Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 3
mut. Cikin kasala ya zauna gefanta. Kansa ya d'auki zafi shin kodai gamo yai ake neman rikitashi. Mi'ka tai ta farka tana fad'in "wash" da sauri ta ware ido tana masa kallon mamaki "hubbyna lafiya kadawo?". "Lafiyarki nazo gani Najwa amma miyasa bakyasan adu'a inkin farka?". Cikin shagwa'ba tace "hmmmmm hubbyna mantawa nayi amma zan kiyaye, hope kamun afuwa?". Ta fad'a tan langa'be kai cikin murmushi ya ri'ko hannunta tai saurin zamewa sabida jitai kamar antsikara mata alura. Da sauri ya dubeta sai taimasa nuni da kumburin hannunsa. Sai lokacin ya tuna da ciwan " miya sameka" ta fada tana 'ko'karin barin kusa dashi. "Oh! Najwa faduwa nai bari inje a gyaramun, a gurguje yai mata bayanin samun aikinsa taimasa fatan alkhairi. Yana fita tai tsaki ta yamutsa fuska ta soma gyara dakin. Muje dai....... 'KADDARARMU CE!. SANAH S MATAZU. 19-20. Satin hannun Mustapha d'aya ya warke zuwa lokacin ya shiga duhu sossai abisa lamarin Najwa. Yau da wuri ya dawo aiki sabida gajiya sossai a tare dashi yana shigowa Najwa tana zaune kusa da saurayin daya gansu a mota baiyi wata-wata ba ya rufeta da fad'a kamar yaci babu da haka ASHIQ ya shammaceshi ya 'bace 'bat. Najwa cikin masifa tace " kagafa nagaji Mustapha walahi nagaji da takurawarka idan kadaina sonane ka sauwa'kemani inhuta basai kayiman shariba. Ina zaune ni kad'ai a d'aki zakace nida wani". Cikin zubar hawaye yace "shikenan Najwa kije na sakeki saki d'aya" Cikin fashion hankali ta d'ora hannu akai "Mustapha karkaimun haka, ina zan dosa ina nakama wazai fuskanceni bayan na'ki kowa sabida kai, dan Allah ka tausayamun".Cikin hawaye yace "Najwa kisa a ranki 'KADDARARMU CE a haka bazan iya cigaba da zama dake ba". Cikin kuka tace "Walahi walahi Mustapha sai kayi nadama sai kayi dana sani da Lanka sai kazo kana nemana". Daga haka ya bar gidan Najwa jikinta yai sanyi saita sami kanta da fad'uwar gaba. Tunaninta ina ta nufa haka ta zari kayanta kala biyu ba wanda ta kula ta nufi gida. Tana shiga yayarsu ta dubeta da alamun tambaya duk ta hargitse a ta'kaice tace mata "sakeni saki d'aya". "Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Najwa mekikai masa haka yadda yake sanki harya sakeki?". "Oho masa shiya rasa ko yanzu nai kwalliya na fita miji zan samu". Ta wuce tana kad'a jiki ta wurgawa Inna harara tuni ta sunkuyar da kai 'kasa. Tunda Najwa ta tafi Mustapha ya tsinci kansa cikin damuwa yanasan yaje gidan biko sabida fad'an Mamarsa. Amma daya tunkari hanyar gidan saiya rasa gane gidan yai d'imuwa. Mama tayi tayi ya fad'amata abinda ya had'asu ya'ki ta tattarashi ta watsar. Nan da nan ya sussuce ya koma 'kazami kullum cikin damuwa. Najwa tunda ta dawo bata zama yawan yau daban na jibi da daban, tun Husnah nai mata magana har takaisu ga gaggarumin fad'a babu wanda ke kula kowa cikinsu.Aikuwa ko cangal batayi ga tara samari matar dako iddah batai ba.'Yan'uwanta sunyi fad'an sun gaji sun ha'kura. Har gida Yaya Zainab tasa aka kiramata Mustapha amma babu batun amsar komawa 'karshe yace mata zaiyi shawara bai sake dawowa ko kiransa tai baya zuwa hakama lesson ya daina zuwa kwata-kwata.Saidai kullum tinanin Najwa na hanashi sukuni saidai ya zauna yaita shinshina kayanta yana kuka. Yauma Najwa tun safe tafita sai magarba ta dawo. Kuma wani ikon Allah indai tafita sai ASHIQ yai dabarar had'uwarsu waje d'aya da Mustapha. Cikin sassarfa ta shiga gida jarkar faro ta gani ajiye zatanta ruwane ta ganshi garai-garai ashe ruwan tofine yayarsu ta kar'bowa Inna wajan Leman cikin hanzari ta d'auka ta soma sha ba tsayawa. Tsawa biyu ta ratsa kunnuwan Najwa lokaci guda, tsawar yayarsu data ASHIQ cikin fad'a take tambayarta miyasa take shamata zatan Najwa siya tai shiyasa ta kara kafa kai da mugunta. Shikuwa ASHIQ takaici ya kasheshi ganin za a wargaza masa shiri sabida tofin ayoyin tsarine wata muguwar sha'ka yakaimata take ta saki jarkar tana kakkari amma ina. Tuni ruwan ya shiga cikinta. Da sauri yayarsu ta tareta tana tambayarta men ene? Dai-dai lokacin ya soma nuna Najwa yana fad'ar kinyi kuskure saidai duk yun'kurinsa ya kasa aiwatar da komai a kanta. Cikin rawar murya tai niyyar gaya mata waye ASHIQ ga mamakinta a wannan karon bakinta yana magana sa'banin shud'ad'din lokutan da suka wuce" Yaya ASHIQ shine shine shine yaiwa Innarmu haka........." Take bakinta ya karkace hallitarta ta sauya daga Najwa zuwa mummunar hallita. KUNEMESHI A KASUWA KATANGAR KARFE ZAI KOMA An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3