Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce kadai ke sawa a shiryu ba,wasu wahala bata sawa su shiryu sai Allah ya so,tunda Allah ya kare mu kawai ya kyalesu a kwai lokacin da komai zai wuce,kuma yanzu ko sun dawo ba abinda zasu iya yi,baza mu zauna gida daya dasu ba kawai ya dawo min dasu kowa ya koma bakin aikinsa abinda nake roko a wajenki kenan tunda yana daukan shawararki watakil idan kece sai ya yarda,Sai da Daddy ya kashe min jiki da nasiha tare da nuna min Muhimmancin yan Uwa da iyaye dole nace Insha'allah Allah zasu dawo Daddy ka daina damuwa.
Haka muka rabu da Daddy ina tunanin ta ya zan iya sa Aayan ya hakura yanda yayi fushi dasu Haka.
Ameer na kira a waya nace yazo ina nemansa,da wuri kuwa sai gashi yazo,bayan mun gaisa nace kasan inda su Abbi suka koma?Ameer yace ae mana na sani kusan kullum ma ina wucewar ta layin kuma ina bibiyar halin da suke ciki,amma baka shiga wajensu ba?yace ae wlh sabo da bari nayi su kara dan nutsuwa sai na fara zuwa wajensu kawai sai naga Ameer yana Hawaye,nace subhanallah Ameer lfy? Allah Anty tausayi suka bani baki ga halin da suke ciki ba,sabo da ko kayan sawa Aayan bai bari sun dauka ba,suna cikin wani Hali,yan uwana ne mun shaku dasu sosai tare muke komai dole bana jin dadin ganinsu cikin wannan yanayi wlh musamman su Khaleel,ni kaina sai naji tausayinsu duk da ban gansu ba ganin yanda Ameer yake ta hawaye,yana fada min halin da suka shiga ga Iyayensu mata sunyi yaji yana gama fada min ya goge Hawayensa yace Anty dan Allah kisa ya dawo dasu ko me zasu yi Kansu Allah yana ganin komai bare nasan yaran gidan duk sun shiryu su Abbi da Hajja ne kawai ban sani ba.
Numfashi Naja tare da cewa tsaya mu tafi gidan nasu,waya na dauka tare da kiran Aayan nace My Man ya aiki?yace alhmdllh Babyna kinyi missing dina?nace sosai ma,dan Allah unguwa Ameer zai kaini idan ka yarda,idan na dawo zan maka bayani inda muka je kaji,ba damuwa sai kun dawo.

Godiya nayi sannan na shirya tare da daukan wanka cikin tsadajjen lace kamar a saceni nasa glass na yayi brown me tsada nayi kyau sosai kai kace yar Gomna ce gaban motar Ameer na shiga muka tafi har gidan dasu Abbi suke,a kofar gidan mukayi parking,Ameer na kalla har ya fara shirin zubo da hawaye wai na tausayin yan Uwansa,nace dan Allah karka karya musu zuciya pls ka daure kamar ba namiji ba,bazan iya shiga gidan ba Anty jeki ki fito ina jiranki,wucewa nayi ina taku dai dai kwas kwas,tun daga tsakar gida na fara Jin tausayinsu ganin su Haneefa kwance saman tabarma jikin bishiya duk sun rame sunyi duhu gashi duk gayun nan babu sunyi shuru sunyi tagumi,kallo daya sukayi min suka ganeni,da Sauri suka mike zaune,da fara'a suka ce sannu da zuwa Mufeeda,kece yau a nan?wa ya nuna miki gidan?da Ya Aayan kuke tare? Nace a'a ni da Ameer ne nace ya kawo ni tunda ku baza kuzo mana ba,da Sauri suka jani har palo,suna kiran kowa na gidan Maza da matan,Kahaleel duk iyayi da gayu babu naji tausayinsu kowa da fara'a da mutunci muka gaisa muna Hira,abinda bamu taba yi dasu ba kenan,Ruwa suka kamfato min a cup na roba,na karba ba tare da na nuna kyama ba nasha haka,sai murna sukeyi kamar sunga daren lailatul qadri.

Hajja ce ta fito tana wacece a gidan bakuwa mukayi,ido muka hada da ita nan take ta bata fuska tare da Galla min harara taja tsaki sannan ta juya cikin daki abinta,khaleel yace share ta me bakar zuciya,dariya mukayi gaba daya,sai ga Abbi su ukun duka sun fito Haneefa ta kirawosu Matar Aayan tazo,Abbi Sani da Abbin Yara duk sun amsa min gaisuwa ba yabo ba fallasa haka dai,Abbi Mustapha kuwa tsaki yaja yana muzurai tare da cewa nayi tunanin wata ta kirki ce ma bakuwar ya saka babbar rigarsa yayi gaba.
Sabeer yace baza su saduda ba fa Anty,Nace to nazo ku sanar musu kawai ku tattara yau da Dare zaku koma gida,Ameer zai zo da Driver ku tafi,ihu suka saki na murna suna tafi ai sai Anty sai Babbar yaya,Allah bar mana ke,ina ta dariya nace Ameer yana waje tare muke dashi,da Sauri suka mike muka fito gaba daya wajen Ameer,Suna ta gaisawa suna tafawa dasu Khaleel,har matan,Sajeeda sai kallonsa takeyi Tana son Ameer kuma tana ikirarin da yardar Allah sai ya aureta, Ameer dai Kuka yake so yayi na tausayin ganin Yan uwansa a haka,na shiga mota ina cewa kowa ya shirya da dare zaku koma Kunji suka ce to.muka tafi suna daga mana hannu abin tausayi.

Abbi Mustapha da suka ji labarin me nace tare da Hajja sai suka ce ai dama mu mun san dole a neme mu,ai na fada muku dole suzo su samemu,da kar suzo mana banzar yarinya tana wani iyayi da yanga harda Sako glass,ai gidan bana ubanta bane gidan dukiyar dana ce da jikana cewar Hajja,Abbi yace banza a banza ta wani taho tana yakewa mutane baki,Khaleel yace da zaku birge sai kuce muje ku ku zauna a nan kuci gaba da rayuwa shine muka san lallai kun tsanesu,Abbi yace shashasha banzaye wanda basu san ciwon kansu ba,ai dole damu za a koma ko dan ganin bayansu,Meenal tace ta Allah ba taku ba mu dai ba Sa hannunmu,Mujaheed yace sai a fadawa su Umma masu yaji su dawo suma ko Abbi? Abbi Sani yace su dawo ina? Ai basu Isa ba,Hajja tace fyalla fyallan yan mata zaku aura dan ubansu su san cewar kunfi karfin a raina muku hankali,t unaninsu a talauci zamu dawwama matsiyata yayan talakawa.










AsmaBaffa
[2/8, 7:44 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA








115-116







Official








By
AsmaBaffa









For u all my FANS













Washe gari da wuri mukayi shirinmu Haka Daddy masu kula dashi sun gyarashi baza kace bashi da lfy ba,Ammah da Aayan sai Yarima sune suka tafi Kai Daddy wurin me magani can kauyenmu.
Ba yanda Aayan baiyi ba cewar a tafi dani Ammah tace a'a bazan je ba,dole muka hakura amma Allah ya gani ban so mijina ya tafi ba tare dani ba,amma tunda kwana biyu ko uku suka ce zasuyi nace su Meenat su shirya mu dawo gidana mu zauna kafin su dawo.

2pm bayan munyi sallah tare da cin abinci sai ga Ameer tare da Sajeeda sun shigo da Sallama,dama Sajeeda a karkashin Ameer take aiki company nasu daya sun tashi tace dan Allah ya kawota gidana shine ba a son ransa ba ya taho da ita,ita kuma Sajeeda burinta kenan dama ta ganta kusa da Ameer shi yasa tace zata biyoshi tazo wajena,da Fara'a na tarbeta,Ma'eesha ce ta kawo mata kayan ciye ciye dana Sha,Meenat kam kamar an aiko mata da mutuwa haka ta kumbura,Sajeeda tace Meenat ko magana babu? Harara Meenat ta aika mata tare da Jan tsakin da kowa sai da ya kalleta,Ameer yana kallon Meenat ko me akayi mata oho shi fa Bai son fushinta,mikewa tayi zata shiga Bedroom sai muka tsinci muryar Sajeeda tace Ya Ameer muga wayarka zan tura abu,Fasa tafiya Meenat tayi ta dawo ta zauna kusa da Ameer tana masa rada karka bayar ai ba wayarta ba ce,Ameer yayi dariya yace Sajeeda me zaki tura? To ai kasan bazan ma yi ma komai a waya ba ko kawai abu zan duba,Mika mata yayi,Meenat sai fushi takeyi kamar zata daki mutane ta Mike zata tafi Ameer ya riko Hannunta ta kwace ta fice can Garden tayi zamanta ita kadai.

Wayarsa Sajeeda ta mika masa yana karba yabi bayan Meenat da Sauri yana dubata har ya hango ta a garden tana zaune tana fushi,zama yayi kusa da ita Kamshinsa na tashi itama Haka,meke damunki Mee.....sai kirrrr wayar Ameer tayi kara ya daga yasan Madinat ce uwar naci tsohuwar budurwarsa, yana dagawa Meenat tana Jin muryar mace tana Haba Sweetyna ka manta dani gaba daya sai na kiraka yafi 10missed calls amma baza ka daga ba,sau nawa zan baki Hakuri Madinat ina da wacce zan aura fa kiyi hakuri kawai kittt...ya datse kiran.
Baki Meenat ta kara turawa gaba tare da dauke kai can gefe tayi shuru,Ameer ya leka fuskarta yace baki da lfy ne? Meenat Sai hawaye Shar...Shar.... subhanallah mene ne?Ameer ya rude,Meenat ta kara fashewa da kuka wiwi yi take ba ji ba gani,Ameer tunaninsa cuta ce ta kamata,Meenat kuma tunaninta ita bata da wani me sonta a duniya sai irin su Tsito tare dasu Kwaja,ga Ameer nan yan mata sai binsa sukeyi kuma wai ma gashi ashe yana da wacce zai aura shima Bai fadawa kowa ba,tana wannan tunani tana Kukanta,Ameer yace cikin ki ne yake ciwo? Meenat kawai ta zabga karya ta daga kai kawai wai ae, Ameer ya koma kalar tausayi ya wani rude yana lallashinta yana mata sannu,Ko Period ne? Meenat kawai nan ma tace ae tare da rike mara dan kawai tayi kukanta yanda take so,sai ko ta dinga rafsa Kukanta,Ameer ya rasa yanda zaiyi da ita ma yace Marar ce?tace ae,muje Hospital kinji yana fada kamar zaiyi kuka,tasan Karya takeyi sai tace a'a ni Maganina yana wurin Anty Mufee, Muje to sai ta baki kisha,Bazan iya tashi ba ni,Ameer ya tsuguna hau bayana na goyaki to,Meenat taki yarda tasan Mufeeda ubanta zan ci in na gansu haka,sai dai ka rikeni,Ameer da sauri ya tallafe Meenat kamar wata gurguwa haka take tafiya yana rike da i ta suka shigo Mana,da sauri Na Mike ina tambaya lfy?Ma'eesha tace Sis Me ya faru da ke kuma,Sajeeda kuwa takaici ya hanata magana ganin yanda Ameer yake rike da Meenat duk ya rude ya shiga damuwa kamar shine bashi da lafiyar, da gani mugun kaunar juna sukeyi,Meenat sai wani kallo me dauke da sirrin so takewa Ameer,Ameer ne yayi min Magana ko Kunya babu Kiyi sauri ki bata maganinta mp ke damunta yana maganar ya wuce da ita Bedroom tare da kwantar da ita,Meenat kuma sai kukan So da kishi akeyi ba a sani ba, Fitowa Ameer yayi yana hada zufa kamar Doctor dan Allah kiyi Sauri ki bata ko muje Hospital gata can kamar zata suma,maybe ma suma takeyi,Bedroom din na shiga ina masifa Meenat karya kike Ba period kike ba nafa San time dinki me akayi miki ke yanzu baki da aiki sai kinzo wajena zaki shiga yi min Iskanci iri iri,gaba daya kwana nan an rasa meke damunki,lallashinta na koma yi bayan na gama Masifa ni irin babbar Anty din nan,Meke damunki haba Meenat katuwa dake yar University guda,Hannuna ta rike na zauna a gefen Bed din kamar me shirin barin duniya tace Sister ni bani da Sa'a a duniya irin su Tsito ne kawai suke so na ta kara fashewa da kuka,san...san..sannan...ma...maaa...wai Ameer yana da wacce zai aura naji yana waya shine ai cin fuska yayi min wai ni zaiwa gori harda wani yin waya a gabana ance masa sonsa nakeyi,ina ruwana ko mata Million ne zasu kulashi,Dariya ce ta kamani wato Du Kishi ne yake damun Meenat dama,Tsokanarta nayi nace Hmm ai kuwa Rannan ma Ameer ya kawo min budurwar tasa,ai ba cin fuska ya miki ba ke da kike frnd dinsa ai labari ya baki,Baki ganta ba wata muguwar kyakyawa duk ta fimu kyau,idan kika ganta sai kin raina kanki,Aayan ya San da ita?Meenat ta tambaya,nace sosai ma ai har kudi ya bata da tazo yar gidan Gomnan Yobe state ce akwai Naira.

Kuka Meenat ta kara kecewa dashi harda shidewa tana gwara Allah ya dauki raina na huta,Wayyo Duniya...Allah sarki duniya...Allah sarki Duniya...Allah Sarki duniya haka Meenat take ta yi kamar me Aljanu,Ameer dama gaba daya ya rude tunaninsa jikinta ne yayi Zafi,da sauri ya shigo dakin yana dan Allah ki daukota muje Hospital,Yaje kan Meenat dake saman Bed tana Allah sarki Duniya,ya tallafota ai kawai sai Meenat ta shake Ameer ta cukwikwiyeshi gam suka fada saman Bed rigija,ta finciko gashin Ameer suma taci uban gyara tasha kyau Ameer ya dinga kara tana cisgar masa suma, sai da na buga mata tsawa sannan ta saki Ameer kuma tana kukanta,Ameer yace Aljanu ne Anty,jeka waje bari na shiryata sai mu tafi Hospital din,Ameer yace ina Palo dan Allah kuyi sauri Aljanune ina Meenat take da karfi haka ai sai na Aljanu.

Yana Fita nace ke kuma haka soyayyar taki lallai kinyi Nisa Meenat Allah ya shiryeki,Harara Meenat ta balla min tare da cewa ai kin fini ke baki ga yanda kike wa Aayan ba a gaban kowa,ai gwara ni wlh ke a gaban kowa kike rungumeshi tsotse masa baki,kina fari kina kashe murya,Hips dinki ma yanda kike juya masa shi daban ne mene ne bamu sani ba,kuma sanda yayi tafiya kuka kika dinga yi a daki muna jinki sai da kika sa ya dawo,shine me to ai miji na ne nace,ke fa? ganin Meenat yanda ta koma yasa naji tausayinta nace wasa nake miki banza Ameer bashi da budurwa,da sauri tace da gaske kike sis?nace sosai ma,dariyace ta kwace mata kadan sai ga Meenat ras da ita,tace dan Allah karki bari Aayan yayi masa auren dole gwara a barshi ya zabo wacce yake so,Dariya kawai nayi wai ni Meenat zata yiwa wayo,kawai nace ki kwantar da hankalinki abokinki baza ayi masa aure da kowa ba sai wacce ya kawo mana amma kiyi kokari ki san wacece yace yana da matar da zai aura?Ni a sanina bashi da ita Sis ko waya da mace bayayi amma sai na binciko ta kuma wlh idan na kamata sai na kusa kasheta,Dariya na karayi nace to ke da kike so ya auri wacce yake so kuma ai sai dai ki tayashi Murna ko? Murmushi kawai Meenat tayi ta miko min wayata gashi Ur Man na kira.

Da sauri na karba na bar dakin tare da shigewa wani Bedroom din na kwanta sannan na daga kiran har ya kira ma sau biyu,Muryata na kashe tare da lankwasheta can kasa Nayi Sallama,sai da tsigar jikinsa ta tashi yaji kamar ma yayi tsuntsu yazo ya ganni ya koma,Honey na ya hanya da fatan kunje lfy? Ajiyar zuciya ya saki kana yace lfy alhmdllh saukar mu kenan Sweetwife am so tired gashi bakya kusa bare ki min wanka ki bani abincinki me dadi ohhh Am damn missing u missing ur food komai ma,dadi yana ratsani nace nafika damuwa tun dazu na kasa cin komai na kasa yin komai a gidan ma just thinking abt u gobe kuma ina da schl anya zan iya karatun ma? Yau shike nan baza muyi bacci tare ba kenan,abinda nake tunani kenan taya zan iya bacci bakya kusa dani,Yanzu me kakeyi ina su Ammah da Daddy? Daddy yana can dakin da aka bamu,Ammah na cikin gida,ni da Yarima kuma mun fito a kauyen muna kallon mutane kawai kafin anjima muje gidan me maganin,eyya mijina yana Shan wahala a kauye baka saba ba ina zaka huta kaji dadi,I wish muna tare,ai idan naji zamuyi 1wk a kauyen to ki Zama Ready kawai gobe zaki taho kema bazan iya zama bakya kusa dani ba musamman a wannan garin can cikin daji ne fa,nima nace sai dai kawai Ammah ta ganni nazo indai baza ku dawo da wuri ba bazan iya barinka a nan ba,yanzu me zaka ci?shine nake tunani,ka duba cikin kayan dana hada ma akwai Snacks,dambun nama da Soyayyen naman rago dana Kaji sai Kaci ko da juice ne,Wow Allah Ubangiji ya miki albarka My Wife ina mugun Sonki,kamar kin San tunani nake me zanci Allah ya gani bazan iya cin abincin da aka bamu ba babu dadi wlh,fura kawai na Sha da nono,Karka damu tunda lafiyar Daddy ake nema komai wahala za a daure, cike da shagwaba yace ni dai gobe kawai Driver ya kawoki garin tunda kin San wajen,an gama ranka ya Dade sai abinda kace,dariya yayi yanda nayi maganar kamar ina gaban Sarki shine ya bashi dariya Haka mukayi ta hira ina lallashinsa karshe nace ya gaida Yarima mukayi Sallama kafin zuwa anjima.

Yana kashe wayar na Kira Ammah muka Sha hira itama na hadata dasu Ma'eesha,lokacin Ameer ya leka dakin da Meenat ke ciki ya hangota ras da ita hira ma sukeyi da Ma'eesha suna dariya suna waya da Ammah ,tunanin Ameer ni na bata magani ta warke,har wani dadi yake ji a ransa,Sajeeda kuwa tuni takaici yasa tace tafiya zatayi gida ba yanda banyi da ita ba ta bari sai magrib nasa Driver ya kaita amma taki yarda,haka na kyaleta ta tafi gida tana kunci.
Tana gefen titi zata shiga Taxi sai ga Tsohon saurayinta Saddiq wanda yake mugun sonta kamar hauka bashi da wata makusa ta ko ina amma Sajeeda ta dinga wulakantashi yanzu yayi parking da mota yasha mamaki ganin yanda ta mutuntashi suka gaisa yace tazo ta shiga motarsa ya kaita gida amma taki sai da kyar ta shiga shi Kuwa Saddiq sai Murna yakeyi ya dauki Sahibarsa,dama gashi lecturer ne matashi bai taba aure ba.

Khaleel da Mujaheed ne suka shirya takanas suka je wurin Iyayensu mata su uku akan maganar suyi hakuri su koma duk da Wahala suke ciki a dangin nasu sabo da talakawa ne amma suka ce Sam baza su dawo ba su sunfi samun kwanciyar hankali a gida,Uwar miji ta gama mallake mazajensu sai abinda tacewa su Abbi,dama aikin Allah ne da sauki amma harkar asiri su kam baza su koma ba,sukace ai da duk bamu gane ba sai yanzu Allah ya ganar damu,Abinda sukewa Daddy da Aayan tare da matansu kadai ya isa ka nemi wajen tsira waye baza suyi wa ba a duniya,Umman Khaleel da suka je wajenta tace da ina da arzikin Shanu sanda ubanka ya Aureni a kauyenmu sunfi goma,Amma duk ubanku ya min wayo ya cinye min shanu kaf shi da uwarsa Hajja,lokacin tun Daddy bai zo kasar nan ba,Itama Mommyn Mujaheed sai da ta mallaki katon gida da Gold ubanka Mujaheed yaje ya lallabata amma ta hanashi sai ko Hajja ta hadata da malamai sai gashi ta dauki komai Nata na dukiya ta basu tun kuna yara,ana zuwa wurin Umman Ameer ta fashe da kuka tace ai wlh tunda har suka iya korar min dana daga gida bazan koma ba,Aayan da Mufeeda Allah yayi musu albarka sune suka rike min shi da tuni ko ya fada shaye shaye amma gashi yana wajensu lfy shi yasa nace yaci gaba da Zama a can,ai zalincin dasu Hajja tare da Yayanta suka yi mana bazai irgu ba,ni dai na gane gaskiya tsakanina dasu sai Allah ya isa,Haka nazo da Kudina Dubu Dari Babana ya bani Naja jari na fara business ina Amarya Abbi uban muguyen gidan kaf ya lallabani yace na kawo na shiga Dashi,sai da na shiga Ashe tuni ya lallaba da daukana yazo ya karbe kudin sai da nace a bani uwar dashi tace wai nice daukan farko mijina ya karba yace nice nace a bani,naji takaicin Abin nan haka na dinga zubin dashi ba dauka har aka gama,bayan nan Babana ya kara aiko min da Dubu Hamsim ya lallaba ya sace,banda sauran abubuwa wanda muka sani da wanda bamu sani ba na zalinci da suka dinga gwada mana wanda Hajja ke sasu komai.
Mujaheed yace to a bamu yaran mu tafi dasu sabo da schl,haka aka basu su Omar su uku yara yan 5-6yrs suka tafi dasu sabo da schl kar su tashi ba ilmi me kyau.

Su Abbi kuwa basu da mataye yanzu sai dai suci su sha su sa sutura me kyau,gasu gwauraye illarsu daya rashin kudi babu kudin da za ayi bariki amma duk da Haka Suna yi sama sama neman mata tunda Suna matsawa dole Ameer yana basu kudi,haka su Khaleel suna Jin tausayinsu su basu Ashe ana basu sai su Kama Hotel su kai mace ciki musamman Abbi Sani yafi kwarewa a wannan fagen.

Haneefa ce ta shigo main Palo taci uban wanka ta Sha kyau sai masifa take,Sabeer takewa fada wlh duk me wulakanta abinci watarana abinci sai ya wulakantashi,ba ku kadai abin bala'in zai shafa ba har mu gaba daya,taya dan Iskanci baza ayi abinci dai dai kowa yaci baiyi kadan ba baiyi yawa ba amma sai kuje kusa ayi ta dafa abincin iri iri kuma a kasa cinyewa,a zubar dashi ko ina kaca kaca daga karshe a watsa a dustbin ga masu aiki kuna sasu wahala,wannan ba dai dai bane,kalli yanda muka Sha wahalar rayuwa amma ko tunawa bakwa yi,wannan bai dace ba babu kyau,Allahu Akbar yaran suka saki kabbara gaba daya Haneefa ta Zama Malama,su Kansu masu aikin gidan yanzu dadi suke ji yaran gida sun nutsu, Hajja ce kawai dasu Abbi ba a shirin tuba sunyi nisa, Haneefa tana gama wa'azinta,Sajeeda ta Mike tace ya kamata mu nemo mazaje,Maza su nemo mataye muyi aure sai ihu yeeeeeee wlh kuwa gwara a dama damu,Sajeeda kinfi kowa iya kawo shawara Cewar Khaleel, Abbi ne ya fito ya daka musu tsawa baku da aiki sai kullum ku cika mana kunne da surutu da ihun banza,zaraf sai ga Hajja tace aikinsu kenan yanzu kullum sai sunyi zaman Palo suna surutun banza da wofi wai su yanzu a dole sun Zama na gari nan wai nutsatsu,Sai kunci ubanku wlh a gidan nan sai na tattaka ku cewar Abbi,Hajja tace gwara haka ai wanda basu San ciwon Kansu ba kwandala bana morarsu gasu nan dasu gwara babu a gidan nan,ni fa takaici nakeyi Ameer baya gidan nan nasan shi kadai ne dan albarka kullum sai ya bani kudi ya siyo min kayan dadi,Abbi yace ai nace masa ya dawo mu zauna yaki yarda wai yafi son wajen yaron can me Jan kunne,ai idan Ameer ya sake sai na masa baki watarana,da Sauri Hajja tace baka isa ba Ameer dan albarka ai duk yafi wannan banzayen,Ameer dina wlh duk Wanda ya ko zageshi bazan yafe muku ba a gidan nan,da dinma da na bari kuka koreshi nayi ne dan ya gyara halinsa badan wai bana sonsa ba. Tabe Baki Khaleel yayi yace mu da kice kina sonmu da ki tsane mu duk daya a wajenmu,kai marar kunya kaji nayi magana da kai shegen Hanci kamar kana Mura kai fa Hasken fatarka na banza ne sabo da bame kyau bane shegiyar Suma kamar ta zabiya,Ameer ne kamar Balarabe,Wannan kuwa ta Nuna Mujaheed ido kamar na dan giya manya dasu,dariya sukayi Sabo da Khaleel Hasken sa da yawa, Mujaheed ma yana da haske amma yafi kowa Dara daran idanu sune ma suke kara masa kyau,duk da Dama su duk gidan kyawawane sosai,Aayan ne yafi kowa ba a hada kafa dashi sabo da shi jinin turawa ne sai Ameer, Hajja ta Gama masifarta ta wuce.

Su Aayan da dare sunje gidan me magani yace sai sunyi sati daya a wajensa,suna dawowa Aayan ya bani lbr kawai na taho gobe,Ammah kuma ta kara Min warning kar na sake na zo taji labarin Aayan yace zan biyosu,Na roki Ammah ta yarda nazo tace bazan zo ba,Aayan na sanarwa yace tunda Ammah ce shike nan mu hakura haka har mu dawo,kullum tare muke dasu Ma'eesha tare muke girki da komai da ya dace muna zuwa schl dinmu ni da Ma'eesha abinmu lfy, kwanan su Aayan Uku alhmdllh Daddy yana samun sauki domin har yana iya motsa hannayensa da kafafu.

Muna zaune tare dasu Ma'eesha,Ameer yana Shan Ice Cream dinsa,Meenat tana kusa da Ameer wai sai ya San mata Ice cream dinsa bayan ta shanye nata, wayata tayi kara naga Kawata Nawwara ce rabon da ta kirani tun ranar da tazo su Haneefa suka kwala mata robar ruwa tace Bom ne sai yau naga kiranta bayan ta tafi na kirata amma taki dagawa,ina dagawa nace kin huce kenan?dariya tayi muka gaisa tace Anjima zan shigo Insha'allah,Nace to bari na tura miki address din mun canja gida ba wanda

Please Login or Register in order to submit comment