Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TARAR ARADU DAKA Littafi na daya 1 Na Umar Lawan Typing:- Shuraih Usman . DANDANO daga cikin littafin •••••••••••••••••••••••••••••••• Umar ya shiga gararin rayuwa Inda ya rasa kwanciyar hankali Sakamakon soyayya da Yarinya mai suna Farida. Wacce akan tane mutane uku Suka rasa rayukansu, Akokarin neman aurenta.kuma Shima an gargadeshi Amma yace yaji yagani Kuma YATARI ARADU DA KA Saboda fadin kai Koya zata kasance kubiyoni acikin wannan littafi mai suna TARAR ARADU KunasooooTARAR. ARADU Littafina daya 1 Na Umar Lawan Page 1 Typing & posted by Shuraih 99% . Na yayi mo takarduna bayan na cika tumbina da waina.nan da nan nafara angizo babur dina Vespa zabuwa .zuciyata na mai dari darin dadewar da zan yi ina bugu kafin ta tashi. Bayan dana hada waya sakamakon gidan makullin (ignition)da ya dade da lalacewa. Abin mamaki yau bugu shabiyar kawai nayi ta tashi .anan da nan wata kara ta cika wajan kamar an kunna injin markade sabon washi, saudadama idan ina sabis acikin gida in har na tasheta yara kanyi sallama ."Ga markade". Ni kaina duk sanda ta tashi nakan toshe kunnena . Lokacin kwanciyar zafi yan unguwar mu har basa so nayo dare . Darana kuwa matan aure basa son wuce wata wai nakan tayar masu rigimammun 'yayansu daga barci,kuma na kan hansu bin sallar jam'I. Dama gababur babu gudu,kuma nakara kasheshi da kaya . Domin kuwa idan nabudema wajen adana kayayyakinsa , babu komai illa tulin fulogi wanda nikain nasan suna ragemin gudu. Amma inkaduba body ,mai motama sai yayi zaton zan iya wuceshi har yagaza kamoni. Nan da nan na dare sama mukafara kokoyi da giya na dade ina shammatarta kafin tafada . Aifa shigar giyar kedawuya na murdashi sai tyafiya ,kar kaso kaga yanda nake doro ina kwambarewa . Kullum nahau haka nake fankama naketakama kamar sarki akan doki. Idan na raina majalisama ko sallama banayi ahaka naita wuta har makarantar dangiwa commercial secondry school. Inda anan nake koyarwa amatsayin malamin English. Da malam sule mai gadi muka fara gaisawa "har an fito" "Allah yayi" Nabashi amsa . Nakafe babur dina a inda aka tanada domin yin fakin. @mr:-Shuraih 99% Na nufi ofishin principle. Ko ba'a fada maka sunansa ba zaka iya ganewa da kanka. Domin kuwa yafi dacewa da malam Abba .akwai kwazon aiki akwai kuma mugun son kudi na gaisheshi muka kuma taba yar hira wadda zolaya acikinta tafi yawa . Da fitowata na nufi wani abokin aikina kabir sabi'u. Muka caccake na dubeshi "naga sai kyalli kake kodai kanasan ka angoncene ban saniba?" Yayi dariya" kaifa tsiyarka kenan baka kyale mutum haka" Muka zauna na shiga dube dube wani lokacin har nakan mike tsaye "wai kai me kake dubawane" Na dawo na zauna bayan na gaza hango abin danake nema "don Allah bakaga shigowar farida ba ?" Na tambayeshi . Ya tintsire da dariya . "Kai mallam tunda farida tafara aiki anan naga sai wani kankajeri Kake kana kara kwalliya ,kodai da watane akasa?"Nace babu komai , don mutum ya tambayi abokin aikinsasai yazama laifi" Ya girgiza kai "To me isa baka tambayar su hafiz? Kosu ba abokan aikin kabane"? Na gyara takarduna sa'arda nake cewa "Kaga mungama hirar ne ban tambayekasuba" "To shikenan tunda boye-boye kake ,amma indai kuka shirya kanku kayi sa'ar mata UMAR" Bancemasa komaiba ,duk dacewa maganar tasa ta kayatar dani . Bada jimawa ba na hangota tana shigowa tana rungume da jakar takardunta . Mace ce mai matukar tsari da kyau tana da yawan kuya da kulawa da Addini,kai ni tunda nakke ban taba ganin kamartaba . Na mike tsaye kabir yabini da kallo "To mallam ka hangota zaka gujeni ko?" Na harareshi "Ai kaine kake yimin wulakanci,ba gara na tafi inda inda za'a karramani ba " ban tsaya wata wata ba nanufi inda take da ganina ta fara murmushi , Murmushin da kullum in tayimin sai nadan rikice . Na dubeta cikin sarkewar murya "Ina kwana hajiya farida " "Lafiya lau umar" Tra amsa cikin daddar muryarta To be conti...... Via:- mr:- Shuraih 99% TARAR ARADU Littafi na daya 1 Na Umar Lawan Page 2 Typing and posted by Shuraih 99% . . "Yau narigaki zuwa " Nace da ita tadan kwatar da kanta "Nadan ragewa mummy aikine saboda batajin dadi" Ashsha Allah ya sauwake" Nadan gyara tsayuwata "don Allah farida idan an tashi tara ina son magana dake' Ta kalleni da fararen idanunta sa'ar da take cewa "Lafya dai ko umar" Na kauda kaina domin bana jurewa kuramata ido saboda wani kwarjini da take dashi. "Lafya kalau akan dai maganar nan ne" Ta sun kuyuyar da kanta kas daga bisani ta dago "To Allah ya kaimu" Muka juya muka tafi. @mr:-Shuraih 99% Tunda farida tafara aiki amakarantarnan Allah yasanya min tsabar kaunarta , nayi kokari in yakice amma ina. Abin yaki yiwuwa . Wannan yasa nafara yi mata isharori amma tayi biris kmar bta gane ba , ga misali nasha sai mata sabulai da mayuka . Amma sai dai tayi godiya ta kuma bini da Addu'ar Allah yabar mutunci. Wannan yasa nafito fili na shai da mata amma sai tace na saurara zata tun tubeni . Kuma shiru kakeji haryanzu taki tuntubata . Dana tina mata saita kama noke-noke shine yau nayi kunar bakin wake domin nasan wacce akeciki. Ana tashi tara na nemi karkashin wata bishiya na hakimce can jimawa sai ga farida tana isowa "Mai yafaru ne umar?" Ta tambayeni bayan data zauna ,nakara jingina sosai ajikin kujerar danake kai. Sannan na dubeta na fara dacewa "Wai dan Allah farida mai yasa har yanzu kika ki bani cikakkiyar amsa ? Nidai idan kina ganin babu dama gwanda ki gayamun insan yanda nayi.mai makon ki kyaleni kullum ina azabtuwa da tsabar sonki, kuma ina hada ki da Allah ki shaudamin hakikanin gaskiya " Na dade ina sauraronta taki tace uffan .sai kawai ta tokare habarta da hannu, Babu tsammani kuma sai naga tafara kwalla . Hakan ya rikitani ,cikin rudewa na fara cewa "Maganata rai ya bata miki" Don Allah kiyi hhakuri" Batace komai ba taci gba da kukanta kawai "Don Allah farida kiyi hakuri bazan sake tambayarkiba" Ta girgiza kai lokacin da take share hawaye "umar ba tambayr kabane ta bata min rai illa iyala wani al'amari dabam , zan amsamaka tambayarka umar,amma saidai in antashi kasameni agida " Nadubeta "Inane gidanku Tadanyi jim sannan tacigaba 'goron dutse bayan gidan isiyaka rabi'u gida mai kallon kudu, na biyu ahannun dama" *** *** ** ** ** *** Dayin sallar la'asar na shiga wankka , nadade ina shekawa domin kuwa awa guda na karar cur, nakarar da ruwa ya kai jarka uku, ba'a batun sabulu wanda nakarar da fakiti guda badon komaiba sai don na kara haske. Aranan sabon man shafawa nasiyo saboda ji nayi nawa nada yana wari, alhalin kuma dukranda nashafashi har tambata ake wannan wane maine?. Saoda tsabar kamshi, na bude kwaba nayi ta zaro kaya ina ajiyewa gefe guda ,har nazo kan na cin yewar ,dukranda na sanyasu ka tabbatar zani muhimmiyar ungwa ko kayataccen fati. Nan da nan nafara jikasu da tirarena. Na makala farin gilkashi. Ban nufi ko'inaba sai gindin dressin mirror don duba haduwar tawa, Hakika nafito kamar yadda nayi tsammani, nakalli takalmana cali-cali wayanda tuni na baiwa shushaina ya wankeminsu harda karin kudi nayimasa domin yayi mani wanki na musamman nan danan na zura kafata nafara takawa cikin takama , Kai kace wani dokin dan sarki, @mr Shuraih 99% Na kulle shagon nanufi cikin gida anan na sami matar yayana tana kokarin dora girki. "Kai umar ina zakne haka kaci kwalliya ?" Nagoge fuskata da hankici "Wallahi zani unguwne ,yaya kika ganni,nafito?" Ta kalleni daga sama har kasa "Wallahi ka fito" Kaga yanda kake kyalli kamar sabon kwabo" Wata dariya ta kwacemin . "Toh madalla dama haka nakesopn ji" "Zanyi miki karin kudin cefane tunda kin yaba " Tayi shewa . "To mai gida, godiya nake,ince dai ba kishiya zakayiminba ko?" Na duba agogona "Ke dai wallahi kin cika tsoron kishiya kimin Addu'a Allah yabada sa'a" Ta kwantar da kai "To Allah ya taimaka " "Amin" Nafito nabarta . Raina yabaci yayinda na iso soro,baodn komaiba sai don bata min lokacin da mashin zaiyi. Na turashi har muka zo waje. Nakafeshi nafara bugawa nayi tayi amma ina ko amsawa bayayi kamar wanda na cika tankinsa da ruwa . Yara kuwa sukazo suka yanyameni,kullum haka sukemin in har nazo fita da yamma ,sukanyi ta dariya sa'arda nake bugawa. Wani lokaci nakanji kaman nasa duka amma sai na daure na rabu dasu. Har ina shirin hakura sai naji yafara amsawa. Wannan yasa nacigaba banfi bugu ashirin ba kuwa yatashi. Yara suka kaure da shewa ye !yatashi yatashi! Nan fa suka da baya yayinda suka ga dare,badon komai ba saidon sun san in yayi wata zabura zai iya bi takan yaro. Raina yakara baci dana tuna yadda zanyi fama da giya ,amma cikin ikon Allah murdawata sau uku sai fada, na murza totur sai tafiya ahaka na ringa tuki cikin hkima da dabara.wai ance inkana da abin hawa dolene kazama makaryaci saboda takurawar yan aro mai zuwa yau dabam mai zuwa gobe dabam. To nidai nakaryata domin kuwa babur dina saudaya wani abokin aikina yataba aronsa da uzurin gaggawa ya kamashi,daga ranar shima bai kara araba. CABDI WANNAN BABUR KO WAHALA DA RAI Zamu cigaba anjima By @mr:- Shuraih 99%TARAR ARADU Littafina daya (1) Written:- shuraih 99% Page 3 Adai dai junnction din bariki yellow fifi ya tsaida mu. Raina yabaci domin kuwa shine abin dana tsana sakamakon rashin wadataccen burki,nayi iya yina domin ya tsaya amma ina ,har nakaiwa yellow fifan sura .yayi tsalle gefe guda . Da kyar babur din ya tsaya bayan daya tungudi ginin express, na juyo domin bawa yallaban hakuri, sai naga ashe bai dauka da zafiba ,daomin ma dan unguwar ne. Ba'ajima ba akabamu hannu nafara kokarin sa giya ina takawa da kafa da kyar na samu ta shiga, Wata rana ma kin shiga takeyi sai nagaji da shan zagi da horn daga masu ababen hawa . Kai har akwai kwandastan daya taba rankwashina wai tare musu hanya . Haka naci gaba da taifya rakakai raka kai kamar wanda yake tafiya akan jaki, sauda yawa mai keke yakan wuceni tinma ba idan na hadu da sabon jini ba. Aje ba'ajeba sai gani a goron dutse na dudduba hakika farida tayi mantuwa wajen kwatantamin gidansu. Domin kuwa gidan daya kamata yazama nasun sam banasu bane ba. Saboda yadda naga tsarin gidan ko yar wanke wankensu tafi karfun tayi koyarwa amakaranta. Sai nafara tunanin yadda ya amata nayi daga karshe na yanke shawarar in sami yaro na tambayeshi. Haka kuwa akayi , Nayafito wani yaro "Dan Allah zo mana kanina" "Gani" Yafada okacin daya iso gareni "Don Allah kasan wata farida malamar makaranta" Ya gyada kai lokacin daya ke nuna min kerarren gidan @mr:-shuraih 99% "Ga gidan sunan" Nacika da mamaki badon ita tace nazo ba da juyawa zanyi domin kuwa nakaraya lallai farida tafi karfina . Wata kila tayimin hakanne domin innaga gidansu sai in hankalta. Har zan juya sai natuna yakamata tasan nazo don kartakamni da laifin saba Alkawari. Na dubi yaron "Don Allah jeka ka kirawomin ita" Ya zura min ido kamar maisan yafada min wani abu, da na dauka bazashi ba Sai naga ya kada kai yace "Amma dai" Sai yatafi nabi yaron da kallo shin me hakan yake nufine? Kokuwa shima yagane cika kainane? Bai jima ba sai gashi yafito tana biye dashi tana biye dashi abaya fuskarta cike da murmushi. Ta tsaya abakin kofa , naga ashe farida kyawunta ya wuce yadda nake gani amakaranta, yaron yazo wucewa kusa dani "Mallam Allah yaji kanka" Yafada yakuma zura aguje bansa abinda yake nufiba . Na kafe babur dina na kuma nufi wajenta "Sannu da zuwa umar" Tace dani idanunta akaina na amsa da "Yauwa" "Bismillah" Tafada sa'arda take juyawa na bita abaya ta cikin soron wanda aka shimfideshi da tayil mai kayatarwa , Araina ina ta sake saken abin daysa farida koyarwa. Shin sha'awar koyarwar take ko kuma me ?. Nidai nasan ba'ace dan tasami kudiba. Banyi aune ba sai na ganni atsakiyar gidan aifa sai na ne mi kidimewa saboda tsabon tsari da kayatarwa. Ta nufi wani daki dani tasa hannu ta tura kyauren na gilashi, Ta tura kai ciki sa'arda ta kecemin shigo, Nasa kafata nayi mamaki danaji sanyi ya dokoni alhali lokacin zafine, sai na tuna A.C babu shakka itace aka kunna , Na ratsa ta wani kilishi daya mamaye ilahirin dakin da a gidan nake to da babu ruwana da katifa kansa kawai zan rinka zuwa ina yin baccina. Na dubi wasu maka makan kujerun dasuka mamaye dakin tai min nuni da daya "Zauna umar" Na juya nazauna sai naji nayi kasa zan nutse ,nan nafra zargin farida da laifin zaunar dani a bulalliyar kujera -kome yasa tayi min haka? Kawai sai naji nadakata nan nagane ahe ba bulewa tayiba duk laushin soso ne. Na jinjina kai lallai masu mura suke da tari. Ta nufi kofa loakcin da takecewa "Ina zuwa" Bata dadeba ta dawo rike da farantin silverm @mr:-shuraih 99% Ta ajiyeshi akan wani karamin table sai naga kofa tabude wata matace ta leko. Ita da farida tamkar an tsaga kara. Sai nagane mahaifiyartane na sauka har kasa na gaidata tayimin kyakkywan maraba, sannan tafita na dubi farida "Mai yasa baki kirani naje nagaishta acan ba sai ki wahalar da'ita kisa tazo nan" Ta waiwayo gareni cike da murmushi "Lallai bakasan momi ba umar, wani irin haline da'ita da kayi wahala dominta gwara ita ta wahalar da kanta yanzuma babu yadda banyiba akan tabari zamuzo ku gaisa tace a'a zan wahalar dakai" Nayi murumushi gami da fadin "Allah sarki" Na gane mahaifyar farida irin mutanenane masu saukin kai,ta zauna akan kujerar dake kusa da tawa bayan ta gama bude tan garayen, Dan kalin turawane wanda akahadashi da kwai aka soya sai kuma wani hadadden kosan doya. Ta tsiya ya ruwan tatacciyar abarba akofuna sannan ta dubeni sa'arda ta ajiyemini cokali mai yatsu. "Bismillah umar" Muka fara gabatarwa harzuwa lokacin danaga ya kamata na dakata sannan na kora ruwar abarbar nayiwa Allah godiya. Ta kawar da kayan gefe sannan ta fuskanceni "To umar naga kana nema kadamu akan rashin baka amsar tambayarka ,to dayardar Allah ayanzunnan zan warwaremaka zare da abawa" Tacigaba "Ni da ka ganni yar wani hamashakin mai ar zikice mai suna. Alh Hashim.jigon dan kasuwane maiyin harkokinsa akasashen turai,kuma nan dakake gani dayane daga jerin gidajensa guda goma,kuma shine mafi kankanta dakuma muni" Nakame baki jin abinda take fada "Kwarai kuwa" Ta tabbatar mini "Yana da gidaje a Kaduna ,legas,Abuja kai harma da birnin london" Zan cigaba @mr:-shuraih 99% TARAR ARADU Littafina daya (1) Written:- shuraih 99% Page 4 Na Jin jina kai taci gaba "To kuma matarsa biyu hajiya halima uwargidan da kuma hajiya safiyya wato mahaifiyata, kuma ita uwargidan yayanta hudu uku maza daya mace. Mazan kuma sune manya kuma abokanan harkar mahifinmu wato masu taimaksa,ni kuma ni kadiace awajen mahaifiyata. Ina da shekara biyu Allah ya karbi abinsa kuma yayyen namu sune suka san kudaden mahaifinmu na banki hakanan kadarorinsa. Wannan yabasu damar yin rubda ciki akan kudin,hakazalika kadarorin, gidajenma cewa sukayi uku kawai yabari duk sauran ya sayar dasu yabiya bashin kamfaninnuwa. Sai suka bamu wannan gida dakuma naira miliyan daya" Nakar kada harshe game da jijjiga kai Taci gaba 'yanuwan mahaifiyata sunta bata shawara akan takai kara amma tace sam wanda yatara dinma yau ina yake? Saboda haka ta hakura Arzikin dake tsakanin suma na 'ya ai ya isa tayi ta renona ta sanyani a nursery kai har zuwa lokacin dana sami shiga jami'a nai ta fama da takardu daga samari. An kuma sha tareni fuska da fuska. To amma ban kula ba domin alokacin burina nayi digri na kuma sami damar tallafawa kaina da mahaifiyata. Kamar kullum na tsaya abakin titi don samun mota akokarina na dawowa daga makaranata. Wata honda hala tayi fakin agabana, ahankali bakin gilashin na kofar direba ta fara janyewa ahankali, yana gama janyewa sai naga ashe wani matashine jibgege bakikkirin mai jajayen idanu. Koda acikin dodanni na tabbata baza akirashi mai kyawuba Ya yaye fuskarsa yazuwa abinda yake murmushine, nikuma aganina abinda yayi yafi kama da hammar jaki "Yan mata shigo na rage miki hanya mana" Yafada awta muryarsa mai kama da kukan balamar tunkiya, na kau dakai daga kallonsa domin tsoratani yake Akuma lokaci guda nakecew @mr:- Shuraih 99% "Jeka abinka na gode" Sai ya leko da kansa waje wanda ke tsugune akan wuyansa mai guru guru Kamar gurun diro.yaci gaba da dubana da idanunsa wanda suke zurma zurma kamar ramin tanda ,wayanda suka sa war ga jejen hancinsa atsakiya. Yaci gaba da magana da bakinsa irin na kada . "Don Allah 'yan mata kishigo mana" Nafara matsawa "Nagode nace dakai" Ya biyoni yaci gaba da nacinsa. Ana hakane mota tazo natare na shiga. Mummunar mutumin yabini da kallo.har muka bace masa bai motsaba , akayi tafiya har akazo inda zan sauka nabiya kudi dana fioto. Nakama hanya zuwa gida bayan na tako kofat gidanmu sai naji horn din mota. Ina waiwayawa sai naga katon mutuminnanne "Zan dawo da daddare" Yafada cikin daga murya kamar kwamandan sojan daya ke bada umarni. Bancemasa komai ba nashige gida, Banma sake yin tinaninshi ba da daddare kuwa sai gashi an aiko. "Wai farida tazo inji wanda sukayi alkawari" Na dade ina kokarin tuno waye wannan bantuna ba sai daga baya mutuminnan yafado min a rai. Babu shakka shine nayi tsaki na dubi dan aiken "Kace mata waidon Allah yayi hakurin anyimata miji" Yayi ta maido dan aiken nace masa kar ya sake shigowa. Nama tsahi nasa sakata akofar gidanmu ganin haka sai yatafi yayi ta zuwa gidanmu jefi jefi na ki fita har watrana mahaifiyata tace min ya wajaba na fita banda zabi dole hakan akayi. Yayi ta suratansa bance masa komaiba Sai da yagama hayaniyarsa. Wadda take bayani akancewa wai yana kaunata ni kuwwa banga abin da zaisa na'auri mutumin wanda yafi kama da naman daji koda kuwa maza sun kare. Wannan yasanya ni cewa dashi "A gaskiya karatu nake kuma bana zaton zanyi aure sai sama da shekaru goma" "Indon wannanne zanyi jiranki" Raina yabaci yanda mutumin ke kokarin likemin tamkar kaska "Kai kaga kaje kawai kanemi wata " "Kece kikayi min" Yaci gaba dafada nayi tsaki sannan nayi tahowata gida. Washe gari yasake dawowa naki fita. Wata washe garin sai yatareni an taso daga makaranta yafara yimin shirme. Nikuma kiyayyar danakeyimasa takai intaha. Wannan yasa na kalleshi afusace "Mallam bari infada ma gaskiyama ni dai bana kaunarka bakuma zan kaunaceka ba , zai fima sauki kaje kanemi daidai da kai" Ya fashe dawata irin dariya wadda take bada amo tamkar ana tuttule ruwa daga jarka. Yadade yanayi har ya tsoratani ,tamkar kuma dauke wutan nepa sai yayi shiru gaba daya. Nan danan fuskarsa takara muni sakamakon bata rai dayayi. "Yarinya kinyi shirme kintafka babban kuskuren dayakamata aganar dake" Ya nunani da dan yatsansa mai kama da busasshen itace, Yayi kasa kasa da murya. "Babu duka babu zagi saidai zaki mutu babu miji" Raina ta baci na watsa masa kasa "Aniyarka tabika saidai kai kamutu babu mata " Yayimin wani kallo sannan yahau motarsa yatafi. Da ganan muka rabu da mummunan mutumin. Baisake zuwa gidanmu bako kuma ya tareni. Ni kuwa gani da farinjini. Aka rinka zuwa wajena naki fita don saboda ina ganin hanani karatu za'ayi. Don babu abinda irin da daddare narinka nazari , ahankali na. @mr:-shuraih 99% Tobe conti....... Tobe cont...... @mr:- Shuraih 99%TARAR ARADU Littafina daya (1) Written:- shuraih 99% Page 5 Ni kuwa gani da farinjini. Aka rinka zuwa wajena naki fita don saboda ina ganin hanani karatu za'ayi. Don babu abinda irin da daddare narinka nazari , ahankali na kammala digirina akan mathematics . Nakuma yi bautar kasa, sai maganar aure . Nan muka fara soyayya da wani matashi habib , dan kasuwar kwari ina mutuwar sonsa ana kokarin samana rana . Watarana yazo tsallakawa titi dominisa wajen motarsa wani mai mota yazo ya bankeshi.ko shurawa baiyiba . Mai motar kuma yagudu" Sai naga hawaye nazuba daga idonta . Tacigaba "Naci kuka har na gode Allah bayan komai yalafa sai muka kulla da wani ma'aikacin savannah bank mai suna isma'il soyayyar dayake nuna min hartamantar dani na habib. Asheshima ba rabonane ba. Babbar motace tabi takan motarsa starlet. Da kyar akaringa banbaro namarsa gashi kuma cikin darene abin ya afku. Ba'asan inda mai motar yayiba. Hankalina yayi mugun tashi yanda kasan nayi hauka sabida yanda nakeson isma'I'll banso habib ba, nakasance cikin damuwa yanda samarina ke mutuwa haka , sai natina zancen mutuminnan shkekaru biyu dasu ka gabata. Babu shakka shirinsane anan na shidawa mahaifiyata. Tace saidai Addu'a tunda ba'asan inda yake ba .kuma ni kaina tundaga ranar bansake jin duriyarasa ba. Aifa wannan abubuwa dasuka faru suka sanya akafara yimin son rakumin yara. Sai dai mutum yabar kaunar dayakeyimin azuciyarsa amma babu damar ya baiyana. Na nesa kuwa ko mutum yafara zuwa sai naga ya janye narasa dalili. San dade ana haka sai wani dan'uwana yace yaji yagani babu wani mamaci sai wanda kwanakinsa suka kare. Saboda haka yace mahaukaci yahau kura Sabida haka muka cigaba da soyayya abin gwanin birgewa har ya mantar dani duk nabaya aka samana rana. Sai da abin yarage sati daya kawai akka tsinci gawarsa a tsakiyar titi. Aifa daganan sai zamto mujiya ma tafini farinjini. Babu wani saurayi da yake fuskan tata" Saita fashe da kuka har nayi zaton bazatayi shiruba. Nima saida kwalla tazubo min don tausayawa taci gaba "Wannan shine dalilin dayasa kaga naki amasa maka, domin kuwa duk wanda ya kulla alakar soyayya dani sunansa matacce, nikuma banso wani abu ya sameka. Na dauki kaddara akan cewa Allah bai yi zanyi aure ba. Domin kuwa har sai na sami wani ya dan kaunace ni sannan zan ji sarai. Wanda ahalin yanzu abune mara yiwuwa" Nadaga mata hannu "Dakata farida ni ina kaunarki" Ta girgiza kai "Bazai yiwuba umar banaso ka mutu sabida kaunar danakeyi maka" Na dubeta "Don Allah farida da gaskene kina kaunata?" Ta gyada kai "Wallahi umar inayi maka kaunar da bantabayi ma wani kamar taba" Na mike tsaye "To in hakane farida na daura damarar neman aurenki koda zan mutu" Na sun kuyo kusa da fuskarta. "Wallahi farida babu wata wuya dazatasa na dakata" Ta girgiza kai kuma alokacin data kirawo sunana ahankali "Umar ,zaifi kyau kaje kasami. Wata domin samawa kanka kwanciyar hankali" Na bata fuska "To ba kya kunata kenan" Ta girgiza kai "Bahaka bane" "To kice kina kaunata da aure" Tayi shiru kawai tana dubana "To shikenan farida barinatafi tunda bakya klaunata" Najuya cikin hanzari ,ta tare kofar na kalleta babu alamar fara'a a fuskata "Way or reply" Nace da ita , murmushine yafara sauka akan lebenta ,sannan tafara fadin wasu kalmomimasu tsada "Ina kaunarka da aure umar" Sai wani farinciki ya mamayeni, kaunarta ya kara shiga raina murmushi ya kubuce min. Akuma lokaci guda dana sula le akan kujera. Ban kula da hadarin dana ke akai ba. "Za kiga abinda ake kira tsantsar kauna farida" Shine abinda bakina yafara fada. ******* ********** ******** Tun daga ranar danaje gidan su farida sai ya zamo a kowane lokaci in ina tafiya akan babur nakantafine cikin taka tsantsan. Kai kace mai keken daya doro ciyawa gaba da baya kuma ya debi garke tumaki,badon komaiba kuwa saidon samun garkuwa daga mutumin da farida tace min shine sanadiyyar mutuwar masi neman arenta har mutum uku Na kirga adadin makwanni cikin tafi daya. Amma har yanzu banga abinda ya sameni ba nida farida. Munyi matukar shiga ran juna. Soyayya agida sannan wani salon dabn a makaranta. Mahaifiyarta tayi matukar faribciki da soyayyarmu, baka da baka ta fadamin Duk samarin farinda dasuka shede bataga wabda suka dace da juna kamar niba. Allah yabar ku tare har abada naji dadin maganar. Yau ranace ta lahadi da kuma muka shirya zuwa yawon bude ido dabi da masoyiyata. Sabbabin jacket nasiyo musamman don tafiyar ta kara armashi Nahadu iya haduwa. Ga wanda bai sanniba zai dauka dan wani ne daga yayan jiga jigan garinnan nan kuwa ba haka lamarin yakeba. Na iso gidan su farida da misalin karfe hudu, ahalin yanzu nazama dan gidan salllama kawai nayinashiga, Na tarar da mahaifiyarta tana karanta wat mujallar Africa banyi mamaki ba Sakamakon cewa na dade da sanin cewa tan jin har shen nasara sakamakon zama a kasar ingla na tsuguna na gaisheta ta amasa da fara'a bisa dukkanin alamu shigar tawa ta burgeta. Ta nuna min dakin farida...... @mr shuraih 99% Tobe con....TARAR ARADU Littafina daya (1) Written:- shuraih 99% Page 6 Ta nuna min dakin farida. "Tana nan inaga shiryawa takeyi" Ba'ajimaba ta leko "Umar shigo mana" Na karasa ,bayau na fara shiga dakinba yanada tasari matukar tsari. Akalla yalunka nawa ko uku ko hudu. Na cusa kaina

Chapter 1 of 3