Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sati guda gaba daya Bashir ya zama gashi nan ne, abubuwa sun rikice masa duk yanda ya dauki shawo kan Ma'u da sauqi abinya shallake haka nacin yake roqon yake amma kamar wanda yake shika dusa dukda shima dai da tasa irin wautar.

Wani irin biko yakeyi me kamada fin qarfi saboda a duk sanda ya tashi yi mata magana nuna mata yake kamar ya zamar mata dole bazata oya rayuwa babu shi ba dan haka ta haqura ta dawo masa wanda sam shi be dauki hakan da wani laifi ba gani yake kamar yana tuna mata da girman soyayyar da take tsakanin su ne wanda ita kuma wannan abun shi yake wara qona mata rai take jin dole ta barshi ko dan ta nuna masa cewar ba tare aka dauro rayukansu aka aiko duniya ba.

Ana saura sati daya a koma makaranta kamar yanda aka saba suka tura mata da Takardar biyan kudi saboda daman lambar wayarta ce akai in an turo mata seta turawa Bashir din ya bada kudin.

A yanda aka saba an samu qarin kudin makaranta ga kudin littattafai saboda sabuwar shekara aka shiga za'ayi canjin aji ga kudin jarabawar WAEC da NECO da JAMB na Aliyu da ze shiga aji shida dan haka da aka hada lissafin sega kudi sun tasarma kusan Miliyan biyu.

Ita kanta seda ta jimanta wannan al'amari ta rasa abinda yasa makarantar suke haka basa bada notice na qarin kudi sedai kawai idan an kawo maka teller ka gani kamar wadanda suka bawa iyayen yaran ajiya koda yake makaranta ce ta yayan masu dashi suma karanbani ya saka suka kai yayansu ai.

Ta Whatsapp ta tura masa da takaddun lokacin yana zaune a Office be dade da gama waya da Amirah ba da take masa zancen kudin siyayyar haihuwa gashi jikin Alhajin su ya qara zafi dan shirin kaishi Kano akeyi ma Asibitin Malam nan ma dai duk wani lissafin kudin ne dai yanzu ga wannan ubannin kudi na makaranta kuma sun taso masa duk a ina ze qwaqulosu?

Wai to ta yaya da duk yake hidimomin sa har ya samu rara a asusun sa ba taredaya girgiza ba? Albashinsa Miliyan daya ne duk wata saboda babu Fansho babu garatuti idan ka gama banda sauran alawan da suke samu kala kala musamman yanzu daya samu qarin matsayi packages harda na banza basu ake dan haka yake facakarsa baya ma lissafi bare ya ajiye na buqatar kota kwana tunda kudinna shigo masa koda yaushe daman Super markets dinsa Gombe sune tanadin Bayan Ritaya wanda se a yanzu yake hango tarin gatan da Ma'u tayi masa data saka shi a harkar kasuwanci nan dan yanzu ba qaramin habaka jarinyayi ba tunda ba'a tabasu duk ribar daΒ  aka samu ciki a ke maidata.


Text ya tura mata akan ayi masa haquri kafin a koma ze bayar nan ya shiga hado ta inda zasu fito, dole dai ya karbi kudi a gurin Sa'ad din idanyaso daga baya ya mayar dan su makaranta babu ruwansu ba jira zasuyi ya samu ba shawarar daya yanke kenan a take kuwa ya kirashi akan yana san ya karbi miliyan uku se Sa'ad din yake gaya masa sunyi sarin kaya, kudin da suke dasu a qasa ko Miliyan daya bazasu kai ba na banki kuma ze dauki lokaci dan yamamta account din ya samu matsala ta yanda sedai kudi su shiga amma bazasu fita ba dan haka dole sedai idan zeje Gomben da kansa ya gyara tunda shine signatory din.

A daren ranar yana zaune a qofar kujera ya dasa kujera yana aikin tunani, daga inda yake yana iya jiyo hayaniyar yara daga gidan Ma'u saboda yanda Estate din yayi shiru.
Hira suke cikin raha anata qyaqyata dariya kamar yanda sukeyi a ko wanne dare lokacin da tana gidansa wani lokacin idan yaga dama ya zauna ayi dashi wani lokacin kuma yana daga gefe yana sauraronsu yana murmushi dan ita irin mutanen nan ce masu biyewa shirmeb yara ta haka take sanin duk abinda suke ciki basa boye mata tunda ta mayar dasu kamar qawayenta.

Ya ilahi me yasa duk beyi tunanin komai ba ya rusa Wannan kyakykyawar rayuwar ta gidansa? Yanzu da ace bata kusada yaran a ina zasu ringa samun wannan walwalar da farincinin saboda yanzu sam babu wata damuwa a tattare dasu, kamar daman a haka suka tashi tsakanin gidaje biyun musamman da baya takura musu da zancen kwana duk inda suka so yanzu zamansu suke shiyasa Aliyu ne kadai yake rayuwar qunci da damuwa a cikinsu kodan shine babba yafi su tunani da gane abinda yake faruwa.

"Abbi tunanin me kakeyi tun dazu ina tayi maka magana baka ji ba" maganar da Aliyu yayai tareda girgizashi ta dawo dashi hayyacinsa. Se ya sauke ajiyar zuciya yana kallonsa yace

"Tunanin da yawa Aliyu, gaba daya kaina ya qulle ga Maminku sam ta kasa fahimta ta tayi haquri akan abinda ya faru ban san yaya zanyi ba Aliyu".

"Abbi duk abinda ya faru ai laifinka ne, haka kawai kaje ka qara aure kuma Abbi ka rasa wa zaka aura se Anty Amirah bayan kasan Mami cefa ta riqeta, kazo ka ringa yi mata abubuwa duk akanta kawai saboda kaga tana da haquri sannan fa Abbi saboda ita ka sake ta sannan yanzu saboda kaga baka jin dadi bata nan kazo kana cewa ta dawo ai kasan bazata yarda ba" Aliyun ya fada bayan daya zauna.

"Na sani kuma duk na karbi laifina, auran Amirah da rabuwata da Maminku duk qaddarace Aliyu gaba daya ba a san raina komai ya faru ba amma babu yanda muka iya da abinda Allah ya qaddar. Ni dai yanzu ku taimaka nasan ai ku zata saurare ku ku bata haquri ta dawo gidan nan nayi Nadama bazan sake maimaita duk abinda ya faru a baya ba.

Idan ma so take Amirah ta koma Gombe zata tafi nidai tayi haquri a mayar da auran mu kawai zanyi mata duk abinda take so kaji kuje dukkan ku ku sameta dan Allah Aliyu nasan ai kai bazaka so kaga rayuwata ta shiga garari ba saboda rashin Ma'u" Bashir ya fada yana kama hannun Aliyu daya tsura masa ido.

"Zanje na sameta dukda tace karmu sakeyi mata maganar ka amma ina so kayi mun alqawari.."

"Koma menene na yarda in har zaka shawo mun kan Ma'u duk abinda kake so zan baka" Bashir yayi saurin tare shi. Seda ya sauke ajiyar zuciya kafin yace

"Kayi alqawarin idan Mami ta yarda zata dawo zaka saki Anty Amirah saboda nasan indai kana tare da ita Mamai bazata taba samun farin ciki a gidan mu indai kana so ta dawo to ka sake ta kawai gidan mu ya koma yanda yake kafin ta shigo rayuwar mu".

Kasaqe Bashir yayi yana kallon Aliyu da jin abinda yake fada, ya saki Amirah fa me yasa se wannan sharadin ze saka na shawo masa kan Ma'u?
Shida yake qoqarin gyara kuskure shine yake so ya sake aikata wani ita kuma idan ya sakeya yanzu kuma wata jarabawar ta sake afko masa fa gaskiya Aliyu yayi haquri banda wannan ya yarda dai ze raba musu gida yanda suke da har na can Gomben ma idan Amiran ta koma ze raba musu kowa gidanta daban.

Hannun Aliyun ya kama yana sake marairaicew kamar wani kalar tausayi yace
"Haba Aliyu so kake na sake yin wani sakin kenan bayan nayiwa kaina alqawarin ko dukana mace zatayi bazan sake sakinta ba. Baka san yanda nake ji akan rabuwata da Maminku ba, Baba fushi yake dani ko magana baya mun yanzu haka su Amiru duk sun dena kulani saboda abinda ya faru so kake na sake maimaitawa itama Dada da sauran yan uwana su tsane ni?"

"Ai daman Baba dasu Uncle Amir ne kawai suke son Mami ni ina ruwana idan sunji haushi kawai in dai kana so Mami ta dawo to kayi alqawari zaka saketa koma zaka dawo da itama daga baya ni babu ruwana amma yanda aka saki Mamanmu saboda ita itama taji irin yanda mukaji" Aliyun ya fada kansa tsaye babu wata damuwa a tatttare dashi.

Bashir kuwa ido ya saka masa yana mamakin a ina ya samo wannan tunanin ko kuwa Ma'u ce ta fada masa hakan ita take so a saki Amirah sannan ta dawo. Kansa ne ya dauki dumi, yanzu idan da gaske ya amince zata dawo din ko kuwa kar ta sake rufta shi se daga baya yayi biyu babu ko daya.

Numfashi ya sauke yana kallon Aliyu da yayi kicin kicin yace

"Na yarda amma se randa aka mayar da aurena da Mamin ku sannan zan cika maka alqawarin"

"Ka dai san hukuncin cika alqawari" Aliyu ya fada yana kallonsa.

Kai shi abun ma ya zarce mamaki wai yau shi Aliyu ya titsiye haka yake bashi umarni, ya ya iya? Haka ya rausayar da kai yace

"Na sani kaima se kayi qoqari ka cika naka alqawarin" ya fadi haka bawai dan har zuciyarsa ze aikata hakan ba. Buqatar sa kawai Ma'u ta dawo idan ya samu bega kuma wanda ya isa ya sake raba shi da ita ba ballantana wani alqawarin Aliyu can.

Haka ya shiga gida da yaqinin cin nasarar yaqin ta wannan sigar daya samu, yasan tana da rauni akan yayanta in Allah ya yarda wannan raunin nata shi ze kaishi ga nasara.

ASMA'U

Ganin da nayi har ana saura kwana uku a koma makaranta Bashir be yi magana ba yasa na sake tuntubarsa. Ta whatsapp call din ya kirani saboda ni nake so muyi magana dan haka na daga muka gaisa yake cemun

"Kin jini shiru ko wallahi Ma'u bani da kudi ne, abinda na saka rai dashi ban samu ba ga shi da saura kafin mu samu salary ina ta dai fafutukar yanda zan samu daga yau zuwa Gobe in sha Allah zan saka miki"

"Toh Allah ya rufa asiri, ayi qoqari dai kasan su bazasu karbe su ba idan ba'a biya ba. Ga siyan su takalmi ma da jaka da dan abinda ba'a rasa ba tunda sabon session ne duk suna da buqatar a canza".

Allah sarki rayuwa shi baya zaton ma ya taba bada kudin wasu jaka da takalmi dan yawanci idan suna Gombe a shagonta suke zuwa a dakko tunda duk tana siyarwa harda su Lunch box din da suka dawo nan kuma sedai ya gansu da abinsu, kudin Uniform da sport wear kadai yasan in suna buqata take gaya masa baya ga wannan sedai yaga tayi musu.

"Shikenan, yanzu zan tura miki da 1M a fara rage kudin kona mutum uku ne zuwa jibin se na ciko" ya fada qasan ransa yana so ya roqeta da yasan bazata rasa kudi ba ta ranta masa amma yana tsoron amsar da zata bashi tunda yanzu kam Ma'un ba ta da bace

"Shikenan toh ka tura amma fa ka tabbata Jibin ka ciko dan ni inaga ma zanje a chanza lambar nan gaskiya can su ringa tura maka duk abinda ya kamata" na fada kafin na kashe wayar.

Wani abu naji kamar tausayinsa ya dan kamani, nasan Bashir da hidimar yayansa indai an gaya masa yanayi ballantana kuma harkar makaranta tunda har ya ce bashi da kudi toh tabbas bashi dasu din.

Ba'afi minti biyar ba sega alert din kuwa ya shigo, wayar na ajiye na janyo durowar gefen gado na sega kudin da Ambassador ya bamu ranar nan tunda na watsa su ban qara bi ta kansu bama dan na manta shi kansa da yace na kira shi ban kira din ba.

A jakata na zuba su da niyar gobe idan na fita zan biya banki se na cire wanda ya turamun na hada da wadannan na biya musu kudin makarantar kawai daman ai kudin Aliyu ne sa ci tare da qannensa.🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR πŸ₯°πŸ‘Ή
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 60



Washe gari Juma'a kuwa da wuri na dauki excuse na kama hanyar banki, seda na fara Zuwa Access bank na cire kudin daga akawun dina na hada da wadancan kafin na wuce Zenith inda ake saka kudin makarantar bayan da nayi printing teller da suka tura mun.

Ina shiga bankin Yusuf ya kirani.
"Ina zuwa dan Allah zan kiraka ina banki ne" na fada bayan da muka gaisa.

"Hajjaju bari nima na turo da akawun a sakamun wani abu mana" ya fada cikin wasa

"Toh shikenan, seka turo ina jira" na bashi amsa ina shirin kashewa ya tareni da cewa

"Har transaction din miliyan nawa zakiyi da se kinje banki?"

"Kudin makarantar yara ne fa zan saka kasan basa karbar transfer dole se cash deposit za'ayi"

"Ke kike zuwa biyan kudin makarantar yaran shi Baban su aikin me yakeyi da baze je da kansa ba ko kema irin matan da suka dauke dawainiyar yara da bata zamar musu dole ba sukeyi ce" ya fadda cikin wani yanayi kamar na bacin rai.

Murmushi nayi nace masa
"To meye a cikin biyan school fees? Ni har PTA ma ni nake zuwa musu kai komai ma na makarantar su lamba tace akai"

"To sannu kinyi abin kirki a tafa miki" ya fada kafin yaci gaba da cewa

"Na rasa me mata kuka dauki kanku yanzu wallahi, gani kuke kamar gwaninta ce ko iyawa ke uwa ki dauki haqqinki ki dauki na uba duk ki hada ki ringayi in ba haka ba ina ruwanki da harkar makarantar yara?

Iya abinda ya shafe ki shirin su na tafiya makaranta kula da tsaftar su da abinci shikenan se bitar karatu idan sun dawo gida ko taya Home work ni banyarda haqqin uwa bane tayi wa yara shi uban aikin me yakeyi idan ya dawo da daddare da baze tara su yaga abinda suke koyo ba se kece zakiyi??

Abin nan yana bala'in bani haushi, Idan ka fita da safe motocin kai yara makaranta in ka hadu da goma bakwai matane a ciki biyu daga ciki shine zakaga Driver aka daukar wa yaran yake kai su se daya ne zaka samu uban da kansa bayan dai qarshe mutum yace yana sauri ze tafi aiki duk sauri dai qarfe bakwai ma'aikaci yake fita kuma suma makarantu bakwai ake budesu me ze rage ka idan ka tsaya ka ajiye yayanka kafin ka wuce naka gurin aiki

Wannan uar dawianiyar da iyaye maza muke kasa jurewa muyiwa yaran mu fa shine abubuwan da har girman su bazasu manta ba kuma a irin lokacin ne fa kadai kake samu da zaka tattauna da yaran kasan matsalolinsu amma ina kai agogo sarkij aiki ka fice ita mata ga aikin gida ta shirya yaran ta rufe gida ta kaisu ta dawo ta dora daga inda ta tsaya in an tashi ta koma kune zuwa PTA kuna wannan kune wancan duk wa ya aike ku ne

Kin ganni duk irin Busy da nake yayan Yaya Umar (Yayansa ne daya rasu) in har kikaga banje na dakko su daga makaranta idan akayi hutu ba to bana qasar ne amma ko a ina nake se na koma na dakko su ko na kaisu tunda boarding sukeyi haka Visiting har personal Visiting indai na samu dama ina zuwar musu saboda ni ne matsayin uban su a yanzu ba kuma naso suga wani abu da akeyiwa wanda ubansa yake raye su sun rasa suyi kukan maraici saboda Babansu babu abinda beyi mun a rayuwa ba duk matakin da na kai da bazarsa nake rawa Dan haka tun wuri ki tashi malama ki San Abinda yake haqqinki da wanda ba naki ba

Ki zauna a inda nake bari na turo yaro yaje ya saka kudin karki kuskura ki shiga bankin nan kuma wannan ya zama na qarshe da zaki sake zuwa biya musu wani kudin makaranta idan baze je da kansa ba a barshi" ya qarasa maganar ta sigar umarni.

Haka kuma na zauna a motar bayan ya kashe ya sake kirana mita ce dai yake tayi akan mata mun fiya zaqewa, se kuma miji ya miqe qafa ya saba da kina masa daga baya kizo kina qorafin yaqi yayi bayan tun farko baki sabar masa da yayi ba.
"Wai dan ma baka san ya na gudanar da nawa zaman auran ba kenan da ina ga bulala zaka sak kayimun shege duka irin wannan masifa da kake daga zuwa biyan kudin makaranta" na raya a raina.

Ba'a jima ba sega kira ya shigo mun da lambar da ban sani ba, uzuri na bawa Yusuf na daga mutumin yake cemun shine wanda ze karbi kudi ina ina na kwatanta masa ina da tsaya se gashi ya qaraso da alama ma'aikacin bankin ne dan ga ID card dinsa nan a wuya.

Seda muka gaisa na dakko Teller na bashi ina zaro kudade daga jaka ya juya ya tafi nayi saurin dakatar dahsi da cewa ga kudin se cemun yayi wai Teller kawai aka ce ya karba yai tafiyarsa. Ko minti goma ba'ayi ba se gashi ya dawo da receipt na karba nayi masa godiya na zaro dala dari biyu na bashiya dakyar ya karba mukayi sallama na kama hanyar makarantar kai tsaye naje na chanza Teller,

kafin na isa ya ringa kirana yana jaddadamun da naje a cire numberta a mayar data Bashir ya kashe wayar sa yaqi bani damar da zan masa maganar biyan kudin ma da yayi oh Yusuf kenan shi ma kowa ya aike shi yin abinda ba haqqqinsa ba oho.

Text na rubuta na tura masa na godiya da irin hidimar da yakeyi da yarana kafin na rufe da cewar na tanadar masa da kyakykyawan labari ina jiran zuwan sa Lagos

"Ki saka ran gani na a ko da yaushe Allah yasa abinda na dade ina muradin jine daga bakinki Asmy" ya dawo mun da amsa. Murmushi nayi dan dagaske ji nake ya kamata na amsawa Yusuf na bawa kaina dama ta gwada sabuwar rayuwa tareda kyakykyawan yaqinin samun chanjin Alkahiri.

A daren ranar ina kwance a dakina saboda kaina da na danji yana mun ciwo aka kwankwasa qofa, Aliyu da sauran yaran gaba daya yana gaba suna binsa a baya suka shigo suka jere mun a gaba na dago ina cewa

"Wane kalar iskanci ne wannan zaku wani tsaya mun aka kamar masu Asambili idan ma wani abun kuke so mutum daya baze wakikce ku ba wai bana hana ku yimun wannan gangamin bane?"

Shiru suka mun, na kunna fitila se a sannanna lura da yanayin fuskokinsu gaba daya babu walwala sun sunkuyar da kawunan su qasa. Wata faduwar gaba naji nayi saurin tashi zaune ina cewa

Babu wanda ya amsa ba kuma su dago kai suka kalleni ba,

"Ku fice mun bana son wulaqanci ana magana kunyi shiru ku fita ku bani guri" na fada cikin tsawa dukda qasan raina ina tsoron abinda ya saka su yo wannan gangamin haka, qafata na sauke qasa da niyyar fafarar su tunda sunqi magana seji nayi kamar hadin baki sun rushe gaba dayan su da kuka yanbiyu suka yo kaina da sauri suka runguneni.

"Meye haka ku fada mun dan Allah wani ne ya mutu?" Na fada a gigice ganin irin kukan da suke yi harda Aliyu da bazan iya tuna rabon da naga kukansa ba.
Gaba daya na rikice jikina har rawa ya dauka a zatona wani abunne ya faru, Farida na janyo na girgizata ina cewa

"Zanci ubanku wallahi kuyi mun magana menene waye ya mutu a nan ne ko a Gombe?"

Aliyu ne ya zube guiwoyinsa qasa a gabana ya kama qafata yana cewa

"Mami da girman Allah ki dawo gidan mu. Wallahi Mami Abbi yayi nadama ki dawo indai kina so rayuwar mu ta inganta karki tafi ki barmu da wannan matar, bana bacci Mami tunda kika bar gidan mu kullum cikin damuwa muke, Abbi baya hayyacinsa su kansu su Abdallah Mami saboda basu gama gane abinda yake faruwa bane wallahi da ba'a kusa damu kike ba da yanzu bansan yaya rayuwar mu zata zama ba saboda babu wanda yake kula damu shi kansa Abbi yanzu neman wanda ze sauta shi ya ringa kula dashi yake kina kallo se ayi sati ni kadai nake kwana acan gidan kuma be damu da ya san Ina sauran suke ba, ba'a bamu abinci acan gidanΒ  to Mami idan bakya nan waye ze bamu? ina zamuje waye ze nemo mu idan be gammu ba?"

Kamar wadda aka watsawa ruwan sanyi haka naji nayi shiru ina jinsa su kuma sunaΒ  ci gaba da kuka tareda fadar maganganu dan Allah na dawo gidan su.

Ajiyar zuciya na sauke me qarfi jin ba mutuwa akayi ba, amma zancen rayuwar su da sukayi ya tabani hasaso yanda suke garari tsakanin gidajen nayi a fili na furta "hasbunallahu wani'imal wakeel" Dagaske da bana tare dasu yaya rayuwar su zata kasance? Ina zasu je su samu gatan da uwa take bawa danta? Waye ze kulamun da tarbiyyar su? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Ni Asma'u yanzu yaya zanyi duk me yasa banyi wannan tunaninba nake shirin yanke wa kaina shawara??

Gaba daya kukan nasu ya dagulamun lissafi nama rasa abinda zance musu, dakyar na iya saka hannu ina bubbuga bayan yan biyu nace

"Ya isa ku dena kuka akan wannan maganar ce zaka tara mun yara saboda wulaqanci ka saka su kuka kai bazaka iya zuwa kai kadai ka same ni ba se kun tayar mun da hankali?"

"Mami bani na gayyato su ba ki tambaye su gasu nan duk tare mukayi magana kowa yana cikin damuwa mun kasa zuwa mu tunkareki shi yasa nace mu taho yanzu ki tausaya mana Mami mu koma irin rayuwar da muka tashi a cikinta" Gwani na gwanyen ya sake fada.

Seda nayi dagaske kafin sukayi shiru na tattara su suka fita suna sake maimaitamun na taimake su na tallafi rayuwarsu na koma gidan Babansu, wai harda yan biyu kai wannan abun ma yafi kama da wasan kwaikwayo tabbas shiri ne Kuma Bashir ne ya shirya shi. Shiyasa dazu kenan gaba daya suka fita ashe gurinsa sukaje ya yiwo musu huduba ta nan ya zagayo kenan tunda ya kasa yi da kansa.

Duk yanda naso na share maganar daga zuciyata na aiwatar da abinda nayi niyya tun farko kasawa nayi da gaske ina tunanin makomar rayuwarsu. Yanzu muna tare bani da tabbacin idan nayi aure Yusuf ze barni naci gana da zama a nan dukda ya ce ze bari kuma nasan ko za'ayi yaya Bashir baze bani su ba kai ni kaina bazan kai yayana Agolanci wani guri ba bayan ubansu nada yanda ze riqe au to yanzu yaya zanyi??

Abu guda uku ne, kodai na haqura na koma gidan Bashir nayi zaman Yayana, ko kuma na auri Yusuf na zubar dasu ko kuma na hauqra da duk biyun na rungume su mu zaunaba tareda na sake wani auran ba wanda na tabbatar bame yuwu bane dan baza'a barni nayi hakan ba to dole cikin zabi biyun farko kuwa na dauki daya, wannene mafita? Komawata gidan Bashir bayan duk abinda ya faru ko kuwa sabuwar rayuwar da nake yaqinin samun chanji a cikinta?? Mene kuma makomar Yarana??

Saboda tunani har wani mugun ciwo kaina ya dauka, dare yayi qarfe sha biyu harta gota amma haka na danna kiran lambar Goggo ba tareda tunanin tsufanta ba karna tayar mata da hankali nima ina da buqatar magana da uwata ne in nemi shawararta tunda tana sona tana kuma jin irin abinda nake ji yanzu akan yarana baznaso na yanke shawarar da zata tauye rayuwarsu a gaba ba.

"Asma'u lafiya? Meya faru kike kiran waya a daren nan" ta fada bayan data daga kamar me jiran na kirata.

"Kiyi haquri Goggo na tasheki daga bacci" na fada a sanyaye, se tace mun

"Ba bacci nake ba, kin ganni ina ta salloli ne da addu'a wane bacci zanyi yanzu Asma'u nida nake da buqatu nake da yaya da nake nema musu shiriya kullum a gurin Allah"

Maganar ta kawai se naji ta sakani kuka dukda bansan kukan na menene ba.

"Goggo dagaske na haqura da Bashir badan na dena sonsa ba sedai kawai hakan shine maslahar zuciyata bazan taba samun yanda nake so a gurin sa ba zan qare rayuwata cikin qunci da ciwon rai da baqin ciki shiyasa na zabi haqura dashi amma Goggo yaya makomar yarana zata kasance idan na auri wani daban na tafi na barsu?

Matarsa ba zata iya riqe min suba bansan yaya tarbiyyarsu zata kasan ce ba musamman a gari kamar Lagos Goggo dama a Gombe ne akwai wadanda zasu saka ido akan su saboda su Goggo bazan iya tsallake wa na sake wani aure ba ki bani

Please Login or Register in order to submit comment