Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan naji, ko kinji wani abin ne."

Dana sani Binta tai da yimata wancan zancen, kanta tai kasa dashi tace "kiyi hakuri Gimbiya bansan manufarki ba."

Kai Zeena ta girgiza alamar bakomai tace "nina fara sannan ba laifi bane in kin rama, haka ake san matar dan sarki bawai kiyi ta bari ana taka ki ba, gaba daya ni na rasa yanda zanyi nasan abinda ke faruwa, shi yasa na ajiye girmana da matsayina na tambayeki."

Binta tace "Kina ganin akwai dalilin sa na yin hakan kenan?"

Shiru Zeena tai dan gaba daya tunda taji jibi xa'ai abin ko nutsuwa ta kasayo gaba daya.
Ta tabbatar da abinda ke faruwa amma batasan menene ba.

Kallan Binta tai tace “shikenan jeki kawai, Binta cikin damuwa tai sallama ta fita.

Fitowa tai ta kalli Fure tace “haryanzu baya bangarensa? Tace eh.

Kallan Fure tai tace “ina san zuwa gun Ramlatu.”

Fure tace “dare yayi Gimbiya.”

Zeena tai shiru cikin tsananin damuwa.

*****
Binta na fita bangaren Junaid taje sai dai Azi yace mata bayanan tun yamma ya fita.

Shiru tai kafin ta kalli duhun da garin yai bari tai sallah in bai dawo ba ta fita.

Bangrenta ta nufa ta wuce daki.
Ba karamin tsoro taji ba ganin mutum lulube da bargo, wutar dakin a kashe.

Tsayawa tai kafin ta nufi gun a hankali, Junaid ne kwance a kan gado ya dukunkune da bargo.

Kusa dashi taje da sauri ta zauna a gabansa tace “Ya Junaid?”

Idanunsa ya bude a hankali ya kalleta sannan yai dan murmushi yace “Bintalo ta dawo?”

Hankali a tashe tasa hannu akansa, hannunta ya rike yace “lafiya ta kalau.”

Ajiyar zuciya tai murmushi ya sakeyi sannan ya kalli idanunta wadanda suka ciciko tana neman kuka yace “karki fara lafiyata kalau.”

Kallansa tai ta kasa magana, mikewa yai ya zauna sannan yasa hannu ya jawota kan cinyarsa ya rungumeta sannan ya fita da wata iska daga bakinsa.

Cikin raunin murya tace “Ya Junaid lafiya dai ko?”

Lafiya kalau, me Umma tace miki?

Dan juyo da kanta kadan tai ta kalleshi tace “hskiri ta bani, ni duk kunya ma ta kamani.”

Shiru yai baice komai ba, ta kara cewa “Amma yaya Umma fa ba lafiya kuma naga bakaje ba.”

Kara rungumeta yai yace “ke kinjemin ai.”

Tace “taya zanje ma bayan nasan tana san ganin danta.”

Bakinta yakaiwa sumba sannan ya kalli idanunta dake lumshe ya sumbacesu, cikin rada yace “kinyi sallah ne?”

Idanunta ta bude tana murmushi, tare sukai sallah ya dade yana addu’oi dan har ta jingina da bango.

Junaid ya kalleta sannan ya sa hannu ya kwantar da kanta akan cinyarsa, yatsarsa yasa yana shafa girarta yace “me kika jiyo a waje?”

Kallansa tai tace banji komai ba amma naji yanzu agun Gimbiya, meke faruwa da zancen murabus?

Zeenah?
Eh yanzu ta kirani take tambayata ko naji wani abu, da alama tana cikin damuwa.

Shiru yadanyi tare da dakatawa da dan shafa girarta da yakeyi cikin wata murya yace “Binta!”

Naam ta fada a hankali, yace “duk abinda Zeena zata miki kiyi hakuri, batada halayen banza rashin tarbiya mai kyau da ganin ta isa ne yasa take abubuwan da take, amma in kika santa a hankali zaki fahimci ba haka take ba.”

Kallansa tai duk tadanji zafi wanda kishi ne kowa yanadashi amma murmushi tai tace “insha Allah, sai dai ina ganin ka fada mata ko hankalinta zai kwanta, tunda harya kirani ta kaskantar da kanta alama ne na ta matsu.

Ba musu yace “Shawararki tayi bari naje yanzu.”

Mikewa tai jiki a sanyaye tana ganinsa ya fita, shiru tadanyi tana tunani dan harga Allah batasan daga fada zaice zaije yanzu ba.

Bangaren Zeena ya nufa tana zaune sai dai gaba daya ta rasa abinda ke mata dadi balle tanaso dare ya kara rufawa ta nufi gun Ramlatu.

Jin sanarwar isowar Junaid ne yasa ta mike zunbur.

Junaid ya shigo ta gaisheshi cikin mamaki tace “Ya Junaid.”

Zama yai sannan ya kalleta yace “Tunanin me kike?”

Kallansa tai sannan ta karaso ta zauna tace “bakomai.”

Binta tace kina cikin damuwa.

Binta?
Ya kalleta tare da daga kai, kallansa tai tace “Ya Junaid akwai abinda ya faru tsakaninka da Abba ne dan Allah?”

Junaid daya zuba mata ido baice komai ba, ta daure tai murmushi tace “nasan ba lalai ka fadamin ba, amma ni nasan haka kawai Abba bazai taba yadda yai murabus ba.”

Idanunsa ya dago ya kara kallanta sannan yace “komenene tsakaninmu ne, kar kiyi bincike kar kuma kiso sani.”
Yadan yi shiru kafin yace “wannan umarnine miji yake ba matarsa, in lokaci yayi komai zaki sani.”

Kallansa tai cikin dakiya duk da rauni da zuciyarta tai sai dai ta daga kai, dan tana san Junaid matuka.

Junaid ya kalleta a ransa yace wannan taimakon kadai zan iya miki a wannan lokacin.

Kafadarta ya dafa yace “ki taimaka.”

Kai ta daga cikin sanyin jiki.

Sai da safe ya fada sannan ya fita.


*******
Gaba daya Abdulsalam ya kasa sukuni, balle zance yazo mai har magana ta fara fita wasu garuruwa.

Sam ya rasa abinda ke mai ciwo, Azeema!
Ita kadaice zata sa Junaid ya bar abinda yakeyi.

Kallan Hadiminsa yai yace “yi maza ka kiramin Azeema.”

Yana fita Hajjo wacce ta gaji da tsayuwa tace “ina zaka?”

Yace “Takawa ne yace na kira Gimbiya.”

Cikin kumburi da bacin rai Hajjo ta dannu cikin turakar Takawa.

Juyowa yai cikin mamaki dan yasan har baici ace tazo ba.

Kallanta yai yace “Hajjo? Me kike anan?”

Cikin masifa tace “koma menake ba damuwarka bace me kake nufi da ni? Wlh sai dai a mutu ai rai amma duk duniya ba wanda ya ksa kwacema Zubair sarautarsa.”

Cikin kuluwa yace “naji jeki dan Allah.”

Wai me ka daukeni.......

Tsawa ya daka mata yace “jeki nace ko?”

Kallansa tai tana hakkin bakin ciki kamar zatai magana ta fita rai a bace.

******
Gimbiya yana jiranki fa.

Kallan Barira tai tace “banace ace bazanzo ba?”

Barira cikin mamaki tace “Gimbiya.”

Azeema ta kalleta tace “fita ki kuma rufemin kofar dakina.”

Nan ya juya ya fita.......

******
Ayusher🏌🏻♀️

*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{44}


Bazata zo ba?

Dan aiken ya zube a kasa yace "tuba nake Ranka ya dade, hukuncina mai karfi ne."

Abdulsalam hankalinshi ne ya kara tashi, har ya yi hanyar kofa zaije gunta sai kuma ya dawo, zama yai tare da hade hannayensa yana tunani, rana a zaune ya kwana dan duk yanda yaso yai bacci kasa wa yai.

Junaid kam baccinsa yai karfe hudu ya bude idanunsa tare da kallan Binta, shawarar daya yanke jiya kafin yai bacci ya sake tunowa, tabbas wannan shawarar itace ta dace a wannan lokacin.

A hankali ya zare jikinsa ya gyara mata kwanciya, kallan fuskarta yai cikin jin dadi sannan ya sumbaceta ya sakko.

Bangarensa ya nufa ya kimtsa suka fito massalaci shi da Azi, bayan sunyi sallah ne ya zauna yai karatu sosai har sai da gari yai haske,ya kalli Azi yace “ka dubo gidan Wazirin?”

Cikin rada yace “eh.”

Tare suka fito suka nufi hanyar waje, masu kula da kofa basu kawo komai ba saboda jalabiya ce a jikin Junaid sannan ya sa hula dan kar a ganeshi.

Gidan Waziri suka nufa kai tsaye, Waziri na soro inda ya maidashi karamar fadarsa.
Yana zaune yana jiran kummalo.

Bafaden sa ne ya shigo ya sanar dashi yayi baki, Waziri cikin mamaki yace “da safen nan?”

Kallan kofar yai bayan ya musu izinin shigowa.

Zumbur ya tashi tsaye cike da al’ajabi yace “Yarima!”

Junaid ya zare hularsa sannan ya kalleshi, hankali a tashe ya fara kokarin shimfida katuwar dadduma akan wata daddumar, yama kasa sawa ayi.

Junaid dake tsaye ne yace “nan ma ya isa.” Ya nunamai asalin daddumar dake shimfide.

Duk ya rasa me zaiyi, Junaid ya zauna sannan Waziri ya gaisheshi.

Kallansa Junaid yai ya mai alama daya sallami bafaden, nan Waziri ya sallameshi.

Azi ya fita ya rufo musu kofa tare da tsayawa a jikin kofar.

Waziri ne ya kalli Junaid yace “Yarima!”
Junaid ya dan kalleshi cikin tsananin kasaita da mulki yace “Zuwa nai nama gargadi da kuma
Kashaidi.”

Waziri ya kalleshi gabansa na faduwa, murmushi Junaid yai yace “ka saki jikinka bawai neman magana nazo ba nazone na nunama hanyar da kuke nema mai bulewa.”

Kallansa Waziri yai a tsorace, Junaid ya kalleshi yace “idan har kunaso na yafe muku laifinku na hada baki gun halakar da mahaifina da kukai, na yafe muku na cigaba da rayuwar da kuke buri bayan rasuwarsa to dole kubi abinda zan sanar dakai a wannan lokacin.”

Yawo Waziri ya hadiya cikin tsananin fargaba kenan yasan hadda su?
Junaid yace “kayi gaggawar sanar da ‘yan uwanka su Shamaki dasu Galadima idan har suna san su da ‘ya’yansu su tsira to tabbas sai kunbi abinda nakeso.”


Waziri ya daure yace “me zamubi?”

Dukanku kar wanda ya sake zuwa gun Sarki Abdulsalam.”

Da sauri ya dago ya kalleshi yace “bangane ba Yarima!”

Junaid yace “duk cikinku nasan kafi kowa fahimta shiyasa nazo gunka, maganar daya ce koya aiko kuje kusan karyar da zakumai karkuje, in kuma har naji labari ko naga daya daga cikinku yaje kiran Sarki daga yau zuwa gobe to lalai daga ku har zuri’arku ku shirya fuskantar babban hukunci.”

Waziri yai shiru yana mamakin wannan yaran wanda sanda ya dawo yaro kamar bashida ilimi, daurewa yai yace “in mukai fa?”

Yace “in kukai abinda nace zan barku a matsayinku sannan zan yafe muku.”

Kallan zargi waziri yama Junaid dan bai yadda da wannan maganar ba.

Junaid ya kalleshi yace “Ruwanka ne ka yadda ruwanka ne kaki yadda sanda karkai tunanin nazo nan a san rai nane bayan nasan laifin da kuka aikata, zansa ido inga abinda zakai.”

Yana kaiwa nan ya mike ya fito bai jira ko Waziri ya tattaro tunaninsa ba.



Yana fita waziri ya zauna yai shiru.


********

Ana kawoma Abdulsalam karin kummalo ya kalli Jakadiya dake basu umarnin inda xasu ajiye yace “Jakadiya a aika a kiran Waziri.”

Da sauri tace to, kallo daya zakama Sarki kasan yana cikin wani hali ko dan yanda yanayinsa gaba daya ya canza.

Sam ya kasa cin abinci har dan aiken ya dawo, sanar dashi yai wai Waziri baya gida, nan ya aika a kira Shamaki, sai dai shima akacemai wai Shamaki bashida lafiya, bai hakura badai ya aika a kiramai Galadima, nan ma aka dawo akacemai wai ya je ganin gona.

Nan ya fahimci zuwa ne basa sanyi wanda hakan ya kara daga mai hankali, dan har tsoronsa ya fito karara dama yana tunanin in su Waziri suka bi bayansa tabbas zai samo mafita, wato suma sun yada shi kenan ko me?

Hankali a tashe yace “Akira Azeema.”

Kallansa dan aiken yai yace to, haka nan ya dawo ya sanar dashi wai tana bacci.

Gaba daya Abdulsalam ya fara neman zaucewa, yace “banda kowa kenan ko me?”

Dan aiken yace “ko na kira Hajjo?”

Hajjo? Me zatamin wannan?

Tausayinshi ne ya kamashi ya mike zai fita, Abdulsalam yace “kiramin hajjo.”

Nan ya fita, Hajjo na zaune ranta duk a dagule, ga Zubair a gefenta, nan aiken Sarki yazo mata.

Mamaki ne ya kamata da sauri ta mike ta zura alkyaba dinta ta fito.

Sarki sai safa da marwa yake a daki haryanzu ko abincin da aka jera mai bai kalla ba.

Hajjo ce ta shigo, mamaki ne ya kamata yanda ta ganshi duk a rikice.

Tace “Takawa mai ya sameka?”

Abdulsalam ya juyo da sauri, hannunta ya kamo ya zAunar da ita, kallanta yai yace “Hajjo ki taimakamin, gaba daya na rasa yanda zan shawo kan matsalar dake gabana.”

Matsala? Kai da kake neman ba Dan Azeema mulki saboda soyayya wace matsala ce dakai?

Abdulsalam ya kalleta yace “ke yanzu a yanda nake din nan kina tunanin har zan iya ba ko dana na cikina ne mulki balle dan da ba nawa ba?”

Cikin rashin fahimta Hajjo tace “bangane ba?”

Kallanta yai yace “Junaid ne duk ya shirya wannan abin, kuma a gobe yake so ya kwace mulkin nan, sam na rasa yanda zan shawowa matsalar.”

Wata dariyar rashin yadda tai tace “har Junaid yakai girman da zai saka kai abunda bakai niyya ba?”

Abdulsalam yai shiru, kallan zargi tamai tace “ko yasan wani sirrinka ne?”

Kallanta yai yace “kema kinsan sirrin nawa ai.”

Tace ni? Ta tambayeshi cikin rashin fahimta.

Kallanta yai yace “Yayana Zubair.”

Baki ta hangame ta bude tace “da gaske kana da hannu a ciki? Amma sanda na tambayeka kacemin bakada hannu harda min fada.”

Shiru yai, can yace yanzu duk ba wannan bane matsala yanda zan kwaci mulkina na koreshi ko na halakashi nake nema.”

Mijin yar taka?

Kallanta yai yace “da dan me na bashi ita? Ai dan kome ya faru ya yafemin ne a matsayin mahaifints.”

Hajjo ta kalleshi tace “da can bakasan dani ba sai data keabe muku kai da matarka ta so? Sannan yanzu bani ba neman ruguza rayuwar yarka kake?”

Yace “shawara na kiraki muyi, kinsan dai in komai yai daidai Zubair danki ne zai gajeni wannan alkawari na miki.”

Kallansa tai tace ka tabbatar?
Da sauri yace eh

Tace ka kwace yar ka kace sai ya hakura da abinda yake shirin yi zaka mai data.

Wani kallan takaici ya mata dama can shiyasa bai san yin shawara da ita gaba daya bata da lissafi, a kufule yace “dama can santa yakeyi? Da har in muka dauketa xai bar abinda yake?”

Tace “eh mana, ka bari na gwada ka gani, ai namiji ba sai yana san mace kadai ba da zaran ya dandana zumarta magana ta kare, nasan yanda na shirya ‘yata.”

Cikin takaici yace “to jeki.”

Mikewa tai tace “zan aiwatar yanzu zakaji sakamako mai kyau.” Haushi yasa ma bai kulata ba.

Jakadiya ce ta shigo da sauri bayan fitar Hajjo ta zube tace “Takawa, sarkin Zazzau da sarkin Kano sun aiko tayaka murnar ba surukinka mulki da zakai.”

Idanu ya zaro yace “mene?”

Jakadiya tace yanzu dakarun dake kula da kofar gari suka aiko a sanar yanzu zasu shigo kofar garin.

Jikinsa ne ya kaure da rawa.

Wannan yaro anyi tsinane

******
Ayusher🏌🏻♀️


*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{45}

Hajjo ta fito daga bangaren mai martaba kai tsaye ta nufi bangaren Zeena.

Zeena na zaune ta gama cin abinci kenan, haka kawai tun jiya takejin dadi, a kalla tasan Junaid ya damu da ita, a hankali takai hannunta kan kafadarta inda ya dafa ta jiya, wani lalausan murmushi ta sake cikin jin dadi.

Fure ce ta kalleta tace "Gimbiya kalau dai ko?"

Kallanta Zeena tai, Fure tace "naga kina dariya ne kamar....." sai kuma tai shiru.

Zeena ta kalleta cikin takaici, tace "wlh fure na kusa koraki gun Hajjo can kika fi dacewa ba nan ba, wato nice mahaukaciya kenan?"

Da sauri Fure tace "Gimbiya ba haka nake nufi ba wlh."

Zeena tace ko?
Da sauri tace eh.

Alama ta mata data matso, da sauri ta matsa kusa da ita da jan gwiwa.

Zeena ta daga hannu da sauri Fure ta runtse ido tana jiran saukar mari.

Jin shiru yasa ta bude ido daya kafin ta bude dayan idan, Zeena tace "nama fasa aikaki gun Hajjo hada kayanki ki koma gun Binta, can itace zata iya da haukarki."

Fure tace "tuba nake Gimbiya wlh bazan iya zaka gun kowa ba in bake ba."

Hannu ta kara dagawa, da sauri Fure da sake rufe ido, Zeena tasa hannu ta dungure mata kai tai baya, tace "tashi kije can waje cikin rana ki tsaya, nama fahimci duka da hannu batawa kaina lokaci ne."

Fure tace "Haba Gimbiyata, kin manta yau kwananki ne? Ai yanzu zamu fara shirin kwana."

Murmushi Zeena tai tace "kin wanke kanki, me zamu shiryama Ya Junaid yau?"

Fure zatai magana Hajjo ta banko kofa.

Baki a sake Zeena ta kalleta, Hajjo tace "tashi."

Tashi? Wa? Ni?

Hajjo tace "a'a ni."

Zeena tace "meya kawoki dakin sirikinki? Bayan ko gaisheki baizo ba tukun?"

A kufule tace "suruku, kin tashi kin fito mun tafi ko sai na sa an ja ki?"

Zeena fuskarta dauke da mamaki tace "wai ni za'a dauka ko kuwa wata? Na tabbatar kinsan halina da abinda zanyi da wanda bazan ba."

Hajjo tace "yau kuwa dole kiyi abinda nakeso, kin tashi mun tafi ko sai na ci mutuncinki, aure ne na raba ya kawo miki takardarki, ya dau uwarsa da matarsa su koma kauye."

Da fuskarta alamar mamaki ta fara nunawa kafin ta sa dariya tace "lalai Hajjo ni yau Allah yasa lfy kike?"

Kin wuce ko kuwa?"
Gyara zamanta tai ta kalli Fure tace "dubo in Ya Junaid na nan kece mai Hajjo tazo zasu gaisa."

Fure data tsaya a kofa tun zuwa Hajjo tai waje da sauri, Hajjo tace "uban wa yace ina nemanshi? Balle har mu gaisa?"

Zeena bata ce mata komai ba sai kallan gefe ma datai.

******

Binta ce ta gaisheda Sabisu cikin sha'awa ya kalleta yace "Masha Allah kece matar Yariman?"

Binta ta kalli Junaid cikin kunya sannan tai kasa dakai."

Sabisu yace "kai lalai Yarima kayi sa'a na tabbatar da Sarki nadarai da ya kasance mai alfahari da zabinka."

Junaid ne ya kalli Binta wace ganin bai dawo yaci abincin safe ba yasa ta bi bayansa yace "nayi laifi amim afuwa."

Dan kallansa tai ta kasan ido tamai alama da zata wuce, dan wata kunyace ta rufeta datasan akwai babban mutum a can da bazata taso ba.

Junaid yace "Baba tun kafin inyi laifim da za'a dakeni bari naje."

Dariya sosai Sabisu yai yace "waya isa tabaka Yarima? Ko 'yarnan?"

Binta tace "zolayarsa ne wlh."

Da sauri ta mike cikin kunya ta fita.

Dariya Junaid yai, Sabisu cikin sha'awa ya kalleta sannan ya kalleshi.

Junaid ne ya canza yanayin fuskarsa yace "Baba kana tunanin abokin naka zai kai takardar wasikar Gayyatar?"

Sabisu yace "ai inaji yanzu ma ya kai, amma me kake nufi da aika takardar gayyata dakai?"

Junaid yai wani murmushi sannan yace "daga jiya zuwa yau kana tunanin ya isa masarauta nawa?"

Sabisu yace "matsalar dansa ne ba shi din bane, amma shi a lokacin Sarki Zubair in aka aikeshi kai sako kwana daya yakeyi ya je masarauta hudu."

Junaid cikin jinjina yace "masha Allah, to d'an nasa musamai ran daga jiya zuwa yau yaje uku kenan?"

Sabisu yace "eh."

Azi dake bakin kofa yana neman izini ne Junaid yace "shigo."
Nan Azi ya shigo ya gaisheshi, sannan yace "Yarima ance Masarauta biyu na kano da Zazzau sun aiko da sako kyaututuka da taya murnar Murabus din sannan da jinjinama Sarki, wasikar yanzu za'a shiga da ita fada."

Junaid ya kalli Azi yace "Alhamdulila komai na tafiya yanda ya dace."

Kallansu yai yace "bari naje na dawo."

Mikewa yai ya nufi bangaren Binta.

Tana zaune akan kujera ta cika ta batse ya tura kofar tare da dan gyara kafadarsa.

Kauda kanta gefe tai cikin nuna alamar fushi, zama yai kusa da ita sannan yadan bige kafadarta da kafadarsa.

Kara kauda kai tai, turata yai daga inda take ta matsa ya kara turata, mikewa tai zata bai gun, da sauri ya maida ita ta zauna yace "Bintalo na tuba."

Kara hade fuska tai.

"Laaaa har na tuno wata rana, muna zaune a waje ana hira cikin hasken farin wata, wata ta......"

Da sauri ta toshe mai baki tace "Na hakura ya isa ba sai ka fadi me nai ba."

Yana dariya yana kokarin yin magana bakin nasa a rufe.

Dan cizo ya mata a tafin hannun nata, sakeshi tai tana cewa "yaya Allah na hakura."

Yace "inaaa ai sai na karasa."

Batasan sanda ta sake rufe bai baki ba ta daddane shi da jikinta tana girgiza mai kai.

Idanunta yake kallo yana dariya sannan ya daga kai alamar ya daina.

Sakeshi tai tare da cewa "Allah Yaya gaskiya ka gama dani, ka gama sanin komai nawa ina yarinya nasan haka zakai ta zolaya ta."

Dariya yai zai sake magana sukaji ana magana a waje.

Baiwarta ce ta shigo ta sanar da ita sakon Fure.

Junaid ne ya kalleta fuskarshi dauke da mamaki, kallan Binta yai yace "bari na dawo yanzu."

Bangaren Zeena ya nufa, Hadimansa na biye dashi.
Yana kokarin shiga yana Hajjo rike da Hannun Zeena ita kuma tana zaune, ta rike kujera da daya hannun.

Hajjo ko da ganin Junaid bai sa ta bar abinda take ba.

Zeena na ganin Junaid ta warce hannunta da karfi ta nufi kusa da Junaid ta tsaya a bayansa tare da rike rigarsa ta baya.

Hajjo ya kalla alamar karin bayani.

Fuskar Hajjo a turbune tace "ka gaida ni ne?"

Junaid yace "jira nake ki zauna."
Haushi ya kamata tace "ba zama nazo ba tafiya da yar Abdulsalam zanyi tunda bakaga darajar yarsa ba kake neman wulakantashi."

Kallansa Zeena tai cikin rashin fahimtar kalaman Hajjo, Junaid ne ya kalleta yace "babu wulakantace a duniya sai wanda ya wulakanta kansa, sannan duk wanda ya wulakanta mutum da saninsa to lalai cikin dayam biyu ne kodai wanda aka wulakanta baisan kanshi ba ko kuma bashida daraja."

Hajjo ta cika da bacin rai tace "bamu 'yarmu."

Junaid ya kalleta yace "gatanan in zata biki."

Da sauri Zeena tace "Ya Junaid?"

Sannan ta kalli Hajjo tace "ba inda zani."

Junaid Hajjo ta kalla tace "bata takardarta, na tabbatar inka saketa dole ta tafi."

"Takarda?"

Hankali Zeena ne ya tashi tace "Hajjo baki da......"

Kallan da Junaid ya mata ne yasa tai shiru ranta yayi matukar baci.
Junaid yace "wannan kuma banga mai sani inyi abinda banyi niyya ba."

Sannan ya sake kallanta yace "ki huta lafiya."

Ya juya ya fita.

Hajjo kam kiris take jira ta fashe da alama.


*******

Isowar masu aiken sarakunan nan ba karamin hargitsa kwakwalwar Abdulsalam akai ba, yana makale a kasa a lungun gado kamar zautace yana cewa "a'a ba wanda ya isa ya kwacen mulki."

Nace sai mugani ai🙄



*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{46}

Gaba daya Azeema banda kwanciya a daki ba abinda takeyi, zazzabin ya barta amma abinda ke zuciyarta ya kasa sakinta, a duk sanda ta tuno abinda ya faru sai taji kwalla na neman kawo mata, ba shakka tasan tama Zubair babban laifi amma inta tuna ta bada kofa anyi amfani da ita ne sannan yanzu hankalinta ya kaimata ai shi Abdulsalam din shine ya kaita gun mai maganin, kenan dama ya gama shirinsa?
Duk sanda ta tuno hakan wani hawaye ne ke zubo mata.

Barira kam ta rasa abinda ke mata dadi, gashi Azeema tace karta sanar da ko Safiyah.

Inta gaji da kwanciyar ta mike tai tasbihi da hailala.


*******

Gaba daya shi kadai ne a cikin tangamemen kilisarsa yana zaune a lungu hankalinsa a tashe.

Jakadiya ce ta sake shigowa tace "Takawa ana jiranka a fada."

Abdulsalam ya kalleta hankalinsa a tashe, sannan yace "to."

Da kyar ya daure hadimansa suka shigo suka tayashi shiryawa.

Junaid yana zaune falan Binta amma gaba daya hankalinsa nakan Azi akan ya dawo ya sanar dashi ko Sarki ya shiga fada.

Binta ce ta fito daga daki ta kalleshi tace "Yaya!"

Kallanta yai yace "zuwan zakiyi?"

Tace "tunda kai bazaka ba gwara ni naje, dan Allah yaya kazo muje Allah Umma batada lfy."

Yanda ya kalleta tasan bazashi ba, fuska ta hade tace "shikenan."

Ta fita, murmushi yai tare da kara jiran Azi.

Binta ko minti biyar da fita batai ba Azi ya dawo.

Junaid na ganinshi ya mike yace “ya?”

Azi yace ya fito daga sashensa.

Nan Junaid yace muje.

Tare suka fito hadiman sa suka bi bayansa suna tafe ya kalla Azi yace “Zeena fa? Tabi Hajjon?”

Yace “a’a tana bangarenta.”

Su Waziri fa?
Sun iso yarima.

Junaid ya jinjina kai sannan yace “Zubair fa?”

Haddashi?

Junaid yadan kalleshi kadan yace “haddashi.”

Nan Azi ya amsa aike sannan ya juya.

Junaid fada ya wuce daga nan kai tsaye.

A fada kuwa Sarki na zaune bayan ya amsa gaisuwa ne, kallan Waziri yai wanda kansa ke kasa, ya kalli Shamaki shima kansa na kasa, ya kuma kalli Galadima.

Daurewa yai yace “banyi tsammanin taran gaggawa haka ba, Allah yasa komai dai lafiya.”

Turaki cikin mamaki yace “Ranka ya dade ai mu sako aka iso mana dashi akan kana neman nemanmu a fada.”

Nan kowa ya amsa da hakan ne, Sarki yai shiru kenan Junaid ne? Uban me yake nema dashi?

Zagi ne ya sanar da isowar Wakilan da aka turo, Sarki ya basu izini cikin dakewa, duk da yanda gabansa ke faduwa.

Suna shigowa Zagi ya sanar da isowar Junaid.

Ba Sarki ba hatta su Waziri sai da gabansu

Please Login or Register in order to submit comment