Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Ga ubangijin talikai daya bani ikon rubuta wannan ta'kaitacan rubutu kan MATSALAR JINNI. Ubangiji yadda kabani ikon farawa kabani ikon kamalawa.Sa'kon godiya ga daukacin member na group d'ina MATA MASU AJI. Ubangiji ya 'kara had'a kawunanmu amin. SADAUKARWA. Gareku bazan manta karamcinku ba. Teemah Cool Safdeeq Cool Maryam Idris Katsina. Jamila Umar Katsina. Aina'u Jega. YABAWA. Taurari cikin NAGARTA (NWA). Ummu Fadila. Miss Hafcy Meesha Luv Aunty YBK. Aunty Chuchu. Addah Jabo. Beneziratu Ammar Saje. JINJINA GA 'DAUKACIN MASOYANA. Kaduna. Katsina. Narasawa. Gashuwa Kebbi Kano Da sauran jahohi ubangiji ya kara mana 'kaunar juna.Sadaukarwata gaba d'aya ga TAURARUWATA ita ce MAHAIFIYATA ubangiji ya bani ikon kyautatta maki. ************ GAMUNAN DAI. Hassana Muhammad Kano. Hassana Zakariyya Shahada Kano Hussaina Garba 'Danlami Kano. Hussaina Zamfara. Hussaina Kaduna Shantaly. Hussaina Gashuwa Munayshat. ************ 1-3 Cikin matsanancin gudu take wuce tsaunika tare da tarin bishiyu, taka 'kayoyi take amma hakan baya d'aya daga cikin abinda ya dameta, burinta kawai ta tseremasa daga mummunan nufinsa a kanta, cikin rashin tsamani ta taka wata 'katuwar 'kaya mai tsanani kaifi. Take ta 'kwala giggitaciyar 'kara hakan yai dai-dai da farkawarta. Cikin hanzari tabi 'kafarta da kallo abinda yai matu'jar tsorata ta. 'Kayar data taka a mafarki gata a tafin 'kafarta ga jini na bin 'kafafunta cikin tashin hankali ta soma waige- waige. Shiru garin babu motsin bil'adama sai kukan karnuka da tsuntsaye. A hankali takai kallonta kan 'kofar d'akinsu cikin sakan guda cikinta ya bada wani sauti. 'Kuuuuuuuuuu. Cikin tsoro ta dinga ja da baya tare da karanto duk adu'ar data zo bakinta. Ta runtse idonta ta jiran 'karasowar 'KADDARARTA saidai ga mamakinta sai ta tsinkayi muryar Mahaifiyarta tana fad'in "Najwa me kikeyi baki kwanta ba? Cikin sauri ta bud'e idonta. Sai ta saki ajiyar zuciya. Cikin azama takaiwa 'kafarta bahagon kallo dansan nunawa mahaifiyarta. Abin mamaki da tsoro babu ciwo babu alamunsa. Nan da nan ta nemi nutsuwarta cikin kaucewa kwataragin daya dumfarota tace "Innarmu farkawa nai". Cikin d'aurewar fuska tace " ina d'ankwalinki?". Nanfa ta kama kame-kame sabida bama dashi ta kwanta ba. Cikin fad'a mara sauti tace " wato Najwa bakya jin magana ko ke kullum baza agaya maki kijiba, kwanciya kai a bud'e ke ba gwanar adu'aba sai anyi magana kice antakura miki ko?". Cikin gunguni tace "Mantawa fa nayi". Cike da mamaki tabita da kallo tana jinjina taurin rai irin nata.Cikin nutsuwa take tafiya tamkar mai tausayi 'kasa, saidai zuciyarta cike da rud'anin mafarkinta na jiya tana jin kodai tagayawa Husnah kotai shiru. Can wata zuciyar tace " Ke Najwa yanzufa zamani ya sauya mutum ba'abun yadda bane, wani zaimiki kwance- kwance yaji matsalarki kawai dan yaji dad'in falasawa. Wani kuwa dan yaji dad'in yimiki gorine. Ki ri'ke matsalarki a ',kar'kashin zuciyarki da sannu ubangiji zai miki maganinta. Saidai ki ri'ki adu'a. Cikin farin ciki tai na'am da abinda zuciyarta ta fad'a.Kamar daga sama akaimata salama" Assalamu alaiki Gimbiyar mata". Shaidar mai muryar ne yasa ta d'ago cike da murmushi tana kallinsa cike da so da kuma 'kauna. Sai taji kaf damuwarta ta wuce. Amma miskilar saita maze. Mustapha yai murmushi yana dubanta yace, "Najwa ina zaki cikin ranar nan?, ta ya mutsa fuska alamun gajiya tace "gidan yaya Maryam zani mijinta baya nan zan tayata kwana zuwa jibi". Cikin jin dad'i yace "kice kwana biyu muna tare"?. Ta gintse fuska "ba lallai bane tunda kasan ra'ayin Innarmu shine nata". Yai ajiyar zuciya " shikenan Najwa sai munyi waya". Yana fad'ar hakan ya juya idonsa jajjir cike da sassarfa. Duk sai ya bata tausayi, to amma ya yakeso tayi ? Yasani sarai mudun ta sami labari rayukane zasu 'baci a haka ta 'karasa 'kofar ruwa cike da kasala. Tun daga soro Walid yake oyoyo. Tilas ta aro juriya ta tari fara'arsa suka shiga gidan. Da fara'a yayarta ta amsheta suka hau wasa da dariya. Cikin zolaya tace 'ina kuwa MUS'AB?". Take fara'ar data aro ta gushe. Kai tsaye d'akin da take sauka ta wuce ta barta anan shanye da baki. Tanata bambamin fad'a. Tana shiga kiranwayarta na shigowa jaka kawai ta ajiye ta wuce kan kujera. Tana karar wayar a kunnanta suka saki ajiyar zuciya lokaci guda. Cikin tausasawa yace "menene?" Kai tsaye ta amsa masa "babu komai hubbynah hope (fat an) ka'isa gida lafiya"?. "Ba wannan ke gabana ba Najwa dalilin ajiyar zuciyarki nake san ji, tai gum tana juya lamarinsa a ranta tasani kad'ai ko muryarta yaji yana gane yanayin damuwarta, bale kuma ga rabuwar da sukai. Jin shiru yayi yawa ya kira sunanta. "Najwah!!!!!!" Yar cigar jikinta ta tashi cikin kasala ta amsa. "Na'am hubbynah". " please menene damuwarki?". "Mustapha kaine damuwata, kaine abinda ke sani damuwa, ina duba yanayin da muka rabu inajin araina ban kyautaba. Kobaka cancanci SADAUKARWA ........"Ya'isa Najwa kinci abinci". Duk saitaji haushin kanta wato shi 'ko'karinsama cikinta, gaskiya inta auri Mustapha zata ga tarairaya. Shigowar Yaya Maryam yasa tai masa salama. Bai matsa da sanjin daliliba ya katse. Zuciyarsa cike da tausayin rayuwarsu cikin azanci yace, "KADDARARMU CE a hakan. Haka ta 'karasa kwanakinta gidan cike da takura sabida rashin samun jin muryar abin 'kaunarta. Ranar da Abdul zai dawo tafi kowa murna da zumud'i tun safe taimata aiki ta had'a kayanta. 'Karfe hud'u ya dawo gida, 'karfe biyar Najwa taiwa unguwarsu tsinke. Tana shiga layinsu ta saki sassanyar ajiyar zuciya sabida hango 'kawarta da tayi cikin sauri ta tarbeta suka shiga gida tana fad'ar ",bestyna miss u more" ( ma'ana nayi kewarki da yawa). Cikin murmushi wanda ya zama al'adarta suka shiga gida.Inna na ganinta ta ta'be baki "wuuuu! Najwa 'yar nema wato har kin gudo ko"?. Ta turo baki " dole in gudo Innarmu aita saka aiki ba godi bare na gode, kuma kanayi ana hantararka". Duk sukai dariya Husnah ta jata d'akinta suna shiga tace "Mus'ab yazo sau biyu bakya nan, ya nemi numbarki Inna ta aiko na bashi, hope ya kiraki?. Next Mustapha ya bani sa'ko anjima in munje makarantar dare zan baki". Tunda ta soma magana sai yanzu Najwa tai murmushi jin an ambaci Mustapha . Cikin zolaya Husna ta d'aka mata duka tai waje, aikuwa a guje ta biyota kafin ta kamata ta kyalle. Cikin dariya Inna tace "sababbu kun dawo zaku adabeni". Cike da haushi ta cire d'ankwalinta ta suri buta zuwa kewaye (band'aki), Inna kawai ta tsaya taga gudun ruwanta, saidai bata da alamun tsayawa ta daura. Cikin hargagi ta daka mata tsawa." Keee! Najwa ina kalabinki? ('Dan kwali) cikin basarwa tace "zan d'aura bari in fito". Bata jira cewartaba ta shiga abinta. Mamaki ya kashe Inna kwata-kwata Najwa bata jin tsoran fad'anta mudin akan saka kalabine ko batun Mustapha tun bata damuwa da lamarin harta soma damuwa. Tana fitowa ta tareta da balbalin fad'a "wato ke Najwa bakyajin magana ko? Nahanaki zama babu kalabi kin'ki ji ko' uwa uba shiga bayi babushi, waikin manta band'akine matattarar jinu amma kike 'kuga (saka) kanki ciki babu hijabi, wanda na tabbatar ko adu'arma da 'kyar idan kinayi". Inkin taka biron hanuna ya tanka haka Inna taita bambaminta Najwa tai biris. Najwah Usmar Salis wadda abokanta suka fi kira da Nus, d'iya ce ga Malam Usman marigayi tare da Inna Hafsatu. Su shida iyayansu suka haifa duk mata. Suna zaune a unguwar dandinshe cikin 'karamar hukumar dala. Babbar yayarsu Zainab na auran wani prof a gadon 'kaya yaranta hud'u. Auwal da Sani da kuma Mahfuz da Mahfuzaht. Sai mai bimata Saudat. Tana zaune a unguwar tudun yola yaranta biyu, Muhseen da Muhseenaht. Sai ta tsakiyar itama yaranta biyu mai suma Fiddausi. Sai Ayshat ita kuma tana 'kurfi tana aure bata ta'ba haihuwa ba. Sai Maryam mai yaro guda tana 'kofar ruwa sai autarsu Najwa. Mahaifinsu ya jima da rasuwa, tun suna yara. Rainansu da kulawarsu duk 'kar'kashin kulawar Inna Hafsatu. Innarsu macece mafad'aciya sossai. Bata san wargi (raini). Haifafiyar Kano ce unguwar 'kwali wajan gidan sarki hakan mahaifinsu haifafan 'kofar nasarawa ne. Tun bayan rasuwarsa danginsa basa basu wata cikakkiyar kulawa kasancewar shine bare cikinsu. Mahaifiyarsa ta rasu, tun tana kai yaran harta daina. Haka nan duk auran yaranta ita tai fadi tashinta babu taimakonsu. Macece mai zuciyar nema babu sanar da bataiba don rufawa kanta da yaranta asiri. Tana tsaya musu sui karatu kafin aure iyakarsu secondary inyaso inkinje mijinki na muradi kya cigaba. Itace yin surfe, wanki da sauransu. Harta gama auransu yaranta sai autarta Najwa. Asalin iyayan Inna Hafsatu 'yan 'kasar Niger ne, kyawawan fararren buzaye masu gashi da kyan fasai. Doguwar mace sam'bal zubin Karas ba d'ata ba. Cikin bayin da ake kawowa gidan sarki aka had'o da mahaifiyarta anan ta had'u da mahaifinta shima mutumin can ne kasan cewarsu 'KABILA d'aya ba jinkiri sukai aure. Inna Hafsat kad'ai suka haifa kyakkyawar mace, shekarunta sha biyu akai wata annobar kwalara suka rasa rayukansu. Hakan ya sa Usman yake tausayinta har ya juye zuwa so ansha fama kafin auransu saidai ikon Allah. MATAR MUTUM....hausawa sukace wai 'kabarinsa. Duk cikin yaranta Najwace ta d'auko komai nata. Dan haka ina keji da d'iyarta. Tunda ta gama aurar da yayyanta sai hankalinta ya kwanta, Najwahce kad'ai gabanta. A da yaranta makarantar gwamnati suke, amma ganin wadata da bud'i daga ubangiji tare da taimakon surukanta. Najwah na gama primaryn makara huta ta sama mata gurbin karatu a gora academic. Najwa ta tashi cikin so da kulawar yayye uwa da mazajan yayyanta. Kullum cikin samun gata da kulawa take. Saidai duk cikin yayyunta tafi shiri da Maryam dan haka tafi zuwa gidanta. Sui tsiya sui dad'i sabida Maryam akwai tsokana. Duk cikin yaran Innarsu Maryam ita ta kwashe halin Inna, akwaita da fad'a ammafa kan gaskiya batasan raini. Najwa bata da 'kawa ko daya sai ma'kwafciyarsu mai suna Husnah, 'kiriniyarsu iri d'ayace saidai akwai kwanyar nacin karatu. Ga masifaffiyar tsokana akwai wata al'adah guda d'aya da Najwa keda ita wadda kullum takesa su sami sa'bani da Inna............. 'Dabi'ar Najwa itace yawo a tsakar gida babu d'ankwali, ko banda'ki zata bata damu ta d'aurashi ba. Ga yawan shigar kaya masu shara- shara ko matsatsu. Duk lokacin da tai hakan sukan haura sama ita da Innarta. Hakan kan 'kona ran Najwa ganinta yadda take da gashi har tsakiyar bayanta bai kamaci tasa kalabiba. Uwa uba 'yan ajinsu na fasa mata kai idan akazo exfection. Najwa irin matan nan ne dogaye masu fad'in ',kugu da cikar 'kirji hakan yasa duk suturar data saka take mata das gata chaculate colour mai haske. Kalar da ba a siyanta komai kud'inka. Tun tana 'karama take fama da'ita tayi dukan duk a banza har zuwa girmanta. Hallayarta na ba'kanta ran mahaifiyarta sossai,tun tana 'karama har yanzu da takai matakin shekaru sha biyar, komai nata ya kara kyau da girma, kullum cikin nuna mata kuskurenta take amma abu yaci tura. Mus'ab matashin saurayine dan bayan layinsu tun Najwa na jss one yake 'kwa'kwar santa, saidai Innarta tace saitayi karatu. Yace yaji ya amince zai jira. Najwa ta tsani Mus'ab kullum ta ganshi wani mugun abu takeji ya taremata 'kirji. Zagi kuwa yana shansa lodi-lodi. Tasha saka yara su sace masa tayar kekensa d'an tsura ta basu lada. Wata ranma ita da shakiyiyyar 'kawarta suke zuwa. Tun bai saniba harya ganosu. Najwa na jss 3 wani ba'kon al'amari yasoma giftawa cikin rayuwarta mai cike da mamaki da ban tsoro. Wasu irin mafarkai take masu tsananin ban tsoro, wasuma ta kanjisu ajikinta suna matu' kar wahalar da'ita tare da rikita tunaninta. Da fari taso sanarwa Innarta saidai tana tsoron tayar mata da hankali. Gashi mafarkin yana sata kokwanto ta kanji anya a kantane koko a kasin hakan. Tsanar Mus'abu ta cigaba da yad'uwa a zuciyarta harzuwa lokacin data had'u da Mustspha. Najwa ta tsinci kanta cikin yawan mafarkai barkatai. Lokuta da dama ta kanyi mafarkin gata a harabar wani babban gida yara 'kanana suna zagaye da ita. Kota ganta rungume da jarirai a hannu. Kota ganta tana tana feeding (shayarwa) d'in jarirai. Lokacin tana jss three, sai ta maida abun tamkar wasa. Tana matakin Sss one ne, ubangiji ya had'ata da Mustapha a hanyar makarantarsu wato 'kofar ruwa. Mustapha nitsattsan saurayine mai tsantseni da Ibadan. Tunda ubangiji yasa ya d'ora idannunsa kan Najwa ubangiji ya jarabceshi da 'kaunarta. Tun yana kkakaucewa har yai shahadar ',kuda ya isar da sa'kon zuciyarsa. Najwa macece mai san soyyaya da kulawa hakan yasa cikin 'kan'kanin lokaci Mustapha yai nasarar samun soyayyarta. Cikin 'kan'kanin lokaci sukai wata irin sha'kuwa mai wuyar fassaruwa. Kullum tafito zuwa makaranta ta 'kofar gidansu take wucewa, yana zaune ya dakkonta (jiranta) in kuwa ta wuce zaimata fatan alkhairi ya shiga gida. Wasu lokutan ya rakata sch yana tsokanarta yanai mata wa'ka. Najwa fara kyayyawa, matata abar sona. Babyna ina sanki Kuma kema nasan kina sona. Inmunyi aure musha 'kauna ke zan miki wanki duk dan 'kauna. Zanmiki wanke- wanke harma da goyo sabida 'kauna. Ira-iran kalaman Mustapha kenan, ya iya salon sace zuciyar mutum. Najwa najin dad'in al'ka dashi gashi mudun zasu zauna hira saita 'karu dashi fanin addininta da all',amuran rayuwa. Irin mazan da ake buri kenan arayuwa. Ubangiji kabamu mazaje nagari. Mus'ab hankalinsa ya tashi ganin kwata-kwata hankalin Najwa baya Kansa. Hakan yasa yasoma yiwa Inna Hafsatu 'barin kud'I a fakaice batare da sanin Najwa ba. Inna Hafsatu hankalinta ya tashi ganin yadda diyarta ta karkata kai ga Mustapha, batare da laifin komaiba. Mugun tsanarsa takeji a ranta. Abinda bata saniba matsalar Najwa ce ta haddasa hakan, saidai rashin kula ya hanata fuskanta. Zagin yau daban na gobe daban, Mustapha yana da hakuri da juriya, bai taba d'aga kai ya kalli Inna da batunba. Sau tari zaizo gida amma Inna ta hanata fita. Yaya Maryam tafi kowa assasa lamarin sabida basa shiri da gidansu Mustapha kan mijinta Abdul nasan 'kanwarsa Farida. Kasancewarsu akwai ma'kotaka saitai amfani da damar dan 'kuntattama danginsu. Mahaifin Mustapha ya jima da rasuwa, daga shi sai 'kanwarsa da mahaifiyarsa. Yana kyautatta musu sossai ya kamala karatunsa na NCE da'kyar. Yanzu koyarwa yake a wata nursery dake kusa dasu mai suna HASMAH INTERNATIONAL SCHOOL PRI- NURSERY AND NURSERY AND PRIMARY. Balaifi yana samun albarka. Bai zauna hakaba yana koyarwa a makarantun dare guda biyu magarba da isha mai suna UMMU SAMHAT TAHAFIZUL QUR'AN da kuma MADINATUL AHBAB. Kwanci tashi babu wuya gurin ubangiji al'amura sunka cigaba da faruwa masu dad'i da akasinsu. Ana hakan kwatsam Mus'abu ya aikowa Najwa kyautar waya sabuwa dal. Wadda mahaifiyarsa ce da kanta ta kawo kyautar kasancewarta aminiyar Inna. Wannan yasa Inna ta 'kara san Mus'ab sossai. Da farko Najwa ta'ki amsar wayar amma data gayawa Husnah tuni ta shirts mata hanya mai 'bilewa. Da sassafe ta tashi cikin shirin zuwa makaranta taima Inna salama ta wuce zuwa gidansu aminiyarta suka rankaya. Tafe suke suna tad'i (hira) su biyu cikin nutsuwa da sanyin rai Najwa tace" aminiyansi jiyafa 'kolo ya kawomani waya 'kirar gione amma ban kar'bata tana gun Innah". Cikin masifa Husnah tace " gaki dai kamar wayyayiya kina neman yin kwa'ba, banda ke ai wayar wata hanyace ta 'karfaffa ala'karki da Mustapha". Tai jim alamun tunani, can ta saki murmushi 'kayatace wanda yasa dimple d'inta motsawa tace "gaskiya Husnaty ke mission ce, aikuwa hakan zanyi walahi, in'kulle a d'aka ina waya da hobby a Inna nayin magana nace 'kolone". Gaba d'aya sukasa dariya dai-dai lokacin suka 'karaso bakin geta d'insu suka shiga makaranta. Najwa alla alla take a tashi makaranta taje ta amshi waya. Ana kuwa tashi kai tsaye tayo gida ko Husnah bata tsaya jiraba. Kasancewar rana ta take haka ta taho tana zumud'i tazo gab da layinsu akwai wata 'katuwar kuka mai koguna da yaw a a kan layin anan idonta yai katari da wani kyakkyawan farin mutum yanai mata murmushi, da farko taji ya birgeta dan yaimata yanayi da hubbynta amma daga bisani saita lura jikinsa duk gashine kuma kasansa maimakon 'kafaffu aaaa jikin micijine. Cikin sassarfa ta bar gurin tana waiwaye yana d'aga mata hannu. Wajan shiga gida tai karo jikake 'kumm ta 'kwala 'kara nan da nan Innarta ta fito tana tambayar ba'asi. Tuni goshinta yayi lukuni abinka da farar fata. Cikin sauri tasoma mulmula mata, suna shiga gida tana zumud'in fadar abunda ta gani. Saita samu kanta da tsanani tsoro domin mutumin kemata barazana yana tsiratatta da wata sharbebbiyar wuka. Luf tai ajikin Inna tana ajiyar zuciya. Uniforma ta cire ta d'aura zani still babu dankwali ta shiga bandaki ta watso ruwa abunta. Tana nan zaune Husnah ta shigo, tana bambamin anbarota saitai turus ganin lukuni a fuskarta, ga wani uban tagumi data rafka, cikin tsoro ta girgizata ajiyar zuciya tai lokacin data dawo daga tunani. " bestyna meya sameki" " bigewa nai tafada cikin bagararwa" " wannan tunaninfa?". Take abinda ya faru ya dawo mata ta bud'e baki zatai magana sai bakinta ya'ki magana tashin hankali kawai saitasa kuka " Besty nima bansaniba walahi bansan abinda ke damuna ba". Husnah tai musmushi duk zatanta Innace ta hana wayar ko garin zumudinta ta fasa musu kwai kawai saita shiga ciki taiwa Inna dad'in baki ta am sonata wayar ta hadamata komi tadangamata tajata d'akinta. Suna shiga ta dubeta da yanayin kulawa. " bestyna menene damuwarki? Zatona Mustaphane kuma kinsamu hanyar jinsa what next"?. Cikin jimami ta bud'e baki zata bata labari amma hakan ya gaggara. Kawai sai Husna ta Samara number Mustapha dake wayarta ta dana kira. Lokacin da kiran ya shiga yana niyyar shiga masallaci saiya share kiran. Ganin shiru bai d'agaba yasa Husnah taimata salama tare da lallashinta ta wuce gida. Najwa tai ajiyar zuciya ta kwanta kan katifarta ya illahi wazata tunkara da batun. Mustapha yana fitowa masallaci yai karo da wani ba'kin 'kadangare ya kawowa babban yatsansa cafka cikin nutsuwa ya furta" hasbunallah". ' Bat ya 'bace babushi babu lamarinsa. Cikin rashin kuzari ya 'karasa kan benci ya zauna. Wayarsa ya zaro ',karama mai sau'kin kud'i mai suna G- best ya kira numbar d'azu. 'Karar wayar ita ta dawo da Najwa daga dogon tunaninta cikin nutsuwa ta d'aga tana murmushi, tana jan jelar gashinta. Jin muryar juna ya haifarmusu da nutsuwa domin rabansu da juna tun had'uwarsu a zuwanta gidan yayarta. Cike da kulawa yace " Najwa yanajiki wani sanyi- sanyi?". Hawaye yabiyo kuncinta tace " bakomai Hubbyna hope kana lafiya ya jikin Mama"?. Cikin sar'kewar murya yace "aa'a Najwah ban aminta ba". "Hmmmm! Kafi 'karfin komai a gurina ka yarda banda damuwar data wuce ka". " To nagode Allah yabar 'kauna inajin dad'in hakan sai dai zuciyata zafi Najwa inajin kamar kin 'boyemun ne. Inasan inji nasamu sanyi inajin kamar idona zasu zubar da hawaye hmmmmmm! Kicema Inna ina gaisheta, ki dinga yi mana adu'a". Sunyi shiru na mintina, ya kauda shirun" ina kika sami waya naga ba layin bestynmu bane?". Dum ' kirjinta ya buga bazata iyayi masa 'karya ba kawai saita gaya masa gaskiya. Jikinsa yai sanyi duk yaji babu dad'i amma yasani sarewarsa na nufin sarewarta. Sarewarta na nufin bijirewa mahaifanta, bazaiso hakan ba baimata adalciba inyai hakan ba santa yake ba cikin murmushi yace . " Najwa You make me smile for no reason whatsoever, you make me laugh at the unfunny things, but most of all, you make me love you when I shouldn't be loving you". Bai jira cewarta ba ya katse kiran. Cikin nutsuwa tabi wayar da kallo tanajin dad'i mara misaltuwa. A fili ta furta "Mustapha ina 'kaunarka". Bazaki aureshiba inko kin sureshi kina tare da bala'i da masifa. Cikin yanayin damuwa Mustapha ya ajiye wayar hannunsa. Zuciyarsa nasan gargad'insa abisa matakin daya ke shirin d'auka. Saidai yana ganin hakan shine dai-dai. Yana tashi gida ya nufa da salama. Farida dake wanki ta amsa masa da kulawa tanai masa kirarin dake sashi murmushi. "Angon Aunty Najwa sai dubu ta taru" mahaifiyarsu ta kallesu cike da murmushi tanaiwa ubangiji godiyar samun nutsattsun 'ya'ya. Cikin ladabi ya zauna ya gaisheta, kansa a sunkuye tace " mai sunan manya ya akai? Bakinka akwai magana". Yai murmushi ya sosa kai "mama dama maganar yarinyar can ne". Sarai ta fahimceshi amma saita bagarar da zancan" ban fahimtaba Mustapha wacce Kenyan?". "Mamanmu Najwah nake nufi". Cikin murmushi tace "to ya akayi ko sunce mu mutsane?". "A'a mamanmu nine dai nake ganin dacewar hakan sabida takai matakin aji biyar". "Hmmmmm! Ban'ki ta takaba amma baka ganin zamui musu riga Malam masallaciba, kasancewar basu but',kaci hakan ba?". "Insha Allah ba matsala". Da haka suka rufe zancan. Da yamma mama ta shiga gidan liman ma'kocinsu ta shaida masa bu'katarta tasan nemawa Mustapha aure tare da wasu cikin abokan mahaifinsa. Sun amshi batun hannu biy- biyu ana sallahr isha'i suka d'auki hanya bisa rakiyar mustapha. Saidai kash sunyi takaicin abinda suka riska, domin Inna taci mutuncinsu tas, tare da shaida musu sati mezuwa zata Karl'bi kud'in auran 'yarta. Sun dawo jiki a sanyaye basu 'boyewa mahaifiyarsa komai ba, tai musu godiya sossai tare da yiwa Mustspha nasiha. Najwa tayi kuka kamar ranta zai fita, washegari taiwa gidan Yaya Zainab tsinke tun daga soro to soma gunjin kuka, da 'kyar ta lallasheta tai shiru tare da yimata bayanin lamarin. Zainab tai jigum tana jinjina batun kaf yaran mamansu babu wanda taiwa auran dole to miyasa zata soma a kan Najwa?. Cikin jimami tace "anya ba laifi kukai mata ba koke ko Mustaphan?". "Walahi Aunty baimata komai ba kawai na rasa shin 'KIYYAYA CE KO SON ZUCIYA Innarmu keyiwa Mustapha?". Ha'kuri ta bata ta nuna mata d'akinta "shiga ki wanka duk wani hargitse". Ba musu ta shiga tai wanka ta kwanta. Sallahr azahar tai kasancewar d'aya ta gota, tana idarwa batai adu'aba ta cire abayar gashinta ya bazo tabi lafiyar katifa ta kwanta. MAFARKI. A hankali ta riski kanta a wani daji mai tsananin duhuwa da koguna, babu abinda takeji sai wani irin 'kugi da gurnani, a hankali wasu halitu suka fara bayyana masu launin ban tsoro, kawunansu manya kamar me, saidai jikinsu na majizai. Can taji ana 'kwalamata kira Najwa! Najwa!! Najwa!!! A rikice ta juya tana waige-waige. Karaf ta had'a ido da fuskar da baza ta mantattaba, saidai wannan karan sa'banin wancan ne, maimakon murmushi fuskarta a d'aure take tamau cikin 'karaji yace " kali nan" a d'imauce ta juya Mustapha da Mus'ab ta gani wasu manyan hallitu sun d'add'auresu hannu, cikin tsananin rud'ewa tai nufin zuwa gur in amma wasu sar'ko'ki sun mata mugun d'auri ta bud'e baki tana kuka tana magiya kan ya sakesu. Cikin murya mara dad'in sauti yace " Najwa waya gayamiki anayiwa ASHIQ kishiya? Kina neman cutar dani na'ki JINSINA sabida ke, amma ke kina neman gujemun, nasanya hijabi tsakaninki da duk wani JINSI inba nawa ba. Da bana samun matsala dake shiyasa bana bayyana kaina a gareki, amma zuwan wan an BIL'ADAMAN kinsoma yimun taurin kai ko shimfid'ata nai 'kokarin kiranki saiki kauce yarana sundaina samun kulawarki. Cikin masifa Mustapha yace "kai la'anan Allah" cikin jin haushi ASHIQ yakai masa duka da takobinsa amma sai wani haske yai sama da mustapha take takobin ya sauka kan wuyan MUS'AB. A firgice ta farka tana fad'ar MUSTAPHA!!!!!!!!!!!.A tsorace takaiwa jikinta bahagon kallo wani mugun bugawa yai das-das-das sakammakon abinda ta gani ku biyoni danjin wai me Najwa ta gani?. Cikin tsananin razani ta soma duban kusan da'ita zahiri jinine a jikin rigarta da gefan gadon. Kanta yai muguwar sarawa ga wata muguwar fad'uwar gaba. Da sauri Zainab ta shigo tana tambayar "lafiya Najwa kike 'kara haka kina kiran Mustapha?". Saita 'kan'kameta tana fad'in "Aunty kingani" tana nunamata jikinta. Take Zainab ta tureta tana nuna tsananin jin haushi "gaskiya Najwa kinfiya abin haushi, period d'in kikewa wannan wula'kancin?". Cikin rudani ta furta " Aunty ba period nai ba, kiduba fa sossai". "To gayamin mekikayi?". Bud'a baki tai da niyyar bata amsa gam baki ya kulle cikin bagararwa Zainab tace." Hmmm! Shiga ciki ki gyara jikinki banasan shirme, koni d'in ba'kuwarki ce?". Take ta fice ta bar d'akin. Jikinta yai sanyi, tana fita d'akin ya gauraye da wata irin hargowa hhhhhhhhhhhhhhh "Najwa kinyi kuskure tunda kikesan BIL'ADAM zakija na dasawa kowa tsanarki, zan tozartaki a duniya, ki kasance dani ni kad'ai zai fimaki kwanciyar hankali". Cikin kuka Najwa ta bud'e baki zatai magana fuuuuuuu iskar tabar d'akin. Cikin hanzari ta d'auki wayarta ta kira Mustapha kira d'aya ya amsa muryarta na rawa tace "Mustapha! Take tsigar jikinsa ta zuba ya amsa "ya akai Najwa? "Lafiya 'kalau kake"? Ta fad'a murya na rawa jin a yanayin da take yasashi cewa. " Cool Najwa menene duk kin rikice ne?". Cikin jimami ya saita kanta "dama........dama" saita kama kame- kame. Murmushi yai yace "

Chapter 1 of 3