Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
, saboda na gama wasa da kai......... . KAI UMAR A TUNANINKU UMAR ZAI TSIRA KUWA TARAR ARADU Littafi na Uku 3 Umar lawan Abdul Typing Shuraih Usman Page 6 . . Na tsakiyarsu ya zo gabana "malam umar sai defa kayi hakuri don kuwa yau zan aikaka kiyama , saboda na gama wasa da kai, dun haka yanzu zan rataye ka kowa ya huta . Daga nan kuma sai ace abun duniya ne sukai maka yawa ka kashe kanka," Yana zuwa nan a maganarsa sai ya kece da dariya mara dadin sauraro, suma gabza gabzan da suke bayanshi suka tayashi suna masu kyakyatawa . Sun dau lokaci suna wannan dariyar alokacin da ni kuma na gama sallama rayuwata jira kawai nake mutuwata ta zo ta daukeni don na tabbata bazan tsira daga hannun wannan mugun mutumin ba . Babu abun da ya fara zuwa araina face yadda farida zata kasance izan na mutu nasan watakila itama ta mutun domin kuwa babu ta yadda zata iya rayuwa in batare da ni ba saboda zunzurutun so da kauna da take yi min . Alokacin dana tuna da iyayena sai wani kwallan bakin ciki ya yagangaro daga idona, sai a sannan na fara nadaman irin abunda nai masu, nasan ba shakka nabar masu abun gori a zuria gashi ni kuma zan riski ajalina a hannun wayannan mugayen mutane, . Katon dazu ya sake dubana lokacin daya tsuke bakinsa ga barin yin dariya, yace "kash Umar da alama naga kana son rayuwa a bankasa sai de nayi maka kashedi kaki ji dun haka sai a gaida Kiyama, " Yana gama fadin hakan sai ya sanya kafarsa ya ture teburin da kafana yake kai , teburin na faduwa sai na zazzago kasa, Igiyar dake daure a wuyana ta shake ni tamau na dunga wuntsila kafa funa ina neman taimako a haka har wani hazo ya ziyarci idanuwana, daga nan ban san Abun daya fsake faruwa dani ba . ******* A firgice na. Farka ina kiran Inna lillahi wa inna ilaihirr ra'ji'un, Na tsinci kaina acikin wani dan madaidaicin daki ina kwance akan gado ga mutane uku a gefen kaina, Na mike na dubi mutanen wayanda sam basu yi mani kama da mutanen dazu ba, don kuwa wayannan sun yi shiga ce irin na ma'aikata, sunci zanzaro sai kace mr mugopark . Wani daga cikinsu ya kariso ya miko min I.D card ,na duba a gaggauce na Hukumar 'yan sanda ne Suna : Azizu jakande Matsayi: Inspector . Take sunan ya fado min arai babu shakka kanin lateef ne wanda yace zai tuntuba da maganata sai na saki jiki . "Ka amice?" Ya nemi ra'ayina Na gyada kai "na amince" "To ina wanda ka kashe?" Na girgiza kai "ban kashe kowa ba" Duk suka bushe da dariya Ya dubi wani dan sanda "ku mai da mu a motarku wajen yana da nisa" Ya kame "an gama yallabai" ***** Ina zaune a dakina mutane uku kewaye da ni, na farko lateef ne sai kaninsa Aziz da kuma wani ban san ko waye ba, na dubi agogon bango karfe takwas na safe da minti hudu $ A sannane lateef ke cewa "Umar Allah ya kiyayeka ka tsallake rijiya da baya, ba dan an kawo agajin gaggawa ba da yanzu ana zaman jimami" Na dube shi "wai yaya abun ya kasance?" Ya gyara zama "izan zaka tuna min yi maganar kanina da kai, a daren jiya na taho da shi nufina ku gana, a sannan cikin sa'a na sami kofar dakin ka a bude, sai na kwankwasa amma shiru baka amsa ba, ganin ganawar dare ya kamata ayi saboda la'akari da cewa an zuba ido akanka, sai na yanke shawarar shiga na ta sheka, hakan nayi kokarin zartarwa ina saka kafa naji sailula na ringing dana duba sai na ganta kusa da kafata na sunkuya na dauka gami da nufar shimfidarka domin na baka ka amsa kiran, banga kowa a shimfidarba, na zaci bandaki ka shiga sai na danna ok domin baiwa mai kiran uzuri Ina fadin "hello' Wata kakkausar murya ta biyo baya "kai malalaci in ce ka shirya ko? Yanzu zamu aiwatar da nufinmu" Nayi shiru ina sauraron murdadden sakon muryar kuma taci gaba "kana iya hutar da kanka, kayi zamanka a daki nan muka zaba maka amatsayin kabari, ko kaje wani wajen sai mun maido ka" . Da fadin haka na tsinke layin da wurwuri na gane mai maganar da kuma inda ta nufa sai nayi saurin durfafar ban daki na kwankwasa da karfi amma ban ji amsa ba jin haka ya sanya ni turawa wayam na sami shi babu kowa a ciki, da sauri na gayyato kanina na labarta masa abin da ake ciki . Ya jinjina kai "zo mu ja jiki, yanzun nan kaga sun zo" Banyi musu ba muka fice daga dakin da sauri bayan da ya ajiye wata yar na'ura, mukaa nufi wani lungu muka rakabe, da labewar mu yayi waya head quarter' din yan sanda 'yan sanda goma ya nema masu zafi iya aiki, fadi inda zasu zo , ko minti ashirin ba ayi ba suka karaso, 'yan dakiku suka harba agogo wadanda su suka isa tattaunawa a kuma kaso rukuni-rukuni . A cikinsu ne kuma fitilar mota ta hasko layin ta durfafo kai tsaye yadda muka zata din haka ta afku a kofar dakinka ta tsaya bayan dan lokaci wani ya fitoo, kwankwasa kofar dakin yayi, kafin daga bisani ya tura kai ciki, ya dan jima kadan me yiwuwa minti biyu, watakila kuma uku ko hudu a cikinsu ya fito ya sake dawowa ga motar bayan 'yan maganganu duk kofofin suka bude, wasu kartin mutane biyun suka fito, 'but' suka daga inda anan suka kinkimo buhu, bamu raba daya biyu ba wajen tabbatar da cewa kai ne a ciki, suka shige dakin da kai . Na dubi kanina "mukai agaji Girgiza kai yayi "tukunna dai akwai sauran lokaci" . Kuyi hkri da short page dinnan Nidinne dai Shuraih Usman Inkiya 99% www.facebook.com/hausaebooksTARAR ARADU Littafi na Uku 3 Umar lawan Abdul Typing Shuraih Usman Page 7 . . Ya kunna wata yar karamar rediyo, daga ita ne muka ji duk abubuwan da ake tattaunawa, bamu mu rasa komai ba, har zuwa sanda suka rataye ka, da ace basu fito da wuri ba ritsa su yan sanda zasu yi, to amma fitowar da su sai ta taimaaka, domin da ba su fito ba din ba, za'ayi abin nan da ake kira anyi ba ayi ba, domin babu shakka da sunji alamar motsi harbinka zasuyi domin baza su so ka kubuta ba, suna kokarin hawa mota ne aka far musu in har kana cikin hayyacinka baza ka gaz jin harbin bindiga ba, suma fito na tasu sukayi akayi kare jini biri jini, sun raunata yan sanda uku su kuma an kashe musu mutum daya, biyu kuma sun shiga hannu bayan da akayi musu raunuka munana, akwai kato gabjeje shine mutumin dake wahal da kai ya kwana karkashin kulawar yansanda a daren jiyan dai an tura yan sanda uku asibiti su kula da farida gudun afkuwar wani abu" . Wani dadi ya cika zuciyata tuni na dungura goshi akas cikin sujjada dayiwa Allah godiya ban san adadin mintunan dana karar ba n dago fuskata cike da hawaye "Lateef kayi min komai kayi min abinda ban san kalmomin da zanyi amfani da su ba domin godiya, kayi min abinda wani mutum ba zai taba yi min ba, ka ceci raina ka kuma kyautata rayuwata, ka tsamo zuri'armu daga bakin cikin da zai dauwama har abada" . Ya dafa kafadata "kar ka damu umar, nayi don Allahh don kuma kaunata da kai, zanyi farin ciki idan kuma na ganka da farida a matsayin miji da mata don kuwa kun sha gwagwarmayar da bata cancanci tashi a banza ba" Na juya ga aziz hawaye na kwaranyowa daga idona "aziz me zance da kai? Na gode bata wadatarba, madalla tayi kadan to ina kalman?" . Yayi murmushi hutar da bakinka bana bukatar godiya wannan shine aikina akansa nayi rantsuwa , kuma don nayi ake biyana, abinda kawai nake nema kataya mu addu'ar Allah yaba mu damar sauke nauyi ya kuma bamu ladan abun da mukayi dai dai , inda muka kuskure yayi mana afuwa da rangwame idan ka yi haka shi kenan" Ya mike tsaye "zan tafi wajen aiki kumaa zan kokarta wajen ganin na sami ganawa da yayanka, zan warware masa komai shi kuma sai ya tunkari iyaye" . Na fashe da kuka "na gode ! Nagode!! Aziz Allah ya cika maka burikanka" Yayi murmushi "amin nima na gode" Muka mike tsaye domin rako su waje shi da mutanen da suka zo tare Ya fuskance ni bayan da muka fito "umar bincikenmu zai rutsa da mutum uku, principal malam Abba, da kuma Abokan zamanka na kasuwa da alama suna da hannu a abubuwa da dama . Yadan saurara daga bisani ya dora "zan yi iya yina don ganin shari'ar bata dauki lokaci ba! Za'ayi a kare a sati daya babu bukatar mai raunin ya warke, tunda raunin bai shafi gabobin hankali ba kafafu wane da hannu, zanyi wannan kokarin" Na ci gaba da jera masa kundin godiya ahaka muka rabu ********* Ina saka kafata dakin ta taso a guje na san nufinta shine rungume ni ni kuma bazan so haka ba musamman saboda ganin manya kusa da mu, cikin hikima na dan goce gami da riko hannunta don gudun kar tasha kasa "Dakata farida da sauran lokaci" Ta fashe da kuka "wayyo Allah umar da yanzu an cuceni da an takaita rayuwata" Naja hannunta zuwa kan gado a hankali na zaunar da ita nima na zauna "Umar barkanmu fa !"Zan cen mummy kenan tana mai zubar da hawaye, Nayi murmushi barka dai" Ta jinjina kai "wai hikimar Allah komai yana da karshe yau karshen wannan yazo" Na sunkuyar da kai"wallahi kuwa haka lamarin Allah yake" Ta mike domin ficewa daga dakin tasan tilas zamu bukaci ganawa Futarta taba farida damar matsowa kusa dani "umar yaka ji da ranka?" Nayi murmushi "naji abinda yafi dadi dadi abunda ya haure farin ciki fari abunda za a soma kwatanta shi da murna ba" Ta lumshe idanu"naji wanda ya ninka naka sau dubu, shi yasa na warke a tsakanin awoyi goma kacal dana sami labarin cewa ka kusa zama angona" "Aina kika sami labarin ke kuwa?" Tayi "a cikin mafarki, naga har an daura mana aure ina baka madara a baki a cikin wani lambu mai matukar kayatarwa" Raina yayi fari dajin kalaminta "to ni kuma fa me na baki ko ban baki komai ba" Ta kara lumshe ido"ka dandana min zuma mai mugun zaki" na jinjina kai you're right da sannu zaki dandaneta a farke da sannu zaki gane abunda ake kira soyayya atare da ni" Tayi murmushi "ka cika garaje kai fadarce babu cikawa , ni kuma ka bari ka gani sai ka ringa kai karata wajen mummy" "Wahalar dani zakiyi kenan?" Ta gyada ki "kwarai kuwa,bazan barka ka sake ba sai ka dandana kudarka , amma fa da zunzurutun kauna" Muka more da dariya Tadan kimtsa "Umar za'abari ka aureni kuwa?" "Me zai hana" "An baka wata baka so" "A ina ki kaji?" Ta kwantar dakai "lateef ya fada min komai na dade ina mamakin yadda ka shirya wa kanka zafi saboda ni" Nayi murmushi "manta d wannan na fada miki dalilin auren, kuma yanzu ya kau ki dauka cewa abubuwan da ki ka gani a mafarki ba mafarki bane, ki dauka cewa an yine a gaske, kuma. Za'ayi din" ."Ka tabbta?" "Na tabbta" "Oh I love you" "I too" muka kara morewa da dariya .......................... AYYA UMAR ANSHA DAKYAR TO AMMAFA AKWAI WATA........... . www.facebook.com/hausaebooksTARAR ARADU Littafi na Uku 3 Umar lawan Abdul Typing Shuraih Usman Page 8 . . Jerin kwanaki suka mirgino gareni cikin farin ciki da walwala, duk wani mutum na jiki yasan cikakken labarina, na shirya da yayana ,iyayena suka yimin uzuri sannan abokaina suka runga zuwa daya bayan daya duk abinda ya afku gareni ya zama kamar an yi ruwa an dauke bani da sauran bakin ciki yayana da kansa ya nemi dana koma gidansa, na kasance cikin jin mamakin yanda abubuwan suka faru, a Naira dubu hamsin malam Abba ya sa aka koreni , jamil kuma shine me sanar da abubuwan da ke faruwa a kasuwa! Tasa kwangilar yayi tane a Naira dubu dari da hamsin . Labarin nasa yana da takaici shi ya sanar da mutumin aiken da aka yi min da kudi shi ya sanar da shi ajiyar agogo, nayi mamaki da kansa mutumin yazo ya dauke shi ta hanyar amfani da master key kuma shi yakai agogon har dakina, wani abun haushi jamilune ya sanya min sailula a aljihun riga bayan da ya dade yana dakona, shi din ne dai ya baiwa mutumin samfurin makullin dakina, ta hanyar luma nawa a sabulu, a fadarsa lamarin ya fari wata rana daya ara bisa karyar zai bude lemo da wanda aka yanka ne karuwa tayi amfani wajen bude dakina a ranar data yi karyar na saba daukota kwanan gida . Kamar yadda aziz yayi min alkawari hakace ta faru ba'a dauki lokaci ba aka kaimu kotu, aka shiga tafka shari'a wadda aka kammala ta a zama biyar . Baya ga laifin kashe mutum uku a baya da kuma wahalar da ni an samu shaidanin da laifin sana'ar miyagun kwayoyi a wani gida da su ke kira birght house, can a wata unguwa nesa da cikin birnin duk wani mutum mai alaka da shi sai da yansanda suka kwakuloshi , aka yankewa kowa hukunci daidai da laifin daya yi Uban gayyar ya biya diyya Naira MILYAN HAMSIN-HAMSIN ga iyayen mutane uku daya kashe, MILYAN ASHIRIN bisa batamin suna ragowar kudin kuma ribar kafa ne aljihun gwamnati za su shiga, kafin daga bisani a rubuta masa takardar sake mazauni daga duniya zuwa kushewa shi da duk mukarrabansa na kusa . ******** . Na kimtsa tun da sassafe domin halartar wata tattaunawa da ake son yi tare dani a gidan mommy, jagoranta shine Alhaji Aminu tsohon mai gidana, hakika yanzu na zama mutum babu sauran wani tabo a tare danu bayan da aka shafe sama da wata guda kafafen yada labarai suna yayin labarina, nayi ta ganin mutane kungiya-kungiya kuma na kusa . Ban amince da cin ko naira daya daga diyyar da aka bani ba balle nayi amfani da su wajen huldar aurena, wanda ya rage mako guda kacal a daura shi na kugure a raina zan nemo tsarkakkun kudi duk inda suke, domin karasa tsaftace soyayyarmu, maimakon amfani da kudin da aka same su ta hanyar sayar da miyagun kwayoyi ksafta su nayi sai kace wani gwamna ko ciyaman, na lateef daban na Aziz ma haka wani kason kuma ga yan sanda da aziz yayi aiki da su, ragowar kudin tura su nayi kauyenmu aje can a gina katuwar makaranta . Da karfe tara daidai na isa gidan su mummy tuni kowa yana nan ni kadai ake jiran isowata mazaunin da aka bani ya dace da ni gani ga gimbiyata muka rinka satar kallon juna . Alhaji aminu ya numfasa"Umar na kirawo ka ne domin na yaba maka namijin kokarin da kayi na baka hakuri gami da baka kyautuka na musamman saboda jarumtar daka nuna umar na amince wa raina kaine mutum mafi da cewa da tallafawa harkokina bisa la'akari da jajurcewarka da kuma cika alkawarinka Ina gayyatarka fare ni kuma da fatan zaka amsa gayyatata . Na gyada kai"na amsa" Yayi murmushi "to ina godiya" Ya miko hannu ya dauko wata yar jaka a hankali ya budeta ya zaro wasu takardu daga ciki . "Matso nan" ya nema yana mai dubana Na tashi na kewaya ya ajjiye min biro "sai kasa hannu takardun gidana ne zan mallaka maka ni na koma sabon gida" Cikin makyarkyata da rawar hannu nayi rubutun ina jin lamarin kamar tatsuniya katoton gida ma'abocin wadatar da furanni zai zama mallakina ina kammalawa ya sanya shedu suma suka sa hannu sai ya miko min takardun gaza sa hannu nayin karba sai na fashe da kuka yajjiye min su gami da komowa ga lalubo wata takardar . Ya dago kai ga dubana "wadannan kuma takardun motane ya zama wajibi na siya maka abin hawa saboda harkar makudan kudade da zamuyi sai dai kayi hakuri ba wata mai tsada bace, Honda civic ce, tana garejin gidan sabuwa ce fil ba'a taba hawanta ba ga takardun da makullin yanzu ma kana iya zuwa ka dauki kayarka" . Wani sabon kukan ya kubuce min farida ma ta tayani da zubarda hawayen, tana mai sa hankaci tana share min nawa . Ya dora "bazan barka haka ba, kana bukatar kudi a hannu ga (cheque) cek nan na naira milyan , farida miliyan daya hajiya ma haka, dawainiyar biki kuma duk na dauketa daga lefen ango zuwa kayan dakin amarya da duk kudaden da za su ci ko su sha, da duk motocin da za'a bukata da duk kudaden da za'a kashe zan ware maku milyan daya" . Bani kadai ba duk mutanen dake wajen sun zubar da hawaye muka jerawa Alhaji kundi kundi na godiya . Ya kade babbar rigarsa "babu komai ai ni ne da riba na dade ina neman amintacce ban samu bayanzu kuwa da Allah ya bni ba zanyi sake ba" . Mummy ta dube shi "naji kayi maganar lefe mu ba ma bukatar lefe sadaki kawai mukeso shima don Allah ya wajabta shi" Ya girgiza kai "ina ! Za a yi lefe, kamar yanda kowacce ya ake yimata lefe, akwati bakwai ya isa?" "A'a a'a kar ka soma" mummy kenan Yayi murmushi "saide kiyi hakuri da ni , dabi'ata kenan idan nayi niyya bana fasawa, ba kuma zan canza yau ba" . ******* . Idan kana neman bikin aure da aka yi abubuwan ka sami namu, sai ka juya an sake iya sakewa ba kuma tare da kwabona ba duk a rigar arziki [ni kaina Shuraih 99% sai da na halarci wannan biki] . Akwai farin ciki marar misali yayin mu ka tsinci kawunanmu mu biyu a daki , bayan da muka gabatar da salloli da Addu'o'I da ake nema daga ango da marya, muka zuge kaji gami da tauna kwainar kwai, muka kuma sha duk abunda rai zai so ya sha, babu abunda ya rage a lokacin illa cin ribar wahalarmu Na bude tafin hannuna "sako naki a nan zamuyi alkawari" Ta sako nata hannun tana mai murmushi wata kunya ta kamani sakamakon jin hannunta dana yi taushi tubus tamkar wani ingantaccen soso ne da babu coge, na hakkake cewa I...... . Ku dai cigaba da bibiya don kuwa da kwai wani babban al'amari dake shirin faruwa game da iyalan Mummy . Nine naku Shuraih Usman Inkiya 99% Daga:- www.facebook.com/hausaebooks TARAR ARADU Littafi na Uku 3 Umar lawan Abdul Typing Shuraih Usman Page 9 . . Bani da amsar data wuce eh na amince musaMman a wannan hali da sai inda tayi da ni Ta matso da bakinta ta jonashi da nawa Abun da yafaru ya mantar dani lissafin dangina, Shakka babu yau ne ranar shayar da juna zuma da madara . Zaune muke a falo muna makale da juna lokacin da kaunarta a raina ya karu da fiye da kaso tamanin cikin dari, ban iya sanin dalili ba amma meyiwuwa saboda bushashhar daren jiya ne daren da nake ta fatan Allah ya cigaba da maimaitashi . Ta kewayo hannayentaa biyu cikin wuyana "baka tambayeni a bunda mummy tace dani ba sanda za'a kawoni" Na kura mata idanu "yaya zan tambayi sirrin da da uwa farida?" Tayi murmushi "amma ka bayar dani ai sirrikana banga wanda zan boye maka ba" Na karkace kai dana ji abun data fada"to me tace maki" "Cewa tayi ta bani sati guda idan taga baka canza ba ni da ita" "Na canza kamar yaya?" Takara murmushi "kamar yadda mutun kan canja idan ya samu kwanciyar hankali,kuma na kudiri aniyar canja ka din ,zan mayar maka da jikina muhalli na hutawa, zanyi iya yina domin ganin cewa wata damuwa bata samu matsuguni a ranka ba, ta hanyar dandana maka kauna salo salo, salon rana zai kayatar da kai a yayinda na dare zai dameshi ya shanye . Nayi kasake dani"ni dama har akwai wani salon kauna da rana" Tayi dariya "hala baka sanshi ba,to zaka sanshi daga yanzu " Ta mike tsam , daki ta shiga ta bar ni nana cikin tunanin shin me zata yi, bayan yan dakiku da basu fi kaza ba sai ta fito Numfashina ya tsaya cak bayan da naga shirin data yi, hakika in banyi a hankali ba farida so take ta zautani . Ta sunkuyo gare ni gami da kama hannuna tashi mu koma daki ko?" Na zuba mata idanu "Kunyarka din me zanji,idan naji kunyarka cutarka zanyi, ba zaka sami kaunar da kake bukata ba, to amma izan so kake naji kunyar ka fada min" Shiru nayi ni cece bayan ta riga ta fara sangartani tuni na mike na bita dakin domin ganin abunda zatayi da ni ko tantama banayi zan sha riba buhu buhu . ******** . HALACCI . Bansan abunda ya sanya mummy cewa mu hallara agidanta ba sai dai koma menene na san muhimmi ne, musamman danayi la'akarri da cewa da tarewarmu ba afi sati uku ba, muka shirya tsaf sannan muka nufo waje a lokacin da muke rike da hannun juna tafiyace irin ta ma'auratan dake cikin soyayyarsu . Muka kulle gidan sannan muka duru a mota na ja mu a lokacin da farin ciki ke mamaye da zuciyata kana iya gane hakan bisa ga la'akari da yanda muke hira cikin murmushi, hatta kallon da mukeyiwa juna na musamman ne, mai bada hannu ya tsayar damu alokacin da muka iso wani junction, sai na taka burki na juya ga abar kaunata muka cigaba da hira . Bayan dan lokaci na waiwayi gefena,waiwayar da ta sanya wani abu ya tuko min a zuicya, wani mutumne dake kan babur ya saki baki yana kalle min mata, don mayata ko kiftawa baya yi . Na miko hannu waje "haba malam me kenan haka?" Ya gaggauta kawar da kansa ni kuma na shiga fadace-fadace ina ruwan matsiyaci anyi zakara, tsugunne bata kare ba, can na hango wani mai mota shima , haushi ya kamani na sa hannuna na janyo mayafinta ta yanda ya rufe fuskarta, ta aka nayi maganin mayu . Bamu isa gidan ba sai da muka bata mini talatin yayinda da muka isa kuma sai muka ga bakon abu, wata jibgegiyar motar jeep ce , motar da ba mu sani mai ita ba, haka muka shiga gidan cikin rudani, sallama muka fara yi muryoyi da yawa suka amsa sallamarmu . Mutum biyar muka samu a zaune Mummy sai wasu maza guda biyu, a gefe guda kuma wasu matan, to wayannan kuma su wane ne, tambayar danayiwa kaina kenan, bayan dana ga ita kanta farida bata shaidasu ba, muka gaisa da kowa , muka zauna sannan mummy ta dubi farida "kin gane su kuwa Girgizaa kai "tayi ban gane su ba" "To yayyanki ne" A guje ta tafi ga matan suka rungume juna , dukkaninsu suka fashe da kuka , na ci gana da kallon ikon Allah lallai dan uwa rabin jiki an manta da duk abunda ya faru a baya, bayan ya n koke koke da maganganu suka saki juna sannan suka sake sabuwar gaisuwa da mazan . Ta share hawaye "ina baba take" "Baba tana asibiti cutar paralise ce ke damunta " Wannan jawabi ya sanya farida kara fashewa da kuka ni ma kuma sai dana tausaya Mai kama da babban cikinsu. Yaci gaba "kamar yadda kika san cewa akwai mu to yau gamu, nasan kin san sunayenmu amma da wuya ki iya bambancemu, to ni ki kirani kamal, shi kuma faisal waccan kuma fauzah yar uwartta salimah Kuma abunda ke tafe damu neman gafara ne da afuwarku bisa abunda ya afku a baya mun ga abubuwa da zamu iya kira isharori wallahi ni din nan sama da shekara kenan kullum ina mafarki da baba, yakan nuna ni da yatsa yace"Allah na jiran isowata " to hakan ya tashi hankalina, kuma nasan ko me nene ya jawo ga kuma mahaifiyarmu yau shekararta goma da cutar kullum abu kara muni yake kuma na tabbata ba komai bane illa hakkinku" Ya share hawaye "ku duba zumunci ku kuma dubi 'yan uwantaka ta addini ku yafe mana abinda ya faru ku dauka cewa shaidan ne ya rudemu, domin raba kawunan mu" . Mummy ta share hawaye "ku manta da komai Allah ya yafe mana gaba daya, mu dama ba mu dauka da zafi ba" Ya shiga godiya yan uwansa ma suka taya shi bayan da aka natsu sai ya jawo wani akwati ya dubi mummy "To hajiya kudinku dake wajenmu sun tunkari bilyan daya, to amma wallahi babu inda zamu samo su domin duk dukiyar ta lalace, yanzu dai mun taho da dan abinda ya samu in ya so sai a rubuta idan da raboon zamu biya saura zamu rinka kawo wa a hankali, har Allah yasa a warware komai" Ta girgiza kai "sam mu baza mu biku bashi ba , abunda aka samu Allah ya amfana sauran mun yafe" Ta waiwayi farida "koke me kika gani" Gyada kai tayi "haka ne mummy" Babban ya sake fashewa da kuka, da kyar aka samu yayi shiru yasa hannu ya bude akwatin tayi wata yar kara sannan ya dage murfin sai ga su kuru kur, tamkar wasu shashasun takardu, zallar dalar aamerica ce numfashina ya dauke ban taba ganin kudi masu yawa haka ba, da

Chapter 3 of 4