Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
" Ya na gama fadar haka ya sa kai ya fice shi ma Cen ya hango Zayd har ya yi nisa da tafiyar shi Da sauri ya fara takawa har ya kamo shi dai'dai ya karaso kofar gidan su Inaya Su na karasowa wajen Abdoul da malam su ka fito da sauri kamar sun ga wani abun gudu Da sauri Moussa ya taro su ya na cewa " Abdoul ina za ku je haka da sauri wani abu ya faru " Abdoul na shirin magana malam ya riga shi cewa " Inaya ce ba ta cikin gidan nan ban San inda ta yi ba " Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " ku kontar da hankalin ku , yanzu nan mu ka baro ta gidan mu, kar ku damu ba abun da ya same ta " wata nanauyar Ajiyar zuciya malam da Abdoul su ka sauke a tare " uncle kun san da yarinyar nan ta na da wanda ta ke so " su ka tsinci Muryar Zayd ya na fada Kallon juna Abdoul da malam su ka yi kafin su kali Zayd har su na hada baki wajen cewa " ita da kanta ta fada maka hakan ? " Jinjina musu kai a hankali ya yi bai ce komai ba Dan murmushi malam ya yi sannan ya ce " yo ai wannan ba matsala ba ce dan..... " Da sauri Zayd ya katse shi da cewa " kamar ya ba matsala ba ce ? no uncle tun da ta na da wanda ta ke so ni zan nemo shi in aura mata shi da kai na , baza ta ji dadin zama da mutuman da ba ta so , a karancin shekarun nan na ta bai kama ta ta shiga cikin irin wannan kunci ba , dama ni ta yi min karama sosai " bai jira amsar malam ba ya juya ya bar wajen Sai da ya bar wajen sannan malam ya kali Moussa ya ce " wai maganar me ya ke yi ne haka ? " Dan karamin murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " wai zai saki babyn malam tun da ta ce ta na da wanda ta ke so ya aura mata shi , ku kyale shi yayi ta neman kan shi har ya gaji , zan koma gida sai da safe " ya juya ya bar wajen Da sauri Abdoul ya yi shirin bin bayan shi, amma malam ya riko hannun shi ya ce " nassan auta ce za ka je daukowa kyale ta, da safe ta dawo da kan ta " Jinjina mishi kai Abdoul ya yi sannan ya juya ya koma cikin gidan malam ya bi bayan shi Da sallama su ka shigo cikin gidan a tare Da sauri Nesrine da ke konce ta tada kai da cinyar mama ta na kuka, ta tasso ta tarbo malam cikin kukan ta ke cewa " Abba ina Inaya ta yi ne " Dan murmushi yayi kafin ya ce " kontar da hankalin ki, ta na gidan mijin ta " Dan zaro idanu ta yi ta na maimaita kalmar miji cikin ranta Ta geffen ta malam ya raba ya wuce ya karaso inda mama ke zaune shi ma ya zauna Shi kuma Abdoul ya wuce bedroom din shi Ya na zama Nesrine ta juyo da sauri ta nufo malam ta zo gaban shi ta tsaya ta ce " Abba wane mijin kuma, Abba Inaya fa shekarun ta 14 ina ta kai aure ko period fa ba ta fara ba " duk cikin kukan ta ke mishi wannan maganar ta ma manta da mahaifin ta ta ke magana Malam na shirin magana mama ta riga shi cewa " yanzu dan Allah malam ina Inaya ta isa aure me ma ta sani a kai , ka hada ta da wanda ba mu san shi ba , wanda ba son shi ta ke ba yanzu in ya je ya cutar mana da ita da wane za muji malam bibiyar da ake mana ko wannan " ta kai karshen ta na sakin kuka Da sauri Nesrine ta karaso wajen ta ta Zube saman guyiwowin ta ta rungume mama ita ma ta na sakin kuka ( shi kukan kawai dan an yi mata aure ne πŸ€”πŸ€”????? ) " yanzu Amina ya ki ke son na yi kin fi son na saka ido wancen yaron ya gano inda muke ya zo ya dauke mana ita, kuma na fada miki auren ya yi wajen shekara biyu yanzu , kuma ta na son mijin na ta , dan ni da kai na na tambaye ta in ta na son shi , ku yanzu a tunanin ku in Sudais ya gano inda muke ba sai ta fi shiga cikin matsa la ba dan Allah ku kontar da hankalin ba abun da zai faru da ita " ya kai karshen ya na kai hannun shi saman kafadar mama A hankali mama ta dago da ga jikin Nesrine ta kali malam ta ce " shikenan na ji abun ka fada amma ba ka fada min wanene wanda ka aura mata " Jinjina kan shi ya yi kadan sannan ya ce " ba kowa ba ne face Zayd " A dubu dari Nesrine ta mike tsaye ta na fadin " Zayd ???? " da karfi ta na zaro idanu, yanzu mutumin da ko hanya ba ta fatan ta hada su wai shi ne mijin kanwar ta, mutumin da ko gani ba ya yi kamm akwai ta " e Zayd , wanda ke zowa gidan nan wanda ku ke ma kallon makaho da kurma shi din dai " malam ya fada ya na kallon ta Cikin bacin rai mama ta ce " haba malam, wannan makaho ta ya zai iya kare mana yarinyar mu , ko shi ta kan shi ya ke , ya zai kula da ita, inda ma abokin shi Moussa ne da sauki amma Zayd ? " Mikewa tsaye malam ya yi cikin bacin rai ya ce " bara ku ji aure dai an riga da an aura kuma ba zai sake ta ba in kun ga dama ku karbe shi in kun ki ku ta matsewa " Ya na gama fadar haka ya kama hanyar dakin shi ya shige ya bar su nan zaune Juya wa ita ma Nesrine ta yi ta koma dakin ta da gudu ta na sakin sabon kuka Ita ma mama ta juya ta koma dakin ta zuciya ba dadi Duk abun da su ke Abdoul na jin su amma ya yi banza da su ya yi konciyar shi Zayd Bayan ya koma gida kai tsaye bedroom din shi ya wuce, ga Dukan allamu ya manta da Inaya da ke cikin gidan Shi ma Moussa ya na shigo wa ya wuce kai tsaye cikin falo A tunanin shi ta na nan amma da ya shigo ya ga ba kowa a cikin falon Da sauri ya juya ya fita falon ya koma wajen da su ka baro ta Ta na nan kamar yadda ya baro ta , amma ta daina kuka sai ajiyar zuciya ta ke saukewa a hankali allamun ta yi barci Dan murmushi yayi kafin ya juya ya koma cikin gidan a hankali Kai tsaye bedroom din Zayd ya wuce Sai da ya yi mishi knocking sannan ya shiga dakin ya na sallama Ya na zaune saman gadon shi ya jingina a bayan gadon ga computer a gaban shi , ya cire wadanan glass din na shi na gado Karasowa wajen shi Moussa ya yi ya tsaya gaban shi ya ce " Amir don Allah je ka dauko babyn malam ta yi barci a wajen motar " Ba tare da ya dago kai ba ya ce " kai me ya hana ka dauko ta ? " Hararrar shi Moussa ya yi kafin ya ce " Amir ban San rainin sens ka fi kowa sani ba muharama ta ba ce bazan iya dauko ta ba , dan haka malam tashi ka je ka dauko matar ka " Dago kai Zayd ya yi ya wurga ma Moussa wani mugun kallo Shi Moussa dariya ma abun ya bashi dama da gangan ya ki dauko ta , ya zo ya tada shi ya je ya dauko ta Wani file da ke geffen shi Zayd ya doko ya tila wa Moussa Da sauri Moussa ya kwace gefe ya na dariya ya ce " to malam da ga taimako na ga dai matar ka ce ba tawa ba in ka ga dama ka bar ta a cen ta mutu " Ya na gama fadar haka ya juya ya fice dakin ya shiga bedroom din shi ya na dariya Dan kauda kai gefe Zayd ya yi ya na jan tsaki a fili ya ce " wlh sai na yi maganin ka, jarabbabe kawai " Ya na gama fadar haka ya ajiye computer din geffen shi sannan ya sauko da ga saman gadon ya fito dakin Kai tsaye parking space ya nufa inda su ka baro ta Ya na zuwa bai tsaya wani dogon tunani ba ya sa hannayan shi biyu ya dauke ta cak kamar baby ya koma cikin gidan da ita Maimakon ya wuce bedroom din shi da ita sai ya kontar da ita saman doguwar sofa sannan ya juya ya koma bedroom din shi ya ci gaba da aikin shi β–ͺWashe gari β–ͺInaya Washe gari ba ta farka da ga barcin wahalar ta ba sai wajen karfe 10 na safe, ko da ta farka ta ga ba motsin kowa a cikin gidan allamun sun fita Jin hakan ya sa ta mikewa ta fara takawa ta bar falon ta fito harabar gidan Abun mamaki babu motar nan a cikin gidan, to ta ina ta fita ? (Ko ni wannan tambayar ta tsaya min a rai , ta ina motar nan ke shigowa bare har ta fita ) Ganin ba ta da me ba ta amsa kawai sai ta sa kai ta bar gidan baki daya ta koma gidan su A hankali ta ke tafiya kamar wadda a ka zarewa lakar jiki har ta karaso gidan su Bakin ta dauke da sallama ta shigo gidan A hankali mama ta dago kan ta, ta amsa mata sallamar ta Ganin ita ce ya sa mama sakin wani dan murmushi ta ce " Auta zo nan ina son magana da ke " Ba musu ta tako a hankali ta zo geffen mama ta zauna ta na sunkuyar da kai ta na gaishe ta Sai da mama ta amsa mata gaisuwar ta sannan ta ce " Auta a ina ki ka kwana ? " Ba tare da ta dago kai ba ta ce " gidan su yaya Moussa " ta fada a takaice Jinjina kan ta mama ta yi kafin ta ce " Auta fada min gaskia ki na son Zayd a yadda ya ke hakan ? " Sai da ta dan doki lokacin kafin ta dago kan ta slowly ta ce " shin mama ko ina son shi ai yanzu lokaci ya kure, Abba ya aura min wani cen daban wanda ban sani ba , ba na kuma so , ni gaskiya ba a yi min adalci ba " ta kai karshen kuka na kubce mata Ta tashi da gudu ta shige dakin su Mama sai kiran ta take amma ina sam ba ta jin ta Dama tambayar da ta yi mata dan ta tabbatar da abun da malam ya ce ne na Inaya na son mijin ta, gashi ta tabbatar amma ta lura ita Inaya ba ta san waye mijin na ta ba , ta so ta fada mata ta ki tsaya wa Jinjina kanta kawai mama ta yi ta ci gaba da yanke kayan lambun da ke gaban ta NI MA NA DAUKI TAKARDU NA , NA BI BAYAN INAYA 😴😴😴😴😴😴😴 SAI MUN HADU GOBE KAR KU MANTA KU NA TARE DA ALKALAMIN MEERAH ✌️✌️❀️ SANNAN A TAIMAKA MIN DA SHARING FISABILLILAHI πŸ™πŸ™πŸ™πŸ’–πŸ’–πŸ’– ❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀ (LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯ ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : MEERAH A.K.A ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊ TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ https://chat.whatsapp.com/IrsjzfoHUHBJzdgRtskPcY TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP CHANEL πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i BOOK 1 β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦β€¦πŸ“šβœβœ [12/08/2024] β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘ PAGE 7 ❀πŸ”₯ Bayan ta shiga bedroom din su , kai tsaye saman gadon ta Haye ta yi rub da ciki ta na sakin sabon kukan Ta na shiga bedroom din su Nesrine ta shigo gidan ta na sallama hannun ta rike wasu ledodi allamun mama ta aike ta cepane , amma duk yanayin face din ta babu alamun fara'a a cikin Inda mama ke zaune ta karaso ta zauna ta na ajiye ledodin gaban ta sannan ta ce " mama wai har yanzu Inaya ba ta dawo ba ? " Murmushi mama ta yi kafin ta ce " hmmmm ta dawo ta na cikin dakin ku " Da sauri Nesrine ta mike ta nufi dakin su da gudu Kallon ta mama ta yi ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " ke ma Allah ya ka miki mijin auren in rabu da wannan shirman naki " Nesrine kuma ta shiga dakin su ba bu ko sallama ta hango Inaya konce saman gado ta yi rub da ciki sai kuka ta ke A hankali ta tako ta karaso bakin gadon ta zauna ta kai hannu ta, ta dan bubugi kafar Inaya Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya a hankali ta mike zaune ta kai hannu ta dauki pillow din ta , ta rungume shi a kirjin ta ta na kallon Nesrine Dan murmushi Nesrine ta yi kafin ta kai hannu kan face din ta , ta goge mata hawayen ta sannan ta ce " haba sister di na, na miye kuka kuma ? " Hadiyar zuciya Inaya ta yi kafin ta ce " Nesi wai fa ki na ji Abba aure ya yi min , ni fa wlh ina da wanda na ke so ba ni son wadan aka aura min " ta kai karshen ta na boye face din ta cikin pillow " sannu malama yanzu har kin San minene so ? " Nesrine ta fada cikin sigar zolaya Dago kan ta ta yi ta wurga mata hararra Yar dariya Nesrine ta yi kafin ta ce " shikenan yi hakuri ai ni dama sai da na fada miki , ba wadda za ta iya son wacen makaho ga shi kuma kurma am........." Ba ta ida maganar ta ba Inaya ta katse ta da cewa " wai dan Allah me ya yi miki a duniya da ki ka tsane shi haka, na ga bai taba shiga harkar ki ba , ko gaisuwa ba ta taba shiga tsakanin ku ba amma kin dauki tsanar duniyar nan kin daura mishi, in ke baki son shi toh wlh akwaye ma su son shi dayawa a duniya ciki har da ni " Ta na gama fadar haka ta tila pillow din hannun ta gefe sannan ta diro da ga saman gadon ta fice dakin Ta na fita Nesrine ta rike habar ta ta ce " yanzu fa ta ce ba ta son shi amma wai shi har da kare shi yanzu ko a tunanin ta ita kadai ke iya cewa ta na son shi ko ba ta son shi " Dan tsaki ta ja sannan ta mike ta fito dakin Ta dawo inda mama ke zaune ta zauna ta na tsuke fuska ta ce " wai wannan yarinyar minene matsalar ta , yanzu fa ta ce ba ta son yaya Zayd, yanzu kuma za ta sake cewa ta na son shi " Yar dariya mama ta yi kafin ta ce " kyale ta haba ina ga ba ta san da shi ne Abba ya aura mata " Kauda kai gefe Nesrine ta yi ta na tsaki ta ce " yanzu dan Allah mama haka za mu zuba ido mu na kallo Abba ya bawa wacen makahon auren Inaya, yanzu da wane ido zai kula da ita , da wane bakin zai yi mata magana ni fa gaskia ban yarda da hakan ba " " toh Nesrine ya za ki yi na ga ba ki da izinin raba auren nan , ko kin ki, ko kin so Inaya matar Zayd ce , ni gwara ZAYD din ma da wancen dan iskan Sudais , ko ba komi ya na da tarbiya da kyawawen halaye kuma nakassar shi bai sa ya zama rago ba, ki na gani tun safe ya ke fita ya tafi aiki duk da baya gani da kan shi ya ke neman abincin shi, to me ya fi wannan ka ci halal din ka , ko wa ya na maka shedar mutumin gwarai, bara ki ji , ni wlh ko da ya fi makaho da kurma, zan aura mishi Inaya dan na san zai kula da ita duk da ba mu San assalin shi ba shekara hudun nan da mu ka yi da shi ya isa ka gane shi wane irin mutun ne " " hmmmm yanzu kennan mama kin yarda da auren nan, autar ta mu guda za a dauka a bawa kurma, makaho wanda bai ma san da me ta ke kama ba " Yar dariya mama ta yi kafin ta ce " to ina ruwan Allah da wannan ai zuciyar mutun ya kamata ki duba , sai ki ga mutun kamar shi ya yi kan shi dan kyau amma zuciyar a bushe ta ke kamar kafiran farko, amma sai ki ga wanda bashi da kyau ya na da zuciya mai kyau tsarkakiya, ke yanzu a ganin ki Zayd bai fi Inaya kyau ba kuma a hakan ya yarda ya aure ta , duk da bai gan ta ba kin ga wannan auren na su ya ishe ki ishara Allah ba ya barci , kaddara ce kawai ta hada su , amma ba dan haka ba ni na san inda zayd na da cikakiyar lafya wlh ko inda ya taka ba ki kai ki taka ba " Nesrine na shirin magana Inaya ta fito da toilet, ta wuce bedroom din su ko kallon inda su mama su ke ba ta yi ba Dan zaro mama ta yi ta na girgiza kai sannan ta ce ma Nesrine " kin ga tashi ni ki yi min aiki na " Da to Nesrine ta amsa mata sannan ta tashi ta shiga kitchen A takaice ranar yau Inaya a cikin bedroom din su ta yi ta, ko harabar gidan ba ta leko ba, abinci ma sai Nesrine ta kai mata daki su ci , abu guda ke fido ta sallat , Zayd kuma yau tun safe da su ka bar gidan shi da Moussa har bayan sallar isha ba su dawo ba Washe gari Yau ta kama ranar monday, tun karfe 6 Nesrine da Inaya su ka tashi su ka yi duk wani aiki na gidan sannan su ka shirya sai karfe 7:30 su ka bar gidan su ka kama hanyar college Tun bisa hanya Nesrine ke yi ma Inaya magana amma ta kyale ta ko kallon ta ba ta yi ba Sai da abun ya bawa Nesrine haushi ta daina mata magana ma Har sai da su ka iso AMINU KANO COLLEGE OF EDUCATION sannan ko wace ta wuce class din ta 11pm Zaune ta ke cikin cafeteria din school din , ta na rike da book , ga bottle drinks nan a gaban ta saman table ta na karatun ta cikin konciyar hankali Ta na a haka wasu yan mata guda biyu su ka zo table din ta su na mata sallama Ko dago kai ba ta yi ba ta kale su amma ta amsa musu sallamar su cen kassan makoshi shi ma dan ya zama dole a matsayin ta na musulma Dayar na mini skert da yar t-shirt colour din uniform din college din babu hijab a jikin ta sai wani dan karamin veil da ta nada a kan ta , ta yi simple make up Dayar kuma ta na sanye da uniform din ta kamar na Nesrine wato wando da riga zuwa guyiwa da hijab zuwa kirji , ta na rike da hand bag guda biyu Wadda ke sanye da mini skert din ta ja chair din da ke fuskantar ta Nesrine ta zauna sannan ta kai hannu ta karbe book din hannun ta ta na fadin " me ki ke karantawa ne haka ? " Hararrar ta Nesrine ta yi kafin ta mike tsaye ta tatare kayan ta sannan ta mika wa yarinyar hannu ta ce " ban Book di na don Allah zan koma class " Mikewa tsaye yarinyar ta yi ta ce " haba Nesi me ya yi zafi haka " " kin ga Ramatou ki ban book di na, sannan kuma sunana Nesrine ba Nesi ba " Dayar yarinyar da ke tsaye ta ce " tooo ! Me ya yi zafi haka ? " Cikin fushi Nesrine ta kale ta ta ce " kin ga Halima ban sanyo da ke ba " Dariya yarinyar da ta kira da RAMATOU ta yi kafin ta ce " yanzu wannan fushin Nesi duk dan Hafiz ya miki fada ne jiya ? " Dawo da kallon ta kan RAMATOU ta yi sannan ta ce " kin ga ko wlh tun wuri ki ce mishi ya fita da ga harka ta , ba ni son shi , in kuma ya matsa na sa yaya na ya yi mishi dan banzan duka " Dariya RAMATOU ta yi har da dafe ciki sannan ta ce " to sai mi in kin fada mishi me zai yi , wlh ko karar shi ya kai gaban yan sanda ba abun da za ayi mishi dan haka tun wuri gwara ki karbi soyayyar shi, ni ban ma ga abun so cikin dirty girl irin ki ba , ni ko abotar da mu ke kawai dan ki na temakamin ne ina samun good grades ba dan haka ba ko kallo ba ki ishe ni ba , ke ba ki san yan mata nawa ne ke biyar yaya na ba da sunnan soyayya amma ya ki dan ya ce ya na son ki shi ne za ki wani ja mishi aji, yar rainin sens kawai, sannan ki ji yaya Moctar ya ga kanwar ki kuma ya ce ya na son ta , na fada mishi gaskiyar sunnan ta da kuma karyar da kika yi mishi na cewa hanya ce kawai ta hada ku wlh idan ki ka matsawa Inaya ta ce ba ta son shi " ta kai karshen ta na kyasta mata dan yatsun ta saitin fuskar ta Cike da izza ta ce " to wlh ki kuka da kan ki " Ta na gama fadar haka ta tila mata book din ta a fuska sannan ta juya ta bar cafeteria din Halima na biye da bayan ta Su na barin wajen Nesrine ta koma ta zauna ta daura kan ta saman table din sannan ta saki kuka kassa kassa Sai da a ka koma cikin class sannan ta tashi ta fara shiga toilet ta wanke face din ta sannan ta wuce class Nassan kowa ya na son ya ji wanene Hafiz , to nima ina son ji πŸ˜‚βœŒ Hafiz dai babban d'a ne ga governor din Kano, Moctar na bi mishi sannan Ramatou sai autar su Nabila , a shekaru zai kai 25 , Moctar kuma 21 , Ramatou 19 years sai Nabila

Chapter 5 of 9