ya kama yaqe gami da murmushin dole muryarsa na rawa yace. “Haba ya kai sarkin sarakuna ai ban isa na qi amsa gaiyatar bikinka ba”. Ita kuwa Nasmirat sai ta dube shi tace “Zaka sha mamaki idan ka ji irin labarum da zan baiwa sarki daga daren yau, zaka ji daga bakinsa”. Koda jin wannan batu sai jikin sarki lamras ya kama tsuma saboda tsananin mamaki gami da razana. Daga nan suka yi gaba abinsu haka dai aka ci gaba da gudanar liyafar bikin na su. Har tsawon wani lokaci kafin aka kammala sarki Ram da amaryasa suka wuce cikin. Da shigarsu sai ta fahimci kan sarki ya fara ciwo nan da nan idanunsa suka juye ya fara tangaxi. 67 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Koda ganin haka sai ta fahimci cewa lallai ciwon sarki ne zai tashi a daidai wannan lokacin maimakon ta ji tsoro ta nisanta da shi sai ta janyo shi jikinta ta shiga yi masa raxa a kunne tana mai cewa. “Ya kai wannan sarki mai daraja ka yi sani cewa an tava yin wani gagarumin sarki a birnin kisra wanda ya shekara xari da ashirin akan karagar mulki batare da ya tava fuskantar wata matsala ba a rayuwarsa amma a karon banza aka rabashi da mulki yana ji yana gani da qarfinsa da lafiyarsa ya dawo bawan sarkin da ya hau karagar alhalin da shi sabon sarkin ya kasance bawansa kuma ko kaxan ba shi da wata alaqa da gidan sarautar”. Koda jin wannan batu sai sarki Ram ya ji kansa ya wattsake take kuma ya ji kansa ya daina ciwo don 68 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI haka sai ya dubi Nasmirat cikin tsananin zaquwa yace, ta yaya wannan al’amari ya faru, maza ki bani wannan labari yake tauraruwar taurari. Sa’adda Nasmirat taga sarki Ram ya zaqu da son jin wannan labarin sai ta qyalqyale da dariya tace. “Ai kuwa akwai xinbin darasi a cikin wannan labarin kuma gashi yanzu dare ya soma yi, ina ganin har gari ya waye ba zan iya gama baka shi ba”. Da jin haka sai jikin sarki Ram ya kama tsuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata qone, kawai sai ya zare takobinsa ya dakawa Nasmirat tsawa yace. “Maza ki ci gaba da ba ni labarin da kika soma ko kuma yanzun na sare miki kai”. Koda jin haka sai Nasmirat ta dubi sarki Ram cikin alamun tsoro tace. 69 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI “Kwantar da hankalinka ya kai mijina ai yanzu nan zan ci gaba da baka wannan labarin” Nasmirat ta yi doguwar ajiyar numfashi sannan tace. 70 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI BABI NA BAKWAI Kimanin shekaru xari da huxu da suka shuxe anyi wani gawurtaccen sarki a birnin kisira mai suna lafayis, sarki lafayis ya kasance shahararren mayaqi kuma babban sadauki mai tarwatsa maza a filin daga. Sarki lafayis ya kasance azzalumin gaske domin bai xauki ran xan adam a bakin komai ba, zalunci kwace gami da fyaxe su ne al’adarsa ta kullum da koyaushe rashin imaninsa bai tsaya akan mazaje ba, hatta mata da qananan yara bai qyale ba, sai da takai cewa gaba xaya qasashen dake makwabtaka da birnin qisra ana tsoron sarki lafayis don haka duk qarshen wata sai kowane sarki ya kawo masa kuxi da bayi kyauta, domin gudun 71 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI kada a kawo musu harin bazato, ko ace za a yaqe su. Haka dai sarki lafayis ya zama alaqaqai kuma qadangaren bakin tulu a nahiyar gaba xaya, ya adabi kowa don haka duk sarkin da ya bashi wannan cin hanci sai dai wani ba shi ba, wato dai ataqaice sai da takai cewa a fakaice sarki lafiyas ne ke mulki gaba xaya qasashen dake nahiyar saboda duk umarnin daya baiwa sarakuna dole su bi kuma duk abinda ya buqata daga gare su sai sun kawo masa. A rayuwar sarki lafayis babu abinda ya tsana sama da ayi masa gardama ko kuma ya bayar da umarni aqi bi, duk wanda ya aikata xaya daga cikin waxannan laifukan a gare shi to sai ya kashe shi, ya qarar da dukkan zuri’arsa domin ya zamo misali ga wasu haka kuma a rayuwar sarki 72 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI lafayis babu abin da yake so sama da labaru da abubuwan ban dariya. Don haka in dai mutum ya iya barkwanci ko kuma ya iya abin dariya to lallai zai samu kusanci sosai da sarki lafayis kuma zai rinqa samun kyautar dukiya mai yawan gaske. Wata rana sai sarki lafayis ya sami labarin wani gari da yake can qarshen iyakar nahiyarsu da nahiyar qasashen nasara wanda ake kira da suna madhuzar. Shi dai wannan birni na madhuzar sabon birni ne wanda fatake suka qiriqire shi asali ma ba a san ko a qarqashin wacce qasa yake ba, akwai ni’ima ta ruwa da yabanya a wajen shi yasa fatake suka zavi wurin amatsayin masauki rabin mutanen dake zaune a birnin nasara ne rabin su kuma larabawa saboda zaman lafiyan da ake yi tsakanin qabilun biyu da kuma 73 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI harkar cinikaiya sai aure ya rinqa qulluwa a tsakaninsu suka rinqa haihuwar kyawawan mata masu kyawun launin fata gami da kwari da kuma jarumta mazansu da matansu duk kyawawa ne na gaban kwatance. Babban abin da zai xaure wa mutum kai shi ne babu wani bambanci kowa yana da ikon yayi irin addininsa da yake so babu mai hana shi, shugabanci birnin a qarqashin qabilu biyu yake babu sarki a garin amma kowace qabila tana da wakili a majalisar garin kuma wakilai a majalisar garin kuma wakilai bakwai ne sannan duk matsayinsu xaya babu wanda yafi wani. Kawai dai waxannan shugabanin su goma sha huxu su ne suke zartar da doka shari’a

Chapter 2 of 3