Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 3
cikin dakin Nasa. Sai da Jarumi Salmanu ya yi sallar issha kurma ya kammala 'yan addu'o'insa sannan ya fito daga cikin dakin nasa. Da fitowarsa cikin harabar gidan sai ya hango Gimbiya Lamrita zaune a can nesa AA Misau ke Magana kadan kusa da bakin wani karamin Lambu mai dauke da 'yan shuke-shuke. Cikin nutsuwa Salmanu ya karasa inda Lamrita take ya zauna da a kalla tazarar taku uku sannan ya numfasa ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki me ki ke dauke da shi a cikin ranki wanda ki ke son ki bayyana mini?" Sa'adda Lamrita taji wannan tarnbaya sai ta yi gyaran murya sannan ta ce, "Da farko dai ina son na baka shawara ne akan wannan gasa da ka shiga ta kambun jarumtaka. Ina son ka sani cewa yanzu ne fa za ka sami makiya irin wadanda za subi kowacce irin hanya don ganin sun sami nasara akanka, kuma su ga bayanka. Ba komai ne zai janyo hakan ba face yanzu ne wannan gasa za ta kara tsamari da tsawo tunda jaruman Gasar sun yi RAGAS, wato Sarki Gurzalu da Jarumi Imhal, kuma sun kwanta jinya. Babbar matsalar ita ce, yanzu bamu san hukuncin da AIkalan gasar za su yanke ba. Shin an kori gasar su Sarki Gurzalu ke nan ko kuwa za a basu dama ne har su gama jinyarsu su ci gaba da wasan?" Koda jin wannan batu sai Salmanu ya yi murmushi ya ce, "Damgane da batun sababbin makiya da zan yi a cikin wannan gasa, ko kadan bana tsoronsu sabo da na dogara da Ubangijina, kuma na san cewa Zai kareni daga dukkan sharrinsu. Abin da ban gane ba shi ne, dangane da matsayin su Jarumi Imhal a cikin gasar, kuma kamata ya yi ace mun yiwa Sarki Taryan wannan tambaya. Abin da na ke so da ke shi ne, ki ci gaba da zama a kan matsayinki na Shugabata wadda ta kawoni wannan gari, tunda dai babu wanda ya san sirrinki face Sarki Taryan. Abu daya da na ke zargin zai iya faruwa shi ne, Jarumi imhal zai riga Sarki Gurzalu samun lafiya, kuma ko yaushe zai iya mikewa ya ci gaba da yin wannan gasa. Ko ma dai menene zai faru yanzu bamu da abin yi face sa ido da jiran lokaci". Gama fadin hakan ke da wuya sai Jarumi Salmanu mike tsaye ya tafi izuwa dakin da aka yi masa masauki ya shige izuwa ciki ya turo kofa ya rufe ya bar Gimbiya Lamrita zaune a wajen tana tunani. Sai da ta shafe 'yan dakiku a cilkin wannan hali sannan ilama ta mike ta nufi dakin nata ta shige tare da turo kofa. SARKI GURZALU na zaune akan gado Kuyangi biyu na tallafe da bayansa, daya kuma na zaune a gabansa tana bashi ruwan Magani a cikin wani jan Kofi na zinare, sai ga wani hadimi nasa ya shigo. Hadimin ya zube kasa cikin biyayya kansa na sunkuye ya ce, "Y ashugabana Sarki Taryan ne ya zo domin ya dubaka" Koda jin wannan batu sai fuskar Sarki Gurzalu a fadada da murmushi ya ce, "Ma za a bude masa kofa ya shigo". Nan take Hadimin ya mike tsaye ya juya ya fice. Jim kadan sai gashi ya dawo Sarki Taryan na biye da shi. A wannan lokaci Kuyangin sun kwantar da Sarki Gurzalu akan gadon suna dan gyara masa shimfidarsa. Koda shigowar Sarki Taryan cikin Turakar sai Kuyangin suka fice da sauri. Sarki Taryan ya Karasa daf da Gadon ya zauna a gele ya Rurawa Sarki Gurzalu idanu cikin alamun tausayawa ya yi masa sannu sannan ya ce, "Ya kai Abokina, yanzu me ka yankewa kanka hukunci akan wannan gasa? AA Misau ke Magana Sa'adda Sarki Gurzalu yaji wannan tambaya sai ya yi murmushi mai nuna rashin gazawa ya ce, "Likitana ya gaya mini cewa a Kalla sai na shafe wala uku a kwance ina jinya sannan zan sami karfin jikina. Abin da na ke so yanzu shi ne, nan da cikar sati biyu zuwa uku zan koma Birnina domin ba zan iya yin jinyar wata uku anan ba, amma lallai bayan na warke zan dawo domin na yi gumurzun karfe da Jarumi Imhal. Ina so ka sa aci gaba da wannan gasa har izuwa tsawon wannan lokaci, kuma ko bana nan ka aika mini da sakamnakon gumurzun wannan bakon Jarumi da Imhal. " Sa'adda Sarki Gurzalu ya zo nan a zancensa sai Sarki Taryan ya bushe da dariya ya ce, "Ai babu wata dama da za ta sa Jarumi Imhal da wannan bako su hadu a filin gasa facc bayan kai da Imhal kun sake kafsawa wanda ya yi nasara cikinku shi ne zai kafsa da bakon Jarumi, domin haka dokar wasan take". Koda jin wannan batu sai Sarki Gurzalu va kamu da matukar farinciki ya yi wani sannan ya ce. guntun murmushi na murna "Ashe ke nan dai burina zai cika akan Imhal" Da jin haka sai Sarki Taryan ya sake bushewa da dariya a karo na biyu ya ce, "Ya kai Abokina, yanzu kana nufin kace nan da cikar kwanaki goma sha hudu ko ashirin da daya manzon da ka tura izuwa Birninka domin ya gano maka labarin yarka Gimbiya Lamrita ya dawo ke nan, kuma a sannan ne za ka dauki matakan da ya kamata ka dauka akanta?" Koda jin wannan tambaya sai Sarki Gurzalu ya kadu ainun, kuma ya kamu da Tsananin mamaki bisa yadda aka yi Sarki Taryan ya san wannan al'amari nasa wanda ya shirya a sirrance ba tare da wani ya gani ko ya ji ba. Kawai sai Sarki Gurzalu ya yunkura cikin matukar karfin hali duk da cewa yana jin tsananin zogi da radadin ciwon da ke jikinsa, take ya dubi Sarki Taryan ya bushe da dariya, lokaci guda kuma ya turbune fuska ce. "ya kai Abokina ka yi sani cewa zai fi kyau mu daina sa ido akan junanmu, domin kowa ya gabatar da lamarinsa yadda ya ke so. Kamar yadda ka tura Dakarunka a boye cikin 6atar da kama suka duba gawar yata don su tabbatar da cewar ta mutu da kuma yadda a yau din nan ka bi bayan bakon Jarumi da Gimbiya Lamrita domin ka karbo Jarumi Imhal a hannunsu babu abin da ban gani ba a jikin bangon dakin nan da iarfin sihirin tsafi. Ka ga ke nan bana bukatar dawowar đan aikena daga Birnina na san cewa 'yata tana nan cikin Birninka tare da Jarumi Salmanu, kuma na san cewa a duniya yanzu babu abin da ta sana sama da ni, domin ta sami labarin yadda aka yi na hau kan Karagar Mulki bayan na kashe dan uwana MahaifinJarumi Imhal. Ni kuma AA Misau Anan nace Musu su duka Da Sarki Guzalu din da Taryan KIFI NA GANINKA MAI JAR KOMA hhhh Zamu dakata anan saikuma wani lokaci zamu cigaba insha Allah Admin AA Misau ke Magana WhatsApp group https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q Facebook page https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295RIJIYA GABA DUBU💕 Littafi Na Bakwai (7)🩸 Part C 💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing By AA Misau ✍️⭐⭐⭐ (Kucigaba da yi mana likes and comments domin samunsu akan lokaci) Labari ya isowa Shagala cewa Marubucin yaci gaba da cewa.... Mulki bayan na kashe dan uwana Mahaifin Jarumi Imhal. Na sani cewa ba zan hadu da 'yata ba domin a yau din nan zan bar Birninka na tafi izuwa nawa Birnin. Sakon da za ka gayawa 'yata shi ne, cikin biyu ta zabi đaya, ko dai ta hakura da Jarumi Imhal ta zabeni ko kuma ita da Jarumi Imhal din su rasa rayuwarsu gaba daya. Sannan kaima jan kunnen da zan yi maka guda daya ne; Kamar yadda na kawo maka Jarumi Imbal da hannuna na sa ka tsareshi a cikin gidan sarautarka to ka bani kayana na tafi da shi ko kuma ka aika mini da shi bayan ya sami lafiyar jikinsa, domin na mayar da shi cikin Kurkukuna mai đauke da masifafliyar RIJIYAR nan ta GABA DUBU! Ba zan fito da shi ba har sai a ranar da nima na warke sosai sannan mu dawo kasarka mu yi gumurzun jarshe ni da shi na KAMBUN JARUMTA. Idan kuma kana ganin cewa za ka ci amanata ko za ka yaudareni ko kuma za ka iya cutar da ni to mu zuba mu gani! Kai kanka ka san cewa ni da kai KAR TA SAN KAR ne!" Koda gama fadin hakan sai Sarki Gurzalu ya koma ya kwanta akan Gadon ya juyar da fuskarsa can gefe đaya. Sarki Taryan ya mike tsaye yana kyalkyala dariya amma mai dauke da yake sabo da tsananin mamakin jin abin da bai taba zato ba. Cikin jin izza da yarda da kai ya dubi Sarki Gurzalu ya ce, "Ya kai Abokina, ka yi sani cewa kai Sarki ne, kuma nima Sarki ne babu yadda za a yi na so wani abu wanda zai kawo karyewarka ko hallakarka. Abin da na ke so kawai na shaida maka shi ne kowanne mutum yana iya yin kuskure a rayuwarsa, kuskuren da zai yi nadamarsa har izuwa ranar karshe ta rayuwarsa. Kuskurenka guda daya ne rak! a rayuwa da ka aikata, abin da ya janyo rugujewar soyayyar da ke tsakaninka da yarka. Babbar matsalar kuma ita ce, babu yadda za ka iya gyara wannan kuskure, kuma dole ne a karshe a cikin mutum biyun nan ka kashe daya. Ko dai ka kashe 'yarka, ko kuma ka kashe Jarumi Imhal, amma ka sani cewa kashe kowanne daga cikinsu matsala ne. Idan ka kashe Imhal tamkar ka kara rura wutare kiyayya ne tsakaninka da yarka, idan kuma ka kashe 'yarka shi ke nan baka da sauran ya magaji a duniya. A matsayina na tsohon Abokinka, shawara daya zan baka, ka gana da Jarumi Imhal a sirrance ka sanar da shi cewa kaine ka kashe Mahaifinsa da Mahaifiyarsa da zuri'arta gaba daya, kuma ya yi kokarin daukar fansa akanka idan zai iya, amma kana neman alfarma guda daya a wajensa. Alfarmar kuwa ita ce duk yadda zai yi ya tankwara Lamrita ta janye gabar da take yi ma ka, don kada ta mutu kokai ka mutu da bakin cikinta. A karshe ina mai tabbatar maka da cewa zan rike amanarka na dawo maka da Jarumi Imhal kamar yadda ka bukata, amma ka iya takunka". Koda Sarki Taryan yazo nan a zancensa sai Sarki Gurzalu ya juyo da fuskarsa da sauri kuma a fusace ya dakawa Sarki Taryan tsawa yana mai tarar numfashinsa ya ce, "Ta ya ya ka ke zaton zan iya neman wata alfarma a wajen Bawana ina matsayin Sarkinsa? Ka fice ka bani wuri! bana bukatar wata shawara daga gareka!! Domin ba ka biyo hanyar da zan iya aminta da kai ba!" Koda jin haka sai Sarki Taryan ya yi murmushi sannan ya juya ya fice daga cikin AA Misau ke Magana Turakar ransa a bace yana mai cewa a cikin "Ai kowa ya kiji ba ya kỉ gani ba ". ransa, Fitar Sarki Taryan ke da wuya sai Sarki Gurzalu ya sake yunkurawa ya mike zaune ya kira sunan daya daga cikin Kuyangin da ke kula da shi wacce ake kira SAHAIRA ya dubeta ya ce, "Ma za ki je ki gayawa sauran Dakaruna cewa su yi sauri su yi shirin tafiya. Lallai na basu rabin sa'a kacal kowa ya gama kintsawa". Koda jin wannan batu saimamaki ya karna Sahaira ta dubi Sarki Gurzalu cikin alamun firgici da tsananin damuwa ta ce "Haba ya shugabana, ya za ka ce mu yi taliya alhalin kana cikin wannan hali? Ka yi hakuri mana har izuwa sa'adda za ka ji kwarin jikinka?" A fusace Sarki ya dakawa Suhaira ISawa, jikinta ya kama tsuma sabo da tsananin Tsoro, ya ce, "Kin fini sanin halin da na ke ciki ne? To ki sani cewa idan na ci gaba da Zama a wannan gari kuma a cikin wannan hali zan iya rasa rayuwata". Koda jin haka sai Sahaira ta mike da sauri ta fice daga cikin dakin. Tana fita ta fara yin kicibus da Likitan Sarki, ta sanar da shi umarnin da Sarki ya bayar. Ta ke hankalin Likitan ya dugunzuma ainun ya dimauce ya fada cikin Turakar, ita kuma Sahaira ta nufi inda Dakarunsu suke da sauran 'yan uwanta IHadiman Sarki Gurzalu. Likitan na shiga Turakar ta Sarki Gurzalu ya kame kamar Gunki sabo da Tsananin mamaki bisa abin da ya gani. Ba wani abu ya gani ba facc Sarki Gurzalu a tsaye bisa kafafunsa biyu ya dogara da Sandarsa ta Sarauta. Nima Fa AA misau saida na dan razana naso dakatawa anan amma na daure naa cigaba🤓 A sanin Likitan ko Sarki Gurzalu zai iya jarraba mikewa Tsaye sai ya shafe a kallah Kwanaki arba'in yana shan Magani, anma gashi kwana uku kacal har ya fara iya mikewar duk da ya tabbatar da cewar ko kadan raunin da ke cikin nasa bai Soma warkewa ba. Ya yin da Sarki Gurzalu ya dago kai ya vi arba da fuskar Likitansa wanda ya yi tsuru- tsuru kamar ace kyat! ya fitra da gudu saho da tsoro da marmaki sai ya yi murmushi ya dubeshi ya ce, "Kwantar da hankalinka ya kai babban Likita babu abin da zai sameni har mu isa Birnina. Tabbas na san cewa babu alamar wani sauki a tare da raunin da ke jikina amma ina So ka sani cewa na sami wannan sauki ne Kawia ta haryar amfani da karfin sihirina, amma ba saukine na zahiri ba. Da wannan dama zan kiyaye dukkanin dokokin da ka kafa mini na rashin motsa gabban jikina har izuwa lokacin da ka bani umarni" Koda jin wannan batu sai fuskar Likitan ta fada da murmushi na samun nutsuwa da kwanciyar hankali sabo da yanzu ya tabbatar da cewar aikinsa ba zai baci ba. Nan dai aka cigaba da shirye-shiryen tafiya har aka kammala. Ba tare da bata wani lokaci ba kuwa aka sanya Sarki Gurzalu a cikin kcken dokinsa Kuyangi biyu suka shiga ciki don kula da shi. Shugaban Dakarun nasa na gefen dama na Keken Dokin bisa dokinsa. A gefen hagu kuma Likitansa ne a Zaune . Sauran Dakarun da suke yiwa Sarki Gurzalu rakiya a cikin wannan tafiya kuwa sun kaisu dubu daya da dari biyu, don haka sai suka rabu gida biyu, rabi suka tsaya a bayan Kcken Dokin Sarki, rabi kuma suna gaba. A hakasuka kama tafiya har suka fice daga cikin Bìrnin gaba daya suka nausa izuwa cikin dajin. AL'AMARIN JARUMI Imhal kuwa, lokacin da ya farfađo daga dogon suman da ya yi sai ya tsinci kansa a kwance akan wani luntsumemen Gado cikin wani kasaitaccen daki wanda babu abin da babu a cikinsa na jin dadin duniya. A gefe đaya ga kayan Abinci iri-iri a cikin Kwanuka bisa wani Tebur an jera gami da Tambulan na Ruwa da Ruwan Inibi. Koda ganin wannan al'amari sai Jarumi Imhal ya kamu da matukar mamaki, domin shi a saninsa kamata ya yi idan ya farka ya tsinci kansa a cikin Kurkukun da aka saba tsareshi. "To yanZU mene ne daliin đa ya sa aka karramashỉ aka kawoshi cikin wannan daki na alfarma?" Amsar da ya kasa baiwa kansa kenan. A dai-dai wannan lokaci ne yaji wata irin azababbiyar yunwa ta kamashi tamkar an yashe duk abin da ke cikin cikinsa. Koda ya yunkura domin ya mike tsaye ya tafi izuwa inda wannan Teburin cin abinci yake sai yaji kamar zai mutubisa tsananin zafi da zogin da yaji a cikinsa. A firgice ya yaye rigar da ke jikinsa sama kuma ya koma kan gadon da sauri ya Zauna, Nan take ya yi arba da babban raunin da ke gefen cikinsa wanda tuni an dinkeshi. Imhal ya daga kansa sama, take ya tuno da karon karshe da suka yi shi da Sarki Gurzalua sama, sa'adda Kowannensu ya sami nasarar sukar dan uwansa da Takobi. Koda ya gama wannan tunani sai hankalin Jarumi Inhal ya dugunzuma ainun, kuma zuciyarsa ta kama tafarfasa sabo da tsananin bakinciki. Abin da ya fara fado masa a rai shi ne Gimbiya Lamrita. Wai shin da gaske ne cewar Gimbiya Lamrita ta nutu sakamakon gumurzun da suka yí shi da ita? Ta ya ya ma za a ce ta mutu alhalin shi ya tabbatar da cewar bai kasheta ba da hannunsa? Kai! Abin la akwai rudani a cikinsa tun da na ga hawaye na zuba a cikin idanun Sarkí Gurzalu, Lallai na tabbatar da cewa da Lamrita ba ta mutu ba, to babu abin da zai sa Sarki Gurzalu yi ya wannan kuka. ldan har Gimbiya Lamrita tana raye ba Ta mutu ba mene ne matsayina a wajenta idan har Sarki Gurzalu ya mutu sakamakon sukar da na yi masa da takobina? Lallai na tabbatar da cewa Gimbiya Lamrita za ta kara tsananta gaba da tsanata ke nan a rayuwarta fiye ma da ko yaushe sakamakon kashe Mahaifinta. Imhal na cikin wannan tunani ne kwatsam! ya ji an turo kofar dakin da yake an shigo. Ya dago kansa da sauri ya yi arba da wanda ya shigo. Ba wani ne ya shigo ba face Sarki Taryan tare da Jarumi Salmanu yana mai take masa baya. Koda Imhal da Salmanu suka hada idanu sai kowannensu ya kasa kau da kansa ga barin kallon daya. Ba komai ne ya janyo haka ba face sun taba haduwa da junansu kimanin shekaru uku baya, amma sai kowannensu ya kasa tuno inda suka taba haduwar. Cikin annuri da walwala Sarki Taryan dubi Jarumi Imhal ya ce, "Ya kai Jarumin jarumai,na tayaka farinciki bisa tsira da ka yi da rayuwarka, amma babu wanda ya cancanci ka yi masa godiya face wannan bakon Jarumi dake tare da ni, domin shi ne ya ceci ayuwarka ya yi maka maganin da ni kaina na yi matukar mamaki sabo da cire tsarnmanin za ka rayu". Koda jin wannan batu sai fuskar Jarumi Imhal ta fadada da murmushi, nan take ya mikawa Jarumi Salmanu hannu suka gaisa. Ba tare da sun saki juna ba sai Imhal ya ce, "Ina godiya mara adadi a gareka ya kai Wannan saurayi ma'abocin kyawu da kwarjini. Ina fatan wannan taimako da ka yi min ya zamo tubalin kafa kafa sabuwar sabuwar Abota tsakaninmu. Kai kuwa mene ne dalilin da ya sa ka ceci rayuwata har ka yi mini Magani?" AA Misau ke Magana Sa'adda Salmanu yaji wannan tanbava sai ya yi ajlyar numtashi sanann ya ce, "da farko dai ba nỉ ne na cacanci ka lara yiwa godiya ba, Ginbiya Lamrita ya kamata ka yiwa", Koda jin wannan batu sai Jarumi Imhal ya kamu da tsananin manmaki ya ce, "Kana nufin ka ce akwai sa hannun Gimbiya Lamrita a cikin ceton rayuwata?" Jarumi Salmanu ya ce "Kwarai kuwa, kuma ita ce ma ta sa nasa hannuna akan ceton rayuwarka a lokacin da ku ka yi RAGAS kai da Mahaifinta Sarki Gurzalu. In ba don mun daukeka ba daga filin gasar mun gudu izuwa cikin daji daga filin gasar ne ma makiya za su karasa hallaka ka sabo da filin ya yamutse har yan kallo sun gwamutse a cikinsa" Koda jin wannan jawabi sai Jarumi Imhal ya kyalkyale da dariyar farinciki duk da cewar dariyar na Kara masa tsananin zogi da radadi na rauninsa. Kawai sai ya dubi Jarumi Salmanu ya ce. "Ya kai Abokina yanzu kana nufin ke nan ka ce Lamrita ta sauya ra'ayinta a kaina ta daina gaba da ni?" Kafin Salmanu ya budi baki ya ce wani abu sai Sarki Taryan ya tari numfashinsa ya ce, "Kwarai kuwa, kuma a yanzu tana Tsananin kaunarka fiyc da komai a duniya kamar yadda 'yata ma Gimbiya Shumaira ta kamu da tsananin sonka. Ni kaina yanzu alfarma daya zan nema a wajenka sabo da bana son lafiyar 'yata ko rayuwarta ta tabu. Kada ka zamo mai wulakaniata ko ka kyamaceta. Ka lallabata a hankali ku rabu lafiya tunda darna ta gane cewa zIciyarka ta karkata Akan Gimbiya Lamrita". Daga wannan lokaci ne na fara koyar da ita yadda ake tafiyar da harkokin Mulki da sirrikan tsafi, amma ko kadan ba ta da sha'awa akan wadannan abubuwa guda biyu, shi yasa na yi takaici ainun. Kai! ina mai sanar da kai cewa har yau kuma har gobe Gimbiya Shumaira ba ta damu da komai na duniya ba, kuma ban taba ganin ta so wani abu ba face kai a rayuwarta. A yanzu da na ke cin wannan Abinci tare da kai sai na aiyana a zuciyata na ce ina ma dai ace kai dana ne na cikina wanda zai gaji Karagar Mulkina, tabbas da na gama cika dukkanin burina na duniya. Babban abin bakincikina shi ne, idan na mutu shi ke nan đaukakata da jarumtakata za su dusashe tun da bani da da namiji. Bisa wannan dalili ne ma yanzu na yanke shawarar na shiga cikin wannan gasa ta kambun jarumta a wannan karon'" Kai Nima Dai AA Misau zan shiga wannan gasa duba da tsantsagwaron JARUMTATA nasan dai baku manta Yadda Nayi JARUMTA ba a wajan Samun yarinya Alfila A SARKIN SARAKAI ba hhhhh Zamu dakata anan saikuma wani lokaci zamu cigaba insha Allah Admin AA Misau ke Magana Ku bibiyemu a wannan shafuka Dandalin Litattafan Yaki By Al'ameen Ahmed Misau DANDALIN LITATTAFAN YAKI BY REAL AA MISAURIJIYA GABA DUBU💕 Littafi Na Bakwai (7)🩸 Part D. 💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing By AA Misau ke Magana ✍️⭐⭐⭐ Labari ya isowa Shagala cewa Marubucin yaci gaba da cewa BISA WANNAN DALILI NE MA YANZU NA YANKE SHAWARAR NA SHIGA CIKIN WANNAN GASA TA KAMBUN JARUMTA A WANNAN KARON'" jama'ar gari da jaruman gasa suna kan matsayin cewa ta mutu. Akwai sauran shawarwari wadanda Sarki :zai baka yanzu. Zan rinka kawo maka ziyara har izuwa lokacin da za ka sami karfin jikinka ka iya mikewa sOsai har ka iya taka kafafunka". Koda Jarumi Salmanu ya zo nan a Zancensa sai ya koma gefc guda ya zauna, shi kuma Sarki Taryan ya juya ya dauko wannan Teburi mai dauke da kayan Abinci, ya kawoshi daf da inda Jaruni Imhal ke zaune , sannan shima ya zauna daf da Imhal din a gefen Gadon da yako kai ya dubeshi ya ce, "Ya kai Jarurnin jarumai, na sani cewa kana jin yunwa, bisa haka ne nasa aka shirya maka wannan Abinci, kuma nima ina jin yunwar domin tun daga ranar da ku ka fafata kai da Sarki Gurzalu ban sami damar cin Abincin kirki ba. Lallai ina son mnu ci wannan Abinci tare domin mu sami damar tattaunawa akan muhimman maganganu". Ba tare da wata gardama ba sai Jarumi Imhal ya sa hannunsa a cikin Abincin, shima Sarki Taryan ya sa hannunsa suka kama ci. Tsawon 'yan dakiku masu yawa suna cin Abincin tare amma dayansu bai ce uffan ba, kumna kowannensu kansa na sunkuyce can kamar hadin balki sai suka dago kai gaba dayansu a tare kuma lokaci guda suka dubi junansu. Ko da suka hada idanu sai zuciyar Jarumi Imhal ta buga da karfi, ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin kwallah a cikin Idanun Sarki Taryan. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke nan, ya dubeshi ya ce, "Ya kai wannan Sarki mai daraja, ina dalilin zubar wannan hawaye na ka?" Sa'adda Sarki Taryan yaji wannan Lambaya sai ya yi ajiyar zuciya kuma ya yi shiru kam ba zai ce komai ba, sannan ya ce, ya kai Inhal, ka yi sani cewa tun kafin na sarmi haihuwa na ke ta fatan na sami haihuwar da namiji, amma ban samu ba. Babu irin kokarin da ban yi ba akan hakan, amrna sai bukata ta ki biya. A karshe ma sai Bokaye suka tabbatar mini da cewa 'ya mace zan haifa guda daya jal! a duniya, kuma daga kanta ba zan sake samun haihuwa ba. Bisa wannan dalili ne na yi bakinciki mara misaltuwa, ba don komai ba sai sabo da sanin cewa 'ya mace tana da rauni ba lallai bane ba ta iya tafiyar da harkokin Mulki ba kaar yadda ya kanata a bayan raina. A ranar da aka haifi Gimbiya Shumaira ban yi wani farinciki ba kuma ban soma jin kaunarta va a cikin zuciyata har sai da ta kai shekaru shida a duniya. Daga wannan lokaci ne na fara koyar da ita yadda ake tafiyar da harkokin Mulki da sirrikan tsafi, amma ko kadan ba ta da sha'awa akan wadannan abubuwa guda biyu, shi yasa na yi takaici ainun. Kai! ina mai sanar da kai cewa har yau kuma har gobe Gimbiya Shumaira ba ta damu da komai na duniya ba, kuma ban taba ganin ta so wani abu ba face kai a rayuwarta. A yanzu da na ke cin wannan Abinci tare da kai sai na aiyana a zuciyata na ce ina ma dai ace kai dana ne na cikina wanda zai gaji Karagar Mulkina, tabbas da na gama cika dukkanin burina na duniya. Babban abin bakincikina shi ne, idan na mutu shi ke nan đaukakata da jarumtakata za su dusashe tun da bani da da namiji. Bisa wannan dalili ne ma yanzu na yanke shawarar na shiga cikin wannan gasa ta kambun jarumta a wannan karon'" Koda jin wannan batu sai hankalin Jarumi Imhal ya dugunzuma, kuma ya kamu da tsananin mamaki, ya dubi Sarki Taryan cikin alamun damuwa ya ce, "Haba ya shugabana, ya ya kai da kafi kowa sanin illar Wannan gasa za ka ce za ka shigeta musarnman a yanzu da bakon Jarumi Salmanu ya shigota?" Koda jin haka sai Sarki Taryan ya yi muraushi ya ce, "Ai shi kadai ka sani, a jiya ma wasu bakin jaruman sun zo daga kasashe uku. Daya daga Birmin Farisa yake, daya daga Bimin Askar, na ukunsu kuma daga Bimin Sumari. Ni kam a iya yawona na duniya da kuma tsawon shekarun da na dauka ina shirya wannan gasa a Birina ban ta ba ganin jarumai irin su ba " Cikin marnaki Imhal ya dubi Sarki Taryan ya ce, "Kana nufin kace baka taba AA Misau ke Magana ganin jarumai masu kirar sadaukantaka bane kamarsu?" Sarki Taryan ya yi rourmushi ya ce, "A'a ba haka nake nufi ba, abin da na ke nufi shi ne, ban taba ganin jarumai masu tsananin zafin nama da tsantsar jarumtaka irin tasu ba, sabo da na gansu sa'adda suke motsa jini ne jiyan da suka zo. Ma'ana sun nuna irin jarumtakarsu anan kofar gidan sarautata ta hauyar yakar junansu, domin kowannensu ya ga irin jarumtakar sauran, kasancewar tafiya ta hadosu tare tun daga Birnin Farisa, Ina mai tabbatar maka da cewa jama'ar gari ma sun tsinke da al'amarinsu " Koda Sarki Taryan yazo nan a zancensa sai Jarumi Inhal ya yi mnurmushi ya ce, "AI ba a sanin maci Tuwo sai Miya ta kare! Idan akwai wani abu mafi muhimmanci da ka ke son ka sanar da ni ina sauraro, amma ni yanzu batun wadannan bakin jarumai da suka zo Bai taba firgitani ba ko ya karyar min da zuciya." Sa'adda Sarki Taryan yaji wannan batu sai ya yi dan shiru kamar ba zai ce komai ba, sannan daga can ya numfasa ya ce, "Tabbas akwai magana mai matukar muhimmanci wadda nake son na gaya maka. Maganar da zan gaya maka kuwa ita ce ka yi kokari ka gano asalinka da matsayinka, domin ta hakan ne kadai hanyar da za ka gane dalilin da ya sa ka tsinci kanka a cikin halin da ka ke ciki a yanZu, kuna ta hakan ne za ka zabawa kanka abin da ka ke ganin cewa zai fissheka a rayuwarka". Koda gama fadin hakan sai Sarki Taryan ya mike tsaye ya juya zai fice daga cikin dakin amma sai Jarumi Imhal yai sauri ya ce, "Ya shugabana ka taimaka min ka gaya min yadda zan yi na gano asalina da matsayina. Ga dukkan alamu ka san komai kaina, ko kuma ka san waní abu akan 'yar uwata wacce ta

Chapter 2 of 3