Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallamar ta zauna kujerar dake dakin guda daya da take gefen gado ta kallesa tace
" lafiya kuwa Abban Abdul"
"To da sauki dai zance" Abba Aliyu yayi maganar yana zama a saman gado"
"Meke faruwa kafadamin"Ummi Hauwa'u tayi maganar ranta a dagule"
"Abba Bukar ne yanzu yake shaidamin Ashe Ahad ya dade yanason Rufaida zuwan da sukayi ma shi Ahad dansu daidaita da Rufaidan yazo shine nake shaidamasa wani yazo yayi maganar ya biyo ta hanyar Alhj Hashim kuma na cemasa a yau din nayi niyyar sanarmasa lamarin"
Ummi Hauwa'u tace
"To shikenan tunda ka fadamasa haka" don itadai dama batason hadin
Abba Aliyu ya nisa yace
"Hauwa'u kinson Abba Bukar yayimin abinda ko iyayenmu sai haka banso hakan ta faru ba,amma tunda an amshi maganar wannan sai a jira aji abinda Allah zaiyi"
Ummi Hauwa'u ta cigaba da lallashin Abba Aliyu har yaji yasamu nutsuwa sosai

9:30pm
Rufaida da tayi shirin barci ta ji karar wayarta ta jawota jikin madubi ganin mai number din data dade da hardaceta yasata murmushi ta daga tare da da sallama ta dora da cewa
"Amarya bakya laifi ko kin kashe 'dan masu gida"ta karasa maganar da da dariyarta
Samiha da taji kirarin tayi dariya tace
Bandai kashe ba
Murmushi Rufaida tayi tace
"Aiko kin kashe Yaya Ahmad zai hakura
" tsaki Samiha taja tace"
Kinga rufani ki saya,waima ba kicemin waya baki number dinki ba"
Rufaida tace"ai nasan Yaya Ahmad ne"
"Eh shine Yaya Ra'uf ne ya turowa Ahmad yanzu,ke ban fadamiki ba gobe jirginmu zai daga UK kinsan a can Ahmad yayi karatunsa Degree to ya samu admission zai koma yayi Masters,shine zamu tafi tare"
Cikin rashin jin dadi Rufaida tace
"Yanzu shikenan Samiha zanyi rashinki har ki tafi wata uwa duniya wallahi banji dadi ba naso ya barki ya tafi shi"
"Wallahi Rufaida nima dai ganin kudinma ba gari daya muke ba yanzu saima mu shekara bamu haduba shiyasa na amince mutafi tare"
Hira suka cigaba dayi kafin suyi sallama zuciyoyinsu ba dadi.
Ra'uf ne ya kira Rufaida bayan gama wayarsu da Samiha da yayi mata saving din number din tashi da sunansa ta daga bayan ta kusa yankewa ba tare da tunanin komai ba.
Sun jima suna wayar kafin suyi sallama da kusan maganar ta Ra'uf tafi yawa
Washe gari su Ahad na gama karyawa suka shirya komawa Zariya dan garin Kanon bayawa Ahad dadi don yaci burin auren Rufaida dukda baya fidda rai amma dai yasan zuciyar Rufaida tana gun wani .

Shakuwa mai karfi ke wanzuwa tsakanin Rufaida da Ra'uf har ma yanzu manya ke niyyar shiga maganar don Ra'uf yace sai an tsaida rana zaikoma Delhi su Amminsa da Safiyya ke shirin komawa kawai da itama Ammin Rufaida ta shiga ranta sosai.

SADIYA KHALIL😊*JININMU DAYA*
NA SADIYA IBRAHIM KHALIL

SHAFI NA TALATIN
Abba Bukar dake zaune a babban falon gidansu Rufaida ya kalli Ummi yace "Hauwa'u yanzu har dake a masu 'boye min maganar kawo ku'din yarinyar nan da za'a yi yau ko?".

Ummi Hauwa'u da take kan carpet zaune tace "Yaya laifin na gurin Abban Abdul da yaron ya shaida zai kawo ku'din aure na ce a fa'da maka shi ne yake sanar min batun zuwanka a ranar da za su zo 'din".

Abba bukar ya ce "yanzu da banzo yau din ba to saidai aji kunya kenan shikadai ne zaiyi gaban kansa kenan a fara kokwanto ga 'yarmu ko vata asali irin haka Ai fada ake yanzu da kunfada nima bazanzo nikadai ba ai ko kuma ma aturasu can Zariyan"
Ummi Hauwa'u tace "adaimana afuwa
Abba Bukar yayi murmushi yace" to Allah ya kawo mana su lafiya".

"Amin yaya". Cewar Ummi Hauwa'u

Yaran ne suka shigo da 'dokinsu suka ruga gurin Abba Bukar suna cewa "oyoyo Abba".

Murmushi ya yi yana cewa Ku 'dagani kar ku 'ballani, tun da kun maida ni abokin wasanku. Hauwa'u ta koya muku wasa da ni ko?" Har dake 'katuwa dake ya nuna Rafi'a ba zaki bar Ra'is yayi ba.
Murmushi sukayi suka sauka cinyarsa suka gaishesa suka fice.

Ya dubi Ummi bayan sun fita yace "wato dai Hauwa'u kin koyawa yaron nan wasa dani ko?".

Ta ce "a'a Yaya laifin yana gurin ka".

Ya 'danyi murmushi yace ya canza zancen da cewa "ban ga Abdul..?". bai 'karasa maganar ba suka tsinkayi sallamarsu a falon.

Abdul da Rumaisa da suka shigo falo suka ha'da baki gurin fa'din "sannu da zuwa Abba".

Amsa musu ya yi da "yawwa".

Kusa da ummi suka zauna suka gaishe da Abban, da tambayar sa ya ya baro mutanan gida?.

Yace "Lafiya k'alau Abdul-Ahad ma yaso biyo ni to kuma sai ya koma gurin aiki jiya, ya banga Rufaida ba?". Ya karkare maganar da tambaya.

Rumaisa tace "tana sama".


Rufaida Da take zaune a carpet da littafi a gefenta da take yiwa Rafi'a assignment inda da ya kirata ta ajiye littafin ta dauki wayar da take kusa da ita sunan mai kiran Ra'uf ne Saida ta kusa katsewa ta daga suka gaisa


Shi kuwa yana falon 'dakinsa yana kallon TV da ya rage volume yake wayar
Ya nisa yace
" Allah Rufee na kosa naje su Dady su karaso yanzu suzo sunema min aurenki asa rana ayi komai"
Tace "haba dai yaya Ra'uf".

"Allah kuwa amma na san ba zaki fahimci 'kaunar da nake miki ba shi yasa".

Murmushi ta yi tace "ni kaina Yaya haka ne".

"Me kenan? Fa'di muji". Ya fa'di haka wanda dalili mai 'karfi kenan yake 'kara jin sonta a ransa saboda yarinya ce mai kunya Rufaida shi kuma mutum ne mai son mace mai kunya kuma wadda bata saurin furta abu koda tasan dai-dai ne sai tanemi izini.

Har da rufe fuskarta kafin tace

"ina kaunarka dan Allah har mamakin kaina na keyi".

"Rufee kenan kar kiyi mamaki da ikon Allah duk da dai nasan kurum fa'da ki kayi dan ki kwantar min da hankalin cewa kina 'kaunata da kika yi, amma na san nafi k'aunarki fiye da 'kaunar da kike min".

"Kar ka fadi haka yaya Ra'uf har cikin raina na fa'di haka".

"To Allah yasa"
Tace masa "Amin"
A haka suka cigaba da hirarsu cikin so da kauna
*****
"Abba sannu da zuwa". Rufaida da ta shigo falon ta zauna 'kasan carpet tana gaishe sa wanda yake shi ka'dai zaune a falon ya na ta'ba abincin da aka kawo masa.

Gaisawa suka yi ganin shigowar Abba Aliyu yasa Rufaida mi'kewa ta bar falon.

Bayan sun gaisa ne

Abba bukar ya dubi Abba Aliyu yace "wato Ali kai ka zama babban kanka shikenan har za'a zo neman auren Rufaida ba zaka fa'da min ba ki?".

"Yaya da naga kace min zaka zo yau kuma ya yi dai-dai da zuwan su shi yasa ban fa'da maka ba, kuma dama niyyar da nayi suje can a nemi auren a can, sai kuma ranar zuwan nasu ya yi dai-dai da naka zuwan".
Wanda zullumin abinda Abba Bukar zaiyi tunanin ganin dansama yanasan Rufaidan idan yafadamasa maganar zuwan baisan ya zai dauki zancenba yasashi kin fadamasa zuwan ganin yayi dai dai da zuwansa.
"To ba laifi yaushe ne zasu zo 'din? Dan yau nake shirin komawa gida".

"Yanzu Alhaji Hashim ya kirani yacemin Ahmad ya kirasa yace sun taho shima Alhaji Hashim din yaso zuwa aiki gaggawane ya samesa a asibiti" Abba Aliyu ya karasa maganar yana kallon fuskar Abba Bukar

*********
Ra'uf ne ya sake kiranta ta mi'ka hannu ta 'dauki wayar da ke gefen gado

Rufee su Dady sun taho suna hanya yanzu haka na fa'da musu ace 2week za'a saka ranar bikin so nake kawai mu koma india tare bayan bikin,basai na sake dawowa"
Itadai murmushi tayi batace komaiba suka cigaba da wayarsu cikin nishadi da kaunar juna

______________________

Motoci ne guda biyu suka kunno kai cikin gidan nasu Rufaida

Dady Usman da sauran mutane uku Abdul ne ya yi musu iso cikin falon bakin a kujerun falon suka zazzauna Abdul ya gaishe su sannan ya bar falon da idon Abba Abdu yanakan Abdul har yabar falon yaron yana da nutsuwa ya fada aransa haka kums yake tama Abdul din kallon sani
********

Rufaida da ta koma ta kwanta bayan ta hango motocin da suka shigo ta taga haka nan ta ji jikinta ya yi sanyi ga kuma bugun zuciyarta da ya karu, Addu'a ta soma yi kafin ta rage jin haka.

*********
Ruwan da Dady Usman ya bu'de ya zuba a kofi ya ajiye a centre table Abba Salmanu ya dube shi yace Usman nifa zan tashi dubi fa zaman da mu kayi jiran shigowar mutanan nan tsabar rashin sanin darajar 'dan adam sun'ki koda kallonmu ni shi yasa ba ko wanne neman auren ake zuwa dani ba
Dady Usman ya duba agogon hannunsa yace" YAYA mudai kara musu hakuri har yau bamuyi minti ko talatin ba fa"

Abba Suleh ne ya mi'ke yana 'ko'karin tashi su Abba suka shigo falon da sallamarsu wanda yasa Abba sulehn komawa ya zauna


Cikin firgici a fuskarsu suke kallon juna

Abba Bukar da yake kallon fuskar mutanan falon ya mi'ke rai 'bace ya soma magana tare da nu na musu 'kofar fita

"Ba zan laminci wula'kanci a gidan 'dan uwa na ba sannan da nasan kune masu Neman auren da buku wahalar da kanku zuwa ba domin dai koda 'dan ku shine ka'dai yayi saura a duniya Rufaida ba zata aure shi ba, indan har nine ma'daurin auren,haka ma indai Aliyu shine uba gareta.

Tun kafin ya kai aya a maganar suka mi'ke Abba Suleh ya fara maida martani cikin zafin rai"Ni kaina bana fata ahalina su ha'da jini da ku, koda bayan ranmu kuwa aure nina haramtasa a gare su, da a ce na san da ku 'dan 'kanina ke son ha'da auran nan da hatta wancen auren na baya kuna da ala'ka ta jini da su da bazan bari ahali na ya ha'da ji'ni da masu butulci masu muguwar sakayya irin ahalinku ba da halayyar ahalinku takesha shafar duk wanda ya hada iri daku,mayaudara

Maganganu masu zafi suke jifan junansu da shi
Da haka su Abba Suleh suka fice daga falon da gidanma baki daya vadan maganganun da suke jifan junansu dasu masu zafi sun kare ba sai dan busuga anfanin cigaba da zama a gidanba
__________________________
"Hauwa'u ban ta'ba tunanin da kanki zaki aikata haka ba, kuma daga ke har 'yar taki ku sani kamar yadda kuka turo da mijin da kuke so ta aura ba zata aure shi ba idan har da rayuwata a doron 'kasa Ahad zan aura mata kota naso ko bataso 'dan cikina kuma dan uwanta, domin ni ban manta ba idan ke kin manta" Abba Bukar yake maganar cikin bacin rai karara a fuskarsa da shigowarsa falon kenan da ko sallama ya gagarayi ya tari Ummi Hauwa'u da wa'dannan maganganun.
Rufaida da ta tsinci maganar tana 'ko'karin saukowa amsa kiran Ummi 'kafafuwanta ne suka yi mata nauyi kafin bugun zuciyarta ya tsawaita.
"ki karaso nan ke da uwarki muji wa ya kira wa'dannan mutanan zuwa ahalinmu,wadanda busu dauki dan adam a bakin komai bare suga darajarsa".
Tsintar muryar Abba Bukar da ta yi yasa ta 'karasowa falon ta tsugunna gabansa tana mai da kallonta 'kasa wanda take jin tsananin ciwan kai lokaci guda ya saukar mata.

"Kin bani mamaki da har kika biyewa wannan mara sanin mutuncin kanta bare musa ran ko zata san tamu ya nuna Ummi " Kuma ki sani indan kinyi hakan saboda tunaninki mun manta da wancen al'amarin to kin makara ki domin zuriyar Tafida bata canza daga ra'ayintaba har ya'u duk wanda yaketa mutuncin zuriyarmu babu sauran mutunci da zai sake samu a zuriyarmu kuma kiyi gaggawar canza shiri domin koda yaron nan shine ka'dai namiji to baza ta aure shi ba, sai ku sake ha'da wani 'kullin kuma,sannan ki kuka da kanki"
ya karasa maganar yana nuna Ummi Hauwa'u da ya tsa.
Abdul da ya tarar da zancen bai tsaya saurare ba ya bar gurin, dan shi ba ko wacce magana yake son ji ba,bare shida tun fil-azal Ra'uf bai kwanta masa a raiba
"Yaya bukar bani da masaniya a kan Ra'uf ban ta'ba ganin shi ba" cewar Ummi Hauwa'u
"Dakata banason sake jin maganar ki amma ki sani ahalinmu ba zasu hada aure da wannan kaskantaccen ahalinba idan da kaddara ta hadamu dasu to yanzu bazan laminta ba matukar ina raye zuriyar Tafida ba zata hada iri da ahalin 'Danbatta ba masu son zuciya da tauye gaskiya ta ko ina akwai banbanci a tsakaninmu"
Ummi Hauwa'u da take jin kalaman har cikin kwanyar kanta falon ta bari tana zubda hawaye batasan maiyasa ake ta allaka haduwar Rufaida da Ra'uf tanada masaniya ba.
Rufaida ma bayanta tabi.
Abba Bukar ya cigaba da fadansa
_______________________

Ra'uf da ke falo zaune shi da Momy Hannatu da ya zuba tagumi da hannu biyu , Momy ce ta kalle sa ta ce "lafiya kuwa, Ra'uf?".

"Momy zuciyata ce naji duk bata min 'dadi, gashi bugun zuciyar yana 'karuwa".

"Ka ri'ka addu'a insha Allah zai ragu, kuma zaka ji komai yazo da sau'ki".

"To momy, yauwa Ammi ta ce cikin satin nan zata koma".

"Eh ta fa'damin jiya a waya".

Abba Sule da bai jira ya 'karasa rufe murfin motarsa ba ya fito ransa a matu'kar bace, Dady Usman da Abba Salmanu da Abba Abdu suna kiran sa amma ko saurarensu bai yi ba ya 'kara sa 'kofar falon ya bu'de ta da karfinsa.

SADIYA KHALIL😊🖊️*JININMU DAYA*
NA SADIYA IBRAHIM KHALIL
SHAFINA 31
Momy Hannatu ta maida dubanta ga Abba Sule wadda take 'ko'karin canza tasha da remote a hannunta, shi kuma Ra'uf yana kwance kan doguwar kujera.

Magana ya fara cikin 'daga murya
"Wato kai Ra'uf har akwai ranar da kai da kanka zaka nemi wula'kanta mu to wallahi in dai har ka kafe da auran yarinyar nan sai dai mu raba hanya da kai kuma hatta mahaifi a gare ka sai dai ku raba hanya da shi, ko da zaka mutu babu aure haka ko da ita ta yi saura a mata a duniya ba zaka aure ta ba".

Su Dady da suke bayansa tsaye suka furta da mun san irin wula'kancin da zamu riska kenan da ba mu yi 'ko'karin zuwa ba, Momy da take 'kokarin furta wani abu, Abba bukar ya dakatar da ita ta hanyar cewa "dakata Hindatu ba na son maganar ki".

Ra'uf ba tare da ya furtawa kowa komai ba ya bar falon inda kansa ya yi masa nauyi, da wayarsa ya ci karo a 'dakinsa a centre table 'din falonsa wayar ya 'dauka ya shiga kiran Rufaida

Rufaida da ta shigo 'dakinsu gado kawai ta fa'da tana kuka, karar wayar ta da taji ne ya sata mi'ka hannu domin nemo inda take wadda kafin ta hango ta kan drower gefen gado har ta katse ta na dauka kira a kalla goma ta gani da duk dai number 'din Ra'uf ce da ta ganesa da sunan data sa masa YAYA RA'UF, Wani kiran nasa ne ya 'kara shigowa bata tsaya 'bata lokaci ba ta 'dauka muryarsa taji cikin 'bacin rai amma duk da haka yadda yake maganar sa babu hargowa haka yake yin ta a tsanake yace

"Rufaida ban ta'ba tunanin ahalina sun cancanci tozartawa a gurin ahalinki ba, sannan ba zan gushe ba face ina miki fatan samuwar rayuwa mai inganci a rayuwar ki ta nan gaba bai saurari wani abu da zata ce ba ya kashe wayarsa gaba 'daya ma duk da ya san Rufaida ba zata kira saba hasali ma yadda ya fahimta ita ba mai damuwa bace da son su ri'ka waya sosai dan sai yace tun da suka fara waya sau 'daya ta kira sa shima Ra'is ne ya dameta ta kira shi su gaisa, yana ajiye wayar sai a sannan hawaye masu zafi suka zubo masa, domin ya san zai yi wuya ya 'kara samun mace kamar Rufaida nutsatstsiya mai sanin ya kamata mai kawaici, tabbas iyayensu basu zamo masu kyautuwa a karon farko a gare shi ba, hawayen nasa ne suka ci gaba da zubowa, daga bisani ya mi'ke ya shiga ban'daki ya 'dauro alwala ya fara nafilfilo da kai kukansa ga mahaliccinmu da neman tuba izuwa ga Allah. Yana idarwa kuma ya fara azkar kafin ya 'dauki alqur'an ya ci gaba da karantawa a hankali yaji damuwarsa tana raguwa, Sai dai kuma garin kano ta masa zafi ba zai iya kwana a cikinta ba a yau , Mukhtar driver ya kira bayan ya shirya kayansa ya zo ya 'dauka yasa a boot, dakin Momy Hannatu kai tsaye Ra'uf ya nufa ya 'kwan'kwasa mata, Ta basa izinin shiga da take a falonta ta zuba ta gumi da alama ita ma tana cikin damuwa, a kujerar dake kusa da Momy ya zauna ya dubi Momy ya na cewa
"Momy dan Allah kada damuwar rabuwa ta da Rufaida ta dame ki Allah ne ya ha'damu dama, yanzu kuma Allah bai sa dama zamu yi rayuwa mai tsawo da ita ba, Amma Momy Kano ta yi min zafi haka ma Nigeria na yanke shawarar zan bi Ammi jibi mu koma Delhi tare".

"Haka ne Ra'uf Allah ya yi maka albarka, Amma ba na son ka tafi domin shi kansa Dady ba zai so haka ba bare kuma ni"

"Amin Momy, sai dai tafiyar tawa itace zata sa na manta da komai in dai Allah ya so na manta 'din dan Allah Momy ki barni na tafi".

Ba dan ta so ba ta amince da tafiyar tasa

Har mota ta raka sa ita da Husna da take magiyar kar ya tafi kallon Husna ya yi yace "banda abin Husna ai kema Dady zai kawoki Delhi idan jarabawarku ta fito".

Motar su ce ta bar gidan

Inda Momy ke hawayen rabuwa da Ra'uf 'dan 'yar uwa a gare ta ba tare da ya cika burinsa ba na auren Rufaida, Da take ganin ina ita 'din da namiji ce kuma tana da iko akan aurawa Ra'uf Rufaida da sai ta yi 'ko'karin aura masa Rufaida.

"Mukhtar ka yi kwana ina so naje Danbatta yi wa Yakumbo sallama". Ra'uf ya ce haka da sai yanzu ya tuna al'kawarin da ya yi wa Yakumbo cewa zai je mata sallama idan zai koma.

SADIYA KHALIL🖊️😊*JININMU 'DAYA*
NA SADIYA IBRAHIM KHALIL
Wattpad Sadiya Ibrahim Khalil
SHAFI NA TALATIN DA BIYU 32

KUYI HAKURI MASOYAN LITTAFIN JININMU DAYA BAZAKU RIKA SAMUN TYPING DINA KO YAUSHE BA,SANNAN A WATTPAD BAN FARA UPDATING BA ANA UKU NAKE A WATTPAD MASU SO DAGA FARKO SU RIKA DUBAWA ACAN.IDAN SUNAYI SABODA ANAMIN MAGANA BANASAMUN DAMAR TUROWA.

Minti na da basu wuce arba'in ta sada su da garin Danbatta a, a kofar wani gida suka yi parking 'din motarsu gidan siminti ne sai dai babu shafe a kofar gidan Yara ne suka baibaye motar domin suga mai fitowa a ciki Ra'uf ne ya fito da gudu yaran da suka san shi mata da maza suka baibaye shi suna masa oyoyo, Hannun yaron ya rike suka isa kofar cikin gidan da gidan yake 'bangare uku 'bangaren yakumbo ne farko said 'bangaren kawu sunusi da na kawu Lami'do gidajen ginin zamani ne bangaren Yakumbo ya nufa kai tsaye sai da ya 'kwan'kwasa mata 'kofarta ta 'karaso 'kofar tana fa'din ince dai wannan yaron ba ne Salmanu ta'karasa maganar ta na bu'de 'kofa, Ganin Ra'uf ya sata saurin matsawa ta basa hanya ya shigo ciki cikin 'dakuna ne guda uku a biranda sai kuma kitchen da 'bandak a daga gefe da kuma 'karamin 'daki

Cikin fara'a take cewa"lale marhabin da babban ba'ko, a garin Danbatta" Tana ko'karin shinfi'damasa tabarma a saman tiles 'din dake barandar gidan da take share, Tsaftar yakumbo tana birge Ra'uf dan shi dama mutum ne mai son tsafta

Zama yayi yana cewa"Yawwa Yakumbo sarkin tsaftar garin Danbatta"

"Kai rufamin asiri ina ni ina zama mai tsaftar Danbatta gaba 'daya , Ko ka 'dauka 'kan'kantarta kamar garin jajayen fatar nan ne

" A'a Yakumbo Allah Delhi ta lin'ka Danbatta sau million ma"

"kada fa karaina Danbatta dan nanne dai asalinka ko ka'ki ko kaso"

"Eh haka ne , Amma kuma gaskiya na fa'da ta lin'ka Danbatta sau 'dari ko fiye da haka,Kuma Allah Yakumbon mu mai tsaftace "

"Ahaf ka dai fa'di gaskiyya da kace ta linka Danbatta sau million To ai yaro tsafta cikon Addini ce, Allah yasa dai Matar taka mai tsafta ce, Ba irin yaron yanzu ba masu 'dan karon son jiki, Dai dai da abinci ma 'danye suke yin shi, Bare a saran shara da wanke wanke"

Bai ce komai ba har yaron da suke shigo da kayan tsarabar da ya tsaya a hanya suka siya da Mukhtar su kashigo da ita , Mukhtar ya na ta yasu, Tsarabar ya bawa yaran suka fice da murnarsu suka nufi gida suna nunawa

Sai a sannan suka gaisa da Yakumbo
Yake tanbayarta ina Baffa

"Tun safe ya tafi gona shida kawunka sai zuwa ya manyar nan muke saran dawowar su"

"Allah ya dawo dasu lafiya , Amma ya kama ta Baba ya daina zuwa gona Amma har yau ya'ki ha'kura"
"Amin , Kai kajini da yaro idan baya motsa jikinsa wacce lafiya zaiyi jini baya yawo yadda ya kama ta"

Mukhtar da ke gefe zaune kusa da Ra'uf dariya yayi

Ya gaishe da Yakumbo yana cewa, "Kwarai kuwa yakumbo kin fa'di gaskiyya

"Ra'uf yace sai kaje kai ta zuga su"

Ruwan hannunsa ya a jiye yana kallon Mukhtar da ke gefen sa saman tabarma yace "Yakumbo bari muje muyi sallar la'asar naga a nata shiga masallaci"

"A dawo lafiya "

A 'kofar fita gidan suka ci karo da Kawu Lami'do 'kanin mahaifiyarsa, Har 'kasa su ka durkusa gurin gaishe sa, Ya amsa musu cikin sakin fuska "yana cewa a'a Ku tashi",

Bayan sun fito gidan Lami'do ya kalli Ra'uf da shima ya fito tafiya masallaci yana cewa "wata saban gani gani yaushe rabanka da zuwa Danbatta sai nace anyi shekara biyu ko anfi haka ma"

"A'a kawu shekara biyu kenan"

"A fa'dar ka ba", Mukhtar shekara nawa raban Ra'uf da zuwa"

Mukhtar yace"Kawu shekara biyu kenan"

"Wato kaima ka biye ta tashi kenan, Dan kaima kaga ba zuwa ka ke ba"

Da haka suka shiga cikin masallacin da baida nisa da gidan

Ra'uf ne ya hangi su Baffa da suke fito wa daga masallaci da fatanya a rataye a kafa'darsu, Saurin 'karasawa gurin su yayi kafin su Mukhtar su 'karasa fitowa gaishe su, cikin ha'din baki suka amsa, Inda Baffa yace

"A'a wa nake gani kamar Abdul-Ra'ufu , Sunusi dubamin shi nagani, Baffa ya fa'di haka"

"Kwarai kuwa nine babu ko kwanto Baffa"

Baffan yace "yaushe Raban duniya da aiya raye", su Kawu Lami'do na 'karasowa, Suka gaisa da Mukhtar su ka shiga cikin gidan"

'Bangaren Baffa suka shiga Fa'da suka sameta ta nayi da yaran da suka shigo 'bangarenta tana cewa su fita karsu 'batama ta gida su koma suyi wasan gurin iyayensu, Ba za'a turo mata su ba su 'bata mata gida ba iyayensu sun gyara nasu gurin, Su ko sunyi shiru suna cigaba da wasa, Da 'kara ta bisu 'kofar 'Bangaren nata inda yayi dai-dai da shigowar su Ra'uf 'din bayan su suka 'boye kada ta dokesu, Karan tayar ta koma ciki, Da yaran suka shigo Baffa da kawu Lami'do suka ajiye fatanyar a biranda, suka shiga falo suka zazzauna, Ra'uf ya kalli yaran da suke zaune kusa da shi da suke su hu'du, mata biyu maza biyu, Yace musu ku Kyale yakumbo idan na sake dawowa tare zamu tafi na maida ku gurin Ammi, Tsalle suka farayi inda Yakumbo ta shigo musu da abinci ta samesu suna tsallen murna tsaki tayi musu tace
"Wannan 'kauyawan za'a kai birni"

"Kwarai kuwa Yakumbo tunda Ammi bata da 'kananun yara ga shi ba kya barinsu suyi wasa a bangarenki"

"Ahaf ai wa'dannan yaron idan ka kaisu wannan 'kasar sai ka kirani ka fa'damin 'barnarsu kuwa"
"Ai yakumbo mun daina ki tambayi su umman mu kiji" yaran suka ha'da baki gurin cewa haka

Kawu Lami'do yace wato su salmanu ana son tafiya birnin india, ya fa'da yana dariya

Abinci suka ci Kafin ya fito su shiga zaga dangi da yawanci suna zaune a kauyen kunya kauyen Danbattan da yake yawanci kauyeb Fulani ne duk inda yaje da irin alkhairun da yake musu da yara ke raka shi a motar sa


Yakumbo ce ta kallesa da ta shigo ta zauna a falo inda Ra'uf da Baffa suke ciki Ra'uf ta duba tace "a lallai Ra'uf yau ansha yawo"

"Wallahi ko Yakumbo ai yau na zaga gari ji nake kamar duka kunya da Danbatta danginmune"

"Baffa yace kai Ra'uf Danbatta fa ba 'kauye bace mai gida nan sai kayi gaba ka tarar da wani,dama kunyan kace saina yadda

"Kyalesa dai baffa ni narasa maiyasa yaran nan suka raina Danbatta, Har da fa yaron nan Bello"
"A'a Yakumbo Allah ba mu raina Danbatta ba"

Hira suka cigaba dayi inda Baffa ya kallesa

Please Login or Register in order to submit comment