Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 10
temako,wani falo muka isa babba mai cike da Kayan alatu wallahi kamar ba gidan mutane ba Zama tayi a wani kujeran one sitter tare da dannna wani kararrawa,can sai ga masu aiki sun Kai goma suka taho ajere,kirari suka fara mata tare da zubewa suna kwasan gaisuwa,Murmushi tayi ta dubi daya daga cikinsu tace"Jakadiya!wacce akakira da jakadiyar na kalla babban macece sanna tafi sauran shekaru kayanta daban ne Kuma duk cikansu suna jinsu neat. Murmushi tayi jakadiyar tare da karisowa tana fadin"gaisuwa nake uwar dakina uwar gida sarautar mata gani gareki fulani. Murmushi tsohuwan nan takuma tace"Uhm kuntashi hala baku ganni ba? Eah wallahi fulani tunda banganki ba nace yanzu haka kinje zaga gari ne kamar yanda Kika Saba. Murmushi tayi tace"Aikam nan take Basu labarina tanuna ni sannar ta sanar masu da duk abinda yafaru,duk cikansu kallo na suke Cike da mamaki da yanda nayi fada da Dan daba,Jakadiya tace"Amma fulani meyasa baki Kira waya ba anzo ankoya Masa hankali? Fulani Tace kada kidamu ko yanzu wannan yarinyar ai tayi gaba Koda zaiyi zai tuna da abinda yafaru,Jakadiya tace haka ne. Duba na fulani tayi tace 'yammata yaya sunanki? Bata amsa nayi da Maryam Amma anfi kirana da Shakeerah,wow Masha Allah tafada,Cike da mamaki na dago ina kallonta,ba komai yabani mamaki ba illa wow dinda tace nikam da bansan meaning dinshi ba. Tambayata tayi nabata labarina,nan kuwa na zayya ne mata komai,abubuwa da dama dariya take nan tadubi Jakadiya tace taje tacema Sarkin gida a shirye motoci uku xataje unguwa. Ba'a dauki lokaci ba muka shirya nidai Ina rungume da bucket din pure water da farantin bread. Shiga motocin mukayi Wanda najini tamkar nashiga cikin jirgin sama tsaban dadin danaji,a haka nadinga musu kwantace har muka Kai kofar gidan mu,ya wanci 'yan layinmu duk sunfito ganin motoci da manya manya a hankali suka tsaya aka budema fulani murfin motan,nima aka budemun. Tunda akaga amfito Dani daga cikin motar 'yan unguwar mu sukafara gulma kala-kala. Fulani ta dubeni tana tambayata gidan mu,nuna mata gidan nayi,jakadiyar ta da kuyangi uku muka shiga sauran kunyangin da dogarai suka tsaya a waje. Tafe suke da carpet dinsu da Sauri Ammi tatashi ganin antaso keyata gashi daga gani masu kudi ne. Murmushi ne a fuskan fulani,sannu da zuwa Ammi tafara mata sannan tashiga dasu daki don wajen babu wajen fakewa Rana. Dakinmu ta kaita,Wanda yake shimfide da wani tsohon dadduma sai dai tsafta yasa yanajinshi fesss. Carpet Jakadiya tayi kokarin shimfidawa sai fulani ta hanata Zama tayi akasa suka fara gaisawa da Ammi cike da fargaba. Fulani ta dubeta tace"kece mahaifiyar wannan yarinyar Koh?Ammi cike da fargaba Ammi tace"Eah nice! Da fatan dai bawani lefi tayi ba? Girgiza Kai Ammi tayi Nan tasanar da ita duk abinda yafaru sannan tace idan Babu damuwa tana son ganin Abba. Nan Ammi tafita tasamu Dan makota yaje kiransa a wajen bread. Basu dau wani time ba suka shigo shima da kaganshi kasan Cike da mamaki yake a tsakar gida Ammi ta tareshi tace Abban su yau Shakeerah ta nemo Mana magana. Shiru Abba yayi tare da sallama ya Shiga,su Jakadiya fulani ta kalla alamun su bamu waje,fita sukayi tsakar gida,nan suka gaisa cikin mutumci da Abba. Tambayar shi tayi sana'arshi yace mata bread ne,tace to yau yarinyar ku ta temakeni da alamu daga gidan tarbiya tafito tunda har tasan darajar tsoho,ganin haka yasa na biyota don ganin iyayen ta. A tare suka sauke nannauyan ajiyar zuciya. Fulani ta cigaba da cewa idan Babu damuwa,zanso in temaka muku da muhalli sannan Kai nabaka jari mai karfi. Jin kalaman fulani mukayi kamar a mafarki,cikin rawar baki Abba yace Ni...n...I...diin..? Daga Masa kai fulani tayi ai a take anan suka fara godiya saboda tsananin murna. Nan takira ma'ajinta Mai kula da harkan komai tace masa tanaso a dubo mata gida mai kyau Mai 3 bedrooms,Kuma yazama dakwai komai da komai da ake bukata na muhalli. Amsa mata yayi da toh,Aiko cikin awa biyu yakirata yace ansamu,tambayar shi tayi a Ina?yace a kwangila. A lokacin Ammi tagama alqlen gwangwani rai-rai da dakaken yaji tafarnuwa,nan akazuba ma fulani da da kuyanginta da fadawa gaba daya,mukuma ko oho,tsabar yunwa tasa mun manta da yunwa,sosai sukaji dadin alalen. Shakeerah ta dubi su Fauzi tace"In takaice muku fulani itace dalilin arzikinmu. Munje munga sabon gidanmu,gaskiya yayi kyau sosai nida Aunty Saudah a daki guda,daki daya na Ammi dake kallon namu sai daya na Abba da yake da kofa ta waje,duka dakuna biyu Italian bed ne,Daya Kuma Royal shine na dakin Abba,dakuna ne manya² Wanda da safayan 1-1 sitter sai na Abba ne da 1-2 sitter da bangaren dining Falon Kuma kujeru ne hadaddu golden saikace glass Sunyi kyau sosai. Jali tabawa Abba na miliyan Daya sannan ta hadAshi da direban ta suka fara sana'ar sai da motoci. Nan kuwa 'yan uwan Abba suka sake tsanar sa suna yawon cewa yankan Kai yafara,watarana muna zaune da Ammi shi Abba bayanan sun fita da direban fulani sunje kano dauko wata mota. Wani yaro ne yayi sallama ya shigo,amsawa nayi na fita tambayata yayi Wai ance Nan ne gidan wai malam muhammadu? Na'amsa da Eah nan ne wake nemanshi? yaron yacemin wasu maza ne su biyu a waje,cema yaron nayi muje nagansu tare muka fita na bude gate din gidan,Cike da mamaki nake dubansu baba Ayuba ne da baba sani,duk yayyen baban mu ne. Ganina yasasu sakin murmushi gaba dayansu,Nima murmushin naayar musu Ina cewa lahh kune?ku shigo,da to suka amsa ko wanne yana kokarin fara shigowa ganin zasu bangaje ni yasani matsawa suka Shiga,gaba daya bin gidan suke da kallo,wani kolulun bakin ciki baba Ayuba ya hadiye har muka shiga falon,daburcewa sukayi ganin kujerun,Cike da fara'a Ammi ta tarbesu Zama sukayi akan kujerun duk da sunsa ba gani a gidan chairmomin local government,gwanda ma baba sani idan yaso kirki yanayi Zama sukayi,Nikuma nashiga kitchen da kyar na iya bude firij saboda kauyan cina yayi yawa lemu na dauko musu da ruwa na Basu. Nan baba Ayuba ke tambayar Ammi Abba Tace Aiko bayanan,sun tafi kano,wani takaicine ya lullubesu baba sani kuwa har Yana kwarewa yace kano Kuma? Baba Ayuba yace oh rayuwa yanzu muhammadu ne da wannan gidan?harda zuwa kano? Idan natuna sanda yake kwasan masai da bola abin mamaki yake bani. Magana suka gasama Ammi itama Kuma tagani,Murmushi nayi nace wallahi kuwa baba gashi yanzu a dalilin katsalan dan dina muka shiga daukar nan,yaran da ake tsine musu idan ba iyayensu ke tsine musu ba ai abin sai kaga Yana tafiya yanda akeso,yau da hjy 'yar mai goro nanan nasan da zatayi alfahari(wato mahaifiyar Abba) harara baba Ayuba yasakin min yace Mai Hali dai Sam baya canza Hali to yanzu dake nayi magana?Nima hararar na wurga mai nace maganar mahaifina fa kakeyi shiyasa nasa baki. Kwafa baba sani yayi yace ai yanzu Dole muhammadu yayi aure tunda arziki yasamu kaga ni saina samo Mai bazawara. Daka tsalle nayi kamar nice za'ama kishiya nace wallahi bazai yuwuba Kuma Abba bazai dauki shawarar na ba,galala suka saki mouth suna kallo na,Ammi tace Shakeerah tashi kiwuce ciki,da toh na amsa mata na mike Suma mikewar sukayi daganan suka fara Dora ashar,inaso in rama saboda jikina har tsuma yake sai dai Ammi ta hanani. _I need ur comment and sharhi_ Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami🖋️Yafi takobi 🗡️ 💕💕 ❤️ [7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨ ( Daukar Fansa ) Story& writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL ______✍🏽______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* 🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *_T.W.A_* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciyar⬇️ _ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_ *DA* _ _MIJIN ZAHRA_ *Littafin diamond ladies (Daukar fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari biyu#200 katin waya ta wannan number 08060719719,sannan a nemeni ta wannan number 08060719719 sai nayi adding din mutum a group a group din diamond ladies (Daukar fansa),Wanda suka biya kadai zan zira a ciki......kushiga daga ciki don Jin labari Mai darasi,nishadi,tausayi,fadakarwa,ilimantarwa da jarumta.Nagode.* Bismillahi-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah Mai rahama mai jin kai* Page:7️⃣&8️⃣🖊️ __________Bayan sunje lectures Sai wajen karfe shida suka dawo,sai da suka wuje restaurant sukaci abinci sannan sannan sukayo take away din Chip's sukayo gida. Sallah suka gabatar Cike da gajiya suke,sannan bayan sallah isha'i khadee ta cigaba da Basu labarin a baya. "Bayan rasuwar Aunty sakina gaba daya 'yan gidanmu sun gama tsorata da al'amarin,haka Kuma 'yan Unguwa har takai ba'ason hulda dasu Ummina. Aunty Nana kuwa jikinta yariga ya gama sanyi tasan cewa yanzu itace next. A kwana a tashi Babu wuya har shekaru suka shude da watanni babu Wanda aka sake kashewa a gidanmu,kwatsam inada 13years lokacin Ina j s s 2 aka wayi gari an tsinci gawar ya Anas Wanda yakebin Aunty sakina innalillahi wa Inna ilaihirrajiun a lokacin hauka ne kawai hajy saddiqa batayi ba,ganin haka yasa Ummina ta shirya wata ranar laraba Babu kowa a gidanmu domin Daddy da hjy sameera wajen aikinsu daya,itakuwa hajy saddiqa tatafi gidansu sha'ani. Shiryawa Ummina tayi ta hada Kayan Aunty Nana gaba daya tasa driver ya daukemu ya kaimu tasha, daganan motar maidugri muka hau wajen yayar Ummina da bata taba haihuwa. Already tasan da zuwan mu,don haka munsamu tarba mai kyau,Bayan munvi abinci munhuta Ummina tayima yayarta bayanin abinda ke faruwa,itama tabata goyon baya hundred percent,sannan Ummina tace to ga amanar Aunty Nana nan tabata ita Amana. Tayi farin ciki mara misaltuwa saboda macece Mai hakuri da son yara,uwa uba ga addini da dukiya,mijinta ma yayi farin ciki duk da bada izini Daddy aka kawo Aunty Nana ba. Washegari suka shirya da Ummina da yayarta sukaje hospital aka juya mata mahaifa bazata sake daukar ciki ba,domin ummina tace"ita tana zargin Daddy ke kashe masu yara. Kwanan mu daya muka dawo duk da nida Aunty Nana munyi kukan rabuwa da juna sai dai hakan shine mafita. Koda muka dawo gida Daddy da Hjy sameera Basu dawo ba sai hjy saddiqa,nan Ummina ta sanar da ita abinda ke faruwa,itama tayi farin ciki sosai Kuma ta bata goyon baya. Wata Rana hjy saddiqa tafara ciwo Wanda anyi magani abin kaman gaba yakeyi,Ashe Daddy ne yafara amfani da ita ta baya,shine fah tsutsotsi suketa cinye mata wajen,hatta kashi Bata iyayi sai dai wajen yayi ta zubar da jini,dalilin sanin ummina kuwa ita da kanta hjy saddiqa ke sanar da Ummina, gaba daya ta rame taui bakinkiri babu kyan gani. Duk mutuwar da akeyi ba'a taba wanda ya girgiza ummina ba sai na wanna Karan,domin Allah yayiwa hjy saddiqa rasuwa,a dalilin homosex da Daddy yayi da ita,sai dai abin takaici likitoci sun boye,shida kanshi yamata sittura aka kaita. Sajida tadawo hannun Ummina da Zama, nida ita sai muka koma kamar twins,ummi dalilin ta dena fita ita kadai saidamu,sanna ta dena aikemmu ko Ina hatta wajen Daddy,wannan dalilin ne yasa Daddy suka fara tsiya da Ummina,sanna yace saita nemo Aunty Nana duk inda ta kaita, Ummina tace bazata nemo taba. Wannan dalilin yasa Daddy ya tsani Ummina sannan hatta abinci yadena bamu,da kula damu,hatta ni saboda tsanar da nanuna Ina Mai karara. Ummina ta Kira ya mashkur ta sanar dashi abinda ke faruwa,yaso daukar mataki,Amma Ummina tana tsoron kada mutumci na Daddy ya zube. A sirrince Daddy ya siyama Ummina gida a garin Zaria. Wani dare Ya mashkur yaturo wani abokinshi ya daukemu muka gudu,komai bamu dauka ba hatta kayan sawarmu,bayan komawarmu da wata biyu aka daura Auren ya mashkur cikin jimamin rashin ganin Ummina da yaranta,ko taron biki 'yan bauchi da dangin Ummina basuyi ba saboda jimami,Daddy na kuwa hankalinshi ya tashi na rashin ganinmu. A halin yanzu Daddy yakara aure da matansa ta haifi yara biyar,Amma yanzu saura uku biyu sun rasu,a shirye nake yanzu Dan daukar fansa da hukunta Daddy na da temakon ki Shakeerah,domin nasan Babu mai temako na sai ke, mahaifina babban mai lefi ne. To wannan shine labari na. Cike da tausayi duk cikansu fauzi da shakeera ke duban khadee, Shakeerah tace"Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun tunda nakejin labari bantabajin irin labari irin wannan ba,tabbas Sai an hukunta shi,ke da duk Wanda keda hannu a wannan annobar hatta munafikin likitan Daddyn ki. Fauzi tace"Tabbas wannan yacika azzalumi Allah yasaka muku,insha allahu sai yayi mummmunar karshe,ki yahakuri mahaifinki ne,Amma meyasa kikace mun ke 'yar bauchi ce? Khadee ta share tears din da suka zubo Mata tace"Eah Mana ni bauchi nasani garinmu,bakiji labarin bNe? Fauzi tace"ok naganae sorry kinji kada kidamu kinji? Khadee tace"kada kidamu am ok. Shakeerah tace"to ya maganar sajida ita tana wane skul ne yanzu? Khadee tace"tana A.B.U teaching hospital ne yanzu tana karantar dental. Shakeerah tace"Allah sarki ummi taga iftila'i,to maganar Aunty Nana fah? Khadee tace"tayi aure yanzu haka tana kasar Argentina ta auri wani dan jarida. Shakeerah tace"Allah sarki rayuwar duniya duk babu dadi,idan kana ganin damuwar ka idan kaga na wani sai jikin ka yayi sanyi. Fauzi tace"Allah sarki ni kuwa sai na dunga ganin kamar tawa damuwar tafi ta kowa. Shakeerah ta buga tagumi tace"Fauzi muna sauraranki. Fauzi ta cigaba dafari dai, "Sunana Fauziyya Aleeyu ni haifaffiyar garin gombe ce,mahaifina mutum ne mai rufin asiri dai-dai gwargwado gaskiya mu ba masu kudi bane,mahaifiyata wacce nike cema Inna mu uku ta haifa nice babba Sai kannena su biyu duka Mata,sana'ar mahaifiyata sai da manja da man gyada Kuma Alhamdulillah Yana rufa Mana asiri,shikuwa mahaifina icce yake siyarwa,a haka Allah ya rufa musu asiri suka samu a makaranta. Kishiyar Inna ta muna kiranta da baba ladi tanada yara hudu duka mata,tunda muka taso muka cidda baba ladi itace ke mulkar gidan mu sai abinda tace ayi akeyi,da yake Inna macece mai hakuri Sam magana ba yadameta bane,a hankali nataso da bakin jini a gidanmu har a wajen Inna ta wanda narasa dalili,ana cewa babu Wanda yakai mahaifiya son 'yayanta,Amma Banda tawa mahaifiyar domin kuwa a cikin wahala na taso,mutum Daya ne zuwa biyu nake raba naji dadi,mahaifina da yayata 'yar-'yan baba ladi itace babbar 'yarta. Sune kawai kesani bakin ciki abubuwa da dama idan Inna ta tayimun Zama nake na tambayeta anya ita ta haifeni? Tunda nataso bantaba Jin dadin uwa ba,itace kyara hantara,lokuta da dama nasha kwana bansa abinci a bakina ba,inda Allah yake temako na wajen kanne na nake kwata nace wallahi Muddin bazanci ba Suma ba zasu ciba,saboda inada bakina to abubuwa da dama su suke temakona,a cikin kannena akwai khadeeja wacce muke cema dijee,yarinya ce mai natsuwa jinimmu ya hadu sosai,hadasiyya itace ke bina sai dai ko kadan bamu ga maciji,itace 'ya mafi soyuwa a zuciyar Inna saboda ita ta amince da talla,muko nida hadasiyya da babbar yayarmu munason karatu ,sai dai ita Kuma baba ladi duk cikin yaranta babbu wacce takeso kamar Yaya kaltume babbar yayarmu,kujifa wayau,eah Mana wayo saboda ita baba ladi tana zuga Inna ta mana tijara Amma ita Sam Bata ma yaranta,yaranta tamkar kawayenta,zata zauna taji duwarsu Amma Banda tamu uwar. Kullum idan na zauna Ina tunanin anya hakanan baba ladi tabar Inna?sai dai ance zato zunubi don haka cikin Sauri nake goge wannan zaton a Raina. Har yazo takai mahaifinmu yakwanta jinya,duk tausayi irin na Inna sai da ta canza hali,daga ita har baba ladi Babu Wanda yadamu da rashin lafiyar baba,nida dijee da Yaya kaltume ke jinyar sa wannan dalilin yasa Inna tace Muddin bamu rabu da jinyar baba ba zata tsine mana nida dijee. Nikam cewa nayi bazan bar jinyar mahaifina mai tausayamun ba,sai dai duk abinda zatayi mun tayimun. Inna bata tsine mana ba,sai dai ta koremu a dakinta,sannan ta dena bamu abinci nida dijee da mahaifinmu,duk wannan abun baba ladi ta bata shawar tace itama bata bashi. Abinda Inna bata sani ba shine baba ladi na Aiko Yaya kaltume da abinci,Kuma duk dare tana zuwa gaishe shi. Maganar kanwata hadasiyya da sauran 'yan uwana yaran baba ladi su uku hassana,usaina,hauwa,su hudun nan sai suka fara harkan karuwanci,domin kuwa maza har cikin gida suke kawowa,suyi iskancin da zasuyi sufita,wannan dalilin yakara haddasa jikin baba yayi zafi. Ya Zama na unguwar mu babu gidan da akewa Allah wadai da tirrr Kaman gidan mal Ali mai icce wato gidanmu. Kunsan Allah daimond ladies sam bamuyi dace iyaye na kwarai ba,domin baba ladi da Inna su suke nuna ma su hadasiyya yanda zasuyima maza suyi iskanci dasu. A kwana a tashi baba ladi ta ragewa Yaya kaltume sanwa,Wanda ake samu taba baba shima ta dena,mu dama tuntuni Inna ta yayemu. Ita burin baba ladi Yaya kaltume ta gujemu tace sam bata yimmu. A hankali muka fara shiga wahala da tagayyarar rayuwa hatta tufafinmu Basu da kyan gani saboda bamu da maraba da almajirai,shawarar Yaya kaltume na nema akan zamu je neman aiki gidajen masu kudi,da kyar ta amince shima sai da taja mana kunne sannan ta amince,ita da kanta ta samammana aiki a gidan wani hamshakin attajiri babban Dan siyasa senator Ahmad shehu tabako. Gidan mutane masu karamci da sanin darajar Dan Adam,Basu da matsalar komai da tawuce ta matan uba,Sam matar shi a maryan Bata da hali. Koda Yaya kaltume taje muka musu bayani ni kadai suka dauka aiki Banda kanwata dijee,munyi kokarin su dauketa Amma abin ya gagara domin sunce tayi karama da yawa a lokacin tana 8years. Haka muka hakura,mub rabu sun daukeni aiki gobe zanfara zuwa wajen bakwai na safe. Bamuyi kasa a gwiwa muka cigaba da bin gidajen masu hannu da shuni don nemawa dijee aiki,cikin yardan Allah muka samu a gidan wani dan siyayasa shima. Alhamdulillah sun dauki dijee,matarshi tana da kirki da fara'a ga son mutane,ta dauki dijee bayan tace itama gone zata fara zuwa,kafin mutafi sai da tayima na ihsanin kudi dubu biyar tace dijee tasai sabulu tayi wanki,sannan ta bamu kayan abinci, taliyace guda biyu da doya hudu. Cike da farin ciki muka dawo gida,duk inda muka wuce zunde a ke Mana da baki,a dalilin 'yan uwan mu da suka fada harkan karuwanci. Bayan munshiga gida Yaya kaltume ta amsa abincin da kudin ta adana mana,makota tashiga gidan wata kawarta ta dafo Mana taliya ta kawo mana mukaci saboda Babu halin girkawa a gidanmu. Wata ranar alhamis da safe usaina ta shigo da kwarton ta sun gama shedan cinsu da masha'a Aiko daganan tsiya ta barke ita dashi,dambe suke sosai tana zazzaginshi. Mari ya kifa mata Yana cewa wallahi kome zakiyi sai dai kiyi bazan aureki ba mezanyi da anawo irinki 'yar titi wacce rijiya ma tafi halittarki daraja. Kukan kura usaina tayi ta cakumo mashi kwalar Riga,gaba daya gida ya hargitse da hayaniya hadda makota sunzo suna saka baki Amma sunki denawa,usaina kuwa anyi anyi ta saki kwarton ta taki. Sake tsinka mata mari yayi Wanda yasata sakin ihu ta kaimasa cizo a kunne,Aiko zafin da yaji ne yasa ya fusgota ya hade kanta da garo. Wani Kara ta saki tare da sulalewa kasa,ko kafin kace me kanta ya fashe sannan ko motsi batayi,da aka dubata aka bincika Allah yamata rasuwa. Domin ko numfashi batayi innalillahi wa inna ilaihirrajiun ranar munga tashin hankali wacce ba'a samata Rana munga iftila'i,kafin kace kwabo 'yan sanda sun zagaye gidammu. Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi 🗡️ 💕💕 ❤️ [7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨ ( Daukar Fansa ) Story& writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL ______✍🏽______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* 🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *_T.W.A_* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciyar⬇️ _ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_ *DA* _ _MIJIN ZAHRA_ 💎💎💎 _Jirgin diamond ladies (Daukar Fansa) tana maraba daku,naji korafe korafen ku Akan littafin Nan,masu yabawa nagode,kamar yanda masoya na suka roka na Kuma amince albarkacinsu na maida book din diamond ladies (Daukar Fansa) Naira #100 only Babu damuwa Allah yabar zumunci_💎💎💎 Bismillahir-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai*.... Page:9️⃣-1️⃣0️⃣🖊️ __________Bayan komai ya lafa na hargitsin gidanmu abinda yafaru da usaina bazamewa iyayenmu darasi ba,dominko a lokacin nema lakafa ya cigaba domin iskancin su hadasiyya gaba yayi,idan kazo gombe kaje unguwarmu duk Wanda kacema gidan mal.Ali mai icce babu Wanda baisan badalar da akeba,ana cikin wannan yanayin na annobar masifa a gidan mu Allah yayiwa baba rasuwa. Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un kunsan iftila'i da muka gani? Girgiza Kai su shakeera sukayi. Fauzi tace sallar gawa an rasa Wanda zaiwa baban mu,haka nida Yaya kaltume muke bin gidaje Kiran makota don yimasa sallah,Amma abin yagagara. Da yake ranar juma'ah baba ya rasu,ganin haka yasa nanufi masallacin juma'ar nayuwa limamin masallacin bayanin abinda ke faruwa. Ana kuwa idar da sallah ya sanar cewa zasuje want sallar gawa,don Allah Mutane su taho a tafi. Haka kuwa akayi manya manyan Mutane masu ilimi da kudi suka dungumo gidanmu don yiwa baba sallar gawa. Ganin haka yasa makota Suma suka fito,akayi Masa wanka a ka tada sallah......hmmmm bansan ranar da abin kunya zai gogu a tarihin rayuwa ta ba,domin ana cikin yima baba sallah hauwa tazo wucewa Tasha giya tayi tatillll a cikin maye, ta karisa bakin gawar ta fincike likkafanin da aka rufe baba. Gaba daya sallame sallar Liman yayi,tuni hayaniya ya kaure a wajen dubban jama'ah Fadi suke subhanallah. Wani yaron Liman ne yakariso inda hauwa take ya Dalla mata wani gigitaccen Mari. Tsalle hauwa tayi gefe guda cikin muryan maye tafara duramai wasu arnan zagi,sake kifa mata Mari yayi Wanda yasata kundin bala ta baje a qasa. Janta yayi da karfi ya Shiga da ita zauren gidanmu,sannan aka cigaba da yiwa baba sallah,cikin yardan Allah aka kaishi gidanshi na gaskiya. Bayan sunkai baba suka jiyo gidanmu,Liman da kanshi yafara yiwa su hauwa da hassana da hadasiyya nasiha akan suji tsoron Allah su shiryu tun kafin duniya ta shiryar dasu,su lallabawa rayuwansu su fito da miji suyi aure..... Wani uban tsaki hadasiyya taja Wanda yasa Liman yin Shiru,Cike da mamaki kowa ke kallonta,hassana itakuma ta dauka"kaga malam dakata! Tayi maganar tana daga Masa hannu,idan wa'azi kakejin yi ga masallaci can kuje kuhau munbari kayi,mu yaranka ne da zakazo kana mana wani nasiha na munafurci? Cikin da bacin Rai samarin dake wajen suka Mike sukayi kan hassana. Dakatar dasu Liman yayi,Wanda koni akaran kaina banso haka ba,naso yabari aci uwar kowacce a cikinsu. "Haba shamsu bai kamata ku biye musu na ni domin Allah nake musu nasiha,duniya CE ta ishesu Riga da wando duk Wanda ya dauki duniya don Jin Dadi ya sauke,sannan yajuyo wajen su Inna yace"ko ba'a fada ba nasan kune matan marigayi inaso ku kula da tarbiyyar 'yayanku kada ku manta 'yaya Mata Allah yabaku,meyasa bazaku gyara rayuwarsu ba? Baba ladi tace"kaga malam Liman don Allah katashi katafi mungode da nasiha,dama ba'asan asalin balbela bace sai Tace daga Sudan take,don kawai yanzu an shiryu shine za'ace ga zance ga magana.? Shiru gabadaya wajen akayi,a hankali Liman da tawagarsa suka Mike batare da kowa ya sake magana ba. Suma matan makota da suka shigo ko wacce mikewa tayi ta fita,baba ladi tace"Eah MUNAFUKAI a gayas shegu. Inna tace"Ai a sararru ne masu kwana da Ido daya. Da nida Yaya kaltume da dijee kuka muke sosai,Ina nadama da danasanin wannan rayuwar na ahalinmu. Washegari da safe muka shirya nida qanwata muka nufi gidajen aikinmu,domin bamuga amfanin Zama da matsiyata irin ahalinmu ba,baba ne Kuma ya rasu Babu abinda yake bukata sai addu'ah. Dijee nafara rakawa gidan aikinta,daganan Sai na na wuce nawa. Tabbas bazance muku banyi dace da gidan aiki ba,sai dai Sam matar da nakewa aiki batasan darajar Dan Adam ba ita da yaranta,idan Ina aiki bana fuskantar komai sai wulakanci da kyara. Inda Allah ya temakeni akwai mahaifiyar Hon Ahmad itace take taka musu burki. Abinci kuwa sai anci an rage ake bani,ban damuwa nakeci saboda a gidanmu ko kwantan kwatan shi bazan gani ba,wata Rana na ragewa khadeeja wata Rana Kuma Yaya kaltume. A daddafe nayi wata Daya a gidannan,albashina aka bani dubu goma,nayi farin ciki sosai,ji nake kaman anbani wan manyan kudi. Dijee itama dubu goma aka Bata a gidan da

Chapter 2 of 10