Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 3
taimakeni tun a iokacin da na Fara yin wannan gasa ta kambun jarumta?" Koda jin wannan tambaya sai Sarki Taryan ya gyada kansa kuma ya juyo yana mai duban Imhal cikin murmushi ya ce, "Dukkanin Jarumi na kwarai yana samnun nasara akan dukkan abin da ya sa a gabansa. Babu abin da zai gagareka muddin za ka zage dantsenka ka yi iya kokarinka. Ina kara tunatar da kai ka ci gaba da mai DAKAKKIYAR ZUCIYA wadda ba ta san tsoro ko fargaba ba, zamoWa Idan ka yi hakan za ka fita daga cikin kowanne irin hadari, kuma za ka sami nasara a bisa dukkan abin da ka sa a gabanka. Shawara ta biyu, ko in ce ta karshe wacce zan baka ita ce, ka ja Jarumi Salmanu a jikinka, kuma ka shawarwarinsa". Gama fadin hakan ke da wuya sai Sarki Taryan ya juya ya fice daga cikin dakin gaba daya ya barsu su biyu kacal shi da Jarurni Salmar u. Koda fitar Sarki Taryan sai Jarumi Salmanu ya mike ya karaso daf! da Imhal ya zauna sannan ya dafa kafadarsa suka fuskanci juna sosai ya ce, "Ya kai Abokina ka kwantar da hankalinka, domin na fuskanci cewar zuciyarka akwai imani da adalci. In da ace ma ka yi imani da abin da na y imani da shi da babu wani abu da za ka yi shakkarsa". Cikin marmaki Jarumi Imhal ya dubi Jarumi Salmanu ya ce, "Mene ne abin da ka yi imani da shi?" Jarurni Salmanu yai gyaran murya Sannan ya sake duban Jarumi Imhal cikin Nutsuwa ya ce, "Ni na yi imani da Allah, wanda Shi ne Sarki guda daya abin bauta. Shi ne wanda ya halicci sammai da Kassai da duk abubuwan da ke cikinsu. Kuma Shi ne Ya halicci Mutum da Aljan ba don komai ba sai domin su bauta maSa," Koda Jarumi Salmanu yazo nan a zancensa sai jikin Jarumi Imhal ya yi sanyi kuma ya kurawa Jarumi Salmanu idanu. Daga can ya kau da kansa ga barin kallon Salamanu tare da yin murmushi ya ce, "Sai yanzu na tuno da inda muka taba haduwa ni da kai". Caraf! Sai Salmanu ya tari numfashinsa yana murmushi ya ce, "A dajin Birninku muka taba haduwa a lokacin ina gabatar da Addinina, kai da wani tsoho ku ka zo za ku gifa ta gabana'" Koda jin haka sai Imhal ya maidawa Salmanu martanin murmushin da ya yi masa ya ce, "Tabbas an yi haka. To wai shin wane irin Addini ne wannan na ga kana yi, kuma me ka ke bautawa?" Sitmanu ya ce, "Ai na gaya maka, Allah na ke bautawa, Ubangijin da bai haifa ba, kurma ba a haifeShi ba. Sannan kuma sunan Addinin nawa ADDININ MUSULUNCI. Addini ne wanda ya zo da adalci, kuma Vasa gaskiya ta kori karya. Addini ne wanda ba ruwansa da matsayi ko nasaba, Talaka da Attajiri da Basarake babu wanda ya fi wani face wanda ya fi tsoron Aliah". Sa'adda Jarumi Salrmanu ya zo nan a zancensa sai Jarumi Imhal ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ya kai wannan Jarumi, ka yi sani cewa ni rainon da na taso a cikinsa ba a taba nuna mini wani abu mai kama da Addini ba, kuma ba a taba kOyar da ni tsafi ba, kuma ko a cikin zuciyata ban ji na yi imani da su ba, anrna yanzu da naji ka yi mini bayanin wannan Addini sai na ji alamun cewa zai iya zama shi ne na gaskiya. Yanzu wacce hujja za ka iya zuwar mini da ita wacce za ta sa na kara gamsuwa cewa lallai wannan Addini shi ne Addinin gaskiya?" Koda jin wannan batu sai Salmanu ya yi murmushi a karo na biyu ya ce, "Hujjar da zan baka yanzu mai sauki ce. Wannan rauni da Sarki Gurzalu ya yi maka a ciki, rauni ne wanda ba zai warke ba a cikin wata biyu ba ma, amma sabo da na yi maka addu'o'i na roki Ubangijina akan Ya baka lafiya gashi har ka iya taka kafafunka. Kuma da izinin Ubangijina nan da sati biyu ma kacal! za ka warke gaba daya". Koda jin haka sai Jarumi Inmhal ya sake cika da mamaki, ya ce, "Y anzu kana nufin ka ce nan da sati biyu kacal Ubangijinka zai iya warkar da ni?" AA Misau ke Magana Salmanu ya ce, "Kwarai kuwa, ko shakka bana yi. Sarki Gurzalu kuwa da ya sami irin wannan rauri naka, ina mai tabbatar maka da cewa sai ya shafe wata uku cur! A kwance yana jinya. Shin yanzu idan ka sami lafiya ka warke sumul! Nan da cikar sati biyu za ka yi imani da Ubangijina?" Jarumi Imhal ya num fasa ya ce, "Ko darr ba zan yi ba zan karbi wannan adduni naka mai daraja matukar hakan ta kasance". Koda jin wannan batu sai farinciki ya mamaye Jarumi Salmanu, sake duban Imhal ya ce, "Tabbas zaton da nake yi maka na alheri yana daf! da tabbata. Idan ba za ka damu ba zan so ka bani takaitaccen tarihin rayuwarka kafin ka ji nawa". Ba tare da 6ata wani lokaci ba sai Jarumi Imhal ya kwashe labarinsa tsaf! tun daga lokacin da aka raineshi a cikin daji yana yaro karami kawo izuwa lokacin da Sarki Gurzalu ya turo Dakarunsa domin hallakasu shi da Tsoho kawo izuwa lokacin da aka kamashi aka kaishi Kurkukun RIJIYA GABA DUBU, da yadda ya sami damar guduwa aka sake kamoshi aka tafi da shi izuwa Birnin Kisra domin halartar gasar jarumtaka. Su Koda Jarumi Imhal ya zo karshen labarinsa sai Jarumi Salmanu ya kamu da tsananin tausayinsa har kwallah ta ciko idanunsa ya ce, "Ya kai Abokina hakika rayuwarka abar tausayi ce, kuma abin da na fahimta a cikin labarinka duk yadda aka yi kai ba jaramin mutum bane , lailai ka fito daga babban gida. Ka ci gaba da hakuri da sannu za ka san ko kai waye." Imhal ya girgiza kai gami da dafa kafadun Salmanu ya ce, "Na gode da kyau ya kai Abokina bisa nuna tausayinka a gareni. kuma ina dada godiya bisa kara min karfin guiwata da ka yi. Haka kuma ina mai sanar da cewa ko da wannan rauni nawa bai warke ba zan kar6j Addininka, sabo da tun a yanzu ma na fara ji a jikina cowar lallai wannan Addini naka Addinin gaskiya ne" Tafiya Fa Ta Fara Nisa AA Misau ke magana SHIIN JARUMI IMIIAL YANA KARBAR ADDININ MUSULUNCI? ME ZI FARU IDAN SARKI GUZALU YA KARASA BIRNINSA YA SIIIGA DAKIN TSAFINSA? YAUSIIE ZAI SAMU LAFIYA HAR YA DA WO YA CI GABA DA GASAR KAMBUN JARUMTA? YA YA MAKOMAR SOYAYYAR GIMBIYA SIIUMAIRA DA LAMRITA GA JARUMI IMIIAL? MAL ZMI FARU TSAKANIN BAKIN JARUMAI UKU DA SUKA BAYYANA DOMIN YIN GASAR JARUMTA? YAUSHIE JARUMI IMIIAL ZAI SAN ASALINSA? YAUSIIE ZA A YI HADUWAR KARSIIE TSAKANIN SARKI GUZALU DA JARUMI IMHAL? IDAN SU YI HADUWAR KARSHIE WAYE ZAI SAMU NASARAR HALLAKAR DAN UWANSA DA KAMBUN? Mu hadu a littafin RIJIYA GABA DUBU (8) kashi na takwas, don jin ci gaban wannan kasaitaccen kayataccen labari. Daga mai đebe muku kewa a kullum da ko yaushe . Sarkin Marubuta Litattalan Yaki ABDUL'AZIZ SANI M/GINI Typing AA Misau ke Magana Ku bibiyemu a shafukan nan Dandalin Litattafan Yaki By Al'ameen Ahmed Misau DANDALIN LITATTAFAN YAKI BY REAL AA MISAU An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3