Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
Najwah ki kwantar da hankalinki kiyimun bayani". Kasacewa komai tayi. *********** Kawai saita samu kanta da yimasa 'karya" dama kiranka nai inbaka ha'kurin abinda Inna tayiwa wakilanka" "dakata Najwa Innafa mahaifiyatace menene abin bada ha'kuri a ciki? Kar insake ji kinji ko". Kawai saita fashe da kuka "yanzu Mustapha kanji kana gani zata rabamu? Kasanfa munasan juna, gaskiya kai wani abu". Cikin dauriya yace "me zanyi Najwa?". "Mustapha kawai mugudu". " subhanallah haba Najwa idan rai ya 'baci hankali baya gushewa, Inna ta isa damu ta isa komai a kanmu bazanso ki gujewa mahaifiyarki sabida niba, kisani idan ubangiji ya nufa muna da raban kasancewa babu wani mahalukin dazai hana idan kuma 'KADDARARMU CE a haka bamu isa hanawa ba. Abinda fa ha'kuri baibamuba rashinsa bazai bamu ba". Jikinta yai sanyi cikin shagwa'ba tace to ani banasan auran dole kuma ba kyau ko a addinan ce kodai ka daina sonane?". Cikin sautin jan hankali yace "Najwaty! Ajiyar zuciya tai ya cigaba Najwa True lovers are like upper & lower eyelids!.They often meet because they miss each other and when they meet, they don't see the world around". Najwa tai shiru kalamansa nai mata dad'i cikin jan hankali yace "Najwah say me something please"( Najwa kice mun wani abu can Allah). Cikin so shau'ki 'kauna tace " Mustapha!! MY HEART IS LOCKED KEYS ARE WITH U OPEN AND SEE HOW MUCH I LOVE YOU". Kawai saita katse layin tana tsananin jin nauyi tamkar yana kallonta. Cikin hanzari ta shiga band'aki ta gyara jikinta tayo alwala lokacin har biyar tayi. Kubiyoni A daran Zainab ta kira sauran 'yan'uwanta Fiddausi Maryam Saudaht tace su had'u gida da safe sabida tattauna matsalar Najwa. Ta kira Husnah tace ta gayawa Inna Najwa na gunta kar hankali ya tashi. Haka Najwa ta kwana sukuku da'ita, washegari drivern Zainab ya d'aukosu zuwa gida. Tun a hanya gaban Najwa ya dinga mugun fad'uwa tana jin kururruwa a kunnuwanta kamar ana kiranta wasu lokutan har rufe idonta takeyi. Suna shiga layinsu taga taron mutane, abin ya tsoratata ya kuma bata mamaki gabanta ya cigaba da fad'uwa har suka wuce taran mutanan da makara zasu ma'kabarta. Ta dinga biybiyarsu da kallo har sukai parking suka fito. Gab da zasu shiga gida taji ankira sunanta, sai taji kamar muryar Mustapha cikin azama ta juya amma ga mamakinta ASHIQ ne cikin murmushi yake nuna mata takobinsa duk jini jikinta a hankali yaimata nuni da hannunsa saitaga MUS'AB kwance cikin jini. Wata giggitaciyar 'kara ta saki daga nan bata sake motsiba cikin sauri Zainab ta shiga gida da'ita. Abin mamaki tana shiga duk 'yan'uwanta na zaune cikin damuwa Inna har sharce hawaye takeyi, ganin sun shigo da Najwa ranga- ranga yasa sukai kanta suna tambayar lafiya. Cikin jimami tace " nidai muntaho lafiya 'kalau kawai sai ganin nai ta zube". Ruwa mai sanyi aka zuba mata ta saki ajiyar zuciya a hankali ta soma motsi can cikin 'karaji ta furta MUS'AB. Gaba d'aya wajan suka bita da kallon tausayawa banda Zainab data bita da kalon mamaki. Inna ta share hawaye "Najwa Mus'ab kuma saidai wani bashi ba ya tafi ya barmiki duniyar saiki zuba ruwa kisha". Cikin rud'ewa tace "Inna ya mutu? Dama mafarki na zama gaskiya? Allah kasa in farka daga wannan mummunan mafarki". Cikin jin haushi Maryam takai mata duka dama cike take da haushin anbawa Abdul auran Farida. Da sauri Zainab ta tare tana tambayar abinda yake faruwa. Inna ta share hawaye tace" Zainab tunda na kori mayen yaron nan da danginsa Najwa ta gudo gidanki jiya, a daran na aikawa iyayan Mus'ab sukace yau zasu aiko ai maganar auransu, yau muka wayi gari da mummunan labari wai Mus'ab ya mutu". Cikin tashin hankali Zainab tace "ya mutu?". Maryam tace "tabbas ya mutu ni walahi badan ance ya shiga dakinsa ya rufeba akajiyo ihunsaba kuma yasa sakata walahi tsaf zance Mustaphs ne ya kasheshi don gadon marasa imanine". Cikin sauri Saudaht ta doke mata baki " garin shegen kishinki saikin d'aukowa kanki masifa". Inna ce tai musu tsawa suka bari. Najwa kuwa jin ana neman la'kabawa Mustapha yasa ta had'e fuska tanasan furtawa amma tsoro ya hanata. Take idonunta suka sauya launi daga fararre tas zuwa jajjaye tamkar gauta. Wata muguwar sha'ka taiwa Maryam ta soma dukkanta tun sunaiwa lamarin kallon wasa saiya zama babba. Sunyi sunyi su 'kwaceta sun kasa bata saketaba saida ta 'bala mata hannu 'baras. Sunyi jigum suna kallonta zuciyoyinsu fal tashin hankali Maryam sai 'burarri takeyi Zainab ta dinga kallon Najwa cike da zargin wani al'amari amma tana tsoran furtawa. Bata tankawa kowa ba ta shiga dakinta tai kwanciyarta dukkansu suka kasa yimata magana tamkar an d'aure musu bakuna. Suka d'auki Maryam suka kaita wajan me gyara. Bayan sun dawo sukaje sukaiwa iyayan Mus'ab gaisuw. Najwa sai laasar ta farka lokacin duk yayyenta sun tafi gidajansu, bata ko kali inda Inna take ba ta shige bayi tayi wanka ta fito ta tada sallah azahar da la'alar ta had'a tana idarwa idonta yakai kan wata leda a d'akinta sai 'kyali take da sauri ta d'auka abin mamaki take a way ne ciki. Batai tunanin waye ya ajiyeba kawai ta bud',a ta hau ci. Husnah ta shigo kamar anjehota cikin masifa tace " Besty baki da imani Mus'ab ya mutu ko ajikinki ko?". "To dan ya mutu sai me? Nina kasheshi?". Yake jikin Husnah yai sanyi ta dinga yiwa Najwa kallon mamaki takai idonta kan abincin gabatanta "waya baki?" "Hmmmm! Sabida kinmaidani matsiyaciya banda kudin siya ko?". Husnah sai taji wani bambarakwai duk Najwa ta sauya mata. Jiki a sanyaye tai mata gaisuwa ta wuce.Tun daga ranar babu jituwa tsakanin Najwa da Inna, hakama Husnah ta kasa gano kanta. Najwa duk ta rame tayi ba'ki ga wasu 'kuraje a fuskarta da suka haddasa mata muni na bagaira babu dalili, hakan yasa duk ta tsangwami kanta ko fita batayi. Chat ta bud'e a wayarta wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajan d'aukemata hankali ga yin adu'a ko sallah tayi tana idarwa zata d'auki waya babu batun adu'a hakama bacci da ita take kwana a hannu. Mutuwar Mus'ab tana nu'kur'kusarta a zuciya hakan yasa mata yawan fargaba mai tsanani. Gani babu sarki sai Allah Inna ta soma janta a jiki tanai mata nasiha zatanta tunanin Mus'ab ne, cikin 'kan'kanin lokaci suka koma dai-dai. Maryam tasha jinya sossai hannu ya warke, saidai bikin Abdul da Farida babu abinda aka fasa. Tayi mitar tayi masifar a banza. A hankali fuskar Najwa ta washe ta dawo normal, suna waya da Mustapha lokaci lokaci yaso ya zo yaiwa Inna gaisuwa saidai tsoro ya hanashi. Yana shakar Inna matu'ka. Bacci yake jinsa yake kamar a farke a hankali 'kadangaran ya mi'ke a tsaye tamkar mutum yana murmushi yace "Mustapha ka cika taurin rai, nace kafita gonata kana neman yimun wasa da hankali sau biyu ina kawoma farmaki kana kufcemin, tabbas zaka tafi ma'kabarta tamkar yadda d'an'uwanka ya tafi cikin rashin tsoro yace " kai ma'kiyin Allah inshaa Allahu nafi 'karfinka, bazakai nasara a kainaba, wai kai waye? Kana neman takuramun fa". Take ya zabga masa wata bulala take Mustapha ya saki 'kara ya farka daga mafarkin abin mamaki da tsoro shatin bulallar rad'au a hannayansa harda kwailewa. Kansa ya d'aure yanasan sanin ainihin abinda ke bibiyarsa amma bayasan sanya kansa cikin hallaka. Adu'a yayi ya mi'ke yai wanka ya fita duk jikinsa a sanyaye. Mahaifiyarsa taitai masa nasiha daya shiga gaisheta zatanta ko batunsa da Najwa ne. Kai tsaye gurin Malamin Islamiyyarsu ya nufa Ustaz Yusuf, bayan sun gaisa yai masa bayyani, yai jim daga 'karshe yace ya bashi gobe zaiyi istihara. Washegari cike da azama ya koma saidai kalaman Malaminsu ya bashi tsoro da mamaki, bayan sun gaisa yace "gaskiyar magana Mustapha lamarinka 'boyyayan sirrine, domin nayi istihara jiya amma bana ganin komai sai wani wani duhu da 'bur'bushin wani 'karamin haske wanda ya rufeka, inaga mubarwa Allah komai mu durfafi adu'a domin ubangiji baya bacci". Haka suka rabu jiki a sanyayye. Ku dakace ni........ Cikin kwanciyar hankali soyyayarsu ta cigaba da bun'kasa a 'boye batare da sanin Inna ba, sukan had'u a gidansu Husnah ko inzata makaranta ko intaje weak end gidan Zainab. Ina na kula da takunta kwata - kwata ta daina maganar Mustapha ammafa kowaye zaizo nemanta bata fita, tayi hancinin tayi dukan harta gaji. Zama ba d'ankwali kuwa sai abunda ya cigaba, musamman yanzu da ake turomata style (samfir) na gyaran gashi da kitso a chat, wani abun birgewa har gashi ake d'auka bayan anyi parking ai disple picture dashi wato (Dp) ba tare da la'akari da wa kake chat ba. In tunaninki kinsan bakya bada numberki ga maza akwai masu had'a number haka kawai. Wata kuma duk sanda takai caji budewa suke su kwashi numbobi kawai dan san zuciya. A duk lokacin da Najwa tai Dpy na parking zakiji freind d'inta na yabawa itoko tanajin dadin haka. Har so take azo exfection a sch dan kawai a yaba gashinta. Kwanci tashi suka zana jarrabawar shiga aji shida ita da Husnah duk sunyi nasara. A hankali Mustapha ya soma zuwa gidansu Najwa, sabida bayasan ke'bewarsu wani waje daban gudun fad'awa TARKON SHAI'DAN gara a gidansu komai zai faru ya faru. Tun yana zuwa ana hanata fitowa harta soma satar jiki tana fitowa. Hankalin Inna ya tashi matu'ka ganinta Mustapha asiri yaiwa Najwa taki kowa saishi. Ta tara yaranta kaf tana kuka kan itafa tagaji susan matakin d'auka. Aunty Zainab cikin lallashi tace "Inna kidaina zubarwa Najwa hawaye, hawayan mahaifa masifane ga yaransu, musamman Najwa da take mace, kamata yai mui mata adu'a. Kuma idan mun duba ai Mustapha baida wani hali da za'a gujewa auransa. Nagartacan mutum ne da kowa yake yabansa". Cikin masifa Maryam tace " inji ubanwa? 'Dan iskane". A zafaffe Zainab ta wanka mata mari " Maryam na fahimci kece jagorar wargaza tafiyar nan sabida mijinki zai auri 'kanwarsa, shi aure ai nufin Allah ne kuma MATAR MUTUM kabarinsa ke baki isa hana abinda ubangiji ya tsaraba. Harkike neman zagina kan rashin gaskiya. To ainayi bincike kan lamarinsa 'karshema yanzu shiyakewa yarana lesson kuma nayiwa Abban yara magana yace yayi bincike Mustapha ko abokin fad'a bashi dashi". Cikin borin kunya Maryam tace " Inna kinji ko wallahi Najwa 'KADDARARMU CE kina kallo yadda Yaya ta mareni akanta kuma ai bashari duk wanda zaifadi halinsu baya nane tunda ni munfi kusa dasu......kallon da Najwa taimata yasata gum dan yanzu mugun tsoranta takeji tunda tasha duka. Cikin tausassawa Saudaht tace "shiyasa yayan 'kurfi take birgeni da tana kusa da tuni ta sasanta mtssss! Auran nesama baiyiba". Fiddausi tai murmushi tace "Inna gaskiya ubangiji ya haramta auran dole miyasa zakiyiwa Najwa bayan mu bakiyi mana ba? Kuma ma yanzu aibata da saurayi inba Mustapha ba mafi a'ala kibarta ta aureshi karta jawo mana magana. Ma'aikifa ya hara ta hakan da kansa ya raba auren dole har sau biyu. Ma'aiki (S A W) yana cewa:- Zuciyoyi rundunane daban- daban, idan wad'anda suka dace da juna suka had'u sai suyi 'kawance. Idan basu dace da juna ba sai suyi baram-baram. Wata rana wata mata mai suna Asmah'u Bint Khidam taje wajan Manzon Allah (s.a.w). Tana mai cewa. 'Babanta ya aura mata wani d'an 'kaninsa dan ya kare matsayinsa a wajansa sai ma'aiki (s.a.w)yace mata:" idan kinso na raba tsakaninku idan kin ha'kura shikenan ki zauna da mijinki". Haka Ma'aiki (s.a.w) ya raba aura tsakanin Usman bin Muz'um da iyalanka. Kamar yadda ya raba na Abdullahi d'an Umar da matarsa". Zamani ya sauya Inna yanzu yara a tsaye suke ko kana tarbiyarsu sai kana adu'a domin duk tsarewarka sai ubangiji ya tsare maka". Jikin Inna yai sanyi nan da nan ta sako. Sun daidaita magana akan Najwa zata kira Mustapha ya turo magabatansa. Aunty Zainab ce ta hana tace zatai masa magana. Da haka taro ya watse saidai tunda aka ajiye magana Najwa ta kasa walwala da farin ciki gaba d'aya ta sauya daga Najwarta zuwa Yaya Zainab hargida tai kiran Mustapha kan maganar inda gaske yake ya fito, yaimata al'kawarin zai sanarwa mahaifiyarsa. Da farko Mama taso tirjewa sabida abinda Inna tai musu, amma yaitai mata nasiha yana bata ha'kuri. Mama tai musu fatan alkhairi akasoma shirye- shiryen kai kud'i naira dubu talatin yakai sai dubu ashirin nasa rana. Mijin Yaya Zainab shiya amshi kud'in anyi komai a mutunce. Gaba d'aya Najwa ta sauya, miskilancinta ya 'karu fiye dana da. Al'amarin mafarkinta ya cigaba da faruwa saima abunda yai gaba. *********** Mustapha kansa ya kasa gane kanta a haka suka cigaba da tafiya. Ko hira yazo ta dinga d'aure fuska tana 'kun'kune daga uhmm sai uhmmm tun baya damuwa har yakai ga nunawa Husnah. Saidai itama bata samun sakin fuska daga gareta. Ko makarantar boko ta daina tsayata saidai abinda ya d'aure mata kai kullum inta dawo makaranta a wajan kukar nan ta layinsu take samunta sannan su jera kamar basuba su tafi makaranta. Inkuwa akaje makaranta itace tsokani wancan yima wancan ba'a. Ga wani 'karfin masifa da take dashi ko malamai sai sunyi da gaske suke tan'kwarata, dukan makara kuwa tuni aka daina yimata sabida duk Malamin daya daketa to kuwa zaikwana yana jinyar hanunsa. Kwanci yashi har suka zana jarrabawar gama makaranta, lokacin Najwa ta 'kara wani kyau na fizgar hankali, abinda basu saniba duk daran duniya ASHIQ ke zuwa ya d'auketa a mafarki ya kaita aimata gyaran jiki irin nasu. Nan da nan ta soma had'uwa da manyan alhazawa saidai bubu wanda taken a fuska, Mustapha kad'aine taurarranta. Saidai zuciyarta najin haushinsa idan bata 'bata masa raiba bata jin dad'i. Gaba d'aya Mustapha damuwa da fargaba ta sashi gaba duk ya zabge yayi ba'ki adu'ace kawai take ri'ke dashi. Kullum ASHIQ cikin tsora tashi yake tare da barazanar d'aukar ransa. A haka har aka tsaida lokacin biki. Najwa zaune a dokin 'kofa Inna tana d'akin girki cikin fad'a tace " waike Najwa wace irin hallitace da bakya jin magana?". Cikin so'baro baki tace "menayi kuma Innarmu?". Cikin takaici tace " Najwa duba fa jikinki kali shigar da kikai kida acikin gida kike kinsan wazaya shigo? Kai babu kalabi ga kuma kin zauna dokin 'kofa mattatarar shaid'anu, anya Najwa wannan rayuwa ce?". "Kefa Inna kinsoma matsa mana , haka ake rayuwa? Kawai ki barmu muji dad'i haba". A zafaffe tace "kee! Najwa saurara ni zaki gayawa maganar banza?". Itama cikin zafi ta waigo take muryarta ta bud'e ta koma muryar babban mutum idonta yai shud'i da ja ta nuna Inna da yatsa take ta soma lan'kwashewa bakinta da hannunta suka soma juyewa cikin minti uku kacal ta koma tamkar mai cutar shan Inna. Ba kowa yai hakanba face ASHIQ, domin lokacin ita Najwa ma tana gefene tana chat jira take Inna ta gama fad'anta ta tambayeta wace Najwar? Najwa tana kallonsa sai hawaye babu bakin magana. Takuma kasa tunanin yin adu'a sai bayan fitarsa ta samu damar mi'kewa tai waje tana kururuwa. Ku biyoni....... 'KADDARMU CE! SANAH S MATAZU 16-17 Da taimakon Maman Husnah Najwa ta fito da Innah daga dakin girki saidai babu hannu babu 'kafa. Hankalin yaranta ya tashi sossai. Aka dirfafi neman magani amma ina, wani ikon Allah da sukayi suka gaza saisuka watsar da lamarin tamkar ankauda tunaninsu da hankalinsu a kanta kullum cikin zaryar kulawa da'ita suke amma basa yun'kurin nema mata magani. Mustapha inya takura Najwa da batun har rigima sukeyi dan haka kowa ya tattarasu ya zuba musu na mujiya. Jikin Inna yasa aka 'kara bikin su Najwa zuwa wata guda, saidai babu wani cigaba tilas aka ha'kura Yaya Zainab ta d'aukowa Inna mai kula da'ita aka soma shirye- shirye. Hankalin Najwa yai mugun tashi zuwa lokacin duk tafita hayyacinta, ko gidansu Husna ta daina zuwa, lokuta da dama kasancewar layinsu shirune in muguntar ASHIQ ta motsa saiya tunkud'ota wajan kukar nan ya kawo yara ya zube yana gefe yana kula da'ita suita shirme. Husna kad'ai ke kula da zamanta a gun amma ta kasa fad'awa kowa. Kullum ASHIQ cikin wasa da hankulan makusanta Najwa yake babu wanda ya ke lura da lamuranta, dana cutar Inna dama-dama Fiddausi tafisu tsayuwa wajan du'a'i. Biki ya 'karato ankawo lefe an tsaida lokacin biki, sati biyu duk wani shige da fice Husnah keyi, dan wayarsma yanzu saita gadama take d'agawa, Mustapha ya gyara 'bangare guda a gidansu babban parlour yayi cikinsa da toilet da kitchen da stor sai bed room da 'bangaran ba'ki d'aki guda. Anyi fenti anyi siminti da komai . Ansoma hidimar biki Inna na kwance, sai gani da'ito duk wanda ta kalla saidai aga tana zubda hawaye hankula sun tashi sossai gidan biki sai koke-koke. Amarya dai gata nan sukukku kawai sha'ani ake amma bata da nutsuwa duk ta zabure. Tunanin kowa cutar Innarta ke damunta. Babban tashin hankalin Najwa matsawar da ASHIQ yai mata kan ta kori Mustapha ta'ki sabida ya kasa nasara a kansa. Babban tashin Najwa duk lokacin datai yun'kurin yimasa rashin mutunci wuyarta su had'a ido ko taji sautin muryarsa take yanke jikinta yakeyin sanyi. A haka aka d'aura aure ka soma shirin kai amarya. Yaya Zainab da sauran 'yan'uwanta sunyi rawar gani sossai. Sun 'kawata dakin Najwa ko mai uba sai haka. Najwa dai gata a gidan masoyinta datafi 'kauna, saidai tsantsar tsanarsa da takeji kamar ta kashe kanta. Amma da zarar taji muryarsa angama tsiya. Da farko zaman nasu ya soma dad'i amma daga bisani sai Najwa ta koma zam Najwan ASHIQ sabida tasoma nasarar hana Mustapha gudanar da wasu ibadunsa, kamar azumin littinin da alhamis. Tsayuwar dare kau daya soma ASHIQ zai soma tsoratata ta dnga iface- iface tilas zai katse ya saurareta. Mijin yayarsu ta 'kurfi tunda yazo yaga jikin Inna yace zai turo mai magani daga can a dan yana komawa ASHIQ ya gama dashi bai kwanaba. Tilas washegari ta koma 'kurfi domin yin takaba. Saidai zuciyarta cike da zargi sabida yadda aka bada labarin mutuwarsa domin kwatankwacin rasuwar Mus'ab ne. Da taimakon Maman Husnah Najwa ta fito da Innah daga dakin girki saidai babu hannu babu 'kafa. Hankalin yaranta ya tashi sossai. Aka dirfafi neman magani amma ina, wani ikon Allah da sukayi suka gaza saisuka watsar da lamarin tamkar ankauda tunaninsu da hankalinsu a kanta kullum cikin zaryar kulawa da'ita suke amma basa yun'kurin nema mata magani. Mustapha inya takura Najwa da batun har rigima sukeyi dan haka kowa ya tattarasu ya zuba musu na mujiya. Jikin Inna yasa aka 'kara bikin su Najwa zuwa wata guda, saidai babu wani cigaba tilas aka ha'kura Yaya Zainab ta d'aukowa Inna mai kula da'ita aka soma shirye- shirye. Hankalin Najwa yai mugun tashi zuwa lokacin duk tafita hayyacinta, ko gidansu Husna ta daina zuwa, lokuta da dama kasancewar layinsu shirune in muguntar ASHIQ ta motsa saiya tunkud'ota wajan kukar nan ya kawo yara ya zube yana gefe yana kula da'ita suita shirme. Husna kad'ai ke kula da zamanta a gun amma ta kasa fad'awa kowa. Kullum ASHIQ cikin wasa da hankulan makusanta Najwa yake babu wanda ya ke lura da lamuranta, dana cutar Inna dama-dama Fiddausi tafisu tsayuwa wajan du'a'i. Biki ya 'karato ankawo lefe an tsaida lokacin biki, sati biyu duk wani shige da fice Husnah keyi, dan wayarsma yanzu saita gadama take d'agawa, Mustapha ya gyara 'bangare guda a gidansu babban parlour yayi cikinsa da toilet da kitchen da stor sai bed room da 'bangaran ba'ki d'aki guda. Anyi fenti anyi siminti da komai . Ansoma hidimar biki Inna na kwance, sai gani da'ito duk wanda ta kalla saidai aga tana zubda hawaye hankula sun tashi sossai gidan biki sai koke-koke. Amarya dai gata nan sukukku kawai sha'ani ake amma bata da nutsuwa duk ta zabure. Tunanin kowa cutar Innarta ke damunta. Babban tashin hankalin Najwa matsawar da ASHIQ yai mata kan ta kori Mustapha ta'ki sabida ya kasa nasara a kansa. Babban tashin Najwa duk lokacin datai yun'kurin yimasa rashin mutunci wuyarta su had'a ido ko taji sautin muryarsa take yanke jikinta yakeyin sanyi. A haka aka d'aura aure ka soma shirin kai amarya. Yaya Zainab da sauran 'yan'uwanta sunyi rawar gani sossai. Sun 'kawata dakin Najwa ko mai uba sai haka. Najwa dai gata a gidan masoyinta datafi 'kauna, saidai tsantsar tsanarsa da takeji kamar ta kashe kanta. Amma da zarar taji muryarsa angama tsiya. Da farko zaman nasu ya soma dad'i amma daga bisani sai Najwa ta koma zam Najwan ASHIQ sabida tasoma nasarar hana Mustapha gudanar da wasu ibadunsa, kamar azumin littinin da alhamis. Tsayuwar dare kau daya soma ASHIQ zai soma tsoratata ta dnga iface- iface tilas zai katse ya saurareta. Mijin yayarsu ta 'kurfi tunda yazo yaga jikin Inna yace zai turo mai magani daga can a dan yana komawa ASHIQ ya gama dashi bai kwanaba. Tilas washegari ta koma 'kurfi domin yin takaba. Saidai zuciyarta cike da zargi sabida yadda aka bada labarin mutuwarsa domin kwatankwacin rasuwar Mus'ab ne. 'KADDARARMU CE!. SANAH S MATAZU. 17-18. Tunda yayarsu ta gama takaba ta dawo gida d'ungurun gum ta soma kulawa da mahaifiyarsu. Kullum takan tofa Ayyatul kursiyu da fala'ki da nasi ta shafa mata cikin sati guda 'kaffafunta da bakinta suka dawo dai-dai saidai bata magana sai nuni da hannu. Tunda ta soma yiwa Inna adu'o'i sai ASHIQ yasoma tsoratata, saitaji ana kiran sunanta ko kuma ana dariya mai 'karfi. Ko taga Najwa na binta da wu'ka. Kanta ya kulle ta tab star matsalar Innarsu daga Najwa ne. Dan haka taje gurin limamin unguwarsu saidai amsar da ustaz Usman ya bawa Mustapha itama haka abata. Saidai ya bata adu'o'i sossai tare da yimata bayani kan kodai Najwa ba jinsusu bace ko kuma ala'ka ta tsakanin MUTUM DA ALJAN. ************* Husnah ta soma ja tanai mata tambayoyi akan Najwa saidai babu wata satar amsa, abu d'aya ta tsinta game da Najwar zuwa biyu 'kiyyayar Mus'ab da zaman bakin kuka. Hankalinta ya karkata da batun kukar dan dama takan yawaita jin tsigar jikinta na harbawa intazo wucewa. Koma menene zata cigaba da adu'a. ******* 'Ya'yanta sunji dad'i sossai saidai sunyi mamakin sauyin da aka samu. Musamman Najwa da tun a gun fuskarta ta sauya idonta yai jajir. Bata wani tsaya dogon bayani ba. Tai murmushi tace "kudai kudinga adu'ar nemawa kanku da yaranku tsari a koda yaushe" duk sai jikinsu yai sanyi. Nan da nan Najwa ta azalzali Mustapha kan sai sun tafi gida basu wani jimaba suka wuce. A hanya yake mata 'korafi kan meyasa tace su taho?. Cikin 'kun'kuni tace " yayar nan zanyi maganinta tana yimana shisshigi" da sauri ya dubeta saita wayance tace " nufina tafimu kusa da Inna sossai". Dariya yai amma 'Kazan zuciyarsa yana auna kalamant. Haka zaman nasu ya kasance, matsalar yau daban ta gobe daban, yanzu abinda ta tsira shine xuwa taiwa Mama rashin kunya wanda hakan kan tunzura Farida su hau dambe. 'Karshe kuma Faridan ake cuta. Dama wazai had'a 'karfin MUTUM DA ALJAN (Munayshst). Kullum cikin kawo 'kararta suke ya rasa yadda zai 'bulowa lamarin. Matsalar da tafi damunsa tun auransu 'barinta uku kenan, yana lura da sakacinta wajan yin sallah kan lokaci inyai magana sai ta hau fushi da 'kun'kuni. Sai ya ha'kura ya 'kyaleta amma da zarar da kwanta ya kan lalla'ba yai mata adu'a. ********** Mustapha na zaune a 'kofar makarantarsu bayan antashi yara 'yan tahafiz sun soma zuwa. Kamar daga sama wata sumammiyar mota ba'ka tai parking a bakin TEEMAH COOL SHOPPING, katafaran kanti saida kayan 'kwalam da ma'kulashe. Bai damu da lura da irin wannanba amma haka nan ya samu zuciyarsa da san ganin na cikin motar. Gabansa ya tsananta fad'uwa yana jin wani irin abu mai nauyi a 'kirjinsa. Cikin dog on wando jeans ta fito yai matu'kar kamata sai wata half best fara tas kanta yasha 'karin gashi. Cikin jin tsanarta yake Allah wadarai da'it. Saidai me ? Hantar cikinsa tai mugun kad'awa lokacin da ya had'a ido da'ita. Ya murza idanuwansa sossai, tabbas itace meya kawota nan? Kayan jikintama zahiri dasu ya barota gida. Karaf idonsa yakai kan na kusa da'ita fuskar tamkar ya santa amma tunani yake ina ya santa?.kafin ya gama d'ibar tashin hankalin daya kwasa har sungama sun fito sunzo giftashi ta sakar masa murmushi ta d'aga masa hannu. Cikin tsananin tashin hankali ya nufi gidan da yake tazararsu babu yawa nan da nan ya isa gida. Gab da zai shiga gida wani yaro yai masa salama ya basji takarda kan yai magana yaron ya gudu. Da sauri zuciyarsa ke azalzalarsa ya bude takardar yana bud'ewa gabansa yai mugun fad'uwa. "MATARKA TA ZUBDA CIKINTA" wasu 'kwalan tashin hankaline suka zobo masa. Yana shiga Farida ya samu cikin rad'a yace mata "yau Auntynki ta fita?" Kai ta girgiza ,"a'a tunsafe tana kwance wai cikinta ke ciwo". Da azama ya 'karasa turus yai lokacin dayai arba da manyan ledojin TEEMAH COOL SHOP. Cikin masifa ya 'kwalawa Farida kira jiki na rawa ta taho cikin hargowa yace "kikace bata fita ba wannan fa?". A tsorace takaiwa kayan kallo tabbas kayan shopping ne to waya kawo cikin tsoro tace " walahi bata fitaba yaya "A zafaffe yace "jeki". Jikinta na rawa ta koma ta cigaba da aikinta. Dai-dai lokacin Najwa ta farka cikin wata giggitaciyar 'kara tana dafe kanta. Ga mamakinsa jini ke bin 'kafaffunta cikin kallon tsana Mustapha ya soma kallonta yana zagaye zagaye d'akin Najwa a tsorace ta soma ja da baya tana mamakin sauyawar Mustapha. Ku dakaceni ya tabbata Najwa ce a mota? Shin menene makomar auransu? Shin cikin ya zubene? Ya batun Inna? Shin ina Auran Farida da Abdul? Mustapha na sakin Najwa?. 'KADDARARMU CE! SANAH S MATAZU. 18-19. Cikin tsananin zafin rai ya soma nunata da yatsa" Najwa kin cutar dani kin zalunceni, bazan yafe miki ba". Kuka ya ci 'karfinsu su duka cikin rauni murya tace "Mustapha menai maka? Meye laifina? Kaimun bayani yadda zangane ka sanyani cikin duhu". Takaici ya kashe Mustapha abu guda ya fad'o masa bayan yawace-yawace tana kora 'kwayoyi banda haka kanmi zata raina mashi wayau. Kawai sakai yai ya bargidan bayan ya gargadi Farida karta fadawa Mama. Cikin sanyin jiki Najwa ta tashi ta gyara jikinta. Shayi me kauri taso had'awa idonta yakai kan TEEMAH COOL SHOP cikin hanzari ta bud'esu ta d'auki kaza guda da nono ta hau ci duk zatanta Mustapha ya ajiyesu. Haka zamansu ya sauya salo kwata - kwata babu jituwa makwancin kowa daban amma basu bari a fuskanta ko a magana bale a fuska sai isu-isu. ********** Jikin Inna saisan barka,kullum samun cigaba akeyi. Cikin 'kan'kanin lokaci Mustapha ya rame yayi duhu, kullum yanayin da zaiga Najwa daban. Najwa zamansu baya damunta koda wasa tamafi sakewa a ganinta takurata yake. Koda Husnah tazo ta kawo mata ankon bikinta bata wani fuskanci akwai matsalaba hakama Yaya Zainab da su Saudaht da sukazo. Ganin babu sarki sai Allah Mustapha ya nemi shiri suka dawo normal. Saidai kuma me? A duk lokacin da yau Yuan',kurin kusantar Najwa wani zafi ke fitowa ajikinta kamar tururin oven na bread. Hankalinsa yai matu'kar tashi sossai yanaji yana gani saidai yaita fama da ciwan ciki. Yauma kamar kullum kwaliya tai cikin dogon wando three quarter jeans yai mata kyau blue. Rigarta pink kanta yasha gyara sai kamshi takeyi abin sha'awa. Cike da kulawa suke hira harya fita taimasa rakiya. Tana dawowa ta ma'kala eirpiece tanaji a haka tai bacci kai abud'e. Tana kwanciya ASHIQ yai muguwar dariya ya soma zagayata. ********** Mustapha yana isa makaranta principle ta bashi takarda shaidar neman aiki da wata makaranta ta nemi yaiwa d'alibanta horo na wata uku. Can zoo road zaije yakai sa'kon, dan haka yad'auki machine d'in abokinsa ya tafi. 'Karfe d'aya da rabi dai-dai yazo kan hanyar titin gyad'i gyad'i zai biya wajan wani abokinsa kamar ance kali can gabasan yai mugun fad'uwa. Najwa ya hango tana tuka mota sabuwa dal 'kirar korolla. Gefanta wani kyakkyawan saurayine suna had'a ido ta kashe masa ido ta 'kara wuta. Mustapha a million ya rufa mata baya amma bai risketa ba 'karshema fad'uwa yai har yai targad'e. Ko gurin mai gyara baijeba ya nufo gida a zafaffe ya shigo gida abin mamaki tana kwance tana bacci. Ko kayan karinsu bata kwasheba ga eirpiace a kunnuwanta. Take jikinsa ya mutu

Chapter 2 of 3