Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : ANISH Marubuciyar littafin TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i BOOK 1 ……………………………📚✍✍ [05/08/2024] ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ PAGE 2 ❤🔥 After some minutes ya fito sanye da wandon three cuter black colour da t-shirt fara mara nauyi , babu takalmi a kafar shi , ya na sanye da bakaken glass kamar kullum Takowa ya ke cike da izza da kwarjini , hannun shi na rike da wata dankareriar waya kirar Iphone 13 pro max mai launin Gold sai shining ta ke kamar zinaryar gaske A hankali ya shigo falon ya nufi sofa three seaters ya Haye ya konta Bayan ya konta ya daura hannun shi daya saman forehead din shi, dayan kuma ya fara latsa wayar shi ( A IYA SANI NA DAI MAKAHO BA YA LATSA WAYAR SHI HAKA 🤔🤔 ) Bai fi ten minutes ba da konciyar shi wani kyakyawan matashi ya shigo falon ya na sallama hannun shi rike da ledodin restaurant Ko motsawa Zayd bai yi ba , ko sallamar shi cen kassan makoshi ya amsa mishi ita Dan karamin murmushi saurayin ya yi kafin ya tako ya zauna saman sofa two seaters da ke geffen wadda Zayd ke konce sannan ya ajiye ledodin hannun shi saman table " Nawfel ga abinci ka nan " ya fada ya na kallon shi ta wutsiyar ido A dubu dari Zayd ya mike zaune ya matse fuska ya nuna saurayin da dan yatsa cikin turanci ya ce " kar na sake jin ka kira ni da wannan sunnan Diya idan ba haka ba " Dariya sosai saurayin ya yi shi ma da turanci ya ce " In haka ne ni ma ka daina kira na da Diya , ni fa yanzu suna na Moussa " ya kai karshen ya na kashe mishi ido guda Dan tsaki Zayd ya ja kafin ya ajiye wayar shi gefe ya matso bakin sofar , ya kai hannu ya janyo table din gaban shi sannan ya bude ledodin da Diya wato Moussa ya kawo mishi Moussa kuma kallon shi ya ke ya na murmushi har sai da ya ga ya fara cin abincin sannan ya ce " Amir wai ka na da labarin......... " Bai karasa maganar shi ba Zayd ya daga mishi hannu akan ya isa haka " Haba Amir yanzu haka za mu ci gaba da zama yanzu wajen shekara hudu kenan , ba ka kewar Al-Amira Tesnim da Malikat ka na tunanin halin da su ke ciki , ko kuma ka manta da Malik " Shiru Zayd ya yi bai ce komai , ya ci gaba da cin abincin shi Sai da ya ida sannan ya mike tsaye ya nufi dining room ya bude fridge ya dauki gorar ruwa guda ya dawo ya zauna inda ya tashi sannan ya bude ta ya fara sha Jinjina kan shi Moussa ya yi cikin ranshi ya ce " Gaskia kam jinin sarauta ba wassa ba ne , ko da ba cikin masarautar ya ke ba " " Amir wai yanzu haka za mu ci gaba da wannan zaman , ka san halin da masarauta ke ciki , kar fa ka manta jinin mayakka ne kai , bai kama ta a ce ka baro filin yakin ka ba " Moussa ya fada cikin raunin murya Sai da Ya ida shan ruwan shi sannan ya mike ya nufi corridor ya na fadin " ai ka san hanyar komawa ni ban tare ka ba " Ya na gama fadar haka ya shige corridor ya shiga bedroom din da ya fito Jinjina kan shi kawai moussa ya yi ya na murmushi ya ce " ni anya ba diyar malan din nan ya fara so ba , ka san dama an ce soyayya ke meda sarki bawa " ya kai karshen ya na bushewa da dariya Sai da ya yi dariyar shi iya son ran shi sannan ya mike ya dauki ledodin saman table ya kai kitchen sannan ya dawo ya nufi corridor ya shiga dayan bedroom da ke kussan wanda Zayd ya shiga * Misalin karfe 8 na dare * Gidan su Inaya Zaune su ke cikin harabar gidan saman tabbarma su na sanye da hijab dark blue har kassa , ko wace ta na rike da littafi Malan na gaban su zaune ya na karatun kur'ani , su kuma sun sunkuyar da kai su na sauraron shi Mama kuma ta na zaune geffen shi ita ma ta na sanye da hijab amma fari Su na a haka wani dan matashin saurayi ya fito da ga cikin dakin da ke fuskantar na su Inaya Ya hadu ba laifi skin din shi chocolate kamar ta Inaya amma ta Inaya ta fi dan haske Ya na da dogon hanci da kontancen saje , ya na da dara daren idanu brown colour , ya na da dan tsayi da mudewar jiki amma ba sosai ba a shekaru ba zai wuce 26 ba amma ya tare kassunba ga kwarjini Sanye ya ke da wando three cuter Fari da shirt red kamar jini ya na rike da waya kirar Tecno pop 6 Bai bi ta kan mutanan gidan da ke zaune kussan kofar dakin shi ba ya sa kai ya fice da ga gidan Malan na kallon shi ta kassan ido amma bai ce da shi komai ba , sai da ya ida karatun shi saman ya dago kai ya kali su Inaya ya ce " Auta, ina ga za mu tsaya a nan gobe sai mu ci gaba " Jinjina mishi kai su ka yi a tare ba su ce komai ba , su ka mike su ka shiga dakin su dan su ajiye littafan su Bayan mintina goma Inaya ta fara fitowa ta na sanye da doguwar riga irin ta barci da dan guntun kyale ta ya yafa a kan ta Ta na fitowa ta ji ana sallama Cak ta tsaya ta na kallon kofar gidan kafin ta amsa sallamar Wani dan karamin murmushi ta saki ganin waye ke tare da yayan na ta Da gudu ta je ta fada jikin yayan ta ta na fadin " yaya Abdoul kenan yaya Zayd ka je nemowa " ta fada ta na kallon Zayd ta geffen ido Raba jikin ta ta yi da na Abdoul sannan ta ce " sannu da zuwa yaya Zayd " Jinjina mata kai kawai ya yi bai ce komai ba Duk abun da su ke Malan ya na kallon su amma bai ce komai ba sai ma murmushi da ya ke " malan Zayd ku karaso mana " malam ya fada cikin zolaya Yar dariya Inaya ta yi ta riko hannun Abdoul, shi kuma ya riko hannun Zayd su ka fara takawa a jere Saman tabbarma da malam ke zaune su ka karaso Saki hannun ta Abdoul ya yi sannan ya ce ma Zayd su zauna A tare suka zauna geffen Malam su ka sa Zayd a tsakiya Ta na ganin sun zauna ta juya ta fara takawa ta nufi hanyar kitchen dan ta taimaka wa mama Kamar an ce ya dago kai ya kali gaban shi Ya na dagowa idanun shi ba su sauka ko ina ba sai saman hips din ta , gashi rigar da ta ke sanye yar shara shara ce a na ganin shape din ta Sai da ya ji zuciyar shi ta buga a dubu dari ya sunkuyar da kan shi dan ya yi arba da abun da ya fi karfin shi Malam da Abdoul sarai su ka lura da shi, dan Abdoul har kumshe dariya ya ke Dan murmushi Malam ya yi kafin ya matso cikin rada ya ce " Zayd in ka shirya ni ban da matsala ka zo ka dauki matar ka ta tare a dakin ka " Dago kai ya yi ya kali malam ya na zaro idanu duk da su na cikin bakin glass Yar dariya malam ya yi dan dama tsokanar shi ya ke son yi Shi ma Abdoul yar dariya ya yi kafin ya daura hannun shi saman kafadar Zayd ya ce " Bro ka yi sauri fa dan kar ayi maka wufff da ita " Dan tsaki Zayd ya ja ya na kauda kan shi gefe Dai'dai lokacin da Inaya je fitowa da ga kitchen ta na rike da tray Da sauri ya kauda kan shi dayan geffen cikin ranshi ya na fara danasanin abun da ya yi shekarun da su ka wuce Gaban su ta zo ta ajiye tray din sannan ta mike ta juya ta koma dakin su Ta na barin wajen Abdoul ya kai hannu ya janye tray din na sama , ya dauki spoon ya mika ma Zayd da malam sannan ya ce musu bismillah A tare su ka fara cin abincin , har su ka Kamala ba wanda ya ce ma dan uwan shi wani abu Sai da su ka ida mama ta zo ta gyara wajen ta kawo musu jug na ruwa da glass biyu , su ka sha sannan Zayd ya ce da Abdoul ya raka shi gida Sai da ya tsokane shi sannan su ka tashi su ka bar gidan a tare Ya na fita Inaya ta fito da ga dakin su Ta na ganin malam zaune shi kadai Da sauri ta karaso wajen shi ta ce " Abba yaya Zayd har ya tafi " ta kai karshen ta na kallon wajen kofar gidan Dan murmushi yayi kafin ya mata nuni da gefen shi Ba musu ta tako ta zauna geffen shi ta na sunkuyar da kai ta fara wassa da yatsun ta Hannu shi ya daura saman kan ta kafin ya ce " Auta , fada min gaskia , ki na son Zayd " A razane ta dago kai ta kaleshi ta na zaro idanu, ta ma rasa amsar da za ta bashi Daga mata gera yayi kafin ya ce " ba ki ba ni amsa ba " Da sauri ta ce " a'a Abba ba ni son shi , kawai dai na dauke shi a matsayin yaya na , kuma ai ku ku ka ce na dauke shi tamkar yaya Abdoul " ta fada cikin shagwaba " kennan ba ki son yayan ki Abdoul " Da sauri ta ce mishi " ina son shi mana " Dan karamin murmushi ya yi kafin ya janye hannun shi da ga saman kan ta ya ce " to shi Zayd me ya sa ba ki son shi , ko ba yayan ki ba ne ?" " ai shi da yaya Abdoul ba daya ba ne , ba zan iya cewa ina son shi kamar yadda na ke son yaya Abdoul " " kamar ya kenan ? " Turo dan bakin nan nata ta yi cike da shagwaba ta ce " Abba ni ma ban sani ba , ni na ma tafiya ta barci na ke ji " ta na gama fadar haka ta tashi da sauri ta koma cikin dakin su Ya na kallon ta har ta shiga dakin su , sannan ya saki murmushi ya na girgiza kan shi , ita dai har yanzu ta na fama da yarinta , da ga yanayin maganar ta kadai ya isa ka gane Bangaran Inaya kuma ta na shiga dakin su ta fada saman gadon su ta yi rub da ciki Bugun ta a baya Nesrine ta yi kafin ta ce " ke dan Allah malama yi a hankali kar ki kare mana gado " Dago kai Inaya ta yi ta zauna ta na kallon ta Dan turo baki tayi cikin shagwaba ta ce " kin ga ko ki daina bugu na ko in fada ma Abba " " ina ruwa na tashi muje na raka ki ma " ta fada ta na meda kallon ta saman book din hannun ta Marairaice fuska Inaya ta yi kafin ta ce " Nesrine, wai Abba tambaya ta ya yi in ina son yaya Zayd " ta kai karshen kamar ta yi kuka Dago kai Nesrine ta yi ta kale ta da kyau kafin ta bushe da wata shegiyar dariya har da dafe ciki Marairaice fuska Inaya ta yi kamar ta yi kuka ta ce " haba Nesrine ya zan yi miki magana ki yi zaune ki na yi min dariya " Dan tsagaita dariyar ta Nesrine ta yi kafin ta ce " Yau ni tambayar Abba ce ta bani dariya , yo mi ne abun so cikin wannan abun , mutumin da ba ya magana , ba ya gani wa zai iya zama da shi ai ni ko sadaka a ke bani shi wlh ba ni so " ta kai karshen ta na sake bushewa da dariya Hararrar ta Inaya ta yi kafin ta ce " kin ga matsala ta da ke wlh ba a iya magana da ke " " yo ai wannan ba magana ba ce zancen gaskia wa zai iya son Zayd, ba dan kyawon shi ba ai ko kallo bai isa wani ba " " wai ke me ya sa ki ke yawwan cin zarafin mutane, me ya yi miki, kullum sai kin kaskantar da shi , ko dan kin ga ba ya da kowa ba ya da idon gani , ba ya da bakin magana ko dan bashi da kudi , kin je makaranta ki yi karatun kur'ani ki san Allah ba ya son mai kaskantar na kassa da shi , yanzu in kin wayi gari kin koma kurma ko makafniya ki na tunanin wani zai so ki ne , Ka zamto mai furta abin alkhairi fiye dana sharri. Domin furta sharri yakan haddasa damuwa , na alkhairi kuwa ya kan sanya walwala da farin ciki. Kasani cewa mara godiyar Allah basa cigaba. Hakama mai furta sharri , wlh Nesrine ki ji tsoron duniya wannan jiji da kai da ki ka dauko ba na familyn mu ba ne , ba mu gado wannan ba gwara tun wuri ki tambayi kan ki ina ki ka dauko su " " ke dan Allah malama ya isa dan kawai na tabo wani banza cen shi ne za ki yi zaune ki na min fada kamar wata uwa ta , ai ba karya na yi ba dan ko ke da kan ki da ki ke protecting din shi ba son shi ki ke ba dan haka ki bani lfy sakara kawai , kamata ya yi ki tafi massalaci ki dauki speaker ki ringa yi musu wa'azi ko ba komi kin samu lada no sens " ta kai karshen ta na saukowa da ga saman gadon ta fice da ga dakin da kallo Inaya ta rakata har sai da ta fita sannan ta ce a fili " wlh karya ki ke, duk abun da zai sa mace ta so namiji yaya Zayd ya malake shi , dan ya ma fi sauran mazan wlh ko cikin dubu za ki duba da wuya ki samu kamar yaya Zayd " ta kai karshen hawaye na zubo mata Da sauri ta koma ta yi rub da ciki ta fara kuka kassa kassa * Zayd Tafiya su ke saman hanya shi da Abdoul, sai zuba ya ke mishi amma shi kuma ko kalma daya bai ce da shi ba " Zayd wai minene cikeken sunan ka " Abdoul ya tambaye shi Cak ya tsaya da tafya ya na kallon gaban shi kamar ya ga wani abu ya kassa gaba ya kassa baya A hankali ya medo da kallon shi kan Abdoul ya zuba mishi ido mai ce komai Ganin ya yi shiru kuma ya tsaya ya na kallon shi ya sa Abdoul cewa " ko sunnan na ka ma ka manta " Jinjina mishi kai Zayd kafin ya fara takawa ya yi gaba Dan murmushi Abdoul ya yi kafin ya ce " to tun da ka san hanya ni zan koma gida " ya fada ya na daga mishi murya Bai ce mishi komai ya ci gaba da tafiyar shi Ganin bai ce komai ba ya sa Abdoul juyawa ya koma gida Shi ma Zayd hanyar gidan shi ya kama Bai fi minti biyu ba ya iso gida Da sallama bakin shi ya shigo falon gidan nan ya isko Moussa ya na zaune saman sofa da ga shi sai short da singlet ya na latsa wayar shi Dago kai ya yi ya na amsa mishi sallamar shi kafin ya ce " Amir wai ina ka tsaya ne haka tun dazu ni ke jira ka " A hankali ya sa hannu ya zame glass din idanun shi Allahuma barik ashe ba banza ba ya ke saka glass ba , ko ni sai da na yaba kyawon idanun shi Ya na da dara daran idanu Farare kal kamar madara Launin idanun shi Hazel mai bala'in kyau , har wani green ya ke yi , sai shining ya ke abun har ya ba ka tsoro kamar idanun mage cikin dare haka su ke Karasowa ya yi cikin falon ya ajiye glass din saman table sannan ya zauna Saman sofa jingina bayan shi a jikin forehead din sofar ya daga kan shi sama ya lumshe idanun shi Duk abun da ya ke Moussa ya na kallon shi amma bai ce da shi komai ba dan ya san abokin na shi ba karamin miskili ba ne ba bazan ba a ka kassa gano shi ba kurma ba ne Ajiye wayar shi Moussa ya yi saman table kafin ya matso bakin sofar ya kai hannu shi ya dafe cinyar Zayd Medo kan shi ya yi a hankali sannan ya bude idanun shi ya daga mishi gera allamar minene ? " Amir wai me ya ke damun ka ne , duk ka bi ka sauya kamar ba Nawfel din da na sani ba , kamar ba magajin Malik , ko dai ka fada soyayya ne " ya kai karshen ya na kashe mishi ido guda Dan tsaki Zayd ya ja kafin ya kauda kan shi gefe kafin ya ce " Diya dan Allah ka bar kira na da wannan su nan, wannan sunnan ya goge da ga cikin rayuwa ta tun lokacin da mu ka shigo garin nan " " in haka ne ka daina kira na da Diya ni ma , yanzu Amir baza ka koma ka karbi mulkin ka ba " Da sauri ya katse shi da cewa " ai Malik bai mutu ba , har yanzu ya na kan mulki kuma ko ya mutu ba ni son mulkin, a kan shi a ka nemi halaka ni dan haka su je na bar musu kayan su , na ga ai kaima yarima mai jiran gado ne me ya sa baza ka koma masarautar ku ba ka karbi mulkin ta ba " Yar dariya Moussa ya yi ya na dauke hannun shi da ga saman cinyar Zayd sannan ya ce " haba kai ma Amir ta ya zan karbi mulki bayan ni ne na uku babban yayan mu na raye zan ce na karbi mulki ? shi ya sa na baro musu kayan su , ni fa mulki sam ba ya cikin tsarin rayuwa ta ba yadda za ka yi an haifo ka cikin jinin sarauta dole ka hakura " Mikewa tsaye Zayd ya yi ya bar falon Har zai shiga corridor ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " ka na da labarin Amira da Malikat ? " Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " kar ka damu su na cikin koshin lafya " Jinjina kan shi kawai ya yi sannan ya fara takawa ya shiga corridor din ya shiga bedroom din shi Ya na shiga shi ma Moussa ya mike ya koma bedroom dinshi shi ma * Washe gari * AMINU KANO COLLEGE OF EDUCATION *Nesrine Zaune ta ke kassan wata bishiya cikin harabar college din ta na rike da wani book ta na karatu Kamar da ga sama ta ji an zabce mata book din ta A dubu dari ta dago kai , wata irin mumunar faduwa gaban ta ya yi lokacin da ta yi arba da wanda ya zabce mata book din ta Wasu samari ne guda biyu su na tsaye gaban ta Wanda ke rike da littafin ta ya fi dayan tsayi kadan ya kuma fi shi haske a shekaru zai kai 25 haka ya na da dogon hanci da kananan idanu ya dan tara gashin kai Ya na sanye da crazy jeans blue da t-shirt blue ita ma Daya kuma ya na da dan duhu kadan amma kamanin su daya sai dai wannan bai tara gashin kai ba, idanun shi kuma brown colour ne , kuma ya na da saje , lips din shi kuma sun dan yi pink kadan a shekaru ba Zai wuce 23 years ba Shi kuma ya na sanye da jeans baki da t-shirt white color Wanda ke rike da book din ta ya fara magana ya ce " baby wai ba na ce da ke ba ki ringa samu na a wajen parking space lokacin break ba " Wasu yawu Nesrine ta hadiye murya na kerma ta ce " yi hakuri Hafiz bazan sake ba " Geffen ta ya zo ya zauna ya na mika mata book din ta ya ce " ba komai baby nan din ma ya na da dadin zama sai dai da mutane dayawa shi ya sa na ce ki ringa tarda ni parking space " Ta na shirin magana ta ji Muryar Inaya ta na yi musu sallama A tsorace ta dago kai ta kale ta Inaya kuma ta yi zaton classmate din nesrine ne sai ba ta ka komai a ran ta ba ta kali yar uwarta ta ce " Nesrine dan Allah in kin tashi tafya gida ki jira ni " Ta na gama fadar haka ta juya da gudu ta bar wajen kamar ta ga wani abun tsoro Tun da ta iso wajen saurayin da ke tsaye ya tsare ta da idanu sai kallon ta ya ke ya na hadiye yawu Sai da ta bar wajen ya na kallon ta har ta kure wa kallon shi sannan ya dawo da kallon shi kan hafiz ya ce " bro wacece wacen yarinyar ta hadu fa, she look so innocent " Dum Nesrine ta ji gaban ta ya fadi dan ta san in Moctar ya lakewa Inaya ta shi ga uku cikin college din nan dan sai ya azabtar da ita shi ma ba karamin mugu ba ne ga mugun son mata , dama dama Hafiz a kan shi Ta yi nisa cikin tunanin ta sai ji ta yi an daura hannu saman cinyar ta A razane ta dawo cikin hayacin ta, ta na kallon hannun hafiz da ke saman cinyar ta " lfy baby ina tambayar ki kin yi shiru " ya fada ya na leko face din ta " minene ? " ta fada cen kassan makoshi Dan murmushi yayi kafin ya ce " who is she , ko sister din ki ce " Da sauri ta ce " a'a kawai saman hanya na hadu da ita " " okay meye sunnan ta " ya tambayeta ya na tsare ta da ido Wasu yawu ta hadiye kafin ta ce " ban sani ba " Lips din ta har kerma su ke yi Ba ta gama rufe bakin ta ba , ta ji Tass saukar mari a face din ta Da sauri ta kai hannu ta saman kumatun ta ta na dafe wajen wasu hawaye na zubo

Chapter 2 of 9