Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Neehal just try to prove him that kin chanza your not that girl anymore and you regret your actions ,duk da cewa your just a teenager at that times " Ɗan shiru ya yi na ƴan mintina har yasa na ɗago ina kallansa sai naga ni yake kallo ɗan murmushi ya yi na gefen baki kafin ya cigaba da cewa
" ko kinsan ta sanadiyar ruwan sanyin da yace kin taɓa zuba masa ya kamu da ciwon sanyi? Baya iya wanka da ruwan sanyi ko shan wani abu mai sanyi, indai abu mai sanyi ya taɓa shi sai ya samu allergies masu ƙarfi. Ya kamu da ciwon nan na sanyi wato COLD URTICARIA "

Wani irin guilt naji ya rufe ni hawaye suka biyo kuncina " But despite all that his the good person da ki ka sani bai taɓa riƙe ki countable a kan haka ba, kawai dai yana jin ciwon wasa da zuciyarsa da ki ka yi wanda hakan ya sa masa ciwo mai tsanani don lokacin da Angel ta same shi yana cikin wani mawuyacin hali she trys so hard a kanshi ta nemo masa family nashi sanadiyar hakan yasa ta samu yardar sa dan ya rufe duk kannin wata ƙofa da zai bari wani ya shiga jikinshi bare har ya samu yardar sa,har ta samu nasarar samun zuciyarsa bayan tasha artabu a kanshi mai ƙarfin gaske"

Tafa hannuwa ya yi ya yarfa "OK enough with the emotional stories . Ina fatan zaki ɗauke ni a matsayin aboki da zaki na kawowa matsalar ki, and don't worry akan abinda Eman ta ce tana faɗa ne kawai bawai dan haka abun yake ba, she is to nice too hate on people sannan duk lokacin da wancan ya yi miki wani abu ba daidai ba just come to me I will wuff his ass for you" cike da wasa ya ƙarasa maganan da har bansan sanda nima na saki murmushi ba. Haisam mutum ne mai barkwanci da ban dariya bai bar office ɗina ba sai da yaga na sake ina dariya har na manta da damuwar da nake ciki.


***

Yau ko da na tashi kasa shiga gurin Eman nayi dan yi mata sallama kai tsaye nayi waje. Tunda na doso gurin da nake tsayewa dan samun mota na hango motar Haisam a fake a gurin shi kuma yana tsaye jikin motar. Yana hango ni kuwa ya sake min murmushi ya ɗagomin hannu. Nima murmushin nayi masa na ƙarasa gaban sa ina ƙoƙarin shiga motar da ya buɗemin tun bayan daya hango ni. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi na rashin ganin Ayaan cikin motar sosai naji daɗin hakan. Hira muke sosai da Haisam har muka je gida na fuskanci shima mutum ne mai surutu dan duk yanda zaka ja jiki baza kasan sanda zaka sake masa ba kuyi ta hira kana kwasar dariya.

Juyawa nayi ina kallanshi sosai fuskata da murmushi dan naji daɗin kasancewa ta dashi saboda ya sani manta dukkanin wata damuwa da nake tattare da ita. Godiya nayi masa ina ƙoƙarin fita daga motar ya ce " Baki ji ba" dawowa nayi na zauna ina kallan wayarsa da ya miƙo min ."Your digits muna gaisawa ko?,Yanzu ma ya kamata ki yi min iso gurin Innati ko kar taga ana kawo ki ba tare da tasan ko waye ba" Ɗan Jim nayi ina tunanin maganan sa kuma haka ne. Karɓar wayar nayi nasa masa number ɗita na fice dan sanarwa da Innati ta yi baƙo zai zo su gaisa. Toh koda na shiga gidan sai na iske Ramlat da alama itama bata daɗe da dawo ba daga gurin aiki. Zama nayi kan tabarman da suke zaune suna hira. Bayan mun gaisa na shedawa Innati abunda yake faruwa. Ɗan jim tayi kafin tace naje nayi masa iso ya shigo. Nai saurin ficewa na barsu suna ɗan ƙara kimtsa gurin.

A tsaye jikin mota na ganshi ya ƙafe ofar gidan da ido har naji yar kunyar idon da muka haɗa dashi. "Ta ce ka shigo" nace masa ina ƙoƙarin juyawa ,ina jin takun tafiyar sa a bayana. Da sallama muka shiga yana biye dani. Samun guri nayi kusa da Innati na zauna kaman zan shige cikin ta .zuwa ya yi ya durkusa kanshi a ƙasa yana gaida Innati dake amsawa fuskarta ɗauke da fara'a. Miƙewa ya yi zai tafi bayan ya jiye rafar yan dubu guda uku wajen ƙafar ta. Daga ni har Innati mukayi saurin tareshi amma ya yi saurin ficewa kafin tace wani abu. Cikin azama na ɗauki kuɗin zan bishi dasu Innati ta rike hannu na "me za kiyi Auta?" Nace "zan mayar masa da kuɗin ne Innati " kai ta girgiza tana cewa "A'a kul ba'a maida Alkhairi ga wanda ya yi shi sai dai in har ansan cewa bada niyar Alkhairin ya yi suba, ai ba tambayar sa aka yi ba Auta nima banji daɗin hakan ba amma tunda ya bayar babu abinda za muyi masa face godiya, kiyi masa godiya sosai amma ki nuna masa bawai don mun karɓa yanzu hakan na nufin zamu kara karɓa bane" kai na jinjina tare da ce mata toh nayi saurin ficewa na bishi. Har yanzu yana tsaye jikin mota. A kunyace na karasa ina yi masa godiya sosai . Hannu ya daga ya ce "godiyar me ki ke mun, na ɗauka ni dake mun zama ɗaya yanzu damuwar ki ai ta zama tawa in har kin ɗauke ni a matsayin ɗan uwa kuma aboki" murmushi nayi bance masa komai ba. Daidai Ramlat ta fito zata tafi. Sai naga gaba ɗaya tayi wani iri ko bata jindaɗi ne?. Cikin sauri na kirata kafin ta shige gida nayi mata bayanin wane Haisam da kuma yanda suke da Ayaan. A sanyaye naga ta gaishe shi bata jira komai ba ta juya cikin sauri ta shige gida. Da kallo na bita zuciya ta fal tunanin abunda ke damun ta.


***

Toh yau tsawon sati biyu kenan da muka fara waya da Haisam sosai na sake dashi dan duk lokacin da muke tare ina ji kaman an ya ye min damuwa ne. Shi ma Ayaan a yanzu bamu cika haɗuwa dashi ba a yanda Eman take min bayani kaman wani aiki ne yake mai muhimmanci da yasa bai cika zama ba yanzu kullum yana hanyar fita waje. Kusancin mu da Haisam yanzu ni kaina yana bani mamaki bazan yi ƙarya ba idan nace na fara jin wani abu game dashi duk da bansan shi me yake ji game dani ba.

Yau a office dina muke break saboda Eman bata zoba wai mijinta yazo daga turkey. Ban taɓa sanin cewa tana da aure ba sai a yan kwanakin nan da Haisam ke gayamin mijin nata balaraben saudiya ne aiki yake a turkey bai cika zuwa ba sai lokaci-lokaci ko ita Eman ɗin taje can turkey ɗin ta same shi. Har mamaki nake ko taya wannan aure zai yiwu kowa yana wata duniya daban?. Ƙofar office din nawa da aka kwankwasa tare da shigowa ba tare da na bada izni ba yasa muka maida hankali gaba ɗaya kan ƙofar.

Tsaye yake jikin ƙofar ya harɗe hannu a kirji. Sanye yake cikin wata dark blue three pieces suit da ta yi masifar kama shi. Farin glass ne a fuskarsa da ya ƙarawa fuskar tasa kyau. Gashin kansa tufke a tsakiyar kansa sai kaɗan da suka zubo goshinsa zuwa gefen fuskar sa. Ba ƙaramin kyau ya yi ba sai naga ya ƙara wani irin girma da tsayi. Ko dan na kwana biyu ban ganshi bane dan gaba ɗaya ya cike ƙofar. Fuskarsa babu wani annuri yake kallon mu nida Haisam da ya miƙe ya nufe sa da murmushi a fuskar sa yace

" Saukar yaushe haka babu waya?"

A maimakon ya bashi amsa sai ya kalle ni yace"My office now" ya juya a fusace ya bar office ɗin. Ni kaina banji daɗin abinda ya yi ba bare shi wanda ya yi wa. Bana so ace laifina ya fara jawo musu matsala a tsakanin su.

"Kije ko akwai matsala ne" yace yana ƙirkƙrar murmushin ƙarfin hali amma idansa kawai zaka kalla kasan ranshi ya baci. Murmushi nayi masa na ban haƙuri na tashi na yi saurin ficewa ƙirjina na dukan uku-uku.

A tsaye na same shi cikin office ɗin ya juyamin baya. Motsin shigowa ta da yaji yai saurin juyuwa yana kallo na naiyi saurin Sunkuyar da kaina kasa dan bazan iya jurar kallan kwayar idansa ba.

"What did you think your doing?" Ɗa gowa nayi ina kallansa ban gane abunda yake nufi ba

"Kina tunanin kin samu wani target ne da za kiyi playing ɗinsa at the end ki barshi ba tare da komai ba?" Sosai nake kallan sa dan kaina ba ƙaramin ƙullewa ya yi ba.

"Tell me ,mene ya burge ki game dashi? Kuɗi, kyau, ko iya dressing tell me" ya karasa maganan da tsawa har saida na firgita. Hawaye ne masu zafi suka biyo kuncina muryata na rawa nace
"Ban gane abunda ka ke nufi ba"

"Stop larying to me ,tell me what make you thinks you can make him fall in love with you just to break his heart?. People like you will never change you will always be the same, so tell is it his money that you want or his fame? " Ya ƙarasa maganan da muguwar tsawa har yana buga tebir wanda babu tantama anji a waje. Kuka na fashe dashi mai ƙarfi na ƙanƙame jikina guri ɗaya dan sai nake ganin kaman dukana zai yi.

Haisam ne ya shigo shima rai a bace da alama yaji duk abunda ya faru. A zuciye ya yi kan Ayaan shima cikin tsawa yace "what are you doing?" da fadɗa shima yace "stay out of this, wannan ba problem ɗinka bane" da wane irin fushi Haisam ya dafe kirjinsa "how dare you za kace ba problem ɗina bane ka ɗauka banji duk abinda kace bane.? Kana so ne kaji? Toh bari kaji Yes I LOVE HER, kai kuma baka isa ka hanani san ta ba i don't care what she did to you, that's was you 6yrs ago. So stop thinking saboda wani laifi da tayi maka zan hana kaina san abunda zuciya ta ke so. Wannan selfish reasons naka ne kawai"

A harzuƙe Ayaan yace " are you mad? Kasan am doing all this just to protect you?. Kasan wace ita and what she's capable of doing"

Shima a harzuken ya bashi amsa da " I dont care, that doesn't stop me from loving her" Yanda suke ta huci kaman zasu daki juna yasa na juya da mugun gudu ina wani irin kuka na fice daga office ɗin. Dukan kirjinshi Haisam ya yi " kaga abunda kayi ,why so cold towards her?,she has change man"
"I dont care, she's a snake, don't come running to me ta yi breaking heart dinka" a fusace ya wuce Haisam ya bar company ɗin ma gaba ɗaya. A jiyar zuciya Haisam ya sauke mai karfi. Shi yasan duk abinda Ayaan ke yi saboda har yanzu bai yarda da ita bane but yasan with time zai gane ta chanza ba yarinyar da yasani bace.

Nikam dana fito ban iya zama ba na ɗauki kayana nayi waje. Tun ba'aje ko ina ba zan fara haddasa musu matsala kan zumuncin su. Ni kaina nasan nayi karya idan nace banajin wani abu game da Haisam a yanzu, amma da ya tabbatar da cewa yana so na sai na kasa tsintar farin cikin hakan dan bana san abunda zai sa ta sanadina zumuncin su ya lalace. Ina ƙoƙarin tarar ɗan sahu wata dankareriyar Prado ta yi Parking gaba . Kafin nayi wani motsi ya fito fuskarsa a murtuke ya ce " Get in" kallon banza na watsa masa ina ƙoƙarin wuce sa ya bugamin tsawa "I said get in "Ban san yanda aka yi ba na tsinci kaina cikin motar ina rigzar kuka kaman wadda a kai wa mutuwa. Kota kaina bai bi ba ya tada motar da mugun gudu ya bar harabar gurin.

A ƙofar wani ƙatan mall naga ya faka motar ya shige ciki bai dade ba ya fito riƙe da ledoji. Ni dai ina binsa da kallo ne kawai sai sharar hawaye nake . Ajiye kayan ya yi ya tada motar muka cigaba da tafiya shiru sai ajiyar zuciya ta kawai dake tashi cikin motar ta wanda yaci kuka ya ƙoshi. Yana fakin a ƙofar gida na fara ƙoƙarin ficewa cikin sauri amma sai naji motar a garƙa me. Sakin murfin motar nayi ban juyu na kallesa ba dan ina jin idansa a kaina.

"Idan kin gama kije kice da Innati ta yi baƙo" yana faɗin haka ya buɗemin motar. Sai da na fita daga cikin motar tukun na juyo ina kallan sa ya zuba min tsuman mun idansa. Nace " Bazan faɗa ba ɗin ai ba yar aike ka samu ba, kuma bamu buƙatar ka cikin gidan mu. In gurin aikin ka kana gayamin abunda kayi niya kana juyani yanda kaga dama ina maka shiru saboda ina ƙarƙa shinka, toh nan ƙofar gidanmu ka ke baka isa ka sani abu nayi maka biyayya ba"

Da wani irin mugun gudu na rufe motar na juya da gudu na shige gida. Innati dake zaune ta ɗan firgita da yanda na shigo kaman wadda aka biyo. Tai sauri tara ta tana "lafiya me ya faru?" Ajiyar zuciya na sauke. Nai saurin tattaro nutsuwa ta cikin yaƙe nace mata " babu komai Innati kawai ina ta ɗokin ganin ki ne" kai ta girgiza tana ɗan bugemin ƙeya tace "Allah ya shirye ki" daidai mukaji sallama a kofar gida. Sai da cikina ya bada wani irin sauti nayi saurin komawa bayan Innati dake amsawa tare da bada iznin shigowa. Shigowa ya yi riƙe da ledoji da tsabar mamaki Innati ke kallansa.

"Ayaan" ta kira shi cikin matsanancin mamaki. Ɗurkusawa ya yi gabanta yana gaishe ta. Cikin sanyin jiki ta zauna tana amsa masa gaisuwar tashi. Sun jima suna magana da ita inda anan nake jin ashe iyayensu larabawa ne dake zaune ƙasar Mali. Ranan sunan su ƴan baƙin ciki suka sace shi saboda kawai Allah ya yiwa iyayen nasu ni'ima dan suna da rufin Asiri daidai gwargwado. Har an fidda rai kuma sai Allah ya sada su ga juna. Toh rayuwa kenan. Itama Innati tun daga farkon tafiyar shi babu abunda bata kwashe ta gaya masa ba har fashin da aka yi mana. Ya daɗe yana jimami cikin damuwa kafin ya mike da alkwarin inshaAllahu zai dinga kawo mata ziyara. Ni dama tun daya shigo banyi kuskuran kallan inda yake ba ban manta maganar dana gaya masa ba. Ledojin ya ajiye kafin ya fice yana ƙara yiwa Innati salama.

Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi bayan fitarsa dan sai nake jin kaman an sauke min dala da gwauron dutse. Ledar na janyo na buɗe. Kayan ciye-ciyene tun daga kan chocolates,biscuits, lemo,burgers gashin kaza da sauran su. Ai kuwa tuni yawuna ya tsinke duniya juyi juyi yaushe rabon da naga chocolate bare a kai ga nama ko shawarma. Zagewa nayi naci abunda raina keso naci nayi nak na ɗebi wasu nayi ɗaki dasu dan Innati ba gwanar wannan cimar bace. Wajen la'asar na ɗebi wasu na kaiwa Ramlat sai na riske ta babu lafiya dalilin da yasa ban dawo gidan ba sai isha. Ina dawowa kuwa nayi sallan na samu guri na kwanta da tunanin abunda gobe zata kunsa. Ga Haisam ya furta min cewa yana sona. Ƙarar wayata yasa na ɗauko wayar da sako ya shigo na Haisam kaman haka

"Good night baby "

Tsintar kaina nayi da win irin murmushi na rumgume wayar har barci ya ɗauke ni.


***

Yau tunda na tashi na tsinci kaina cikin faɗuwar gaban da na rasa dalilin ta. Jiki a mace na gama komai nayi wa Innati sallama na fito, sai dai abun mamaki motar Haisam na tara a kofar gida da alama ya daɗe yana jirana. Motar na nufa na shiga sai na tsinci kaina ina matuƙar jin kunyarsa na kasa haɗa ido dashi. Inajin sautin murmushi sa ya tada motar muka tafi. Har mukaje kalamai yake kashe ni dasu masu sanyi da ƙara jaddadamin san da yake min yace shi a shirye yake ya fito saboda nasan cewa ba wasa yake ba.

Har office ya raka ni sannan ya yi nasa floor ɗin dan shi yana kasanmu ne. Bayan tafiyarsa kuma naji bugun kirjina ya ƙaru . Ban kawo komai ba na hau aiki yanda ya kamata. Takardun na haɗa bayan na gama shigar dasu na fito dan kaiwa Ayaan saboda Eman bata dawo ba.

A bakin ƙofar na tsaya tare da kwankwasawa. Shiru babu amsa sai nayi tunanin ko baya ciki ne dan haka cikin sauri na buɗe ƙofar dan na ajiya masa saboda bana san ma haɗuwa dashi.

Mugun ganin da nayi yasa naci burki a bakin ƙofar na kasa shiga. Ni ban shiga ba ni ban fita ba. Idanuwa ƙur suka turke kan Ayaan dake zaune a kan kujera mace zaune kan cinyarsa ta bani baya saboda shike kallan ƙofar. Tayi straddling ɗinshi wato ta sashi a tsakiyar ta. Kananan kaya ne ajikin ta wanda da alama ko botorane da rigar ko kuma ziff saboda gaba daya rigar tana wajen kafadar ta ne hakan ya bawa farar fatar ta da bata cika haske ba fitowa, jar breziyar dake jikinta a waje muraran. Bata da gashi sosai dan da alama tayi ƙari ne. Gaba ɗaya fuskarsa na kwance cikin kirjinta ta rungume kansa kaman zata mayar cikin ƙirjin nata hannusa riƙe da ƙugun ta. Tsabar yanda ta fice a hayyacinta da alama bataji shigowa ta ba amma shi yaji dan idan sa kyam akan nawa . Wani irin nishi naji tayi tana "ohh yes baby"kafin ta yunƙura kaman zata tashi a jikinsa sai kuma ta koma da karfi ta zauna tana cigaba da sunbatu tana "yes.ohh..yes baby..". Lura da tayi hankalinsa baya kanta yasa ta juyu bayanta.

Wani irin mugun sarawa kaina ya yi lallaɓana na furta "Ninah" amma kalman ta kasa fitowa fili. Kaman da gayya ta cigaba da riding ɗinshi tana kallo na wanda hakan ya ƙara tabbatar min da sex suke. Da wani irin mugun gudu na juya na fice daga office ɗin.




Ƙaƙa- ƙara -ƙaƙa😂
Wannnan shi ake cewa CHAKWAKIYA mai zafi🔥🤣🤣🤣🤣


Ina masu addu'ar Allah yasa Ninah kaza, Ninah this🤣🤣🤣kuzo addu'ar ku ta karɓu😂😂😂😂😂😂🤣🤣🤣


Wasan fa yanzu ya fara.
Ga HAISAM ya furta yana son ta fa, ya kuma fito da karfin sa.💪
Kuna ganin wannan fushin da Ayaan yake ba kishi bane ba kuwa??



Masu buƙatar biya zasu fara biyan NAIRA 400 SU👌 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER ƊIN
👇

AISHA SANI DANJUMA
FIRSTBANK
3078293374

A TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER
👇
08140754777

KU HANZARTA ,SHOW ME THE LOVE AND SUPPORT DA KUKE BANI.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment