Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 3
. [8:18AM, 10/23/2016] Rash Kardam: MOTAR KWADAYI By Rash Kardam & Khadija Candy ~ Da safe kuwa yanda naga, idon Ayshat ya yi ja, nasan ta niku ba kad’an ba. Khaleel ko sai tarairayata yakeyi, tamkar kwai. tundaga wannan rana suka shimfid’a soyayyansu, mai cike da burgewa, komai tare sukeyi, inka gansu gwanin ban sha’awa, Khaleel ta tattala matarsa, itama tana gudun abunda zai bata masa rai. Ayshat tayi kyau ta k’ara haske. Niko Rash “nace anya wannan ,haske haka na kalau ba”. Sannu a hankali rayuwa ke tafiya dad’i da ba dad’i, kayan garansu ya kare, randa inya samo musu mai maik’o suci. Randa in bai samu ba har garin kwaki suke ci, ko kad’an Ayshat bata taba nuna fushinta ba, kulum tana cikin masa, Addu’a da fatan alkairi. Safiyar yau ta tashi da zazzabi mai tsanani, ga jiri da ke d’ebanta. Hankalinsa ya tashi matuk’a, gashi ko si- si bai kwana dashi ba. Ko dayaje gidansu, yatarar da iyayensa, gari kwaki suke sha, ya gaida su Mamansa tace”Khaleel lafiya na ganka haka?. Cikin damuwa yace”Aysha ba lafiya kusan sati d’aya, gashi banda ki naira a hannuna. “Yasalama towo gashi muma haka muka wayi gari, amma ga wancan tv kaje ka sayar sai a samu a mata jinya. Tv ya d’auka yaje ya sayar dubu biyar da d’ari bakwai, sukaje asibiti a ka mata gwaji, likita ya tabbatar da tana d’auke da juna biyu, har na wata hud’u. Magunguna ya rubuta musu, sauran ya sai musu kayan abinci, rabi ya kaimusu, saura ya kai ma su Ummansa. Ko da Ayshat ta samu sauki, yace ta shirya, kaita gidansu ta gaida iyayenta, daga nan suka wuce gidansu Khaleel da murnan Umma ta tarbeta, tarinka ina zansaka dake. Da daddare da zasu tafi, “Umma ta mata nasiha sosai, da takara hak’uri da yanda mijinta ke. Ayshat”tayi godiya ma Umma suka tafi. Khaleel result ya fito yayi kyau sosai, yanzu aiki ya dunkufa nema, kulum sai ya fita amma shiru, Ayshat ko kulum tana cikin masa addu’a da fatan alkairi. Safiya kam harka take ba sanya, ta maida bariki kamar rigan sakawanta, ko shakka babu, yanzu motanta biyu, kud’i kuma ta tarasu ba’a magana. Samarukanta na da duk ta canza, Abuja kuma ya dawo mata kamar gida. Kwanki sun ja, Aysha ta shiga watar haihuwanta, Khaleel ko kula ta musamman yake bata, yana tattala yar matansa. Safiyar yau ta tashi da nakuda, hankalin Khaleel ya tashi, mai napep ya nimo suka nufi asibiti, aka shiga da ita labour room, “addu’a yaketayi Allah ya sauketa lafiya. Wayarsa kiran nokia, irin mai tocin nan, ya kira Baban Aysha ya sanar ma, ya kira gidandu ma ya fad’a musu. Ayshat ta kasa haihuwa da kanta, likitoci sukazo suka sanar masa dole sai an mata tiyata. Ba k’arami min tashin hankali ya shiga ba, don kud’in da ya tara 8k ne, ana haka sai ga iyayensa, nan ya sanar musu, Malam yace”abasa ruwa a kofi da ruwa, murfin flaks aka miko masa, Addu’a ya yi, dake wanda suke kanta mudulmai ne, ba’a samu matsala ba, sukabata cikin ikon Allah ba’ayi minti biyar ba, ta zankad’o yaranta guda biyu, mace da na miji. Wayyo karkuga murna gun khaleel, bayan nurses sun gyarata, ta huta suka dawo gida. Yan’uwa da abokan arziki sai murna sukeyi, Khaleel daman ya sai ragonsa yana kiwo bai samu matsalaba, ana gobe sunane aka kirasa ne, fidelity bank suka kirasa, daman ya rubuta musu Application, ya samu aiki a gurin. Cikin murna ya zo gida ya sanar musu kowa sai murna yake masa. Ko ni Rash nayi murna sosai, gaskiya yan biyu sunzo da goshi. ….Na…. Rash Kardam & Khadija Candy [8:18AM, 10/23/2016] Rash Kardam: MOTAR KWADAYI By Rash Kardam & Khadija Candy ~ Cikin ikon Allah anyi aiki lafiya lau, acire ciki murna agun Sofy ba’a magana, Alhaji ya had’o mata magunguna, da kayan ci masu kyau. Kula ta musamman yake bata, sai da ta warke sosai, tukun suka sake komawa ruwa don bata bar Abuja ba sai da tayi samaru biyi, kuma duk halin d’aya ne,Ta samu kud’i ba kad’an ba suka dawo Kaduna. Kwanaki sun tafi, yanzu Ayshat ta kamala jaraba wanta, biki yarage saura sati d’aya duk dangi sun had’u sai shirye-shirye akeyi. Sofy kuwa waya tayi ta sanar da Alhaji, dubai ya aika aka sayomata, wasu ready mate d’in kaya, Kala 6 da takalama su, wanda zatayi fitan biki kawai. Inna ta kuwa wani mai shago ta wanka ya bata Swiss less masu kyau, tabayar aja d’inka mata. Ayshat bata shirya yin wani event ba, kasancewan mijinta bayida k’arfi, d’aurin aurene da yini kawai. Haka akayi ta su cin-cin, ranar jimma’a ta zago aka d’aura aure, da daddare mota uku sukazo d’aukan amarya, aka kaita gidanta, washegari yini karkuso kuga inna da d’iyarta don sunyi wanka kece raini, wankan nuna masa’a. Ko ina a gidan biki su ake nunawa, baran Sofy duk kayanda tasaka abinsone. Wasu kuma gulmasu suke a ina take samun kud’i haka?. Yayinda wasu dangin uban yan neman k’ora, sun makale musu, yini kam a gidan amarya Alhamdulilah! Biki ne na rufin asiri bana k’arya ba. Da dadare yan’uwan Umma, suka saka Ayshat tayi wanka ta canza kaya, nasiha sosai suka mata, da gwada mata irin gidan ta suke, tarike bakinta banda gulma, kuma duk kashin abunda mijinta ya kawo, tamasa godiya, ta amsa da mutunci. Kuka tayi sosai dakyar ta barsu suka tafi. Ni ko Rash na zo gulma don inga yanda d’akin Amarya ya tsaru. ‘Daki d’aya ne, sai gadonta da kujeru guda biyar, sai d’an fridge karami, da tv karami. ‘Daki dai sai son barka a talakance yayi, abokan ango ne sukayi sallama, bayan sun zauna, nasiha sosai sukayi Ayshat, sannan suka musu fatan alkairi, suka tafi abunsu. Bayan tafiyansu ne, Khaleel ya umurceta da tayi alwala suyi Sallaha, ba musu ta d’auro alwala, suka gatar da sallah, yan tambayoyi ya mata gameda addini, ta bashi amsa. Kayan da yazo dashi ya d’auko musu, tana yar kunya ya ringa bata abaki, saida ya tabbatar ta qoshi tukun shima yaci. Daga nan yasoma janta da hira, ganin ango da amarya suna buk’atar hutu, yasa na fito a d’akin, don ba hurumina a gun, nidai Rash na musu fatan alkairi, naja musu qofa aci Amarci lafiya. …..Na….. Rash Kardam & Khadija Candy [8:18AM, 10/23/2016] Rash Kardam: MOTAR KWADAYI By Rash Kardam & Khadija Candy ~ Ranan suna yara sukaci sunan,Ameena da Kabir, ana kiransu da Amrah da Ameer. Cikin ikon Allah Khaleel ya fara zuwa aiki, ya kasance mai hazaka da k’okari a gun aiki, yanzu Alhamdulilah suna cikin rufin asiri. Safiya duniya gidan dad’i a gunta, yau tana shirin zuwa Abuja gun wani saurayinta, a motarta ta tafi, tana zuwa office d’insa direct ta tafi.tana zuwa kanciyansa ta d’ale, “my honey nayi missing d’inka da yawa. rungumota yayi suka soma bad’alansu, office d’in aka turo Alhaji Tijjanine yazo, wani kalo ya bisu dashi, “oh! Sorry nashigo ba excuse! Tk yace”no! Ka shigo kawai, Sofy ta mike ta zauna a d’aya kujeran, tunda taji ya ambaci sunan sa, ta gane abokinsa TJ dake bata labarinsa. Yana da kud’i sosai, TJ yace”barinje na kawo maka, files d’in ya fita. Yana fita Sofy ta matso kusa dashi, tare da kashe masa ido, ganin bai kula ba ta soma balle botilan riganta. Cikin zuciyan TK yace”yarinya bakisan waye Tukur ba, ganin kar TJ yazo ya gansu, ya mika mata phone d’insa. Number ta tasaka masa, ana haka sukaji za’a bud’e qofa, da sauri takoma mazauninta. TJ ya basa komai yamusu sallama ya fita. Daga office gidansa suka nufa, suka bud’e babi iskancin su, kwanta uku suna tare tace”zata tafi”. Badan TJ yaso ba, ya bata kud’i ta masu yawa tamasa sallama, tana fita TK ta kira ya bata address d’in ida zata samesa. Wani gidane kayatace na gani na fad’a, ko da tashigo da man, ya sanar da masu gadi zuwanta. Sai da ta wuce gate uku bayan babban gate, sai qofofi hudu, asalin cikin gidan yana da duhu, ko da tashigo k’irjinta, ya soma duka uku-uku. TK da murna ya karbeta sai da ya kaita wani d’aki, sai da suka zuba iskancin su yayi wanka ya fita. Wani d’aki ya shiga, waya yakira yace” gatanan ta iso, a turo da masu aiki, sannan ka basu sabon wukan. Daga d’aya bangare akace”ok! In kun cire abunda kuke so, ina son gan-gan jiki. “To ba matsa”. Ya kashe wayar yana wani muna fukin dariya. ……Na….. Rash Kardam & Khadija Candy [8:18AM, 10/23/2016] Rash Kardam: MOTAR KWADAYI By Rash Kardam & Khadija Candy ~ “Ok! Ba matsala”. Wayar ya kashe yana wata munafuk’in dariya, hahaha “Yarinya ke baki da wayo, an gaya miki mata suna gaba nane?. “kud’i shine da muwata, war har damin signal da ido. ‘Dakin ya dawo, ita ko cikin wasu matsatsun kaya wanda shi da babu duk d’aya ne, tazo ta rungumesa bakinta ta sanya anasa, da zai tureta, amma da yatuna karta gane target d’insa, sai ya biye mata suka sake kalacea. Yana kwance a gefen gado, sai maida numfashi yake wayarsa ne tayi k’ara, da sauri ya d’aga yace”ya kun isone? Daga d’aya b’an garen akace”eh! Gamu a cikin gidan. “Ok! To ku shigo. Ya kali Safiya yayi murmushi yace”baby taso muje”. Cikin shagwab’a tace”ina zamuje haka?. “Oh! Baby kitaso da sauri, wani big deal zamuyi. Jin babban harka yasa ta mik’e da sauri. Suka nufi wani d’aki, wasu k’arti ne su hud’u, suka shigo, nan take fiskan TK ya canza tamkar bai tab’a dariya ba. Safiya da tawani kwanta a jikinsa, tana sha-shafa shi, hankad’ata yayi gaban wayannan k’arti, Yace”gata ku rike min ita. Cikin azama suka damketa, Safiya tace”TK wani irin wasa ne haka?. Dariya ya bushe dashi”kee angaya miki TK sakarai ne irinki?. “Mayyar kud’i banza, akan kud’i kin zubar da kimanki, darajanki, kin bargidan iyayenki, kina bin maza don subaki kud’i. “Safiya kin d’au ma kanki abunda zaki wahala. “Kisani duk abunda d’a namiji yayi ado ne garesa, banda’ya mace. “Yau zan koya miki hankali. “Ku rufe mata baki. Safiya ta fara cewa”TK dan Allah kayi hak’uri, kar ka cutar da ni. “Na maka alkawarin daga yau na daina iskanci daga yau. Dariya yayi yace”ke ta shafa, yanzukan kijira zuwanki kiyama. Safiya ba halin magana an rufe bakinta. Wanu abu ya d’auko a gidansa, kamar na shentos, yarike ya kaleta yace” na manta ban sanar miki ba, ayanzu duk wanda kika ga yayi kud’i kazamin kud’i to ba duka bane na gaskiya, suna had’awa da yankan kai da shan jini. “Nima ina d’aya daga ciki, son kid’in ki ya kawoki. “Ko TJ da kike gani ba zaman office bane ya tara mishi wannan kud’in, shima yana yankan kai, abunda ya hana bai yanka ki ba, sabida yana matuk’ar sonki. Shiru yayi na d’an wani lokaci, Safiya ko hawaye ke zuba sosai, tana sonyin magana ba dama. TK yacigaba da cewa”Safiya amma ke tsaban bariki da cin AMANA, abokinsa yazo kika nuna kuyi tarayya dashi, ni kuma ba na sonki niman mata baya gabana, wacce nakeso d’ayace kuma bana had’a soyayyanta dana kowa. Yana gama fad’an haka, yace”kurike min ita”. Safiya naji tana gani yazo gabanta wannan abun, yafesa mata a ido, take taji wani azaban, da bata taba’a jin irinsa ba, tana kuka haka suka saka wuka cikin kwarewa, ya cire mata idonta duka biyu. Suna gamawa yace” ku kaimasa gan-gan jikin na d’auki abunda nakeso. Safiya da azaba yasa ta suma, kattin nan suka d’auki ta suka sata a Mota suka bar gidan. Ko da suka fito wani abun mamaki, gidan da ke cikin gari ya koma jeji, gudu suka soma shararawa a titi. Nikam Rash da tsoro yacikani, kasa bin su nayi, har sai sunyi nisa nabisu inga mai zai wakana, don kar nima a yanken kai. …..Na…. Rash Kardam & Khadija Candy [8:20AM, 10/23/2016] Rash Kardam: MOTAR KWADAYI By Rash Kardam & Khadija Candy ~ Gudu sosai sukeyi, sai da sukayi tafiya mai nisa, d’aya daga cikin mutane hud’un nan yace”ya Baba nifa yarinyan nan tun d’azu na kamu da KWA’DAYINTA, ko zamu ratse da ita ne, in mun kwashi gara, sai mu kaimasa ita, kuma kaga yanayin jikintan nan zamu huta. Duka suka yarda a haka, kwana da motarsu sukayi, suka nufi wani k’aramin gida mai kyau, nan suka kaita, biyu suka shuga cikin gari suka sayo musu abinci da juice, sai da suka yayya fa mata ruwa ta far-fad’o, suka bud’e mata baki, d’ayan yace akwai sauran maganinane ka bata, don oga yaso mata mugunta ne, da ya shafa maganin nan bazataji zafi ba. ‘Dayan ya d’auko wani ruwan magani, suka shafa mata, take taji idon ya rage zafi, abinci suka tura mata, sai da taci ta koshi suka bata ruwa tasha. ‘Daki suka kaita nan suka cire kananun kayan jikinta, suka fara cika aiki. Safiya duk son Sex d’inta yau tashiga nadama, yau ta yarda da karin maganan hausawa dasuke cewa duk wanda yashiga MOTAR KWA’DAYI zai sauka a tashan wulakanci. Yau maza hud’u a kanta gashi bata da ido, nan tafara addu’a Allah ya kwaceta. Sai da suka gama biyan buk’atar su suka tashi. ‘Dayan yace”gaskiya tunda nake d’ana mace, ban tab’a jin mai test kamar wannan ba, haka sukayi tayin hira, da yamma biyu suka fiya d’aya yashiga wanka, wanda ya yaba da ita yace”ke zan taimake ki, zai kaiki qofar gida kisan yanda zaki gudu, don banzo acinye ki, kin min kyau, kai ta d’aga masa alamar eh!. Kama hannuta yayi yana leke ya tura ta waje yace ta mike da gudu, yana komwa daman a falo suke da ita, daki yashiga ya kwanta kamar bai san komai ba. Gudu take sosai gashi bata gani, haka zata fad’i ta tashi duk ta gwara jikinta sai jini yakeyi, a haka harta fito wani titi batayi aune ba sai jin kiiiii kake mai mota ya kad’eta, yana gani ba mutane kusa ya juya yasa gudu, mutane da suka gansu, suka zo da gudu suna salati, ko dana leka me zan gani, k’afar Safiya guda d’aya ya dagargaje tundaga cinya, a sume akayi asibiti da ita, sai da ta far- fad’o. Aka tambayeta ita yar inane, tace”a Kaduna na ke” bata sake cewa komai ba ta suma, nan take a ka d’auketa sai asibitin Kaduna, kwanata uku bata san ida take ba, hakan yasa aka d’au photo ta aka saka a gidan Tv ana cigiyar iyayenta. Inna Safiya tana zaune tace”oh! Yau barin kali labarai”. Tana kunawa dai-dai lokacin da’aka nuno fiskan Safiya. “Ihu tasaka a guje tayi d’akin Malam tana fad’a masa da kamar bazai tashiba amma tuna hakkinsu yasa ya mike, take suka nufi asibiti, suna zuwa a ka nuna musu Safiya Malam ya jin-jina al’amarin, nan likita sukace su kawo dubu d’ari da hamsin a mata aiki. Malam yace”nikam banda shi daman duk wanda bai ji bariba yaji hoho. “Duk wanda yashiga MOTAR KWA’DAYI to ba makawa zai sauka tashan wulakanci. “Kee na yarki gashi kun gani, kisani ba balabarinta da ban sani ba, ido na zuba muku, harda zuwanki gun boka, amin asiri Allah ya kareni, yanzu sai kisan nayi, ya juya yatafi ko wai-waisu baiyi ba. Inna mashin tahau da ta je gida ta d’au gwala-gwalan Safiya duka taje kasuwa, da tambaya taje shagon masu sayan gwala-gwalai, tasayar dubu d’ari biyu. Asibiti taje ta basu kud’in aiki aka shiga da Sofy, sunaji suna gani aka yanke ma Sofy k’afa d’aya. Haka Inna tayi zaman jinya a asibiti. Wanamaker sun tafi cikin ikon Allah, kafan Sofy ya warke, har tafara tafiya da sanda. Cikin da ke jikunta ya fito watansa shida, Inna tana cikin tashin hankali, ga Sofy ba k’afa, gashi ta samo cikin shege, tabbas bariki baiyiba bariki ba gurin zama bane. ……Na…. Rash Kardam & Khadija Candy [8:22AM, 10/23/2016] Rash Kardam: MOTAR KWADAYI By Rash Kardam & Khadija Candy ~ Inna ta fashe da kuka tabbas, KWA’DAYINA shi ya jawo min, na cikin yanayin aka basu sallama, ta k’arba suka d’au hanyan gida. Ayshat suna rayuwansu cikin jin dad’i da rufin asiri, duk wata yana d’aukan 70k a haka har gida 3 bedroom ya sai musu, iyayensa ya gyara musu gidansu suma, ya sai yar motarsa k’arama, ya shigo gida cike da fara’a, My Sweetheart, kina ina kizo kuga abun Alkairi, da sauri suka fito da yara, kama hannuta yayi suka fita qofar gida, kimga amaryan mu, Allahu Akbar tafad’a tare da hamdala, cike da murna yace”dan haka ki d’au himar d’inki tare zanuje gida asanya mana albarka. Cikin gida ta koma, ta sauya ma twins kaya, suka shiga mota sai gidansu. Inna sun iso gida, suka shigo Malam yabkaleta yace”ina kuma zaki ae ki d’auketa kukoma ida kike turata, nikam na yafeta a cikin ‘ya’ya na, Inna ta fara basa hak’uri, har waje ya korosu, ana haka sai ga su Aysha da sauri tafito, ta rike Safiya tana kuka. Hak’uri suka ringa bama Malam tare da nasiha, Ayshat tace”Baba ina to zasuje ai bata da gidan da yafi wannan. “Kuma gannuka baya rub’a kace zaka yar. Umma ma hak’uri ta basa, sai Khaleel yasa baki hakan yasa Malam ya hak’ura, yace”kekam Inna na sakeki saki uku, kuka ta fara tana rike rigansa ya kwace ya tafi. Yace”kuma bana son ganinki a gidana. Dole Inna ta d’auki Sofy suka tafi, duniya juyi-juyi. Haka su Ayshat sukayi gaisuwa suka tafi. Bayan kwana biyu, Matar abokin Khaleel bata da lafiya, suka shirya zuwa asibiti sai da suka gaidasu, sunzo zasu shiga mota, Aysha taji ana kiranta, ko da tajuya wata tagani, baka ta rame tamkar skeleton. Nan tsoro ya kamata ta rike Khaleel, wacce ta kira sunanta tace”baki ganeni ba ne?. “Seema ce kawar Safiya” Ido Ayshat ta zaro cike da mamaki tace”kee ce haka?. Seema tace”eh! Nice, Ayshat tayi”salati nasiha ta fara mata. “Ga irin abunda ake gudun muku, ke da k’awarki duk k’arshe ku baiyi kyau ba. Cikin kuka Seema tace”ae mugani kam itama naga ba k’afa ba ido. ” munyi nadama tabbas na yarda da kalman da kuke fad’a mana duk wanda ya hau MOTAR KWA’DAYI zai sauka a tashar wulakanci. Kuka take sosai Ayshat ta bud’e jakanta ta bata dubu biyi, godia tayi mata suka shiga mota, suna hanya kenan, juyawan da zatayi taga wasu kamar su Inna suna bara, cike da mamaki tasa Khaleel ya dawo, ae ko sune fitowa tayi tace”Inna kune ana subhanallah, Inna sai kuka, sofy ma kuka ta fara, saida Aysha ta musu nasiha ta ciro dubu biyar ta basu, Inna tace” yaranki kenan har sun girma, Aysha tace”eh sun girma. Inna ta kira Amrah ama fir taki zusa haka suka musu sallama suka nufi gida cike da jimami. Ayshat tace”tabbas iskanci bayida rana, kuma duk wanda ya hau MOTAR KWA’DAYI zai sauka a tashan wulakanci. Nima Rash na kali Khadija Candy nace”My Mumcyna tabbas hausawa sunyi gaskiya, duk wanda ya hau MOTAR KWA’DAYI to zai sauka tashan wulakanci. BAN HAK’URI Ina mai baku hak’uri, makaranta littafin MOTAR KWA’DAYI, na tak’aita labarin sabida k’aratuwan Azimi. I a muku fatan Alkairi da kuma murnan zuwan wata amai Alfarma, Ya Allah ka amshi, ibadun mu, Ya Allah kasa muna daga cikin wayanda za’a yanta daga wuta zuwa Aljannah, Ya Allah ka yafe mana laifukan mu Ameen. KIRA GAREKU YAN’UWA Kira ga reku yan natan zamani, kuyi hattara da rayuwa, bariki back matabbata bane, iskanci baida amfani, karuwanci back komai acikinsa said nadama da zubuni. Kung a daily yanda k’arshe Sofy ya koma, muji tsoron Allah, Ya Allah ka bamu, ikon tsare mutuncin mu, da Imanin mu Ameen. ALHAMDULILAH Dukkan yabo tsarki, Mulki su tabbata ga Allah, da yabam ikon kawo k’arshen, wannan labari maisuna MOTAR KWA’DAYI, kura-kuren da ke ciki, Allah ya yafe min, ya bani ikon ganewa na gyara. Ina fatan kun wa’azantu dashi kuma ya nisha d’an tar da ku. SADAUKARWA Na sadaukar da wannan littafin ga masoya da yan’uwa Allah ya barmu tare, taku a kulum RASHEEDA ABDULLAHI KARDAM tare da KHADIJA CANDY KUNA RANMU Duk Marubuta Online Hausa Wtriters, muna muku fatan alkairi. GODIYA Godiya mai tarin yawa ga wayan nan group d’in EXTREME HAUSA WRITERS WISDOMS HAUSA WRITERS BEST WRITERS GROUP GALAZAY WRITERS MODERN HAUSA WRITERS CLEVER WRITERS Luv u all my fanz Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: +2347039625239 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3