Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaune a Bayajidda street ita da mijinta da yaronta 'daya.
Ra'uf shima yayi kyau cikin shaddarsa Golden colour yake yasha malum malum dinsa kamar shine angon shine kadai a motar Mukhtar yana can shi zaikaisu Momy Hannatu wajen Dinner din wajen motar suka karaso suka yi masa sallama ya amsa musu ya komar da kansa cikin motar da tunda suka taho yake kallo Rufaida da yake ji sonta yana kara yawa a tare dashi har mamakin kansa yake da farat daya sonta ya shigesa koda yake babu mamaki da ikon Allah kofar motar ya bude musu suka shiga yaja yana yi musu tsiyar sun shanyasa tuntuni yake jiransu

wajen Dinner din suka karasa inda suka bar jakunkunansu motar Ra'uf kasancewar a motar zasu koma suka bada pass dinsu suka shiga ciki sun haska a gurin sosai kuma gurin a tsare yake kujerun da aka jera na karfe da aka jera a hall din suka zauna akansu da aka jera musu abinci kala kala da lemuka akan babban teburin jin abinci da kujeru suka zagaye teburin cikin tsari akeyin komai
Ra'uf ne ya ja Husna da Safiyya su gaisa da Rufaida da suma suke cikin ankonsu golden colour da kalar ce ankon dangin Ahmad maza da mata gurinta suka karasa da Ra'uf yayi musu jagora cikin mutuntawa suka gaisa kamar ta sansu yaji dadin yadda Rufaida ta mutunta 'yan uwansa suma inda suke zaune suka koma suna koda Rufaida kuma suna fadin kyawunta Ra'uf shima cikin 'yan uwansa maza ya koma bayaso taga kamar yana takuramata basu jima a gurin ba aka kira Rufaida ta ba da labarin yadda amarya takasance ba dan tasaba ba tayi magana da harshen hausa cikin kyawawan lafuza da haka takoma da mutane suka fara maganarta Aunty Malika da su Husna suka nuna mata itace budurwar da Ra'uf keso sosai taji ta shiga ranta har daga kallon farko data yi mata har qaguwa tayi a tashi Dinner din ta je gida ta fadawa Ammin Ra'uf yadda surikartasu take dan kafin a kira Rufaida su Momy Asma'un suka bar wajen Mukhtar ya daukesu a mota zuwa gida.
Shima Ra'uf da yake hango sanda take maganganun nata cikin kyawun lafazi sai ya qara jin Rufaidan a ransa itace matar da ya dade yana addu'ar samun irinta tabbas ta hada komai na irin matar da yakeson takasance abokiyar rayuwarsa addu'a daya yake Allah yasa takasance mata a garesa.

Sai da aka yi hotuna da amarya da ango sannan aka fara kokarin tashi daga Dinner din.

9pm aka tashi daga Dinner din aka fara dibar mutane zuwa gida a motoci

*********
"Nasiba yanzu ina zankaiku naji kince min ba gidan amarya zaku kwana ba"
Ra'uf yayi furucin da yake kokarin tada motarsa da yanzu shike tuka motartasa da kansa.

"Eh gidan Auntyn su Rufaida zamu je a Bayajidda street take"

"Ok kice Auntynmu ba"
yayi maganar yana Jan motarsa ba tareda ya kuma magana ba.

Da taimakon Rufaida da take masa kwatance ya kaisu har kofar gidan gidanta maikyau da karamin gate dinsa ,yayi parking din motarsa suka fito su Hudu Rufaida,Nasiba,Zainab,Iklima
Yatsaida Rufaida daya fito daga motar
"Zanje gida zan kiraki wayar Nasiba,ki gaida Aunty idan batayi barci ba idan na kira zaki hadamu"
"To Allah ya kaika lafiya"
"Amin nagode sarauniyar mata"
Da haka tabar gurin tabi bayansu Nasiba
Shima murmushi yayi yabi bayanta da kallo yayi waajen motarsa yaja yabar gurin
"Yam mata har kungama hirar"
Zainab ta furta haka bayan sun kai kofar gidan Aunty Zainab da suke cewa Aunty da Nasiba ke kokarin kiran Aunty Zainab da Ummi Hauwa'u ta turo musu Number dinta.
"Zee banasan wulakanci..."
Wake wulakancin Aunty Zainab da taji Rufaida na fadar haka da ta fito bude musu kofar gate din,shiga sukayi ta rufo kofar"
"Wallahi Aunty Zee ce daga mun gaisa da wani wanda ya kawomu nan yanzu take min maganarsa"
Aunty ta 'dan ha'de rai kana ta furta
"Ni banasan kula kulan nan na abokan anguna ya wanci dukda matansu wasu kuma da wadanda zasu aura ko idan sunada auran da wadanda zasu kara bakuba sakarci ne yawanci yakesa kawayen amarya soyayya da abokan ango gurin bikin kawarsu har su amince musu kuma yawanci da angama bikin zasu manta da yarinyar idan ta zurfafa ita zata jiyo kusan mutuncin kanku" tana maganar tana kokarin tura kofar falon su Rufaida suna biye da ita
Jin tayi shiru yasa Nasiba tayi caraf ta karfe zancen
"Aunty saurayin Rufaida ne abokin Ahmad ne,tun kafin biki suka ha'du da shi da bikin ne soyayyarsu ta kara kulluwa"
Murmushi Aunty Zainab tayi ranta tana yiwa 'yar dan uwan nata Allah yasa na kirki ne ya kuma tabbatar musu da alkhairi
shiga cikin falon sukayi duk suka jefar da jakarsu a saman kujerar falon suna maida gajiya
Rufaida tana ganin Asad 'dan Aunty Zainab a falo ta daukesa tana masa wasa
Ruwa da abinci ta kawo musu suka ci daganan suka gaishe da Aunty Zainab da take musu tsiyar busu fadamata Dinner din ba aida taje wayar Nasiba ce tayi kara ta mika hannu inda ta aje ta ta duba mai kiran ganin Ra"uf ne yasata mikawa Rufaidha wayar saida sukayi yar fira yace taba Aunty su gaisa sosai Aunty zainab taji Ra'uf ya kwanta mata arai nan ta yi wa Rufaida addua a ranta Allah yasa da gaske yake da aure yazo gareta ya kuma kareta da fadawa tarkon mayaudara suna gama wayar Aunty Zainab tayi zaman dirshan suna fira kamar duka tasansu alhalin Nasiba kawai ta sani bayan Rufaidan da haka mijinta Haris ya shigo ya samesu sannu da zuwa suka masa tare da gaishesa ya amsa fuska sake kana yace wa Rufaida
"Ansha Dinner baki gayyace mamarki Ba bare nasa ran zaki gayyace ni ,da mukayi waya da Yaya Aliyu da Mamarku suke sanarda mu zaku zo anjima ku Kwana anan yanzu kuna wajen dinner"
"Uncle Haris ayimin afuwa yanzu Aunty taga ma mana maganar walllahi mantawa nayi kuma kaga bamu baro Sokoto da wuri ba"
"Zaki tuna ne ai Allah ya sanya Alkhairi"
Ya na gama furta haka yabar wajen da Asad a hannunsa da yana shigowa ya daukesa shigewa ciki yayi Aunty Zainab tami ke tabi bayansa
Da Amin suka bi addu'arsa suka cigaba da fira
Rufaida ta dubi Nasiba ta fara magana
"Wai niko Nasiba ina duriyar Sir Abdul-Rahman"
"Ke dai bari mun rabu da waya tun waccen ranar amma bari nakira mana shi mugaisa"
Ta karashe maganar tana mika hannunta inda ta aje wayarta ta dannan number din Abdul-Rahman Ringing biyu tayi ta katse baifi sakan biyu ba wayarta tayi kara ta duba taga Abdul-Rahman ne ta 'daga ta kunna karar wayar da zolaya ya fara yana
"Amare to ya hidindimun biki"
"Sir Alhamdulillah,ina yini"
"Lafiya lau ya biki"
"Alhamdulillah sir"
"Ina Amarya"
"Wallahi Sir tana gidanta yau aka kawota mukuma muna gidan Kanwar Abbansu Rufaida sai zuwa gobe zamu dawo Kano insha Allah"
"To Allah ya tabbatar da Alkhairi ya kaimu naku,ina Rufaidan da take bata"
"Amin"
Nasiba ta mikawa Rufaida waya suka gaisa sukayi sallama.
Aunty Zainab ta dawo falon tace su koma daki suyi shirin kwanciya.


*SADIYA KHALILULLAH🖊️*️*JININMU 'DAYA*
*BY SADIYA IBRAHIM KHALIL*
*(SADIYA KHALIL)*

*PAGE 24*
*WANNAN SHAFIN NAKUNE SADIYA KHALIL CONVERSATION ROOM,DA JININMU 'DAYA FAN'S GASHINAN KUYI YADDA KUKESO DASHI MASU COMMENT KU CIGABA DA COMMENT'S KU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAHIN🥰🥰SADIYA KHALIL NAGODIYA*

*PAGE 24*


***
9am
Suka gama shirinsu suka fito kofar gate din gidan da Ra'uf yazo yake jiransu su fito ya kaisu gidan amarya Aunty Zainab itada mijinta Haris har kofar gida sukayi musu rakiya Ra'uf da ya fito ya gaishesu cikin girmamawa da Aunty Zainab taji kunya sosai tunda ya girmeta kuma taji ya kwanta mata a rai haka suka shiga mota ya jasu ran Aunty Zainab ba dadi bataso tafiyarsu ba.
Ra'uf suka gaisar ya amsa yana tada motarsa
Saida suka soma tafiya ya cewa Nasiba da take gaban motar
"Yana ji Rufee Sarauniyar mata shiru kodai kun mata laifi ne"
Nasiba ta juya ta kalleta daga bisani ta furta
"Ko 'daya ba laifin da aka mata kasan miskilace budurwar taka,saika riqa hakuri"
Dariya yayi ya furta
"Baruwana keda kawarki kuma tana jinki"
"Ai tasan hakane"
Rufaida da tana jinsu tayi banza dasu dan Nasiba akwai surutu sunsan halinta
Basu jima suna tafiya ba suka karasa Isa kaita Road suka shige kwanar gidan Samiha saida Ra'uf ya fita ya bude gate din gidan kasancewar basuda mai gadi kafin yakoma yaja motar zuwa cikin gidan a harabar gidan suka tarar da su Aunty Samina da har sun shirya tafiya Ahmad ya kira Drivernsu zai maidasu gida Sokoto da Samiha harta fara kuka na tafiyarsu kamar wata yarinyar goye bayan basu duka zasu tafi a lokacinba
Sai da suka gaisa kafin Yaya Balki ta furta
"Ku kuma sai yanzu zaku dawo kun daka tasu Rufaida da ita Rufaida a gida take"
"Mama bahaka bane abokin ango ne baizo da wuri ba"Zainab tayi maganar da sigar tsokana
"Ba wani laifinsa basai kun shirya zaku kirasa ba,ku wuce ku shiga mota keda Iklima"
Ra'uf yaji dadi da yaga Yaya Balki bata goyi bayansu ba ya kuma fahimci Zainab da wasa tayi maganar dako anan yana kyautata zaton ya samu shiga murmushi yayi
Da haka su Zainab suka shige suma sauran matan da Yaya Balki suka shige motar har jikin motarsu su Rufaida sukaje yi musu rakiya sukuma suna zolayar Rufaida said bikinta zasu zo Kano itadai murmushi tayi Ra'uf da matso shima yayiwa su Zainab da iyayensu sallama bayan sunyi ne ya zaro kudi masu yawa ya mika musu sunji godiya suka yi masa da haka motarsu tabar gidan motarsu
Cikin gidansu Aunty Samina suka koma da ita da Aunty Samira da Nasiba su sai anjima Ahmad yace musu Ra'uf zai ajesu gida da shima yau zaikoma Kano

*******
"Rufaida gaskiya kinyi sa'ar masoyin gaskiya samun masoyi kamar Ra'uf a wannan lokacin abu ne mai matukar wahala Dan inada yakinin da gaskiya yazo aurenki zaiyi dan Allah ki riqesa hannu bibbiyu dan yanada kyakkyawan hali,Ahmad yasha fadamin kyawawan hali irinna Ra'uf kuma yafadamin da gaske yake sonki har sun kira Abbanmu sun shaidamasa zasu je tanbaya kuma yanaso kafin yakoma Delhi ya tura magabatansa asaka rana ayi komai""
Rufaida da take kokarin gyara kayan jakarta takalli Samiha
"Gaskiya ne Samiha insha Allah zan riqesa da hannu bibbiyu ina godiya kawata"
"Babu komai kawata nidake tamkar abu daya ne,ina tunanin nama fiki jindadin hadin nan"
Ido ta zaro
"Eh mana dan yaya Ra'uf yace min bakya wani sansa kike nuna masa"
"Kijimin da mutumi idan ba goyasa ya keso na riqa yi ba bansan maiyakeso nayi ba"
"A to kidai gyara dan gaba kadan mijinki zai zama dan nama rage miki zance ban fadamiki Abba dazu ya kira Ahmad a waya yake shaidamasa Abbanku ya masa izinin zuwa gurinki zance yamace basai sunzo Kanon ba,kinga nanda wata shida zamusha biki ni tuwona maina abu namu"
Ni kinga ki kyaleni haka da wannan maganar tayi maganar tana mikewa
"Au zamu rabunma shine zaki mike kibani guri"
Hannun Rufaidan ta riko
"Yi hakuri kawata dawo ki zauna,tunda abin na laifi ne dan na miki maganar rabin ranki kuma gaskiya na fadamiki"
"Wani gaskiya indai irin wannan maganarce banaso"
"Zaki sone malama ki kyaleta samiy ina tunanin tafara jin kunyar mune shiyasa bata san mu riqa mata maganar Ra'uf din"
Nasiba tayi maganar tana karasa zama a bakin gado dan duk tanajin mai suke cewa dan ta shiga bandakine sanda suka fara maganar"
"Allah ya kyauta min jin kunyarku ai indai naji kunyarku gaskiya na fado"
"Eh lallai fa munyarda,kuma indai ba kunyar bace mai zaisa kice abar maganarsa"
Inji Nasiba
"Saboda kuna sawa zuciyata da kunnuwana da idanuna son ganinsa dan jin muryarsa da sauraron sakon da zai isar ga zuciyata"
Rufaida tayi maganar kamar ba ita tayiba Dan tagaji da maganar Ra'uf da suke mata dukda yadda xuciyarta ta aminta dashi lokaci guda da har mamakin kanta take dukda cewa kuwa tun ranar data taba sasa a idanunta take yabon halayar saurayin a ranta dan ko alamun fushi bata gani ba a fuskarsa ba tadai kawar da mamakin son da take masa da ya shige ta farat daya Dan babu mamaki da ikon Allah,dariyarsu ce ta maidota daga tunanin da take"
Dariya maganar tata da tayi ta basu kuma sunga tayi shiru kamar ba ita ta yi maganar ba,nan suka hada baki gurin cewa
"Allah ko yayi masoya"
"Nasiba ta furta
" ni kunga bari nayi sallar walhar nan nayi alwala na zauna fira"
",dadai yafi miki da kin zauna in kunji kunji"
Rufaida ta karasa maganar tana kokarin barin dakin
*"**"**********
Abba Aliyu yayi murmushi bayan ya cire wayarsa daga kunnensa ya maida kallonsa ga Ummi Hauwa'u da Abdul-Rafi da suke saurarensa suji mai zaice musu dan sunsan dai da ganin murmushin fuskarsa akwai magana mai dadi a bakinsa
"Hauwa'u kinsan dawa na gama waya,Alhaji Hashim ne yanzu ya kirani ne akan cewa wani abokin Mijin Samiha ya ga Rufaida wajen bikin yace yana sonta to yanzu dai Abba Hashim din yace ya ari bakina ya cumin albasa gurin amincewa yaron fara zuwa zance,su dan fara fahimtar juna kafin ya turo magana
Abdul-Rafi ne ya soma magana dalilin da ya sa Ummi Hauwa'u ta maida maganar da take kokarin yi sai dai murmushin farin cikin dake kan fuskarta sai kuma taji Abdul-Rafi 'din yayi wata magana
"Allah yasa nagari ne" fadin Abdul-Rafi da tunda aka fara maganar yaji ransa yafara baci da baisan dalilin fadin hakan ba"
"Wacce irin magana kake ne wai Abdul" Ummi Hauwa'u tayi maganar tana kallonsa
"Ummi addu'a nayi mata fa"
Injishi yana kokarin mikewa danko maganar ma saiyaji duk ta gundiresa
Abba Aliyu yasa baki a lokacin yana fadin
"Saboda haka ake addu'ar dama ko,kai wai maiyasa bakada wani tunani kafin kafurta abu kamar wani karamin yaro,duk fadan da akema bakaji"
"Abba kaya hakuri bada wata manufa nayi maganar ba"yana maganar yana karasawa wajen dining
" ai dama haka zakace sakarai kawai"
Ummi tayi maganar cikin bacin rai
"Abdul yana kokarin zama a kujera yaji furucin Ummi Hauwa'u yaji le'ben kasa matukar haushi kalmar Sakaran da ummin nasu takirashi dashi yaji
" Haba Hauwa me ye haka ya zaki ce masa sakarai yanzu da a gaban kannensa kika fadamasa ai rainasa zasu yi"
Abba Aliyu ya fadi haka.
"Allah Abban Abdul yaron ne baida tunani wani lokacin ko daya sai shegiyar wauta ya iya"
"To naji dukda haka kidaina cewa yaran nan haka mu riqa musu addu'a"
Da haka suka canza babin firarsu ko maganar Rufaidan busu sake bi takan taba

11AM
Ra'uf ya fito falo cikin shigarsa ta shaida Ash ruwan toka Hajiya ta dubesa da take zaune a falon itada Yakumbo da Mama da sauran yan biki da busu gama tafiya ba
"Kai mai kake nufi ne wai,badai tafiyar zakaiba,wa zaka tarar a gidan idan kaje ca nake ita kanta Hannatun sai zuwa gobe zasu koma"
"Mama tasa baki a maganar
"Keko Hajiya Hanne banda abinki saurayi kamar Ra'uf kya tanbayesa ina zashi,gida bakowa idan yaje,kika sani ko amarya muka samu a kano zashi gurinta"
Murmushi yayi yace
"Kamar ko kin sani Mama,na samo muku amarya tunda ku kun tsufa"
"Hajiya Hanne ta ha'de rai ta kallesu gami da furta
" wanne irin amarya bayan ga Karima nan ban fadama maganar ta ba tun kwanaki"
"Eh kin fadamin amma nasamu Karima da maganar tace tanada wanda takeso"
"Kodai kai ka fadamata kanada wadda kakeso ba"
"Haba Hajiya ku daina gardamar nan kibar kowa da zabinsa mana, mudaiyi musu addu'a Allah yasa Alkhairi a zabin nasu"wata saga ciki tayi maganar mai suna Habi
Shikenan Habi wallahi donke kikai maganar nan ne amma kinsan cewa Karimah bazata furta wa Ra'uf tanada wanda takeso ba,sai dai idan shi ya fadamata yanada wanda yakeso dan dama shiba dan mutunci bane uwarsa tagama lalatasa shi kuma ubansa an mallakesa,bare ya tabuka wani abun"
Ra'uf ganin bazai iya jure kalaman kakartasa ba yasashi barin falon dan indai ya cigaba da sauraron kalamanta to zai iya fadamata duk maganar da tazo bakinsa,Yakumbo da Mama suma baya suka rufowa jikan nasu da sunaji Hajiya Hanne nace musu munafukai jika dai natane ko mace tace natane to tafi iko dashi bare ma kuma harda su karere wato Mama Suwaiba murmushi sukayi da fitowarsu harabar gidan har Ra'uf ya karasa wajen da motarsu take ajiye dan da saurinsa ya fito falon Mama Suwaiba ce ta kirasa da sunan da ita dince kadai take kiransa da sunan wato Babban mutum,dan sunan babban danta garesa danko da wasu sun fadamasa to gurinta sukaji tana fadamasa suka kwakkwaya ,gurin da suke tsaye ya koma hakuri suka shiga basa akan halin Hajiya Hanne shima hakuri ya basu dan yasan sums suna matukar hakuri da ita fiye dashi namiji tunda shi koda yana kadunan ba zama yake ba a gidan idan sunzo shida Amminsa bare kuma yanzu da basa ma kasar dan Hajiya Hanne wata macace mai wuyar sha'ani halinta kwata kwata babu wani wanda za'a yaba gata da zafin kishi da son zuciya da sonkai da take gaskiya da haka sukayi sallama suka rabu cikin tunanukan rayuwa kala kala haka Mukhtar yaja motar suka bar gidan zuwa Bayajidda street gidan Ahmad suna zuwa daga kofar gidan yacewa Mukhtar ya tsaya anan,wayar Nasiba ya kira yace su fito ba jimawa suka fito harda Samiha da Ahmad inda Ahmad ke masa tsiyar yaki shigowa ciki,ko kulasa baiba shima jin hakan yasan ran mazane ya baci,da haka suka shiga motar Mukhtar ya fito yasa musu kayansu a boot ya hau yana kokarin tada motar Ra'uf yace sai sunyi waya shima a lokacin Ahmad kai ya 'daga Ra'uf ya murmusa dan ya fahimci Ahmad haushi yaji addu'a Samiha take musu da idonta ya cicciko da kwalla da Rufaida gudun kar a banbareta jikin Samiha suna kuka yasata riga kowa shiga motar tanajin sheshshekar Samiha itama ta fashe da kuka a motar a haka suka bar kofar gidan da Ra'uf ya juyo ya kalleta kallo daya ya maida kansa da kukannata baya sansa ko alamu saidai a gaban su Aunty Samira baya tunanin ya iya lallashinta saboda yanada yakinin suma zasu bata hakuri haka ko akayi su Aunty Samina ke kokarin bata hakuri da suma sunsan shaquwar Samiha da Rufaida ranar da daya zai rabu da daya Dole suyi kuka.

*LIMATU KHALILULLAH*❤️💞*JININMU 'DAYA*
BY SADIYA IBRAHIM KHALIL
Wattpad:Sadiya Ibrahim Khalil

*PAGE 25*

DAN ALLAH KUYI HAKURI KUYI MANAGE BA YAWA MORE COMMENT'S MORE TYPING


3pm suka sauka a Kano kai tsaye gidan Aunty Samina suka ajesu da take a Sharada phase 1 da sai sun huta kowacce zata tafi gida Ra'uf yace wa Rufaida su jira zaizo ya kaisu gida badan taso ba ta amince Ba jimawa da shigarsu gidan Ra'uf ya turo Mukhtar gidan Aunty Samina da lemuka da yoghurt dasu Ice cream Nasiba ce ta fito ta amsa tayi godiya ta koma ciki.

Aunty Samina ta dubi himin kayan
"Kai wannan hidima haka baya gajiya shidai kiduba Alkhairin da yayiwa su Yaya balki kuma da siyayyar da yayiwa su Khalil (wato tana nufin 'ya'yansu Khalil,Kalim)"
"Wallahi kuwa Allah yasa dai yasa ya dore har aurensu ya kuma sa ya kasance mijin nata indan shine mafi alkhairi a gareta amma gaskiya naga alamun yanada kirki"
Cewar Aunty Samira
Aunty Samina ta amshe da "Amin dai"
Itako Nasiba harta bude tafara shan ice cream dan yunwa take ji gashi taga Aunty Saminan batada niyyar cewa su dora girki itako Rufaida Kitchen ta Shiga ta dora girki don gidan Aunty Samina Ba bakonta bane Iran suka zo da Samiha bata musu iyaka da komai dan sun maida Rufaida kamar Samiha su,kuma aranta bata tunanin zata iya cin kayan dan gaskiya yunwa takeji bazasu kosar da ita ba tadaifi gane ko zata cisu sai dai da marmari

5pm Suka shirya suka fito gidan Aunty Samina ita da Aunty Samira da Nasiba da Ra'uf ya turo Mukhtar Driver ya kaisu gida,kasancewar mijin Aunty Samira baya gari a lokacin shine dalilin shiga motar ya ajeta a gidanta da take rijiyar zakin itama da sai ka fara zuwa gidansu Rufaida kafin nata
******
"Oyo oyo Yaya Rufaida munyi kewarki"
Su Rafi'a suka cacimeta suna fa'dar haka
"Nima nayi kewarku,gashi ba nida waya bare mu riqa gaisawa"
"Dama dole kiyi kewarsu gashinan harkuna angijemin dana ba"
Ummi Hauwa'u ta karasa maganar tana karasowa gurin da Ra'is yake yana kuka da yake can gefe da shima hardashi a rugowa tarar yayartasu da akayi gefe dashi
Daukarsa tayi ta'aje jakar hannunta tana"Ummi yi hakuri kinsan halin dai su Rumaisa da Rafi'a"tayi maganar tana shiga cikin falon da ta zauna kujera
"Kodai halinki ba"Ummi Hauwa'u tayi maganar itama ta nemi guri cikin kujerun falon ta zauna
Murmushi Rufaida tayi kawai ta gaisheda Ummintasu da Abbansu da shigowarsa gida kenan,Rumaisa kuma ta kinkimi jakar Rufaida tayi Upstairs(saman bene)da ita
Da murmushi Abba Aliyu ya dubeta bayan sun amsa gaisuwartata
"Wato saida kuka huta gidan Samina kukayo hanyar gida ko saida Umminku tagama girkin tarbarki kika zarce gidan Auntynku"
Dariya tayi "ni bangama Yaya Abdul 'din ba" d shine ya kira Nasiba sanda suka dawo har suke shaidamasa suna gidan Aunty Samina,
"Eh yanzu suka fita shida Abdul-Rashid Umminku ta aikesu,da naji yana zasu biya daukokuma keda Nasiba"
Sallamarsu Abdul ita ta katse maganar da Ummi ke kokarin yi
Amsa musu suka yi ya shigo falon
Abdul ya dubi Rufaida da take masa sannu da zuwa yana fa'din
"Yar rainin wayau bazan amsa miki ba,banda rainin wayau kinsan tahowa zakuyi kika samu wahala kukace zaku jira nazo daukarku saida muka je Aunty Samina tace drivern daya kawoku yadawo kaiku gida"
"Yi hakuri Yaya Abdul mun kikkiraka mu fadama bata shigaba"
Abdul yace dama mana haka zakice waye yakawoku gidan ne,Aunty Samina tana fadamin ko driven Ra'uf ko waye bandaiji sosaiba"
Rufaida tace"Eh drivern gidansu Ahmad ne mijin Samiha"
Shiru suka yi nawani lokaci
Ummi Hauwa'u ta katse shirun da cewa nasan dai kuncika cikinku gidan Samina bakya bukatar abinci yanzu"
Murmushi tayi tace" Wallahi Ummi a cike cikina yake,maikika girkamin"
Ummi Hauwa'u tace"Alala"
"Allah Ummi zanci zubomin ko dayane"
Harararta Ummi Hauwa'u tayi
"ni zan zubomiki ma lallai yarinya,nida ko tsaraba baki kawowa 'dana bama"
"Rufaida tace" Ummi kinsan banida kudi,yanzu Aunty Samira data siyawa Kalim chocolate a flyover ta bani nakawowa Ra'is tana jaka ta"
Abba Aliyu yacewa Abdul-Rafi
Kaga Abdul taho mu hau sama naga an manta damu uwa da 'ya sai fira suke ba'asamu ciki"
Rufaida tace
"Yi hakuri Abba bahaka bane"
"Kinga kyalesu Rufaida,muje dining kici abincinki"
Cewar Ummi Hauwa'u
Abdul dai baice komaiba dan har lokacin Ummi Hauwa'u bata daina fushi da shiba kan maganar da yayi akan saurayin Rufaidan,wanda shikuma a ganinsa addu'a yayi ma yar uwartasa"
Maganar Abba Aliyu ita ta katse tunanin Abdul
"Shikenan gwara ku tashi kubarmu muyi firarmu muma"
Dining Area su Ummi Hauwa'u suka koma Rufaida ta zuba alalan tafaraci suna taba firar da Ummintasu

SADIYA KHALIL*JININMU 'DAYA*
NA SADIYA IBRAHIM KHALIL
Wattpad :Sadiya Ibrahim Khalil
26
*WANNAN SHAFIN NAKI NE AISHA UMAR IBRAHIM(AUI) ALLAH YABADA SA'A YA KARA BASIRA A'I..MARUBUCIYAR ZANJIRATA ,DA NABARWA ZUCIYATA ALLAH YA BAR ZUMUNCI*

*Shafi na Ashirin da shidda 26*

Sallamar da Rufaida taji Ummi Hauwa'u tayi yasa ta aje Alqur'anin da take Karantawa kan sallayar data idar da sallar isha tayi hanzarin amsa mata ciki ummi Hauwa'u takarasa shigowa ta dubi Rufaida cikin kulawa tace
"Tilawa kike ne"tayi karasa maganar tana zama bakin gado"
"Eh Ummi"
"To Allah ya taimaka su Rumaisa sunyi sallah ko nagansu sun sauka kasa suna kallo"
"Eh Ummi sunyi tarema mukayi"
"To shikenan kizo Abbanku yana kiranki Ummi Hauwa'u takarasa maganar tana mikewa
Rufaida Alqur'an din ta dauke tasa cikin loka tabi bayan Ummin nasu

*****
Assalamu Alaikum Rufaida ta gabatar da sallamar a kofar dakin mahaifinsu saida ta jira aka amsa ta tashiga cikin dakin a zaune ta samu Ummi Hauwa'u saman Carpet da shigar ta kenan itama kusada mahaifiyar tata ta zauna tana cewa "Abba Sannu da hutawa"
Ya amsa
"Yawwa Rufaida"
Kafin yayi gyaran murya ya soma magana
"Rufaida Alhaji Hashim ya kirani yayimin maganar wani yaro kun hadu wajen bikin Samiha ya nuna yana sanki shine ya kira Alhaji Hashim ya nemar masa izinin fara zuwa fira wajenki,kuma yace daga gobe zai fara zuwa,ina fatan dai da izininki yayi maganar kuma kinasanshi kar azo yafara zuwa zance yayi karfi azo asamu Matsala dukda cewar ba a fatanta"
Murmushi tayi bata ce komaiba dan ita bata San mai zatace ba ga dokin San ganin Ra'uf da take don akwana dayan harta fara sabawa dashi saboda ya iya kalamai masu tausasa zuciya
Jin tayi shiru yasa Ummi Hauwa'u cewa
"Ai Abban Abdul ta amince tunda kaji tayi shiru"
Abba Aliyu ya girgiza kai
"A'a ki barta dai tayi magana shiru aiba amincewa kadai yake nufi ba akwai shirun da zakayi ba son abinda aka fadama kawai kake nufi ba,ki bata wayarki ta turomin message idan takoma dakinsu"
Ummi Hauwa'u tace"to amma wayar na gurin Rumaisa tana game"
"Na hanaki bawa yaran nan waya bakyaji ko wacce irin

Please Login or Register in order to submit comment