Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cushe saboda rashin gyara. Sai da ya ɗan cije baki ya ƙara kallo na yace " Hajiya tabbas ina da magana sai dai ina tsoron furtawa dan bansan da wace manufa zaki fuskanta ba." Murmushi nayi na ƙara gyara zama nace " Akwai abinda za kaji tsoron furta min? Na dauka munyi shaƙuwar da zaka daina jin tsoron furta min duk wata magana da ka ke da burin yinta"

"Kuma haka ne Hajiya" ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa " a da gaskiya nayi tunanin kina ɗaya daga cikin irin mutanen nan da suke ganin idan Allah ya basu kuɗi ko mulki to tunani suke kaman yafi son su a kan kowa shi yasa suke taka mutane yanda suka ga dama . Amma sai naga ashe nayi saurin yanke hukunci akan ki. Ba haka ki ke ba Hajiya, ke mutumce ce mai kyakkyawan hali sai mutum ya zauna dake zai fuskanci haka,idan aka cire kuruciya da yarinta a tattare dake tabbas duk namijin da yasa meki a matsayin mata ya yi sa'a a duniya. Dan haka ne nake kawo kokon barata nasan ban can-can ci soyayyar ki ba Allah kuma ya jarrabeni da son ki Neehal, wlh tun ranan da na ganki na kamu da sonki nayi iya bakin kokarina naga na cireki a zuciya ta amma n kasa ,kaman karamin sonki ake a kullum na ganki."

Tunda ya fara maganan na kafeshi da ido fuskata ɗauke da murmushin amma zuciyata wani irin tuƙuƙi take min . Mai maita kalman Ina sanki nake tayi a zuciya inajin wani irin ɗaci saboda rashin daɗin kalman a guri na. Murmushi da yagani kwance kan fuskata ya yi tunanin ko sakon shi ya karɓu. Nan da nan fuskarsa ta cika da wani irin annuri kaman an masa albishir da Aljanna. Bance masa komai ba har muka ƙarasa makarata. Da azamar sa ya buɗemin ƙofa yana min wani irin kallo da shi a dole kallon soyayya.

Wata irin dariya ce taso kubcemin nayi saurin riketa ita murmushi na wuce cikin makaranta. Kaman dai koda yaushe yauma suna zaune Garding na school ɗin suna hira kaman zata shige jikisan dauke kai nayi kaman ban gansu ba. Kai tsaye nayi dakin hutu saboda sai 9 muke da class. A nan na tarar da Ninah da alama ni take jira. Ina shiga kuwa na kwashe da dariya har cikina ya ƙulle. Ido Ninah ta zubamin cikin mamaki tana kallo na. Saida nayi mai isata hawaye nabin fuskata na bata labarin duk abinda ya faru. Itama cikin dariyar tace

"Tun kafin abin nashi ya yi yawa mu kawo plan ɗinmu ƙarshe Queen dan ya fara ban tausayi walahi"

Tabe baki nayi nace "wannan kuma shi ya sani, i don't care, like how dare him ma zaice yana so na? kuma ai ke ki ka kawo plan din sannan yanzu kice a fasa?"

Kafin ta ƙaramin magana mukaji muryar Zain yana "Babe" shigowa ya yi cikin dakin da muke na hade fuska tamau ina kallanshi. Yaƙe ya yi irin na kwararron ƴan iska yace " Haba Babe kinsan duk wata mace sai dai ta biyo bayanki ,am sorry please bani da kamarki, Hanan ke bina wlh kema kin
sani" Harara na watsa masa nace " ko? "

Hannu ya ɗaga sama irin deafeted ɗin nan yace " OK naji am sorry please bazan ƙaraba. Kin san ina sanki" saurin ɗaga masa hannu nayi "kaga karka damu kanka, already nayi moving on, I have a boyfriend " ɗan zaro ido ya yi waje kafin yace " are you serious? Waye shi? Ya kaini ni Zain? Tell me yana da kyau, yana da kuɗi, yana da class?...does he?"

Cikin inda -inda nace "Yes ya fika komai " Wata irin dariya ya saki yana ƙara matsowa gabana murya ƙasa- ƙasa so husky yace " no Babe babu wani namiji da zai kai Zain a gurin ki, am sorry mana Alright, you can't live without Zain, you love me too much. Koma waye breakup with him, am back now, bazan kuma ƙara barin side ɗinki ba I promise "

Irie-ire wannan kalaman nasa ke kashe min jikk na kasa musa masa. Na yarda ina sanshi so bama kaɗan ba(yarinta dai...). Ganin ya samu nasara ya yi wani mugun smirking yana cewa "Alright then ,zan ki raki anjima" ƙarasa maganan ya yi yana kashemin ido ya fice a ɗakin. Jan kafafuwana nayi da sukayi sanyi kalau na zauna kan kujera. Wato ba ƙaramin crushing nake akan shi ba,ya iya soyayya. Banga laifin mata dake mutuwa a kanshi ba.(Hmmm)

Ninah dake ɗakin tun ɗazu tayi sauri cewa "Queen karfa ki bari dadin bakinshi ya ruɗe ki, ki bari ki koya masa hankali sosai tukun. Kinsan gobe Bday dina nasan kuma dole zasuyi attend. Mu gyara deriban ki kuje dashi ya ganshi ya tabbatar da gaske ki ke. Yanzu yana ganin kaman wasa ki ke ne baza ki iya rayuwa ba dole sai dashi, amma idan ki ka je dashi ya ganshi zai san cewa da gaske ki ke next time ya kara cheating ɗinki zaki bar stupid ass ɗinshi"

Kai na jinjina nace "kuma haka ne Ninah , bari mu koma gida in kai shi shopping ".


***


Ido na zuba masa ina kallan shi zaune a gabana cikin ɗaya daga kujerun dake cikin garding ɗin mu. Bayan mun dawo ban shiga gidan ba nace yazo Garding za muyi magana.

Ajiyar zuciya na sauke na kira sunan shi " Ayaan " ƙwayar idansa daya kafeni da ita na zuba wa ido. Yana da manyan idanuwa da suke a lumshe sannan ƙwayar idan nashi brown ish colour ce dake da haske. Ita kanta ƙwayar idan nashi nada girma sosai.

"Nima ina sanka" Murmushi ne ya kubce masa da ya bani damar ganin double dimples ɗinshi da ban taba lura dasu ba dan yana da ƴar ƙiba da yasa yake da kumatu. "Amma idan ka yarda gobe zamuje birthday party na besty ɗina dan haka zamuje shopping anjima ka samu kayan da zaka sa"

Murmushi dake kan fuskarsa ne ya suɓuce yace " taya zan bari ki kaini shopping Hajiya ƙato da ni? Karki damu inshaAllahu baza kiji kunya ba zanje na shirya da kaina" cikin rashin gamsuwa nace " aa kaga wannan party ɗin na kece raini ne, ya zama dole komai nawa ya fita daban da sauran, ko kana so muje ana Boyfriend ɗin Queen is a garbage?" Ban lura da yanayinsa ba na cigaba da cewa "so kaga dole in har kana boyfriend ɗina ka fita daban da kowa ,I'm the queen of my school everything should be perfect "

Kanshi yana ƙasa har na gama maganan bai ɗago ba dan haka bansan wane yanayi ya shiga ba. Wajen minti biyu ya yi a duke kafin ya ɗago cikin murmushi yace "inshaAllahu Hajiya baza kiji kunya ba" murmushi nima nayi cikin jindaɗin fahimta ta da ya yi nace masa "yauwa" na miƙe dan shigewa gida.

Da ido ya bita cike da bege. Shi yasan cewa ita ɗin bata dace da rayuwar sa ba. Amma Allah ya jarrabeshi da son ta, so bana wasa ba. Sosai zuciyar sa ta sosu da maganan ta amma baiga laifin ta ba in har yana son soyayyar sa tayi karfi a zuciyarta dole zai zama perfect kaman yanda ta ambata.




E 9-10.


Toh washe gari saboda wannan gagarumin Bday da za muyi dagani har Ninah babu wanda yaje school. Tun 8 na safe ya sauke ni a gidansu dan shirya party . Sai da nayi ta ƙara jaddada masa da ya fita yanda ya kamata tunda yaƙi bari muje na zaɓa masa kayan da zaisa. Wajen 4 muka fara haramar zuwa party bayan mun shirya.

White gown Ninah tasa da akayi masu ado da pearls masu masifar kyau da tsada sai Bday crown data dora akai. Ni kuma na shirya cikin riga da sket black and white. Sosai mukayi kyau nida ita kafarmu yasha hills. Direban Ninah ne ya kaimu hall ɗin da ta kama musamman saboda party ɗin. San da muka isa guri ya cika da manyan yara da alama mu ƙadai ake jira. can na hango Zain cikin shiga ta kece raini ƴan mata sun kewaye shi cikinsu harda Hanan da tafi sauran zaƙewa. Ko wa ya
gayyato ta ma oho? wa yaga shiga sharo babu shuni.

Gaba ɗaya sai kallo ya dawo kanmu bayan mun fito daga motar. Ɗauke kaina nayi kaman ban gansu ba na fara neman inda zanga Ayaan. can jikin wata mota na hango shi a takure. kana ganin shi kasan dole ce ta kawo shi ko daga yanda yake ta ɓoyewa saboda gaba ɗaya gurin babu Age mate nashi duk yara ne. Ajiyar zuciya na sauke na nufe sa fuskata ɗauke da murmushi. Babu laifi ya yi dress yanda ya kamata dan ya yi kyau dai-dai gwargwado. Doguwar rigar shadda ce fara a jikinsa da take har ƙasa ya gyara gashin kansa dan da alama yasha wanki. Sai bakin takarmi mai yatsa a ƙafarsa.

"Me ka ke yi a tsaye a nan ?" nace ina ƙarasawa inda yake tsaye. Murmushi ya yi yana kallo na. A maimakon ya bani amsa sai ya faɗi wata maganan daban " kinyi kyau Neehal" ɗan far nayi da ido na nace "muje ciki mana an fara event ɗin" ƙofar gurin ya kalla kafin ya dawo da hankalin sa kai na yace " kiyi hakuri Neehal, bazan iya shiga ba. Bazan iya shiga cikin yara ba babu age mate ɗina gurinnan amma nazo saboda na saki farin ciki" jinda nayi yana neman rushemin plan yasa na ɓata fuska. Hakan da ya gani yace mu shiga. Jerawa mukayi dashi fuska ta ɗauke da murmushi. Bamu kai ga shiga ba Zain da maƙarraban sa suka sha gaban mu. Ɗauke kaina nayi ina kallan gefe kaman ban gansu ba. Kallan Ayaan yake tun daga sama har ƙasa yana wani smirking ya ce "is this the fake boyfriend?" Saurin juyuwa nayi ina kallanshi dan bansa ta yanda akayi yasan hakan ba.

Kallan da yaga ina masa ya saki murmushi ya ce "Na san komai Babe, but Babe wannan ai old geaser ne ,why not baki sami young fresh meat ba sai wannan da ya yi Baban ki gashi so fatty" Gaba ɗaya suka rushe da dariya harda masu tafawa. Kunya ce ta kamani nace

Nace "toh sai me dan yana da shekaru a haka nake sanshi"

Katseni ya yi saurin yi "No Babe am sorry mana, ki daina gayamin wannan maganan kar zuciyata ta buga. Kinsan ina sanki kaman yanda ki ke so na. I cant help mata suna so na. Just look at me mana" (Tab wannan Zain akwai ignorance gashi so arrogant ).

Ajiyar zuciya na sauke dan gaskiya ya faɗa dole mata su so shi. Ban juya na kalli Ayaan ba da nake jin idanshi a bayana kaman zasu huda bayan. Wuce wa nayi muka jera da Zain yana cigaba da kashe ni da kalamai da nake jin tamkar babu wata mace da ta kaini sa'ar saurayi. (Hmmm).

Gab da magriba na fito zan tafi saboda Innati da tayi tamin kashe din kar na kuskura na kai dare. Walahi gaba ɗaya na manta da Ayaan dan banyi tunanin yana nan ba muka fito da Zain zai sauke ni a gida. Can gefe na hango motar tawa. Nufar motar mukai ina cewa Zain basai ya kaini ba tunda direba na yazo. Shi ya buɗemin motar na shiga ya ɗan sunkuyo kafin ya rufe motar yana kallo na ya ce " Call me da zarar kin je gida OK?. I love you " murmushi nayi cikin jindaɗi a kunya ce nima nace "I love you too". Ido ya kashe min ya rufe motar. Toh da yake garin ya ɗan fara duhu kuma motar a ƙarƙashin bishiya ya faka ta yasa baiga Ayaan ɗin sosai ba dake zaune a mazaunin deriba ya kwantar da kansa jikin sitiyarin motar. Ajiyar zuciya na sauke na jindaɗin rashin ganin fuskar sa da baiyi dan ba ƙaramar kunya zanji ba idan ya gane Ayaan direba na ne.

Wajen sakan biyu nayi a zaune cikin motar kafin ya tashi daga kwancen da yake . Bai juyu ya kalleni ba yaja motar mukabar harabar gurin.
Ƙoƙarin buɗe motar nake bayan ya yi fakin a harabar motocin mu na gida,amma sai naji motar a garƙa me. Juyawa nayi ina kallan Ayaan da ya juyu yana kallo na idanuwanshi sunyi ja hawaye kwance a cikinsu. Ɓata fuska nayi nace "lafiya dai ka rufemin ƙofa?"

"Why?, me nayi miki? dama kince kina so na ne dan kiyi amfani dani?. Kince kina so na dan ki kaini inda za'a wulaƙanta ki cika burin ki? Me yasa ki ka yaudare ni da kalman so?"

Ido na zuba masa yana magana muryar sa har rawa take kaman mai shirin kuka . Sosai ya ban tausayi amma sai na dake na kara haɗe rai nace " And so what dan nayi wasa da feeling ɗinka?, Babu wani maganan cin amana anan tunda babu son da zanci amanar ka in the first place .Kai yanzu in banda rashin ta ido kana ganin na dace da macen da zaka ce kana so? Ko dan kaga na baka fuska ne?. Look at you, kaga Zain da kai dashi kun yi hanya ɗaya? So stop this nonsense wai kana so na. Ni bana sanka tun wuri idan wasa ka ke gwanda ka daina"

Wasu hawaye ne naga sun biyo kuncinsa ya ce " Mene aibuna? Saboda bani da kuɗi ko kyau? na ɗauka kyawawan halayya ma yana sawa a so mutum? Walahi ina sanki Neehal don Allah ki bani chance zan zama...

"Hey,hey kaga malam dakata" nai saurin ɗaga masa hannu ina cigaba da cewa " i dont care ko me zaka zama. Maganan ɗaya ce bana sanka .Dama nace ina sanka ne saboda wani dalili bawai dan haka maganan take ba. Sannan ma in banda rainin hankali irin naka taya ka ke tunanin zanyi soyayya da babban mutum while am just 16?.your just my driver so stay at your limit" mugun tsaki naja na fice daga motar.

Ina shiga gida kuwa ya yi daidai da kiran da Innati tayi min a waya. Jikinta na faɗa nace " wash na gaji walahi Innati"

Tace "toh ba dole ba , kun ɗorawa kai wata bida'ar banza da wofi. Wani Bdy party. Ai walahi badan Baban ki ba babu inda zakije gwand ki zauna a gida kiyi ta bitaar karatu da wannan shirmen banza da wofi" turo baki nayi idan da sabo yaci ace na saba da wannan faɗan na Innati.

"Tashi maza kije kiyi sallah magriba ta yi kizo kici abinci" Ban musa ba na tashi na yi hanyar ɗaki na.


***


Washegari ya kama weekend duk muna gida. Wajen karfe goma na fito sanye da ƴar duguwar riga mara nauyi iya gwiwa. Gashin kaina tufke a tsakiyar kaina. Dining nayi kai tsaye dan karyawa ina tafe ina hamma tare da ƴar miƙa. Turus na tsaya a tsakiyar falon ganin Abbu da nayi zaune kan kujera Ayaan a gefen shi. Banyi tsammanin ganin Abbu yanzu ba dan ya saba duk weekend baya fitowa sai wajen sha biyu na rana.

Duk kallo na sukayi. Muna haɗa ido da Ayaan na zuba masa harara a kaikaice ya yi saurin Sunkuyar da kai ƙasa.

"Zo nan Auta, je ki ɗauko hijabi kizo akwai magana mai muhimmanci daza muyi" Inji Abbu dake kallo na da ɗan murmushi a fuskarsa. Mugun kallo na kara jefan Ayaan dashi wanda kanshi ke kasa. Me hakan ke nufi? Wai ƙarata ya kai gurin Abbu ko me?. Kwafa nayi na juya na koma ɗaki dan ɗauko hijabi.

"Auta, Ayaan yazo min da magana mai muhimmanci yanzu da safe nan, na kuma tsaya na duba maganan tashi. Lallai idan har abun da ya faɗa gaske ne zanfi kowa farin ciki da kuma bakin ciki saboda abu biyu da maganan tashi ta ƙunsa".

Abbu ne ke magana bayan na dawo falon. Yanzu gaba ɗayan mu ne harda Innati. Cigaba da magana Abbu ya yi yana nuna Ayaan ya ce

" yazo min da muhimmin abu cewar yana sanki Auta" A rikice na dago ina kallan Abbu daya zuba min ido ya cigaba da cewa "sai dai yace shiɗin bai can-canci ki amsa soyayyar sa ba saboda shi ba kowa bane bashi da komai da zai baki dan haka yake so ya bar aiki, ni kuma nace babu inda zanshi dan shi yake da komai da zai baki Auta,Domin samun nagartattan mutum kaman shi zaiyi wuya. Dan haka na yanke hukunci da zarar kin yi Waec zan ɗaura muku aure dake da shi duk ɗaya ku ke a guri na. Inajin Ayaan kaman ɗan dana haifa nasan sai kin fi kowa jindaɗin kasance warshi abokin rayuwar ki. Bazaki fuskanci abinda nake nuna miki ba sai nan gaba Auta. Bazamu taɓa baki abinda zai cuce ki ba dagani har Innatin taki mun amince mun kuma yi na'am da wannan magana."

Wani irin ihu nasa da kururuwa cikin matsanancin kuka nace "walahi ni Abbu bana sanshi, ina da wanda nake so. Shima jira yake mu gama school ya fito muyi aure. Ni walahi bana sanshi"

Sosai nake kuka harda birgima a tsakar ɗakin. Daga Innati har Abbu babu wanda yace min komai sai ido da suka zuba min. Shi kuma munafikin sai ƙara ƙasa yake da kanshi. Wato duk kashedin da nayi masa baiji ba shi ne ya biyo ta wannan hanyar. " shi wanda ki ke son waye shi?" Inji Abbu. Ajiyar zuciya na sauke na mike zaune ina share hawaye nace

" Sunan shi Zain ɗan gidan commissioner ne. Yanzu yana ss3 ne amma yace da ya gama zai zo asan dashi".

Dan jim Abbu ya yi baice komai ba Innati ta karɓe zance da cewa " kaga wani shirmen banza da wofi. Shi ma ba ishashshen hankali ne dashi ba ashe tunda har yanzu bai gama sakandiri ba. In banda shirme ma shi yace miki zaiyi aure da zarar ya gama makaranta bai nemi na kanshi ba duk da yana ɗan commissioner? Shi namiji ne fa ke kuwa mace ce. Zancen da zarar kun gama makaranta za kuyi aure wannan ai tatsuniyar banza ce"

Kuka na kara rushewa dashi nace "Ni walahi bana san shi " Murya Ayaan mukaji cikin sanyi ya ce " Kayi hakuri Alhaji tunda tace bata sona na hakura "
Abbu ya yi saurin katse shi " aa Ayaan saboda rashin amincewarta bazai sa kabar aikin ka ba. Ni a matsayin ɗa na ɗauke ka. Dolen ta kuma ta amince ai ba yardar ta muke nema ba . Za kuma kaci gaba da zama anan har zuwa lokacin da wannan burin nawa zai cika"

Da mugun gudu na tashi nayi ɗakina cikin matsanancin kuka. Walahi ina ji ina gani bazan bari a cuce ni ba. Dole ma yaje ya janye wannan maganan tashi. Tsawon kwana biyu nan fushi nake da kowa ko falo bana iya fito wa daga Abbu har Innati babu wanda yabi ta kaina amma Innati sai tasa Abu mai aikin mu kullum ta kawo min abinci safe,rana,dare. Dana fara yiwa kaina huron yunwa naga cewar nice a wahalce ,idan an kawo abincin zagewa nake naci tunda ba shigowa suke inda nake ba bare su nuna damuwar rashin cin abincin da bana yi.

Wannan halin ko in kula dasu Abbu suke min ya samun mugun tsanan Ayaan. A karo na farko Abbu da Innati sunyi burus da damuwa ta saboda wani banza can. A kullum neman hanyar da zan ƙuntata masa nake ta yanda dan kanshi zai kaɗa ƴan ƙafafuwansa yabar gidan. Babu abinda ya dameni dan shi maraya ne ,ai can gidan marayun yana da gurin zama. Tsawon sati na ɗauka a gida banje makaranta ba, Ninah na kira na kullum tana ƙara bani shawara sai nake ganin kaman ta fini damuwa da san da yace yana min . Shi ma Zain muna waya dashi duk da ban gaya masa abinda yake faruwa ba nace masa dai bani da lafiya ne kawai.

E 11-12



Yau tashi nayi da niyar cika ƙudurina na shawarar da Ninah ta bani. Sai da na tabbatar Abbu ya fita aiki na fito sanye da riga da wando masu ɗan fadi ,sai ƴar hula dana kifa a kaina na saki gashin kaina ya zubo gadan baya na. Flat shoe ne a ƙafata daya yiwa ƙafar tawa kyau sosai saboda janlallen da nayi bai gama fita ba. Naci sa'a kuwa sanda na fito Innati bata falon da alama bata fito daga ɗaki ba. Cikin azama na shige kitchen na buɗe fridge na dauko lemo mai sanyin gaske nayi waje dashi.

Can kofar ɗakin mai gadi na hango shi zaune kaman yanda ya saba. Sai nake ganin kaman ya rame a ido sannan kallo ɗaya zaka masa ka fuskanci yana cikin damuwa. Hango ni da ya yi yai saurin miƙewa yana kallo na har wata ajiyar zuciya naga ya sauke. Murmushi ne kwance kan fuskata na boye lemon a bayana. Shima Murmushi ya saki yana tunanin ko na fara sakkowa ne. Ina ƙarasowa gabanshi kuwa ban jira komai ba na ɗaga lemon nan cikin jug na juye masashi akai. Yar ƙara ya saki kaman mai shirin shiɗewa saboda lemon ya yi masifar sanyi dan har ya fara ƙanƙara. Jikinshi ya ƙanƙame yana rawar ɗari ya zuba min idon shi da suka kaɗa sukayi ja. Kuguna na riƙe nace

"Ai baka ga komai ba, badai kai maye ba? Toh wlh sai ka gwammace baka taɓa taka ƙafar ka gidan nan ba. In banda ma tsabar rainin hankali dana yi maka kashedi shi ne kabi ta hannun iyaye na ka haɗani dasu?. Tunda na taso ko kallan banza Abbu na bai taba yimin ba amma saboda kai suna fishi dani saboda kai banza. Toh wlh kaje kace musu ka janye in ba haka sai ka gwammace ƙida da karatu. Ka kuma kaɗa kafafuwan ka kabar mana gida tunda baka iya cin arziƙi ba"

Mugun tsaki naja na zabga masa wata muguwar harara na juya zan koma ciki. Sai a lokacin na lura da Baba maigadi dake kallan Ayaan cike da tausayi. Shi ma hararar na zuba masa na wuce ina mita na barsu a tsaye yana faman rawar ɗari har haƙoransa sun fara haɗuwa. Ko kaɗan abun da nayi bai damen ba dan nasan ba iya faɗa zaiyi ba.

Bayan sallahn isha ina kwance a ɗaki muna waya da Ninah ina gayamata na aikata shawarar da ta bani. Dariya mukayi nida ita tana ƙara bani wata shawarar indai hakan baisa ya janye maganan shi ba. Kai na jinjina ina sauraran ta. Ban taɓa sanin cewa Ninah nada matuƙar wayo haka ba.(mugun hali dai). ƙofar ɗakina da aka buga ita ta janye min hankali na maida hankali kanta ina zaton Abuh ce ta kawo min abinci, amma saɓanin haka Abbu ne tsaye a bakin ƙofar yana kallo na. Cikin hanzari na tashi daga kwancen da nake ina kallan Abbu fuskata ɗauke da murmushi. Tunda na fara fushin nan suka yi burus dani.

"Kizo falo Auta ina san magana dake" yana faɗin haka ya juya ya fice a ɗakin. Bin ƙofar nayi da kallo tunani kala-kala a raina. Kai na jinjin na miƙe na fito daga ɗakina ban damu dana sa hijabi kan kaya barcin dake jikina ba. Shi kaɗai da Innati na tarar a falon dan nayi tunanin zan ga Ayaan tunda ya zama babban banza da bashi da aiki sai kai ƙara. Guri na samu kusa da Innati na zauna duk suka bini da kallo.

Gyaran murya Abbu ya yi yace " Abinda yasa na kiraki Auta ba komai bane sai dan in ce miki burinki ya cika. Ayaan ya bar aiki kaman yand ki ka so ya kuma janye maganan da ya yi nacewa yana sanki" Wani irin murmushi ne ya kubce min na farin ciki da har na manta a gaban su Abbu nake. Girgiza kai Abbu ya yi ya cigba da cewa " amma ina so ki sani Auta samun nagartaccen mutum kaman Ayaan abu ne mai matuƙar wahala,dan in tani ne wlh ko mutuwa za kiyi aure tsaƙanin ku babi fashi. Amma tunda har da kansa yace ya janye

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment