Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abinci baya yanke wa agidan sa koda kuwa ba dadi dama ya dade yana don zeey taƙi yadda amma saboda tana gani kamar basu dace ba,lokacin da baban ta ya ce mai yazo zai bashi auren ta sosai yayi farin ciki sai dai kuma ance mai ita yanzu ba budurwa bace sai da aka faɗamai duk abinda ya faru gudun kada yace an cuce shi sannan ya amince akai musu auren Yana da mata guda ɗaya da yara gida ɗaya aka hadusu da zeey dan haka hidimar gidan tayiwa zeey yawa sabida girki ɗaya suke yi _______________"To yanzu da kike Wannan maganar ina zaki samu kudin da zaki tafi Lagos ajirgi? "Kasan Allah bash saina bisu Lagos din nan karkaji yadda zuciya ta takemin zafi yadda ya nuna Rufy tafini mahimmanci harda hawa jirgi ya barni a wajan "Yazakiyi abinda ya faru ai ya faru yanzu sai ki shiryawa dawowar su kisan abinyi Amma binsu bashine mafita ba "Ni duk ba Wannan ne ya tsaya min araiba bash tunda suka tafi kwata kwata bai kirani ba ni naƙi kiran shi sabida na nuna nayi fushi ya bani hakuri shine shima ya share ni watakon bani da matsayi ya samu matar shi ko Ko a online bayamin magana kuma yana hawa bare yace bayayi "To ai ke saiki kirashi tunda ke kike buƙatar shi bashike nan ba Waya jamsy ta ɗauka ta danna kiran wayar Ibrahim dai dai lokacin shi kuma ya fita siyo maganin da aka rubutawa Rufy kuma yabar wayar a wajan dan haka har kiran ya katse ba'a ɗaga ba dan haka ta sake kira cike da kunar zuci sabida bai daga wayar ta ba Haka tayi ta ringing nana ba ba'a ɗaga ba harta kusa katse wa taji an daga cike da kashe murya ta fara magana "Hello baby shine ko daga wayar tawa bakayi ba Kuma tunda katafi baka kirani ba bare kaji ya nake "Kiyi hakuri bashi bane abokin sane baya kusa yaje siyo magani Hafiz ya bata amsa cike da jin haushin ta dan gaba ɗaya jamsy bata masa ba tun ransa ya fara ganin ta da Ibrahim "Ohhh sorry amma ina babyn ya tafi waye kuma ba lafiya? Ta jefomai tanbaya "Cike da kosawa da jin maganar ta yace matar shice ba lafiya muna asibiti idan ya dawo zance kin k.... Dai dai lokacin Ibrahim ya dawo dan haka ya miƙamai wayar ba tare da yace komai ba sabida gaba ɗaya jamsy batai mai ba Gani mai kiran yasa Ibrahim ya kara wayar akunnan shi dai dai lokacin kuma da yake cewa Rufy "Kinci abinci? Kai kawai ta ɗaya mai ba tare da tayi magana ba Dana haka yace "Tashi kisha magani to kinsan dai dole sai ana shan magani akwme warke wa Duk abinda ke faruwa jamsy naji dan haka ta ƙulu iya ƙuluwa saboda me ya ɗaya wayar ta kuma zai tsaya magana da wata Ibrahim kuwa yama manta da wayar da ya kara akunann shi gaba ɗaya sai da jamsy tayi magana ya tuna "Hello baby kana jina kayi shiru! "Oh sorry ina asibiti idan na koma gida zamuyi magana Daga haka ya kashe wayar ba tare da ya jira abinda zata ce mai ba Sosai abinda Ibrahim yayi ya ɓata ran jamsy watakon bata da matsayin da zai tsaya ya saurari abinda take cewa shine zai ce yana asibiti idan ya koma zai kira ta har yaushe Rufy ta samu matsayi haka azuciyar sa yaushe ya fara sonta haka har yake tanbayar taci abinci.... "To komai dai ciki ne da ita? Zuciyar ta ta jefo mata tambaya take gaban ta ya faɗi da sauri ta tashi tsaye tana faɗin ina wallahi bazai yiwu ba ba yadda za'ai ace Rufy tan da ciki har yaushe ma Ibrahim ya fara son ta da za'a ce ya mata ciki.. Gani surutun da take ba mai bullewa bane yasa da sauri tafita waje domin kuwa tabbas komai zai faru dole gobe taje Lagos sai dai kawai su ganta idan ta sauka agarin ta kira Ibrahim tace yazo ya dauke ta Da wanann tunanin da take ne ta hau napep ta nufi nasarawa GRA zuciyar ta cike da tunanin kala kala. Ta saƙa wancan ta ƙulla wancan naso yafi haka Bani da chaji ne lokacin da aka kawo kuma dare yayi idan na tsaya typing zakuyi bacci banyi Posting ba ngd🥰 🍃🍃 SECONDARY SCHOOL🍃🍃 (Love& romantic story) Shalele ce💃 Paid page 55&56 ___________Washe gari aka sallami Rufy bayan anyi musu bayanin ta daina shan kayan sanyi da kwana cikin Ac Sannan suka tafi gida ranar ma sai da hafiz yazo shida matar shi a wannan dan zaman asibitin da sukayi sosai suka fara sabawa tsakanin su,kuma anan ne matar hafiz ta fahimci akwai matsala tsakanin Ibrahim da matar shi duba da yadda suke rayuwar su sosai ta fahimci akwai wani abu a ƙasa domin a matsayin su na ma'aurata ya kama ta ace kulawar da suke bawa junan su yafi haka Lokacin da suka koma gidan yayi kura dan haka matar hafiz tace zata share musu anan ne ta kuma fahimtar wani abu sai dai bata nuna musu ba har suka tafi nasu gidan bayan tayi musu abincin dare sunci su duka hudun Bayan tafiyar su hafiz ne Ibrahim yaje wajan sai da katifa siyo mata yayi sabida baya tunanin zai iya kwana waje ɗaya da ita lokacin da ya dawo harta kwanta akan shinfiɗar ta Sannan ya tashe ta yasa mata katifar ta kwanta sabida ba kwari jikin ta sai ahankula Washe gari da asuba da tayi Sallah a wajan ta koma ta kwanta ba ita ta tashi ba sai wajan ƙarfe goma sosai ta tsorata ganin lokacin da ta kai tana bacci gashi ɓatamai abincin da zai ci ba,falo ga fito sai dai baya nan dan haka ta wuce kitchen din da sauri Plas ta gani an ajiye a kan kitchen cabinet din sai jug a gefe budewa tayi kunun gyaɗa ne a jug din Mai zafi yasha madara cikin plas ɗin kuma doya ce da aka soya taji kwai sosai, tunani ta shiga yi to wannan abincin fa waya aje mata ko kuma dai shiya siyo zaici sabida bata yimai ba,ganin flat da cup a gefe wanda aka ci abu acikin hakan yasa ta gane ya riga da yaci nasa dan haka ta ɗauka tayo waje zata ci,ta kadda ta gani ya aje akan tum tum din dake falon dauka tayi ta buɗe "Ga abinci nan a kitchen kici sannan Kisha magani kar kiyi girki zan bayar a kawo miki Batasan sanda murmushi ya kwace mata ba sosai taji daɗin yadda ya nuna kulawar sa akanta tun daga zuwan su asibiti har zuwa yau Wajan azahar aka kawo mata abinci mai rai da lafiya taci ta koma ta kwanta zuwa yamma ta tashi tayi shara tasa turaren wuta afalon Da daddare tuwan shinkafa ya tawo musu da shi take away biyu yasha man shanu sosai yayi wa Rufy dadi kamar me Washe gari da safe taji daɗin jikin ta sosai dan haka ta tashi da wuri tayi musu abin karyawa sannan ya fita har lokacin ba wata magana tsakanin su bayan ta gaishe shi amsawa kawai yayi ya tanbayi jikin daga nan bai kuma cewa komai ba har ya fita Yana hanyar zuwa wajan aiki ne yaji wayar sa na ƙara yi yayi kamar bazai dauka ba sai kuma ya duba jamsy abinda yagani kenan har kiran ya katsa bai daga ba wani kiran ya sake shigo wa shima sai da ya kusa katsewa sannan ya ɗaga "Hello jamsy ina hanyar zuwa aiki ne kike kirana ya akai? "Haba baby ya zan kira ka ka dinga tanbaya ta ya akai tun da na kira kasan dole da yadda akai ai "To naji yanzu dai faɗamin ina da abinyi sauri nake "Ok dama so nake kazo ka ɗauke ni na sauka Airport yanzun nan... "Bangane kin sauka Airport yanzun nan ba daga ina kuma ina zaki ? Ibrahim ya tanbaya cike da neman karin baya ni "Baby wannan wacce irin tanbaya ce tunda kaji nace kazo ka ɗauke ni ai kasan Lagos nazo ko... "To ai sai ki kira wanda kika zo wajan su amma ni bamuyi dake zaki zo ba kuma bansan ya zanyi dake ba gaskiya "Baby ko dai baka gane mai magana bane jamsy ce fa..kuma da kake maganar nakira wanda nazo wajan su wajan wa zani to idan ba kaiba suprise din ka nayi fa "Gaskiya bana buƙata idan inason ganin ki dole kinsan zan nemeki muma ahalin yanzu ma ni aiki ne dani bani da ishashshan lokacin kuma Rufaida bata da lafiya so kinga zama gidan mu bai kama kina kenan Daga haka ya katse wayar kasan cewar ya ƙaraso wajan aiki Sosai maganar Ibrahim ta ɓatawa jamsy rai bata san me yake nufi da ita ba kenan tayi wahalar banza yake nufi ko me!kuma ma da yake maganar Rufy ba ta da lafiya meye nata acikin to Shawara ta yanke akan ta rabu dasu shi sai weekend ta neme shi su hadu *********** Yanzu haka cikin indo yayi girma sosai ya shiga wata na takwas ta dawo zama da ƙyar tashi da ƙyar zuwa yanzu inna ta daina fushin da ita sabida yanzu ta zama abin tausayi,sai dai abinda inna bata sani ba har yanzu indo tana ma'amala da habu sai yanzu ne da cikin ya kuma girma ta hakura shima sabida idan sunyi fama take da ciwon baya Zaune take a tsakar gida tana cin abinci,kallon inna tayi tana faɗin "Yanzu kenan inna idan na haihu shike nan nima na sama umma kuma zan dinga bawa yarona nono yana sha ko? Kallon ta inna tayi cike da mamakin shashancin indo wata kon ita burin ta ace mata umma kuma ta bawa yari nono yasha shi kawai take so bata san hadarin dake tare da haihuwar ba ko gudun abin kunya ita duk wannan bai dame ta ba.... "Inna nayi magana kinyi shiru ko ni bazan ba yaron nawa nono ba kuma ma ai naga baya fitar da ruwa yanzu ya zanyi kenan idan na haihu? "Banason shashancin da hauka indo ke duk wannan masifar da kika samu ba itace gaban ki ba kawai ki bawa yaro nono kike so ko...to indai haihuwa ce gaki gatanan zakici gidan kune Inna ta faɗa cike da ɓacin rai Shiru indo tayi tana suna nin maganar inna ita dai tasan batayi abinda za'a mata faɗa haka ba amma ji yadda inna take mata bala'i kuma dai ɗane idan ta haifa dole yace mata umma kuma ta bashi nono ita ma ************Kwanan ta uku sannan ta kuma kiran Ibrahim a waya zuwa lokacin gaba ɗaya ya manta da babin ta sabida aikin da ya shamai kai a kwana kinnan Ta nemi su hadu a wani wajan shaƙatawa kuma ta amince zaije dan haka take ta shirye shiryen yadda zata ja hankalinsa idan yazo tayimai maganar aure Bayan sallar magariba ya isa wajan da sukayi da shi zaune ya same ta tasha riga da wando matsatstsu sai wani yauƙi take ita ba kuɓewa ba Tasowa tayi zata rungume shi ya daga mata hannu "kinga baki ganin cikin mutane muke ne Ya faɗa yana zama cikin daya daga kujerun wajan "Kiyi sauri muyi maganar da kika ce sabida ina sauri ne zanyi baƙi.. "Nikam gaba ɗaya na kasa gane kanka baby kwana biyu duk ka canza kamar ba kaiba gaba daya baka nuna farin ciki da gani naba ko kuma ka daina sona ne bansani ba ? "Basai sonki ne banayi ba jamsy amma yaka mata kigane nazo Lagos aiki ne bawai soyayya ba dan haka bani da ishashshan lokaci "Okay to naji,tunda haka ne to kawai ka aure ni mana ba shike nan ba kaga daga nan sai na dinga taya ka wasu aikin naka koya kace! "Eh naji amma gaskiya wannan abun bazai yiwu ba gaba ɗaya yaushe nayi auren yanzu a kuma jin zanyi wani ai kinga da matsala "A'a toba zai ka faɗa musu matar ka ba budurwa ka aura ba cutar ka akai kaga shike nan za'a bamu damar auren junan mu Ta ƙara sa maganar tana fari da ido cike da hango alamar nasara "Gaskiyar magana hakan bazai yiwu ba jamsy koba komai mahaifin Rufaida aminin Baba nane to bazan iya tozar ta shiba ko wani daga cikin a halinsa "Ban gane ba to yanzu me kake nufi zaka cigaba da zama ne da wacce take neman maza koya dan asara duk wani uba ai yanaso ya samawa yaranshi uwa ta gari koba haka ba Ta faɗa tana tsare shi da ido dan taga yanayin fuskar shi Shiru yayi yana tunanin gaskiya ne maganar jamsy uwa ta gari ta ke bada yara na gari kuma a gaskiya kwata kwata Rufy bata dace da shi ba Kallon ta yayi kamar zai magana sai kuma yayi shiru "A'a baby kayi shiru kace wani abu mana "Haka ne maganar ki amma zanje gida inyi tunani duk yadda ta kama zamuyi waya Daga haka ya tashi yabar wajan zuciyar shi cike da tunani kala kala akan maganar jamsy Ihun farin ciki tayi ganin alamun nasara a tafiyar tata Dan haka tace "Muje zuwa. . 🍃🍃 SECONDARY SCHOOL🍃🍃 (Love& romantic story) Shalele ce💃 Paid page 57&58 __________Sosai maganar da sukayi da jamsy ta sashi tunani a haka har ya dawo gida, lokacin da ya shigo Rufy ta cikin aeke mai abinci dan haka tamai sannu da zuwa sannan ta shiga dakin ta Da kallo ya bita sosai yarinyar wani zubin take jefa shi cikin tunani yadda take a nutse haka bata da haya niya baza'ai tunanin zata aikata ba Haka dai ya kwana yana wannan tunani da jamsy ta maƙalamai Washe gari kuwa yana cikin karyawa hafiz yazo tare da matar shi da niyyar zata wuni wajan Rufy sosai Rufy taji daɗin hakan sabida ita kanta ta gaji da zaman shirin da take fama dashi gaba ɗaya kaɗaici ya ishi rayuwar ta Bayan ta fitar su Ibrahim wajan aiki sosai Rufy ta saki jikin ta da matar hafiz suka sha hira a wannan yinin da sukayi tare sosai matar hafiz ta kuma fahimtar abubuwa da yawa akan Rufy Dan tunda mazan su suka fita kwata kwata batayi maganar Ibrahim ba ko sau ɗaya haka kuma bataga ya kira ta awaya ba ita ma kuma haka sai abin ya bata mamaki dan haka ta kasa shiru tayi niyyar tanbayar ta ko suna da wata matsala a cikin zaman su "Nikuwa sister dan Allah na tanbaye ki wani abu idan ba damu ? Kallon ta Rufy tayi kafin tace "A'a ba damu tanbaye ni Allah yasa na sani "A'a wallahi kin sani sai dai idan zaki ɓoye min Dama wani abune yake ban mamaki keda Ibrahim kamar ba auren saurayi da budurwa ba, kamar ba masoya ba,kwata kwata bakwa nuna ƙaunar junan ku,ba nuna kulawa,bare ku dinga kewar juna Tunda nazo kwata kwata bakiyi maganar Ibrahim ko sau ɗaya ba Ni kuwa nayi maganar hafiz yafi sau ashirin ga wayar da muke akai akai ya ƙirani ko na ƙirashi dan muji ya kowanne mu yake amma ke ko sau ɗaya baki kira Ibrahim ba shima kuma haka Sannan da zasu tafi ba nuna alamar zakiyi kewar shi hasalima ko raƙashi bakiyi ba kanki na ƙasa kika ce Adawo lafiya shike nan Shine abun wake bani mamaki wannan wanni irin aure ne haka Rufy da tayi shiru tana sauraran abinda matar hafiz take cewa murmushi tayi wanda ya tawo tare da hawayan da ya taru a idon ta Kallon ta tayi tana faɗin "Na yarda dake na ɗauke ki kamar ƴar uwa ta dan haka zan baƙi labarin rayuwa ta yau tare da abinda ko iyaye na basu sani ba Sunana Rufaida amma friend dina suna cemin Rufy ni ƴar Kano ce shekara ta Ashirin da biyu............. Sosai matar hafiz tayi kuka ta kuma tausa yawa Rufy fiye da tunani tabbas Rufy ta faɗa sharrin ƙawa ne kuma gashi yanzu taba bibiyar lamarin ta Kallon Rufy tayi da fuskar ta tayi jaga jaga da hawaye da majina tayi kuka kamar ranta zai fita "To yanzu ina ita jamsyn take ne? Matar hafiz ta tanbaya cike da neman ƙarin bayani "Bazan iya ce miki ga inda take ba nasan dai mun barota a airport ranar da zamu tawo kuma ita ce wadda ta kira Ibrahim ranar da ina asibiti "Shike nan aniyar ta ta bita amma yanzu ba zamane ya kamaki ba dole ne kisan yadda zakiyi ki janyo hankalin mijin ki zuwa gare ki koda kuwa ta kasan ce ya auri jamsyn ya kasance kema kina da matsayi a zuciyar sa bawai kiyi ta tafiya a matsayin bora ba "To taya kike ganin zan samu wannan matsayin duk macen da kika ganta cikin jin dadi a gidan mijin ta to takaimai budurcin ta ni kuwa fa ! Kallon ta matar hafiz tayi tabbas abinda ta faɗa gaskiya ne to amma itama idan taji gyara komai zai dawo dai dai "Karki damu zamuyi gyaran jiki wanda zai sa wajan ya matse kamar ba'a taɓa shiga ba kuma dole ne ki san yadda zakiyi ki jawo hankalin mijin ki domin ko baya sonki to tabbas akwai tausayi tsakanin ku kinga nan ma wata nasarar ce Dan haka yanzu abinda zamu fara da shi shine gobe zamuje siyayya dole ki dena zama da wadan nan hijja ba zamu siyo ƙananan kaya domin sune zasu zama na sawar ki indai yana nan "Ƙananan kaya kuma gaskiya bazan iya sawa ba idan yana nan bare kuma na fito Rufy ta faɗa kamar zatayi kuka "Ai kuwa ya zaman dole idan har munaso mu cimma buƙatar mu domin duk taurin kan namiji yaga kina jujjuyamai wallahi sanu sanu zai sakko Sannan zaki fara kokarin yin hira da shi ta hakane shakuwa zata shiga tsakanin ku ke da shi To haka dai suka ƙara sa wannan yinin suna tattana yadda za'a samu mafita sai dai a kwai abubuwa da yawa da Rufy take ganin baza ta iya ba Da yamma tayi tare suka shiga kitchen sukayi tuwan semo da miyar kuɓewa,sannan matar hafiz tasa aka dafa shayi yasha kayan ƙamshi sabida garin da sanyi sanyi ***********Wunin yau gaba ɗaya sai a hankula yayi aikin sabida tunanin da ya addabi ƙwaƙwalwar sa zuciyar shi ce ta tanbaye shi "A ina jamsy tasan cewa Rufy ba budurwa bace? Girgiza kai yayi alamar bai sani ba dan shi dai yasan bai gaya mata ba iyaka yace auren haɗi akai musu ba tare da suna san juna ba shike nan to amma a ina ta samo wannan maganar tabbas akwai wata a ƙasa Da sauri ya tashi tsaye wajan jamsy zashi ya jiyo inda taji wannan labarin Wayar ta ce tayi ƙara dai dai sanda ta fito daga wanka ƙaran kiran ne yasa ta ƙara so da sauri sabida mutum ɗaya ne yake da wanann ringtone din da sauri ta ɗaga "Kizo mu hadu inda muka hadu jiya yanzu ina jiran ki Iya abinda yace kenan ya kashe wayar Da sauri ta fara shiryawa sabida karta ɓatamai lokaci Bayan ta gama ne ta fara yiwa wanda ke kwance kan gadon magana "Alhaji nifa na shirya ka sallameni zan wuce ana jirana Kuɗi wanda ta kira da alhajin ya dakko ya bata zasu kai dubu hamsin ta karɓa tayi gaba dan burin ta taje taji kiran me Ibrahim yake mata Lokacin ta ta ƙara so harya tashi zai tafi dan ya gaji da jira gashi yana da aiki a office ya fito Bako sallama haka ta zauna a wajan tana faɗin "Sorry baby na barka kana jirana wanka nake ne lokacin Okay kawai ya iya ce mata ya tsaya yana ƙare mata kallo jamsy ba mummuna bace sai dai tayi kama da waɗan da idon su ya bude ga bakinta yayi kamar tana san wani abu,ganin kamar zan shiga zargi kuma yasan ba kyau hakan yasa ya kawar da wannan tunanin ya fara mata magana "Dama akan maganar da mukayi jiya ne tabbas nayi tunani abinda kika faɗa gaskiya ne sai dai kuma wani abu da ya bani mamaki taya akwai kikasan Rufaida ba budurwa bace waya faɗa miki ? Ya jefa mata tanbayar yana tsare ta da ido "A'a...ba kaine ba ka faɗamin lokacin da muka hadu da kai Ta faɗa cike da alamun rashin gaskiya tare da ita "Ni kuma jamsy gaskiya ki sake tunani dan banyi wannan maganar da ke ba kwata kwata sai dai idan wani wajan kika jiyo Shiru tayi tana tunani "Nashiga uku surutu na zai jawomin ya gano koni wacce amma bazan bar hakan ta faru ba dole na san mafita "Kinyi shiru kin barni ina magana ni kaɗai a ina kikaji wannan maganar? Ya sake jefa mata tanbaya "Tunani nake sai dai kuma baby na kasa tunawa sai nake ganin kamar kaine ka faɗamin idan ba haka ba a ina zanji "Kinga a rayuwa ta banason munafirci idan har kinaso alaƙa ta da ke ta dore to tabbas ki fito ki faɗamin gaskiyar inda kikaji wannan maganar Daga haka ya tashi yabar wajan Zama tayi ta zuba tagumi garin neman hanyar shiga tana neman ta fita yanzu me zata ce mai idan ya kuma tanbaya tabbas ya zama dole tasan abinyi kafin lokacin *********** Sanda suka dawo gida sosai yadda hafiz da matar shi suka tari juna ya burge Rufy da Ibrahim sabida sun nuna iya wannan yinin sunyi kewar junan su Wannan shine karon farko da Rufy ta taɓa karɓar jakar Ibrahim bayan ya dawo, shima sabida matar hafiz ta mata nuni da hakan ne Dan haka ta karɓe tana faɗin sannu da zuwa sai yaga abin wani iri sabida bai saba ba,hanyar ɗakin shi tayi cike da fargaba domin wannan shine karon farko da zata shigar mai ɗaki Bayan ta dawo ne ta tarar matar hafiz ta zubawa mijin ta abinci sannan ta sa hannu sun fara ci suna hira Zubawa Ibrahim Rufy tayi dan wannan shine karo na farko da ta fara zubamai abinci tashi ta so yi zata bar wajan matar hafiz tace "A'a ina kuma zaki ke da kike ta cewa yunwa kike ji kisa hannu kici idan kun gama sai ku rakamu mu tafi karmu ta kure ango da amaryar sa Ta ƙara sa maganar tana dariya ƙasa ƙasa "Da gaskiyar ki sweetie Dan da ganin abokin nan nawa kinsan lamarin sa ba sauki Hafiz ya faɗa yana mai dariyar shakiyan ci Gaba daya kunya ce ta rufe Rufy jin maganar da sukeyi duk sai tayi wata irin kunya ta kamata gashi hannun ta cikin kwano ɗaya da Ibrahim duk sai ta jita a takure "A'a amarya ya dai naji kinyi shiru ko duk cikin salon korar mune Matar hafiz ta faɗa tana dariya Rasa abin faɗa yasa Rufy cewa "A'a kuyi zaman ku ba komai To bayan sun gama cikin abincin ne Ibrahim ya tashi zai rakasu amma matar hafiz tace

Chapter 9 of 16