Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 3
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels RIJIYA GABA DUBU💕 Littafi Na Bakwai (7)🩸 Part A. 💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing By AA Misau ✍️⭐⭐⭐ (DUBA DA YADDA KUKE MANA LIKES AND COMMENTS ZAMUYI IYAKAN BAKIN KOKARIN MU WAJAN NISHADANTAR DAKU DA LITATTAFAN YAKI WANDA BAKU KARANTASU BA A INTERNET KO DA A ZAMANIN BAYA DA MUKAYI TYPING) Labari ya isowa Shagala cewa Marubucin yaci gaba da cewa.. LOKACIN DA GIMBIYA LAMRITA Ta ji abin da Sarki Taryam ya fadi, sai ta kamu da tsananin mamnaki garni da Cikin sanyin jiki da sanyin murya ta dubeshi tana mai risinawa ta ce, "Ya shugabana me ka ke tunanin ina kullawa dangane da Mahaifina, kuma mene ne ya sa ka biyo mu nan?" Koda jin wannan tambaya sai Sarki Taryan ya yi ajiyar numfashi sannan ya dubesu duk su biyun ya yi guntun murmushi ya ce, "Na sani cewa yanzu kin san dalilin da ya sa Mahaifinki ya tsani Jarumi Imhal har yake son ya kawar da shi? Don haka ba ki da burin da ya fi ki sanar da Jaruni Imhal komai domin ya dauki fansa a To ki sani cewa yin hakan a gareki shi ne babban kuskuren da za ki yi nadamar aikatashi a rayuwarki. Shawarar da zan baki ita ce, ki bar wannan al'amari a cikin ranki har abada, idan har Jarumi Imhal zai san wannan sirri to ya sani a wata hanyar, anma ba ta ke ba. Shawarata ta biyu da zan ba ki ita ce, 'Kada ki kuskura ki bari mutane su gane cewa kina ran a raye ba a kashe ki ba a filin gasa, domin idan aka san kin lalata wannan gasa ke nan har abada, sabo da mutane za su daina sonta da sha'awarta. Dangane da tambayarki ta biyu kuwa, ba wani abu bane ya sa na biyoku nan ba sai sabo da na gana da bakon Jarumi Salmanu," Koda gama fadin hakan sai Sarki Taryan ya dubi Jarumi Salmanu cikin murmushi. Cikin biyayya Jarumi Salmanu ya risina ya yi gaisuwa ga Sarki Taryan sannan ya taho gareshi suka koma gefe daya suka tsaya. Tsayuwarsu ke da wuya sai Sarki Taryan ya dubeshi cikin nutsuwa ya ce, "Ya kai wannan babban Jarumi mai ban al'ajabi, ka yi sani cewa Jarumi Imhal ne babban abin dogarona a cikin wannan gasa ta kambun jarumtaka na duniya, amma a yanzu na sauya shawara, kaine gwanina domin na tabbatar da cewar kaine za ka lashe wannan gasa." ya Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Jarumi Salmanu, ye dubi Sarki Taryan cikin alamun rashin yarda ya ce, "Ya kai wannan Sarki, kai kuwa mene ne dalilin da ya sa ka zabeni a matsayin gwaninka alhalin akwai alarnun cewa tsakanin Sarki Gurzalu da Jarurni Imhal ne za a sami zakaran wannan gasa? Ta ya ya ni da ba ka tafa ganina ba sai yau, kuma ba ka ga iyakar juriyata ba da iyakar jarumtakata ba za ka ce ka zabeni a matsayin gwaninka? Ina mai baka shawara akan cewa ka sauya gwani, idan ma hasashe ka yi a kaina ko kuma tsafi ne ya sanar da kai hakan to ka saki Reshe ne ka kama Ganyc" Koda jin wannan batu sai Sarki Taryan ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ya kai Jarumin jarumai, ka yi sani cewa, Makaho ba ya cewa ayi Wasan jila face ya taka hoge!" Ni na san wani al'amari boyayye a tare da kai wanda ka ke zaton ban sani ba. Kada ka damu, lokaci ne zai bambance ma na komai. Yanzu dai ina so ka sani cewa ba zai yiyu a ci gaba da gasa tsakanin Sarki Gurzalu da Jarumi Imhal ba sakamakon raunin da ke jikinsu, dole ne su yi jinya ta yan kwanaki don haka kaine za ka ci gaba da debewa 'yan kallo kewa ta hanyar cigaba da wasa har izuwa lokacin da za su sami lafiyar jikinsu su yi wasan karshe a tsakaninsu in ya so wanda ya yi nasara kaine abokin gwaminsa. Ya ke Gimbiya Lamrita, ki yi sani cewa kin kamnu da tsananon son yarimna Imhala yanzu kamar yadda shima ya kamu da tsananin sonki, to ki sani cewa 'yata Gimbiya Shumaira a yan haka tana kwance cikin mugun yanayi sabo da tunanin cewa Jarumi Imihal ya rasa rayuwarsa, sabo da itama ta kamu da tsananin sonsa fiye da ke. Ina mai rokonku alfarma ku bani Jarumi Imhal na tafi da shi domin 'yata ta ganshi don kada rayuwarta ko lafiyarta ta salwanta". Koda Sarki Taryan yazo nan a zancensa sai jikin Gimbiya Lamrita da Jarumi Salmanu ya AA Misau ke Magana yi sanyi, suka dubi junansu suka yi shiru aka rasa wanda zai ce kala. Daga can sai Jarumi Salmanu ya dubeta ce, "Bamu da wani zabi a yanzu wanda ya fi mu Mika Imhal ga Sarki domin mu ceci rayuwar "yarsa". Da jin haka sai Gimbiya Lamrita ta murtuke fuskarta ta dubi Salmanua fusace ta ce. "Ta ya ya ka ke zaton cewa zan iya hakura da Jarumi Imhal a yanzu alhalin na san cewa. shi ne kadai dan uwana da ya rage a duniya a wnnan duniya? Idan har akwai abin da zai iya rabani da Imhal a yanzu ba zai wuce takobi ba". Tana gama fadin hakan sai ta zare takobinta ta fuskanci Jarumi Salmanu da Sarki Taryan ta ce, "Ku kasheni idan kuna so ku rabani da dan uwana kamar vadda Ubana ya ha'inceni ya rabani da shi tsawon shekaru, kuma ya Sa na zama babban abokiyar gabarsa." Nan take hawaye ya zubowa Gimbiya Lambrita, kuma hannunta mai rike da takobin ya kama karkarwa. Al'amarin da ya karya zuciyar Jarumi Salmanu da ta Sarki Taryan ke nan, suka kamu da tsananin tausayinta. Kawai sai Jaruni Salmanu ya mika hannunsa ya karbe takobin Lamrita sannan ya dubeta a nutse cikin alamun tausayawa ya ce, "Ya ke Gimbiya, kin sani cewa in da so na ke na cutar da ke ba zan ceci rayuwarki ba daga sharrin wannan Macijiya da take son hallaka ki a cikin Kogi. Ki kwantar da hankalinki, na yi miki alkawari cewa ko Mahaifinki ya gane cewa yanzu kin san Jarumi Imhal a matsayin dan uwanki ba zan bari ya sake rabaku ba," Sa'adda Gimbiya Lamrita ta ji wannan batu sai hankalinta ya kwanta. Nan take Jarumi Salmanu ya dauki Jarumi Imhal ya dorashi akan dokin Sarki Taryan gaba daya tamkar ya dora gawa domin ko alamar rai babu a tare da shi. Nan dai duk su ukun suka hau dawakansu suka juya da baya suka durfafi hanyar da za ta mayar da su cikin Birnin. Wannan shi ne abin da ya faru ga su Gimbiya Lamrita bayan an yi gasar kambum jarumta tsakanin Sarki Gurzalu da Jarumi Imbal L'AMARIN Sarki Gurzalu kuwa shima bai farfado daga dogon suman da ya yi ba sakamakon sukar da takobin Jarumi Imhal ta yi masa ba sai bayan Likitansa ya gama yi masa aiki da nisan sa'a uku. Koda ya bude idanunsa ya tsinci kansa a kwance cikin masankinsa na gidan Sarki Taryn sai kawai ya ji 'yarsa Gimbiya Lamrita ta fado masa a rai, ai kuwa sai ji ya yi zuciyarsa ta buga da karfi, al'amarin da yai matukar dugunzuma hankalinsa ke nan, ya rasa abin dake mesa daci, kuma ya ji ban da son ganin Lamrita babu abin da yake so. Nan take ya yunkura da nufin ya mike tsaye daga kan gadon da yake kwance, amma sai yaji ya kasa sakamakon wani irin zafi da zogin da yaji a gefen cikinsa. Bisa dole ya koma ya kwanta cikin tsananin takaici da bakinciki, sabo da nan take ya tuno da duk abin da ya faru a fiin gasar kambun jarumtaka tsakaninsa da Jarumi Imhal. Bayan haka kuma sai tunanin yarsa Gimbiya Lamrita ya sake fado masa zuciya. Cikin tsananin kaduwa da firgici Sarki Gurzalu ya kwalawa Likitansa kira ya shigo cikin turakar. Da shigowarsa ya zube guiwoyinsa yana mai amsa kira. kasa bisa Cikin karfin hali Sarki Gurzalu ya dubi Likitan ya ce, "Ina labarin Sarkin yakina? Shin ya dawo ne daga Birnin Kisra?" Likitan ya sake risinawa ga Sarki Gurzalu cikin biyayya ya ce, "Ya shugabana ai tun da Sarkin Yaki ya tafi har yau bai dawo ba. Yau fa kwananka uku a kwance cikin mugun hali, bamu taba zaton cewa za ka tsira da rayuwarka ba". Koda jin wannan batu sai hankalin Sarki Gurzalu ya sake dugunzuma fiye da koyaushe, ya juyo da kansa da kyar ya dubi Likitan ya ce, AA Misau ke Magana "Yanzu tsawon wanne lokaci ka ke ganin cewa zan iya dauka kafin na warke har na ci gaba da wannan gasa?" Sa'adda Likitan yaji wannan tambaya sai ya sunkui da kansa kasa cikin alamun damuwa da fargaba ya ce a cikin murya mai sanyi, "Ya shugabana tun da na fara aikin Likitanci ban taba ganin mutumin da ya sami irin wannan rauni naka ba har ya tsira da rayuwarsa face kai kadai. Takobin da Jarumi Imhal ya soka maka a gefen cikinka sai da ta 6ullo ta gadon bayanka, kuma kaima haka ka sokeshi, amma na sami labarin cewa shima ya tsira da rayuwarsa. ina mai tabbatar maka da cewa a kalla sai ka yi kwana sittin a kwance kana jinya sannan za ka iya mikewa tsaye har ka iya tafiya". Koda Likitan yazo nan a jawabinsa sai zuciyar Sarki Gurzatu ta kama tafarfasa kamar za ta kone sabo da tananin bakinciki, bai san sa'adɖa hawayen takaici ya zubo masa ba, ya dubi Likitan ya ce, "Yanzu shi ke nan kana nufin ba zan iya ci gaba da wannan gasa ba ke nan har a kammalata?" Koda Likitan ya ga hankalin Sarki Gurzalu ya tashi ainun sai ya ce, "Ka kwantar da hankalinka ya shugabana, domin kuwa shima abokin gabar taka Imhal bai isa ya ci gaba da yin wannan gasa ba tunda shima yana dauke da irin raunin da ke jikinka, kuma komai saurin warkcwarsa da rashin kan jikin nasa sai ya kwana a kalla talatin a kwance yana jinya". Koda jin wannan batu sai zuciyar Sarki Gurzalu ta yi dan sanyi kadan har ya yi dan guntun murmushi na mugunta ya ce, "Ni kam gwara ace na mutu da dai wannan yaro lmhal ya lashe wannan gasa alhalin ina raye, kuma ina ji ina gani. Ya kai babban Likita abin da na ke so da kai shi ne, duk yadda za ka yi ka hada baki da Likitocin Sarki Taryan domin a sawa Jarumi Imhal Guba a jikinsa wacce Za ta zamo sanacin ajalinsa. Kudi ko nawa ka ke bukata zan bayar. kuma idan aka yi nasara kaf! A Birnin Kisra ba za a taba samun Attajiri kamar ka ba". Koda jin wannan batu sai jikin Likitan ya kama karkarwa sabo da tsananin murna. Muryarsa rawa ya ce, Ya shugabana ai kuwa duk yadda zan yi na ga wannan bukata taka ta biya zan yi ta kowanne hali" Sarki Gurzalu ya dan yi mumushi na farinciki sannan ya kira sunan wani babban Hadimi nasa kuma amintaccensa wanda ake kira SALUHU Salahu na tsaye a kofar Turakar da Sarki Gurzalu ke kwance sai ya ji kira. Nan da AA Misau ke Magana nan ya fada cikin Turakar da sauri ya zube kasa a gaban sa yana mai amsa kira. Sarki Gurzalu ya dubi Sahalu ya ce, "Aiki biyu na ke son ka yi mini yanzu. Da farko ina son ka tashi Dakarı arba'in daga cikin Dakarunmu da suka rage anan Birnin su garzaya izuwa can Birnina domin su jiyo mini labarin Sarkin Yaki, kuma su gano mini halin da 'yata Gimbiya Lamrita ke ciki, domin na tabba tar da cewar tana nan a tsare a cikin gidan Sarautata kamar yadda na bayar da umarni. Lallai wadannan Dakaru su hanzarta dawowa kafin a kammala gasar nan ta kambun jaruntaka. Aiki na biyu da za ka yi shi ne yanzu ka baiwa Likita dinare dubu dari bakwai domin yaje ya fara gudanar da babban aikin da na ba shi". Koda jin wannan umarni sai Hadimi Sahalu ya risina ya ce, "An gama ya shugabana". Nan take Sahalu ya mike tsaye ya fice daga cikin Turakar Likita na biye da shi. Fitarsu ke da wuya sai Kuyangin Sarki Gurzalu guda uku suka shigo cikin Turakar suka shiga aikinsu na yỉ masa hidima. Koda Sarki Gurzalu ya ga yadda ake shriya masa abincinsa, shimfidarsa da kuma kawar da ke cikin dakin duk da cewa yana cikin wannan hali na jinya sai ya bushe da dariyar murna a cikin yana mai cowa, "Hakika duk wanda bai danđani Mulki ba a cikin wannan duniya to bai san dadin duniyar ba. Kawai dai rakiyar wasu ya zo a cikinta. Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin Sarki Gurzalu da Likitansa da suka yi tattaunawar siri. AL'amarin su Sarki Taryan kuwa, lokacin da suka iso cikin gari sai ya dubi Jarumi Salmanuda Gimbiya Amrita ya ce,"'Ku tafi izuwa Masaukinka, kuma ke Gimbiya ki ci gaba da 6oye fuskarki kada ki kuskura wani ya shaidaki har izuwa ranar, da za a kamnmala wannan gasa". ob Koda jin wannan batu sai mamakiya kama Gimbiya Lamrita, yå dubi Sarki Taryan ta ce, "Wai shin akan wanne dalilizan ci gaba da boye kaina alhalin ma yanzu shi Mahaifin nawa ta kansa ya ke, babu tabbacin ma zai iya tsira da rayuwarsa? Ai ni burina a yanzu shi ne, na je mu yi gaba da gaba ni da shi na gaya masa duk irin mugayen abubuwan da ya shuka a rayuwarsa da kuma irin tsananin kiyayyar da na ke yi masa a yanzu, in ya so mu yaki juna ni da shi" Koda Sarki Taryan yaji wannan batu ne Gimbiya Lamrita sai ya tuntsure da dariya, al'amarin da yai matukar baiwa Jarumi Salmanu da Gimbiya Lamrita mamaki ke nan suka tsaya suna duban Sarki Taryan. Lokaci guda Sarki Taryan ya murtuke fuskarsa kamar wanda aka aiko masa da sakon mutuwa ya ce, "Ya ke Lamrita, ina so ki sani cewa duk wanda ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi, kuma koda Zaki yaje kasa to fa gawarsa ma abar tsoroce, kuma abar shakka ga dukkan dabobin daji! Mahaifinki tsohon makiri ne, masanin tuggu da makirci! Kuma wanda bashi da imani da tausayi ko kadan. A yanzu hakan da yake kwance zai iya haddasa masifar da za ta sa gaba daya duniyar nan ta hautsine, don haka ni kaina ina shakkarsa. Ni dai yanzu burina da kwanciyar hankalina kawai shi né ya amince cewar janye batun cigaba da wannan takara ta kambun jarumta ya tafi Birninsa domin karasa jinyar da yake yi". Koda jin wannan batu sai Hawaye ya zubowa Gimbiya Lamrita ta ce, "Ni kuwa burina shi ne Mahaifina ya rasa rayuwarsa a cikin wannan gasa da ake yi, domnin ban ga amfanin rayuwar tasa ba a doron kasa a matsayinsa na azzalumi, kuma maci amanar da ya kashe dan uwansa na jini sabo da kawai ya hau karagar mulki." Sa'adda Sarki Taryan yaji wannan batu daga bakin Gimbiya Lamrita sai ya yi dan guntun murmushi ya ce, "Haba Gimbiya ai naka, naka ne har bada! Komai irin mugun halin Mahaifinki ai ba ki isa ki cire jininsa daga cikin naki ba. Mahai finki ba zai mutu a filin daga ko a cikin gwagwarmaya ba, don haka ma ki daina tunanin cewar zai mutu a cikin wanran gasa. Ina mai tabbatar miki da cewa in ba don baya tare da Gurunsa na tsafi ba a yanzu da tuni ma ya dade da zama Zakaran wannan gasa. Ba wani ne ya sace masa wannan Gurin tsafi nasa ba face Muzaina kanwar Mahaifiyar Jarumi Imhal, wacce ita ce kadai ta rage daga cikin zuri'ar tasu. Koda jin wannan batu sai mamaki da muma suka sake turnuke Gimbiya Lamrita ta dubi Sarki Taryan cikin zakuwa da damuwa ta ce, "Yanzu a ina zan ga Muzainat kuwa?" Sarki Taryan ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ai kin tambayeni abin da ban sani ba, sabo da a halin yanzu babu wanda zai iya sanin inda take sabo da karfin sihirin Gurun tsafin da ke jikinta. Mutum đaya ne kacal zai iya gano hakan, kuma ba wani bane wannan mutumi face shi Mahaifin naki... TopA nikaina AA Misau a nan zan tsaya Zamu dakata anan saikuma wani lokaci zamu cigaba insha Allah Admin AA Misau ke MaganaRIJIYA GABA DUBU💕 Littafi Na Bakwai (7)🩸 Part B. 💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing By AA Misau ✍️⭐⭐⭐ (Hallau Yau Ma Dai Ina Dauke Muku Da cigaban Wannan Littafi Ku Bamu Aron Kunnuwanku Kucigaba da antaya manaa likes and comments domin Samun cigabansu akan lokaci) (Sannan ina dauke muku da group din da zamu cigaba da kawo litattafan da kuke nema ko kuka karanta kuke son sake karantawa Wato https://facebook.com/groups/1511287118906332/ SAIKUNZO Labari ya isowa Shagala cewa Marubucin yaci gaba da cewa... MUTUM ĐAYA NE KACAL ZAI IYA GANO HAKAN, KUMA BA WANI BANE WANNAN MUTUMI FACE SHI MAHAIFIN NAKI. Kuma shi din ma sai idan ya shiga đakinsa na sihiri da ke can Birninku ya yi bincike. Abin da na sani kawai shi ne, Muzainat tana tare da mu a koyaushe, domin ba za ta yarda ta yi nisa da mu ba, tunda ta san halin da Jarumni Imhal ke ciki". Sarki Taryan ya dubi Jarumi Salmanu cikin nutsuwa ya ce, "Ya kai wannan bakon Jarumi mai abin al'ajabi, yanzu kuwa tsawon wane lokaci Imhal zai shafe yana yin wannan barci? Ka sani cewa bani da wani buri wanda ya fi na ga ya dawo cikin hayyacinsa domin na kaishi wajen 'yata ta ganshi a raye, sabo da hakan ne kadai abin da zai ceto rayuwarta". Koda jin wannan batu sai zuciyar Gimbiya Lamrita ta buga da Karfi sosai, taji ta kamu da tsananin kishi. Jarumi Salmanu ya numfasa ya ce, "Ai da izinin Ubangijina nan da kamar tsawon sa'a uku kacal! Imhal zai farka daga barcin da yake yi, kuma insha Ailahu zai sami lafiyar da zai iya mikewa har ya taka afafunsa". Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube Sarki Taryan da Gimbiya Lamrita. Ba tare da 6ata wani lokaci ba Salmanu da Gimbiya Lamrita suka yiwa Sarki Taryan sallama suka tafi izuwa nasu Masaukin, shi kuma sai ya nufi hanyar da za ta kaishi Fadarsa dauke da Jarumi Imhal a gaban dokinsa. GimbiyA SHUMAIRA na kwance akan gado a cikin Turakarta tana ta faman shara barci mai nauyi sakamakon Maganin barcin da Likita ya ba ta ta sha, Kuyanginta sun kewayeta a zazzaune dulkkaninsu fuskokinsu na nuna alamun damuwa da fargaba, sai kawai suka ga ta mike zaune zumbur! A firgice kamar wacce ta farka daga yin mugun malarki mai ban tsoro. Abin da ta fara ambata a bakinta shi ne sunan Jarumi IMHAL. Koda ta duba ko ina da ina a cikin Turakar ta ta ta fahimci a inda take sai ta sauka daga kan Gadon na ta da sauri kuma a. dimauce da nufin ta ruga waje. Kawai sai ta ga an turo kofar dakin na ta an shigo. Ba wani bane ya shigo ba face Mahai finta Sarki Taryan fuskarsa cike da annuri. Shumaira ta karasa gareshi da gudu ta rungumeshi tana mai fashewa da kuka ta ce, "Ina masoyina Imhal? Shin ya mutu ne ko kuwa tuni ma an binnc gawarsa?" Sa'adda Sarki Taryan yaji wannan lambaya sai ya janye jikinsa daga cikin na Shumaira ya sa hannu ya share hawayen sannan ya ce, "Kwantar da bankalinki ya ke 'yata, ina mai yi miki albishir da cewar Masoyinki Jarumi Imhal na nan a raye kuma nan da cikar tsawon sa'a biyu da rabi ma zai farka daga barcin da yake yi har ya iya mikclewa tsaye ya yi tafiya da kafafunsa". Koda jin wannan batu sai farinciki ya mamaye Gimbiya Shumaira, ta dubi Sarki ta ce, "Ma za ka kaini inda yake na ganshi da idanuna domin na samu kwanciyar hankali". Sarki Taryan ya cc, "Haba ya ke 'yata, me ki ke ci na baka na zuba? Ai kamata ya yi dai ki yi hakuri har ya farka daga barcin tukunna, in son samu nc tunda yana dauke da babban rauni a jikinsa". Gimbiya Shumaira ta ce, "A gaskiya zuciyata da jikina ba za su iya daukar wannan hakuri ba har na tsawon sa'a biyu da rabi. Ya kai Abbana, ina rokonka da ka hanzarta kaini wajcn abin begena domin idan AA Misau ke Magana ban ganshi ba yanzu zan iya shiga cikin wani halin mara dadi". Koda jin haka sai Sarki Taryan ya gyada kai cikin alamun damuwa ya ce, "Shi ke nan zo mu je na kai ki inda yake". Nan take Sarki Taryan ya kama hannun Gimbiya Shumaira ya ja ta suka fice suka nufi wata hanyar dabarm a cikin gidan sarautar. Sai da suka yi tafiya mai nisa sannan suka iso wani babban daki na musamman inda aka saba saukar manyan Baki. Shi dai wannan daki an kebeshi ne a wuri dabam inda ba kowane ya san da shi ba, hatta kuwa da yawan Hadiman gidan. Kusan shi ne đaki na karshe a cikin gidan sarautar, kuma sai an kure wani dogon lungu mai duhu sannan za a iso wani babban fili inda dakin yake. Da isowarsu kofar đakin sai suka iske Dakaru sama da guda dari ukun sun kewaye đakin don tabbatar da tsaro. Koda Dakarun suka ga Sarki Taryan tarc da 'yarsa Gimbiya Shumaira sai suka risina suka kwashi gaisuwa, kuma suka dare da sauri suka basu hanya.Kai tsaye Sarki Taryan da Shumaira suka kunna kai cikin dakin. Sai da suka ratsa ta cikin wani katon falo sannan suka shiga cikin dakin da Jarumi Imhal ke kwance. nan Shumaira na sa kafarta guda cikin đakin sai ta hango Jaruni Imhal kwanceua akangado yana ta faman shara barci, gai alamar numfashi akan kirjinsa. Nan take ta ji wani irin dumbin farinciki ya lullu6eta, har ta yunkura za ta juya da baya tunda hankalinta ya kwanta sai ta ji Jarumi Imhal ya fara sambatun Mafarki. Cikin hanzari ta juyo da baya ta nufi kan gadon da yake kwance, sai da ta iso kansa sannan ta zauna akan gefen gadon daf da shi sannan ta kara kunnenta daf da bakinsa domin taji abin da yake fadi sakamakon cewar yana magana ne a hankali. Koda ta ji kalmar da yake ambata sai zuciyarta ta buga da Karfin gaske, hankalinta ya dugunzuma ainun, kuma ta kamu da Tsananin bakinciki, ba ta san sa'adda hawayen takaici suka zubo ma ta ba. Sarki Taryan da ke tsaye sai shima hankalinsa ya tashi sakamakon ganin halin da 'yarsa ta shiga. Bisa wannan dalili ne shima ya karaso daf da Jaruni Imhal ya sunkuyo dai-dai kansa ya kara kunnensa. Kawai sai yaji Imhal baya ambaton komai face sunan Gibiya Lamrita. Yana hada idanu da Shumaira sai ta fashe da kuka sannan a mike tsaye ta rungumeshi tana mai cewa, "Ya kai Abbana yanzu ina zan sa raina na ji dadi tunda ba ni da gurbi a cikin zuciyar wanda na ke bege dare da rana?" Koda jin wannan tambaya sai Sarki Taryan ya kamu da tsananin tausayin 'yarsa Gimbiya Shumaira ya kara kankameta a kirjinsa kuma yai shiru ya ma kasa cewa komai, kawai sai ya janyeta suka juya da baya suka fice daga dakin. LOKACIN DA Jarumi Salmanu da Gimbiya Lamrita suka isa Masaukinsu wato gidan da suka karba Haya tun daga ranar da suka iso Birnin sai kowanncnsu ya tsaya a kofar dakinsa ya kasa shiga. Al'amarin da ya bai wa Kowannensu mamaki ke nan. Ba tare da Salmanu ya dubi fuskar Lamrita ba ya cc, "Kina da wata magana ne da ki ke son ki yi min?" Koda jin wannan tambaya sai Lamrita ta yi murmushi ta ce "Ai kaima ka sani cewa ina da maganganu da yawa, to amma tun da yanzu Magariba ta yi me zai hana mu huta tukunna har ma ka yi Ibadarka in ya so sai na zo dakinka mu zauna mu tattauna?" Koda jin haka sai Salmanu ya girgiza kai ya ce, "A'a ba za a yi haka ba, duk abin da zai sa mu kadaita ba zan yarda da shi ba, domin karya dokar Addinina ne. Sai dai ki bari bayan na kammala 'yan ayyukana na fito harabar gidan nan". Larnrita ta yi murmushi ta ce, "Shi ke pan ba nstsala" Tana gama fadin hakan sai ta shige cikin dakin na ta, shina bai tsaya bata wani lokaci ba sai ya kunna kai izuwa

Chapter 1 of 3