Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI HIKAYOYIN AL’AJABI Abudulaziz Madakin Gini 1 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI 2 HIKAYOYIN AL’AJABI A MADAKI BABI NA XAYA wani zamani can baya mai tsawo an yi wani mashahurin sarki a birnin Hindu wanda Allah ya albakace shi da tarin dukiya, tarin ‘ya ‘ya mata. Girman qasa da qarfin mulki. Komai na jin daxin duniya babu abinda wannan sarki mai suna Ram ya rasa, a duniya babu abinda wannan sarkin yake tsoro sama da mutuwa, don haka wannan zamani masana sun tabbatar da cewa babu wani sarki da yake da tsoro sama da shi a duniya. A cikin gidan sarautarsa dakaru na bil’adama miliyan xaya ne ke gadinsa, gami da dakarun aljanu guda miliyan biyu yana da likitoci masu kula da lafiyarsa, guda ashirin da uku, kuma duk abin da zai ci ko zai 3 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI sha sai bokansa ya duba shi yayi bincike ya tabbatar da cewa abin ba zai tava cutar da shi ba. Sarki Ram baya yarda yayi tafiya da ta wuce tsawon rabin sa’a kuma duk inda zai je komai rashin nisan wajen sai dakaru tsoronsa sun raka shi suna masu sashi a tsakiya, aljanu na shawagi a samansa don tabbatar da tsoro. A rayuwar sarki Ram bai yarda da kowa ba, hatta matarsa da ‘ya ‘yansa kuwa ko ruwan sha baya yarda so bashi,yasha face bokansa ya duba shi kuma ko jima’i zai yi da matarsa sai bokansa na zaune a qofar xakin saboda kada matar tasa ta cutar dashi. Ana cikin wannan halin ne watarana kwatsam sai wata cuta ta kama sarki Ram wadda shi kansa 4 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Bokan nasa ya kasa gano maqasudinta da yanayinta, haka ma likitocinsa yanayin cutar shi ne haka kawai sai ransa ya vaci, ya zare takobi ya yi ta saran hadimansa da dakarunsa, tamkar wanda ya zautu. Dole sai an riqe shi da qarfin tsiya, an kwance takobi an bashi wani magani yasha sannan hankalinsa ke dawowa cikin jikinsa amma rabin sa’a na yi sai ciwon haukan ya dawo. Bisa dole aka hana matan sarki da iyalinsa kusantarsa, amma kuma a kullum a cikin rusa kuka yake saboda an hana shi yin tarayya da matan nasa, bisa wannan dalilin ne Bokan ya matsa da bincike ya gano cewa dole sai an samo wa sarki Ram sabuwar amarya kuma kyakkyawar budurwa masaniyar labarai na ban al’ajabi, tana kusantarsa a kowane 5 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI dare sannan sarki Ram zai daina wannan cuta ta hauka. Akan wannan dalilin ne aka baza shela ana neman budurwa da zata iya wannan aikin mai haxari wanda ta san cewa idan ta kasa gamsar da sarki Ram da dadaxan labaranta kashe ta zai yi. Nan fa aka yi ta cigiyar har tsawon wata uku da qyar aka sami wata budurwa mai suna Nasmirat tace zata iya wannan aikin. Nasmirat bata da uwa kuma ubanta makaho ne kullum sai tayi masa jagora sun yi bara a cikin gari sannan suke samun abin da za su ci, domin talakawa ne fitik! Maqasqanta amma kuma ta kasance kyakkyawar gaske, mahaifinnanta ba shi da kowa a duniya sai ita kaxai,basu da gidan kwana sai a runfunar kasuwa sai dai su shiga daji. 6 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Lokaci da makaho Marhat mahaifin Nasmira ya ji cewa ‘yarsa zata auri sarki bisa wannan sharaxi sai ya fashe da kuka ya ce “Idan kika je mutuwa za ki yi, idan na rasaki wa zai ci gaba da kula da ni?” Koda jin haka sai hawaye ya zubowa Nasmirat ta dafa kafaxarsa “Ka kwantar da hankalinka ya kai Abbana ka yi sani cewa ina da waxansu labarai na hikayoyi masu ban al’ajabi waxanda lallai za su iya magance wannan cuta ta sarki, ka tuna cewa idan na auri sarki zan siya maka gida mai daraja da tsada, a garin nan kuma shi ken an ka daina bara, har abada abinda nake so da kai kawai shi ne ka taya ni da addu’a”. Koda jin haka sai marhat ya rungume Nasmirat yace “Ya ke ‘yarta ki yi sani cewa rayuwarki da farin cikinki ya fiye mini komai a cikin 7 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI wannan duniyar, da dai na samu gida da dukiya koda ta kai cikin garin nan gwara na ci gaba da kwana a kasuwa ina bara a titi muddin za ki rasa rayuwarki, ko farin cikinki ki tuna cewa fa ni girma ya kamani, ina nufin tsufa ya riske ni, abu ne mawuya ci na daxe nan gaba, ke kuwa yanzu ne za ki fara shirya rayuwarki ta gaba,idan kika sami matsala tun a farko to fa abu ne mawuyacin komai na ki ya tafi daidai. Sa’adda Marhat ya zo nan a zancensa sai Nasmirat ta janye jikinta daga cikin nasa sannan ta ruqe kafaxunsa da hannayenta biyu ta dube shi cikin murmushi tace. “Na yi maka alqawarin babu abin da zai same ni kuma sai suna na ya shahara sosai a wannan nahiya gaba xaya, ba mai wai a garin nan ba”. Koda jin haka sai marhat ya gyaxa kai cikin alamun karayar zuciya 8 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI yace “Haba yake ‘ya ta yaushe wannan mafarkin na ki zai zama gaskiya? Ni dai kawai bazan hanaki jarraba sa’arki ba amma dai hankalina ba zai tava kwanciya ba, face na ga kin auri wannan sarki na mu da tsawon watanni kin rayu”. Koda jin haka sai Nasmirat ta kama tsohon Marhat ta kwantar da shi akan shimfixarsa a cikin rumfar kasuwar sannan ta janyo mayafinsa ta lulluve shi sakamakon sanyi da ake busawa a cikin dare. Gama haka ke da wuya sai itama ta je ta kwanta a kan shimfixarta ta janyo mayafi da nufin ta lulluva sai ta hango dakarun gidan sarki kimanin su goma gami da wata kuyanga sun shigo cikin kasuwar kuma sun durfafo inda suke. A firgice Nasmirat ta miqe tsaye, shi ma marhat ya miqe tsaye 9 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI lokacin daya ji motsin takon sawayen dakarun sai ya miqe zaune zumbur a tsorace, ya fara kiran Nasmirat yana cewa “Ya ta su waye suka durfafo mu ina fatan dai ba irin ‘yan iskan nan ba ne da suka tava zuwa domin su yi miki fyaxe, masu gadin kasuwa nan suka cece ki?” Nasmirat tace “A’a Abba basu bane waxannan dakarun gidan sarki ne”. Koda jin haka sai marhata ya miqe tsaye a firgice ya kamo hannun Nasmirat ya damqe da kyau, yace. ‘Ina fatan dai ba wani laifi muka yi musu ba?” Kafin Nasmirat ta qara cewa wani abu tuni dakarun da wanan kuyangar sun iso daf da su, kawai sai kuyangar ta dubi Nasmirat cikin murmushi tace. 10 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI ‘To yarinya mai sa’a ki yi sani cewa gobe ne za a xaura aurenki da sarki bisa wannan dalilin ne sarki ya bayar da umarnin a xauke ku daga nan akai ku can sabon gidan daya baiwa mahaifinki kyauta”. A cikin gidan akwai komai babu abin da zaku buqata a can ne za a yi miki kwaliyar amarya kuma da magariba za a kai ki wajen angonki”. Koda jin wannan batun sai Nasmirat ta kamu da tsananin farin ciki shi kuma Marhat sai hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe. Nan da aka ga waxansu haimai na gidan sarki sun qaraso da keken doki batare da vata wani lokaci ba aka sanya Nasmirat da mahaifinta a cikin keken dokin aka tafi da su izuwa wannan sabon gidan da sarki ya basu dakaru na take musu baya tamkar sun kasance jinin sarauta. 11 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Gaba xaya sauran almajirai dake kwana a cikin rumfuna kasuwa sai suka tashi daga barci suka bisu da kallo kawai suna matuqar mamakin yadda aka yi wannan xaukaka ta zowa Nasmirat da mahaifinta a dare xaya. Mutane da basu da kuxi siyan doki su hau yau ga su a cikin keken dokin ma sun kame ana jansu. To dama masu iya magana sun ce dare xaya Allah kan yi bature wannan fa shi ne Allah ya yi aure da mara kwabo. 12 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI BABI NA BIYU A she lokacin da wannan kuyangar ke faxawa Nasmirat cewa gobe ne za a xaura mata aure da sarki wasu daga cikin ‘yan uwanta almajirai sun ji nan da nan kuwa labari ya cika birnin Hindu ya zamana cewa duk inda ka gifta sai di ka ji ana tsagegumi ana faxin cewa gobe sarki zai auri ‘yar almajiri marhat. Aikuwa sai kowa ya rinqa faxin albarkacin bakinsa, wasu su kushe wasu su yaba wasu ma sai suka rinqa cewa ai talauci ne yasa Nasmirat ta siyar da rayuwarta domin ubanta ya amfana tunda dai ta tabbatar da cewa ita mutuwa za ta yi. Lokacin da keken dokin su Nasmirat ya iso qofar gidan da aka basu suka yi arba da gidan sai 13 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Nasmirat ta kamu da tsananin mamaki domin gaba xaya birnin in banda gidan sarauta babu wani gida mai kyansa. Koda ganin haka sai hawaye ya zubowa Nasirat saboda tsananin farin ciki ta kama hannun mahaifinta suka sauko daga cikin keken dokin a ka yi musu jagora izuwa cikin gidan da shigarsu cikin gidan sai Nasmirat taga yadda aka qawata shi ainun aka shirya aljannar duniya, a cikinsa sai ta sake kamuwa da matuqar farin ciki mara misaltuwa bata san sa’adda ta fashe da kuka ba. Al’amarin da ya razana mahaifinta Marhat kenan ya damqe hannunta da kyau kuma ya janyo ta izuwa kan qirjinsa yace. “Ki kwantar da hankalinki yake ‘yata na sani cewa tsananin farin ciki ne ya saki wannan kuka gami da takaicin cewa ba ni da idanu bare 14 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI naga wannan daula da muka samu kanmu, to ki sani cewa ni farin cikina guda xaya ne kawai cewa ko a yau na mutu naga yadda qarshen ‘yarta ya yi kyau. Ko a mafarki ban tava zaton cewa zamu tsinci kanmu a cikin irin wannan daula ba, tabbas mai rai baya fidda rabo. Haka dai aka yi ta kewayawa da su Nasirat a cikin gidan har sai da suka gama ganin ko ina duk inda suka shiga sai sun ga bayi, kuyangi da hadimai suna ta gabatar da aikaceaikace su, tamkar a haka za su shuxe, har izuwa qarshen rayuwarsu. Bayan hadiman da suka kawo su sun tafi sai hadiman gidan suka kawo wa Nasmirat da mahaifinta abinci mai rai da lafiya suka kimtsa cikinsu suka yi hani’an da yake dare ne sosai sai Nasmirat ta yi gyaran murya. 15 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Take wata kuyanga dake tsaye a bakin qofar falon da suke ta rugo da gudu ta zube a qasa gabanta bisa gwiyoyinta tace. “Ya shugabata me kike da buqata?” Koda jin wannan tambaya sai Nasmirat ta ji kamar kanta zai fashe wai yau ita ake kira da shugaba alhalin ta kasance ‘yar almajiri mai bara a titi kuma mai kwana a kasuwar rumfa. Cikin murna da annushuwa Nasmirat ta dubi kuyangarta tace. “Ina son ki raka Abbana izuwa xakin barcinsa, bayan nan kuma ina so ki faxa wa gaba xaya hadiman gidan nan su je su kwanta su yi barci tunda yanzu mun gama samun nutsuwa, ni da mahaifina sai gobe da safe ku zo gaba xayan ku ina son yin magana da ku”. 16 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Koda jin haka sai kuyangar tace “An gama ya shugabata”. Nan take kuyanga ta miqe tsaye sannan ta kama hannun tsoho marhat ya tashi tsaye sannan suka fice daga falon. Fitarsu ke da wuya sai Nasmirat ta miqe tsaye ta shige cikin qurya turakar inda tayi arba da wanni fankacecen gado tun data ke a rayuwa bata tava ganin shimfixa kamar wannan ba tun tana qarama har kawo yanzu data girma ta zama cikakkiyar budurwa. Samari da dama gami da dattijan banza sun sha nuna mata kuxi domin su yi lalata da ita amma bata yarda, sau goma sha xaya ana yinqurin yi mata fyaxe Allah na kareta, wannan rayuwa da take ciki ta jefa ta cikin matsanancin tsoro da damuwa, don haka a yanzu da sarki yasa aka 17 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI kilace su aka kawo su, cikin wannan gidan sai ta tsinci kanta a cikin nutsuwa da farin ciki mara misaltuwa. Matsalarta kawai shi ne yadda zata kare kanta a wajen sarki Ram ta rinqa ba shi daddaxan labarai da za su gusar masu da ciwonsa na hauka batare da ya kashe taba. Dogaron Nasmirat xaya ne, akwai wata rana da ta shiga cikin daji domin ta kawar da buqatarta a lokacin dama sun zo giftawa ta bayan gari ita da mahaifin nata marhat. Koda ta ji bawali ya mats eta sai ta sanar da shi, cikin kaxuwa yace. “Yake ‘yarta kin gaya mini cewa yanzu muna bayan gari ne,vangaren dajin husur kin sani cewa yaune ranar farko da muka tava zuwa wannan vangaren a yawon bararmu don haka ba mu san haxarin da ke wajen ba kuma gashi nan inda muke 18 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI tsaye kan hanya ne mutane na xan giftawa lokaci bayan lokaci,kinga ashe ba za ki iya kawar da laruraki ba anan xin, ki shiga cikin wannan dajin ki nemi inda ya dace amma dai ki yi taka tsantsan kuma ki kula da kanki sosai ko yaya kika ga wani abu wanda baki yarda da shi ba ki juyo da baya da gudu izuwa nan, inda nake mu gudu tare. Koda tsoho marhat ya zo nan a zancensa sai Nasmirat tace “Babu komai ya kai Abbana ka jira ni anan kada ka damu koda ka ga na xan vata lokaci saboda dole sai na ga inda ya dace na kawar da buqatar tawa”. Marhat yace “Babu komai kije ‘ya ta mai girma saljil zai kare ki”. Saljin gunki ne na wata giwa wanda shi ne abin bautar zuri’ar su tsohon marhat wannan addini nasu 19 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI yana daga cikin addinai na farko a birnin Hindu. Ba tare da vata wani lokaci ba kuwa Nasmirat ta bar tsoho marhat a bakin hanya ya sami wuri ya zauna, ita kuma sai ta kunna kai izuwa cikin daji. Abin ka da wadda dama ta saba shiga cikin daji ko alamar tsoro babu a tare da ita har ta yi ‘yar doguwar tafiya kaxan, kawai sai ta hango wani qaton kogon dutse wanda qofar shigarsa duk ta lulluve da yana tamkar fiye shekaru arba’in ba wata halitta bata shige shi ba. Al’amarin da ya yi matuqar baiwa Nasmirat mamaki ke nan tace a cikin ranta “Mene ne dalilin da yasa fatake ko dabobi ko waxansu mugayen mutane basa shiga cikin wannan kogon dutse don fakewa ko vuya? Amsar ta kasa baiwa kanta ke 20 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI nan kawai sai ta aiyana a cikin ranta cewa za ta zagaya bayan wannan kogon dutse domin ta yi bawalinta. Koda ta zo giftawa tab akin qofar kogon sai ta ji an kirawo sunanta daga ciki. Take hantar cikin Nasmirat ta kaxa, ta kamu da tsananin tsoro ta yunqura da nufin ta falfala da gudu da baya kawai sai ta ga an toshe hanyar da qaton dutse. A firgice ta sake juyowa da baya don ta koma inda ta fito nan ma sai taga an toshe hanyar da wani dutse. Kafin ta yi wani yunquri sai taga gaba xaya yanar da ta lulluve qofar gogon ta vace vat tamkar bata tava wanzuwa ba a wajen sai ga wata mace tsohuwa tukuf gashin kanta ya zama fari sol saboda tsufa, kuma tana sanyi da farare tufafi tana dogara farar sanda ta fito daga cikin kogon dutsen. 21 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Koda Nasmirat ta yi arba da wannan tsohuwar sai ta kamu da tsananin mamaki, ba komai ne ya sata wannan mamaki ba face ta san wannan tsuhuwar sosai, ana kiran wannan tsohuwar da suna jarisa, kuma itama almajira ce wajen kjwanansu xaya a kasuwa kuma duk inda Nasmirat da mahaifinta suka je bara sai sun ganta a wajen koda kuwa sun baro ta a can baya. Hakan tasa suka fara tsorata da ita suna zargin ko aljana ce, amma da yake tun kafin a haifi Nasmirat tsohuwa jarisa ke rayuwa a cikin almajiran kasuwa kuma ba a tava ganinta cutar da wani ba sai ba a damu ba duk da cewa kuwa babu wanda yasan asalinta ko daga inda ta fito. Lokacin da Nasmirat ta yi arba da tsohuwa jarisa sai jikinta ya 22 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI kama tsuma saboda tsananin tsoro ta qura mata idanu,kuma ta kasa motsawa ko da taku guda, walau gaba ko baya. Koda ganin haka sai tsohuwa jarisa ta dub eta cikin murmushi tace “Haba yake Nasmirat tun fa kina cikin mahaifiyarki nake tare dake, in da so nake na cutar da ke ai da tun a asannan zan cuce ki, a gaban idanuna aka haife ki har kika girma a matsayin marainiya mara uwa har kawo iyanzu yau ne ranar da za ki san ko ni wacece, da kuma dalilin da yasa nake ta bibiyarku, tun kina cikin mahaifiyarki. Ki kwantar da hankalinki na rantse da darajar uwata da ubana ba zan tava cutar da ke ba, ki sani cewa sau goma sha huxu ina kare mutuncinki daga sharrin mugayen mazajen dake kawo miki harin fyaxe. 23 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Tun kina jaririya nake kare lafiyarki da rayuwarki, idan baki manta ba kimanin watanni shida baya kin yi arba da wata qatuwar baqar macijiya a bayan gonakin nan na cikin gari inda macijiyar ta taso miki da nufin ta kashe ki a bakin qoramar salbil amma sai wani kada ya taso sama daga qarqashin ruwa ya afka wa macijiyar suka yi baqin gumurzu daga qarshe sai kadar ya sami nasarar kashe macijiyar to ba wani bane wannan face ni xin nan”. Koda jarisa ta zo nan a zaucenta sai Nasmirat ta kamu da tsananin mamaki kuma ta qara tsorata ainun ta dubi jarisa tace “To wai shin ke wacece? Shin kin kasance bil’adama mai qarfin sihirin tsafi ko kuwa ke aljana ce?” Koda jin wannan tambaya sai tsohuwa jarisa ta bushe da dariya 24 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI sannan ta dubi Nasmirat tace “Biyo ni muje cikin kogon dutsen nan na baki ajiyar da kakarki ta wajen uwa ta barmin domin ke kaxai jal”. A cikin wannan duniya sai na damqa miki wannan ajiya sannan zan sanar dake komai akaina, da kuma dangantakata da kakarta ki”. Koda gama faxin hakan sai tsohuwa jarisa ta juya ta nufi cikin kogon dutsen tana dogara farar sandarta, cikin alamun tsoro da xarixari Nasmirat ta bi jarisa a baya tana kalle-kalle da waige-waige a cikin kogon dutsen kamar kace kyat ta fita da gudu. 25 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI BABI NA UKU Sai da suka yi doguwar tafiya ta kimanin daqiqa xari tara da saba’in da uku sannan suka iso wata qatuwar fada wacce kana ganinta kasan cewa ba fada bace irin ta mutane sai dai aljanu domin komai na cikinta girmansa ya wuce na bil’adama haka ma kamaninsa da yanayinsa. Babu komai a cikin fadar face wata qatuwar karagar mulki sai gumaka na dakarun yaqi masu siffofin iri-iri na ban al’ajabi da ban tsoro wasu dakarun jikinsu na za ki ne, amma kawunansu da hannayensu na aljanu wasu kuma sai ka ga rabinsu bil’adama rabinsu kuma na aljanu sama da qasa. 26 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Kai wasu ma tsagin rabin jikinsu ne daban-daban wasu kuma jikinsu na bil’adama ne amma kawunansu na dabbobi, dukkaninsu suna riqe da muggan kayan yaqi kuma sun kewaye qatuwar karagar mulkin dake fadar. A gaban karagar mulkin akwai wata farar akwatin qarfe wacce ke rufe kuma babu alamar murfi a jikinta ko kuba wacce za a iya buxe ta. Tsohuwa jarisa ta ci gaba da tafiya tana ratsa wa ta tsakiyar miliyoyin waxannan dakarun yaqin ta tunkari inda wannan farar akwatin take cikin tsananin firgici Nasmirat ta bi bayan jarisa tana kallon dakarun a firgice saboda gani take kamar a koyaushe za su iya zama masu rai su halakata. Koda jarisa tai so inda farar akwatin take ta dafata da sandarta sai 27 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI gaba xaya dakarun tsaron suka zama masu rai kowannansu ya yunqura ya zare takobinsa. Sai suka yi ca izuwa kan tsohuwa jarisa za su ragargazata sai ta yi wuf ta xauke sandarta daga kan akwatin take gaba xayan dakarun suka koma da baya kowannansu ya tsaya cak! A inda yake da ya zama gunki. A daidai wannan lokaci ne tsohuwa jarisa ta waigo ta dubi Nasmirat tace duk faxin duniyar nan kece kaxai za ki iya buxe wannan akwatin ki xauko ajiyar ciki wacce kakarki ta bar miki duk wanda yayi gangancin buxewa savanin ke ko da ni ce kuwa sai waxannan dakarun sun hallaka shi. Da farko yanzu sai ki je ki buxe akwatin ki xauko abin dake ciki sannan na yi miki bayanin komai. 28 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Koda jin wannan batu sai Nasmirat ta dubi tsohuwa jarisa cikin alamun fushi tace “Ta yaya za ki ce na je na buxe akwatin da bata da murfin ko mabuxi”. Koda jin wannan tambaya sai jarisa ta yi murmushi cikin lokaci guda kuma sai ta murtuke fuskarta ta dubeta a fusace tace “Xiga xigon jininki akan akwatin”. Koda jin wannan batu sai Nasmirat ta rikice kuma ta ximauce ta kasa koda motsawa daga inda take koda ganin haka sai tsohuwa jarisa ta yi wuf ta kamo hannu Nasmirat tasa farce hannunta ta yanke xanyatsanta guda sannan ta jata izuwa kan akwatin. Koda jinin Nasmirat ya xaga akan wannan farar akwatin sai akwatin ta buxe tamkar an buxe tsakiya littafi babu komai a cikin akwatin face wani xanqaramin jan littafi akan bangon 29 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI littafin an yi rubutu da baqar tawada mai kauri kamar haka HIKAYOYIN AL’AJABI shi dai wannan bango littafin an yi shi ne daga dutsen zinare, rubutun kuwa da baqin dutsen lu’u lu’u aka yi shi sai sheqi da walwali littafin yake yi. Nasmirat bata san sa’adda sha’awar littafin ta kamata ba ta zura hannayenta biyu cikin akwatin ta xauko littafin. Koda ta fito da littafin daga cikin wannan farar akwatin sai gaba xaya gumakan dakarun suka kama tsattsewa suna rushewa tamkar an tsoma alli a cikin ruwa. Nan da nan gaba xayansu suka rugurguje xayansu bai tsira ba. Al’amarin da ya matuqar baiwa Nasmirat mamaki kenan ita kuwa tsohuwa jarisa sai ta bushe da dariya farin ciki har da qyaqyatawa 30 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI kuma nan take ta rikixe ainahin sufarta ta aljana ta buxe fukafukanta ta tashi sama tana shawagi a sama Nasmirat tana mai ci gaba da qyalqyala dariyar murna daga can kuma sai ta sauko qasa ta fuskanci Nasmirat har a sannan bata daina kallon littafin dake hannunta ba cikin matuqar al’ajabi. Koda taga jarisa ta dira a gabanta sai tax ago kai ta dubeta tace “Yake wannan aljana mene ne dalilin wannan farin ciki naki haka? Me ximbin yawa?” Koda jin wannan tambaya sai aljana jarisa tace “Ba komai ne ya jefa ni cikin wannan farin ciki ba face sai yanzun nan na sami ‘yanci da zan daina zama tare dake, da kuma tsare wannan littafi na tsawon shekaru ashirin tun kafin a haife ki,kamar 31 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI yadda na gaya miki da farko zan yi miki bayanin komai yanzu. Kakanki na wajen uwa shi ne mutumin da yafi kowa sanin labarai na ban al’ajabi waxanda suka faru a ko ina cikin wannan duniya, domin sai da ya yi shekaru xari da biyar yana binciko ire-iren waxannan labarai a cikin madubin tsafinsa. Don haka duk inda wani abin al’ajabi ya faru a duniya a ko ina sai ya ganshi sannan ya zauna ya rubuce labaran da qarfin sihirin tsafi a cikin kwanaki casa’in da tara da ya kammala wannan aikin ne ya gyara littafin sosai ya san ya shi a cikin wannan bangon na zinare da lu’u lu’u ya kawoshi nan kogon dutsen ya adana a cikin akwatin nan. Bisa binciken daya yi duk wanda ya karance gaba xaya labaran dake cikin wannan littafin walau a fili 32 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI ko a cikin ransa sai ya samu mulki gami da xaukaka da babu wani mahaluki da zai iya samun kamarsa face shi xin ya bar duniya. Koda ya gano hakan sai ya sana’anta wannan farar akwatin wacce bata da murfi ko mabuxi yayi ta yadda babu abinda zai iya buxeta face xigon jininsa ko na zuri’arsa. Ya sani cewa kece kaxai kika rage a cikin zuri’arsa don haka saboda ke kaxai ya adana wannan littafin. Ya ke wannan yarinya me sa’a kiyi sani cewa akwai labarai na ban al’ajabi guda dubu biyu da xari biyu da ashirin a cikin wannan littafin kuma a kullum za ki iya karanta kowane labari kina gama karance labaran su zauna a cikin qwaqwalwarki tamkar akan takarda aka rubuta da alqalami. Karanta sun kuwa zai xauke tsawon daqiqa casa’in da tara ne kacal 33 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI idan kina shakka ko yanzu za ki iya jarrabawa. Koda jin wannan batu sai Nasimat ta qyalqyale da dariya tace, “Ai kuwa in dai haka ne wannan kakan nawa ya cika babban matsafin da babu kamarsa a wannan zamani. Aljana jarisa tace “Ai dama hakanne kuma kece kaxai za ki iya gadarsa sirrin wannan littafi shi ne kada ki kuskura ki karanta shi a gaban wani mahaluki face idan kin kaxaita ke kaxai a cikin xakin ki na barci, don haka dole ne ki kasance kina mai ci gaba da voye littafi a cikin wannan akwati ya zamana cewa kullum kina karantashi sau xaya har sai kin shafe kwanaki xari uku da sittin kullum kina karanta labarai bakwai sannan ki kammala shi. 34 HIKAYOYIN AL’AJABI MADAKI Koda jin wannan batu sai hankalin Nasmirat ya dugunzuma ainun tace. “Ta yaya zan iya voye wannan littafi da wannan akwatin ba tare da kowa ya gani ba, kuma yanzu kina nufin cewa kullum idan ina son na buxe wannan akwatin sai na yanke jikina jikina na xiga jinina a kanta?”. Aljana jarisa tace “Shakka babu sai kin yi haka amma akwai abin da za ki iya ki sami babban sirri a cikin al’amarin yadda babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai

Chapter 1 of 3