Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

ya sani me zai min? Ka manta abinda ya mana?”

Hannunta ya kama ya zaunar da ita gaban abincin sannan yadau cup din tea dinta ya kurba sannan ya mika mata.

Amsa tai ta kurba ba tare da ta musa ba, tsamen dake gabanta ya dauka ya kai bakinta, ba musu ta bude bakin yasa mata sannan yace “zan tura Azi ya nemoshi.”

Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa sai murmushi da tai kawai ba tare da tace komai ba.

Gefen kanta ya shafa yace “yau Bintoto...”

Ture hannun tai ta harareshi tace “Ya Junaid kasan banasan sunan ko?”

Dariya yai yace “Bintalo...”

Ajiye cup din tai tace bazan maci ba.

Na tuba a yafemin.

Dariya tai tace “sai ka fadi abin.”

Yace ah to bari na shirya.

Hanayenta ta hade tana jiransa.

Dariya yai yace “Nana Fadima na tuba....”

Dariya yai sosai shikuma ya hade fuska.

Tace “Ya Junaid dan sake.”

Naki din.

Ya fada cikin wasa.......

Ayusher🏌🏻♀️

*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{41}

Kallan Azi yai yace “ka fita wajen gari ka yadamin jita jita cewar Sarki Abdulsalam ganin dawowar asalin dan Sarki Zubair yasa zaiyi Murabus ya ba asalin magajin sarki mulkinsa.”

Azi ba tare da tambaya ba yace “To Yarima.”

Nan Ya fita da wasu hadiman Junaid, haka sukai ta yadawa tun daga cikin fada har wajen masarauta.

*******

Sam Abdulsalam ya kasa zaune ya kasa tsaye, afa da marwa kawai yakeyi a cikin kilisarsa.

Isowar su Shamaki ce yasa ya koma ya zauna.

Cikin tashin hankali suka shigo, Mai Martaba meke faruwa?

Abdulsalam ya kallesu yace “yaran nan ya san komai.”

Galadima yace “taya za’ai ya sani abinda akai yana tsimma? Hatta wanda yai maganin fa mun ga bayansa.”

Abdulsalam yace “to kamar mai aljannu yaran nan hankali a kwance yazo ya sanar dani komai, Sabisun kansa baisan abinda ya faruba rabi da kwata in dai har ba aljanu ne dashi ba to ba yanda za’ai ya sani.”

Waziri ne cikin nazari yace “ko dai Gimbiya ta fadamai abinda ta sani ne?”

Taya zata fadi abinda tasan zai ja mata matsala?

Shiru sukai suna tunanin abinyi.

Jakadiya daga waje ta nemi iso cikin tashin hankali.
Kallan juna sukai sannan sukace lafiya?

Jakadiya ce ta shigo ta zube tace “Allah ya taimaki sarki yanzu labari ya karade ko ina akan wai zakai murabus.”

Hankali a tashe suka kalli juna sannan a tare sukace “Murabus?”

Jakadiya tace “wai zaka maida sarauta inda take, tunda magajin sarki ya dawo.”

Cikin tsakanin tashin hankali sukace “magajin sarki? Junaid?”

Jakadiya tace “ ka gafarce amma zance ya gama karade gari anata jinjinawa adalcinka.”

Sallama tai ta fito.

Ba karamin tashin hankali bane ya bayyana a fuskokinsu, musammsn Abdulsalam wanda yakeji duk duniya ba mai rabashi da kujerar mulkinsa.

Shamaki ne yace “yanzu ya zamuyi? Ya riga ya samu a karshen layin da babu mabula, yanzu inkace bazaka bashi ba mutane zasu fara zargin halayarka gaba daya mutane zasu bar bayanka, sannan inka bashi mu kuma gaba daya tamu ta kare.”

Ran Galadima a bace yace “wai yaran nan ba sirikinka bane?”

Gaba daya hucci kawai Abdulsalam yake, yama rasa me zaice.

********

Zeena na zaune Hajjo ta aiko tazo, tace “ace mata zanzo anjima.

Kafafunta da ake gyara ma farce ta kara mikawa sannan ta kalli Fure tace “waccen matar mara galihu tana ina?”

Fure tace “tana bangarenta ranki ya dade.”

Baki Zeena ta tabe sannan tace “Yarima fa? Ta tambaya cikin alamar tambaya mai karfi.

Fure ta fita da sauri dan dubawa, bata dade ba ta dawo cikin jin dadi tace “bayacan Gimbiya.”

Dadi ne ya kama Zeena tai murmushin farin ciki.

Hadimar Hajjo ce ta shigo cikin tashin hankali tace “Gimbiya, Hajjo na nemanki cikin gaggawa.”

Zeena ta kalleta tace “kai!”
Kamar zata sake magana sai kuma ta mike ta zura alkyabarta wace ke kara mata kyau suka fito.

Mamaki ne ya kama Zeena ganin Hajjo a bakin kofa.

Tana ganin Zeena ta ja hannunta suka shiga ciki.
Ramlatu, Zubair da kanin Hajjo Suna zaune a kilisar.

Hajjo ta zaunar da ita a kasa a gabanta tace “fadamin dake a ka hada baki?”

Zeena cikin rashin fahimta tace “aka hada baki a me?”

Bakin Hajjo ne ya fara kumbura, fuska ta turbune cikin kunar rai tace “uban waye ya isa yasa Sarki murabus?wato ke dan hauka mijin da kwata kwata baki dade da aura ba shine yafi mahaifinki ko?”

Zeena tace “nifa bansan me kike cewa ba.”

Ramlatu ce tace “nifa nafi tunanin Azeema ce, matarnan ba karamin shiri ta iya ba.”

Hajjo cikin tsananin bacin rai ta kalli Zubair dake zaune kamar zaiyi kuka, tace “haka kawai an yada wai Sarki zaiyi murabus yaba asalin magaji mulki, inba Junaid ba wazai yadda wannan abin?”

Zeena ta mike tace “ni wlh na dauka ma wani abin ne, to in an yada dama ba mulkinsa bane, tun asali nashi ne dan yace yana san abinsa laifi ne?”

Hajjo ce ta mike ta daga hannu kamar zata kifa mata mari sai kuma ta tsaya tana hucci, Zeena kam kyar take ba alamar tsoro tace “Wai Hajjo sai yaushe zaki daina tunanin ba ya Zubair mulkin nan? Bayan ke kanki kinsan bashi da abinda Sarki yake dashi?

Ran Hajjo ya kara kololuwa gun baci, Zubair ne yace “bani dashi kuma a hakan zan amshi hakkina, daga yau Hajjo karki kara kirana ki kira yarinyar nan.”

Juyawa tai ta fita rai a bace, Hajjo cikin tsananin takaici ta bita da kallo.

******

Barira ta kalla tace “mene?”
Barira ta kara sanar da ita tace “yanzu duk abinda yake yawo keman a masarautar nan.”

Komawa tai ta kwanta, saboda zazzabi da ciwon kai data kwana dashi, kallan Barira tai tace “Barira ki aika a kiran Junaid, kice a fadamai banda lafiya.”

Nan Bari tace dakaina ma zani, ta fita.

Junaid na zaune suna dan hirar da shida Sabisu yana bashi labarin Sarki Zubair aka sanar da isowar Barira.

Sabisu ne ya shiga ciki sannan ya bata dama.

Zubewa tai ta gaisheshi sannan ta sanar dashi aiken Gimbiya.

Kallanta Junaid yai yace “Allah ya bata lfy.”

Barira ta dan dago tace “Yarima rabanta da abinci tun jiya shima dakyar tasha kunu.”

Kallanta Junaid yai yace “ki koma ki kula da ita tafi kowa sanin bazan zo ba.”

Barira ta bude baki zatai magana Junaid ya mata wani kallo, mikewa tai ta mai sallama ta fita.

Jin yanda sukai da Junaid yasa Azeema tai murmushin takaici tace “nasan nima bazsi taba zuwa ba sai dai zuciyata na fatan zaizo din.”

Barira tace “Gimbiya dukda bansan meke faruwa ba amma dan Allah kici abinci.”

Tashi ki fita.

Mikewa tai har zata fita sai Azeema tace “kiramin Binta.”

Kallan ta tai da sauri tace “Binta?”

Kai Azeema ta daga cikin azabar ciwon da kanta ke mata.

Binta tana zaune tanata gyara fuskarta, dan itama so take ta dinga fitowa das kamar Zeena.

Tayi kokari sosai dan tayi kyau, yanzu bata komai saboda jiya Harira ta kawo mata hadimai su uku.

Barira ce ta sanar da ita sakon Gimbiya.

Cikin jin dadi ta mike, kallan Barira tai tace “bari na aikama Yaya Mu tafi.”
Nan ta tura aka sanar da Junaid, kamar ya hanata sai yaga inya hanata tabbas xatai xargin wani abin.

******

Nan suka fito.
Suna kokarin barin kofar Zeena na dawowa daga bangaren Hajjo.

Kallan Juna sukai ita da Binta, kafin Binta ta gaisheta, Zeena cikin isa ta amsa su kuma suka wuce.

Cikinta shiga.

***

Binta ta shiga cikin daki, Azeema na kwance, hannu Azeema ta mika mata alamar ta matso inda take, mamaki ne ya kama Binta ta kasa matsawa harsai da Barira tace “Binta ki karasa.”

Azeema dake zaune Binta na matsowa ta kama hannunta cikin dana sani da takaicin abinda ta aikata.

Binta!

Kallanta Binta tai cikin sanyi.

Azeema tai murmushi tace “Junaid fa? Yana nan lfy?”

Binta ta daga kai alamar eh.
Barira ta kalla ta mata alamar ta fita.

Nan ta juya ta rufo musu kofa tana mamakin meke

damun Gimbiya? Yau ita ke yima Binta haka???

Nace daga baya kenan🙄🚶🏻♀️
Ayusher🏌🏻♀️

*🌞ZAFIN RANA🌞*
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻*

{42}

Gaba daya jikin binta ne yai sanyi, yanda Azeema ke rike da hannunta.

Can tace “Mamanki kince ta rasu ko?”

Kai Binta ta daga cikin sanyin jiki.
Murmushi tai tace “kiyi hakuri ban dubi maraicinki na jaki a jiki ba.”
Binta ta share kwallar da ta zubo mata.
Babanki fa?
Tunda ya koremu bansake komawa ba, sai dai bayan na girma munganshi da yaya shima yayan ne ya kaini sai dai bamuyi magana ba.”

Dayan hannunta ta dan daura a saman hannunta data rike.
Binta ta kalleta tace “nice mai laifi, na san ko wanene dole yaki amincewa dani, balle dan sarki?”

Kai Azeema ta girgiza tace “ko kadan san kai da dan zuciya ne irin nawa, a koda yaushe ina dauka nice nake tafiyar da rayuwata sai dai yanzu na fahimci duk rayuwata amfani ake dani, san kai dana ke tunanin ina dashi na gane duk shi ya jamin wannan rayuwar dana sa kaina.”

Binta bata san me take nufi ba hakan yass ta kslleta ganin yanda Azeema tai shiru cikin wani yanayi, daurewa tai ta kalleta tace “karki damu da halin da nake ciki ni nasa kaina a ciki.”

***********

Junaid ne ya kalli waje, ganin rana tadan fara sanyi ya kalli Azi yace “muje.”

Nan suka fito, Junaid ya sa kaya wanda ko ranar bikinsa baiyi irin wannan kyan ba, Alkyabar dake jikinsa mai tsananin kyau ce tamai kyau sosai, yayi rawani wanda bayi yake yi ba in ba da dalili ba.

Tunda suka fito ake gaisheshi, har suka isa fadar sarki.
Sarki wanda ke zaune cikin fada ya kalli manyan masu mukamai dukansu da suka iso akan abinda sukaji.

Turaki ne ya kalleshi yace “Dolene mu taso jin wannan babban al’amari, taya Ranka ya dade zaka yanke wannan babban hukunci ba tare da munsan komai ba.”

Sarki ne ya kalleshi, Waziri ya dafa Shamaki wanda yaga yana neman yin magana, Shamaki cikin takaici ya kalli Galadima wanda shima ya cika ya batse, Sarki ne ya kalli Turaki bayan yayi murmushi yace “to mudai wannan magana..........”

Kafin ya karasa aka sanar da isowar Junaid.

Hankalin Abdulsalam a tashe sai dai baiko kalli kofa ba, isowar Matawalle Junaid ne yasa duk kowa ya zubawa kofa ido.

Junaid ya shigo sannan ya gaisuwa ya ja ya zauna.

Sarki ne ya kalleshi yace “Matawalle kaima ka fito?”

Junaid yai murmushi yace “munzo ban hakuri ne akan abinda kake neman aikatawa.”

Kallanshi Sarki yai a ransa yace “me kuma kake shirin yi?”

Junaid ya sunkuyar dakai yace “Tuba nake ranka ya dade amma ina ganin hukunci da umarninka na ajiye mulkin nan yayi tsauri.”

Kallansa sukai da sarki dasu Shamaki, gaba daya shamaki da Galadima sun bude baki, Junaid ya dan kara dagowa yace “kace haka kama Marigayi Sarki Zubair alkawari amma ina ganin a sake dubawa.”

Gaba daya kasa magana sukai saboda tsananin mamakin wannan dabaibaiyo daya faru.

Turaki ya kalli Sarki yace “Amincin Allah ya tabbata a gareka, ashe alkawari kukai da sarki?”

Nan ragowar na fada suka fara jinjina ma imani da adalci irin na Sarki.”

Wale ne ya kalli Sarki yace “gaskiya Sarki Allah yasa ka gama da duniya lafiya, ba karamin mamaki mukai ba da jin wannan abun, da ranmu ya baci amma jin dalilinka yasa mun fahimci abinda kake nufi.”

Allah ya sa haka ne mafi alkairi.

Nan kowa yace Ameen

Gaba daya kwakwalwar Abdulsalam ta kulle, kallan Junaid ya shiga yi, Junaid yai murmushi sannan ya kallesu yace “ku ba Sarki hakuri taya zan hau mulki bayan da karfinsa?”

Turaki ne ya kalli Sarki yace “Takawa kaji abinda yace? Sai dai nasan alkawarin sarakuna ba’a ajiye shi.”

Da kyar Sarki ya daidaita nutsuwar sa sannan yace “To ka gani, dole dai ayi abinda ya dace.”

Junaid ne ya sake yin kasa dakai yace “ku ba Takawa hakuri ba jibi na ya bari sai nan da shekara.”

Jibi? A tare suka fadq harshi sarkin dai baisan ya fadi hakan ba.

Kallansa sukai jin muryarsa, murmushi yai yace “Jibin dai.”

Turaki yace “Allah ya kara ma yawan rai.”

Sarki ne ya kallesu yace “kaina nadan ciwo ina san shiga ciki.”

Nan suka kara gaisheshi ya fita.

Waziri dasu Shamaki suka fita suma.

Junaid ya tsaya suna ta gagaisawa dasu kafin ya fito.

Yana sa takalminsa ana sanar dashi Sarki na nemansa.

Bai musa ba ya nufi bangarensa kai tsaye.

Sarki na tsaye ya juya baya gaba daya hankalinsa ya kai kolokuwa gun tashi, idanunsa sunyi jaaa alamar tashin hankali.

Junaid ne ya shigo ya zauna zaman cin abinci a kasa sannan ya daura hannayensa a kan cinyarsa baice komai ba.

Juyowa yai ya kalleshi Junaid na zaune yana kallansa shima.

Cikin tsananin bacin rai Sarki ya kalleshi yace “me kake shirin yi?”

Junaid ne ya kalleshi yace “kai me kake shirin yi?”

Baki Abdulsalam ya bude yace “ni kake fadawa magana haka kanka tsaye?”

Ya kake so nawa makiyina magana?

Makiyi? Abdulsalam ya maimaita cikin jin haushi, Junaid na fada maka duk abinda ya faru akan mahaifiyarka ne ko? Ko duk ba akanka aka aikata ba?”

Wani murmushi yai yace “ita kenan itace zata yadda akanta ka aikata amma ni dakai munsan ba a kanta ka aikata ba.”

Hura hanci yai yace “Kasan ka kiyayeni?”

Junaid yai murmushi yace “duk abinda zaka aikata min inaso ka tuna abu biyu na farko kowa yasan ni zaka ba mulki jibi dan haka duk abinda ya sameni cikin dayan biyu ne ko kai ko Zubair danka ne, to sai dai matsalar na riga na sanarwa yarka duk abinda ya saman kaine, kaga shaidarta ta isa komai naka ya wargaje.”

Gaba daya Abdulsalam ya gama shan jinin jikinsa, ya kalli Junaid yace “to ka fito ka sanar da duniya laifin nawa mana.”

Junaid yai dan dariya yace “ karka damu komai da lokacinsa, sannan ina duba darajar yarka ko nace wacce ka bani ita saboda kana san boye laifinka ne, hakan yasa bazan fada ba, sai dai wannan shine kashaidi na karshe da zan ma, daga gobe ka tattara ka koma inda aka ajiyeni na zauna ko kuma ka nemi wani gidan ka zauna inba haka ba duk abinda ya biyo baya karkaga laifina, inada shaidu da zan lalata ma suna cikin mintina kadan wanda fita ma gagararka xatai.”

Mikewa yai zai fita, ita Azeemar fa? Badai kana tunanin ajiyeta anan ba?

Junaid bai kalleshi ba yace “duk wani mai laifi sai ya amshi laifinsa ko itace kuwa.”

Ya juya ya fita abinsa.
Yana fita Abdulsalam ya saki wani kara tare da zama a kan gado cikin tsananin bacin ran da tunda yazo duniya bai taba fuskan tarshi ba.

*****
Zeena ce ta kalli Fure tace “da gaske hakan ake yadawa?”

Fure tace “yanzu ma jinai ance wai jibi Sarki zaiyi murabus.”

Shiru tai tana nazari meke faruwa Ya Junaid?

Hajjo kam cikin kumburin baki ta sabi alkyabarta ita da Zubair suka nufo bangaren Sarki sai dai an sanar dasu bazai gansu ba.

Wannan abu ya kara koma mata rai matuka wanda takeji ko zata kwana a wajen nan bazata tafi ba sai ta ganshi....

****

{43}

Binta tana dawowa daga bangarenta taga Fure a bakin kofar sashenta, da sauri fa karasa.
Fure na ganinta ta azamo itama ta gaisheta.
Binta ce ta kalleta tace "lafiya?"

Fure tace "Gimbiya ke san ganinki."

Ba ta kawo komai ba ta bi bayanta suka nufi sashen Zeena.

Tana zaune a kilisarta Binta ta shigo, sai data gaisheta sannan Zeena ta sallami yan falan, kallan Binta tai sannan tace "Yarima ya fada miki wani abu ne?"

Kallan ta Binta tai cikin rashin fahimta tace "kamar me kenan?"

Zeena cikin isa tace "koma menene abinda dai ya shafeshi a wannan lokacin."

Cikin mamaki Binta tace "banji komai ba sai dai in ke bansan ko kinji wani abin ba." Ta fada cikin dakewa.

Mamaki ne ya kama Zeena yanda ta maida mata magana, sai dai yanzu ita duk ba wannan bane a gabanta.
Kallanta tai tace "Yace yana da abubuwan da yake so ya kammala a kwana uku, yau ne karshen kwana na farko, saura kwana biyu kenan, shi yasa nake san ji ko ya fada miki sama da haka."

Basuyi wannan maganar da Ya Junaid ba, kenan ita yake fadawa matsalarsa? Daurewa tai ta kalleta tace "nima abinda yacemin kenan, sai dai ya kara abu daya."

Zeena ta kalleta tace mene?
Shiru binta tai tana tuno abinda zata ce can tace "Yana san muyi hakuri har saikomai ya kammala sai nan zai samu nutsuwar fuskantar matanshi."

Zeena ta kalleta rai a bace kenan magana take fada mata akan karyai datai ya kwana da ita?

Binta ce ta kalleta tace "Gimbiya bada wani abin ma fada ba ina fada miki abinda na sani ne."

Zeena ta daure tadan daga girarta kadan kafin tace "kinsan zancen Sarkin yanzu zaiyi murabus ya ba Junaid mulki?"
Mamaki me karara ya bayyana a fuskar Binta, wanda kallo daya xaka mata kasan tana cikin tsananin mamaki, kafin Zeena tace "kinsan kuma murabus din jibi ne?"

Binta tace "bashida lafiya ne?"

Zeena tace "a'a lafiyar Abba kalau shiyasa na kiraki

Please Login or Register in order to submit comment